Muassasar alhasanain (a.s)

Abuzar Algiffari

7 Ra'ayoyi 03.0 / 5

Da sunnan sa madauakaki

Tarihin Abuzar Algiffari


Shi ne jundubu dan janadata ko kuma a ce abu zarril gifaafi yana  daga acikin manyan sahabban manzo tun a farkon manzanci ya kasance daga cikin wadanda suka yi imani da manzo. Kafin zuwan musulunci ya kasance daga cikin masu bautar allah makadaici a lokacin da ya san Manzo (saw) sai ya karbi musulunci, sabanin sauran musulmai abu zarri a lokacin da ya shiga musulunci bai zauna a maka ba sai ya koma wajen kabilarsa sannan har zuwa lokacin yakin ahzab, sannan ne ya zo madina ya shiga cikin rundunar ma’aiki.
Bayan mutuwar abubukar sai ya koma sham (syria). Alokacin yusman saboda yawan nuna rashirin yardar sa da budi’o’in da mu’awuya ke kirkirowa sai aka dawo da shi madina daga karshen saiaka kora ko aka nisanta shi zuwa kauyen rizbah, kuma a can ya rasu abu zar, na daga cikin sahabbai jarumai masu magana daya da tsayawa a kai ta yadda ya zo daga Manzo (saw) yana cewa: “sama ba ta yiwa awani inuwa ba kuma kasa ba ta dauki wani mutum mafi fadin gaskiya fiye da abu zarri ba” kuma abu zarri na daga cikin mutanen da suke kukusanta imam Ali (as) bayan da abin da ya faru a sakifa ya afku abu zarri ya kasance tare daga cikin ‘yan tsirarun sahabban da suka yi saura a gefen imam Ali (as) kuma yana daga cikin shi’ar imam Ali (as).

Abu zarri na daga cikin manyan sahabban Manzo (saw) wanda tun a farkon kira ya mika wuya zuwa ga musulunci kuma yana da cikin na farko da shuka shahara a tarin musulunci.
Mashahurai malaman tarihi sun ambaci sunan sa cikakke da cewa: shi ne Jundubu dan Janadata dan Kaisu dan amru dan malil dansu’airu dan huram dan Gaffa wanda da shi ake danganta shi kuma aka san shi da shi, (gaffari).  Babar sa ma ‘yar kabilar Gaffari ce; an kiranta Ramlatu ‘yar waki’ata.  Kafin aiko Manzo (saw) abu zarri ya kasance mai bautar Allah Ta'ala kuma daga karshe ya samu sannaya da Manzo (saw) kuma ya shiga musulunci.  Abu zarril giffari ya kasance sabanin sauran musulmai a lokacin da ya musulunta bai zauna a makka ba, shi komawa ya yi wajen kabilarsa har bayan da Manzo (saw) ya yi hijira bai koma madina ba da ma lokacin yakoki badar da uhudu da khandak duk a lokacin yana tare da kabilarsa har ya zuwa bayan lokacin yakin kahndak sannan ne ya zo madina wajen Manzo (saw) kuma ya ci gaba da zama a madina har lokacin har Manzo (saw) ya yi wafati.  Kuma har zuwa lakacin da halifa na farko ya muta Abuzarri ya ci gaba da zama a madina.
Abuzarri ya kasance daga cikin sahabbai masu harshe mai tsage gaskiya da jarumtaka kuma kowa ya san shi da haka har ma an rawaito cewa Manzo (saw) ya ce: ya daukar Manzo (saw) alkawrin cewa kyamar mai kyama ba za ta taba sawa ya juya baya . Kuma wannan ruwayar mai zuwa na nuna matsayin Abuzarri na musamman “sama ba ta lullube wani ba kuma kasa ba ta ba ta dauki wanu mutum ma’abocin baki da ya kai Abuzarri gaskiyar harshe ba”.  
Bayanin wannan ruwayar kan matsayin mai girma ya sa wasu daga cikin ‘yan shi’a shun shuga rudani cewa kenan Abuzarri ya fi ahlulbaiti ma matsayi kenan k kuwa? Daya daga cikin ‘yan shi’a ya tambayi imam sadik kan wannan ishkalin: shin Manzon Allah Ta'ala (saw) bai fade cewa: “sama ba ta lullube wani ba kuma kasa ba ta ba ta dauki wanu mutum ma’abocin baki da ya kai Abuzarri gaskiyar harshe ba”? sai imam ya ce eh haka ne. Sai ya tambaya: to Manzo (saw) da imam Ali (as) da hasan da husai (as) suna cikin su wa?, imam sadik a wajen ba shi amsa sai ya ce da shi a tsawon shekara wata nawa muke da shi? Sai ya ce sha biyu, sai ya ce watanni masu alfarma guda nawa ne a cikinsu? Sai mai tambayar ya ce: guda hudu ne. Sai ya ce shin watan ramadhan na cikinsu? Sai ya bada korarriyar amsa. Sai imam ya ce sai ya ce tabbas a cikin watan ramadan akwai wat arana wacce ta fi wata dubu, kuma mu ‘yan gida ne da ba’a auna mu da ko wadanne irin mutane”.
Abuzarri ya kasance mai tsage gaskiya da fadin hakikar abu har zuwa karshen rayuwarsa kuma ta yiyu wanna shi ne dalilin da ya sa aka kore shi wanda hakan ya zama sanadiyyar wafatinsa a karshe, kuma ya kasance daga cikin daidaikun mutane na kusa kusa da imam Ali (as), kuma bayan faruwar aika aikar Sakifa Abuzarri shi da wasu ‘yan tsirarun sahabbai na daga cikin wadanda suka wanzu a gefen  imam Ali (as) kuma suka ksance daga cikin shi’arsa na kurkusa wannan tafakin na sa ne ya sa aka rawaito hadisai masu yawa kan yabonsa. Imam Ali Al ridha (as), yan cewa: “ son aminrul muminin imam Ali (as) wajibi ne kasa ma son wadanda suka wanzu tare da shi ba su chaja ba ba su bada baya ba ga barin addini kamar su salmanul farisi da Abuzarril Giffari da mikdad dan aswad da Ammar dan Yasir dss Allah Ta'ala ya kara yarda a gare su ya yi musu rahama”.  
Bayan mutuwar halfa abubukar Abuzarri ya yi hijira zuwa sham, amma nisantarsa daga madina baya nufin ya yi nisanta daga musulunci, kuma ya zauna a can har zuwa lokacin halifancin usman
Da ya bada umarni a dawo da shi madina, kuma dalilin bada wannan umarni shi ne, a cen syria Abuzarri ya zame wa Mu’awiya karfen kafe a fagen yakar budi’o’in da mu’awuya yake ta kirkiroka, ya tsaya kyau da harshensa na gaskiya a gaban mu’awuya kuma yana yin fito na fito da munanan ayuukan mu’awuya a sham yama wayer da mutane kan addininsu da hakkokinsu. Doh haka ne mu’awuya ya rubuta wa suman wasika yana nuna masa hadarin Abuzarri a Sham.  Bayan dawowar Abuzarri madina bai rufe bakinsa ya yi shiru kar barnar da usman  ke yi ba, kai har ma sai da suka yi sa- in- sa mai tsananin da ta fatar baki da usman a gaban sahabbai.  Daga karshe sai usman kore shi zuwa rizbah kuma a can ne Abuzarri ya zauna har ya yi wafati a shekara ta 33 bayan hijira, sannan Abdullahi zan mas’ud ya yi masa salla.  
A lokacin da ya yi haramar tafiya rizba imam Ali (as) ya yi masa tattaki sannan ya gaya masa wannan maganar: “ ya Abazarri kamar yadda ka yi fushi saboda Allah Ta'ala to ka zama kana da fatan ka kadai kan wanda  ka yi fushi saboda shi. Hakika wadannan mutanen suna jin tsoronka ne kan duniyarsa kai kuma kana jin tsoronsu kan addinika, don haka ka bar musu duniyarsu da suke jin tsoronka saboda ita kuma ka rike addinika wanda kake jin tsoronsu a kansa ya tsananin bukatuwarsu kan abin da kake tsaratar da su a kan sa na duniya. Kuma ya tsananin wadatuwar ka zuwa abin da ka hana su kuma ba da dadewa ba za a gane waye ya ci riba gobe, kuma wa ya fi kyakkyawar makoma, da ace sama da kasa za su hada da bawa sannan ya kasance ya ji tsaron Allah Ta'ala to da sai Allah Ta'ala ya ba shi mafita, kar ka taba samun nutsuwa da wani abu sai gaskiya kuma kada ka taba dimaucewa da wani sai bata da barna, da ka karbin duniyarsu da sun so ka, kuma da ka dan ci wani abu daga cikinta da sun kyale ka”.  Wannan bayanin da imam Ali (as) ya yi ya bayyana hakikanin yadda Abuzarri ya ke tare da kokawa kan matakin da ka dauka kan Abuzarri na nisanta shi ka korar shi daga cikin al’umma.


Na fassaro daga sait din islamquest.net
Munir Muhammad Said Alkanawi

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)