Fifita Wasu da gabatar da su a Kanmu
Fifita Wasu a Kanmu
Fifita wasu a kanmu yana daga cikin manyan dabi'u da aka yi umarni da koyi da su a addinin musulunci madaukaki, da wannan halin mai girma ne aka samu cigaba a wannan duniya kuma aka samu daidaituwa a lahira, idan babu wannan halin to fa ba yadda za a yi a samu sadaukarwa da kokarin kai domin samar da gyara da horo da kyakkyawa da hani daga mummuna a cikin al'umma, wasu ruwayoyi sun zo da cewa ita wannan dabi'a ta fifita wasu a kan kawukanmu tana daga mafifitan halaye na gari , kuma alama ce ta bayin Allah na gari .
Yawancin abin da ya sanya al'ummarmu ci baya a wannan zamanin ya taso ne daga rashin wannan halayya mai kyau ta gari, kuma abin da ya sanya al'ummar farko da ta tare a gefen Manzon Allah (s.a.w) samun dacewa shi ne fifita wasu a kanta, don haka ne ma aka samu cigaba. Kuma Allah madaukaki ya yi yabo game da wannan hali da mutanen da suka sifantu da shi a fadinsa cewa: "Suna fifita wasu a kan kawukansu koda kuwa su suna da bukata" .
Sannan kuma muna ganin wasu ruwayoyin sun sifanta wannan dabi'a mai kima da daraja da cewa ita ce mafi kyawun kyautatawa, kuma mafi darajar matakan imani . Ko kuma ita ce mafificiyar ibada, kuma mafi girma a jagoranci .
Girman Wannan Halin
Wannan lamarin ba komai yake nuna mana ba sai cewa wannan sifa tana kunnen doki da salla, domin ansifanta ta da mafificiyar ibada kamar yadda ruwayoyi game da salla suka zo suna fifita ta da wadannan sifofin masu kima da daraja. Na biyu suna nuni zuwa ga cewa babu sifa mafi girma ga shugaban al'umma kuma jagoransu da ta kai wannan sifar girma, kuma dole ne a kanduk wani jagora ya sifantu da ita.
Asasin Ci Gaba
A nahiyoyi irin namu babu wani abu da ya kawo mana ci baya fiye da nisantar wannan sifa madaukakiya da kusantar sifofin da suke kishiyantar ta da suke munana kamar son kai, da fifita kawukanmu a kan wasunmu. Idan mun duba sosai zamu ga jagororin al'umma suna sace dukiyar al'umma kuma suna nuna halin ko in-kula da arzikin mutane, sannan kuma suna da karancin nuna abin da ya damu wannan al'ummu nasu na musibu da bala'o'i, kuma sun kebanci kansu da kula ta musamman kamar zuwa kasashen ketare don magani da kula da lafiyarsu da kuma mafi girman bala'in da ya kawo mana jahilci ya yi yawa sakamakon sun kebanci kansu da su da duk masu karfi da dukiya da makarantu, sai makarantun 'ya'yan talakawa suka rage babu wani abin azo-agani da suke da shi, ga karancin kulawa da abin da suke ciki, to fa wannan duka ya taso ne daga mummunar sifar nan ta nisantar fifita juna da son kai, da fifita kawukansu a kan wasunsu.
Imam Ali (a.s) ya kasance ba ya bacci sai ya tabbatar da babu wani mutum da yake cikin yunwa, kuma yana fifita wasu a kansa da komai tun daga wurin zama har a abin sawa da kuma rabon arzikin kasa, don haka ne ma sai hukumarsa ta kasance abin buga misali a adalci a duniya kuma gun duk ma'abota addinai daban-daban har ranar da kiyama zata tashi.
Da masu karfi da mulki ba su so kansu ba, da ba su fifita kawukansu a kan al'ummarsu ba, to tabbas da mun ga sun yi tarayya da su a abinci da abin sha da wurin zama da makaranta, da dukiyar kasa da rabon arzikin kasa. Da ba mu ga suna hankoro a kan wasoson dukiyar al'umma ba, da ba mu ga sun kebanta da zuwa kasashen waje don lafiyarsu ba, da ba su lalata asibitoci suna wari da karancin gyara da rashin isassun magunguna ba. Da mun ga sun gyara tsaron al'umma ba kawai tsaron kawukansu ba.
Darajar Fifita Wasu
Imam Ali (a.s) bai tsaya a kan sifanta wannan sifa madaukakiya da wadannan kalmomi da muka yi nuni da su ba, ya kara ne ma yana mai nuni da cewa babu wata kyauta mafificiya fiye da fifita wasu a kan kawukanmu, a nan muna iya ganin yadda wannan hali na gari ya samu ladan kyauta da kima da darajar data kai ya dara na kyauta ma domin an ambace shi kuma an sifanta shi da cewa shi ne mafificiyar kyauta .
Fifita Mumini Kawai
Amma idan muka duba ta wani bangaren zamu ga wannan halin ya kebanta da mumini ne kawai da ma’anar cewa mumini ne zamu fifita a kan kawukanmu, da za a ce an kawo ragar sauro to sai mu fifita shi a kanmu, da mun kaddara cewa wannan ragar tana da huda ne a daya bangaren to sai mu juya bangaren da ya fi kyau wurinsa, da sauran sifofi da halaye da suke nuna mun fifita shi a kanmu. Amma muna iya cewa shin wannan misalai sun yi kama da yi wa wasunmu adalci ne ko kuwa sun fi kusa da fifata wasu a kan kawukanmu, domin adalci shi ne ka yi wa mutane abin da kake so a yi maka?.
Wannan yana kasa da fifita wasu a kan kawukanmu, domin wannan shi ne abin da aka umarci mumini ya yi wa duk wata halitta da ya hada da Kafirai da Kirista da Yahudawa da 'yan Buda, da Majusawa, da sauran bayin Allah a matsayinsu na mutane masu hakkin ya yi musu adalci, ya yi musu duk abin da shi ma zai so a yi masa, kuma ya nisantar musu abin da idan aka nisantar masa da shi zai ji dadi.
Amma a koyarwar da shugaban alayen Muhammad (s.a.w) ya nuna wacce kuma ya koya daga dan'uwansa annabi Muhammad (s.a.w), koyarwar sayyidina kuma jagoran jarumawa, sadaukin sadaukai, wanda ya fi kowa jarumta a fagen fama, amma ya fi kowa rauni da kaskan da kai da rusunawa a gaban miskinai da marayu da gwagwaren mata sayyidina Ali (a.s) ya nuna mana cewa ana yin mu'amala da sauran mutane da ba muminai ba da adalci ne, amma kuma mumini sai ka yi mu'amala da shi da fifitawa ne , ka fifita shi a kanka a cikin kowane lamari.
Kuma haka nan Imam Ali (a.s) ya fifita wannan sifa da cewa ita ce kololuwar kyawawan aiyuka lamarin da yake nuni da girman wannan sifa. Kyawawan ayyuka sun hada duk wani alheri da aka yi umarni da shi na ibada ne ko na mu'amala ne, kuma an sanya wannan hali na fifita juna a kan kawukanmu a matsayin kololuwar kyawawan halaye gaba daya, sai aka ambace ta da ita ce kololuwar kyawawa ba tare da togiya ba, don haka ne ma muka ce sun hada da ibadoji da aiyuka da mu'amuloli.
Samun Karubuwa
Wata falala da kima da wannan hali mafi kyau yake da shi ya hada da cewa; da wannan halin ne ake iya mayar da ‘ya’ya bayi a samu karbuwa gun kowa. Mun sani cewa ya zo a cikin hikima cewa: Idan ka girmama mai daraja da mutunci sai ka mallake shi kuma wadannan su ne 'ya'ya, amma idan ka girmama maras mutunci mai taurin kai da girman kai sai ya yi maka dagawa ya daga maka kai ya ma wulakanta ka, wannan kuwa shi ne ya zo a cikin wasu hikimomi daga alayen Annabi (s.a.w).
Ban da Mai Jin-kansa
Don haka ne saudayawa mukan girmama mutum sai ya yi mana girman kai ya wulakanta mu yana dauka cewa wannan girman da aka ba shi sakamakon ya fi kowa cancantarsa ne kuma duk wanda ya girmama shi to yana nuna yana kasa da shi kenan, to haka ne kaskantaccen mutum yake kallon girmama shi, don haka ne ma girman kai gareshi yake zama ibada kamar yadda ya zo a cikin wata hikima. Amma mutum mai karimci da mutunci da kima da sanin yakamata idan aka girmama shi sai ya dada kaskan da kai kuma ya san falalar wannan mutumin da ya girmama shi yana mai kallonsa ta mahangar mutuntaka da kimantawa.
Don haka ne sai masu wadannan kyawawan halaye suka kasance ‘ya’ya, masu wadancan munanan halaye suka kasance bayi, kuma ‘ya’ya a nan ana nufin su masu ‘yancin tunani ne a cikin bayi koda kuwa su bayi ne a wurin Allah (s.w.t), domin ganin da yake yi wa kansa a matsayinsa na bawa a wurin Allah shi ya ba shi wannan sifa a tsakanin mutane ta cewa shi ‘yantacce ne.
Amma wanda yake ganin kansa a matsayin da mai ‘yanci a wurin Allah madaukaki to tabbas shi bawa ne gun bayi koda kuwa a zahiri suna ganinsa a matsayin 'yantacce ko mai 'yanci tun asali, don haka ne ma sai wannan sifa ta fifita wasu a kan kawukanmu take mayar da 'ya'ya bayi a wurin bayin Allah, sai su kalli kansu a matsayin bayi a gaban Allah da kuma a gaban bayin Allah na gari koda kuwa sun kalli kansu a matsayin 'ya'ya masu 'yanci a gaban mutakabbirai masu tsaurin kai da girman kai ko fasikan bayi iyalan shedan.
Misalan Gidan Daukaka
Bisa bayanan da suka gabata na kima da darajar da masu fifita wasu a kansu suke da ita zata bayyana garemu koda ba a ambata ba cewa ma'abota wadannansifofin da halayen kyawawa suna da falala da fifiko fiye da wasunsu, kuma duba zuwa ga yabonsu da madaukaki ya kawo a cikin surar Hashri ya isa girmamawa da jinjinawa ga wadannan bayin Allah na gari.
Ruwayar da Abu Huraira ya kawo ta isa misalin fifikon masu wadannan halaye na gari. Abu Huraira yana cewa: Wata rana wani mutum ya zo wurin Manzon Allah (s.a.w) ya koka da yunwar da yake ji, sai Manzon Allah (s.a.w) ya aika wurin matansa ko zai samu wani abu, sai suka ce: Ba mu da komai sai ruwa. Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Wa ye zai dauki nauyin wannan mutumin a yau? Sai Ali dan Abu Talib ya ce: Ni ya Ma'aikin Allah! Sai ya zo wurin Fadima (a.s) ya ce mata: Me kike da shi ya ‘yar Ma'aikin Allah? Sai ta ce: Ba mu da komai sai abincin dare, sai dai mu zamu fifita bakonmu. Sai ya ce: Ya ‘yar Muhammad! Sanya yara su yi bacci, ki kashe fitila.
Yayin da Ali (a.s) ya wayi gari da safe sai ya zo wajen Manzon Allah (s.a.w) ya ba shi labarin, sai Allah ya saukar da wannan aya. "Kuma suna fifita wasu a kan kawukansu koda kuwa su suna da bukata…” .
Sa'annan muna iya duba misalin fifita wasu a wannan sifa kuma halin ma'aikin Allah Manzon rahama daga daya daga cikin matansa A’isha yayin da take cewa: "Manzon Allah (s.a.w) bai taba koshi a rana uku majeranta ba har ya bar duniya, da ya so da ya koshi, sai dai shi ya kasance yana sadaukar da kansa saboda wasu ne” . Wannan kuwa shi ne mafi girman misali na sadaukar da kai da fifita wasu a kan kawukanmu. Kuma tabbas duk wani wanda ya karanta tarihi ya san cewa annabin rahama shi ne jagoran al'umma kuma shugabanta da Allah ya dora shi a kanta, kuma ya san yadda dukiya wani lokaci take kwararowa musamman a lokutan shekarun karshe na rayuwarsa yadda arziki yake tuttudowa daga ko'ina cikin sasannin yankin nan na larabawa, amma sai ga fiyaiyen halitta ya zabi wasu su koshi shi kuma ya yi kwanaki bai koshi ba! Lallai wannan misali ne mafi girma da ba za a iya samun sa a duk fadin duniyarmu a yau ba!
Kamar yadda hikayar Abut Tufail take nuna mana yadda imam Ali (a.s) ya sayi wani tufafi da ya kayatar da shi amma sai ya yi sadaka da shi yana mai kafa hujja da fadin Manzon Allah (s.a.w) cewa: "Duk wanda ya fifita wasu a kansa, to Allah zai fifita aljanna gareshi ranar kiyama , lamarin da yake nuna mana cewa mafificiyar aljanna ta wadanda suke fifita wasu a kansu ne.
Haka nan idan mun koma zamu ga fadin Imam Sadik (a.s) jikan Sayyida Zahara (a.s) yana mai nakalto labarun sadaukarwar da ta yi ta hanyar fifita wasu a kanta yana mai cewa: "Ya kasance akwai wani sha’ir gun Fatima (a.s) sai ta yi tuwo da shi, yayin da ya dahu sai suka sanya shi a gabansu, sai wani miskini ya zo ya ce: Allah ya yi muku rahama, sai Ali (a.s) ya tashi ya ba shi sulusi –kaso daya cikin uku-. Ba a jima ba sai ga wani maraya, sai marayan ya ce: Allah ya yi muku rahama, sai Ali (a.s) ya tashi ya ba shi sulusi. Sannan sai wani ribatacce ya zoya ce: Allah ya yi muku rahama, sai Ali (a.s) ya tashi ya ba shi ragowar sulusin, ba su dandani wannan abincin ba. Sai Allah madaukaki ya saukar da ayar nan a kansu, kuma wannan aya tana aiki kan kowane mumini da ya yi hakan . Wannan lamarin mai nuna kololuwar sadaukarwa da fifita wasu a kan kawukanmu yana nuna mana girman wannan gida da yake karkashin tarbiyyar Annabi (s.a.w) kuma har ila-yau yana nuna mana cewa wannan lamari bai kebanta da wannan gida ba, shi dai lamari ne da mu ma aka umarce mu da kamanta shi kamar yadda muke iya ganin karshen wannan ruwaya yana nuni da hakan.
Muna iya cewa da za a ba wasu mutane wani abu don su raba a tsakaninsu, sai ya kasance dole ne daya ya fi yawa ko yaya ne, idan kana son ka nuna fifita zabin wasu a kanka to sai ka bari su fara zaba, idan kuwa kai ne mai rabawa sai ka bari su fara dauka, idan kuwa kai ne zaka ba su sai ka mika musu mafifici kuma mafi yawa a ganinka.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.haidarcenter.com