Asasin Addini da Rassansa
Asasin Addini da Rassansa
Allah ya shaida cewa; Lalle ne babu abin bautawa sai shi, kuma mala’iku da ma’abota ilimi sun shaida, (ubangiji) yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face shi, Mabuwayi, Mai hikima. Lalle ne addini a wurin Allah shi ne musulunci …[1] Shimfida
Da Sunan Allah Mai Rahamn Mai Jin kai
Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin annabawa da manzanni da alayensa tsarkaka
Muhimmancin bahasi kan akidar musulunci yana kafuwa ne a kan asasin da samuwar musulumi take doruwa a kansa ne, sakamakon haka ne ya sanya zamu ga kur’ani ya sanya akida ita ce kashin bayan kaiwa zuwa ga Allah (s.w.t).
Madaukaki ya ce: “Zuwa gare shi ne kalma mai tsarki take hawa kuma yana daukaka aiki na gari”[2].
Abinda ake nufi da kalma ta gari shi ne akida ta gaskiya wacce mutum yake arzuta ta hanyar riko da ita ya kuma gina ayyukansa a kanta, kuma wacce ake da yakini da ita, ita ce kalmar tauhidi da dukkan sauran abubuwan kudurcewa suke komawa zuwa gareta kuma daukakar akida tana tare da girman abin kudurcewa.
Na’am aiki na gari yana da muhimmiyar rawa da zai taka wanda ya hada da kiyaye tabbatar akida da kuma karfafa ta, domin duk sa’adda aiki ya maimaitu sai kudurcewa da shi ta dada kafuwa da daukaka kuma tasirinsa ya karfafa, idan aiki na gari ya kasance saboda Allah ne sai ya taimaki akida ta gari ta karfafa.
Hanyoyin da a kan bi wajan tabbatar da samamme na farko madaukaki, sun kasu kashi daban-daban sakamakon ma’abota dalilan suna da mahanga mabanbanta, kuma saudayawa yakan zama an fara da dalili na hanakli kafin na nakali -Kur’ani da ruwaya- da ya hada da dalilin wanda aka samar a kan cewa akwai mai samarwa, da dalilin tsari a kan samuwar mai tsarawa, da dalilin mu’ujiza a kan gaskiyar annabtar mai da’awarta. Hankali yana riskar samuwar Allah wanda shi ne mai samarwa mai tsarawa mai samar da dukkan samuwa.
Sannan duk sa’adda mai da’awar annabta ya zo da mu’ujiza sai hankali ya yi furuci da ita, sannan sai shari’a ta karfafa abin da hankali ya riska, yayin nan sai ya zamanto wajibi ne a kanmu mu bi shi muna masu koyi da shi da zancensa, da ayyukansa, da abin da ya tabbatar, mu kuma yi aiki kur’ani da ruwayoyi da sauran al’amuran da zasu zo bayan haka. Don haka ne yake a fili cewa ilimin sanin Allah wato akida shi ne ilimi na farko kuma mafi daukaka.
Akida, ko ilmul kalam, ko ilahiyyat, duk suna da ma’ana daya ne, wanda yake nufin ilimin da yake bincike game da samuwar Allah da siffofinsa da ayyukansa ta hanyar kafa dalili a kan samuwar Allah da kadaitakarsa da kuma magana kan siffofinsa subutiyya da salbiyya, da kuma adalcinsa, sannan sai aiko annabawa da kuma halifancin wasiyyansu, har zuwa ga ranar sakamako da hisabi, wadannan a dunkule muna kiransu da ayyukan ubangiji madaukaki, kuma wadannan su ne usuluddin:
Tauhidi Da Adalci Da Annabci Da Imamanci Da Alkiyama.
Yawancin dalilan da zamu kawo a cikin wannan ‘yar makala sun shafi na mutakallimin (malaman ilimin sanin Allah) ba na malaman falsafa ba, don haka mun yi shi yadda malami da dalibi zasu iya dubawa, amma ba mu rubuta shi domin masu falsafa tsantsa ba, domin wannan yana bukatar matsayin da ya fi wannan ne, kuma shi ma muna shirya shi da zai zo nan gaba in Allah ya so, koda yake waccan marhalar ba ta da amfani ga mutane sai ‘yan kalilan, don haka saudayawa mukan bayar da karfi ne wajan rubuta abin da kowa zai iya amfana da shi.
Wannan ‘yar makala zata yi bincike game da shika-shikan addini a bisa dalilai na hankali da nakali -kur’ani da sunnar annabi da alayensa (a.s)- muna masu kaunar ubangiji ya karba daga garemu ya kuma kyautata mana, ya kuma sanya shi ajiya garemu ranar sakamako. Muna rokon Allah ya sanya wannan risala gajeriya mai amfani ga ‘yan’uwana muminai, kuma ya ba mu dacewa da arzutar duniya da lahira.
Menene Addini? Muhimmancin Addini Da Matsayinsa? Musulunci? Usuluddin Da Furu’a
Usuluddin?
Menene Addini
Addini a luga: biyayya: Allah madaukai yana cewa: “Biyayya gaba daya tasa ce”[3]. Ma’ana: biyayya da da’a dawwamammiya tasa ce”.
Haka nan yake cewa: “Ba sa biyayya da biyayya ta gaskiya”[4].
Kuma kalmar addini ta zo da ma’anar sakamako kamar fadinsa madaukaki: “Mamallakin ranar sakamako”[5].
Don haka kalmar addini a luga tana nufin sakamako ko biyayya[6].
Addini a isdilahi: shi ne imani da mahaliccin halitta, da mutum, da kuma koyarwa, da ayyukan da suke da tushe da asasi daga karkashin wannan imanin.
Saboda haka ne ma ake kiran wadanda ba su yi imani da mahalicci ba da marasa addini[7].
Muhimmancin Addini
Wasu suna iya cewa menene amfanin addini? Me zamu samu daga gareshi? Kai wasu ma suna da’awar cewa akwai cutuwa a addini.
Sai mu ce: Addini shi doka ce ta Allah da take tsara rayuwar dai-daikun mutane da jama’a gaba daya, domin kai wa ga kamala da daukaka a dukkan fagagen rayuwa masu muhimmanci da suka shafi rayuwar mutum wanda ya hada da;
Gyara Masa Tunani Da Akida Da Tsarkake Shi Daga Camfi Da Surkulle:
Addini yana fassara mana hakikanin yadda samuwa take da kuma cewa akwai mai samarwa, masani, mai iko, da ya halicci dukkan halitta da kuma asalinta, da iyakance asalin da dokokinta. Kamar yadda yake fassara ma’anar rayuwar mutum da cewa ba haka nan kawai ta ke ba, ba a halicci mutum don wasa ba, sai domin wani hadafi babba da zai kai zuwa gareshi ta hanyar biyayya ga koyarwar da annabawa da masu shiryarwa suka zo da ita daga Allah.
Karfafa Asasin Kyawawan Dabi’u
Akida ta addini ita ce madogara mai karfi ta asasin kyawawan dabi’u, domin sanya dokoki da daure mutum da su yana sanya masa wahala da kuma bukatuwa zuwa ga juriya da mutum zai yi, kuma jure su ba ya yiwuwa sai da imani da Allah da zai saukaka su, da kuma kwadaitar da mutum zuwa ga sadaukar wa ta hanyar gaskiya da adalci da taimakon raunana.
Kyautata Alakar Zamantakewa:
Akidar mutum ta addini tana karfafa asasin zamantakewa domin zata sanya mutum ya zama mai addini da kuma lizimtar takalifi da bai halatta ya saba masa ba kamar sadar da zumunci da girmama iyali da sauransu.
Jefar Da Bambance-bambance:
Addini yana ganin mutane dukkansu halittu ne na ubangiji guda daya, kuma dukkansu a wajan Allah daya ne ba bambanci tsakanin balarabe da ajami da fari da baki[8].
Wadannan al’amura guda hudu suna nuna mana muhimmanci mai girma a fili da addini yake da shi, kuma bayan haka ba zai yiwu ga wani ba ya bar addini domin gudun kada wani nauyi ya hau kansa ko son hutu da holewa, ko kuma domin addini yana sanya wa mutum dokoki da zasu hana shi aiwatar da abin da ransa ta ga dama.
Kur’ani mai girma yana siffanta irin wadannan mutane da su ne mafi bata daga dabbobi: “Mun sanya wa jahannama dayawa daga aljnu da mutane da suke da zuciya da ba sa tunani da ita, da kuma idanu da ba sa gani da su, da kunnuwa da ba sa ji da su, wadannan kamar dabbobi suke, kai sun fi dabbobi bacewa, kuma wadannan su ne gafalallu”[9].
Ina karawa da cewa; duba ga irin wadannan fa’idoji da addini yake da shi imani da mahalicci da aiki da hakan koda an kaddara da cewar babu shi ya fi zama abin hankalta a kan rashin yarda da hakan, domin idan an koma masa; idan an kaddara babu shi to da mu da wadanda ba su yi imani da shi ba mun zama daya, amma idan akwai shi fa! kenan mun tsira su kuma sun halaka.
Musulunci
Musulunci yana da ma’ana biyu; gama-gari da kuma kebantacciyar ma’ana wadanda zamu kawo bayaninsu kamar haka;
Musulunci da ma’ana gama-gari:
Shi ne karkata da mika wuya zuwa ga Allah da abin da ya saukar na shir’a da hukunce-hukunce.
Allah madaukaki ya ce: “Kawai addini a wajan Allah shi ne muslunci”[10].
Musulmi shi ne wanda ya mika wuya ga abin da aka saukar na shari’a daga Allah, saboda haka akwai musulunci tun lokacin annabi Adam (a.s) da Nuhu da Ibrahim da Musa da Isa (a.s) da kuma cikon manzanni da annabawa Muhammad (s.a.w).
Musulunci da ma’ana kebantacciya:
Shi ne addinin da manzo Muhammad Dan Abdullahi (s.a.w) ya zo da shi, muslmi shi ne wanda ya yi furuci da harshe yana mai cewa; “Na shaida babu abin bautawa sai Allah, kuma na shaida Muhammad manzon Allah ne”. Ana kiran wannan da kalmar shahada da take kunshe da shaidawa biyu.
Don haka sakamakon wannan furuci yana tilasta rashin musun duk wani abu laruri na akidar musulunci da huknce-hukuncensa, da kuma rashin musun annabtar annabawa da suka rigaya suka gabata da aka ambace su a kur’ani mai girma, wato kada ya yi musum wani abu da musulmi suka hadu a kansa gaba daya kamar wajabcin salla da azumi da hajji, da haramcin shan giya da cin riba, da sauransu.
Musulunci tsarkakakke shi ne cikon addinai, domin shi ne mafi kamala da cika wanda ya zo daga Allah da ake bukatar mutum ya mika wuya zuwa gareshi[11].
Saboda haka ne ma ba a karbar wani addini sai shi: “Duk wanda ya nemi wani addini ba musulunci ba, ba za a karba daga gareshi ba, kuma shi a lahira yana cikin masu hasara”[12].
Usuluddin Da Furu’arsa
Addinin musulunci addini ne na duniya gaba daya da ya game komai, kuma yana dogara bisa rukuni biyu ne na asasi:
Usuluddini: su ne asasi tabbatattu da ba sa sabawa komai sabawar al’ummu kamar Tauhidi da Adalci da Annabci da Makoma. Wadannan su ne shika-shikan addini.
Furu’uddini: su ne janibin shari’a, wanda yake kunshe da koyarwa, kuma da kyawawan dabi’u da suka zo domin maslahar mutum da al’umma gaba daya da kuma rabautar duniya da lahira, bai kebanta da wasu jama’a ba su kadai. Wadannan su ne rassan al’amuran addini[13].
Shika-shikan Addini
Kamar yadda aka sani cewa addini yana da jiga-jigai da kuma rassan al’amuransa. Asasi ko ginshiki yana nufin doka da ka’idar da addini ya doru a kanta, ana cewa da tauhidi da adalci, da annabci, da imamanci, da makoma ranar lahira, wato: shika-shikan addini.
Zai iya yiwuwa a wajenmu bahasin imamanci ya shiga karkashin annabci, kamar yadda adalci yake shiga karkashin bahasin tauhidi, sai su koma guda uku: Tauhidi Da Annabci Da Makoma.
Yana wajaba a kan kowane baligi ya san shika-shikan addini da bayanansu zasu zo nan gaba dalla-dalla[14], in Allah ya so.
AN CIRO DAGA www.haidarcenter.com
[1] – Surar Ali imrana: 18 – 19.
[2] Fadiri: 10.
[3] Nahal: 53.
[4] Tauba: 23.
[5] Fatiha: 3
[6] Almunjidul abjadi: 454.
[7] Durusun fil akida, Yazdi, J 1, shafi: 25.
[8] Muhadharatun fil ilahiyyat, Subhani, shafi: 13 – 14.
[9] A’arafi: 179.
[10] Ali Imarana: 19.
[11] Albabul hadi ash’ra: 2. Da kuma, Aka’idul islam: 1/182.
[12] Ali Imrana: 85.
[13] Ulumul kur’an, durusun manhajiyya: 31.
[14] Hayatun nafsi wa usulul aka’id: 8.
HAIDAR CENTER