Halifanci Wajibin Musulunci 2
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
HALIFANCI WAJIBI NA MUSULUNCI
Ci Gaba Daga Makala Tafarko:-
ME YA SA ANNABI
YA ZABI ALI?
Da dama sukan yi tambayar cewa me ya sa ne Annabi (s.a.w) ya zabi Imam Amirul Muminin Ali (a.s) a matsayin halifa a bayansa? Amsar wannan tambaya dai a fili take, saboda ya duba ne da idon basira cikin dukkanin sahabbansa da danginsa bai ga wani da ya dace da wannan matsayi mai girman gaske kamar Imam Amirul Muminin Ali (a.s) ba. Saboda shi ne ya fi sauran mutane kusanci da Manzon Allah (s.a.w) kuma wanda ya fi su sanin hakikanin sakon Musulunci da manufarsa, don haka ya ayyana shi a matsayin halifa a bayansa. Hakan lamari ne da ba shi da alaka da son zuciya ko 'yan garanci, Allah Ya kiyaye Manzon Allah (s.a.w) daga hakan, saboda matsayin annabcin da Manzon Allah (s.a.w) yake da shi ya tsarkake shi daga bin son zuciyarsa. Manzon Allah (s.a.w) dai ya zabi Ali (a.s) ne a matsayin shugaban al’ummarsa gaba daya kuma halifa a bayansa saboda irin dacewar da yake da shi ga wannan matsayi sama da wanisa. Ga kadan daga dalilan da suke tabbatar da hakan:
Na Farko: Imam Ali (a.s) ya mallaki kwarewa mai girman gaske na ilimi, da cikakkiyar masaniyan hukumce-hukumcen Musulunci musamman a bangaren shari’a inda ya zama gagarabadau. Malaman tarihi sun ruwaito shahararriyar maganar nan ta halifa Umar inda yake cewa: “Da ba don Ali ba da Umar ya halaka”, babu wani da yake da irin wannan kyauta da ni'ima da Ali yake da ita. Imam Ali (a.s) ya kasance daga cikin shugabannin da suka yi fice wajen ilimi da sanin ya kamata a bangaren siyasa da zartarwa. Wasiyyarsa ga Malik al-Ashtar (lokacin da ya nada shi gwamnar Masar) babbar hujja ce da take tabbatar da hakan. Wasiyyar ta sami mazauni cikin sha’anin siyasar Musulunci sama da duk wata wasiyya ko umarni a siyasar Musulunci da ma waninta. A cikinta an bayyana hakkin al’umma kan hukumarsu irinsu nauyin dake kanta na tabbatar da tsaro da walwalar al’umma, kamar yadda aka bayyana alakar da ke tsakanin rayuwar mahukunta da talakawansu, haka nan kuma an yi bayani kan sharuddan da dole ne mahukunta su mallaka irinsu kwarewa, amana da cikakkiyar masaniya kan ayyukan da aka dora musu, mallakar dabi’u na kwarai, tsantsaini cikin addininsu da dukiyar gwamnati da dai sauran bangarorin da wannan wasiyya ta kumsa da suka kasance tushen siyasar Imam Ali (a.s) wajen tabbatar da adalci a bayan kasa. Akwai kuma wasu wasiku da wasiyoyinsa ga gwamnoninsa da ma’aikatansa inda yake kiransu zuwa ga kula da al’amurran al’umma da kyautata rayuwarsu, hakan na tabbatar da irin masaniyar al'amurran siyasa da yake da ita.
Kamar yadda Imam Ali (a.s) ya kasance mafi sanin al’amurran siyasa cikin musulmi haka ya kansace mafi saninsu cikin sauran ilmummuka irinsu ilimin akida da falsafa, ilimin lissafi da sauransu. Al-Akkad yana cewa: Ya bude da dama daga cikin kofofin ilmummuka da suka kai talatin. Bisa la’akari da irin wannan gagarumin ilimi da Imam Amirul Muminin Ali (a.s) yake da shi, ya ya za a yi Manzon Allah (s.a.w) ba zai zabe shi ga wannan matsayi na halifanci ba wanda ‘yanci da mutumcin al’ummarsa suka dogara da kansa.
A mahangar Musulunci wanda yake fifita maslahar al’umma kan komai dimbin ilimi maras haddi da Imam Ali (a.s) yake da shi ya isa ya sanya shi ya zamanto wanda za a zaba wajen jagorantar al’umma sama da waninsa, saboda Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:
﴿هَلْ يَسْتَوِي الَّذِينَ يَعْلَمُونَ وَالَّذِينَ لاَ يَعْلَمُونَ﴾
“Ashe wadanda suka sani, suna daidaita da wadanda ba su sani ba?[1]”. Ashe ba wauta da bata ba ne maganar da wasu suke yi na halalcin gabatar da wanda aka fi a kan wanda ya fi, hakika wannan zance ya saba wa koyarwar Musulunci wacce ta wajabta gabatar da malamai a kan waninsu wajen dora musu kula da lamurra masu muhimmanci da hatsarin gaske, hana su wannan matsayi kuwa ba abin da zai haifar in banda lalata al’amurra.
Na Biyu: Imam Amirul Muminin Ali (a.s) ya kasance daga cikin mafiya jaruntar mutane, wanda jaruntakarsa ta mamaye ko ina. An ruwaito shi yana cewa: “Da dukkan larabawa za su hadu wajen yakana ba zan juya baya ba”. Addinin Musulunci ya tsaya ne da takobinsa ya kuma ginu ne sakamakon jihadi da kokarinsa. Ya taka gagarumar rawa da nuna jaruntaka a yakin Badar, Hunain da Ahzab, shi ne ya sare kawukan mushirikai da sanya bakin ciki cikin gidajen kafiran Kuraishawa. Babu wani gibi da za a samar cikin Musulunci face ya toshe shi. Manzon Allah (s.a.w) ya kan gabatar da shi a matsayin shugaba a dukkan lokuta, kamar yadda ya nada shi jagoran sojojinsa na gaba daya. Babu wani yaki da makiya za su kawo wa musulmi face sai Allah Ya ba da nasara ta hannunsa. Shi ne ya kaskantar da yahudawa da wulakanta su, sannan ya karya garkuwar Khaibar, ya kassara karfinsu sannan ya kashe wutar fitinarsu.
Jaruntaka wata siffa ce da wajibi ne duk wani jagoran al’umma ya zamanto yana da ita, saboda idan ya zamanto rago to babu shakka kasa za ta fuskanci bala'i da barazana.
Sakamakon samuwar wannan siffa da dukkan ma’anarta wajen Imam Amirul Muminin (a.s) ya ya za a yi Manzon Allah (s.a.w) ba zai ayyana shi a matsayin halifa kuma imami a bayansa ba…jaruntakar da Imam (a.s) yake da ita wacce dukkanin siffofi na kamala take biye mata ta sanya ya dace da jagorantar al’umma ko da kuwa babu wani nassi daga wajen Annabi (s.a.w).
Na Uku: Daya daga cikin siffofi masu muhimmancin da dole ne duk wanda zai zamanto halifa ya mallaka ta ita ce watsi da son kai da fifita maslahar al’umma sama da komai da taka tsantsan cikin dukiyar musulmi. Wadannan siffofi suna daga cikin siffofin da aka san Imam Ali (a.s) da su lokacin hukumarsa. Musulmi da wasunsu ba su san wani shugaba mai gudun duniya da dukkan kyalkyale-kyalkyalenta kamar Imam Amirul Muminin (a.s) ba. Bai taba tara dukiyar gwamnati don amfanin kansa ko iyalansa ba, ya kasance mai nesantar duniya iyakacin nesanta. Ya nuna wa musulmi siyasar da tushenta shi ne adalci da gaskiya hakikaninta. Ya kasance mai daidaita tsakanin musulmi dukkansu wajen hakkoki da wajibai, da kuma wajen bayarwa haka nan a gaban doka. Babu wata mazhaba ko addini da ya kafa doka ko tsara wani tsari na daidaitawa da adalci tsakanin al’umma da take tabbatar da karamar ‘yan’Adam da hakkinsu na rayuwa kamar yadda ya yi.
Na Hudu: Daga cikin siffofin da wajibi ne duk wani jagoran al’umma ya mallaka ita ce dole ya zamanto mai tsoron Allah da tsantsaini, babu wani abin duniya da zai yi masa tasiri wajen biyayya ga Allah Madaukakin Sarki. Wannan siffa tana daga cikin fitattun siffofin da aka san Imam Amirul Muminin Ali (a.s) da su. Ya kasance mai kyamar duk wani abin da ba zai kusanta shi da Allah Madaukakin Sarki ba. Ya kasance yana cewa: “Wallahi da za a bani sammai bakwai da abin dake kasansu don in saba wa Allah wajen kwace kwayan hatsi a bakin tururuwa lalle ba zan aikata haka ba”. Shi ne babban mai kira zuwa ga Allah bayan Ma’aiki (s.a.w), ya kawata tafarkinsa da hudubobin dake cike da kira zuwa ga tsoron Allah da tsoratar da mutane ukubar Allah da ba a taba ganin makamancinsa ba daga wani daga cikin shugabannin musulmi.
Daga cikin alamun tsoron allansa shi ne kin amincewar da yayi ga bukatar da Abdurrahman bn Awf ya gabatar masa na ba shi halifanci bayan kashe Umar da sharadin zai yi aiki da sunnar ‘manya biyu da suka gabace shi’ (halifa Abubakar da Umar), amma ya ki amincewa da hakan yana mai jaddada cewa zai yi aiki ne da Littafin Allah da Sunnar ManzonSa da ijtihadin kansa. Da a ce yana daga cikin masu son mulki ido rufe ne da ya amince da hakan daga baya ya yi aiki da ra’ayin kansa idan Ibn Awf ya yi masa magana ya sa a tsare shi.
Hakika duniya, duk da irin abubuwan da suka faru a cikinta, ba ta taba ganin wani shugaba irin Imam Amirul Muminin Ali (a.s) ba wajen tsantsaini, tsoron Allah da nesantar soyace-soyacen zuciya ba. Ya shirya kansa wajen aiwatar da adalci tsakanin musulmi ta yadda ba a taba jin kukan wanda aka zalunta, mara shi ko fakiri ba.
Wannan kadan kenan daga rayuwar Imam Ali (a.s), ya ya za a yi Manzon Allah (s.a.w) ba zai ayyana shi halifansa ba. Idan ma muka koma ga batun gado da Muhajirai suka kafa hujja wa Ansar da shi har suka yi galaba a kansu, to ai Imam Ali (a.s) shi ne ya fi cancanta ga Manzon Allah (s.a.w) sama da waninsa, domin shi dan baffan Annabi (s.a.w) ne, mijin ‘yarsa kuma mahaifin jikokinsa. …yana cewa: Idan ma abin a amince da mahangar gado ne da hakan ya taimaka wa Ali tun farko, da ya hana rikice-rikicen da suka faru da zubar da jini a Musulunci. Da mijin Fatima ya kara wa matsayinsa hakkin gado a matsayinsa na halaltaccen magajin Manzon Allah (s.a.w), kamar yadda yake da hakki ta bangaren zabe. Dubi da idon basira da tunanin da ya saba wa son zuciya suna iya tabbatar da cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ayyana Imam Amirul Muminin Ali (a.s) a matsayin halifa kuma shugaba a bayansa ba tare ma da la’akari da ka’idar gado da sauransu ba, kai siffofin shugabanci da yake da su ma kawai sun wadatar.
Babu shakka maganar cewa babu wani abin da Manzon Allah (s.a.w) yayi wajen zaba wa al’ummarsa halifa a bayansa da cewa ya bar al’amarin ne a hannun musulmi su zabi wanda suke so lamari ne da babu gaskiya cikinsa. Hakan ya saba wa rayuwar Manzon Allah (s.a.w) wanda ke nuna damuwarsa matuka kan sa’adar al’ummarsa da kare ta daga dukkan bata da kauce wa hanya.
Amincin Allah ya tabbaga manzo muhammad da alayensa tsarkaka
[1]- Suratuz Zumar 39:9.