Haihuwar Manzon Rahama Manzo Munhammad (A.S)
HAIHUWAR MANZON ALLAH MUHAMMAD
Manzo Muhammad Al-Habib Dan Abdullahi
Sunansa da Nasabarsa: Muhammad dan Abdullahi dan Abdul mudallibi dan Hashimi dan Abdu manafi dan Kusayyi dan Kilabi, nasabarsa madaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim (a.s).
Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu 'yar wahabi Dan Abdu Manafi Dan Zuhrata Dan Kilabi.
Alkunyarsa: Abul Qasim, Abu Ibrahim.
Laqabinsa: Almusxafa yana da sunaye da suka zo a cikin Kur'ani mai girma kamar, Khataman nabiyyin, da Al'ummi da Almuzzammil da Almuddassir da Annazir da Almubin da Alkarim da Annur da Anni'ima da Arrahma da Al'abdu da Arra'uf da Arrahim da Asshahid da Almubasshir da Annazir da Ad'da'i da sauransu.
Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi'ul Auwal Shekarar Giwa (571m) bisa mash'hurin zance gun Ahlul Baiti (a.s), an ce, 12 ga watan da aka ambata. Wurin haihuwarsa: Makka. Aikoshi: An aiko shi a Makka 27 Rajab yana xan shekara arba'in.
Koyarwarsa: ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da 'yan'uwantaka da rangwame na gaba xaya ga wanda ya shiga musulunci, sa'annan ya kafa shari'a maxaukakiya da dokoki na adalci da ya karvo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karva daga gare shi.
Mu'ujizozinsa: Mu'ujizarsa madauwamiya ita ce Kur'ani amma waxanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.
Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a voye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma. Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi'ul Auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa.
Yaqoqinsa: Allah ya yi wa Manzo izinin yaqar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi xauki ba daxi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune: Badar- Uhud- Al-khandak (Ahzab)- Khaibar- Hunaini.
Matansa: KHadija 'yar Khuwailid (a.s) ita ce matarsa ta farko, amma sauran su ne: Saudatu 'yar Zami'a da A'isha 'yar Abubakar da Gaziyya 'yar Dudan (Ummu Sharik) da Hafsa yar Umar da Ramla 'yar Abu Sufyan (Ummu Habibia) da Ummu Salama 'yar Abu Umayya da Zainab 'yar Jahash da Zainab 'yar Huzaima da Maimuna 'yar Al-Haris da Juwairiyya 'yar Al-Haris da Safiyya 'yar Huyayyi dan Akhdabl.
'Ya'yansa: 1-Abdullah 2-Al-Qasim 3-Ibrahim 4-Faxima (a.s) a wani qaulin da Zainab da Ruqayya da Ummu Kulsum.
Ammominsa: Tara ne, su 'ya'yan AbdulMuxallib ne: Al-haris da Zubair da Abu dalib da Hamza da Al-Gaidak da Dirar Al-muqawwam da Abu Lahab da Abbas.
Ammominsa mata: Su shida ne daga iyaye mata daban-daban su ne: Amima da Ummu Hakima da Barra da Atika da Safiyya da Arwa.
Wasiyyansa goma sha biyu ne, su ne: Amirulmuminina Ali dan Abi Dalib (a.s) da Hasan dan Ali da Husain dan Ali da Aliyyu dan Husaini da Muhammad dan Ali da Ja'afar dan Muhammad da Musa dan Ja'afar da Ali xan Musa da Muhammad dan Ali da Ali dan Muhammad da Alhasan dan Ali da Muhammad dan Hasan Mahadi (a.s).
Mai tsaron qofarsa: Anas dan Malik. Mawaqinsa: Hassan dan Sabit, da Abdullahi dan Rawahata, da Ka'abu dan Malik.
Mai kiran sallarsa: Bilal Al-Habashi da Abdullahi Dan Ummu Maktum da Sa'ad Al-kirdi.
Tambarin zobensa: Muhammadur Rasulullah!
Tsawon rayuwarsa: shekaru 63. Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23. Tarihin wafatinsa: 28 Safar 11 H. Wajan da ya yi wafati: Madina. Inda aka binne shi: Madina a Masallaci Maxaukaki Mai alfarma.
Ka sani cewa Muhammad (S.A.W) shi ne qarshen annabawa kuma addininsa shi ne musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari'arsa zata wanzu har zuwa qiyama kuma ita kadai ce shari'ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa qarshen rayuwar duniya da lahira. Kamar yadda shi kaxai ne mutum abin koyi ga dukkan duniya baki xaya, dukkan mutanen duniya idan suna son alheri ga kawukansu to dole ne su bi tarfarkinsa su yi koyi da kyawawan halyensa (S.A.W) da kuma sanin sashen tarihinsa da ba makawa mu kawo wasu daga siffofinsa (S.A.W):
Shi ne Muhammad xan Abdullah (S.A.W) kuma babarsa ita ce Aminatu 'yar Wahab. An haife shi a Makka ranar juma'a goma sha bakwai ga watan Rabi'ul awwal bayan vollolwar alfijir a shekarar giwa, a zamanin sarki mai adalci Kisra . (wato idan an kwatanta shi da ire-irensa).
Aiko Annabi Mai Daraja (S.A.W)
An aiko Annabi Muhammad (S.A.W) da saqo a 27 ga Rajab bayan yana xan shekara 40 yayin da Jibrilu (A.S) ya sauka gareshi daga wurin Allah (S.W.T) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makka ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Alaqi .
Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makka a lokcin akwai jama'a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da saqon Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi yana cewa da su: "Ku ce babu abin bauta sai Allah kwa rabauta" .
A lokacin tunda mutanen Makka mushrikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka riqa yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk sa'adda ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutar da shi har ya ce: "Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni" .
Ba wanda suka yi imani da shi sai mutane qalilan, na farkonsu Imam Ali sannan sai matarsa Hadiza (A.S) sannan sai wasu mutane.
Farkon wanda ya yi imani da shi daga maza Imam Ali sannan daga mata sai Hadiza (A.S).
Yayin da takurawar mushrikai ta yi yawa sai ya yi hijira zuwa Madina wannan kuwa ita ce hijirar farko a tarihin Musulmi, yayin da suka yi yawa sai qarfinsu ya daxu kuma suka samu koyarwa daga Manzon Allah da shari'arsa mai sauqi mai hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da mutumtaka da wayewa da cigaba a Madina har suka fi dukkan duniya da addini na sama da wadanda ba na sama ba.
Kuma an samu yaqoqi masu yawa a Madina kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga maqiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zavar vangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin waxanda ake kashewa daga vangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yaqoqinsa tamanin da wani abu, wato; waxanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu daya da dari hudu ba.
Mutuwa Mai Zafin Gaske
Tun lokacin da aka aiko Annabi da saqo har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu (A.S) shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji (S.W.T) a hankali a hankali har littafin Kur'ani ya ciki a cikin shekaru ishirin da uku, sai Manzo (S.A.W) ya yi umarni da a haxa shi kamar yadda yake a yau xin nan.
Manzo (S.A.W) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu'amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu.
Bayan cikar addini da kafa Ali xan Abu Dalib (A.S) shugaba na al'umma kuma halifa bayan Annabi (S.A.W) wannan kuwa ya faru a ranar Gadir ne goma sha takwas ga zulhajji a shekarar hajjin bankwana sai Allah ya saukar da ayar: "A yau ne na kammala muku addininku, na cika ni'imata gareku kuma na yardar muku da musulunci shi ne addini" . Sai Annabi ya yi rashin lafiya mai sauqi, sai dai ya yi tsanani har sai da ya haxu da Ubangijinsa a 18 ga watan safar na 11H.
Kuma wasiyyinsa halifansa Imam Ali (A.S) shi ne ya yi masa wanka da salla da binne shi a dakinsa a Madina inda qabarinsa yake yanzu.
Ya kansace abin koyi ne shi a riqon amana da ikhlasi da gaskiya da cika alqawari da kyawawan halaye, da girma, da kyawawna xabi'u, da baiwa, da ilmi, da haquri, da rangawame, da afuwa, da sadaukantaka, da tsentseni, da taqawa, da zuhudu, da baiwa, da adalci, da qasqan da kai, da jihadi.
Jikinsa ya kasance qololuwa wajen kyau da kuma daidaito da dacewa, kuma fuskarsa kamar wata ne mai haske da ya cika, kuma zuciyarsa da ruhinsa sun kai matuqa wajen kamala, mafi kamalar halaye da ladabi da xabi'a kuma sunnarsa tana haske kamar rana a tsaka-tsakinta.
Ataqaice, ya tattara dukkan wata xabi'a mai kyau da girma da xaukaka da kuma ilimi da adalci da taqawa da kuma iya tafiyar da al'amuran duniya da na lahira, wadanda babu wani mahaluqi da yake da irinsu.
Wannan shi ne annabin musulmi kuma wannan shi ne addinin musulunci, kuma addininsa shi ne mafificin addinai, littafinsa shi ne mafifcin littattafai domin shi: "Barna ba ta iya zo masa ta gabansa da ta bayansa, abin saukarwa ne daga mai hikima abin yabo" .
MAULUDIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W.A)
Mauludi: Wani buki ko taro ne domin tunawa da ni'imomin Allah da ya yi mana da rahamarsa da ya saukar zuwa ga bayinsa domin shiriya ga dukkan talikai. Magana kan mauludin Annabi (s.a.w) da sak'on da ya zo da shi abu ne mai matuk'ar k'ima da daraja wanda babu wani abu da ya kai shi muhimmanci, domin kuwa yana nufin bayanin sak'on da d'an Adam ba zai samu tsira ba sai ya yi rik'o da shi. Don haka zamu yi gajeren bayani kan Mauludin Annabi (s.a.w), da Sak'onsa, da kuma Musulmi.
Sai dai an samu wasu masu k'arancin diraya da fahimtar littafin Allah da sunnar Annabinsa (s.a.w) suna ganin munin Mauludi. Jama'a ce da ta tasirantu da koyarwar Banu Umayya masu gaba da Manzon Allah (s.a.w) masu jin haushin shelanta "Ash'hadu anna Muhammdar Rasulul-Lah" da ake yi a kan mimbari sau biyar a kowace rana. (Sharhu Nahajul Balaga: Ibn Abil Hadid; 1/113, 1263. Muwaffak'iyyat: Ibn Bukair. Murujuz Zahab: 1/341. Tahzibut Tahzib: 7/319).
Don haka babu mamaki idan an samu masu rik'o da koyarwar da ta samu daga wannan asalin suna k'iyayya da tunawa da mafi girman ni'ima da Allah ya yi wa bayinsa ta samar da Manzon Allah (s.a.w). Dalilan da ake kafawa domin nuni ga halascin mauludin Annabi (a.s) duk ishara ce kawai ga mai hankali, domin wanda yake musun Mauludi shi ne ake neman ya kawo dalili kan haramcinsa:
A cikin Kur'ani Mai daraja da Sunnar Ma'aiki an yi nuni da abubuwan da suke haramu, kuma Mauludi ba ya daga cikinsu. Don haka mai son k'aryata Mauludi shi ne mai buk'atar ya kawo dalili kan wannan haramcin, domin haramun a bayyane take kuma tana da iyaka, amma abubuwan da aka halatta suna da fad'i kuma ba su da iyaka.
Daga cikin dalilan akwai ayoyi kamar haka: "Ba mu kasance masu azabtar da mutane ba sai mun aiko wani d'an sak'o". Da yake nuni da cewa; Duk abin da babu wani haramncinsa da muka sani a shari'a to halal ne yin sa, sannan a hankalce akwai munin azabtarwa ba tare da bayani ba". Wad'annan lamurran an san su da "Bara'a shar'iyya da ak'aliyya" a cikin ilimin Usulul Fik'hi, da suke nuni da cewa; Duk abin da ba a san haramcin ba daga nassin shari'a kuma babu wani abu da yake nuni da shi, to halal ne. Wad'annan abubuwan fararru sababbi suna da yawa matuk'a kamar; Mauludin Annabi, da Musabak'ar Kur'ani, da kafa k'ungiyoyi domin ayyukan alheri, da wasannin motsa jiki.
Sannan kuma ga wata ayar tana cewa: "...Kuma ba a sanya muku wahala a cikin addini ba..." (Hajji: 78), da take nuni da cewa; Babu wani k'unci da dabaibayi da aka yi mana a kan halaccin abubuwan da haramcinsu ko halaccinsu bai bayyana ba. Don haka hannyenmu a sake suke babu wani k'aidi da k'untata wa kawuka. Sannan kada wani ya ce: Ai tana d'auke hukunci ne ta mayar da shi yalwa ga abin da ya ta'azzara ko ya wahalar? Sai na ce: A nan ma akwai k'unci domin duk haramta alheri a cikinsa akwai k'unci, kuma duk halal a cikinsa akwai yalwatawa, don haka wannan ayar tana shafar abin da muke magana a kai.
Ayar nan da take cewa: "Kuma amma ka zantar da ni'imar Ubangijinka" (Dhuha: 11). Musulmi bai san wata ni'ima da zai ambace ta ya ji dad'i da tafi samuwar Annabi (s.a.w) ba, kamar yadda Allah (s.w.t) bai k'ayyade mana nau'in ni'imomin ba, don haka ne ma ya ce: "Ni'imar Ubanginka" ba tare da ya k'ayyade su ba, sai k'ayyade su ya sanya shi a hannun mutane, domin su ne suka san ni'imomin da ya yi musu. Sai dai ya bayyana musu wasu daga ciki amma fa ba domin ba su san su, sai domin ya k'arfafa wa hankali abin da yake riskarsa domin tunatar da shi ni'imominsa.
A wata ayar kuwa mad'aukaki yana cewa: "Babu wani alheri a cikin ganawarsu -taronsu- sai wanda ya yi umarni da sadaka ko wani kyakkyawa, ko gyara tsakanin mutane...". Ashe akwai wani alheri da ya fi taruwa da tuna wa mutane ni'imomin Allah da rayuwar annabinsu, da nuna musu kyakkyawan koyi a cikinsa?! Yanzu akwai wani mai basira da zai haramta taruwa irin wannan?!
Da wani zai yi raka'a d'ari biyu kowace rana ba tare da ya jingina ta da wata aya ko ruwaya ba, sai dai kawai domin yana son ya aikata alheri don samun lada. Sai ka ga mai irin wannan tunanin musun Mauludi ya ce: Ba komai, da hujjar cewa kyakkyawan abu ne. Sai dai a nan wani yana iya cewa: Ai sallar asham a zahiri kyakkyawa ce domin ibada ce, amma sai ga shi a shari'a tun farko manzon Allah (s.a.w) ya hana ta, sai dai Halifa na biyu ne ya dawo da ita kuma ya yi mata kirari da "Madalla da wannan bidi'a!. Don me Mauludi ba zai zama irin wannan ba!?
Sai in ce masa: Abin da manzon Allah (s.a.w) ya hana shi ne yin ta jam'i a masallatai a dararen Ramadan, da umarnin da ya yi na su yi ta d'aid'aiku -a gidajensu- domin jam'i a sallar nafila ba ya inganta . Don haka ne ma Imam Ali (a.s) ya hana jam'in ta a masallatai a lokacin da ya zo Kufa ya ga mutane suna yi yayin da ya aika Imam Hasan (a.s) ya shelanta haramcinta bisa sunnar Annabi (s.a.w), sai masallaci ya kaure da ihun Wayyo zai kashe sunnar Umar! (Muntahal Mad'alib: Allama Hilli; 358-360). Duba littattafai kan sallar Tarawihi kamar: (Buhari, da Muwatta, da Muslim).
Sai dai Halifa na biyu ya mayar da ita farkon dare, kuma ya sanya mata jam'i, sab'anin umarnin manzon Allah (s.a.w) da ya hana jam'inta ya sanya k'arshen dare ya fi farkonsa. Sai lamarin sallar asham ta bidi'a ya yi kama da mai yin sallar azahar raka'a takwas ne da nufin ninka ladanta, a maimakon ya yawaita ladansa sallarsa zata b'ace ne.
Da wannan ne magana zata fito a fili cewa: Babu wani abu da yin sa yake haram shari'a ba ta yi bayaninsa ba ko da kuwa a zahirinsa wani yana ganin kyawunsa. Don haka idan wani abu ya zo mana wanda muke kokwanton muninsa ko kyawunsa, da hukuncin wad'annan ayoyin da wasunsu ma yana nuna babu laifi a kan yin sa. Sannan mai Mauludi yana kafa hujjarsa da dokokin shari'a ne tabbatattu wad'anda suke iya tabbatar da duk wani alheri ko wane iri ne kuwa har zuwa k'arshen duniya ba tare da da'awar nassi ba.
Sau da yawa da za a canja wa bikin Mauludi suna da wa'azin k'asa, ko tunatarwa, ko ambaton rayuwar Manzo, da mai k'in sa ya karb'a yana mai yarda. Amma saboda kawai an sanya masa kalmar sunan "Murnar Haihuwar Annabi" to sai ya zama laifi babba da zukata suke bak'in ciki da shi. "... Ka ce: Ku mutu da bak'in cikinku"!.
Idan ka ce: Wasu suna aikata haramun lokacin Mauludi, kamar kawo 'yan mata su yi rawa a gaban samari da sauran jama'a? Sai in ce maka: Ya kamata ne ka yi fad'a da haramun da aka sanya a cikin wannan taro, da k'ok'arin ganin an fitar da ita daga ciki, ba fad'a da asalin taron ba. Domin wani lokaci a tarurrukan wa'azi har fad'a ne yake kaurewa, amma ba ya haramta yin taron wa'azi!.
Da zamu tsawaita magana kan Mauludi ne da yana buk'atar littafi ne cikakke, sai dai zamu dakata hakan. Duba a ci gaban mak'alar a bayani mai suna: Sak'on Annabi Muhammad (s.a.w)
YABON ANNABI MUHAMMAD (S.AW.A)
"Kuma Yabo babu shakka wata alama ce ta soyayya, kai bari dalili ne na ingantar imani babu jayayya". Hakika zuciyata ta tsaya cik! Akan shin abin da nake aikatawa yana gudana ne karkashin shari'a da yarda ne, ko kuwa karkashin hani ne da kin yarda?! Amma abin da dai na sani shine; sai dai a zuciya ta akwai nutsuwa da kwanciyar hankali da aminci, babu wani bantare na damuwa da firgici, wanda wannan yanayin shine halin mafi yawancin masu yabon Annabi masoyi tsarkakakke. Hakanan kuma wannan yanayin shine wanda ya tunkudani akan hujjar dalilin shar'ancin Yabo da jinjina ga fiyayyen halittu Annabi Muhammadu (S).
"Kuma hakika tabbas kana kan halayen kirki, manya", Wannan bayani ne daga gaskiya Jalla cikin daukakarsa Ubangiji bisa doron hakkin Yabo ga Annabi.
Hakika wannan aya maigirma duk da ta kasance daga harshen Ubangiji, to kuma sam-sam bawai ta zamo abar nufi da tsayuwarta akan yabon Ubangiji ne kadai gareshi ba (Manzo). Ta inda kai bawa ne Mumini Musulmi ya halasta gareka jinjina ga Annabi tare da Biki gareshi kai da ma yabonsa a cikin sauki mafi kusanci gareka daga kiftawar idonka, da ka tsaya da tsantseni a gaban Ubangiji kuma kayi salloli kayi karatu a cikinsu daga abin da ya sauka a cikin yabon Annabi, kamar kace:
"Lakad jaa'akum rasuulun min anfusikum aziizun alaihi maa anittum hariisun alaikum il-mu'miniina ra'uufun rahiim" (Taubah:128).
Arra'ufu Arrahiimu siffofi ne na yabon daukaka, ko kace Wa innaka la'alaa khulukin aziim, kana nufin kai ma'abocin halayen kirki ne, ko kana nufin ka daukaka akan kyawawan halaye, kai ko dai wannene ya kasance kake nufi, to hakika kana yabon Muhammadu ne da harshen Ubangijin Muhammadu. Kuma babu wani mutum da zai iya bugun kirji akan ya hana ka sallar da zata kusanta ka da Ubangiji da kuma soyayya da Manzon Allah.
Ubangiji na cewa: "Wamaa arsalnaaka illaa rahmatan lil'aalamiin" (Al-anbiyaa' :108). Ba tare da an tsawaita ba Annabi shine rahma (Jinkai) ga dukkanin duniya ko ga dukkan talikai, don haka biyo ni zuwa surati Yuunus inda Ubangiji yake cewa: "Kul bifadlillaahi wa birahmatihii fabizaalika falyafrahuu huwa khairun mimmaa yajma'uun" (Yuunus: 58).
To ka duba mana menene ya motsu cikin zuciyarka daga wadannan ayoyin guda biyu na suratul-anbiyaa' da surati Yuunus? Hakika abinda za a gane daga garesu shine: Hakika Ubangiji yana fadin da falalar Allah da jinkansa (Bifadlillah wa birahmatihi) to wannan jinkan shine Annabi Muhammadu don haka kuyi farin ciki (Fafrahuu). Don haka wannan
shine dalili yankakke gamsasshe akan halascin farin ciki da Annabi.
Wannan shine abin da na fahimta ni, kuma ina zaton kaima zaka yi tarayya da ni a wannan fahimta tawa yakai mai karatu, daga wadannan ayoyi guda biyu. To shin akwai wani wanda shima ya yi dace da mu a cikin wannan fahimta tamu daga cikin magabatanmu masu girman daraja?
Malam Ahaafiz Jalaaluddiin Assiyuudiy: a cikin littafinsa (Durrul-manthuur) yace: Abus-shaikh ya fitar daga Ibn Abbas (R) a cikin fadinsa madaukakin Sarki Kul bifadlillaahi wa birahmatihii fabizaalika falyafrahuu - sai yace: Fadlullaahi tana nufin ilimi, Rahmatuhu kuwa tana nufin ne Annabi, Allah na cewa: "Wamaa arsalnaaka illaa rahmatan lil'aalamiin" .
Malam Aluusiy kuwa a cikin Ruuhul-ma'aaniy cewa ya yi: Ai ayar ta tabbatarwa ce da hukuntarwa bayan komawar samuwar Rahmar da aka ambata a cikin ayar itace Annabi (S), yace abin da yafi shahara siffanta Annabi da Rahma kamar yadda ya nuna gareshi fadin madaukakin Sarki "Wamaa arsalnaaka illaa rahmatan lil-aalamiin" .
Malam Fakhrurraaziy a cikin Tafsiirul-kabiir cewa yayi: wajibi ne ga mutum kada ya yi farin ciki sai da wannan. Wato Alfadlu wan-Nabiy (S) …har zuwa karshe.
Ya jama'a wannan wane irin Annabi ne wannan wanda daga siffofin cikarsa ya dauki siffofin Allah, kana daga sunayensa ya dauki sunan Allah?!
Shine Arra'uufu Ubangijinsa shima haka, shine Arrahiimu Ubangijinsa shima haka, shin hakan bai halasta ba a yabeshi, ga wanda Magana tazo take tsarkakeshi a cikin littafin da baci ko karya bata zuwan masa daga gabansa ko bayansa, ta yaya a'a, bacin jinjina gareshi da tasbihi gareshi wajibi ne!
Menene abin da Malam Fakhrurraaziy yake fada a cikin fadinsa Ubangiji: "Lakad mannallaahu alal-mu'miniina iz ba'atha fiihim rasuulan min anfusihim yatluu alaihim ayaatihi wa yuzakkiihim wa yu'allimuhumul- kitaaba wal-hikmata wa'in kaanuu min kablu lafii dalaalin mubiin" (Aali Imraan:164).
Abin da yake cewa shine: hakika aiko Manzon Allah (S) kyautatawa ne ga dukkanin talikai, Ubangiji ya girmama Larabawa da shi, ya canja su da albarkar da ta gabace shi (S) daga mai kiwon dabbobi zuwa ga mai kiwon mutane da jama'a. Ya dauke su daga cikin karkatar Jahiliyya zuwa matsayin shugabanci da shiryarwa kamar yadda Madaukaki yace: "Wa innahu lazikrun laka wa likaumika wa saufa tus'aluun" (Zuhraf:44).
Hakika mai duba da idon basira na gaskiya ga wannan nassi na Kur'ani zai samu hakika yin biki da farin ciki da yabo ga Annabi ko da ba a sami wani nuni akansu ba sai wannan ayar kadai to wallahi da ta ishe mu, kan mu bayyana farin cikin da shi da yabonsa kamar yadda yadda Shugabansa ya yabeshi "Wa innaka la'alaa khulukin aziim".
Lallai manyan Malamai masana sunyi rubuce-rubuce masu tarin yawa, akan nuna tabbas Yabon fiyayyen halittu Annabi Muhammad (S) a kebance ko a cikin jama'a wani kusanci zuwa ga Allah madaukakin Sarki ne, haka nan aiki ne karbabbe (A wajen Ubangiji), kana sam ba Bidi'a ce marar kyau ba, haka nan babu wani mai inkarin hakan sai wanda ya zamo Dan-bidi'ar kuma Jahili. Wasu ma kacokan sun ce Yabon na Manzo (S) wajibi ne daga cikin wajiban addini kamar yadda yazo a baya da kuma zai zo nan gaba.
Ubangiji madaukakin Sarki ya fada a cikin littafinsa mai tsarki:
"Kuma wadanda suka yi imani da shi (Annabi Muhammad) kuma suka yabe shi sannan suka taimake shi, kana suka bi hasken da aka saukar tare dashi, wadannan sune masu rabo".
Fadinsa madaukakin Sarki da yake cewa: "Wa azzaruuhu" wannnan kalma a wajen wasu masanan tana nufin ne suka Yabeshi, suka Girmamashi. Don haka ne a wannan madakata Manyan Malamai suka kawo cewar lallai da wannan nassi na wannan aya to Yabon Annabi (S) wajibi ne ga dukkanin Musulmi, haka nan Girmamashi da tsarkakeshi shima wajibi ne daga abubuwa muhimmai na addini, kuma aiki ne daga cikin ayyukan masu rabo, haka nan tafarki ne na Waliyyan Allah da Salihan bayi. Wanda kuwa tauye shi Manzon tsira (S) ko kyamarsa ko kyararsa lallai bata ne kuma kafirci ne, Allah ya kiyashe mu da ku baki daya daga cikin mabarnata.
Sau da yawa nakan fada na dada nanatawa, idan har kai mai kiyayya da ayi Yabo ga Annabi a kadaice ko a cikin jama'a, haka nan dai kake gaba da Murnar Haihuwarsa da irin salo na biki ko ba biki ba, da har tsaurin idon ka ya kai ka ga cewa wadannan abubuwa Bidi'a ne, sakamakon karancin saninka da karancin fahimtarka, watakila ma ma iya cewa ta'assubancinka. To ga mawarwara nan guda daya nan tal ta ishe ka warware dukkanin matsalarka.
Hadisi nanan garau a cikin ingantaccen littafin hadisai na Malam Muslimu da yake cewa Manzon Allah (S) yace: "Dukkanin wanda ya kawo wani abu a cikin Musulunchi kyakkyawa, to yana da ladan wannan abu da ya kawo, haka nan da ladan duk wanda ya aikata ta a bayansa ba tare da an rage ko kaka ba daga cikin ladan nasu ba"
Mu dauka baki daya babu wani Hadisi da aka samu da yake nuna wadanda suka yi Yabon Annabi (S) a gabansa bai hane su ba, illa ma yabonsu da bushara gare su da ta biyo baya. Haka nan babu wani Babban Malami da aka taba samu ya yi Yabon Annabi (S) musamman a bayyane ko a cikin Jama'a. To wannan Hadisin kadai shima ya ishi dogaro wajen yin Yabon Annabi (S) a fili da boye kai har da dandazon jama'a.
Bahaushe ma yakan ce: "So hana ganin laifi". Shin takakamarku ce da soyayyar Annabin (S) ta sanya ku kuke ganin yin Yabonsa ba dai-dai bane ko kuwa?! Ai irin yadda Kalmar ma tazo YABO, duk mai cikakken hankali yasan ba kalma ce sahuhuwa ba. Fadin daraja, kyawun hali, ilimi, kyawun siffa, daukaka, da sauransu ga wanda ya cancance su shine fa yabon. Sabanin idan mutum bai cancanta ba aka kira shi da su ya zama ZAMBO. Idan har fadin kyawawan dabi'u da daukakar Shugaba Annabi Muhammad a matsayin yabonsa ne kuke ganin kure ne to hakika zamu iya karyata ku kai tsaye a soyayyarku. Har akwai wata kalma da za a kirawo Shugaba da ita ta daukaka indai ba ace shine Ubangiji ba da za a ce an kauce?
Ai ya ishi Manzo (S) girman daraja da Yabo da ya kasance Ambasado na Ubangiji a doron kasa. Kayi duba mana yadda matsayin Ambasada yake a irin zamantakewa tamu ta mutane da ake iya ganin Shugaban kowace kasar, amma ga irin fawar da Ambasado yake da ita. Mataimakin shugaba a irin zamantakewa tamu yaya girman mukaminsa yake yayin da akace ma yau shi shugaban ya yi balaguro?!
Ubangijinmu babu wani lokaci ko rana da za a ce yau gashi ya zo wannan duniya tamu da sunan ziyara ko duba aikin wakilinsa Annabin Muhammad (S), sam babu wannan lokacin! A'a duk abin da ya zartar ya zartu, abinda ya fada ya fadu, abinda ya aikata ya aikatu! Babu tuhuma Abadan! Wanda ya turo shi ya bashi satifiket tuni na tabbatar da shi, na tabbatar da hukuncinsa, maganarsa duk na Allah ne (Laa yandiku anil-hawaa, in huwa illaa wahyun yuuhaa…). Don haka zamowar Shugaba ma wakili na Ubagiji a doron kasa kadai ma ya ishe shi mafkharatan ilaa yaumil-kiyaamah.
Duk da kasantuwar Shugaba wakili ne na Ubangiji gare mu, domin bamu isa ba balle mu
kai ga Ubangiji! Shi wata matattakala ce, wani tsani ne ga Ubangijin domin kaiwa gareshi, amma Ubangijin bai gushe ba a gurare da dama cikin Littafinsa mai tsarki yana Yabonsa fiyayyen halittu Annabi Muhammadu (S) kamar yadda muka kawo wasu a baya.
Ubangiji da yake cewa: "Ashe bai same ka maraya ba, sannan ya tallafe ka, haka nan ya same ka abin nema (Ga jama'a) sai ya nunaka/sanar da kai (Ga jama'ar), haka nan ya same ka marar shi ya wadata ka".
Shin wannan ba yabo bane?! Wa muka samu Ubangiji ya tallafa kasantuwarsa maraya?! Wa muka samu Ubangiji ya nuna shi yace shine shiriya baki dayanta idan ba Shugaba ba?! Tuni kafin zuwansa Annabawa da dama sun shude suna baiwa mabiyansu bayani akan Shugabansu na nan tafe wanda shine zai shiryar da dukkan duniya, inda suka bada wasicin binsa kai tsaye.
Mabiyansu sun kasance suna bibiya da bincike da neman wannan mai shiryarwar domin su bishi, katsam Ubangiji ya turo shi, kuma ya nunawa jama'a shi akan shine wannan mai shiryarwar.
Amma ba kamar yadda wasu dolayen mutane jahilai wadanda basu san isdilahin yare akansa ba ma, balle yaren larabci suke fassarawa suce wai an same shi batacce wal-iyaazu billah. A wannan fage Ubangiji na cewa:
"Wadanda suke bin Manzo Annabi Ummiyyi wanda suke samun sa rubuce a wurinsu, a cikin Attaura da Injila….".
Haka nan wanene Ubangiji ya sama marashi yace na wadata ka idan ba Shugaba?! Anan ma akan sami wasu dolayen da suke cewa wai Shugaba ya rasu ne talaka! To Allah na tuba ba Ubangiji ba, ko mataimakin Shugaban kasar Najeriyar nan ne Good-luck yace maka kai Wane jeka mun wadataka, ai kai da talauci har abada, balle Ubangiji da kansa yace Ya wadataka! Ko a cikin kananan sirori muka karanta zamu ga ana cewa Shugaba Ya rasu yabar Bayi dari, Rakuma dari, …. Wanda kuma duk shine yake ciyar da su, to talaka ta yaya zai ciyar da wadannan?!
Ubangiji na cewa: "Kuma muka daukaka maka ambatonka". Shin wannan ba yabo bane?! Wa ka taba samu Ubangiji ya fadi hakan akansa?!
Kai a bisa dogaro da ayar da ta gabata da tazo da horo akan Yabon Annabi (S) har Manyan Masana suka zartad da cewa wannan horo umarni ne na wajibi kamar na ibadu, to ai babban lada ne ko kuma ince yafi lada kazo cikin mutane domin sauke wannan wajabcin na Ubangiji domin gudun kada jama'a su zaci kana daga cikin wadanda basa sauke wannan wajabcin Yabon, wato sai muyiwa wannan Yabon hukunci irin na wajabcin Salla ta farilla, da aka fison sauke wajabcin nata a cikin jama'a kuma yin hakan ma yafi lada.
Hakika Yabon Manzo (S) ya tabbata a wajen jama'a a cikin hadisai guda biyu kuma ingantattu, na dayansu Hadisin da Malam Imam Ahmad bn Hanbali ya ruwaito a cikin Musnadin sa daga Hadisin Anas dan Maliku (R): Hakika Habashawa sun kasance suna harrakawa a cikin Masallacin Manzon Allah (S) suna fadin (da yarensu): "Muhammadun abdun saalih" (Annabi Muhammadu bawa ne nagari), sai Manzon Allah (S) yace: "Me suke fada?" sai aka ce masa suna cewa ne: Muhammadu bawa ne nagari. Haka nan Malam Bazzaar ya ruwaito a cikin Musnadinsa: Hakika Habashawa sun kasance suna harrakawa a gaban Manzon Allah (S) suna cewa: "Abul-kaasim dayyiban" wato Baban Alkaasim tsarkakakke ne, wannan Hadisin Malam Haafiz dan Kuddaan ya inganta shi a cikin littafinsa "An-nazru fiy ahkaamin-nazr" . Wanda kuma shi fiyayyen halittu Annabi Muhammad (S) bai kyari wannan Yabo nasu gareShi ba balle ya hana su.
Masana yaren larabci sunce: "Azzafnu Arraksu - wa Mad-hurrasul ibaadatun". Wadannan hadisai kalmomin da suka zo a cikinsu na Azzafnu da aka ce suna harrakawa, harrakawar tazo ne da Kalmar Azzafnu. Don haka ne masana lugga suka ce ba komai ake nufi da wannan kalma ba face harrakawa - yabon Manzo kuwa Ibada ne, a cikin baitin wakar da ya gabata na masana Yaren larabci ba Ajamanci ba!
Hakanan yana daga cikin abin da Manyan Malamai Alhaafizus-Suyuudiy da Alhaafiz Ibn Hajar da wasunsu suka ruwaito cewa; hakika Abbas dan Abdul-muddalib ammin Manzon Allah (S) yace: nace: ya Manzon Allah (S) ni ina yabonka da wasu baitukan waka, sai Manzon Allah (S) yace: "Ka fadeta Ubangiji ba zai tozarta bakinka ba".
Hakika sananne a wajen ma'abota ilimi da bincike kamar yadda ya gabata cewa Yabon fiyayyen halittu Annabi Muhammad (S) a halin dayantaka wato kai kadai a kebe ko kuwa a halin hadaka wato cikin jama'a a bayyane tabbatacce ne kuma ingantacce, inda Manyan
Maluma suke cewa dukkanin wanda kuwa ya yi inkarin hakan to hakika shi mai riko da Bidi'a ne wato Dan-bidi'a ne, haka nan kuma shi jahili ne.
Daga karshe nake goyewa da wasu baituka na yabon fiyayyen halittu Annabi Muhammad (S):
Muhammadun sayyidul-kaunaini was-thakalaini - Wal-fariikaini min urbin wamin ajamin,
Huwal-habiibullazii turjaa shafaa'atuhu - Likulli hawlin minal-ahwaali muktahama,
Faakan-nabiyyiina fii khalkin wa fii khulukin -Walam yudaanuhu fii ilmin wa fii karami.
GA TAMBAYAR NAN:
Dai-dai lokacin da kuke ganin cewa; fahimtar ku akan Kur'ani ta yi masa fassara ba tare da la'akari da juyawar Yare ba, lallai sai dai a fassara Kur'ani gaba-gadi, da kuma kudurin ku na lallai komai na Ibada da wanda ba na Ibada ba Kur'ani ya fade shi filla-filla dalla-
dalla. Mu kuwa muke ganin wannan fahimta taku ba dai-dai bace, dole ne sai anyi a'akari da juyawar Yare musamman ma na Larabcin da aka saukar da Kur'anin da shi, kuma muke ganin mu lallai Kur'ani ba komai ya kawo filla-filla dalla-dalla ba, ya bar wasu abubuwan sai Manzon da aka turo yayiwa al'umma bayanin yadda zasu gabatar da su. Wanda wannan ne zai bada cikakkiyar fassarar ayoyin da suka gabata a sama da ma wasunsu da ban kawo ba, akan biyayyar Manzo, da rashin saba masa,... Da muka zo muna yi muku bayananmu akan tabbatar da hakan, kuma muka tabbatar muku da hakan na lallai abinda muke fada din nan shine fa akan hanya dodar, a fage na Nassin Al-kur'anin, wanda dukkanin wani mai hankali idan da zai yi hukunci da hankalinsa kadai, wanda misali ma ya zamo ba Musulmi ba, ya karanta abinda muka kawo da abinda kuka kawo kai tsaye zai bamu tutar gaskiya.
Nacewarku akan lallai ku kuna kan madakatarku wacce babu wata cikakkiyar hujja ga dukkanin wani mai hankali, ya sanya don muyi muku kwaf-daya ba tare da mun ta jan Magana ba, ganin kowannen mu yana da abubuwa wadanda su ma muhimmai ne a gabansa, muka shigo da maganar Ibadu don a datse maganar nan da nan. Kawo maganar Ibada sam ba fita bane daga cikin Maudu'i, domin ku kuna ganin dukkanin Ibadu sun zo a cikin Al-kur'ani cif da cif, mu kuma muke cewa wannan Magana sam ba haka take ba, dole ne sai an duba Hadisan da suka tabbata kafin a sami cikamakon wasu Ibadun. Kun ja, mun ja, to don tantance gaskiya, dole ne sai an baje koli, domin a ga su waye suke tare da gaskiya. Wannan dalilin ne ya sanya muka dore muku da tambaya akan; idan har kuna ganin baku yarda da wadannan rututun dalilan namu da muka kawo muku ba, to muna son ku tabbatar mana da a ina Salla ta fito a cikin Al-kur'ani dalla-dalla filla-filla, kamar yadda Alwala ta zo dalla-dalla filla-filla? ! Kaga ashe wannan ba fita bane daga cikin Maudu'i.
Mu masu bin Mazhabin Ja'afariyyah, mun yarda da cewar lallai Al-kur'ani akwai abinda ya kawo wadanda ba su da bukatar kari ko ragi ko bayanin yadda za'a gudanar ko gabatar, wanda daga cikinsu akwai irinsu Alwala da Taimama da sauransu. Haka nan lallai akwai abubuwan da ya kawo da suke da bukatar bayanin yadda za'a gabatar da su daga bakin Manzonsa Annabi Muhammad (S), irinsu su Sallah da Azimi, da sauransu.
Tunda mun samu ku baku yarda da wannan kuduri namu ba, shine ya sanya muka ce; to ku kawo mana tafsilin bayanin Salla da Azimi,… , amma a cikin Al-kur'ani, wanda ina dada maimaitawa, duk mai hankali kuma mai amfani da hankalinsa ya san ba'a fita daga Maudu'in maganar ba.
Babu laifi idan kuka nemi alfarmar a dan daga muku kafa, domin ku sake bincike, ku sake komawa ga Malaman ku domin ku sami bayanan da zaku yi mana su gamsar da mu. Amma fa ku sani babban laifi ne kuce ba zaku bamu amsar wadannan tambayoyi ba, kuma ko da mun dage alkalumanmu wajen cigaba da wasu maganganun bamu aikata wani laifi ba, kuma har wala iyau yana dada nuna gazawarku ne tare da rashin wata hujja wajen riko da akidarku. Domin mutumin da yake da hujja abisa abinda yake aikatawa, baya damuwa da yin tsokaci a cikin wata maganar da ba akan ta ake ba, ko kuma bata ma shafe ta ba. Kai bar ma akai kan tsokaci, har idan abokin maganar ta sa ya nemi a janye wannan maganar kafin ya dan kintsa, a jefo da wata, yakan yarda a cigaba da watan kafin ya kintsa. To ina ga maganar da ma akan turba take, babu wani ratse bare ketara?!
Lallai ketarewarku daga bada wadannan amsoshi kamar yadda muka bukata yana nunawa ne karara baku da wata hujja, idan kuwa kuna da ita to, Bisimillah, ga fili ga mai doki.
A maganganunka akwai abubuwa da yawa wadanda suke da bukatar a dan karkade musu kura a gyara musu zama, domin su zamo ababen karba, to amma lokaci bazai bari muyi hakan ba, don haka ne lokuta da dama mukan dauki muhimmai daga ciki, mu warware su, warwarar da duk mai hankali zai yarda da mu, ba domin komai ba sai don kada rubutun yayi yawa har ma a fita daga Maudu'in da ake akai.
MUWAR MANZON ALLAH MUHAMMAD {S.A.W.A}
wanda ya cirato ya shigar Dan'uwa Sa'idu Funtua