Wanen Halifan Annabi (s.a.w)
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
WANE NE HALIFAN ANNABI (S.A.W)?
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ake ga ne shi idan anyi duba zuwa ga halittunsa, wanda ikonsa da iliminsa ke hukunta rashin gajiyawarsa, wanda ya girmama daga masu siffantashi zuwa ga jiki, wanda ya girmama daga nakasa ko wace iri, wanda yake gigitar da masu tunani a kansa, wanda idanuwa basa iya riskarsa, muna gode masa godiya irin ta bayi managarta, muna godiya akan ni’imominsa wandanda basu da iyaka, muna gode masa a kowanne hali.
Tsira da aminci su kara tabbata ga Annabinsa Muhammad (s.a.w) ma’abocin ayoyi da bayanai cikakku wanda ya tabbata akan hanyarsa da shari’arsa cikin kamala, da kuma iyalen idansa masu shiryarwa daga bata zuwa gaskiya, wadanda Allah ya tsarkake su daga dukkan datti tsarkakewa, ya Allah kayi salati garesu har ya zuwa ranar sakamako.
Bayan haka tabbas Allah madaukakin sarki bai halicci wannan duniya don wasa ba, balantana ya kasance daga cikin masu wasa, sai dai abin sani yayi halitta ne saboda gayar hikima tabbatacciya ga masu tunani kuma ya yi bayani akan haka a cikin littafinsa mai tsarki, inda yake cewa: {{ وماخلقت الجن والانس الا ليعبدون }{ Ban halicci Mutum da Aljani ba sai don su bauta mini}(1) .
Sai dai karan bani gigiwa da rashin sanin maslaha irin ta Mutane tasa mun shiga wani abu daban sabanin hakikar manufar halittar mu, haka kuma mutum ya kasa gane Ubangijinsa da yayi masa ni’ima balantana ya gode masa akan ni’imar da yayi masa, mai makon haka ma sai ya jefa kansa cikin halaka. Daga cikin abu mafi wahala a rayuwar dan Adam shine karbar gaskiya wacce a mafi yawan lokuta maslahar rayuwarsa ce .
Daya daga cikin mas’ala dake sa kai ruwa rana a tsakanin al’ummar musulmi a lokuta daban-daban ita ce mas’alar khalifanci bayan Annabi, hakika al’ummar musulmi sunada sabani sosai akan wannan batu na halifanci bayan Manzon Allah (s.a.w), kamar cewa: shin wane ne Halifan Annabi? A wannan rubutun zamu kalli wannan mas’ala da kyau don gane hakikanin gaskiyar wannan magana tsakanin bangarorin al’ummar musulmi, zamu duba muga shin wa ya kama ta ya zama Halifan Annabi? Zamu nemo dalilai na hankali da na ruwaya akan wannan batu. Kuma bana nufin saba kowa akan abin da nake kiran ku zuwa gareshi, bana nufin komai face gyara gwargwadon damar da na samu. Bana neman da cewa ga kowa sai ga Allah, A gare shi na dogara kuma zuwa gare shi na ke tawakkali.
ALI NE HALIFA BAYAN ANNABI (S.A.W).
Dalili na hankali a kan halifancin Aliyu (a.s).
Wani abu da dukkan mutum mai hankali zai iya hukuntawa shine, a duk lokacin da wata ma’asla ta ta so, ana neman wanda yafi sani yake kuma da tajjiriba akan abu, misali kamar mara lafiya yana neman likitan da yake kwararren ne a kan sauran likituci wanda yake da kwarewa sosai, ba yanda za a yi yana kallon kwararren likita sai ya barshi ya tafi wajen wanda bai kai shi kwarewa ba, wannan ya saba wa aikin mai hankali a ko ina. A wani bayanin na daban kuma zamu iya cewa: dole ne a gabatar da wanda yake da fifiko akan komai domin gabatar da wanda bai kai shi ba wannan rashin hankali ne.
Yadda kur’ani ya gabatar da ma’abocin falala akan wanda bai kai shi ba. Wannan bato yazo a kur’ani dama ruwayoyi misali ga wannan ayar da take cewa:
{ أفمن يهدي الي الحق أحق أن يتبع أم من لايهدي الا أن يهدى فمالكم كيف تحكمون }
{{ Shin wanda yake shiryarwa ne mafi cancantar a bi shi, ko kuwa wanda baya shiryarwa face dai shi a ke shiryarwa? To minen a gare ku yaya kuke yin hukunci?}}(1) .
Ko kuma wannan ayar mai girma da ke cewa: {{ Shin wadanda suka sani zasu yi dai dai da wadanda basu sani ba. {هل يستوى الذين يعملون والذين لا يعلمون}.
Da kuma ruwayoyin da suke nuni a bisa gabatar da wanda yafi falala:
A littattafan shi’a da sunna akwai ruwayoyi da daman gaske da suke nuni akan gabatar da ma’abocin falala, misali ga wata ruwaya da ibnu Abbas ya nakalto:
{ من ولي من المسلمين شيئا من أمورالمسلمين وهو يعلم أن فى المسلمين من هو خير للمسلمين منه, فقد خان الله ورسوله وخان جماعةالمسلمين }(3) .
(( Duk wanda ya jagoranci musulmai wani abu daga cikin al’amuran musulmai alhali tabbas yasan cewa daga cikin musulmai akwai wanda yafi shi alkairi ga wannan abun, hakika ya ha’inci Allah da Manzonsa ya kuma ha’inci al’ummar musulmai)).
FIFIKON IMAM ALI (A.S) A KAN SAURAN SAHABBAI.
Idan muka ce zamu kawu siffofin Imam Ali (a.s) tufa sauran sahabbai zasu zamo fanko wadanda suka gaza, sannan zamu gane cewa tabbas Ali (a.s) shi ne ya cancanci jagorantar al’ummar musulmai bayan Annabi (s.a.w), saboda haka a nan zamu kawu wasu daga cikin siffofin Imam din wadanda a hankalce zasu tabbatar mana da cancantar sa wajen al’amuran musulmai.
Na farko: Ilimin Ali (a.s)
Dangane da ilimin Imam Ali (a.s) ga wasu daga cikin hadisai mutawatirai da wasu daga cikin littattafan Sunna suka ruwaito: An nakalto daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ( Ni ne Birnin ilimi Aliyu kuma kofarsa duk wanda yake son ilimi to yazo ta kofar shi)
[ أنامدينة العلم وعلي بابها فمن أرادالعلم فليأت من بابها](4) .
Ibnu Abbas yana cewa: hakika kaso casa’in (90) cikin dari 100 na ilimi (90% ) an bawa Ali (a.s) ne, kaso goma 10% kuma sauran mutane, ina rantsuwa da Allah tabbas Aliyu ya yi tarayya da sauran mutane a cikin kaso goman.
Da kuma dai wata ruwayar duk dai daga Ibn Abbas din ya ce: ( Ilimi na da ilimin Sahabban Annabi idan aka hada su da ilimin Ali kwatan kwacin dugo ne daga cikin Tekuna bakwai.
[ لقد أوتي علي تسعة أعشارالعلم, و أيم الله لقد شار كهم فى العشر العاشر](5) .من ابن عباس قال : وأيضا[ وما علمي وعلم اصحاب محمد فى علم علي الا كقطرة فى سبعة ابحر ](6) .
Haka ma daya daga cikin matan Manzon Allah (s.a.w) ta yi shaida a kan ilimin Ali (a.s), (A’isha) ta ce: { Aliyu ne mafi sanin mutane Sunna}{ علي أعلم الناس بالسنة}(7) .
Sa’id dan Musaiyab yana cewa: { Babu wani daga cikin Sahabbai da ya ke cewa ku tamyeni sai Aliyu bn Abi Dalib (a.s).
{ لم يكن أحد من الصحابة يقول سلوني الا علي ابن ابى طالب (ع)}(8) .
Tabbas ilimin Aliyu bn Abi Dalib sannan abu ne a tsakanin Sahabban Manzon Allah (s.a.w) wanda baya bukatuwa zuwa yin wani sharhi ko karin bayani ta yanda a gurare da daman gaske Aliyu (a.s) ya warware matsalolin halifufi da man gaske ta yadda wasu daga cikin ruwayoyin Ahlussunna suka tabbar da cewa sama da sau saba’in 70 aka na kalto wannan jumala daga bakin halifa na biyu inda yake cewa:{ لولا علي لهلك عمر}( Ba don Ali ba da Umar ya halaka)(9) . Da kuma sananniyar magnarsa cewa: ( Ina neman tsari ga Allah kada yasa a bijiro min da wata tambaya mai wahala Baban Hasan baya nan(10) . {اعوذ بالله من معضلة ليس لها ابوالحسن }.
Wannan jumala ta Umar tana tabbatar da cewa Aliyu bn Abi Dalib shi ne wanda yafi dukkan Sahabban Annabi ilimi.
Haka kuma idan muka kalli ayar mubahala zata tabbatar mana da cewa Aliyu shi ne gaba a kan dukka nin Shabban Manzon Allah (s.a.w) miyasa saboda siffan ta shi da aka yi da irin siffar Manzon Allah (s.a.w) cewa shi da Manzon Allah (s.a.w) duk abu guda ne, sannan sananen abu ne cewa duk wanda zai gaji Annabi tabbas ilimin sa da na Annabi abu guda.
JARUMMATAR IMAM ALI (A.S).
Ahlusunna ma sun tabbatar da jarumkatar Aliyu bn Abi Dalib (a.s) a kan sauran Sahabbai, domin kuwa sun nakalko ruwaya a kan jarumtar Aliyu daga bakin Halifa na biyu inda yake cewa:
(( والله لولا سيف علي لما قام عمود الدين)) ya ce: ( Ina rantsuwa da Allah ba don takobin Ali ba da addini bai tabbata ba)(11) .
Haka ma munsan cewa Annabi (s.a.w) a yaki daban-daban ya tabbatar da jarumtar Aliyu (a.s) misali a yakin khandak inda Imam Ali ya kara da Amru bn abdul wuddi ya kuma yi nasara a kansa a nan ne Manzon Allah (s.a.w) ya ce: (( ضربة علي يوم الخندق أفضل من عبادةالثقلين)) ( Dukan da Ali yayi a ranar khandak falalarsa tafi ibadar aljanu da mutane)(12) .
Bayan da yawan Sahabbai sun kasa tarar wannan kasurgumin jarumin saboda sun san cewa duk wanda ya yi gaba da gaba da Amru bn Abdul wuddi sai dai labarinsa, sau uku Manzon Allah yana yiwa Sahabbai tayi cikin ku akwai wanda zai tari wannan kafirin ya yi mubaraza da shi a Aljanna yana tare da ni amma kowa cikin su sai dai ya sunkuyar da kansa kasa, a irin wannan halin ne duk lokacin da Annabi (s.a.w) ya yi magana sai Aliyu (a.s) ya daga hannunsa sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce masa ya zauna sai da a ka yi haka sau uku sannan Annabi ya bawa Ali dama. Manzon Allah (s.a.w) ya ce: kafircin duniya da kuma imanin duniya ne zasu gwabza inda daga karshe bayan Annabi ya yi wa Imam Ali addu’ar ya kuma dauko rawanin sa mai albarka ya dora mashi a kanshi, haka Ali (a.s) ya tari wannan kasurgumin kafiri kuma Allah ya ba shi nasara a kansa ya halaka shi wanda bayan ya kai shi kasa anga Imam Ali (a.s) kamar zai sare kansa sai ya fasa ya juya sai bayan wani dan lokaci kadan sannan ya dawu ya sare kan kafirin, an tamye shi miyasa da farko bai sare kan Abdul wuddi ba? Sai ya ce: ban ya kai shi kasa ya tofa masa yawu ne sai ya yi fushi to shi ne ya dan tafi kadan fushin sa ya sauka domin ba ya son ya yi wani abu a kan fushin sa yana so ya yi don Allah ne, shi yasa sai da ya bari fushin sa ya sauka sannan ya dawu ya sare kan kafirin, ka ji masu yi don Allah da Manzonsa.
Haka ma ta faru a yakin Uhdu inda sanadiyyar shagala da kuma sabawa umarnin Manzon Allah da wasu daga cikin sahabbai suka yi, ya jawu mummunan yanayi tsakanin Musulmai inda hatta Manzon Allah (s.a.w) sama da ciwu saba’in 70 ne a jikin sa mai albarka harma wasu sun fara yada karyar cewa wai an kashe Annabi (s.a.w), wannan karyar da aka yada tasa musulmai sunyi rauni sosai, saboda haka su kuma kafirai suka sami karfin gwuwa, ta yadda aka kashe da yawa daga cikin Musulmai wasu kuma aka ji musu mummunan ciwu wadanda suke jefan Annabi sunyi rauni sosai suna cikin firjici da tsoro daga karshe duk suka watse suka bar Annabi shi ka dai, wani daga cikin Musulmai ya zo yana tambayar wani sahabi mai suna Sa’ad bn Rabi’i wanda an ce akwai ciwu a jikinsa sama da sha biyu 12 ya tsallako wajen sa yana cewa naji an ce an kashe Manzon Allah (s.a.w) ? yana tambayar Sa’ad din ne. sa’ad ya ba shi amsa da cewa amma ai Ubanjigin Annabi rayayye ne kuma shi ba zai taba mutuwa ba, miyasa kai ba zaka yi wani aiki ba shin ba zaka kare addinin Allah ba? Aikin mu ba shi ne kare Manzon Allah (s.a.w) kadai ba, da za a ce idan an ka she shi shikenan aikin mu ya kare, dole ne mu kare addinin Allah kuma wannan ne ai kin mu koda yau she.
Akwai ruwayoyi da yawa da suka tabbar da firjicin da tsoro da Sahabbai suka shiga a yakin Uhdu, kuma da yawa daga cikin banya bayan sahabbai sun gudu sun bar Manzon Allah (s.a.w) ga ma wasu daga cikin wadanda suka gudu din kuma suka yi bayani da kansu:
(( خطب عمر بعد رسول الله يوم الجمعة, فقرأ ال عمران, فلما انتهي الى قوله: ان الذين تولوا منكم يوم التقى المجعان , قال: لما كان يوم أحد هزمنا هم ففررت حتّى صعدت الجبل, فلقد رأيتنى انزو كأننى اروى (13) .
• وفرّعثمان بن عفان وعقبة بن عثمان وسعد بن عثمان رجلان من الأنصار ثم من بنى زريق حتّى بلغواالجلعب جبلا بناحيةالمدينة فأقاموابه ثلاثا ثم رجعوا الى رسول الله صلى الله عليه واله وسلم (14) .
• Umar yayi huduba bayan Manzon Allah (s.a.w) [ ma’ana bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w) ] a ranar wata Juma’a, sai ya karanta Ali imrana, lokacin da ya kai wannan ayar: Inanal lazina tawalau minkum yaumal takal jam’ani. Sai ya ce: Na kasance a ranar Uhdu da muka afka masu, na gudu ina tsalle a kan dutse hakika na tsinci kai na kamar Bunsurun arwa.( wani Bunsuru ne da yake rayuwa a daji ya iya hawa da sauka akan duwatsu).
Da kuma yanda su Usman suka gudu: Usman bn Affan ya gudu da Ukba dan Usman, da Sa’ad dan Usman, suna daga cikin Ansar, sanan daga cikin kabilar zuraik, har sai da suka kai wani wuri mai suna jal’aba a cikin garin Madina suka yi kwana uku a wurin sannan sai suka koma wajen Manzon Allah (s.a.w).
A irin wannan yana yin ne Aliyu bn Abi Dalib (a.s) ya tsaya tsayin daka wajen kare Annabi (s.a.w) inda harma sai da aka ji Muryar Mala’ika Jibrilu daga sama tana cewa: (( لا فتي الا علي لا سيف الا ذوالفقار)) ( Ba wani saurayi sai Ali ba kuma wata takobi sai zulfiar)(13) . [zulfikar takobin Imam Ali ce] haka Imam Ali (a.s) ya kasan ce yana bawa Manzon Allah (s.a.w) kariya a ko ina har zuwa wafatinsa (s.a.w).