Muassasar alhasanain (a.s)

BABBAR FITINA 4

4 Ra'ayoyi 01.3 / 5

BABBAR

FITINA

 

CI GABA DAGA MAKALA TA UKU

 

4 – Mikdad

Shi kuwa Mikdad yana daga cikin zababbun sahabban Imam Ali (a.s) kuma mai tsananin biyayya gare shi. Yana daga cikin wadanda suka nuna rashin amincewarsu ga Abubakar kan hawa kujeran halifanci da yayi; wata rana ya ce masa:

“Ya Ababakar, ka dawo daga zaluncinka, ka tuba wa Ubangijinka, ka lizimci gidanka ka yi kuka saboda zunubinka, kuma ka mika lamarin ga ma’abucinsa wanda ya fi ka dacewa a kansa. Don kuwa kai kanka ka riga da ka san nauyin da Manzon Allah (s.a.w) ya daura a wuyanka na yi masa mubaya’a[1], ya lizimta maka aiwatar da shi karkashin tutar Usama bn Zaid, ya sanar da rashin ingancin wannan al’amari gare ka da wanda ya taimaka maka isa gare shi, sannan kuma hada ku da shugaban munafukai Amr bn al-Aas wanda Allah Ya saukar wa AnnabinSa (s.a.w) da aya kansa: ﴿إنَّ شَانِئَكَ هُوَ الأَبْتَرُ “Lalle mai aibantaka, shi ne mai yankakkiyar albarka[2].

Sai ya ci gaba da cewa:

“Ka ji tsoron Allah, ka gaggauta yin murabus kafin lokaci ya kure saboda hakan shi ya fi dacewa gare ka a rayuwarka da bayan mutuwarka, kada ka karkata zuwa ga duniyarka, kada ka bari Kuraishawa da wasunsu su rude ka, da sannu duniyarka za ta yi watsi da kai daga nan ka tafi zuwa ga Ubangijinka ya yi maka hukumci kan abin da ka aikata. Ka riga da ka san cewa Ali bn Abi Talib shi ne ya cancanci wannan al’amari bayan Manzon Allah (s.a.w), don haka ka mika masa abin da Allah Ya ba shi, hakan shi ne garkuwa gare ka kuma abin da zai rage maka nauyin abin dake kanka. Lalle wallahi na yi maka nasiha idan ka karbi nasihata, to zuwa ga Allah ne al’amurra suke komawa…[3]”.

Idan da a ce wadannan mutane sun karbi wannan kira ta gaskiya da al’umma ba ta fada cikin fitinu da rarrabuwa tsawon tarihi ba.

5- Buraida al-Aslami

Shi kuwa Buraida al-Aslami[4] yana daga cikin wadanda suka yi imani da hakkin Imam Amirul Muminin Ali (a.s), wata rana ya nuna rashin amincewarsa ga Abubakar da cewa:

“Hakika daga wajen Allah muke kuma hakika wajenSa za mu koma, wani bala'i ne ya fada wa gaskiya daga karya. Ya Ababakar shin ka mance ne ko kuma ka mantar da kanka (da gangan) ne, shin an yaudareka ne ko kuma ka yaudari kanka ko kuma an kawata maka karya ne. Shin ba za ka iya tuna abin da Manzon Allah (s.a.w) ya yi mana umarni da shi na kiran Ali sunan shugaban muminai alhali Annabi yana tare da mu, da kuma fadinsa a lokuta daban-daban cewa: “Wannan Aliyun shi ne shugaban muminai (Amirul Muminin), wanda ya kashe marasa gaskiya (al-kasitun)”. Ka ji tsoron Allah, ka dawo cikin hankalinka tun kafin lokaci ya kure, ka ceto ranka daga abin da zai halakar da shi. Ka dawo da lamarin ga wanda ya fi ka cancantarsa, kada ka ci gaba da kwace shi, ka mai da shi tun kana da halin mayarwa. Lalle na yi maka nasihar gaskiya da kuma shiryar da kai zuwa ga tafarkin tsira…[5]”.

Hakika an kawata wannan huduba da hadisan da aka ruwaito su daga wajen Annabi (s.a.w) da suke magana kan falalar Imam Amirul Muminin Ali (a.s) da kuma cewa shi ne yafi cancantar halifancin Annabi sama da waninsa.

6- Ubaiyu bn Ka’ab

Ubaiyu bn Ka’ab[6] yana daga cikin manyan sahabbai, masu gaskiya da tsoron Allah. Ya ki yarda da halifancin Abubakar da kiransa ga mayar da halifanci ga Imam Ali (a.s) yana cewa:

“Ya Aba Bakar kar ka yi jidali kan hakkin da Allah Ya bai wa waninka, kar ka zamanto mutumin farko da ya saba wa Manzon Allah (s.a.w) dangane da wasiyyinsa da kauce wa umurninsa. Ka mayar da hakki zuwa ga masu shi, ka tsira. Kada ka yi taurin kai sai ka yi nadama. Ka gaggauta mika shi, a saukaka maka nauyin dake kanta. Kada ka ci gaba da rike wannan lamari da Allah bai sanya shi gare ka ba, sai ka fuskanci sakamakon mummunan aikinka. Nan ba da jimawa ba zaka rabu da abin da kake kai, ka tafi zuwa ga Ubangijinka inda zai tambayeka kan laifin da ka aikata, Ubangijinka bai zamanto mai zalunci ga bayi ba…[7]”.

Cikin wannan huduba akwai kira zuwa ga gyara ta gaba daya. Idan da a ce sun amince da wannan kira, da al’umma ba ta fada cikin bala'i da rikicin da ta fada ba.

ZAMU CI GABA A FITOW ATA GABA IN ALLAH YA YARDA

 

[1]-- A nan yana ishara ne ga hadisin Ghadir inda musulmi suka yi bai’a ga Imam Amirul Muminin Ali (a.s) a matsayin halifa. Wannan hadisi ne da malamai suka tafi kan ingancin isnadinsa. Ana iya duba littafin Al-Ghadir, na Allamah Amini, juzu'i na farko

[2]- Suratul Kauthar 108:3.

[3]- Al-Ihtijaj na Tabrisi 1/101.

[4]- Buraida bn al-Hasib al-Aslami: ya musulunta ne kafin yakin Badar, sai dai bai halarci yakin ba sai dai yakin Khaibar da Fathu Makka. Manzon Allah (s.a.w.a) yayi amfani da shi…ya zauna a Madina daga nan kuma ya koma Basra daga nan kuma zuwa Marwa inda ya rasu a can. Ya ruwaito hadisai daga wajen Annabi (s.a.w.a) sannan jama’a kuma suka ruwaito daga wajensa. Ibn Sa’ad Tahzib al-Tahzib 1/432 ya ce ya rasu ne a shekara ta 63 hijiriyya.

[5]- Al-Ihtijaj na Tabrisi 1/101.

[6]- Ubaiy bn Ka’ab: Ba ansare ne (mutumin Madina) shugaban masu karatun Alkur’ani sannan daga cikin sahabban da suka yi bai’a ta biyu ga Ma’aiki a Akaba. Ya halarci yakin Badar da sauran yakukuwan da Manzo (s.a.w.a) yayi, ya kasance daga cikin masu rubuta wahayi kuma daga cikin masu rubuta wa Ma’aiki (s.a.w.a) wasika. Wata rana Manzo (s.a.w.a) ya ce masa: Ya Aba Munzir, wace aya ce ta Littafin Allah tafi girma a wajenka? Sai ya ce: ﴿الله لا إله إلا هو الحي القيومsai Annabi (s.a.w.a) ya bugi kirjinsa ya ce masa: “Allah Ya wadataka da ilimi Ya Aba Munzir”. Ya kasance daga cikin masanan sahabbai. Dangane da shi Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Mafi karatun al’ummata shi ne Ubaiyu”, Umar ya kasance ya kan kira shi da shugaban musulmi. Ya rasu lokacin halifancin Uthman bn Affan a shekara ta 39 hijiriyya kamar yadda ya zo cikin al-Isabah 1/3-32.

[7]- Al-Ihtijaj 1/102.

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)