Hikimar Boyuwa
Hikimar Boyuwa
Ma'anar Boyuwar Jagora
Boyuwa a nan yana nufin bacewa daga ganin mutane ba rashin halarta ba, don haka ne a wannan bangaren zamu yi magana game da boyuwar Imam Mahadi (a.s) daga ganin mutane alhalin yana cikinsu, yana kuma rayuwa tare da su, wannan al'amari ne da ya zo a ruwayoyin imamai (a.s) Imam Ali (a.s) yana cewa: Na rantse da Ubangijin Ali, yana tsakanin mutane, yana zuwa gidajensu, yana kaikawo a gabashi da yammacin Duniya, yana jin maganar mutane, yana yi musu sallama, yana ganinsu ba sa ganinsa har sai alkawarin Allah ya zo .
Na'ibinsa na biyu yana cewa: Imam Mahadi (a.s) yana halartar aikin hajji, yana ganin mutane, yana kuma saninsu, amma su suna ganinsa amma ba sa saninsa . Wannan ya nuna yana da buya kala biyu kenan, wani lokaci ba a ganisa, wani lokaci kuwa ana ganinsa amma ba a gane shi.
Akwai Boyuwa A Farkon Duniya
Imam Mahadi (a.s) ba shi ne farkon wanda ya boyu ba a cikin bayin Allah (s.w.t), da yawa daga annabawan Allah sun boyu, wannan kuwa ba domin komai ba sai maslaha ta Ubangiji da take cikin hakan, ba maslaha ce ta su ba ko ta iyalansu, saboda haka ne buya ta zama daya daga sunnonin Allah da ta faru a lokacin annabawa kama Idris, Salih, Ibrahim, Ysufu, Musa, Shu'aibu, Iliyas, Sulaiman, Daniyal, da Isa (a.s), kowanne daga cikinsu a bisa sharudda na musamman ya boyu wasu shekaru . Don haka ne ruwayoyi da suke nuna buyan Imam Mahadi (a.s) suna nuna shi ne a matsayin daya da sunnonin Allah madaukaki.
Iama Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: "Hakika Imam Mahadi (a.s) yana da buya da zai tsawaita, sai mai ruwaya ya ce: menen dalilin wannan buyan ya dan Manzon Allah (s.a.w) ? sai ya ce: Ubangiji yana son ya dora shi bisa sunnar annabawa a boyansu" .
Manzon rahama yana cewa: Mahadi yana daga 'ya'yana ne… yana da boyuwa da a cikinta za a samu dimuwa da zata mamaye mutane har sai mutane sun kauce daga addininsu, sai ya zo a wannan zamanin kamar shihabun sakib "Tauraro mai walkiyar haske" sai ya cika Duniya da adalci da daidaito kamar yadda aka cika ta da zalunci da danniya .
Hikimar Boyuwar Imam Mahadi (a.s)
Mene ne dalilin boyuwar Imami kuma hujjar Allah (s.w.t) a kan talikai daga mutane? Mene ne ya sanya mutane suka haramtu daga albarkarsa?
An yi maganganu masu yawa game da wannan al'amari kuma ruwayoyi masu yawa sun zo game da hakan, amma kafin mu bayar da amsar wannan tambaya ta sama dole ne mu yi nuni da wasu bayanai muhimmai; Mu mun yi imani cewa Ubangiji masani ne wanda ba ya wani aiki babba ne ko karami sai bisa hikima da maslaha, ko mun san wannan maslahar ko ba mu sani ba. Kuma dukkan al'amuran Duniya ana tafiyar da su ne ta hannun Ubangiji madaukaki, kuma daya daga mafi muhimmancinsu shi ne al'amarin fakuwar da buyan Imam Mahadi (a.s). Don haka buyansa ma ya kasance ne bisa hikima da maslaha koda kuwa mu ba mu fahimci hikimar hakan ba.
Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Ba makawa Imam Mahadi (a.s) yana da boyuwa guda biyu wacce dukkan ma'abota bata zasu fada cikin yin kokwantonsa. Sai mai ruwaya ya tambayi dalilin boyuwar, sai Imam (a.s) ya ce:
Boyuwar ta kasance ne saboda wani al'amari da ba mu da izinin gaya muku shi… ita sirri ce daga asiran Allah (s.w.t) tunda mun san cewa Allah mai hikima ne mun yarda cewa dukkan ayyukansa suna kan hikima ne, koda kuwa hikimar hakan ta boyu garemu .
Kodayake duk da cewa ayyukan Allah bisa hikima suke kuma wani lokaci wannan hikima tana boyuwa garemu, amma muna neman sirrin hakan ne domin mu san hikimar wasu al'amuran domin ya ba mu nutsuwar zuciya sosai. Don haka ne zamu yi bincike game da wasu hikimomi da alamomi na boyuwar Imam Mahadi (a.s) da kuma nuni da ruwayoyi da suke magana game da hakan:
Ladabtar Da Mutane
Idan wata al'umma ta kasance ba ta san matsayi da kima na wani annabi ko imami ba, kuma ba su yi abin da ya kamata ba game da shi, suka ma ki biyayya ga umarninsa, to ya kamata a raba su da shi domin masu zuwa nan gaba su amfana daga samuwarsa.
Ganin albarkar samuwarsa zai sanya maslahar boyuwarsa ga al'umma duk da cewa ko su ba su gane hakan ba, ko kuma ba su san hakan ba.An rawaito daga Imam Muhammad Bakir (a.s) yace: Idan Allah ba shi da wani mai gadonmu ko halifanmu a cikin al'umma sai ya dauke mu daga cikinta .
'Yanci Da Kubuta Daga Bai'ar Wasu
Duk masu son kawo wani sauyi a Duniya tilas ne su bi wasu sharudda da kulla wasu alkawura da yarjejeniya a farkon fara gwagwarmayarsu, amma Imam Mahadi (a.s) ba zai kai ga kulla wata yarjejeniya da wani karfi na zalunci ba game da kafa hukumar adalci ta Duniya mai karfi da girma. Kamar yadda ya zo a ruwayoyi shi za a umarce ne da fito-na-fito ne a fili da dukkan azzalumai ne. Don haka ne dole sharuddan bayyanarsa su kammala kafin ya bayyana domin kada a tilasta shi kulla sharudda da wani azzalumi.
Wata ruwaya daga Imam Ridha (a.s) tana cewa: Domin a wannan lokacin da zai motsa da takobinsa, ya kasance babu wani da ya yi wa bai'a .
Jarraba Mutane
Yana daga cikin sunnar Allah (s.w.t) ya jarraba bayinsa ta hanyoyi daban-daban domin su kai ga tafarki madaidaici. Kodayake sakamakon jarrabawa a wajen Allah sananne ne, amma bayi ne nasa yake jarrabawa domin su kai ga kamalar samuwarsu. Imam Musa Kazim (a.s) yana cewa: yayin da dana na biyar zai boyu ku kula sosai game da addininku kada wani ya zo ya fitar da ku daga cikinsa… wannan boyuwar tasa jarrabawa ce da Allah yake jarraba bayinsa da ita .
Kariya Ga Imami (a.s)
Kare rayuwa da rayuka yana daga cikin dalilan boyuwar annabawa daga cikin mutanensu domin su samu damar isar da sakon Allah a lokutan da dama ta samu, su kan boyu da izinin Allah a wasu lokuta kamar yadda Manzo (s.a.w) ya buya a kogon kuma wannan duk da umarnin Allah ne. Kuma haka lamarin yake game da Imam Mahadi ma, kuma ruwayoyi masu yawa sun zo suna bayanin haka:
Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Kafin Imam Mahadi (a.s) ya tashi da motsinsa zai faku daga ganin idanuwa wani lokaci mai tsayi. Sai aka tambaye shi dalilin haka. Sai ya ce: Yana tsoron ransa ne .
Duk da cewa shahada wani buri ne na bayin Allah a wajen isar da sakon Allah da kawo gyara ga al'umma da kuma addinin Allah. Amma idan kashewar ta kasance tana nufin rashin kaiwa ga hadafin da ake son kaiwa gareshi ne to tsoron kisa al'amari ne da ake hankaltar sa.
Kashe Imami (a.s) na goma sha biyu wanda yake shi ne karshen ajiyar Allah a bayan kasa gaba daya, kamar rushe ka'aba ne gaba daya, da rashin kaiwa ga samuwar cikar burin dukkan annabawa da waliyyan Allah (a.s), da kuma rashin tabbatar alkawarin Allah (s.w.t) na kafa hukumar adalcin Allah a karshen Duniya ne.
A cikin wasu ruwayoyin an ambaci wasu dalilan boyuwarsa wadanda ba zamu iya kawo su ba saboda karancin lokaci, amma dai abin sani shi ne, boyuwar tana daga cikin sirrorin Ubangiji madaukaki, kuma hikimar haka zata bayyana ne bayan bayyanarsa (a.s) kuma wadannan abubuwan da aka fada abubuwa ne da suka sabbaba boyuwar tasa (a.s).
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation