Jagoran Al'umma
Jagoran Al'umma
Jagoran Al'umma Da Bukatuwarsa
Tun da akwai Kur'ani da sunnar Annabi (s.a.w) wace bukata kuma ake da ita ga Imami kamar yadda Shi'a suke imani da hakan?
Mafi muhimmancin bahasin da sabuwar al'ummar musulmi ta fara samun kanta a cikinsa bayan wafatin Manzo (s.a.w) shi ne al'amarin halifanci da mas'alar mai maye gurbin Manzo (s.a.w), wasu daga sahabbai sun karbi halifancin Abubakar bisa dogaro da ra'ayin wasu manyan sahabbai duk da suna da masaniya a kan cewa Imam Ali (a.s) shi ne halifan Manzo (s.a.w) wanda ya ayyana, tun daga wannan zamanin ake kiran jama'ar farko da sunan Ahlussunna ko Sunna, jama'a ta biyu kuwa ake kiran ta da sunan Shi'a ko 'yan Shi'a.
Mafi girman abin da za a kula da shi a nan shi ne; sabani tsakanin Shi'a da Sunna bai tsaya a kan wanda zai maye gubin Manzo kawai ba, sai dai ya hada har da ma'anar Jagora da siffofinsa wanda wadannan mazhabobi guda biyu suka saba a kan ma'anarsu. Domin wannan lamarin ya bayyana a fili sosai dole ne mu yi bincike game da ma'anar imamanci ko halifanci da kuma bayyanar da sabanin da aka yi game da shi a sarari a wadannan mahangai guda biyu.
Imamanci a lugga yana nufin jagora, Imam shi ne wanda yake jagorantar jama'a domin nuna mata hanya a bisa wata manufa, amma a ma'anarta ta ilimi an yi mata fassara da ma'anoni daban-daban.
Sunna suna ganin halifanci yana nufin jagoranci a wannan Duniya da babu wata ayyanawa daga Ubangiji ga wanda zai jagoranci al'umma bayan Manzo (s.a.w) kamar dai yadda sauran al'ummu suke da bukatar jagora da suke zabensa da kansu, don haka suna ganin bayan Manzo (s.a.w) al'ummar musulmi su ne suke da zabin sanya wanda zai jagorance su tun da babu wata hanya da addini ya sanya domin zabar shugaba! Don haka suna ganin zabar halifan Annabi (s.a.w) zai iya yiwuwa ta hanyoyi daban-daban; kamar koma wa ra'ayoyin mafi yawancin mutane, ko manyan al'umma, ko ta hanyar wasiyyar halifan da ya gabata ga mai maye gurbinsa, ko kuma ta hayar juyin mulki da kwata da karfi.
Su kuma Shi'a da suke ganin jagoranci a matsayin ci gaban isar da sakon Allah (s.w.t) ne, kuma hujjar Allah ce kuma tsani tsakanin Allah da bayinsa, suna ganin cewa dole sanya halifa ya zama daga Allah ta hanyar wahayi ga Manzonsa (s.a.w) wanda kuma saboda girman halifanci da jagoranci ne a mahangar Shi'a, da cewa imamai ba kawai mai kula da al'umma ba ne ta musulmi, al'amarinsa ya hada har da bayanin umarnin Allah da fassara Kur'ani mai girma, da kuma jagorantar al'umma zuwa ga tafarkin rabauta.
Abin nufi shi ne; Jagora shi ne makomar al'umma a kan al'amuran Duniya da lahirarsu, ba kamar yadda Sunna suka dauka ba na cewa aikinsa shi ne tafiyar da al'amuran mutane na Duniya kawai.
Bayan yin bayanin wadannan nazarorin, ya dace mu bayar da amsar wannan tambayar mai cewa; tun da akwai Kur'ani da sunnar Annabi (s.a.w) wace bukata kuma ake da ita ga Imami kamar yadda Shi'a suke imani da hakan?
Game da wajabcin samuwar Imami akwai dalilai da dama da aka yi bayanin hakan, amma mu a nan zamu kawo wasu bayanai ne takaitatttu.
Dalilin da yake nuna wajabcin bukatuwa zuwa ga Annabi shi ne dalilin da yake tabbatar da bukatar Imami, domin musulunci shi ne addinin karshe kuma Muhammad (s.a.w) shi ne karshen annabawan Allah, saboda haka ya zama dole ne musulunci ya amsa dukkan bukatun dan Adam har zuwa alkiyama.
A wani bangaren kuma Kur'ani mai girma shi ne asasin dukkan hukunce-hukuncen Allah wanda bayaninsa yake kan wuyan Manzo (s.a.w), amma kuma a fili yake cewa Manzo (s.a.w) a matsayinsa na jagoran al'ummar musulmi ya yi bayanin bukatun da suka kebanta da zamaninsa ne, kuma dole ne a samu wani mai maye gurbinsa domin ya ci gaba da bayani ga al'umma, wanda yake masani da ilimin sakon domin ya yi bayanin abin da Manzo (s.a.w) ya bari na bayanai, da kuma amsa bukatun musulmin kowane zamani.
Haka nan jagorori su ne masu gadin abin da Manzo (s.a.w) ya zo da shi, masu kuma bayani da fassarar Kur'ani domin kada addinin Allah ya samu karkacewa daga tafarkinsa da hadafinsa a hannun makiya, ya kuma wanzu mai tsarki har zuwa ranar kiyama.
Kuma dole ne Imami ya zama mutum kamili, koyi ga al'umma a kowane bangaren rayuwa na dan Adam, domin ya zama misali ga mutum, wanda ta haka ne za a tarbiyyatar da dan Adam zuwa ga kamalarsa, kuma ya zama karkashin tarbiyyar mai tarbiyyar da yake da alaka da Allah madaukaki, kuma ya kare shi daga karkacewa da fadawa hannun shaidan na zahiri.
Idan mun duba abin da muka fada a sama ne zamu fahimci cewa bukatarmu zuwa ga Imami bukata ce ta rayuwa, kuma zamu kawo wasu daga ayyukan imamai (a.s);
1. Jagoranci da tafiyar da al'amuran al'umma (kafa hukuma).
2. Kare addinin da annabin rahama ya zo da shi daga Ubangiji daga karkacewa da kuma bayanin Kur'ani bayani ingantacce.
3. Tsarkake rai da shiryar da mutane zuwa ga kyawawan dabi'u.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation