Muassasar alhasanain (a.s)

Annabta

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

ANNABTA

HIKIMAR AIKO ANNABAWA:

Hakika mun kudurce Allah (SWT) ya aiko Annabawa da Manzanni domin shiryar da mutum da kai shi ga samun cikakkiyar kamala da samun arziki tabbatacce, wannan manufar ba ta tabbata har sai idan Allah ya aiko Manzanni, ba dan haka ba da mutum ya nutse a cikin tabon bata; Allah ya ce: (Manzanni ne masu bishara da yin gargadi, domin kar mutane su sami wani hanzari a wajen Allah bayan Manzanni, Allah mabuwayi ne mai hikima).([1])

Tabbas mun kudurce a cikin Manzanni akwai manyansu guda biyar, su ne ma’abota sababbin shari’o’i da sabon littafin Allah, na farko shi ne Annabi Nuhu (A.S), Annabi Ibrahim, Annabi Musa, Annabi Isa, na karshen su Annabi Muhammad (SAW). Allah ya na cewa: “Ka tuna lokacin da muka karbi alkawuransu, da na ka da na Nuhu (AS) da na Ibrahim (AS) da na Musa (AS) da na Isa dan Maryam (AS) mun karbi alkawarin ku da gaske [wato ba wasa]).([2])

Allah (SWT) yana cewa: (Ya Muhammad ka yi hakuri kamar yadda manyan manzanni suka yi).([3])

Lallai mun kudurce tabbas Annabi Muhammad (SAW) shi ne cikamakin Annabawa kuma karshen Manzanni, shari’arsa ta game duk mutane kuma wanzajjiya ce matukar duniya ba ta kare ba, ma’anar hakan shi ne duk ilumummuhka da hukunce-hukunce kai har ma da koyarwar Musulunci sun game komai tare da amsa duk bukatun dan Adam na fili da na zahiri, duk wata sha’awa sabuwa ta Annabta ko Manzanci da’awar karya ce wacce dole a yi watsi da ita, Allah ya ce: (Muhammad (AS) bai zama mahaifin daya daga cikin ku sai dai shi Manzon Allah ne kuma cikamakin Annabawa, Allah fa shi ne masanin komai).([4])

 

(13): ZAMANTAKEWA TSKANIN MABIYA ADDININ ALLAH:

Duk da cewa mun lura addinin Musulunci shi ne addinin Allah na gaskiya a wannan zamanin, mun sakankance da wajiban zaman lafiya da sauran mabiya addinai, sun zauna ne a kasashen Musulmai ko sun zauna a wajen kasashen mu ne, sai dai wanda ya daga tutar yakar Musulmai da Musulunci, Allah yana cewa: (Allah bai hana ku yin alheri har ma da yin adalci ga wadanda ba su yake ku ba, kuma ba su fitar da ku daga gidajen ku ba, hakika Allah yana son masu adalci).([5])

Tabbas mun sakankance cewa zai yiwu a bayyana hakikanin Musulunci har ma da koyarwarsa ga kowa ta hanyar gudanar da magana ta hankali tare da yin munakasha (wato karar da juna ta hanyar hujja) a cikin wasu mas’aloli, mun gamsu da cewa Musulunci yana da karfin jawo masu neman gaskiya zuwa gare shi tare da waiwayo da su gare shi idan aka bayyana musu menene Musulunci, musamman a wannan duniyar da mutane suka fuskanto shi domin kiyaye wannan sakon.

Don haka ne bamu yadda da a dankarawa mutane Musulunci ba, Allah yana cewa: (Babu tilastawa a cikin addini, ai shiriya ta bayyana bata ya matsa gefe guda).([6])

Hakika mun gamsu da cewa babu kirna da ya fi kamar Musulmai su yi riko da koyarwar addinin su, kamar yadda Imam Ja’afarussadik (AS) yake cewa: (Ku kasance masu kiran mutane ba da harshen ka ba (wato da aikin ta hanyar bin addini sak da kafa) ba bukatar a takurawa mutane tare da yi musu dole don su karbi Musulunci.

 

(14): ISMAR ANNABAWA:

Mun gamsu da cewa duk Annabawa Allah ya kare su daga yin laifi da kura-kurai a gaba dayan rayuwarsu (kafin Annabta da bayanta), Allah ya tsare su daga kura-kurai ko kuma abu ya rikice musu, Allah ne ya karfafe su da haka; domin Annabin Allah idan ya yi kuskure ko laifi to ya rabu da wannan makarin da yake tsare da kambun Annabta, to a wannan lokacin mutane ba za su aminta da shi ba a matsayinsa na tsani tsakanin su da Allah, ballantana ma su rike shi abin koyi kuma shugaba a cikin ayyukan su.

Saboda haka muka kudurce duk zahirin wasu ayoyin Kur’ani wadanda akan iya zaton cewa wasu Annabawa sun yi kura-kurai, to wannan yana nufin barin abin da ya fi ne (manufa zabin abinda bai fi ba, akan wanda ya fi, tare da cewa kowanne ya halatta), ko kuma mu ce kamar yadda daya daga cikin A’immatu Ahlil baiti (A.S) ya ce: “Kyawawan ayyukan bayi masu nagarta su ne kura-kuran makusanta, (wadanda Allah ya yadda da su).([7]) domin kowane mutum ana duba irin aikin da ya dace da matsayinsa ne.

 

(15): ANNABAWA BAYIN ALLAH NE:

Mun kudurce cewa babban abin alfahari a wajen Annabawa (AS) shi ne kasancewar su bayin Allah masu yi masa biyayya, don haka ne kullum a sallolin mu na yau da gobe muke mai-maita kalmar ‘ash’hadu anna Muhammadan Rasulullah, wa ash’hadu anna Muhammadan abduhuu wa rasuluhu’.

Mun tabbatar cewa ba wani Annabi da ya yi da’awar allantaka, ballantana ya kira mutane su bauta masa; {Ba wani mutum don Allah ya bashi littafi da hukunci da annabta ya cewa mutane ku bauta mini ku bar Allah}.([8])

Haka Annabi Isa (A.S) bai cewa mutane su bauta masa ba, shi kansa ya dauki kansa a matsayin bawan Allah kuma Manzonsa, Allah yana cewa: (Annabi Isa baya kyamatar ya zama bawan Allah, haka ma Mala’iku ba sa kin su zama bayin Allah).([9])

 

(17): MATSAYIN CETON ANNABAWA:

Hakika mun tabbatar cewa Annabawa (A.S) musamman Sayyadina Muhammad (SAW) suna da damar ceto; domin za su ceci wasu masu laifi: {Babu wani mai ceto sai bayan izinin Allah (SWT)}.([10])

{Waye zai yi ceto a wajen Allah, ai sai bayan Allah ya bada izini}.([11])

Idan wasu ayoyi sun kare ceto kamar: (Tun kafin wata rana ta zo wacce babu ciniki, ba soyayya ba ceto)([12]), to ana nufin ceton da ba izinin Allah, ko ceton wanda bai kai matsayin yin ceto ba; domin ayoyin Kur’ani - kamar yadda muka fada - wasu sashi suna fassara sashi.

Tabbas mun hakikance mas’alar ceto tsari ne mai muhimmanci na tarbiyyar dai-daikun mutane, tare da mayar da masu laifi zuwa ga madaidaiciyar hanya tare da karfafa su akan takwa da raye manufa a cikin zukata; saboda mas’alar ceto ba aba ce mara kan gado ba, ta game wanda ya can-canci a cece shi ba kowa ba, abin nufi wanda laifuffukan sa ba su yi yawan da zai zama alaka tsakanin mai sabo da mai ceto ba ta yanke ba; dangane da haka ceto a matsayin tsoratar da masu laifi ya ke don kar su rusa gadar dake bayansu, kar kuma su bar hanyar dawowa dan kar su rasa can-cantar a waiwaye su don a cece su.

Muna karantawa a kissar Annabi Yusuf (A.S) ‘yan uwansa sun yi tawassali da mahaifin su (Sun ce: ya mahaifin mu ka nema mana gafarar laifin mu, hakika mun kasance masu laifi). Sai mahaifin su ya amince da abin da suke so, sai ya ce: (Ai zan neman muku gafarar Ubangijina).([13]) Wannan dalili ne wanda ke nuni akan cewa tawassali ya watsu a wannan al’ummar.

Sai dai wajibi ne kar yin tawassali ya jawo a ketare abin da hankali ya yadda da shi, kar kuma a shige gona da iri a cikin yinsa, kar kuma a bawa waliyyai kudra ta kansu a wajen tasiri, kar kuma ya surantu a zukata cewa za’a iya wadatuwa da izinin Allah, wannan zai jawo yin shirka da kafirci.

Kamar yadda tawassali ya wajaba kar a dorashi ya yi kama da bautar waliyyai; saboda hakan kafirci ne kuma shirka ce, saboda basa iya mallakarwa kansu amfani ko cutarwa ba tare da yardar Allah ba: (Ka ce ban mallaki amfani da cuta ba a karan kaina, sai dai abin da Allah ya so).([14])

Muna iya ganin shige gona da iri da kuma sakaci a cikin mas’alar tawassali a cikin baki dayan jahilan kungiyoyin Musulunci, wanda wannan yana bukatar shiryar da su tare da nusar da su.

 

 

([1])            Suratun Nisa’i: (165).

([2])            Suratul Ahzab: (7).

([3])            Suratul Ahkaf: (35).            

([4])            Suratul Ahzab: (40).

([5])            Suratul Mumtahina: (8).

([6])            Suratul Bakara: (206)

([7])            Mujlisi ya kawo wannan ma’anar a Biharul Anwar daga dayan ma’asumai, 25: 2.5.

([8])           

([9])           

([10])           Suratu Yusuf: (97-98).

([11])           Suratul A’araf: (188).

([12])           Suratul Nisa’i: (64).

([13])          

([14])          

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)