AHLULBAITI (A.S) A KUR'ANI DA HADISI 3

CIGABA DAGA MAKALA TA BIYU:-

WILAYAR SHI'A
GA AHLULBAITI

Hakika wilayar ‘yan Shi'a da kaunarsu ga Ahlulbaiti (a.s) ba ta kasance ta son zuciya da koyi ido rufe ba, face dai bisa bayyanannun hujjoji daga Littafin Allah da Sunnar Ma’aiki (s.a.w). Don haka suke kaunarsu da kuma riko da su don babu yadda za su iya juya wa Littafin Allah da Sunnar ManzonSa baya.

Tun farko-farkon tarihinsu an san Shi'a da imani da kaunar Ahlulbaiti (a.s) a matsayin wani bangare rayuwarsu ta akida. A nan wajibi ne mu yi bayani kan wilaya da kaunarsu ga Zuriyar Manzon Allah (s.a.w), shin akwai wuce haddi ko kauce wa addini cikin hakan:

Da Farko: ‘Yan Shi'a suna karbar hukumce-hukumcen addini ne gaba daya daga wajen Imaman Ahlulbaiti (a.s), sun yi imani da wajibcin aiki da maganganu da ayyukansu saboda hakan na daga cikin Sunnar da wajibi ne a yi aiki da ita. Don haka suka gina akidunsu bisa ruwayoyin da aka ruwaito daga wajen Imamai (a.s), ba wai bisa son zuciya ba, sai dai saboda samuwar ingantattun nassosi da suka wajabta hakan. Imam Sharafuddeen Allah Ya yi masa rahama yana cewa:

“Hakika rikonmu da abin da ya saba wa Ash’ariyya cikin akida da mazhabobi hudu cikin furu'i ba don kungiyanci ko ‘yan garanci ba ne, ba kuma don shakku cikin ijtihadin Imaman wadannan mazhabobi ba ne ko kuma rashin adalcinsu da amanarsu da tsarkinsu da daukakansu ta ilimi da aiki ba ne.

Sai dai don hujjoji na Shari’a sun wajabta mana riko da mazhabar Ahlubaitin Annabi, matsugunin sako, wajen shige da ficen Mala’iku, wajen saukar wahayi. Don haka muka koma wajensu cikin furu’in addini da hukumce-hukumcensa da Usulin fikihu da dokokinsa, da ilimin Sunna da Alkur’ani, da ilmummukan kyawawan dabi’u da hukumce-hukumce, muna masu koyi da Sunnar Shugaban Annabawa da Manzanni tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da dukkanin Alayensa.

Da a ce nassi ya ba mu damar saba wa Imaman Ahlulbaiti (a.s) ko kuma yiyuwar samun kusanci da Allah Madaukakin Sarki wajen aiki da mazhabar da ba tasu ba da mun bi tafarkin sauran musulmi, da mun yarda da tafarkinsu, don kyautata abokantaka da karfafa ‘yan’uwantaka. Sai dai dalilan da ba za a iya rufe ido kansu ba sun kasance garkuwa ga mumini da hana shi bin son zuciyarsa”[1].

Imam Sharafuddeen ya ci gaba da cewa:

“Ba na jin akwai wanda zai iya cewa Imaman sauran mazhabobi sun fi Imamanmu a wajen ilimi da aiki, saboda su ne Imaman tsarkakakkiyar zuriya, jiragen ruwan tsiran al’umma, kofar tubanta, kariyarta daga sabani a addini, mila-milan shiriyarta kuma nauyayan Manzon Allah (s.a.w). Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Kada ku wuce su sai ku halaka sannan kada ku nuna gazawa dangane da su sai ku halaka, (kada ku ce za ku karantar da su) saboda sun fi ku sani” face dai kawai siyasa ce, me ya sanar da kai abin da ya faru a farko-farkon Musulunci…”.

Shehin Azhar Sheikh Salim ya goyi bayan wannan magana yana cewa:

“Lalle Imamanku goma sha biyu su ne suka fi cancantar a bi su sama da Imamai hudu saboda dukkanin wadannan imamai sha biyu suna kan mazhaba da tafarki guda ne sabanin wadannan hudun, saboda sabanin da ke tsakaninsu a fili yake cikin dukkanin babukan fikihu. A fili yake cewa abin da mutum guda ya cimma ba za a iya hada shi da abin da Imamai sha biyu suka cimma ba…”[2].

A fili yake cewa riko da maganganun Ahlulbaiti da bin tafarkinsu na fikihu ba wuce haddi cikin kauna ba ne, face dai hakan yin abin da ya dace ne.

Na Biyu: Daga cikin abubuwan da suke tabbatar da wilayar ‘yan Shi'a ga Imamansu (a.s) shi ne shirya bukukuwan tunawa da su, bayyana falalolinsu, shirya bukukuwan juyayin musiban da ta same su daga wajen mahukuntar lokacinsu wadanda ba sa fatan samun natsuwa daga Allah, wadanda baa bin da suka sa a gaba in banda kisa da azabtar da su da ‘yan shi’ansu.

Na Uku: Ziyarar da ‘yan Shi'a suke kai wa hubbaren tsarkakan Imamansu don neman albarka da kusanci da Allah suna daga cikin mafi girman alamar kauna da riko da Ahlulbaitin da Allah Ya wajabta wa dukkan musulmi kauna da soyayyarsu. A nan gaba za mu yi bahasi kan rashin ingancin da’awar wasu na cewa ziyarar kabari bidi’a ce.

Wasu kenan daga cikin alamun wilayar Shi'a ga tsarkakan Imamai da babu wata alama ta guluwi cikinta …bisa hakan ne Shi'a suka gina tushen akidarsu ta soyayyar Ahlulbaiti (a.s).

SHI'A DA WUCE HADDI
(GULUWI)

Cikin rashin adalci ana tuhumar ‘yan Shi'a da guluwi (wuce haddi) ga Imamansu duk da cewa sun barranta daga wannan tuhuma. Don haka ya zama wajibi mu dan yi karin bayani kan wannan lamari.

ªHakikanin Guluwi

Hakikanin guluwi shi ne jingina allantaka ga tsarkakan Imamai (a.s), da cewa su ne suka halicci wannan duniya, kuma masu gudanar da al’amurranta, hakan ne ma yasa aka ruwaito wasu masu guluwi kan Imam Amirul Muminin Ali (s.a.w) suna cewa:

Shi ne wanda Ya halaka Adawa

Da Samudawa da azabarSa

Wanda Ya yi magana da Musa

A saman dutsen Tur yayin da ya kira shi.

Wanda ya ce a kan mimbari

Wata rana alhalin yah aye a kansa.

Ku tambaye ni ya ku mutane

Sai suka dimauce a cikin ma’anoninsa

A fili ana iya ganin cikakken guluwi cikin hakkin Amirul Muminin Ali (a.s) cikin wadannan baituka. Wasu ‘yan Gullatun suna riya cewa Imam Amirul Muminin (a.s) dan Allah ne. Sayyid Al-Humaira ya yi magana kansu cikin fadinsa:

Wasu sun wuce iyaka kan Aliyu, babu uba gare su

Sun wahalar da rayuka cikin sonsa suna gajiyawa.

Sun ce shi dan Allah ne, Ya daukaka Mahaliccinmu

A kan Ya zama yana da da ko Ya kasance uba [3].

Wannan shi ne hakikanin guluwi da ke nuni da jingina allantaka ga Imam Ali (a.s) ko kuma ga daya daga cikin ‘ya’yansa tsarkakan Imamai (a.s).

ªBarrantan ‘Yan Shi'a Daga Guluwi

‘Yan Shi'a sun barranta daga ‘yan Gullatu, sun yi imanin cewa su ba sa daga cikin mazhabobin Musulunci, su da kafirai daya suke. Imam Sadik (a.s) yana fadi wa Ruzam cewa: Ka gaya wa ‘yan Gullatu cewa su tuba wa Allah, saboda ku fasikai ne kafirai kuma mushirikai[4].

Sudair ya ruwaito cewa: “Na gaya wa Abi Abdillah (a.s) cewa wasu jama’a suna da’awar cewa ku alloli ne. Sai ya ce masa: Ya Sudair ji na da ganina da fatata da jinina duk sun barranta daga wadannan mutane, Allah da ManzonSa sun barranta daga gare su, lalle wadannan ba sa kan addina da addinin iyayena[5].

Hakika Imaman Shi'a sun barranta daga ‘yan Gullatu, sun bukaci mabiyansu da su kaurace musu da fitar da su daga da’irar addini. Sahl bn Ziyad ya ruwaito cewa: “Wasu daga cikin ‘yan shi’anmu sun rubuta wa Abil Hasan al-Askari (a.s) cewa: In zamanto fansanka Ya shugabana, Ali bn Haska na daga cikin mabiyanka, yana yada cewa kai ne na farko fari (Ubangiji) shi kuma shi ne kofarka kuma Annabinka, wai kai ne ka bukace shi da yayi kira zuwa ga hakan. Yana kuma da’awar cewa saninka ya wadatar daga salla da zakka da hajji da azumi, jama’a da yawa sun yarda da shi. Lalle idan za ka amsa wa mabiyanka hakan zai tseratar da su daga halaka…”.

Sai Imam (a.s) ya rubuta masa amsa kamar haka:

Ibn Haska ya yi karya Allah Ya la’ance shi, kaiconka lalle ni ban sanshi cikin mabiyana ba, Allah Ya la’ance shi. Na rantse da Allah ba a aiko Muhammad da sauran Annabawan da suka gabace shi ba sai da….salla da zakka da azumi da hajji. Kuma Muhammad bai taba kiran mutane ba sai zuwa ga Allah Shi kadai ba Shi da abokin tarayya, haka mu ma wasiyyai daga cikin ‘ya’yansa, mu bayin Allah ne ba ma hada shi da wani.

Ina barranta da Allah daga maganar Ibn Haska, na nesanta kai daga gare shi…na kaurace masa da mabiyansa, Allah Ya la’ance su, ku takura musu, idan kun ga wani daga cikinsu ku buge kansa”[6].

Imam Sadik (a.s) ma ya shelanta bara’arsa daga ‘yan gullatu, wata rana ya ce wa Abi Basir: Ya Aba Muhammad, na barranta daga mutumin da yayi da’awar cewa mu alloli ne, kuma na barranta daga wanda yayi da’awar cewa mu annabawa ne[7]. Malaman tarihi sun tafi kan cewa Amirul Muminin Ali (a.s) ya taba kona wasu mutane da suka ce shi ubangiji ne[8].

Imaman Shi'a (a.s) sun barranta daga ‘yan gullatu, sun tabbatar da kafircinsu da fita daga Musulunci. Malaman Shi'a sun rubuta littafa wajen tabbatar da rashin ingancin akidunsu, daga cikin irin wadannan littafa har da wadanda malamai irinsu Aali Naubakht, Fadhl bn Shazan, Sa’id bn Abdullah al-Ash’ari suka rubuta. Bari mu rufe wannan bahasi namu da maganar Imam Sheikh Muhammad Husain Al Kashif al-Ghita inda yake cewa:

“’Yan Shi'a dai sun barranta daga wannan kungiyar – wato kungiyar ‘yan gullatu – wannan kungiyar ba wai ma tana fadin abin da Kiristoci suke fadi ba ne, a takaice abin da suke fadi shi ne cewa Imam shi ne Allah Madaukakin Sarki a dukkan bangarori da makaman irin wadannan maganganu da mafi yawa daga cikin sufaye da shehunan dariku suke fadi. Mai yiyuwa ne a ruwaito wasu maganganu daga wajen Hallaj da Al-Kilani da Al-Rufa'i da Al-Badwi da makamantansu, idan ka so ma ka kira su kamar yadda suka ce: ….da zahirinsa ke nuni da cewa suna da matsayi sama da allantaka da kuma cewa suna da wani matsayi kari kan allantakan[9] duk da cewa akwai kari ma kan hakan, mafi kusancin hakan shi ne abin da ma’abuta....

Su kuwa ‘yan Shi'a Imamiyya, wato ina nufin (‘yan Shi'a) na Iraki da Iran da Tekun Fasha da Jazirar Larabawa da miliyoyin musulmi na kasar Indiya da darurrukan dubban mutane Siriya da Afghanistan dukkansu suna ganin irin wadannan maganganu a matsayin mafi munin kafirci da bata, tafarkinsu ya saba wa tafarkin Tauhidi da tsarkake Ubangiji Madaukakin Sarki daga dukkanin wata kama irinta abin halitta, ko kuma sanya masa wata siffa ta nakasi da yiyuwa da sauyi da samuwa da duk wani abin da ya saba wa wajibcin samuwa da rashin farko bare karshe da sauran siffofi na Ubangiji da suka yi”[10].

Hakika ‘yan Shi'a sun barranta daga guluwi da bayyana batan ‘yan gullatu da kafircinsu. Jingina guluwi gare su kuwa bata ce da kirkiran (karya) akan ‘yan wannan kungiya wadanda suka yi imani da Allah Shi kadai Wanda ba shi da abokin tarayya da kuma cewa Annabawa da Wasiyyai da sauransu bayin Allah Madaukakin Sarki ne kuma halitta daga halittunSa

 

AMINCIN ALLAH YA KARA TABBATA GA MANZO MUHAMMAD DA ALAYENSA TSARKAKA

 

 

 

[1]- Al-Muraja’at, shafi na 40-41.

[2]- Al-Muraja’at, shafi na 44.

[3]- Al-Aqdul Farid.

[4]- Hayatul Imam Muhammad al-Baqir, 2/106.

[5]- Minhaj al-Maqal, shafi na 207.

[6]- Minhaj al-Maqal, shafi na 229.

[7]- Minhaj al-Maqal, shafi na 320.

[8]- Al-Milal wa al-Nihal, 1/101.

[9]- Daga cikin abin da wasu ‘yan gullatun suke faxi kan Imam Amirul Muminin (a.s) shi ne mafi qarancin abin da za a ce kansa shi ne cewa shi Ubangijini ne makaxaici.

[10]- Hayatul Imam Muhammad al-Baqir, 2/101.