Karamomin Mahadi
Karamomin Imam Mahadi (a.s)
An samu karamomi da yawa da suka faru a lokacin farkon rayuwar Imam Mahadi (a.s) kafin lokacin buyansa, wadannan karamomi an gafala ga barinsu amma zamu kawo misali daga gresu:
Fadar Abin Da Yake Zukata
Ahmad dan Ibrahim Naishaburi yana cewa: A lokacin da Amru dan Aufu ya so kashe ni, na tsorata kwarai da gaske, don haka sai na yi bankwana da iyalina na tafi gidan Imam Askari (a.s) domin in yi bankwana da shi. Da na shiga gidan Imam Hasan Askari (a.s) sai na ga wani yaro kamar wata yana mai haske da na dimauce saboda hasken fuskarsa, na kusance shi har na manta da abin da yake cikn raina na tsoron mutuwa. Sai yaron nan ya ce da ni: "Ya Ibrahim babu bukatar ka koka kan haka, da gaggawa Allah zai kare ka daga sharrinsa. Sai na sake dimauta, na ce da Imam Askari: Wannan wane yaro ne? Sai ya ce: Wannan dana ne kuma mai maye gurbina. Ibrahim ya ce: Sai na fito waje a lokacin ina mai dogara da nutsuwa da abin da na ji daga Imami na goma sha biyu (a.s), bayan dan lokaci ammina ya ba ni labarin albishir da cewa an kashe Amru Dan Auf .
Amsa Tambayoyi
Imam Mahadi (a.s) ya sha ba wa shi'arsa amsa mai gamsarwa game da mas'aloli daban-daban, yana mai sanya nutsuwa a zukatansu, ga wata ruwaya a takaice game da hakan:
Sa'adu dan Abdullah kummi daga manyan Shi'a tare da Ahmad dan Ishak kummi wakilin Imam Hasan Askari sun tafi wajansa da wasu tambayoyi domin neman amsarsu, yana fada game da wannan haduwar cewa: Na so in yi tambaya sai Imam Askari (a.s) ya nuna dansa (a.s) ya ce: Ka tambayi hasken idanuna (a.s), sai wani yaro ya kalle ni ya ce: "Ka tambayi duk abin da kake so"… sai na tambayi ma'anar (K.H.Y.A'.S.)? Sai yaron (a.s) ya ce da ni; wannan labarin gaibi ne da Allah ya ba wa bawansa Zakariyya (a.s) ya kuma sake bayar da shi ga Muhammad (s.a.w).
Lamarin shi ne: Annabi Zakariyya (a.s) ya roki Allah ya sanar da shi sunayen biyar daga bayinsa mafi daukaka (a.s) sai Allah ya aiko Jibril ya sanar da shi. Duk sa'adda Zakariyya ya ambaci sunan Muhammad (s.a.w) da Ali (a.s) da Fadima (a.s) da Hasan (a.s) sai duk matsalarsa ta kau bakin cikinsa ya dauke, amma da ya ambaci Imam Husain (a.s) sai makogwaronsa ya rike da bakin ciki. Wata rana sai ya ce: Mene ne ya sanya idan na ambaci sunan hudu na farko sai bakin ciki da damuwata su tafi, zuciyata ta nutsu, amma idan na ambaci Husain (a.s) sai hawaye su zubo mini, sautin kukana ya daukaka?! sai Ubangiji ya sanar da shi labarin Imam Husaini (a.s). ya ce da shi: (K.H.Y.A'.S.).
K- Tana nufin Karbala;
H- Tana nufin kashe shi da shi da zuriyarsa;
Y- Tanan nufin Yazid Wanda zai kashe Husain (a.s)
A'- Tana nufin kishirwarsa;
S- Tana nufin hakurinsa da juriyarsa da dagewarsa;
Sai na ce ya shugabana! Mene ne ya sanya aka hana mutane su zabi shugaba da kansu? Sai ya ce: Shugaba mai gyara ne ko mai barna? Sai na ce mai gyara ne. Sai ya ce: Saboda cewa ba wanda ya san abin da yake cikin zuciyar wani cewa yana tunanin gyara ne ko kuma barna, shin babu tsammanin mutane su zabi mai barna? Sai na ce: Haka ne. Sai ya ce: Wannan shi ne dalilin .
Karbar Kyauta Da Hakkoki
Daga cikin ayyukan Shi'a akwai bayar da kyauta da fitar da hakkin dukiyoyinsu na wajibi da aika su zuwa ga imamai (a.s), kuma da wadannan dukiyoyi ne imamai (a.s) suke kawar da matsaloli da kuma daukar nauyin bukatun al'umma. Ruwayoyi da dama sun zo game da kai irin wadannan dukiyoyi zuwa ga Imam Hasan Askari (a.s) da kuma yadda Imam Mahadi (a.s) yana karamin yaro ya ware dukiyar haram daga cikin irin wannan dukiyoyi kuma ya ayyana masu su, da kuma masu su na asali, kuma ya yi umarni da a mayar da ita ga ma'abotanta na asali. Wanda yake neman karin bayani sosai game da irin wadannan ruwayoyi ya koma zuwa ga littafin Kamaluddin, juz'i na 2, hadisi 21, shafi 190 .
Sallar Imam Ga Babansa
Imam Mahadi (a.s) ya kasance yana kebewa daga mutane kafin farawar boyuwarsa a karshen rayuwar babansa Imam Hasan Askari (a.s), bayan wafatin babansa shi ne ya yi mahaifin nasa sallar janaza. Akwai ruwaya mai tsayi game da wannan al'amari da Abul Adyan mai hidima ga Imam Hasan Askari (a.s) ya ruwaito, wanda yake son karin bayani ya koma zuwa ga littafin: Kamaluddin, hadisi 25, shafi 223 .
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation