AHLULBAITI (A.S) A QUR'ANI DA HADISI

AHLULBAITI (A.S) A MAHANGAR ALKUR’ANI DA SUNN

 

 

Manzon Allah (s.a.w) ya sanya garkuwa don kare al’ummar daga fitina da bata a bayansa su ne kuwa Ahlubaitinsa, magada iliminsa, masu yada hikimarsa sannan mafiya imanin al’ummarsa da shiriya da kyawawan dabi’u. Ya tarbiyatar da su tsoron Allah, tsantsaini da riko da Musulunci. Alkur’ani mai girma da hadisan Ma’aiki (s.a.w) cike suke da bayanan falalolinsu da matsayinsu mai girma. Ga wasu daga cikinsu da suke da alaka da abin da muke magana a kai:

A MAHANGAR ALKUR’ANI
MAI GIRMA

Alkur’ani mai girma, wanda bata ba ta zuwa masa ta gaba ko ta baya, ya ambaci falalar Ahlulbaiti (a.s) da girman matsayinsu, Allah Madaukakin Sarki Ya yabe su da hakan ya wadatar da su daga yabon masu yabo da kuma siffantawar masu siffantawa. Ga wasu daga cikin ayoyin da suka yi magana kan falalolinsu:

ªAyar Soyayya

Allah Madaukakin Sarki Ya wajabta soyayya da kaunar Ahlulbaiti (a.s) cikin LittafinSa mai tsarki, Yana cewa:

﴿قُل لاَ أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ أَجْرًا إِلاَّ الْمَوَدَّةَ فِي الْقُرْبَى وَمَن يَقْتَرِفْ حَسَنَةً نَّزِدْ لَهُ فِيهَا حُسْنًا إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ شَكُورٌ

“Ka ce: ‘Ba ni tambayar ku wata lada a kansa, face dai soyayya ga makusanta’. Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, Za mu kara masa kyau a cikinsa, lalle Allah Mai gafara ne, Mai godiya”[1]. Hakika soyayyar Ahlulbaiti (a.s) lada da sakayya ce ga aikin da Manzon Allah (s.a.w) ya yi da kuma godiya gare shi kan wahalar da ya sha wajen tseratar da musulmi daga shirka da ‘yantar da hankulansu daga camfe-camfen jahiliyya. Allah Madaukakin Sarki Ya sanya wilaya ga Zuriyar Ma’aiki a matsayin wajibi a kan dukkan musulmi.

Imam Muhammad bn Idris al-Shafi'i yana cewa:

Ya Aāli baitin Manzon Allah son ku

Farali ne daga Allah cikin Alkur’ani da ya Saukar.

Ya ishe ku babban abin alfahari cewa ku ne

Duk wanda bai yi salati a gare ku ba, ba shi da salla[2].

Ibn al-Arabi yana cewa:

Na fahimci biyayya ta ga Zuriyar Daha a matsayin wajibi

Duk da kin ma’abota nisanta, son ya gadar mini da kusanci.

Wanda aka aiko bai nemi lada akan shiriya ba

Don isar da sako, face kaunar makusanta.

Al-Kumait Mawakin Ahlulbaiti yana cewa:

Mun sami aya a gare ku cikin Alu Hamim

Wanda fakihi cikin mu da masanin larabci suka fassara.

Maruwaita suna cewa: Wani Balaraben kauye ya zo wajen Manzon Allah (s.a.w) ya ce masa: Ya Muhammad, ka nuna min Musulunci, sai ya ce masa: Ka shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Shi da abokin tarayya, kuma Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa. Sai Balaraben kauyen yace:

  • “Shin kana bukatar wani lada ne daga wajena kan hakan”?
  • “A’a…sai dai kauna ga makusanta…”
  • “Makusantana ko makusantanka?”
  • “Makusantana…”.
  • “Kawo hannunka in yi maka mubaya’a, la’anar Allah ta tabbata ga wanda ba ya sonka, kuma ba ya son makusantanka”.
  • “Amin..”[3].

Shugaban masu sujada Imam Zainul Abidin Aliyu bn Husain (a.s) ya kafa hujja da wannan aya mai girma lokacin da aka zo da shi gaban Fir’aunan zamaninsa Yazid bn Mu’awiyyah a matsayin fursunan yaki yayin da wani mutum daga mutanen Sham ya ce masa:

  • “Godiya ta tabbata ga Allah da Ya kashe ku ya kawo karshenku, sannan Ya yanke tushen fitinarku..”.

Sai Imam (a.s) ya kalle shi, ya fahimci mutum ne da bai san inda aka sa gaba ba, farfagandar Umayyawa ta yi masa tasiri, ta kautar da shi daga hanyar da ta dace, sai ya ce masa:

  • “Shin kana karanta Alkur’ani?..”.
  • “Na’am…”.
  • “Shin ka taba karanta Aāli Hamim?..”.
  • “Ina karanta Alkur’ani, amma ban karanta Aāli Hamim ba”.
  • “Shin ba ka karanta:

﴿قُل لاَ أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ أَجْرًا إِلاَّ الْمَوَدَّةَ فِي الْقُرْبَى﴾.

Nan take mutumin ya dawo cikin hankalinsa, ya fahimci cewa yana bisa kuskure, sai ya ce:

  • “Ku ne wadannan mutane?...”.
  • “Na’am…”[4].

Wata rana Jikan Manzon Allah (s.a.w) Imam Hasan (a.s) ya yi ishara da wannan aya mai girma da cewa ta sauka ne dangane da su, yana cewa: “Ina daga cikin Ahlulbaitin da Allah Ya wajabta soyayyarsu kan dukkan musulmi, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:

﴿قُل لاَ أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ أَجْرًا إِلاَّ الْمَوَدَّةَ فِي الْقُرْبَى وَمَن يَقْتَرِفْ
حَسَنَةً نَّزِدْ لَهُ فِيهَا حُسْنًا

Allah Ya sanya abu mai kyau shi ne soyayyarmu Ahlulbaiti”[5].

Kaunar Ahlulbaiti (a.s) na daga cikin manyan farillolin Musulunci kuma daga cikin mafi muhimmancin wajiban addini saboda alakar da take da shi ga Manzon Allah (s.a.w).

ªAyar Mubahala

Daga cikin bayyanannun ayoyin Alkur’ani da suka yi bayanin falalolin Ahlulbaiti (a.s) da siffofin da suka kebanta da su daga wasunsu ita ce ayar Mubahala. Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:

﴿فَمَنْ حَآجَّكَ فِيهِ مِن بَعْدِ مَا جَاءكَ مِنَ الْعِلْمِ فَقُلْ تَعَالَوْاْ نَدْعُ أَبْنَاءنَا وَأَبْنَاءكُمْ وَنِسَاءنَا وَنِسَاءكُمْ وَأَنفُسَنَا وأَنفُسَكُمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَل لَّعْنَةُ اللّهِ عَلَى الْكَاذِبِينَ

“To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, bayan abin da ya zo maka daga ilimi, to ka ce: “Ku zo mu kirayi ‘ya’yanmu da ‘ya’yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, sa’an nan kuma mu kankantar da kai, sa’an nan kuma mu sanya la’anar Allah a kan makaryata”[6].

An saukar da wannan aya mai girma ne sakamakon faruwar wani lamari mai muhimmanci cikin tarihi da ya gudana tsakanin Manzon Allah (s.a.w) da wata tawaga ta Kiristocin Najran da suka zo Yathrib (Madina) don yin mubahala da Manzon Allah (s.a.w) kan Musulunci. Bayan tattaunawa tsakaninsu, sai suka cimma yarjejeniyar sanya la’anar Allah da saukar da azabarSa ga makaryata wadanda suka kauce wa gaskiya, daga nan sa suka tsayar da lokacin da za a yi wannan mubahala. Da lokacin yayi sai Manzon Allah (s.a.w) ya fito da mafi girman daukaka cikin musulmi wadanda Allah Ya fi sonsu, wato kofar birnin iliminsa mahaifin jikokinsa Imam Amirul Muminin Ali (a.s), da tsokarsa tsarkakakkiya shugabar matan duniya Fatima al-Zahra (a.s) da Hasan da Husain shugabannin matasan ‘yan Aljanna.

Tawagar Kiristocin dai ta hada da wani tsoho da malami tare da ‘ya’yansa cikin adon zinariya da sauran kayayyakin ado tare da Farsan bn al-Harith cikin koshin lafiya da cikakken shiri. Amma lokacin da suka ga tawagar Manzon Allah (s.a.w) tare da Ahlulbaitinsa sai suka firgita tsoro ya kama su. Manzon Allah (s.a.w) ya yi musu ishara da mubahalar, ganin haka sai wannan tsoho da malamin suka taso haibar Ma’aiki ta rufe musu ido suka ce masa:

“Da su waye za kayi mubahalar da mu?...”.

Sai Manzon Allah (s.a.w) ya amsa musu da cewa:

“Zan yi mubahala da ku ne da mafi alherin mutanen kasa (duniya) kuma wadanda suka fi girma a wajen Allah” yana mai ishara ga Imam Ali (a.s), Fatima da Hasan da Husain (a.s).

Sai suka ce masa:

“Me ya sa ba za kayi mubahalar da ma’abuta girma da daukaka, wadanda suka yi imani da kai kuma suka bi ka ba”?.

Manzon Allah (s.a.w) ya ci gaba da jaddada musu cewa Ahlulbaitinsa su ne mafiya girma da daukakan halittu wajen Allah Ta’ala yana cewa:

“Na’am zan yi mubahala ne da ku da wadannan mafiya alheri da daukakan halittu..

Sai suka ja da baya, suna masu tabbatar da cewa Manzon Allah (s.a.w) yana kan gaskiya, suka koma wajen shugabansu suka ce masa:

“Ya Aba Haritha, me kake gani (mene ne abin yi)…”?

Nan take shugaban nasu ya rude, sakamakon haibar Ma’aiki (s.a.w) da Ahlubaitinsa, sai ya ce:

“Hakika ina ganin wasu fuskokin da da wani zai roki Allah da su da Ya kawar da dutse daga inda yake, da Ya kawar da shi. Ba ku ga Muhammad ya daga hannuwansa ba, na rantse da al-Masihu idan ya roki wani abu ba zamu koma ga iyali ba….

Ya ci gaba da jan kunnensu yana cewa:

“Ashe ba ku ga rana ta sauya launinta ba, girgije ya mamaye sama, iska ta fara karkadawa ba, ga kuma hayaki na tashi daga wannan dutse. Azaba ta kusan sauko mana, ku dubi tsuntsaye yadda suke aman abin da suka ci, wadannan bishiyoyi kuma yadda suke zubar da ganyayensu, ga wannan kasa yadda take motsi a kasan kafafunmu”.

Wadannan fuskoki masu girma a wajen Allah sun firgita su, nan take sai Kiristocin suka juyo wajen Manzon Allah (s.a.w) suna cewa:

“Ya Abal Kasim, ka rabu da mu Allah……”

Sai suka amince da sharuddan Manzon Allah (s.a.w) yana mai ce musu da sun yarda sun yi mubahalar da dukkan Kiristoci sun halaka:

“Na rantse da Wanda raina ke hannunsa, lalle azaba tana yawo kan mutanen Najran da mun yi mubahalar da sun koma birrai da aladu, da sun kone cikin tafkin wuta, da Allah Ya tumbuke Najran da mutanenta hatta tsuntsayen dake kan bishiya, da shekara ba ta zagayo wa Kiristoci dukkansu ba”[7].

Kissar mubahala tana nuni da irin matsayin da Ahlulbaiti (a.s) suke da shi ne da kuma zamantowarsu tilo da ba su da na biyu a Musulunci wajen imani da tsantsaini. Da a ce Manzon Allah (s.a.w) ya san akwai wasu da suka fi su da ya zabe su wajen yin mubahalar, kai da ma a ce akwai kamansu wajen falala da ya kaddamar da su saboda munin fifita wani abu ba tare da abin fifitawar ba – kamar yadda malaman Usul suke fadi -.

Manzon Allah (s.a.w) bai dauko wani daga cikin iyalansa don yin mubahalar ba, bai dauko baffansa Abbas ba, ko kuma wani daga cikin ‘ya’yan Hashim ba, haka nan bai dauko wani daga cikin ma’abuta daukaka ba, ko wata mace daga cikin matansa ba ko kuma matan halifofi ko wasu daga cikin matan Muhajirai da Ansarawa ba-. Hakan yana nuni da falalar Ahlulbaiti da irin matsayin da suke da shi mai girma a wajen Allah

﴿ذَلِكَ فَضْلُ اللَّهِ يُؤْتِيهِ مَن يَشَاء وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ

“Wannan falalar Allah ce, Yana bayar da ita ga wanda Ya so. Kuma Allah Mai falala ne Mai girma”[8].

Imam Sharafudden Allah Ya yi masa rahama yana cewa: “Kai kanka ka san cewa mubahalarsa (s.a.w) da su da bukatar su dinga cewa amin idan ya yi addu’a hakan shi kansa wata falala ce mai girman gaske. Haka nan zabansu da yayi ga wannan aiki mai muhimmancin gaske da fifita su kan wasunsu daga cikin wadanda suke kan gaba falala ce kan falala da babu wani da ya rigaye su kuma mai riska ba zai riske su ba. Haka nan saukar ayar Alkur’ani mai girma kan a yi mubahala da su wata falala ce ta uku da ke kari kan falalar mubahalar, sannan kuma ya ishe su daukaka da karin haske kan hasken da suke da shi…”[9].

Haka nan kuma ayar tana nuni da cewa Amirul Muminin Ali (a.s) shi ne tamkar Annabi (s.a.w), kamar yadda fadinSa Madaukaki ﴿أَنفُسَنَا وأَنفُسَكُمْ yake nunawa. Idan har Imam Ali (a.s) shi ne tamkar Annabi (s.a.w) to shi ne yafi cancantar halifanci sama da waninsa saboda shi ci gaba ne na zatin Manzon Allah (s.a.w). Kamar yadda ayar take nuni da cewa Imam Ali (a.s) yana sama da dukkan halittun Allah saboda shi tamkar Annabi (s.a.w) ne shi kuwa Annabi (s. a.w.a) shi ne mafi daukakan dukkanin halittu. Imam Fakhrurrazi yana cewa: “Akwai wani mutum mai suna Mahmud bn Hasan al-Hamsi malami ne na (Shi'a) Ithna Ashariyya, ya kasance yana da’awar cewa Aliyu yafi dukkanin Annabawa in banda Annabi Muhammad (s.a.w) yana dogaro da ayar ﴿أَنفُسَنَا وأَنفُسَكُمْ, ba tamkar Annabi (s.a.w) ake nufi ba a nan saboda mutum ba ya kiran kansa, face dai waninsa ne ake nufi. Dukkan malamai sun tafi kan cewa wannan wanin shi ne Aliyu bn Abi Talib (a.s). Ayar tana nuni da cewa ran Aliyu shi ne ran Muhammad. Ba ana nufin shi wannan rai shi ne wancan rai din ba, abin nufin shi ne wannan rai irin wancan ran ne. Hakan yana tabbatar da daidaito tsakaninsu a dukkanin bangarori in banda annabta, saboda Muhammad Annabi ne shi kuwa Ali ba haka yake ba. Babu kokwanto cewa Muahammad (s.a.w) yafi Ali (a.s)… kuma dukkanin malamai sun tafi kan cewa Annabi Muhammad (s.a.w) yafi dukkanin Annabawa (a.s), idan haka ne kuwa to Ali yafi sauran Annabawa[10].

ªAyar Abrar

Daga cikin bayyanannun ayoyin da suka bayyanar da falalar Ahlulbaiti (a.s) da fifikonsu kan wasunsu ita ce Ayar Abrar, Allah Madaukaki na cewa:

﴿إِنَّ الْأَبْرَارَ يَشْرَبُونَ مِن كَأْسٍ كَانَ مِزَاجُهَا كَافُورًا َ*عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا عِبَادُ اللَّهِ يُفَجِّرُونَهَا تَفْجِيرًا* يُوفُونَ بِالنَّذْرِ وَيَخَافُونَ يَوْمًا كَانَ شَرُّهُ مُسْتَطِيرًا

“Lalle ne mutanen kirki za su sha daga finjalin giya, abin gaurayarta ya kasance kafur ne. Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna bubbugar da shi bubbugarwa. Suna cikawa da alwashin (da suka bakanta), kuma suna tsoron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne”[11]. Dukkanin malaman tafsiri[12] sun tafi kan cewa an saukar da wannan aya ne kan Ahlulbaiti (a.s). Malaman sun ce dalilin saukar ayar shi ne cewa wata rana Hasan da Husain (a.s) sun yi rashin lafiya, sai Manzon Allah (s.a.w) da wasu daga cikin manyan sahabbansa suka zo gaishesu. Sai ya bukaci Imam Ali (a.s) da ya yi bakancen azumin kwanaki uku ga Allah in Ya ba su sauki. Sai Imam Ali (a.s) ya yi bakancen azumin kwanaki uku, Fatima al-Zahra (a.s) tare da mai musu hidima Fiddha su ma suka yi. Lokacin da Hasan da Husain (a.s) suka sami sauki sai dukkansu suka dauki azumin, alhali kuwa Imam Ali (a.s) ba shi da komai na abinci a gidansa, don haka sai ya karbi aron sa’i uku na Sha’ir, sai Fatima al-Zahra (a.s) ta dauki sa'i guda ta yi biredi da shi. Lokacin da suka zo shan ruwa sai wani miskini ya kwankwasa kofa yana neman su taimaka masa da abinci, sai suka ba shi abin da suka tanada na abinci, suka ci gaba da azumin ba su ci komai ba in banda ruwa.

A rana ta biyu ma ‘yar Manzon Allah (s.a.w) Fatima (a.s) ta shirya biredin da za su ci, lokacin da suka zo shan ruwa sai ga wani maraya nan yunwa ta dame shi ya bukaci su taimaka masa sai suka ba shi dan abincin da suka tanadar, ba su ci komai ba in banda ruwa.

A rana ta uku ma Shugaban matar duniya (a.s) ta shirya biredi da sauran abin da ya rage na Sha’iri din, lokacin da suka zo shan ruwa sai ga wani fursunan yaki ya kwankwasa kofa yana bukatar su taimaka masa da abinci, sai suka tsame hannunsu daga abincin suka ba shi.

Tsarki ya tabbata ga Allah, wace sadaukarwa ce tafi wannan, wace kyauta ce tafi wannan kyauta wacce ba a nufin komai da ita in banda yardar Allah Madaukaki.

A rana ta hudu sai Manzon Allah (s.a.w) ya gansu cikin mawuyacin hali jikkunansu sun yi laushi saboda yunwa, sai ya ce:

“Subhanallah! A’a ga Ahlulbaitin Muhammad nan za su mutu da yunwa”.

Manzon Allah (s.a.w) bai rufe bakinsa ba sai ga Jibrilu (a.s) ya sauko yana dauke da gaisuwa da yabon Ahlulbaiti daga wajen Allah, yana gabatar musu da sakayyar wannan kyauta tasu, sakayya ce da ba za a iya kwatantata da wani abu ba, kyauta ce ta gafara da rahama da yarda ta Allah Madaukakin Sarki. Allah Ya yi musu sakayya da Aljanna da tufafin hariri saboda hakurin da suka yi, ya kuma saukar musu da Sura cikin LittafinSa da take nuni da girman matsayinsu a wajen Allah.

ªAyar Tsarkakewa

Daga cikin ayoyin Alkur’ani mai girma da suka sauko kan Ahlulbaiti (a.s) ita ce ayar tsarkakewa. Allah Madaukakin Sarki na cewa:

﴿إِنَّما يُرِيدُ اللّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَ يُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا

Hakika Allah Yana nufin Ya tafiyar da kazanta daga gare ku ne, Ya ku mutanen babban gida, Ya tsarkake ku tsarkakewa”[13].

An ruwaito Uwar Muminai Ummu Salma tana cewa: “An saukar da wannan aya ce a gidana a lokacin Fatima da Ali da Hasan da Husain (a.s) suna nan, sai Manzon Allah (s.a.w) ya rufe su da wani mayafi ya ce: ‘Ya Allah wadannan su ne Ahlubaitina, ka tafiyar da kazanta daga gare su ka tsarkake su tsarkakewa’ ya ta nanata hakan. Ummu Salma tana tsaye tana gani sai tace: Ni ma ina cikinku Ya Rasulallah? Sai ta daga mayafin don ta shiga, sai ya rike shi ya ce mata: Ke dai kina kan alheri[14]. Daga nan sai aka saukar da wannan aya dangane da su[15] da a fili take nuni da tsarkakarsu daga dukkan dauda da zunubi. Ayar ta fara ne da kalmar (إِنَّما) wace kalma ce ta kebancewa, sannan kuma aka kara da sanya ‘lam’ da kara maimaita lafazin tsarkakewa, dukkan hakan na nuni da kebance su daga kawar da dukkanin kazanta da zunubi. Hakan shi ne ma’anar isma da Shi'a suke cewa Imamansu suna da ita…

Wasu kenan daga cikin ayoyin da aka sauka da su saboda Ahlubaiti (a.s).

 

[1]- Suratush Shura 42:24.

[2]- Al-Sawa’ik al-Muhrika, shafi na 88.

[3]- Hilliyatul Awliya’, 3/201.

[4]- Tafsir al-Dabari, 25/16.

[5]- Hayatul Imam al-Hasan, 1/68.

[6]- Suratu Al Imrana 3:61.

[7]- Nurul Absar, shafi na 100.

[8]- Suratul Hadid, 57:21.

[9]- Al-Kalimat al-Garra’, shafi na 184.

[10]- Tafsir al-Razi, 2/488.

[11]- Suratul Insan, 76:6-7.

[12]- Asbab al-Nuzul na al-Wahidi, shafi na 33, Tafsir al-Razi, 8/392, Ruhul Ma’ani, 6/546, Yanabi’ul Mawadda, 1/93 da Imta’ul Asma’ na al-Makrizi, shafi na na 502.

[13]- Suratul Ahzab: 33:33.

[14]- Mustadrak al-Hakim, 2/416 da Asad al-Gabah 5/521.

[15]- Tafsir al-Fakhr 6/783, Sahih Muslim 2/331. al-Khasa’is al-Kubra 2/264, Al-Riyadh al-Nadhra 2/188, Musnad Ahmad bn Hambal 4/107, Sunan al-Baihaki 2/150, Jalaluddeen al-Suyuti cikin Durul Mansur ya kawo ruwayoyi ashirin da suke nuni da cewa an saukar da ayar ne kan Ahlulbaiti. Shi kuwa Ibn Jarir ya kawo ruwayoyi goma cikin tafisirinsa.