Annabta 2
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
CI GABA DAGA INDA MUKA TSAYA
(17): MATSAYIN CETON ANNABAWA:
Hakika mun tabbatar cewa Annabawa (A.S) musamman Sayyadina Muhammad (SAW) suna da damar ceto; domin za su ceci wasu masu laifi: {Babu wani mai ceto sai bayan izinin Allah (SWT)}.([1])
{Waye zai yi ceto a wajen Allah, ai sai bayan Allah ya bada izini}.([2])
Idan wasu ayoyi sun kare ceto kamar: (Tun kafin wata rana ta zo wacce babu ciniki, ba soyayya ba ceto)([3]), to ana nufin ceton da ba izinin Allah, ko ceton wanda bai kai matsayin yin ceto ba; domin ayoyin Kur’ani - kamar yadda muka fada - wasu sashi suna fassara sashi.
Tabbas mun hakikance mas’alar ceto tsari ne mai muhimmanci na tarbiyyar dai-daikun mutane, tare da mayar da masu laifi zuwa ga madaidaiciyar hanya tare da karfafa su akan takwa da raye manufa a cikin zukata; saboda mas’alar ceto ba aba ce mara kan gado ba, ta game wanda ya can-canci a cece shi ba kowa ba, abin nufi wanda laifuffukan sa ba su yi yawan da zai zama alaka tsakanin mai sabo da mai ceto ba ta yanke ba; dangane da haka ceto a matsayin tsoratar da masu laifi ya ke don kar su rusa gadar dake bayansu, kar kuma su bar hanyar dawowa dan kar su rasa can-cantar a waiwaye su don a cece su.
Muna karantawa a kissar Annabi Yusuf (A.S) ‘yan uwansa sun yi tawassali da mahaifin su (Sun ce: ya mahaifin mu ka nema mana gafarar laifin mu, hakika mun kasance masu laifi). Sai mahaifin su ya amince da abin da suke so, sai ya ce: (Ai zan neman muku gafarar Ubangijina).([4]) Wannan dalili ne wanda ke nuni akan cewa tawassali ya watsu a wannan al’ummar.
Sai dai wajibi ne kar yin tawassali ya jawo a ketare abin da hankali ya yadda da shi, kar kuma a shige gona da iri a cikin yinsa, kar kuma a bawa waliyyai kudra ta kansu a wajen tasiri, kar kuma ya surantu a zukata cewa za’a iya wadatuwa da izinin Allah, wannan zai jawo yin shirka da kafirci.
Kamar yadda tawassali ya wajaba kar a dorashi ya yi kama da bautar waliyyai; saboda hakan kafirci ne kuma shirka ce, saboda basa iya mallakarwa kansu amfani ko cutarwa ba tare da yardar Allah ba: (Ka ce ban mallaki amfani da cuta ba a karan kaina, sai dai abin da Allah ya so).([5])
Muna iya ganin shige gona da iri da kuma sakaci a cikin mas’alar tawassali a cikin baki dayan jahilan kungiyoyin Musulunci, wanda wannan yana bukatar shiryar da su tare da nusar da su.
(19): ASALIN KIRAN ANNABAWA DAYA NE:
Mun kudurce cewa baki dayan Annabawa masu yin tarbiyya ne kuma suna nuni a kan manufa daya, wannan manufar ita ce ci gaban mutuntaka ta hanyar yin imani da Allah da ranar alkiyama da koyarwa tare da yin tarbiyya ingantacciya, kai har da karfafa tushen dabi’u masu kyan a zamantakewar al’umma; don haka muna girmama baki dayan Annabawa, wannan shi ne abin da Kur’ani ya dora mu a kai: (Bama banbantawa tsakanin Manzannin Allah).([6])
Hakika addinin Allah sun cika a hankali, sannan koyarwawr Addinin ta yi zurfi tare da wucewar zamani, kuma tare da yunkurin mutane don su karbi wannan koyarwar, har dai a karshen zangon cikar addinan ya zo wanda shi ne karshe, wato addinin Musulunci: (A yau ne na kammala muku addinin ku na cika muku ni’imata na yadda da ku yi addinin Musulunci).([7])
(20): ANNABAWA MAGABATA SUN BADA LABARIN ANNABAWA MASU ZUWA:
Tabbas mun sakankance cewa Annabawa da yawa sun bada labarin zuwan Annabawan da ke bayan su, tabbas Annabi Musa (A.S) da Isa (A.S) sun bada labarin zuwan Annabi Muhammad (SAW) har da bada bishara, domin wasu littattafan su sun kunshi hakan har ya zuwa yau: (Su ne wadanda suke bin Manzo na Ummulkura wanda suka same shi a rubuce a cikin Attaura da Injila, wadannan su ne masu rabauta).([8])
Don haka ne tarihi ya rawaito mana cewa; Yahudawa da yawa sun kasance suna kaiwa da komowa a Madina kafin zuwan addinin Musulunci domin jiran bayyanarsa; saboda littattafansu sun bada labarin zuwan sabon addini a cikin wannan kasar mai tsarki, tabbas wasu sun yi imani bayan bayyanar addinin a lokacin da wasu suka yi tawaye kuma suke ganin ci bayan su ya zo.
(21): ANNABAWA DA GYARAN AL’AMURAN RAYUWA:
Lallai mun kudurce cewa addinan da Allah ya saukarwa da Annabawa, musamman addinin Musulunci, ba fa wai kawai sun zo ne domin gyaran rayuwar dai-daikun mutane ba ne kawai, ba su kebanta ba a cikin wasu al’amura da gyaran dabi’u ba kawai, su wadannan addinan suna yunkurin gyara al’amuran duniya ne gaba daya, hakika mutane da yawa sun koyi wasu ilumummukan rayuwar yau da kullum daga wajen Annabawa, wanda wannan shi ne abin da wasu ayoyin Kur’ani suka nuna.
Mun gamsu da cewa tsayar da adalci shi ne babbar manufar Annabawa a cikin al’umarsu: (Tabbas mun aiko Manzanni da hujjoji, sannan mun saukar musu da littafi da ma’auni domin mutane su tsaida adalci).([9])
(22): WATSI DA KABILANCI:
Tabbas mun kudurce cewa Annabawa (AS) musamman Annabi Muhammad (SAW) sun kasance suna watsi da kabilanci da fifita dangi, suna yiwa mutane gaba daya kallon abu daya, duk da cewa sun banbanta a yare da jinsi; littafin Allah mai girma yana yiwa dangogin mutane magana: (Ya ku mutane! Hakika mun halicce ku maza da mata, kuma mun sanya ku dangogi da kabilu don ku san junan ku, hakika fiyayyen ku a wajen Allah shi ne wanda ya fi tsoron Allah).([10])
An rawaito a wani sanannen hadisi, an karbo daga Manzon Allah (SAW) yayin da yake magana a Mina lokacin aikin Hajj mutane kewaye da shi: “Ya ku mutane! Hakika Ubangijin ku daya ne, mahaifin ku ma daya ne. babu fifiko ga balarabe akan ajami, babu fifiko ga wanda ba balarabe ba akan balarabe, haka nan ma baki bai fi fari ba, kamar yadda fari bai fi baki ba sai dai wanda ya fi tsoron Allah. Shin na isar da sako?”, sai suka ce: Kwarai, sai ya ce: “Wanda ya ji ya isar da sakon ga wanda bai ji ba”.([11])
(23): MUSULUNCI DA FIDIRAR DAN’ADAM:
Tabbas mun kudurce cewa tsiron iri na imani da Allah da tauhidi da koyarwar Annabawa tabbataccen abu ne tare da kowane mutum, Annabawa ne suka shayar da su da ruwan wahayi kuma suka nisantar da su daga cutarwar shrika da lalacewa: (Fidirar Allah wacce ya halicci mutanen a kanta babu sauyi gamew da fidirar Allah wannan shi ne Addini madai-daici sai dai mafi yawan mutane ba su sani ba).([12])
Saboda haka, mutum tun asalinsa yana tare da addini, amma tunanin rashin addi daga baya ya zo kamar yadda malaman tarihi suka fada - lallai an gane cewa duk bangaren da aka takura masa dan ya bar addini, to da zarar ya sami sararawa zai dawo ya yi riko da addininsa, a nan ba zai yiwu mu yi musun cewa lalacewar wayewar magabata ce ta jawo gurbatar tunanin addini har ya cudanya da karyace-karyace a wajen mutanen ba, Annabawa sun kasance suna bada gudunmawa mai muhimmanci don a kawar da karyace-karyace daga addini da kuma tabbatar da tauhidi wanda hankali ya amince da shi.
([1]) Suratu Yusuf: (97-98).
([2]) Suratul A’araf: (188).
([3]) Suratul Nisa’i: (64).
([4])
([5])
([6]) Suratul Bakara: (285).
([7])
([8]) Suratul A’araf: (157).
([9]) Suratul Hadied: (25).
([10]) Suratul Hujurat: (13).
([11]) Totsinu Kurdubi, 9:6162.
([12]) Suratul Rum: (30).