Muassasar alhasanain (a.s)

Binciken Addini

2 Ra'ayoyi 02.0 / 5

MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com

Da sunan Allah madaukaki
Bayani kan Addini wani abu ne da aka samu sabani mai tsanani tsakanin ma'abota tunani a kansa, sai dai mu zamu takaita game da wasu bayanai masu sauki da sukan iya ba mu ma'anar da ta fi kowacce cika.
Addini a luga: biyayya: Allah madaukai yana cewa: "Biyayya gaba daya tasa ce" . Ma'ana: biyayya da da'a dawwamammiya tasa ce". Haka nan yake cewa: "Ba sa biyayya da biyayya ta gaskiya" . Kuma kalmar addini ta zo da ma'anar sakamako kamar fadinsa madaukaki: "Mamallakin ranar sakamako" . Don haka kalmar addini a luga tana nufin sakamako ko biyayya .
Addini a isdilahi: shi ne imani da mahaliccin halitta, da mutum, da kuma koyarwa, da ayyukan da suke da tushe da asasi daga karkashin wannan imanin. Saboda haka ne ma ake kiran wadanda ba su yi imani da mahalicci ba da marasa addini .
Wasu suna iya cewa menene amfanin addini? Me zamu samu daga gareshi? Kai wasu ma suna da'awar cewa akwai cutuwa a addini. Sai mu ce: Addini shi doka ce ta Allah da take tsara rayuwar dai-daikun mutane da jama'a gaba daya, domin kai wa ga kamala da daukaka a dukkan fagagen rayuwa masu muhimmanci da suka shafi rayuwar mutum wanda ya hada da;
1- Gyara Masa Tunani Da Akida Da Tsarkake Shi Daga Camfi Da Surkulle:
Addini yana fassara mana hakikanin yadda samuwa take da kuma cewa akwai mai samarwa, masani, mai iko, da ya halicci dukkan halitta da kuma asalinta, da iyakance asalin da dokokinta. Kamar yadda yake fassara ma'anar rayuwar mutum da cewa ba haka nan kawai ta ke ba, ba a halicci mutum don wasa ba, sai domin wani hadafi babba da zai kai zuwa gareshi ta hanyar biyayya ga koyarwar da annabawa da masu shiryarwa suka zo da ita daga Allah.
2- Karfafa Asasin Kyawawan Dabi'u
Akida ta addini ita ce madogara mai karfi ta asasin kyawawan dabi'u, domin sanya dokoki da daure mutum da su yana sanya masa wahala da kuma bukatuwa zuwa ga juriya da mutum zai yi, kuma jure su ba ya yiwuwa sai da imani da Allah da zai saukaka su, da kuma kwadaitar da mutum zuwa ga sadaukar wa ta hanyar gaskiya da adalci da taimakon raunana.
3- Kyautata Alakar Zamantakewa:
Akidar mutum ta addini tana karfafa asasin zamantakewa domin zata sanya mutum ya zama mai addini da kuma lizimtar takalifi da bai halatta ya saba masa ba kamar sadar da zumunci da girmama iyali da sauransu.
4- Jefar Da Bambance-bambance:
Addini yana ganin mutane dukkansu halittu ne na ubangiji guda daya, kuma dukkansu a wajan Allah daya ne ba bambanci tsakanin balarabe da ajami da fari da baki .
Wadannan al'amura guda hudu suna nuna mana muhimmanci mai girma a fili da addini yake da shi, kuma bayan haka ba zai yiwu ga wani ba ya bar addini domin gudun kada wani nauyi ya hau kansa ko son hutu da holewa, ko kuma domin addini yana sanya wa mutum dokoki da zasu hana shi aiwatar da abin da ransa ta ga dama.
Kur'ani mai girma yana siffanta irin wadannan mutane da su ne mafi bata daga dabbobi: "Mun sanya wa jahannama dayawa daga aljnu da mutane da suke da zuciya da ba sa tunani da ita, da kuma idanu da ba sa gani da su, da kunnuwa da ba sa ji da su, wadannan kamar dabbobi suke, kai sun fi dabbobi bacewa, kuma wadannan su ne gafalallu" .
Ina karawa da cewa; duba ga irin wadannan fa'idoji da addini yake da shi imani da mahalicci da aiki da hakan koda an kaddara da cewar babu shi ya fi zama abin hankalta a kan rashin yarda da hakan, domin idan an koma masa; idan an kaddara babu shi to da mu da wadanda ba su yi imani da shi ba mun zama daya, amma idan akwai shi fa! kenan mun tsira su kuma sun halaka.
Musulunci yana da ma'ana biyu; ma'ana mai fadi da ma'ana kebantacciya kamar haka;
Ma'ana mafi fadi ; Shi ne karkata da mika wuya zuwa ga Allah da abin da ya saukar na shir'a da hukunce-hukunce. Allah madaukaki ya ce: "Kawai addini a wajan Allah shi ne muslunci" .
Musulmi shi ne wanda ya mika wuya ga abin da aka saukar na shari'a daga Allah, saboda haka akwai musulunci tun lokacin annabi Adam (a.s) da Nuhu da Ibrahim da Musa da Isa (a.s) da kuma cikon manzanni da annabawa Muhammad (s.a.w).
Ma'ana kebantacciya: Shi ne addinin da manzo Muhammad Dan Abdullahi (s.a.w) ya zo da shi, muslmi shi ne wanda ya yi furuci da harshe yana mai cewa; "Na shaida babu abin bautawa sai Allah, kuma na shaida Muhammad manzon Allah ne". Ana kiran wannan da kalmar shahada da take kunshe da shaidawa biyu.
Don haka sakamakon wannan furuci yana tilasta rashin musun duk wani abu laruri na akidar musulunci da huknce-hukuncensa, da kuma rashin musun annabtar annabawa da suka rigaya suka gabata da aka ambace su a kur'ani mai girma, wato kada ya yi musum wani abu da musulmi suka hadu a kansa gaba daya kamar wajabcin salla da azumi da hajji, da haramcin shan giya da cin riba, da sauransu.
Musulunci tsarkakakke shi ne cikon addinai, domin shi ne mafi kamala da cika wanda ya zo daga Allah da ake bukatar mutum ya mika wuya zuwa gareshi .
Saboda haka ne ma ba a karbar wani addini sai shi: "Duk wanda ya nemi wani addini ba musulunci ba, ba za a karba daga gareshi ba, kuma shi a lahira yana cikin masu hasara" .
Usuluddin Da Furu'arsa
Addinin musulunci addini ne na duniya gaba daya da ya game komai, kuma yana dogara bisa rukuni biyu ne na asasi:
1- Usuluddini: su ne asasi tabbatattu da ba sa sabawa komai sabawar al'ummu kamar Tauhidi da Adalci da Annabci da Makoma. Wadannan su ne shika-shikan addini.
2- Furu'uddini: su ne janibin shari'a, wanda yake kunshe da koyarwa, kuma da kyawawan dabi'u da suka zo domin maslahar mutum da al'umma gaba daya da kuma rabautar duniya da lahira, bai kebanta da wasu jama'a ba su kadai. Wadannan su ne rassan al'amuran addini .
Shika-shikan Addini
Kamar yadda aka sani cewa addini yana da jiga-jigai da kuma rassan al'amuransa. Asasi ko ginshiki yana nufin doka da ka'idar da addini ya doru a kanta, ana cewa da tauhidi da adalci, da annabci, da imamanci, da makoma ranar lahira, wato: shika-shikan addini.
Zai iya yiwuwa a wajenmu bahasin imamanci ya shiga karkashin annabci, kamar yadda adalci yake shiga karkashin bahasin tauhidi, sai su koma guda uku: Tauhidi Da Annabci Da Makoma.
Yana wajaba a kan kowane baligi ya san shika-shikan addini da bayanansu.
Musulmi da Musulunci
A bisa abin da yake saukakke daga Allah madaukaki shi ne cewa "Addini a wajan Allah kawai shi ne musulunci", wanda yake shi ne Shari'ar Ubangiji ta gaskiya wacce take Shari'ar karshe, mafi kamala da dacewa ga rabautar dan Adam, wacce ta fi kunsar maslaharsu ta duniya da lahira, mai dacewa da wanzuwa, wacce ba ta canjawa ba ta sakewa, mai kunshe da dukkan abin da dan Adam yake bukata daga tsarin rayuwar mutum da jama'a.
Kuma tun da ita wannan shari'ar ita ce ta karshe to babu makawa wata rana ta zo da Addinin musulunci zai yi karfi har ya game rayuwa da adalcinsa da dokokinsa. Wannan kuwa alkawari ne da Allah ya yi shi a cikin littattafansa.
Sannan tun da wannan addini na musulunci shi ne mafi kamala da dacewa da rayuwar dan Adam, lallai da an dabbaka shi kamar yadda ya dace, da aminci da rabauta sun mamaye 'yan Adam, da sun kai kololuwar abin da suke mafarkinsa na yalwa, da walwala, da izza, da annashuwa, da kyawawan dabi'u, kuma da zalunci ya kau daga duniya, soyayya da 'yan'uwantaka sun yadu a tsakanin mutane, talauci da fatara sun kau gaba daya.
Idan a yau muna ganin halin ban kunya da kaskanci da ya samu wadanda suke kiran kansu musulmi, to domin ba a aiwatar da addinin musulunci ba ne a bisa hakika kamar yadda yake a nassinsa da ruhinsa suke tun daga karni na farko.
Sai kangare wa koyarwar musulunci, da tozarta dokokinsa, da yaduwar zalunci, da ketare haddi daga bangaren Sarakunansu da talakawansu, da kebantattu da kuma baki dayansu suka kawo kaskanci ga musulmi da lahanta yunkurin ci gabansu, da raunana karfinsu, da ruguza tsarkin ruhinsu. Allah madaukaki yana cewa:
"Wannan kuwa domin Allah bai kasance yana canja wata ni'ima da ya ni'imtar da ita ga wasu mutane ba face sai sun canja abin da yake ga kawukansu". Surar Anfal 53. Da fadinsa "Kuma wannan ita ce sunnar Allah a halittunsa cewa tabbas masu laifi ba sa cin rabauta". Surar Yunus: 17. Da fadinsa madaukaki: "Kuma Ubangijinka bai kasance mai halakar da alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara". Surar Hudu: 117.
Da fadinsa: "Kuma haka nan kamun Ubangijinka yake idan ya kama alkarya alhali tana azzaluma lalle kamunsa mai radadi ne mai tsanani". Surar Hudu: 102.
Ta yaya ake sauraron Addinin musulunci ya tayar da al'umma daga dogon baccinta, alhali kuwa shi a wajanta kamar tawada ce a kan takarda da ba a aiki da mafi karanci daga koyarwarsa. Imani, da amana, da gaskiya, da tsarkin niyya, da kyautata mu'amala, da sadaukarwa, da musulmi ya so wa dan'uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, da makamantansu, tun farkon assasa Addinin musulunci musulmi sun yi bankwana da su tun da can har zuwa yau. Kuma duk sanda zamani ya ja gaba sai mu same su suna kara rarraba jama'a-jama'a da kungiya-kungiya, suna kifuwa da goggoriyo a kan duniya, suna ta fagamniya a cikin duhu, sashensu na kafirta sashe da wasu ra'ayoyi gagara fahimta, ko kuma a kan wasu al'amura da babu ruwansu a ciki, suka shagaltu ga barin asasin Addini da maslaharsu da maslahar al'ummarsu, da fadawa cikin jayayya game da halittar Kur'ani ko rashin kasancewarsa abin halitta, da batun narkon azaba da Raja'a, da kuma cewa aljanna da wuta halittattu ne a halin yanzu ko kuma za a halicce su ne nan gaba.
Sai ga shi a yau yammacin duniya wayayye, fadakakke, ya samu damar mulkin mallaka a kan wani yanki da yake na musulmi, su kuwa sun yi zamansu cikin gafala da rafkanwa yadda har ya iya jefa su cikin mummunan halin da Allah ne kadai ya san iyakarsa da lokacin karewarsa. Allah madaukaki yana cewa: "Kuma Ubangijinka bai kasance yana halakar da alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara". Surar Hudu: 117.
Don haka musulmi ba su da wata mafita sai koma wa kawukansu su yi wa kansu hisabi a kan sakacin da suka yi, su yi yunkurin gyara kawukansu da zuriyoyi masu zuwa, ta hanyar ba su koyarwar Addininsu mai inganci domin su gusar da zalunci da ja'irci tsakaninsu.
Da haka ne kawai zasu tsira daga wannan halaka mai girma, kuma babu makawa bayan nan su cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci kamar yadda Allah (s.w.t) ya yi musu alkawari. Kuma kamar yadda ake saurare daga addininsu da yake shi ne cikon addinai da ba a kaunar wani gyara na duniya ko lahira sai da shi .
Babu makawa wani Imami ya zo ya kakkabe wa musulunci abin da aka lillika masa na daga bidi'o'i da bata kuma ya tserar da 'yan Adam, ya kubutar da su daga abin da suka kai matuka gareshi na daga fasadi, da zalunci mai dorewa, da kiyayya mai ci gaba, da izgili da halaye nagari da 'yan'adamtaka. Allah ya gaggauta bayyanarsa ya saukake mafitarsa.
Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Tuesday, April 13, 2010

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)