Fa'idar Boyuwa-2
Fa'idar Boyuwa-2
Tabbatar Mazhaba
Duk wata al'umma tana da bukatar samun jagora masani domin kiyaye samuwarta domin ta kai zuwa ga hadafinta datake buri, domin al'aummar ta kasance mai motsawa karkashin jagorancinsa. Samun jagora wani wani kariya ce mai karfi domin mutane su samu tsari mai karfi wanda yake bayar da kariya ga al'amarinta da ya gabata, kuma karfafa al'amarin da zai zo nan gaba.
Shugaba rayayye kuma mai aiki koda kuwa baya cikinjama'arsa amma ba zai ta ba takatitawa ba wajen nuna mata hanyar da zata bi, kuma zai tsawata mata ta hanyoyi da dama daga kauce wa hanya.
Duk da Imam Mahadi (a.s) ya kasance a boyuwa amma samuwarsa wani babban lamari ne wajen kare mazhabin Shi'a; yana maganin mummunan makarkashiyar makiya ta hanyoyi da dama, kuma yana kare tunanin shi'arsa daga karkacewa, kuma yayin da makiya suke yaudarar ma'abota addinai da akidu ta hanya daban-daban to shi yana kangiya daga kaidinsa ta hannun malmai masu shiryarwa da gyara da yake zaba.
Domin misali bari mu kawo kulawar Imam Mahadi (a.s) ga shi'arsa na Bahrain, daga bakin Allama Majalisi:
Wata rana wani shugaban rundunar mayaka wanda yake makiyin Ahlul Baiti (a.s) yana jagorancin hukuma, wanda yake wazirinsa a gaba da Ahlul Baiti (a.s) kamar ba shi da na biyu, wata rana ya shiga wajen komanda ya taho da wani ruman a jikinsa an rubuta "La'ilaha illal-Lah, muhammadur rasulul-Lah, Abubakar da Umar da Usman da Ali halifofin Manzon Allah". Sai ya nuna wa komanda, shi kuma da ya ga haka sai ya yi murna, ya ce da waziri: Wannan ya nuna lalacewar shi'anci da karyarsa; Yaya kake ganin waziri game da Shi'a'wan Baharain?
Waziri ya ce: Dole ne mu kawo su mu nuna musu wannan, idan sun karba sun fita daga mazhabarsu to shi kenan, amma idan ba haka ba, to sai mu ba su zabi uku, ko su kawo dalili, ko kuma su biya jiziya, ko mu yake su, matansu su koma ribatattu, dukiyoyinsu su koma ganima.
Komanda ya karbi wannan ra'ayi kuma ya kirawo Shi'a, sannan ya nuna musu Ruman ya ce: idan ba ku da wani dalili to zan ribace matanku da dukiyoyinku, ko kuma ku biya jiziya.
Malaman Shi'a suka rasa yadda zasu yi, amma bayan tattauanawa sai suka zabi mutane goma daga garuwansu, sannan kuma suka zabi uku daga cikinsu, a dare na farko suka aika mutum na farko domin ya je sahara bakin ruwa ya yi tawassuli da Imam Mahadi (a.s) amma bai samu wata amsa ba, a rana ta biyu suka aika mutum na biyu shi ma ya dawo babu amsa, amma a rana ta uku da dare suka tura wani mutum mai suna Muhammad dan Isa ya tafi sahara ya yi kuka ya yi addu'a ya nemi taimako daga Imam Mahadi (a.s) sai ya ji kira da sauti mai cewa: ya kai Muhammad dan Isa yaya na gan ka a wannan halin? Yaya ka fito a sahara?
Sai Muhammad dan Isa ya nemi ya nuna masa shi waye.
Sai ya ce: Ni ne ma'abocin wannan zamani, ka fadi bukatarka!
Sai Muhammad dan Isa ya ce: Idan kai ne Imam Mahadi (a.s) ka san halina kuma ba ka bukatar wani labari daga gareni!
Sai ya ce: ka yi gaskiya, yanzu saboda wannan musibar ne ka zo nan?
Ya ce: Na'am, ka san abin da ya same mu, kuma kai ne imaminmu mafakarmu.
Sai Imam (a.s) ya ce: ya Muhammad dan Isa! A gidan wannan wazirin akwai bishiyar ruman, yayin da ruman ya fara sabonsa, sai ya kwaba tabo da wannan shakalin ya raba shi biyu, kuma a tsakiyarsa sai ya rubuta wadannan kalmomin, ya kuma sanya wannan shakalin a cikin ruman da yake dan karami sabon farawa sannan ya rufe, tun da ruman ya girma ne a cikin wannan shakalin sai wannan zanen ya fito masa! Gobe ka je wajen wannan komanda ka gaya masa ni zan ba ka amsa ta a gidan waziri ne. Idan ka shiga gidan waziri sai ka shiga daki kaza akwai wani buhu fari da wannan shakalin na tabo yake cikinsa, kuma ka nuna wa komanda wannan.
Alama ta biyu wacce take ita ma karamarmu ce, ka gaya wa shugaban rundunar mayakan ya raba wannan ruman din gida biyu, zai ga ba komai a ciki sai tsutsa da toka!
Muhammad dan Isa ya yi farin ciki da wannan magana, ya koma ya gaya wa Shi'a. A rana mai zuwa suka zo wajen komanda kuma dukkan abin da Imam (a.s) ya gaya masa sai da ya tabbatar da su. Da komanda ya ga wannan karamomi sai ya zama Shi'a kuma ya bayar da umarni aka sare kan wannan waziri mai yaudara .
Gina Kai
Kur'ani mai girma yana cewa: "Ku yi aiki, da sannu Allah da Manzonsa da muminai zasu ga ayyukanku" .
A ruwayoyi masu yawa ya zo cewa: Abin da ake nufi da muminai a nan su ne imamai ma'asumai . Don haka ne ayyukan mutane suke a gaban Jagoran zamani (a.s) kuma shi yana ganin wadannan ayyuka, wannan kuwa wani nau'i ne na tarbiyya da yake iya ba wa Shi'a damar gyara ayyukansu gaban Allah da kuma imaminsu, domin su gyara ayyukansu kuma su kawar da dukkan wani sabo. Don haka ne ma duk sadda mutum ya fuskanci makomarsa to ya fi tsarkaka kuma zuciyarsa ta fi tsakarka da samun haske, wannan kuwa abu ne wanda yake afili kuma bayyananne.
Madogarar Ilimi Da Tunani
Jagorori ma'asumai su ne masu ilmantarwa da bayar da tabbiyaya ga al'umma kuka mutane suna sha daga dadadan ruwansu a lokacin boyuwar Imam Mahadi (a.s) duk da cewa ba ma iya samun sa kai tsaye mu amfana daga garesu amma dai shi ne ma'adinin ilimin Allah wanda dukkan matsalolin ilmin da tunani na Shi'a shi ne yake bude su ya warware. Kuma a lokacin boyuwarsa karama an samu tambayoyi masu yawa daga malamai da mutane da ya amsa su ta hanyar tambyoyi da sa hannunsa da suka shahara.
A amsar wasikar Ishak dan Ya'akub Imam Mahadi (a.s) yana cewa: Ubangiji ya shiryar da kai kuma ya tabbatare dakai, amma masu musunmu da ka tambaya daga 'ya'yan amminmu ka sani cewa Allah ba shi da alakar jini da wani, duk wanda ya yi musuna, ba ni, ba shi, kuma karshensa kamar na dan Annabi Nuhu (a.s) ne… amma dukiyarka matukar ba ka tsarkake ta ba, to ba zamu karba ba… Amma dukiyar da ka aiko mana daga irin wannan mai tsarki ce kuma zamu karba…
Duk wanda ya ci dukiyarmu ya dauke ta a matsayin halal to ya ci wuta ne…, amma yadda za a amfana daga gareni kamar yadda ake amfana daga ranane da take boye bayan gajimare, kuma ni aminci ne ga mutanen Duniya kamar yadda taurari suke aminci ga mutanen sama. Kuma duk abin da ba shi da amfani gareku kada ku tambaya game da shi, kuma kada ku wahalar da kanku wajen sanin abin da ba a nema daga gareku ba, kuma ku yi addu'a matuka domin neman bayyanata, wannan shi ne farin cikinku, aminci ya tabbata gareka ya Ishak dan Ya'akub, kuma aminci ya tabbata ga dukkan wanda ya bi shiriya.
Bayan boyuwa karama saudayawa malaman Shi'a sun yi tambaya game da matsalaoli masu yawa kuma sun samu amsa daga Imam (a.s).
Daya daga daliban Mukaddis Ardabili wato; Mir Allama yana cewa: Wata rana rabin da re a Najaf a haramin Imam Ali (a.s) na ga wani mutum yana tafiya zuwa harami sai na tafi wajensa, koda na yi kusa da shi sai na ga wani tsoho ne da wani malami mai suna Ahmad Mukaddis Ardabili, sai na boye kaina. Ya tafi kusa da haram sai kofa da take kulle, nan take ta bude masa sai ya shiga, sai bayan wani lokaci ya fita ya tafi Kufa. Sai na bi shi a baya ta yadda ba zai ganni ba, kuma ya shiga masallacin Kufa kuma sai ya kusanci wurin da a nan ne aka sari Imam Ali (a.s) sai bayan wani lokaci ya fita daga wurin sannan sai ya tafi Najaf kuma ni duk a hakan ina ta binsa, har ya kai masallacin Hanane, sai tari ya kama ni, da ya ji tarina sai ya juyo ya kalle ni ya ce: Ko mir Allama ne? sai na ce: na'am. Sai ya ce; me kake yi a nan? Sai na ce: ai tun lokacin da ka shiga haramin Imam Ali (a.s) ina bin ka a baya, don Allah ina hada ka da girman wannan kabari sai ka gaya mini me ya faru tun da farko na daga sirrin wannan al'amari da ya faru!
Sai ya ce: da sharadin matukar ina raye ba zaka fada wa kowa ba! Sai na dauki alkawari, sai ya ce: wani lokacin mas'aloli sukan rikice mana ta yadda ba yadda zamu samu warwara sai ta hannun tawassuli da Imam Ali (a.s), a yau ma wata mas'ala ce nake tunanin warware ta don haka sai na ga bari in tafi wajansa in yi tambaya. Amma da na kusanci harami sai na ga kofa ta bude kamar yadda ka gani, sai na shiga na yi kuka domin in samu amsa, sai na ji sauti daga kabarin ya ce: ka tafi masallacin Kufa domin Imam Mahadi (a.s) yana can, kuma shi ne imamin zamaninka, don haka ka tambaye shi. Sai na tafi masallacin Kufa na tambaye shi kuma na samu amsa, yanzu haka zan tafi gidana ne.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation