Wanen Halifan Annabi (s.a.w)2

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
HALIFAN ANNABI IMAM ALI (a.s)
GUDUN DUNIYAR SA
      Daya daga cikin wasu siffofin Aliyu bn Abi Dalib (a.s) kuma ita ce gudun duniya, gudun duniya yana daya daga cikin manya-manyan halayya masu kyau a ko wace al’umma, shi ya sa ma ake bukatar shugaba ya kasan ce mai gudun duniya domin idan shugaba ya sakan ce mai son Duniya tofa akwai matsala domin barna da son rai zai shigo cikin al’umma. Daga cikin siffofin da Annabi (s.a.w) yake siffanta Imam Ali da su shi ne zuhudu ( wato gudun duniya) inda yake cewa: wanda yake so ya ga zuhudun Isa (a.s) to ya kalli Aliyu bn Abi Dalib (a.s), wannan shaida ce mai girman gaske daga fiyayen halitta kuma fiyayyen amintattun Halitta zababbe daga Allah madaukakin sarki Annabi Muhammad (s.a.w) tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da iyalen gidansa tsarkaka.
      Ga wani bayani akan zuhudun sa a wata wasika da ya rubutawa Usman bn Hanif: ( Ku saurara! Ga ko wace al’umma akwai shugaba wanda ake binsa kuma ake haskaka da hasken  ilimin sa, ku saurara!! Tabbas  wannan shuban na ku   ( yana nufin shi da kansa) hakika tsufaffin riguna biyu ya mallaka a Duniyar ku, kuma bashi da abinci sai busashiyar Gurasa. ((الا وان لكل مأموم اماما يقتدى به ويستضى ء بنورعلمه, وان امامكم هذا قد اكتفى من دنياكم بطمرية ومن طعمه بقرصيه))(14) . Duba kaga yanda shugaba na Allah yake.
    A  tsakanin shi’a da sunna a tabbatar da cewa idan ana maganar zuhudun Imam Ali (a.s) a cikin sahabbai sai dai a shafa fatiha a ta shi domin kuwa ba kamar sa, domin ya bar son duniya da zabin sa ne ba wai rashin samun abin duniyar yasa ya barta ba, inda yake cewa: ( har a ba da sai dai ki rudi wani na bana bukutuwa zuwa  gare ki, hakika na sake ki saki uku sakin da ba bu ko me cikin sa).  
هيهات غرى غيرى, لا حاة فيك, قد طلقتك ثلاثا لا رجعة فيها))(18) .
      Haka ya kasance wajen gudun duniya, ta yadda saboda gudun duniyar sa da yawa daga cikin mabiyansa suka barshi wai suna na  ganin yayi tsauri da yawa.
          ISMAR ALIYU (A.S)
         Isma  ita ma daya ce daga cikin mafi mahimmancin siffar wanda zai kasance khalifan Annabi, domin kariya ga addinin musulunci, haka kuma cikar ma’ana a kan wajib cin abin da yake larura na addini.
     Ismar Imam Ali a cikin Alkkur’ani mai girma da kuma ruwayoyi.
         Tabbatar da Ismar sa daga kur’ani: Farkon ayar dake tsarkake Ali daga dukaknin wani sabo ita ce ayatu Tadhir wato ayar tsarki a cikin suratu Ahzab aya ta 33 in da Allah yake cewa:
 { انما يريدالله ليذهب عنكم الرجس اهل البيت ويطهركم تطهيرا}(17) .{ Abin dai sani shi ne Allah yana nufin ya tafiyar da datti daga gare ku, ya ku ahlalbaiti ya kuma tsarka ke ku tsarka ke wa}}.
       Zamu iya fahimtar wasu yan nukdodi akan wannan ayar:
Na farko: nufin iradar Allah madaukaki da wannan kalma ta ( انما ) ta yadda wannnan kalma ta tattara ma’ana a dunkule zahiri da badini mu samman idan muka kalli ma’anar arijsa wato alif da lam, wanda ke nuni da tattara dukka nin ma’ana wanda ta tattaro ko wane irin datti na zahiri da na badini.
       Abu na biyu: Misdakin ahlilbaiti din wadanda babu shakka  Aliyu (a.s) yana cikin ahlil baitin Annabi (s.a.w) wanda a zamanin Manzon Allah (s.a.w) hakan ya tabbata kuma  magan ganun Annabi zasu zamo shaida akan hakan wanda babu wani daga cikin Sahabbai da ya yi inkarin hakan.
      Manzon Allah (s.a.w)  tun bayan saukar da wannan ayar  kafin sallah da bayan salla sai ya bi ta gidan Ali (a.s) yana cewa:                                                                                                                                                           (السلام عليكم يت أهل بيت النبوة).
 Haka kuma hadisin  kisa’i shaida ne akan haka ta yadda Ali yana daga cikin wadanda suka shiga wannan mayafi lokacin saukar wanann aya mai girma, kai nassosi da dama zasu tabbatar maka da Aliyu (a.s) yana cikin iyalen gidan Annabi (s.a.w) wandanda Allah ya tsarka ke su daga duk wani datti.
     AYAR ULUL AMRI:
             ( (يأيهاالذين ءامنوا أطيعواالله و أطيعواالرسول و أولى الأمر منكم))(18) .
         [[ Ya ku wadanda suka yi imani ku yi wa Allah da Manzon sa da’a da kuma Ulul amri daga cikin ku}[ Nisa’i aya ta 59] idan ka hada wannan ayar da kuma wacan ayar ta tadhir zai tabbatar maka da cewa lallai Ali ma’asumin ne wato wanda baya sabo ko wane iri.
      Saboda haka abin da zamu iya fahimta a wannan aya ta ulul amri shi ne, Allah madaukakin sarki ya cakuda yi masa da’a da Annabinsa da kuma ulul amri ya zama wajibi, idan har ka sa wadannan ayoyi biyun kusa da juna zaka gane ismar ma’asumai (a.s) Ali kuma yana daya daga cikin su. A hakika wannan ayar ta ulul amri tana karfafar wacan ayar ta Tadhir ne.
   Wata ayar daga cikin ayoyin da suke tabbatar da Aliyu (a.s) Ma’asumi ne kuma ita ce ayar Mubahala,  ayar mubahala dai ita ce: 
{ فمن حاجك فيه من بعد ما تبين ما جاءك فقل تعالوا ندع أبناءنا و أبناءكم ونساءنا ونساءكم وأنفسنا وأنفسكم ثم نبتهل فنجعل لعنة الله على الكذبين }(19) .{ Duk wanda yayi maka jayayya bayan hujja da tazo masa ta gaskiya to ka ce: ku kira ‘ya’yan Ku muma mu kira ‘ya’yan Mu da Matan Ku da Matan Mu da Kawukan Ku da Kawukan Mu sannan mu roki Allah ya saukar da tsinuwa ga makaryata}} [suratu Ali imrana aya ta 61]. Tabbas wannan ayar ta haska mana hanya sosai ta yadda zamu gane wanda Annabi ya zo da shi a matsayin kanshi din ba wani bane face Aliyu (a.s), idan har ya tabbata Manzon Allah (s.a.w) zai zo da shi wajen wannan al’amari mai girman gaske to kuwa ba makawa shi da Annabi abu gudu ne, wanda hakan yana nufin kamar yadda Annabi yake da Isma shi ma Ali haka yake da ita.
      TABBATAR DA ISMAR ALI (A.S) A RUWAYOYI.
  Nafarko: akwai ruwayar Aliyu ma’al hakki wacce take tabbatar da ismar sa. (( (( الحق مع علي وعلي مع الحق, يدور الحق مع علي, كيف ما ((Gaskiya na tare da Ali  kuma Ali na tare da gaskiya gaskiya na juyawa duk inda Ali ya juya)) kalli wannan ruwayar da kyau ka gani malam yanda Aliyu (a.s) yake, ta yadda duk inda gaskiya ta juya Ali na tare da ita, ba ma haka ba duk inda ya juya gaskiya tana tare da shi, idan muka kalli wannan ruwaya zata tabbatar mana da Aliyu (a.s) ma’asumi ne saboda ba wani mutum da za a ce duk inda ya juya gaskiya na tare da shi sai ma’asumi wanda baya sabo ko wane iri, kuma duk cikin sahabbai ba mai wannan siffar da matsayin sai Ali dan Abi Dalib (a.s).
       Ruwaya ta biyu: Ruwayar Manzila tana tabbatar da Ismar Ali (a.s): Manzon Allah (s.a.w) ya ce: 
(( (( أنت منى بمنزلت هارون من مو سى الا أنه لا نبي بعدى(20) .(( Kai a waje na kana da matsayi irin matsayin da Haruna yake da shi a wajen Musa sai dai a baya na babu Annabi)).
     Wannan ruwayar tana nuni akan gaba daya siffofin da Manzon Allah (s.a.w) yake dasu Ali (a.s) yana dasu kwai Annabta ce ba shi da ita. Ma’ana duk wani matsayi da Annabi Haruna yake da shi idan an dan ganta shi da Musa to idan ka dan ganta Ali da Annabi yana da wadannan siffofin shi ma.
    MUKAMIN HARUNA A CIKIN ALKUR’ANI
  1 Annabta, 2 Yan uwantaka, 3 khalifanci, 4 Ahlibaitin Musa, 5 Tarayya cikin aikin Musa, 6 Wazirin Musa, 7 Sulhu cikin Al’ummar Musa, 8 Kawar da masu barna, 9 Wajibcin yi masa da’a, 10 Mazlumiyya, 11 Fasahar sa.
        Duk wadannan matsayi da muka lissafa a sama da Haruna yake dasu Aliyu (a.s) yana da su sai dai Annabta ce kadai ba shi da ita.
     Annabi (s.a.w) Ma’asumi ne haka ma Ali (A.S) Ma’asumi ne. saboda haka wadannan dalilan sun isa su tabbatar mana da cewa Ali (a.s) Ma’asumi ne ba tare da wani ja in ja ba, a  wannan rubutu ba ma bukatar sake kawu wata ruwaya don tabbatar da tsarkin Aliyu (a.s).
      Saboda haka zamu iya cewa: yayin da wadannan siffofi suka tabbata akan Aliyu (a.s) tunda ga kan ilimin sa, jarumtar sa, ismar sa, zuhudun sa, s.d. kuma shi kadai ke da irin su babu wani daga cikin Sahabbai da yake da irin su, a bisa duba zuwa ga dalilai na hankali ayoyi da ruwayoyi da suka tabbatar mana cewa Aliyu (a.s) Ma’asumi ne muma zamu iya bugun kirji mu ce: Ali (a.s) shi ne khalifan Annabi (s.a.w).
          Aminci ya tabbata ga wadanda suka bi shiriya har zuwa ranar sakamako.