Muassasar alhasanain (a.s)

Ziyarar Arba'in Din Imam Husain (A.S)

3 Ra'ayoyi 02.3 / 5

Ziyarar Arba’in Din Imam Husaini

Daya daga cikin bukukuwa masu mihimmanci a Addinin Musalunci masuamma ma a Mazahabar Shi‘anci bikin arba’in din shahadar Imam Husain (as). An rawaito daga imam Hasan Al-askari yana cewa a cikin hadisin alamomin mumini a inda ya jero abubuwa duga biyar a inda yake cewa: “salla raka’a hamsin da daya da ziyarar arba’in da sa zobe a dama dss....”

Masu tarihi sun rawaito cewa Jabiru dan Abdullahi shi da Adiyyu sun ziyarci Imam Husaini bayan shahadarsa a ranar arba’in ta farko daga lokaccin.

Sayyid ibn Dawusu ya  nakalto cewa: a lokacin da matan Imam Husaini (as) da ‘ya’yansa suke kan hanyar dawo wa daga Sham a yayin da suka iso Iraq sai suka ce da  mai yi musu Jagoranci: ka kai mu hanyar karbala. A lokacin da suka isa inda Imam Hasaini (as) ya yi shahada shi da sahabbansa sai suka ga Jabiru dan Abdullahi Ba’ansare da wasu gungu daga bani Hashim da wani mutun daga alayen Manzon Allah sun zo su ziyarci imam Husain (as). A lokaci guda gaba dayansu suka iso karbala saka fara rusa kukan bakin ciki suna dukan kawukansu da fusakunsu suka yi zaman makoki mai kuna da radadi wanda ya wuce tsammani kuma matan kabilun da ke zaune a yankin ma sun hadu tare da su suka ci gaba da yin zaman makoki, a dunkule sun zauna a wajen wasu 'yan kwanaki suna yin zaman makoki.

Munir Muhammad Said Akanawi

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)