Muassasar alhasanain (a.s)

Haihuwar Mahadi

5 Ra'ayoyi 01.8 / 5

Haihuwar Mahadi

Yanayin Haihuwarsa
Ruwayoyi masu yawa sun zo daga Manzon Allah game da cewa wani zai zo mai suna Mahadi daga zuriyarsa kuma zai tsayu da gina adalci, kuma shugabannin Abbasawa saboda wannan ruwaya ne suke son su kashe Imam Mahadi (a.s) tun farkon haihuwarsa. Saboda haka ne ma tun lokancin Imam Jawad (a.s) rayuwar imamai ta fara samun takurawa mai tsanani, kuma a lokacin Imam Hasan Askari (a.s) ta kai matuka ta yadda mafi karancin motsinsa da kai-kawon gidansa suka zama karkashin kulawar hukuma da ba abin da ya buya garesu. A fili yake cewa a irin wannan yanayi haihuwar hujjar karshe kuma alkawarin Allah dole ne ta zama a boye kuma nesa daga idanuwan wasu mutane. Don haka ne ma hatta makusanta Imam Hasan Askari ba su da masaniya game da haihuwar Imam Mahadi, kai har zuwa wasu awowi kafin haihuwarsa ba a ga alamar ciki ga mahaifiyarsa ba.
Hakima 'yar Imam Jawad (a.s) tana fada game da abin da ya faru a haihuwarsa (a.s) da cewa: Imam Hasan (a.s) ya aika a kirawo ni, ya ce: Ya ammata! Yau da dare ki kasance tare da mu! Domin yau daren rabin sha'aban ne, kuma Allah (s.w.t) a wannan daren ne zai bayyanar da hujjarsa na karshe a bayan kasa.
Sai na tambaya wace ce babarsa, sai ya ce da ni Narjis! Sai na ce: Amma ai ba ta da alamar ciki! Sai ya ce: wannan shi ne abin da nake gaya maka! Sai na shiga wajan Narjis, na yi sallama na zauna. Ina shiga sai ta gaggauto wajena ta kwabe mini takalmana ta ce da ni: Yaya kike ne tawa? Sai na ce: Ai ke ce tawa kuma ta cikin dangina! Amma ba ta yarda da abin da na fada ba, amma sai ta ce da ni, ya ammata mene ne? Sai na ce: ya 'yata, yau da dare Ubangiji madaukaki zai ba ki da wanda zai zama jagoran Duniya da lahira gaba daya, sai ta ji kunya.
Hakima tana cewa: Bayan sallar isha sai na ci, na sha ruwa, na kishingida kan shimfidata, a tsakiyar dare na tashi domin yin sallar dare, na idar da sallar, a wannan lokaci Narjis tana bacci ba tare da wani abu ya same ta ba, bayan na gama wuridin bayan salla sai na yi bacci. Sannan sai firgigi na tashi, amma har wannan lokaci tana bacci, sannan sai ta tashi ta yi sallar dare ta koma bacci.
Hakima ta kara da cewa: Sai na fito waje ina kallon sama ko zan ga alfijir ya keto. Sai na ga alfijir din farko amma Narjis har wannan lokaci tana cikin bacci, sai na fada kokwanto! Bagatatan sai na ji kira daga wajan da Imam Hasan Askari yake yana cewa: Ke amma kada ki gaggauta, al'amarin haihuwa ya kusata. Sai na zauna ina karanta surar sajadati da kuma yasin, sai Narjis ta tashi da rawar jiki. Sai na gaggauta zuwa wajanta na ce: Ismul-Lahi alaiki. [Sunan Allah ya tabbata a gareki] shin kina jin wani abu ne?. Ta ce haka ne ya ammata. Sai na ce ki samu nutsuwa waje daya ki kuma daidaita zuciyarki, domin wannan shi ne abin nan da na gaya miki. A wannan lokaci sai wani rauni ya same ni da ni da Narjis. Sai na ji kira daga shugabana [jaririn da aka haifa] ya zo da kansa, na dauke lullubin da yake jikinsa, sai na same shi a cikin sujada! Na kuma dauke shi, na kuma same shi da cikakken tsarki! A wannan lokaci ne Imam Askari (a.s) ya kira ni: Ya amma kawo mini dana! Sai na kai masa shi, ya dora shi a kafadarsa ya ce: Ya dana ka yi magana, sai ya bude bakinsa ya ce: Ash'hadu an la'ilaha illal-Lah wahdahu la sharika lah, wa ash'hadu anna Muhammadar rasulullah. Sai kuma ya nemi tsira da amincin Allah ga Imam Ali (a.s) da imamai biyu -Hasan da Husain- (a.s) har ya kai zuwa ga sunan babansa (a.s). Sai Imam Askari ya ce: Ya amma mayar da shi wajan babarsa domin ya nema mata tsira da amincin Allah.
Hakima ta ce: Wani mutum a wannan rana ya zo wajan Imam Askari ya yi masa sallama, na kawar da labule domin in ga shugabana (Imam Mahadi (a.s) amma sai ban gan shi ba, sai na tambayi babansa (a.s), ina fansarka da raina yaya ban ga shugabana ba? Sai ya ba ni amsa da cewa: Na bayar da ajiyarsa wajan wanda babar Musa ta bayar da ajiyar Musa (a.s) wajansa.
Hakima ta ce: Ranar da rana ta bakwai ta zagayo, sai na yi sallama na zauna. Amma Imam ya ce. Kawo mini dana, sai na kawo shugabana. Imam (a.s) ya ce: Ya dana yi magana! Sai jaririn ya bude bakinsa bayan ya yi kalmar shahada da kadaita Allah da mika gaisuwa da aminci zuwa ga Manzon Allah (s.a.w) da kakannisnsa ma'asumai (a.s) sai ya karanta wadannan ayoyi na Kur'ani mai girma: "Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Muna son mu yi baiwa ga wadanda aka raunatar {zalunta da kuntatawa} a bayan kasa mu sanya su shugabanni mu kuma sanya su masu mayewa {gajewa}, kuma mu ba su iko a bayan kasa, mu nuna wa Fir'auna da Hamana da rundunarsu abin da suka kasance suna gudunsa" .
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation

 

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)