K'ungiyoyin Bata
K'UNGIYOYIN B'ATA
Mu'assasar Al-Balagh
Ra'ayin Ahlulbaiti Game Da Batattun Kungiyoyi
Babu shakka makiya Musulunci sun san cewa Ahlul-baiti (a.s) su ne mabubbuga ta asali da tsarkakar addini mai kwaranye wa musulmi dukkan wahalhalu da bala'u. Su masu daraja ne a zukatan musulmi bai daya.
Kowa yana ganin girman alkadarinsu, yana tsarkake duk abin da ya fito daga gare su ko ya karkare zuwa gare su. Don haka ne masu neman rushe addini da shuka masa dasisa suke fuskantar wannan tushe na Musulunci domin su sami damar shuka barna alhali suna karkashin inuwar Ahlulbaiti (a.s). Suna daukar tutar Ahlulbaiti (a.s) da sunan goyon bayansu domin su sami damar kaidi da rushe akidar tauhidi, alhali Ahlulbaiti (a.s) sun barranta daga gare su da kuma tsine musu albarka. Wadannan irin jama'a sun kirkiri akidun bata da karkatacciyar falsafa mai cewa Allah Yana hululi (wato Ya shiga jikin wata halitta daga cikin halittunSa) cikin Imamai - Allah Ya daukaka ga barin hakan- da cewa Allah Ya sakar wa Imamai (a.s.) al'amurran arzurtawa da tasiri cikin halittar aljanna da wuta.
Ba su tsaya nan ba sai da sashinsu ya dangantawa Imamai (a.s.) allantaka. Duk hakan kuwa sun yi shi ne domin kaidi wa Musulunci da musulmi da rusa akidar tauhidi. Hakika masu wannan aiki sun sami asali ne daga kungiyoyi irin na Majusawa, Manawiyya da Mazdakawa wadanda suka shiga Musulunci a munafurce, ba tare da sun yi imani ba. Haka nan, akwai tunanin kiristoci da yahudawa a cikin wannan yunkurin rusawa( ) (*).
Wadannan mabarnata sun bi wancan hanyar suka rudar da hankula da shuka rikici da kirkirar ruwayoyi da ra'ayoyi fandararru, suka danganta su ga Ahlulbaiti (a.s) bisa karya. Saboda haka manyan malami suka rubuta littattafai kan masu ruwaya wato Ilmul Rijal domin tona asirin makaryata da masu kirkira da masu munanan akida tun zamanin Manzon Allah (s.a.w.a.) har ya zuwa karshen jerin Imamai (a.s.), amintattun maruwaita daga Manzon Allah (s.a.w.a.). Ta hanyar ne suka jefar da duk wata ruwaya ta karya da kuma duk wani maruwaici mai kirkira ake gane shi, kamar yadda Najashi ya yi cikin sanannen littafinsa nan na Rijalul Najashi da Shaikh Dusi cikin littattafansa na Al-Fihrist da kuma Rijalul Dusi da dai sauransu.
Tarihi yana sanar mana samuwar wasu kungiyoyi fandararru wadanda suka danganta kansu da Ahlulbaiti (a.s) kamar 'yan Gullatu da 'yan Mufawwidha, alhali kuwa Ahlulbaiti (a.s) sun barranta da su, sun la'ane su da kuma koransu. Baya ga haka ma, malaman mazhabar Imamiyya (Shi'a) suna hukumta su da cewa su najasa ne.
Al-Nawbakhti( )(*) cikin littafinsa mai suna Firakush Shi'a ya ambato kungiyoyi daban-daban na 'yan Gullatu da 'yan Mufawwidha, da kuma ambaton matsayar Imaman Ahlulbaiti (a.s) dangane da su, ga kadan daga cikin abin da yake cewa:
"Amma batun sahabban Abul Khaddab Muhammad bn Abi Zainab al-Ajda al-Asadi da duk wanda yake da ra'ayi irin nasa, to lallai sun watse lokacin da suka ji cewa Imam Sadik (a.s.) ya la'anci Abul Khaddab, ya kuma barranta daga gare shi da sahabbansa".
Har zuwa inda yake cewa:
"Wata kungiya daga cikinsu ta ce Abu Abdullah Ja'afar bn Muhammad Sadik shi ne Allah - Allah Ya daukaka ga barin haka daukaka mai girma - sannan Abul Khaddab kuma Annabi ne mursali.
Wata kungiyar kuwa cewa ta yi: "Ja'afar bn Muhammad shi ne Allah - Wal iyazu billah- kuma Shi Allah (S.W.T.) wani haske ne mai shiga jikkunan wasiyyai ya kuma zauna a cikinsu. Wannan haske sai ya kasance shi ne Ja'afar bn Muhammad Sadik, sannan ya fita daga jikinsa ya shiga jikin Abul Khaddab( )".
Bayan al-Nawbakhti ya bijiro da wadannan batattun akidu sai ya ce:
"Wadannan kungiyoyin 'yan Gullatu masu da'awar Shi'a, sun sami asali ne daga addinan Kharmadaniyya(**) da Mazdakiyya( )(*)da Zindikiyya( )(**) da Dahriyya( )(***) duk madaurinsu guda ne, Allah Ya la'ancesu. Dukkansu sun tafi a kan kore rububiyyar Allah Mahalicci (Allah Ya daukaka ga barin hakan), sun kuma tabbatar da ita wa jikkuna ababen halitta da nufin wai jikkunan su ne bigiren da Allah Yake zama, sannan kuma shi Allah Ta'ala wani haske ne da ruhi mai ciratuwa daga wannan jikin zuwa wani. Face dai su sun sassaba ne kurum wajen shugabannin da suke bi, sashinsu yana barranta daga sashi yana kuma la'antarsa( ).
Al-Nawbakhti ya kara da nakalto fandararrun kungiyoyin da suka riga suka mace, masu fakewa da jingina kansu ga Ahlulbaiti (a.s) kamar haka:
"Wata kungiya ta ce wai Muhammad bn Hanafiyya dan Imam Ali (a.s.) 'shi ne Mahdi, Imam Ali ya kira shi da Mahdi, bai mutu ba kuma ba zai mutu ba, wannan ba ya halatta, sai dai kawai shi ya faku ne, ba a kuma san inda yake ba. Zai dawo ya mallaki kasa, babu wani Imami bayan fakuwarsa har zuwa dawowarsa wajen sahabbansa, su ne kuma sahabban Ibn Karb( )". Sannan ya ce:
"Hamza bn Ammara al-Barbari cikinsu yake kuma shi mutumin Madina ne, sai ya rabu da su ya yi ikirarin cewa shi Annabi ne, shi kuma Muhammad bn Hanafiyya shi ne Allah - wal iyazu billahi -. Ya kuma ce shi ne Imam sannan kuma wasu abubuwa guda bakwai za su sauko masa daga sama, da su ne zai cinye dukkan kasa ya mallake ta. Ya kuma sami mutane daga Madina da Kufa da suka bi shi kan hakan. Imam Bakir (a.s.) ya tsine masa ya barranta daga gare shi, ya karyata shi, a sanadiyyar hakan ne kuma ya sa 'yan Shi'a suka barranta daga gare shi( )".
Haka nan ma Imam Sadik (a.s.) ya la'anci Sa'id al-Nahdi wanda wadannan fandararrun kungiyoyin nan suke bi. Imam din ya kira shi shaidan, wanda ya yi wa Imam karya( )".
Ga wasu ruwayoyin malaman Shi'a kan matsayin da Imam Sadik (a.s.) ya dauka dangane da wadannan 'yan Gullatu da kuma fandararrun ra'ayoyinsu. Misalin hakan shi ne abin da Imam din ya ce kan Abul Jarud da mabiyansa kamar yadda Ibnu Nadim ya nakalto cikin Alfihrist.
"Imam Sadik (a.s.) ya la'ance shi ya ce: 'shi makahon zuciya ne da idanu( )'.
Kamar yadda kuma Imam din ya la'anci Abu Mansur al-Ajli, daya daga cikin 'yan Gullatu, an ruwaito cewa:
'Al-Kishshi ya kawo cikin Rijal dinsa shafi na 300 cewa Imam Sadik ya la'ance shi sau uku. Sannan kuma Yusuf bn Umar al-Thakafi, gwamnan Iraki, ya tsire shi a zamanin Hisham bn Abdul Malik( )'.
Hakika Imam Sadik (a.s.) ya bayyana matsaya kan wadannan 'yan gullatu, daga nan ya ambaci wasu daga cikinsu, su ne: Mughira bn Sa'id, Bazi, Sirri, Abul Khaddab Muhammad bn Abi Zainab al-Ajda', Mu'ammar, Bashshar Sha'iri, Hamza Barbari da Sa'id Nahadi, sai ya ce: "Allah Ya la'ance su, mu dai ba mu rabuwa da makaryata msu yi mana karya ko kuma wani mai gurgun tunani. Allah Ya isar mana ga dukkan makaryaci, Ya kuma dandana musu zafin karfe( )".
A wani hadisin kuma Imam Sadik (a.s.) ya barranta daga 'yan Gullatu, inda yake cewa:
"Ya ku jama'ar Shi'a - shi'ar Alu Muhammadu- ku kasance matsakaita, wadanda suka wuce gona da iri (masu guluwi) su dawo gare ku, wadanda kuwa suka yi nawa su risko ku". Sai wani mai suna Sa'id ya ce: 'Allah Ya sanya ni fansarka! Wane ne mai guluwi? Sai Imam ya ce masa:"Wasu mutane ne masu fadi game da mu, abin da mu ba mu fada ba, wadannan ba su daga gare mu, mu ma ba mu daga gare su". Sai mutumin ya ce: 'To wane ne mai nawa? Sai ya amsa masa da cewa: "Shi ne mai bidar (gaskiya) yana nufin alheri, alherin zai same shi kuma za a sakanta masa da shi( )".
Daya daga cikin sahabban Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito cewa yayin da Imam din ya sami labarin cewa Abul Khaddab na wuce gona da iri sai idanunsa suka cika da hawaye yana cewa:
"Ya Ubangiji, na barranta ya zuwa gareKa, daga abin da Al-Ajda yake ikirari a kaina, gashina da fatar jikina sun ji tsoronKa. Ni bawa ne a gare Ka dan bawanKa, makaskanci mai tawali'u".Daga nan sai ya sunku'i da kai na dan lokaci kamar yana ganawa da wani abu, sai ya daga kansa yana cewa:"Haka yake, haka yake! Bawa mai tsoro, makaskanci gaba ga Ubangijinsa, kankani, mai tsananin tsoro. Wallahi ina da Ubangijin da nake bautarSa, bana yi masa tarayya da kome. Me ya same shi (Abul Khaddab)? Allah ya kunyata shi, Ya zuba masa tsoro. Kada kuma Ya ba shi aminta daga firgici a ranar kiyama…..ba haka amsawar Annabawa take ba, ko ta mursalai, ba kuma amsawa ta ba. Amsawa ta kam ita ce fadar cewa: Ya Allah na amsa maKa, na amsa maKa Ya Allah ba Ka da abokin tarayya( )".
Sadir ya ce:
'Na ce da Abu Abdullah (a.s.) cewa wasu mutane suna ikirarin cewa ku alloli ne, suna kuma kafa hujja da fadar Allah (S.W.T.) cewa:"Kuma Shi ne Wanda ke abin bautawa a sama, kuma bautawa a kasa"", (Surar Zukhruf aya ta 84),sai ya ce:"Ya kai Sadir! (Ka sani) jina da ganina da fatata da namana da gashina duk sun barranta daga wadannan mutane, Allah ma Ya barranta da ga gare su. Ba kan addinina wadannan suke ba, ba kuma kan na iyayena ba. Na rantse da Allah ba zai tara ni da su ba ranar lahira, kuma ba su zo a wannan rana ba face Allah Na fushi da su( )".
Kamar yadda suka yi wa Imam Bakir da Sadik (a.s.) karairayi kuma suka barranta daga gare su, haka nan ma suka yi wa Imam Musa Kazim (a.s.) bayan shahadarsa. Suka ce bai mutu ba, sai dai kawai an daukake shi ne kamar yadda aka daukaki Annabi Isa (a.s.) kuma nan gaba zai dawo. Imam Ridha (a.s.) dan Imam Kazim (a.s.) sai ya barranta daga gare su, ya kuma la'ance su.
Kamar yadda Imam Sadik (a.s.) ya ce ba za a rabu da masu yi wa Ahlulbaiti (a.s) karya ba, domin su rikita tafarkinsu, domin kaidi ga Musulunci, haka nan Ahlulbaiti (a.s) suka bayyana matsayinsu dangane da wadannan masu niyyar ruguza Musulunci.
Yana daga ni'imomin Allah ga Musulunci da musulmi cewa wadannan kungiyoyi sun gushe, babu abin da ya rage sai ambatonsu cikin littattafan tarihi. Sai dai abin ban mamaki da takaici shi ne wasu masu mugun nufi suna danganta tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da tatsuniyo-yi da barnace-barnace domin bakanta tafarkin Ahlulbaiti (a.s). Duk wani mai nufin alheri ba zai yarda da wannan ba bayan kuwa su Ahlulbaiti (a.s) da kansu sun barranta daga duk abin da ya saba wa tafarki madaidaici, kamar yadda muka ambata a baya. Babu shakka babu abin da masu sukar mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) suke yi face barazana ga hadin kan musulmi.
A daya gefen kuma, duk masu bincike suna iya ganin abubuwan da ake danganta su da sauran mazhabobin musulmi na akida, kamar su jabru da cewa Allah jiki ne kuma Yana zama a bisa kujera da cewa fadin kujerarSa taki bakwai ne, da cewa Allah zai shigar da kafarSa cikin wuta a ranar lahira sai Ya bice zafinta, da cewa Shi Yana saukowa nan duniya bisa wani farin jaki da dai sauransu.
Hakika a sarari yake cewa duk wadannan zantuttuka, kamar tatsuniyoyin Gulatu, suna warware akidar tauhidi, addinin Musulunci kuwa yana barranta daga gare su.