Tarbiyyar Yara
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
Tarbiyyar Yara
Kyatata Dadi'u A Musulumci.
Magana kan yara wani abu ne da babu abin da ya kai shi muhimmanci a tarihin rayuwar dan Adam Saboda su ne manya a gobe, kuma idan ba a tarbiyyatar da su yadda ya kamata ba to wannan yana nufin rushewar al’adun al’umma da shafe kufan abin da ta gada kaka da kakanni. Shi ya sa ma a tarihin juyin juya hali na kowace al’umma zaka ga yana faruwa da Yara da Samari ne sannan ya yiwu, idan mun duba tarihin Annabawa (A.S) da Manzon Rahama (S.A.W) da ma juyin da ya faru a bayansu, za mu ga ya faru ne ta hannun samari da yaran al’ummu.
Duba ka gani yadda mushirikan Makka suke cewa: Manzo ya zo ya bata tunanin samarinsu, Sabaoda samari su suke karbar canji, amma tsohon jini da ya kafu a bisa wata Akida da ta kafu a kwakwalwarsa to wannan yana da wahala ya canja sai daidaiku, don haka ne ma Ku’rani ya bayar da muhimmaci a kan shekarun samartaka zuwa arba’in.
Shi ya sa Malaman tarbiyya suke cewa: Yana da wahala ga mutum ya canja da wuri bayan ya yi shekaru arba’in kan wani ra’ayi, misali idan mutum ya kai shekara arba’in ba ya sallar dare to yana da wahala ya iya jurewa ya dage a kai, Shi ya sa idan saurayi ya dore a kan hanya ta gari to yana da wahala ya canja Sai dai idan ya zama akwai wani sirri tsakaninsa da Allah da ba shi da kyau, ko kuma lallai zuciyarsa ba ta kama hanya ta gari ba, ko ba ta doru bisa mahanga sahihiya da Allah ya dora Addininsa a kai ta hannun Manzonsa (S.A.W) ba.
Haka ma idan ya zama yana da dauda a zuciya kamar hassada ko mugun kulli kan bayin Allah na gari to duk wannan yana iya tasiri wajan lalacewarsa koda yana ayyuka ta bangaren ibada a nan ba mamaki ba ne karshensa ya ki kyau. Duba Bil’am dan Ba’ur mana ka gani da malami ne shi amma saboda ya yi wa Musa (A.S) hassada sai ya lalace, haka ma Iblis yana daga mala’iku masu ilimi na koli, amma sai ya yi hassada, shi ke nan sai ya kaskanta, darajarsa ta yi kasa.
Shi ya sa ya zo a wata ruwaya cewa: Kada a duba tsawon ruku’u ko sujadar mutum, ta yiwu wata al’ada ce da ya saba da ita, idan ya bari sai ya ji babu dadi, amma a duba ayyukansa da mu’amalarsa. Kamar wanda ya saba da sallar jam’i ko ta dare ko azumin nafila amma ba sa tasiri a ayyukansa.
Haka ma yaro idan ya saba da wani abu haka zai taso da shi a matsayin saurayi, idan da ya saba da karatu sai ya zama saurayi to ba zai iya bari ba kuma haka zai manyanta, haka kuma zai tsufa matukar wani yanayi na tilas da lalura bai fado ba. Amma yaron da ya taso yana bin ‘yan iska da samarin banza yaya zai taso? Don haka ne tarbiyyar yara take bukatar hukuma, da iyaye, da ‘yanuwa, da makwabta, da malamai, duk su sa hannu wajan tarbiyyantar da ilmantar da yara da samarin al’umma domin a samu al’umma ta gari.
Kur’ani Ya Yi Nuni Da Mu’amala Da Yara
Kur’ani mai girma ya himmantu da tarbiyyar yaro da kula da shi, don haka ne a ayoyi masu yawa ya yi magana game da ‘ya’ya da hakkokinsu, da yadda ya kamata a kalle su, da zama da su, da zamu iya kawo su a dunkule kamar haka:
الما ل و البنون زينة الحياة الد نيا
1- ‘Ya’ya adon rayuwar duniya ne: Kahafi: 46.
2- ‘Ya’ya su ne asasin jarrabawa daga Allah: Tagabun: 15.
3- Wasu daga ‘ya’yanmu makiyanmu ne: Tagabun: 14.
4- Kada ku damu da nauyin ‘ya’yanku a kanku: An’am: 151.
5- Kada ku yi alfahari da yawan ‘ya’yanku: Saba’: 35.
Kyatata Dadi'u A Musulumci.
Godiya ta tabbata ga Allah madaukaki tsira da aminci su tabbata ga wanda aka aiko shi rahama ga talikai don ya cika kyawawan dabi’u, Ubangijin kasa da sama ya siffanta shi da “Hakika kai kana da kyawawan dabi’u masu girma” . Wanda mutane masu neman daukaka suke koyi da shi.
Da Allah ne muke neman taimako a kan kawukanmu da kuma dukkan abin da ya halitta gaba daya, tsira da aminci su tabbata a kan wanda ubangijin halitta ya siffanta shi da cewa shi yana da kyawawan dabi’u, sai ya aiko shi domin ya cika mafi kyawawan dabi’u, Annabin rahama da mutuntaka Muhammad dan Abdullahi (S.A.W) da alayensa tsarkaka (A.S).
Al’amarin kyawawan dabi’u al’amari ne na ‘yan Adam da aka yi tarayya a kansa tsakanin mutane gaba dayansu da dukkan sabanin addinansu da nisan yankunanasu da kuma yarukansu. Mutum yana rayuwa a jama’a ne da a cikinsu akwai na nesa, da na kusa, da karami, da babba, da mace, da namiji, da mai neman sani, da malami, kuma da mai kasuwanci, da maras aiki. Mutum yana bukatar abubuwan da ta hanyar su ne zai kiyaye mu’amala da sauran mutane don cimma gurin rayuwarsa da bukatunsa kamar yadda Allah ya yi umarni.
Don haka ne ma kyawawan dabi’u suka zama tsani domin nuna yadda ya kamata a yi mu’amala da wasu, da kuma yadda za a yi mu’amalar mutum tare da wani mutumin a bisa ka’idar “Yin mu’amala da mutane kamar yadda kake so a yi mu’amala da kai”. Ko kuma “Kamar yadda ka yi za a yi maka” .
Saboda haka mutum ba ya wadatuwa gabarin wannan dabi’a da zata kare ayyukansa, ta kuma tsarkake tunaninsa, da kuma bayar da gudummuwar nisantar da kai daga ayyuka marasa kyau, domin ba komai ne ya sa aka halicci mutum ba sai domin ya samu daukaka zuwa ga kamala, da kuma gina al’ummar da adalci da taimakekeniya zasu zama su ne suke jagorantar ta domin kariya daga zalunci da fasadi.
Wannan shi ne abin da ake kira “Kyawawan dabi’u wato Akhlak” Wanda ya kasu zuwa na nazari da na aiki. Ta wani bangaren kuma wajibi ne a nisatar da kai daga karya, da ha’inci, da hassada, da riya, da rudin kai, da jiji da kai, da mugun kuduri, da giba, haka nan wajibi ne a siffantu da gaskiya, da amana, da burin alheri ga juna, da sauransu na daga kyawawan dabi’u da ya zama wajibi ne a kan mutum ya san su, kuma ya san munananta da kyawawanta, wannan duk ana cewa da shi Ilimin Kyawawan dabi’u na nazari.
Sannan sai a siffantu da su a rayuwa a aikace tare da iyalai, da ‘yan’uwa, da makwabta, da wadanda suke gefe, wannan shi ne ake kira Ilimin Kyawawan dabi’u na aiki.
Da mun kula mun yi la’akari da zamu samu cewa mafi yawancin mutane da suka siffantu da Kyawawan dabi’u su ne annabawa, musamman Annabinmu mafi girma Muhammad (S.A.W) ta yadda ya zama yana daga sababin aiko shi, shi ne domin ya cika manyan dabi’u kamar yadda shi da kansa (S.A.W) ya shelanta, ya kasance yana siffantuwa kafin a aiko shi da mai gaskiya amintacce; saboda gaskiyar zancensa da aiki da amana har Allah madaukaki ya yabe shi da cewa: “Lallai kai kana da kyawawan dabi’u masu girma”
[MUNA YI MUKU FATAN ALKHAIRI].
MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA
Mail= munirsaid92@gmail.com
Whatsapp da telegram +2348038557822.