Muassasar alhasanain (a.s)

Ruwayoyin Karya Da Aka Kirkiro

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5
Godiya ta tabbata ga Allah (s.w.t) 
Kuma Aminci ya k'ara tabbata ga bayinsa wad'anda ya zab'a
Za a samu masu ruwayar da suke rawaito Hadisi daga gare ni, to ku kawo hadisinsu ga Kur'ani, abin da ya dace da Kur'ani ku yi riko da shi, abin da kuwa bai dace da Kur'ani ba to ka da ku yi riko da shi ".
 
GABATARWAR MAWALLAFI
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Godiya ta tabbata ga Allah mai rahama mabuwayi da ya yi mana baiwar ni'imominsa. Amincin Allah ya tabbata ga manzon Allah da alayensa tsarkaka
 
Ya dan'uwa mai karatu wannan littafin yana son yin bincike ne kan asasin da aka gina mafi ingancin ruwayoyi a mahangar wani Bangaren musulmi da suke ganin litattafan Buhari da Muslim a matsayin mafi ingancin litattafan ruwaya. Na fara da gabatarwa kan hanyoyin salon binciken ingancin ruwaya da tace ta gun Sunna da Shi'a a matsayin wani bincike na ilimi da zai zama haske kan tsarin da al'ummar musulmi suka doru kansa wurin gano gaskiyar hadisai.
Sanin hakikanin kowace akida yana bukatar koma wa littattafan ma'abota wannan akidar domin sanin inda ta samo asali. Don haka ne ya kamata mu yi bincike a cikin Buhari da Muslim domin sanin me suka kunsa don sanin tasirin da suka yi a akidar wasu musulmi, da tantance abin da yake dacewa da koyarwar Kur'ani mai daraja da wanda ya saBa masa.
Ruwayoyin da ake karBowa daga annabin rahama sun fuskanci neman jirkita su a hannun wasu mutane marasa amana ko wadanda suke kuskure ba tare da sani ba. An fara yi wa annabi karya tun lokacinsa ne sai ya dauki matakai don dakatar da wannan lamari mai hadari. Ya sanya dokokin tace ruwayar gaskiya da ta karya wacce da an bi ta, da lamarin ruwaya bai Baci ba.
Bayan wafatin annabin rahama sai aka kona hikimominsa da ya sanar da musulmi, kuma aka tsananta hana yada maganganunsa, sai abin da ya zama ana bukatarsa kawai wasu lokuta. Sai sunnarsa ta Bace daga cikin al'adun musulmi, aka maye ta da sunnar jahiliyya. A yayin da musulmi suka fadaka don hada sunnarsa sai ya zama an riga an samu rarrabar kawuka, da mazhabobi, da ra'ayoyi mabambanta, don haka kowa yana hada abin da ya yi masa ne, ko wanda yake gani shi ne Musulunci a wurinsa.
Annabin rahama ya san cewa za a samu wannan matsalar don haka ne ya tanadi hanyar tace ruwayar karya da ta gaskiya. Hanyar da annabi ya gindaya ba ta samu karBuwa ba gun musulmi sakamakon cewa yana da masu saBa masa kan wannan lamarin kuma zai hana su cimma hadafinsu. Don haka ne aka maye gurbin wannan hanyar da wata hanyar daban, sai aka fifita ma'aunin mazaje kan ma'aunin Kur'ani da hankali, mazaje suka zama su ne asasin gane ruwaya, hanyar ma'aikin Allah ta ma'aunin Kur'ani da alayensa kuwa aka yi watsi da ita gefe guda, aka wurga ta kwandon shara.
Sai lokacin hada ruwayoyi ya zo, bayan nan aka shiga marhalar taciya da hadawa, ga mutane suna kan addinin sarakunansu, don haka babu wani abu da ake tsammani a wannan lokacin sai tace ruwaya bisa asasin tsarin da al'umma ta samu kanta cikinsa. Don haka ne Buhari da Muslim ba su iya kauce wa tsarin da aka gadar musu ba, sai suka doru kansa suka yi aiki bisa koyarwarsa.
A wannan bahasin da na sanya wa suna "Buhari da Muslim a Sikeli" zamu dora Buhari da Muslim kan sikelin salon binciken da ya doru kan Hanyar binciken Matani da manzon Allah ya sanya don tace ruwaya, kuma musulmi baki daya Sunna da Shi'a suka ruwaito, sai dai aka yi watsi da ita ba a yi amfani da ita ba.
Fatanmu mai karatu ya bi mu daki-daki har karshen littafin don sanin dalilin da ya sanya al'umma ta tsinci kanta a wannan yanayi.
Ga Allah muke neman taimako, shi ne madogara, kuma shi ne wakili.
 
 
DALILAN KIRKIRO RUWAYA
An yi wa annabi (s.a.w) karya da yawa tun a lokacinsa har ya dauki mataki kan hakan kuma Ahlul-baiti sun ci gaba da kokarin daukar wasu matakai don hana kirkirar hadisai a bayansa, sai ya fara da matakin samar da kawo canjin iya rubutu cikin sahabbansa ta yadda babu wani wanda ya rage bai iya karatu da rubutu ba.
Bayan haka Annabi ya dauki matakin umarnin kowa ya rubuta duk wani abu da ya ji daga gare shi don gudun ka da a samu yaduwar karya gare shi bayansa. Mutane masu yawan gaske daga sahabbansa sun rubuta duk abin da suka ji a gabansa, sun kiyaye su tare da su don gudun ka da wani ya kirkira masa karya a nan gaba.
Sai kuma ya sake daukar matakin gargadin wuta ga duk wani wanda ya yi masa karya ko ya kirkira ya jingina masa . Ruwayoyi masu yawan gaske ne suka zo suna karfafa cewa "... duk wanda yake yi wa annabi karya to ya tanadi masaukinsa a wuta ...", ko "...shi dan wuta ne", da sauransu.
Sai dai an samu wasu jama'a daga cikin sahabbai da suke ganin rubuta hadisansa bai dace ba, don haka ne suka dauki matakin hana hadisansa. Yunkurin hana rubuta hadisansa ya soma tun lokacinsa mai tsira da aminci, kuma mai daraja da daukaka ya tsananta kan rubuta sunnarsa saboda ya san hadarin da rashin hakan ya kunsa. Wannan lamarin ne ya haifar da fikirori biyu; mai bin fikirar annabi ta rubuta sunnarsa, da mai kin fikirar rubuta sunnar annabi.
A cikin abin da Abu Dawud ya ruwaito cewa; Abdullah dan Amru bn Aass yana cewa: Na kasance ina rubuta duk abin da nake ji daga annabi ina son hardacewa. Sai kuraishawa (wasu daga manyan sahabbai) suka hana ni, suka ce: Yanzu zaka rubuta duk abin da kake ji daga annabi wanda shi mutum ne da yake magana cikin fushi da yarda! Sai na daina rubutawa. Sai na gaya wa annabi wannan lamarin. Sai ya nuna bakinsa ya ce mini: Rubuta! Na rantse da wanda raina take hannunsa babu wani abu da yake fita daga cikinsa sai gaskiya .
Sai dai kai tsaye karfi ya koma hannun fikirar da take hana rubuta sunnar annabi (s.a.w), kuma bayan wafatinsa ne kai tsaye aka kona duk abin da sahabbai suka rubuta a gabansa a lokacin halifan farko, wannan ya faru ne sakamakon karfi ya koma hannun jama'ar da take da ra'ayin cewa Kur'ani kawai ya isa ban da hadisin annabin rahama saboda daukar manzon rahama da wannan jama'ar ta yi cewa yana yin kuskure, da kuma daukar cewa yana yin ijtihadi ne a wasu wurare, don haka littafin Allah ya ishe mu. 
Kanzul Ummal, da Tazkiratul Huffaz da sauran littattafai masu yawa suna nakalto cewa; Halifa na farko ya kwana yana mai jujjuyawa. Da ya wayi gari sai 'yarsa Umar muminai take ce masa: Wane bakin ciki ne yake damunka. Sai da ya wayi gari sai ya ce: Kawo mini hadisaina. Sai ta kawo masa hadisansa da ya rubuta lokacin annabi kusan guda 500, sai ya kona su baki daya. Wasu ruwayoyin sun kawo cewa ya kona ne don gudun ka da ya zama ya rubuta bisa dogaro da wani wanda ya gaya masa ruwaya sai ya kasance ba daidai ne aka gaya masa ba .
Sai dai masu rubuta tarihi sun kawo wasu tambayoyi kamar haka? Me ya sa halifa bai rubuta da kansa ba alhalin yana tare da annabi tun a Makka har Madina har karshen rayuwarsa? Me ya sa bai kawo hadisan 500 ba wurin sahabbai domin su duba su tabbatar da shin akwai kuskure ko babu kuskure? Shin hakan bai fi ya kona har ruwaya 500 ba!?.
Don me ya sa ba a kona Attaura da Injila ba, sai aka bar su bisa dogaro da ruwayar da take cewa: Annabi ya hana kona Attaura?! . Idan dai ya hana kona litattafan da muke da yakini an canja bayanai masu yawan gaske a cikinsu, ina kuma ga maganarsa mai tsarki da ya yi umarni a rubuta?!.
Sai dai tambayar da ta fi muhimmanci a wannan bahasin ita ce: Don me ya sanya aka kona duk abin da sahabbai suka rubuta kai tsaye bayan nan?!. Idan halifa ya kona nasa, to me ya sa aka kona na sauran sahabbai?!.
Marubuta masu yawan gaske sun kawo cewa; Kai tsaye bayan halifa na farko ya kona hadisan da ya tara, sai halifa na biyu ya shelanta wa mutane cewa: "... ka da wani ya bar wani abu da ya rubuta sai ya zo mini da shi..., sai suka yi tsammanin za a duba ne don a daidaita su kan wani lamari da zai hana wani saBani ne, sai suka zo masa da duk litattafansu, sai ya kona su da wuta, sannan sai ya ce: Almarori ne kamar almarorin ahlul-kitab .
Lokacin da na hada ruwayoyin baki daya sai na ga halifofi sun kona hadisai saboda wasu dalilai da suka kawo kamar haka: 1)Tsoron cakuda ruwaya da Kur'ani. 2)Tsoron shagaltuwa da karanta ruwaya da barin karanta Kur'ani. 3)Tsoron ka da a samu wani rubuta ma a cikin musulmi ba Kur'ani ba. Wadannan su ne uzurorin da halifofin farko suka bayar.
Sai kuma kalmar da halifa ya yi amfani da ita wato kalmar "umniyatun" ko mathnatun" kamar yadda ya zo a ruwayoyi mabambanta, a nan zamu ga na fassara ta da "almara" sai dai dukkan kalmomin suna da ma'ana da suka zo a littattafai kamar haka:
Halifa ya yi amfani da kalmar "umniyat" wanda aka fassara shi da karya, ko kage, da larabci ana cewa da mutum "a haza shai'un rawaitahu au tamannaitahu" ma'ana wani abu ne da ka ruwaito ko kagarsa ka yi, wato ba shi da asali. Bahaushe yana cewa masa kagaggen labari, wani lokaci tatsuniya ko almara. Allah madaukaki yana cewa: "...Daga cikinsu akwai wanda bai san littafi ba sai dai karairayi..." Bakara: 78. Sai Mujahid ya fassara kalmar "amaniyyu" wacce take jam'in "umniyat" da karya .
Idan kuwa halifa ya yi amfani da kalmar "mathnat" ne wacce jam'inta yake zuwa "mathaniya" to kalma ce da ake gaya wa rubuce-rubucen malaman yahudawa da suka sanya dokoki yadda suka so wanda ba ya cikin littafin Attaura. Sai ya zama halifa ya kwantanta hadisan annabi (s.a.w) da wannan, sakamakon yana ganin hadisan annabi saBanin littafin Allah, don haka ba a bukatar su sai a wasu lamura da ya rasa nasa ra'ayin .
Yayin da mabiyar makarantar Sunna suka ga wannan lamarin yana da muni sai suka nemi kirkiro masa wasu hanyoyin uzuri, sai abin da suke fada ya fi abin da halifa ya fada muni. Sun nemi ba wa ayyukan halifa uzuri da cewar ya ji tsoron ka da a cakuda ruwaya da ayar Kur'ani sai Kur'ani ya gurBata. Mafi hadari da muni shi ne kirkiro ruwayoyin da suke hana rubuta sunnar annabi da jingina wannan ruwayoyin gare shi, sai yi wa annabi (s.a.w) karya ya fi sauki don kariya ga abin da halifa ya yi.
Sai dai wannan uzurin ba zai zama karBaBBe ba saboda musulmi sun san Kur'ani da siyakinsa da sigar lafuzansa, kuma da yawa sun hardace shi tun wannan zamanin, don haka wannan tsoron babu shi. Sannan ya ya zasu yi da fikirar wannan jama'ar ta cewa: "...Littafin Allah ya ishe mu...", sannan yaya zasu bayar da amsar " Tatsuniyoyi ne kamar tatsuniyoyin ahlul-kitab ". Kamar yadda sauran dalilan ma a fili yake cewa suna da rauni matukar gaske.
Sai rubutun ruwaya ya zama takaitacce, ya zama babu mai iya ruwaya sai wanda aka ba wa izini cikin iyakancewa, sai ya zama sahabi yana jin tsoron yin ruwaya don yana iya kai shi ga bulala ko kunci, sai ruwayar Hadisi ta yi karanci matukar gaske. Da umayyawa suka zo sai suka samu damar yin abin da suka ga dama na kirkira, sai dai a karshen mulkinsu daya daga sarakunansu ya nemi a dawo da rubuta hadisai bayan fikirori da mazhabobi sun riga sun fantsama.
 
KIRKIRAR RUWAYOYI
Haifar da wannan yanayin da ya gabata ne ya kawo masu ruwayar karya suka yawaita. Akwai dalilai masu yawa da suke sanya kirkiro ruwaya da jingina su ga annabin rahama (s.a.w) da suka hada da:
a- Hadafin Siyasa
Mafi yawan ruwayoyin da suka zo don yabon wasu mutane da ake ganin suna da matsala da Imam Ali (a.s) suna cikin irin ruwayoyin da aka kirkiro don hadafin siyasa. Wasu suna kawo su kamar hadisin nan da su kansu Sunna suka ce ba shi da asasi mai cewa: Allah ya sanya Abubakar halifana a kan addinin Allah da wahayinsa. Ibn Jauzi ya kawo shi cikin littafinsa na "Almaudhu'at" . Ko ruwayar nan da take cewa: Amintattu a wurin Allah uku ne; Jibril, da ni, da Mu'awiya . Da sauran ruwayoyi kan falalar sahabbai da Shafi'i da waninsa suka tafi a kan cewa duka karya ce da aka jingina wa annabin rahama don kalubalantar falalolin Imam Ali. Haka nan irin ruwayoyin biyayya ga azzalumi komai zaluncinsa .
b- Bata Addini
Wasu mutanen kuwa suna kin addinin Musulunci ne baki daya, don haka sai suka ga babu wata hanyar rusa shi sai hanyar kirkiro masa ruwayoyin karya da sunan an karBo daga annabi ko daga alayensa. Kamar yadda Mugira dan Sa'id yake yi ga Imam Sadik (a.s), har Imam ya shelanta sunansa cikin masu Bata addinin Allah. Ya kasance yana karBar ruwayar Imam Bakir (a.s) sai ya cakuda ta da wasu karairayi. Ya kasance yana ba wa Imam Sadik da babansa Imam Bakir siffofin Allah don haka ne Imam Sadik ya la'ance shi .
c- Hadafin Mazhaba
Wani lokaci wasu kan kirkiro ruwayoyi don sukan wasu mazhabobi kamar yadda muka samu ruwayoyi masu yawa daga Bangaren hanifawa da shafi'awa suna la'anar juna. Wasu ruwayoyin suna nuna Shafi'i a matsayin wanda ya fi Iblis cutar da wannan al'ummar, da Abuhanifa a matsayin wanda yake shi ne fitilar wannan al'ummar .
Duk wani yabo ko suka ga ma'abota mazhabobin malaman Sunna dukkansu kirkira ce. Kamar yadda aka kirkiro falala mai yawa kan sahabbai daban-daban don kishiyantar matsayin Ali haka aka kirkiro game da masu mazhabobi don kishiyantar tsarkakan imaman shiriya daga zuriyar annabin rahama (s.a.w).
Haka ma hadisan da aka kirkiro da suke sukan masu cewa Kur'ani abin halitta ne. Wannan ma yana daga kirkiren wasu mazhabobi kan wasu mazhabobin .
Jahilcin Maruwaita
Wani lokaci masu ruwaya suna jahiltar cewa wanda yake ba su ruwaya makaryaci ne, su kuma ba su san gaskiya ba, sai ya gaya musu wata ruwaya su kuma sai su yada ta ko'ina a matsayin maganar annabin rahama (s.a.w).
Kamar hadisin Abi Isma da ya yi da'awar cewa daga Ikrama ya karBo shi daga Ibn Abbas, sai aka tambaye shi cewa yaya ya samo wannan alhalin duk masu ruwaya daga Ikrama ba su da shi. Sai ya ce: Na ga mutane suna kaurace wa Kur'ani suna shagaltuwa da littafin Abuhanifa da Magazi din Ibn Ishak, don haka sai na kirkiro wannan ruwayar don su shagaltu da Kur'ani kawai .
Hadafin Kai
Wani lokaci neman matsayi ne ko dukiya ko neman girma yake sanya wasu suna yin karya ga annabin Allah (s.a.w), irin wannan yana da yawa a tarihi. A lokacin Mu'awiya wannan mas'alar ta yawaita matukar gaske yayin da aka samu wasu makaranta da suke nuna tsoron Allah a zahiri, sai suka shagaltu da kirkiro ruwayoyi domin su samu shiga gun sarakunan garuruwa .
Duk wanda ya kirkiro wata ruwaya game da falalar wani sahabi, ko kuma ya kirkiro kan sukan Imam Ali (a.s), to yana samun kudi masu yawan gaske, don haka sai ruwaya kan haka ta yawaita. Musamman ma bayan umarnin da Mu'awiya ya bayar na kirkiro ruwayoyi masu aibata Imam Ali, da wasu ruwayoyin masu ba wa wani daga sahabbai falala irin wacce yake da ita .
Wasu lokutan samun abin rayuwa kawai ya wadatar a kirkiri ruwaya kamar yadda zamu ga Giyas bn Ibrahim yana ganin halifan abbasawa Mahadi yana wasa da tattabaru sai kawai ya kirkiri ruwaya kan wasa da tattabaru, shi kuwa Mahadi ya ba shi kyautar dirhami 10 000 na take .
Don haka ne abin da yake hannun mutane ya zama cakude ne tsakanin kirkirar karya da aka yi ga annabin rahama (s.a.w), da kuskure ko rashin fahimta, ko mantuwar mai ruwaya, da abin da yake an shafe shi a shar'ance, sai kuma abin da yake gaskiya ne. wadannan abubuwan ne suke cakude hannun mutane kamar yadda Imam Ali ya gaya wa wani mutum da yake tambayarsa dalilin da ya sanya abin da yake hannun Ahlul-baiti yake saBa wa da na hannun mutane .
Kuskuren Kiyayewa
Idan muka tsaya kan batun kuskuren kiyaye ruwayar da aka karBo daga annabin rahama zamu ga wannan lamarin ba ya kirguwa. Misalai masu yawa suna cikin littattafai masu yawan gaske. Wani lokaci mai kuskure yana manta wani Bangare na ruwayar, wani lokaci kuwa ya fadi karshenta da tsakiya, wani lokaci ya fadi farko da karshe ko farko da tsakiya, wani lokaci kuwa mai ruwaya ba ya nan manzon Allah ya fara bayani, sai ya tarar da karshe, sai ya bayar da labarin karshe yadda ya fahimta ba tare da ya gane lamarin ba kamar wani mai bayar da kissar wata magana da ya jingina ta ga annabi (s.a.w) kuma Zubair dan Awwam ya kama shi, sai ya ce: Ai ba ya nan a farkon maganar ne, wannan kuskuren ne ya sanya ya jingina wa annabi (s.a.w) maganar wani bayahude .
Hada da cewa babarmu A'isha ta ci gyaran mutane masu yawa kan mas'aloli daban-daban. Ta ci gyaran Abdullahi dan Umar dan Khaddabi a batun kuka ga mamaci da cewar bai ji daidai ba ne . Haka nan Abuhuraira ya shahara da cakuda ruwaya tsakanin abin da ya ruwaito daga annabi da wanda ya ji gun Ka'abul Akhbar bayahude, sai ya rika jingina abin da ya ji wurin Ka'abu zuwa ga annabi (s.a.w) .
Wannan lamarin yana sake karfafa abin da ya gabata na matakan da annabi da alayensa suka dauka don tace ruwayoyi don hana karkacewar al'umma daga shiriya da fadawa cikin Bata.
 
BUHARI da MUSLIM a SIKELI

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)