TABIYYA A MUSULUNICI
TARBIYA DA KOYARWA
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Allah madaukaki cikin littafinsa mai daraja ya na cewa:
هو الذي بعث في الأميين رسولا منهم يتلو عليهم آياته ويزكيهم ويعلمهم الكتاب والحكمة[1]
shi ne wanda ya aiko manzo cikin mutanen da basa karatu da rubutu daga gare su ya na karanta ayoyinsa a kansu yana tsarkakesu ya na sanar da su littafi da hikima )
dukkanin wani gari da ya ginu da cigaba cikin wannan zamani da muke ciki dole ne ya kasance cikin ma'aikatu akwai ma'aikatar tarbiyya da koyarwa kuma ya zamanto ya na da kwalejin tarbiyya da kuma kasancewa ya na da littafin tarbiyya da darasinta cikin makarantun jami'o'i da firamare da ragowar makarantu saboda rabautar dan adam na tattare cikin iliminsa da tarbiyarsa, kamar yadda cigaban dukkanin wani gari da al'ummarsa na tattare cikinta, addinin muslunci ya qafa wadannan asasi guda biyu tarbiyya da koyarwa cikin rayuwar dan adam cikin rayuwarsa shi kadai da kuma rayuwarsa da ragowar jama'a , haqiqa qur'ani ya yi nuni kan hikimar turo annabi mai daraja da cewa annabtarsa ta tattaru kan abubuwa biyu sune tarbiyantarwa da koyarwa: يزكيهم ويعلمهم ya tsarkakesu ya sanar da su. tsarkakewa ta na nufin tarbiyya kalmomin biyu na da matsayi guda kamar fuka-fukan tsuntsune bangaren dama da bangaren hagu haqiqa dan adam idan ya so tashi zuwa sararin samaniyar darajoji da sassan ma'arifa ya samu qololuwar rabauta da kamala hakan kadai na kasancewa ne ta hanyar tarbiyya koyarwa dole ne su kasance bai daya, a na dai kawai gabatar da bayanin tarbiyya kan koyarwa ta fuskacin muhimmancin tarbiya ba don tarbiyya da har abada dan adam ba zai amfanu da iliminsa ba da iliminsa ya zame masa katanga mafi girma gabarin gaskiya da qara nesanta daga ita. haqiqa ya fada cikin qasqanci da wulaqanta babu ilimi matukar babu tarbiya, batun tarbiyya ya tattaro dukkanin muhimmancin shari'a da zamantakewa cikin tarihin bil adama har sai da ta kai ga zama mafi girman batu cikin dukkanin makarantun tunani da na ubangiji .
cikin tarihin wannan zamani da muke ciki rubuce-rubuce kan tarbiya sun cika maqil albarkacin taka rawar da ta yi wajen fadakarwa da gina iyali da canja al'umma ta yanda ake la'akari da ita tushe wajen gina iyali kuma maudu'i wajen canja zamantakewa wannan wani tushe ne da ya mamaye gurbin da ya dace da shi cikin ginin muslunci da tarihin musulmi na baya da na yanzu saboda muslunci qari kan gabatarsa kan mazhabobi da aqidoji na zamani to haqiqa ya tattaro fusaken wayewa cikin hukunce hukuncenshi da ilimansa bari ma dai cikin gabadayan tsarin muslunci ya mai da hankali kan batun tarbiyya kuma ya dayantu da taka rawa kan gina tarbiya cikin rayuwa kowanne mutum da al'umma ballantana ma iyali, muslunci bai qasa a gwiwa ba wajen zurfafar tarbiyya da qoqarin dawo da sigar mutum da matakinsa na kankin kansa da dangantakarsa cikin al'umma da jama'a abinda zai sanya dacewa tare da tanadin halittarsa da aka halicce shi kanta da abinda zai bashi tsari ya motsa shi cikin tsare tsaren tauhidin ubangiji don ya wayi gari halifa na gaskiya . bin da muke nufi anan da tarbiyar halitta shi ne wacce ta ratayu da duniyar halitta, fitar abin da ke da qarfin afkuwa nan gaba da iko ya zuwa tanade tanade lokaci ya zuwa lokaci ya zuwa haddinsa kammalalle cikin wannan duniyar halittu saqi babu qaidi a duniyar jikkuna da abubuwa da basu da jiki sai dai su bijirowa jiki kamar launi, babu banbanci cikin duniyar halittun sama da qasa, babu banbanci cikin duniyar mutum a kankin kansa da waninsa, ana kiran baki dayan wadannan da tarbiyyar duniyar halitta, kasantuwar maniyyi gudan jini daga gudan jini zuwa tsoka sannan qashi sannan a lullufe qashi da tsoka, sannan a haife shi jariri ya dinga tsallake marhaloli daga duniyar jinjirantaka ya zuwa yarinta ya zuwa samartaka daga nan ya tsallaka ya zama kammalallen mutum daga nan zuwa dattijantaka daga nan ya zuwa tsufa da gazawa dukkanin wannan na cikin tarbiyyan halitta na halittarsa cikin wannan duniya, mai tarbiya na farko ga wannan duniya shi ne ubangijin talikai.
amma tarbiyar shari'a: muna nufin hukunce hukunce shari'a wadanda Allah madaukaki ya saukar cikin littafan annabawa (as) don shiriyar da mutane da tarbiyantar da su tarbiyya ta `yan adamtaka malakutiyya, haqiqa qarqashin tarbiyarsa ta shari'a mutum ya na iya kaiwa ga tsakanin qaba qausaini daga kamala da rabauta madawwamiya ya rabauta cikin rayuwarsa da bayan mutuwarsa, domin addini ya zo don rabautar da mutane da shiryar da su hanya miqaqqa ya sanar da su yadda za su rayu da yadda ya kamata su mutu, tarbiyya ba komai ba ce face matattakala da tsani na samun rabauta duniya da lahira.
WANENE MAI TARBIYA ?
mai tarbiya na farko cikin duniyar halitta da dabi'a da abin da ke qunshe bayanta shi ne Allah matsarkaki , haqiqa shi ne ubangijin talikai, haqiqa kalmar رب da abubuwan aka keto daga gare ta sun zo cikin qur'ani har kusan wurare (980) qur'ani ya tattaro mutanen farko da wanda za su zo daga baya haqiqa shi qur'ani ya tattara dukkanin abinda ke cikin littafan sama da addinan ubangiji, shi littafi ne mai gadi kan littafan sama da qasa, shi ya tattara dukkanin iliman magabata da wanda za su zo daga baya, sannan an tattara abin da ke cikin qur'ani cikin surar fatiha, surar ta fara da fadinsa madaukaki:
الحَمْدُ للهِ رَبِّ العَالَمِينَ[1]
(godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai)
sai ya siffanta kansa da ubangijintaka, haqiqa shi ne mai tarbiya na farko ga dukkanin duniyoyi madaukaka da akasinsu, da abubuwa mujarradai marasa jiki da masu jiki, saboda kare dokokin sabubba wanda ke jagorantar wannan duniya sai Allah ya sanya
فَالمُدَبِّرَاتِ أمْر[2]ا
sa'annan su kasance masu shirya gudanar da al'amari.
ta kasance sanadin samuwar abubuwa da dokokin tarbiya ke jagorantarsu dukkanin wannan kadai ya kasance bisa rahamarsa duniya da lahira.
Sannan tarbiya ta yi tajalli da dauko iliman ubangiji cikin annabawa (as) haqiqa su annabawa sune mabayyanar tarbiyyar ubangiji haqiqa ya aiko su don tarbiyar mutane da shiriyar dasu da tsayar da adalci da daidaito haqiqa annabi ya kasance mabayyanar ubangijintakar ubangiji, bauta zinare ne wanda zurfafarsa ubangijntaka, annabi muhammadu ya kasance cikamakin annabawa shugaban manzanni bawan Allah manzonsa .
sannan bayan annabawa wasiyyai da imamai (as) sun kasance kan tafarkinsu da hanyarsu da shiriyarsu, sun kasance mabayyanar tarbiyar ubangiji da annabi, an daura nauyin tarbiyyar mutane da shiryar da su a wuyayensu, sannan kuma bayansu nauyin ya koma kan malamai domin sune magada annabawa da wasiyyai cikin iliminsu da dabi'unsu da dukkanin matsayin da suke da shi, haqiqa su anayi musu hukunci da magadan da aka dora musu nauyin tarbiyyar mutane bayan sun tsarkake kawunansu da badininsu da ilimantuwa sannan sai su fito ya zuwa ga mutane zuwa ga abin da zai rayasu su rungumi daukar nauyin tarbiyantarda su tarbiyya ingantacciya ta gargaru.
da hukuncin malamai nagargaru iyaye maza da mata sune suke tarbiyya cikin iyali da dangi kamar yadda malamai suke tarbiyya a fagen makarantu da fagagen koyarwa, haka al'amarin ya ke cikin ragowar fagagen rayuwa, haka ma cikin ragowar mutane dole a samu wani mai tarbiyantarwa da koyarwar saboda hakan na daga sunnar ubangiji kuma ba za ka taba samun sauyi ko canji cikin sunnar ubangiji
wadannan da muka kawo dukkaninsu mabayyana ne na ubangijin talikai a muqamin tarbiyya, abin da sukayi tarayya ciki shi ne tarbiyya amma sukan banbanta a bangaren fadadawarta da tsukewa bisa la'akari da fadin duniyar da take cikin kowanne dayansu.
misali cikin ilimin mandiki mas'alolin nazari dole su tuqe ga badihiyat (sanannun abubuwa ) ma'ana zatin abubuwa saboda shi zatin abu bai buqata kawo dalili kansa,ba don hakan ba da ya lazimta maimaici da tasalsul wanda gurbatattu ne a mahalinsu, saboda haka iliman nazari na tuqewa ya zuwa muqaddimar badihiyya na zati haka al'amarin ya ke cikin tarbiya da mai yinta haqiqa ita ma tana tuqewa ga tarbiya ta zati wacce ta ke tarbiyya ce ta ubangiji da ta bubbugo daga rububiyarsa girmansa ya girmama, iyaye masu tarbiyya ne da suke komawa ga malamai cikin tarbiyantar da kawukansu, su kuma malamai na koma ga annabawa da imamai (as) wanda ke dauke da tarbiyyar zati haqiqa su kuma imamai (as) suna komawa ga Allah ubangijin talikai domin shi ne mai tarbiyya na farko, sai tarbiyyarsa ta halitta cikin halittu da ta shari'a su yi tajalli cikin halittunsa, haka cikin annabawa malamai da iyaye, tarbiyya da ke bijira wadda a ke tsiwirwirarta a wannan lokaci na tuqewa ya zuwa tarbiyyar ta zati tabbatacciya sai a lura.