Muassasar alhasanain (a.s)

Gajerar Boyuwa

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Gajerar Boyuwa


Boyuwa Mai Gajeren Zango
Bayan shahadar Imam Hasan Askari Imami na goma sha daya (a.s) a shekarar hijira 260, daga wannan lokaci ne karamar boyuwa ta fara har zuwa shekara ta 329 kusa shekaru 70 kenan. Kuma mafi muhimmancin lamarin wannan lokaci shi ne alakar mutane da Imam Mahadi (a.s) tana kasancewa ne ta hanyar wakilai kuma ta hanyarsu ne ake aika masa da tambaya ana kuma karbar amsa. Kuma wani lokaci har da sa hannunsa ake samu ta hanyar su . Wadannan wakilai na musamman dukkaninsu suna daga cikin malaman Shi'a wadanda Imam Mahadi (a.s) ya zaba daga cikin malamai domin su kasance 'yan sakonsa wadanda su hudu ne kamar haka:
1- Usman dan Sa'id Umari; wakilin Imam Mahadi daga farkon boyuwa kuma ya mutu a shekarar 265, kuma shi ne wakilin Imam Hadi da Imam Askari (a.s).
2- Muhammad dan Usman Umari; dan wakili na farko wanda ya samu matsayin wakilcin Imam Mahadi (a.s) bayan mutuwar dansa, shi kuma ya mutu a shekarar 305 hijira.
3- Husaini dan Ruhu Nobkhati ya mutu a shekarar 326, bayan ya yi shekara 21 yana wakilcin Imam Mahadi (a.s).
4- Ali dan Muhammad Samuri; ya mutu a shekarar 329, kuma da mutuwarsa ne karamar boyuwa lokacinta ya kare gaba daya, kuma aka shiga dogowar boyuwa. Wadannan wakilai na Imam Hasan Askari da Imam Mahadi (a.s) su ne suke zabarsu da hannunsu, aka kuma sanar da su ga mutane.
Sheikh Dusi yana rawaitowa a littafinsa na "Al'gaiba" cewa: wata rana mutane arba'in daga shi'a sun kasance tare da Usman dan Sa'id amari wakilin Imam Mahadi na farko a wajen Imam Askari (a.s) sai Imam (a.s) ya nuna musu dansa da yake gabansa ya ce: Bayana wannan yaron shi ne imaminku. Ku yi biyayya gareshi… ku sani cewa daga yau ba zaku sake ganinsa ba har sai shekarunsa sun cika. A boyuwarsa duk abin da Usman ya gaya muku ku yarda da shi ku karbi umarni daga gareshi, domin shi ne wakilin imaminku, kuma dukkan ayyuka suna hannunsa .
A wata ruwayar ya zo cewa; Imam Hasan Askari da Imam Mahadi (a.s) sun yi magana suna masu fada karara game da wakilcin Muhammad dan Usman wakili na biyu na Imam Mahadi (a.s).
Sheikh Dusi yana cewa: Usman dan Sa'id yana tattara dukiyoyin shi'ar Yaman da umarnin Imam Hasan Askari (a.s) yana kawowa, wasu mutanen sun san abin da yake gudana sai suka zo suka gaya wa Imam (a.s), sai ya ce: Na rantse da Allah! Usman yana daga mafifitan Shi'a'rmu, kuma da wannan aikin da yake yi yana dada bayyana garemu a fili (cewa shi mutumin kirki ne).
Imam Hasan Askari (a.s) yana cewa: Haka ne; ku shaida Usman dan Sa'id wakilina ne, kuma dansa Muhammad wakilin dana ne . Wannan ya kasance a lokacin kafin boyuwar Imam Mahadi (a.s) ne, kuma a tsawon wannan boyuwar tasa karama kowane daga wakilansa kafin mutuwarsa aka umarce shi da ayyana wani wakilin da umarnin Imam Mahadi (a.s).
Wadannan mutanen sun cancanci wakilci ne saboda siffofi na gare da suke da su, sun ada amana da tsarkaka da adalci a magana da aiki, da rike sirri, da boye sirrin Ahlul Baiti (a.s). Kuma su mutane ne da ake dogara da su da kuma yada mazhabar Ahlul Baiti (a.s).
Wasu daga cikinsu tun suna da shekaru 11 suke tare da tarbiyyantarwar imamai (a.s), kuma iliminsu yana tare da imani mai karfi a tare da su. Sunansu na gari ya yadu a harsunan mutane, tare da hakuri da juriya da dauke duk wata matsala da nauyi da wahalhalu da ya cakuda da samuwarsu, ga kuma cikakkiyar biyayyarsu ga imaminsu (a.s). Hada da dukkan wadannan siffofi na gari kyawawa kuma suna da karfin tafiyar da al'amuran Shi'a da cikakkiyar fahimta da kamala da sanin zamaninsu da amfana daga al'amura, da kuma shiryar da al'ummar Shi'a zuwa ga tafarki na Ubangiji na shiriya kuma suka wuce karamar boyuwa da aminci.
Binciken karamar boyuwa da kuma rawar da muhimmiyar gudummuwar da wakilai hudu suka bayar wajan samar da alaka tsakanin Imam Mahadi (a.s) da al'umma yana nuna wani bangare mai muhimmanci na rayuwar Imam Mahadi (a.s). Kuma samuwar wannan alaka da kuma samun damar ganin Imam (a.s) ga wasu jama'a na Shi'arsa a tsawon wannan boyuwa yana da tasiri mai yawa wajen tabbatar da tabbacin haihuwa da samuwar Imam Mahadi (a.s) Imam na goma sha biyu kuma karshen hujjar Allah a Duniya. Wannan ci gaba mai girma da aka samu ya faru ne a daidai lokacin da makiya suke kokarin ganin sanya shakku game da samuwar haihuwar dan Imam Hasan Askari (a.s), hada da cewa lokacin ya yi daidai da faruwar babbar boyuwa wanda a cikinta mutane ba su da wata alaka ta saduwa da haduwa da imaminsu ta hannun wasu mutane ayyanannu, amma da samuwar wannan nutsuwa ta zuciya a wannan lokuta da kuma amfanuwa daga albarkar samuwarsa sun share fagen boyuwarsa babba.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation

 

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)