Muassasar alhasanain (a.s)

WATAN RAMADHANA MAI ALFARMA

5 Ra'ayoyi 01.6 / 5

  Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Watan Azumin Ramadhan Watan Gafara Da Rahama

Allah Ta’ala Ya Kira Ku zuwa Liyafa Ta Musamman

 

Watan ramadan xaya ne daga cikin watanni masu alfarma wadanda Allah mdaukaki ya kebance su da wasu fifice- fifice, wanda daga ciki akwai cewa: shi wata ne da aka haramta zubda jinni a cikinsa (yaki), dss.

Ruwayoyi masu yawa sun zo a kan falalar wannan watan mai albarka, hakika Allah Ta`ala ya cika shi da dumbin falaloli domin ya zama cikakkiyar dama a gare mu, mu masu  zunubai, shi ne watan da dararen sa suka  fi kowane dare, awoyin sa suka fi kowace awa, hakika Allah ya kira mu zuwa liyafarsa a cikin sa, kuma an sanya mu a cikin sa daga cikin ma`abota karamcin ubangiji. Numfashinmu a cikinsa tasbihi ne, barcinmu kuma ibada ne, ayyukanmu ababbna karba ne, kuma addu`o`in mu ababn amsawa ne.

) هو عند الله أفضل الشهور وأيامه أفضل الايام ولياليه أفضل الليالي وساعاته أفضل الساعات هو شهر دعيتم فيه إلى ضيافة الله وجعلتم فيه من أهل كرامة الله أنفاسكم فيه تسبيح ونومكم فيه عبادة وعملكم فيه مقبول ودعاكم فيه مستجاب.(

Hakika na ga ya dace in fitar da hukunce-hukuncen azumi a dunkule, duk da karancin lokacin. Amma wanda yake neman Karin bayani ya nemi: (fassarar littafin (احكا م الاسلام ),  zuwa hausa ko ya koma zuwa karatuttuka da jawaban Allama Shekh Hafiz Muhammad wanda yake turawa ta hanyar sadarwar telegram ko kuma don samun karin bayani.

 

Azumi da hukuncen-hukuncensa.

Za`a iya kasa su magana kan azumi da hukunce- hukuncensa da abubuwan da suke bata shi

zuwa kashi biyar:-

1. Kashe-kashen azumi

2. Sharadan sa.

3. Masu bata shi.

4. Ramuwa.

5. Fatawoyi, duk da cewa wannan kason na karshe zai yi wahala mu samu yin Magana a kan sa saboda karanci lokaci.

 

1->Na farko kashe-kashen azumi.

Azumin ya kasu zuwa kaso hudu.

I. Wajibi, ko dai ya zama, mai zaman kamar azumin watan Ramadan, ko kuma ya zamo wanda wani abu ke sa ya zama wajibi kamar Azumin bakance, da na kaffara dss.

ii. Mustahabbi, shi ma, ko dai ya zama ayyanan ne kamar na alhamis da juma`a da rajab dss, ko wanda ba ayyanan ne ba, shi ne dukkanin azumin da ba na wajibi ko mustahabnbi ko makruhi, ko kuma wanda aka haramta ba.

iii. Makruhi, kamar bako ya yi azumi ba tare da izinin wanda ya sauke shi ba.

iv. Haramtacce, kamar yin azumi ranar idoji guda biyu, (Sallar cin abinci da ta layya).

2-> Sharadan azumi sun kasu zuwa kaso biyu, akwai na wajibci da na inganci.

Amma sharadan wajabcin sun hada da,

  1. Balaga da hankali
  2. wofinta daga haila da na biki.
  3. Rashin cutuwa da kuma rashin lafiya.
  4. Rashin yin tafiyar da take wajabta yin kasaru.

Sharadan ingancin sun hada da

  1. kari a kan sharadan da suka gabata akwai
  2. musulunci da imani
  3. Niya, kuma lokacin ta yana zarce wa har zuwa karkatar rana, idan har a kwai uzurin da ya hana shi yin ta da wuri.

3-> Abubuwan da suke bata azumi

1-2 Ci da sha 3- fitar da maniyyi 4- yin alura ta ruwa 5- ganganta yin amai, 6-ganganta wanzuwa da janaba har zuwa alfilir 7- nutsar da kai a cikin ruwa bisa itayadi 8- shakar kura mai kauri har ya isa makogwaro 6- jima’i wanda ya yi da wanda aka yiwa. kuma baya baci ta hanyar mantuwa da kuma fin karfi, amma yana baci ta hanyar tilastawa, 10 ganganta yiwa Allah Ta’ala da manzo (saw) karya da imamai da sauran manzanni [A. S.]

4->Ramuwar azumi

Ramuwar azumi nau’o’i uku ne,

1) Wannan ramuwa ta kasu zuwa kashi bakwai

A. Ramuwar da ba kaffara

i] Da mai janaba zai yi barci na biyu ko na uku kuma barcin nasa ya ci gaba har alfijir ya bullo tare da cewa yana da niyyar yin wanka .

11, Da zai bata azumin sa ta hanyar yin niyyar yanke azumin ko kuma saboda riya, tare da cewa bai aikata wanji abu da yake karya azumi ba .

iii. Idan ya yi wani abu da yake karya  azumi kafin ya lura da cewa alfijir ya  keto, sai kuma ya gano cewa ya riga ya bullo.

iv. Idan ya manta da wankan janaba har  kwana daya ko har kwanaki suka shude masa.

V. Ci bisa dogaro da labarin cewa yanzu dare ne alhali alfijir ya keto.

v1, Ci bayan mai labari ya ba shi labharin bullowar alfijir, a bisa kudirewar sa cewa izgilance yake masa.

V11, ci abinci ta hanyar dogaro kan labarin cewa rana ta fadin alhali  bata fadi ba, idan mai bada labarin ya zama wanda  za`a iya dogaro  da labarin sa ne.

viii. Cin abinci saboda ya yi yakinin dare ya yi ashe bai shiga ba tare da cewa babu wani dalili da aka samu a sama.

iv. Zarcewar ruwa zuwa cikin makogwaro bayan shigar da shi cikin baki, domin kuskurar shi ko sanyaya shi.

v. Ramuwa tare da kaffara (babba)

I. Zuwa da abin da yake karya azumi da gaggan, banda amai, kuma bisa ihtiyadi idan mutum ya nutsar da kansa cikin ruwa da kuma allura kuma bisa fatawa a cikin sauran, amma ganganta amai baya wajabta kaffara.

II. Kaffara it ace `yanta wuyaye (bawa ko baiwa) ko azumtar watanni biyu ko ciyar da miskinai sittin kuma ba`a maimaita kaffarar da maimaituwar abin da yake wajabta ta a cikin rana guda, koda jinsin ta ya bambanta.

C. Ramuwa tare da kaffara da ta`aziri.

Da zai tara da matarsa cikin watan Ramadan da rana alhali su biyun suna azumi, idan ya zama ya tara da ita tare da yardarta, to kowanne daga cikin su za`a yi masa bulala ashirin da biyar, sannan ya yi kaffara, idan kuma tilastata ya yi, zai dauke mata kaffara da ta`aziri.

D. Ramuwa tare da zuwa da dukkanin kalolin kaffara

Da zai yi kalaci da abin da aka haramta a watan ramadana, wajibi ne ya zo da dukkanin kalolin kaffara guda uku.

E. ramuwa ba tare da kaffara ba.

1. Tsoho/tsohhuwa da mai cutar kishirwa idan ba za su iya yin azumin ba wajibi ne su rama azumin ba tare da kaffara ba idan har suka sami dama ma’ana (za su iya).

ii. wanda ya ci saboda wani uzuri kamar tafiya, sai uzurin ya ci gaba har zuwa wani azumin, ramuwa kawai zai yi.

F. fidiya (fidda`u).

1). mai ciki makusanciya da mai shayarwa mai karancin nono, da ace azumin zai cutar da su ko ya cutar da yayan su.

ii. kaffarar ta su, ita ce su bada uku bisa hudun kilo na abinci.

G. Ramuwa tare da fidda`u

i. wanda ya ci saboda rashin lafiya kuma yanayin ya ci gaba da shi har zuwa wani ramadanan, ya yi kaffara da mudu daya a maimakon kowace rana, kuma ramuwar ta saraya.

2) Hukunce-hukuncen ramuwar watan Ramadan.

i. bai halatta a jinkirta ramuwa zuwa wani watan na Ramadan bisa zabi ba.

 

11, idan ya jinkirta da gangan, ya yi sabo, kuma ramuwar zata zamo tare da kaffara mudu daya a kowace rana.

111, Ya halatta a ciyar kafin karkatar rana idan har ba zai takura kuntata ba

1V, Idan ya karya azumin bayan karkatar rana ya yi sabo kuma kafafra ciyar da miskinai 10 ta hau kansa, idan kuma ba zai iya ba sai ya yi azuin kwana uku.

V. Ya wajaba ga waliyyi ya rama abin da ya tserewa mamacinsa wanda rama shi ya zama wajibi, banda wanin sa, waliyyi a nan shi ne: Babban da namijia cikin `ya`yan da mahaifin su ya rasu ya bari,

3) Wadanda ramuwa bata wajaba a kan su ba.

I. Mahaukaci da wanda ya suma bai wajaba su rama azumin da suka sha ba a lokacin da suke cikin uzuri .

II. Kafiri na asali, ba zai rama abin da ya sha a lokacin kafircin sa ba.

III. Basunne bayan da ya yi istibsari, ba zai rama abin da ya yi daidai da mazhabarsa da ko mazhabar da ya koma ba.

IV. wanda ya balaga da rana, koda kuwa ya kasance kafin karkatar rana ne, ba wajibi ba ne ya yi azumin wannan wunin ba, kuma ba zai rama shi ba.

V. Wanda azumi ya kubuce masa a cikin watan Ramadan saboda rashin lafiya ko haila ko biqi, sai ya/ta mutu kafin watan (ramadanan da yake ciki) ya kare  .

[Muna yi muku fatan alkhairi ]

 

Makomar bincike

Hiwaratun fikihiyya -        na   sayyid sa id alhakim

Uyunu  ahbarir ridha –      na   shek sudduk

Raudhatul wa izin -           na    alfattalun  nasaburi

Aljadid fi tadrisil fikihu-  na    ibrahim  dihini

 

AMINCI YA TABBATA GA MANZO MUHAMMAD DA ALAYENSA DA SS.

 

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)