Dukiya Da Hukuncinta

Da sunan Allah madaukaki
Dukiya ita ce duk wani abu da yake da amafani kuma ake iya amfana daga gareshi domin ci gaban rayuwa, wanda yake karbar a yi musayansa da wani abu. Wannan abin yana iya kasancewa na sanyawa ne, ko ci, ko ajiya, ko hawa, da sauransu. Dokiya ta kasance wani abu ne da yake hanyar biyan bukatun mutane, don haka ne ta kasance wani bangare mai muhimmanci a cikin rayuwar al’umma.
Magana kan dukiya wani abu ne mai muhimmanci matuka domin tana nuna mana hanyar da ake samun asasin tafiyar da lamurran rayuwar mutane. Musamman da yake dukiya ta zama ma’auni na musayan abubuwan rayuwa da ake iya mallaka bisa yardar bangarori biyu na mutane. Kuma ana iya mallakar dukiya ta hanyar gado, ko kyauta, ko saya, da sauran hanyoyin da shari’a ta yarda da su.
Sannan duk wani abu da zai iya kasancewa a yi musaya da shi, kuma yake karbar a saya ko a sayar da shi, yana iya kasancewa an kira shi dukiya.
Akan yi bayanin nau’in dukiya bisa yadda aka yi la’akari da kashe-kashenta ne, sai wasu suka kasa dukiya zuwa ga ainihin abu, da mafaninsa, wasu kuwa suka kasa ta gida biyu: imma dai dukiyar al’umma, ko ta mutum daya.
Dukiyar al’umma ita ce dukkan dukiyar da aka sanya ta domin maslahar dukkan al’umma, kamar ta zakka, da humusi, da baitul mali, da haraji, da ganima, da sauransu. Amma dukiya kebantacciya ga wani mutum ita ce wacce wani yake mallakarta, kuma babu mai ikon tasarrufi da ita sai da izinin mai ita. (Riyadus Salihi: Sayyid Ali Dibadiba; j 2, s 40).
Muna iya ganin yadda imamai jagororin al’umma wasiyyan manzon Allah (s.a.w) suka ki yarda da taba dukiyar al’umma da wajabcin mayar da ita kamar yadda zamu bayar da misali kan hakan:
A ruwayar Ali bn Rashid ya ce: Na tambayi Abul Hasan (a.s) na ce masa na sayi kasa kusa da gidana da dinare dubu biyu, yayin da na biya kudi sai aka ba ni labarin cewa wannan kasar wakafi ce, sai ya ce: "Sayan wakafi bai halatta ba, kuma abin da ka samu ba ya zama naka, sai dai ka bayar da shi ga wadanda aka yi wa wakafinsa. Sai ya ce: Ban san wai mai ita ba. Sai ya ce: Ka yi sadaka da amfaninta (Makasibul Muharrama: Khomain / j 2/ s 268).
A fili yake cewa wannan dukiya ta wakafi da yake ita mallaka ce ta al’umma babu wani mai ikon mallakarta koda kuwa ya saya, ya zama dole ya mayar da ita mallakar al’umma gaba daya. Sannan wannan ya taimaka mana wurin sanin hukuncin dukiyar da aka san adadinta, amma ba a san mai ita ba wanda yake nuni da tilascin yin sadaka da ita.
Akwai hanyoyi da shari’a ta sanya domin mallaka kowace iri ce kamar raya abu, taskacewa, farauta, bibiya, gado, lamuni, ramuwa, da kuma kullawa kamar ciniki, rance, inshore, juyar da bashi kan wani, sulhu, tarayya, wakafi, wasiyya da sauransu. (Alfikihul Islami fi Saubihil Jadid: Sheikh Mustapah Azzarka; 1 / 60-61).
Da wannan ne zamu ga cewa; lallai ilimin fikihu yana iya warware duk wani abu da ya taso na rayuwar dan Adam, don haka ne muka ga ya himmantu da bayani kan alakoki mabambanta, wadannan alakokin sun hada da: Alakar mutum da ubangijinsa, da Alkar mutum da iyalinsa, da Alakar mutum da wasu abubuwa kamar dukiya, da Alakar mutum da al’ummarsa. Wadannan alakokin suna farawa ne tun daga lokacin da aka haife shi har mutuwarsa.
Hakika imam Ali (a.s) ya himmantu da lamurran kula da dukiyar al’umma da kiyaye ta, da matukar yakar kebantarta da wasu mutane a cikin al’umma.
Irin wannan lamarin ne ya kasance a cikin duniyar musulmi kafin zuwan imam Ali (a.s) kuma ya sanya shi cikin wahalar yakar wadannan mutanen Banu Umayya da suka salladu kan dukiyar al’umma kamar yadda ya kawo a wata hudubarsa a cikin Nahajul Balaga.
Idan dai mulkin al’umma ya kasance ya doru ne bisa biyan bukatun mutane, da daukar nauyinsu, to bai halatta ba a kebanci wani aji na mutane da ita, ya zama dole ne ta shiga cikin rayuwar mutane. Imam Ali (a.s) yana cewa da wani daga cikin gwamnonisa: "Ka duba abin da ya taru gunka na dukiyar Allah sai ka yi wa wadanda suke nan hidima da shi, daga masu iyali da talauci, da yunwa, kana mai bin duk inda ake da bukata da rashi, abin da ya rage kuwa sai ka zo mana da shi domin mu raba shi ga wadanda suke gunmu” (Dirasatun Fi Nahjil Balaga: Muhammad Mahdi Shamsuddin; s 135).
Akwai irin wadannan kalamai na imam Ali (a.s) ga wadanda yake turawa don kula da dukiya ko kuma gwamnoni a garuruwa masu yawa shigen irin wannan. Kamar Ash’as dan Kais gwamnansa na Azarbaijan, da Ziyad dan Abihi, da sauran mutanen da yake turawa don kula da ayyukan Sadaka, da Maskala dan Habira, da Usman dan Hanif, da Usum dan Abbas.
Kamar yadda imam Ali (a.s) ya yi nuni da raba dukiya ga al’umma da yi musu hidima da ita daidai gwargwadon yanayi da yanayin hidimar da suke bukata a cikin wani hadisi da fadinsa: "Amma hakkinku a kaina shi ne in yi muku nasiha, in tanadi dukiyarku, in sanar da ku domin kada ku yi jahilci, in ladabtar da ku domin ku yi ilimi” (Nahajul Balaga: Bayani 34, shafi 138).
Sannan malamai sun rarraba dukiya bisa la’akari da sanin mai ita, da saninta ko rashin hakan kamar haka:
1- Sanin Mai Dukiya Da Sanin Adadi
Dukiyar da aka san mai ita da adadinta; ita wannan dukiyar hukuncinta shi ne a bayar da ita ga mai ita, kamar yadda take da adadinta. Wannan lamarin kuwa a fili yake idan muka duba shi a matsayin asasin rayuwar al’umma ta yau da kullum.
Ba don wannan hukuncin ba da tsarin al’umma ya yamutse, da an samu halatta dukiyoyin al’umma bisa barna, da duniya ba ta samu nutsuwa ba.
2- Sanin Mai Dukiya da Jahiltar Adadi
Dukiyar da aka san mai ita, ba a san adadinta ba kuwa, ita wannan dukiyar sai a yi sulhu bisa wani adadi da zai yardar da juna. A bisa yanayin wannan dukiya tun da an san mai ita, to a shar’ance dole ne ta koma hannunsa, sai dai zai kasance an samu fuskantar matsala guda daya ta cewar ba a san adadin wannan dukiya ba.
Kamar dai wanda ya ba wa wani mutum rance ne amma sai suka manta da adadinta, to a nan sai su yi sulhu bisa wani adadi na dukiya da zamu samu yarda da nutsuwa a kai.
3- Jahiltar Mai Dukiya Da Sanin Adadi
Dukiyar da ba a san mai ita ba, amma an san adadinta tana da hukuncin yin sadaka da ita ga mai ita. Sai dai wannan yin sadakar da ita ba ya nufin idan mai ita ya zo wata rana ko aka gano shi cewa ba za  a ba shi dukiyarsa ba.
Don haka duk sa’adda aka gano mai ita a koda yaushe ne kuma komai tsawon lokaci, ya zama dole a yi mata hukuncin dukiyar da aka san adadinta kuma aka san mai ita, don haka ya zama wajibi ne a biya shi.
4- Jahiltar Mai Dukiya Da Jahiltar Adadi
Dukiyar da ba a san mai ita ba, ba a san adadinta ba, sai a bincika game da shi, idan ba a same shi ba, alhalin wannan dukyar tana cakude da dukiyar wanda take hannunsa.
Wannan dukiyar idan ta yadu a cikin dukiyarsa sai fitar da humusin dukiyarsa domin tsarkake ta.
Malamai sun yi sabani kan cewa shin dukiyar gwamnati wato wacce take ta al’umma ce dukiyar da aka jahilci mai ita ce, ko kuma dukiyar da aka san mai ita ce, sai wadannan hukunce-hukuncen su bi ta.
Idan malami ya yi ijtihadi a kan cewa dukiyar gwamnati an san mai ita, to a nan babu wani ikon dauka a yi amfani da ita, amma idan malami yana ganin ta a matsayin dukiyar da aka jahilci mai ita, to a nan yana nufin ya halatta mutum ya yi tasarrufi da ita.
Sai dai hatta malamanmu da suka tafi a kan ra’ayin cewa dukiyar gwamnati tana da hukuncin wanda ba a san mai ita ba ne, su ma sun tafi a kan cewa duk wani tasarrufi da ita wannan dukiya dole ne ya kasance da izinin mujtahidin mabiyi.
Sannan kuma ba zai yiwu ya yi wani abu na gaban kansa da irin wannan dukiyar ba sai da izinin wanda yake biyayya gareshi na daga malamai.
Don haka babu wani abu da babu tsari gareshi a cikin shari’a, da shari’a zata yardarwa kowane mutum ya dauki dukiya koda kuwa babu izini gareshi a bisa tsarin kasa da an zo da barna mai girma, da an koma wa rashin tsari wanda zai kai ga arzuta wasu, da talaucin wasu, da wasu sun samu damar fakewa da hakan domin barnar dukiyar al’umma.
Sai dai wannan hukuncin yana kebantar wanda aka ba wa fatawar yin hakan shi ma bisa wasu la’akari da shari’a ta gindaya su. Don haka sai kowa ya koma wa madogararsa domin neman cikakken bayani kan wannan lamari mai hatsari, domin ya kare kansa daga dora wa kansa hakkokin al’umma a kansa, kuma ya samu tsira wurin Ubangijinsa.