Muassasar alhasanain (a.s)

Halifanci Wajibin Musulunci 1

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

HALIFANCI  WAJIBI NA  MUSULUNCI

Halifanci a Musulunci yana daga cikin tabbatattun abubuwa na asasi wajen gina al’umma musulma sannan daga cikin wajiban rayuwa ta Musulunci da ba za a iya wadatuwa daga shi ba. Da shi ne ake kafa abin da ake bukata na tsarin duniya da lahira, da shi ne ake tabbatar da adalcin da Allah Yake son ganin an tabbatar da shi a bayan kasa. Don haka dole ne mu tsaya kadan don yin bahasi kansa saboda alakar da yake da shi da Shi’anci. Ga kadan daga ciki:

ªMa’anarsa

Halifanci a isdilahi na shari’a shi ne jagorancin al’umma na gaba daya cikin lamurran duniya da lahira a madadin Manzon Allah (s.a.w). Ibn Khaldun ya fassara shi da cewa: Halifanci a mahangar shari'a daukan nauyi ne na gaba daya wajen tabbatar da maslahar duniya da lahira saboda a mahangar shari'a al'amurran duniya suna komawa ne ga maslaha ta lahira, a hakikanin gaskiya halifanci riko ne da aikin wanda ya zo da shari'a wajen kare addini da siyasar duniya[1].

Al-Mawardi kuma ya fassara shi da cewa: Halifanci ne annabta wajen kare addini da siyasa ta duniya[2].

ªIttifakin (Musulmi) Kan Wajibcinsa

Dukkan musulmi sun tafi kan wajibcin tabbatar da halifanci. Ibn Hazm al-Andalusi yana cewa:

“Dukkanin Ahlussunna, da marja’ah da dukkan ‘yan Shi'a da dukkan Khawarijawa sun yi ittifaki kan wajibcin imamanci, da kuma wajibcin dake kan al’umma wajen tabbatar da shugabancin shugaba adali da zai tsayar da hukumce-hukumcen Ubangiji wanda Manzon Allah (s.a.w) ya zo da su in ban da wata jama'a na wadanda suka kauce wa tafarki, su sun ce tabbatar da imamanci ba wajibi ne na al’umma ba, face dai wajibin shi ne su aiwatar da adalci a tsakaninsu. Babu abin da ya saura na wannan kungiya a halin yanzu, ana jingina su ne ga Najda bn Umair al-Hanafi. Ra’ayin wannan kungiya dai yasasshe ne bisa abin da dukkanin kungiyoyin da muka ambata a baya suka tafi a kai na rashin ingancinsa. Alkur’ani da Sunna sun tafi kan wajibcin samar da shugaba kamar yadda ya zo cikin fadin Allah Madaukakin Sarki cewa:

﴿أَطِيعُواْ اللّهَ وَأَطِيعُواْ الرَّسُولَ وَأُوْلِي الأَمْرِ مِنكُمْ

“Ku yi da’a ga Allah, kuma ku yi da’a ga ManzonSa, da ma’abuta al’amari daga cikinku”, har zuwa karshe[3].

ªBukatar Halifanci

Amma dangane da bukatar halifanci tsakanin al'umma hakan lamari ne da babu yadda za a iya wadatuwa da barinsa a dukkan yanayi saboda alakar da yake da shi rayuwar musulmi gaba daya. Saboda dole ne al'umma su sami wani shugaba da zai dinga kula da al’amurransu, ya magance musu matsalolinsu, ya tsayar da hukumcin Allah da Sunnar Ma’aiki, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa, a tsakaninsu saboda shari’ar Musulunci wani gungu ne na hukumce-hukumce da dokoki da suka hada da haddi, ukuba, da umurni da kyawawa da hani da munana, da kuma jihadi fi sabilillah, da fada da talauci da kore laifuka da yada ilimi da kyawawan dabi’u da ladubba da sauran hukumce-hukumce da mutum guda ba zai iya aiwatar da su ba tare hannun hukuma ba.

Ibn Taimiyya yana cewa: “Kula da al’amurran mutane na daga cikin manyan wajiban addini kai addini ma ba zai tsaya ba tare da shi ba, saboda Allah Ya wajabta umurni da kyawawa da hani da munana, da taimakon wanda aka zalunta da sauran abubuwan da Allah ya wajabta irinsu jihadi da tsayar da adalci da tsayar da haddi, dukkan wadannan abubuwa ba za su tsayu in ba tare da karfin hukuma ba”[4].

Wasu marubuta suna cewa: “Halifanci wata dawwamammiyar bishiya ce, tushenta tsayayye ne karfin girmanta kuwa yana ci gaba tsawon tarihi cikin zukatan dukkan musulmi. Haka nan shi (halifanci) wata bishiya ce da ba ta mutuwa kuma ba ta lalacewa. Kowani musulmi yana son ganin an samu wani da zai wakilci annabinsa, shin wanda ke zaune ne yankin Saberiya mai tsananin sanyi ko kuma wanda ke zaune yankin Chadi mai tsananin zafi da bushewa. Halifa shi ne mutumin da yafi soyuwa cikin zukatan musulmi, sannan halifanci shi ne kudubin Musulunci da musulmi gaba dayansu suke kewaye da shi[5].

Ala kulli hal, halifanci tushe ne na gina al’umma musulma sannan garkuwa ta musamman wajen kare musulmi daga wuce haddin makiya. Shi ne ke kare musu mutumcinsu da ‘yancinsu da kare su daga makircin kafirai masu kulla musu makirci ba dare ba rana.

Akwai hadisan Ma’aiki (s.a.w) da yawa da suke magana kan wajibcin samar da shugaba ga musulmi. Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Duk wanda ya mutu ba tare da bai’a a wuyansa ba, ya yi mutuwar jahiliyya da sauran hadisan da aka ruwaito daga gare shi.

ªAnnabi da Halifanci

Manzon Allah (s.a.w) ya ba da gagarumin muhimmanci ga sha’anin halifanci da imamanci a bayansa saboda yana daga cikin rukunai masu muhimmanci wajen tabbatar da hukumarsa ta Musulunci, saboda shi halifanci ci gaba ne na hukumarsa da wanzuwar shari’arsa. Ya kwatanta shi da sakonsa na kadaita Allah lokacin da ya kira zuriyarsa zuwa ga imani da sakon da ya zo da shi don ya dauki wani mutum daga cikinsu a matsayin mataimakinsa wajen isar da sakonsa sannan wazirinsa kuma halifansa a bayansa. Babu wanda ya amsa daga cikinsu in ban da Imam Amirul Muminin Ali (a.s), don haka ya ce musu: Wannan shi ne dan’uwana, wazirina kuma halifana a bayana, ku saurare shi kuma ku yi masa biyayya[6].

Saboda tsananin muhimmancin da yake ba wa lamarin halifanci, Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Duk wanda ya mutu ba tare da ya san imamin zamaninsa ba ya mutu mutuwar jahiliyya.

A lokacin rayuwarsa Manzon Allah (s.a.w) ya magance dukkanin matsalolin da suke fuskantar musulmi ta hanyar tsara hanyoyin da suka dace mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne ayyana halifa a bayansa da zai ci gaba da tabbatar da adalcin Musulunci da yin hukumci tsakanin mutane da shari’ar Allah Madaukakin Sarki. Hakika mafi wautan ra’ayuyyuka kuma wanda yafi nisa daga gaskiya shi ne fadin cewa: Manzon Allah (s.a.w) ya yi watsi da wannan bangare mai muhimmanci wadda sa’adar al’umma da kare ta daga fadawa cikin fitina da bata ke cikinsa. A hakikanin gaskiya yin rikon sakainar kashi ga wannan lamari tamkar ruguza al’ummar da Musulunci ya gina ne da barinta cikin bala'i da fitinar rayuwa.

Manyan matsaloli da rikice-rikicen da musulmi suka fuskanta da suka yi sanadiyyar mutuwar dubban musulmi, – ko shakka babu – sun samo asali ne daga rikon sakainar kashi da aka yi wa nassosin da suka fito daga wajen Ma’aiki (s.a.w) da suka ayyana wanda zai zamanto halifan Ma’aiki a bayansa da kebanci ga Ahlulbaitin Manzo (s.a.w) a matsayinsu na masu isar da sakon Allah a bayan kasa.

Sayyid Muhammad Sayyid al-Kilani yana cewa: “Hakika wasu mutane sun yi tsananin gasa da rikici kan halifanci wanda da wuya a samu irinsa cikin sauran al’ummomi. Sun aikata duk wani nau’i na wuce haddi da mu kanmu ba za mu iya aikatawa ba wajen cimma wannan manufa da suka hada da zubar da jini, ruguza birane da kauyuka, mai da mataye zaurawa da mai da yara marayu”[7].

Ala kulli hal, ta ya ya za a yi Manzon Allah (s.a.w) wanda aka aiko shi a matsayin rahama ga dukkanin talikai, wanda batar al’ummarsa ta kasance abin damuwa gare shi, ya bar al’amarin al’ummarsa haka nan kawai cikin rudu ba tare da ayyana mata wani shugaba da zai kula da al’amurranta ba a bayansa.

ªAnnabi ya Ayyana ALI

Yana da kyau a san cewa halifanci a Musulunci ba lamari ne na son zuciya da 'yan garanci ba, face dai lamari ne mai matukar muhimmanci a duniyar musulmi, saboda daga nan ne ake tsara dukkanin al’amurran da suka shafi makomar al’umma.

Abin da babu kokwanto cikinsa bisa ga tabbatattun hujjoji na ilimi da tarihin Ma’aiki (s.a.w) shi ne cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ayyana Imam Ali (a.s) ga wannan matsayi mai girman gaske da nada shi a matsayin halifansa a bayansa kamar yadda wasu ingantattun nassosi daga wajen Ma’aiki (s.a.w) suka tabbatar da hakan suna masu nuni da irin matsayin da yake da shi na cewa shi ne kofar birnin iliminsa, kuma yana tare da gaskiya sannan gaskiya tana tare da shi sannan kuma matsayinsa a wajensa kamar matsayin Haruna ne a wajen Musa. A bangare guda kuma al’amarin Ghadir ma ya tabbatar da hakan a fili yayin da Manzon Allah (s.a.w) ya karbi mubaya’ar al’ummar musulmi ga Imam Ali (a.s) a matsayin shugaban musulmi a bayansa. A wancan lokacin matayen Manzon Allah da sauran musulmi sun yi masa bai’a kamar yadda Umar bn Khaddab ma ya taya shi murnar wannan matsayi da ya samu da cewa: “Ina taya ka murna Ya dan Abi Talib, daga yanzu ka zamanto shugabana kuma shugaban dukkanin muminai maza da mata”[8].

Mubaya'ar da musulmi suka wa Imam Amirul Muminin Ali (a.s) a Ghadir ya kasance wani bangare ne na sakon Musulunci kuma rukuni daga cikin rukunansa, duk wanda ya yi inkarinsa kuwa ya kauce wa hanya.

Zamu ci gaba a fitowa ta gaba inshallahu:-

Amincin Allah ya tabbaga manzo muhammad da alayensa tsarkaka

 

 

 

[1]- Muqaddimat Ibn Khaldun, shafi na 166.

[2]- Al-Ahkam al-Sultaniyya.

[3]- Al-Milal wa al-Ahwa, 4/87, ayar kuma tana cikin Suratul Nisa'i 4:59.

[4]- Al-Siyasat al-Shar’iyya, shafi na 172-173.

[5]- Ittihad al-Muslimin, shafi na 207.

[6]- Dukkan musulmi sun tafi kan ingancin wannan hadisi.

[7]- Athar al-Tashayya’ fi al-Adab al-Arabi, shafi na 15.

[8]- Hadisin Ghadir yana daga cikin abin da dukkanin musulmi suka amince da shi.

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)