Muassasar alhasanain (a.s)

Ayar Tsarki

3 Ra'ayoyi 03.3 / 5

AYAR TSARKI

 
 
Mu'assasar Al-Balagh
Tsarawar: Hafiz Muhammad Sa'id
 
Kur’ani Mai Daraja:
"Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .
 
Ayar Tsarkakewa
(إنَّما يُريدُ الله لِيُذْهِبَ عنْكُمُ الرِّجْسَ أهْلَ البَيْتِ ويُطهِّرَكُمْ تَطْهيراً )
"...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa". (Surar Ahzabi, 33:33)
Hakika tafsirai da ruwayoyi sun hadu a kan cewa abin da ake nufi da Ahlulbaiti shi ne mutanen gidan Annabi (s.a.w.a) wadanda kuma su ne, Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.). Bayani ya zo cikin littafin Durrul Mansur na Imam As-Suyudi cewa: (Al-Dabarani ya fitar da hadisi daga Ummu Salma cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce da Nana Fadimatu cewa: "Taho min da mijinki da 'ya'yansa biyu", sai ta taho da su sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya lullube su da wani mayafi, sa'an nan ya sanya hannunsa bisansu ya ce: "Ya Allah! Wadannan su ne Ahlulbaitin Muhammadu (a wani lafazin zuriyar Muhammadu) to Ka sanya tsirarKa da albarkarKa wa zuriyar Muhammadu kamar yadda Ka sanya wa zuriyar Ibrahima, lalle Kai ne Abin godiya, Mai girma".
Sai Ummu Salma ta ce: "Sai na daga mayafin domin in shiga in kasance tare da su, sai Annabi (s.a.w.a) ya janye shi daga hannuna ya ce: "Lallai ke kina tare da wani alheri "( ).
An ruwaito hadisi daga Ummu Salma, matar Annabi (s.a.w.a) cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance a dakinta bisa wurin kwanciyarsa yana rufe da wani mayafi sakar Khaibara, sai Fadima ta zo da wata tukunya da abinci a cikinta. Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ki kira mijinki da 'ya'yansa Hasan da Husaini". Sai ta kira su. Yayin da suke cin abincin sai aya ta sauko wa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkake-ku tsarkakewa".
Sai Annabi (s.a.w.a) ya kama gefen ragowar sashen mayafinsa ya rufe su da shi, sannan ya fitar da hannunsa daga mayafin ya nuna sama ya ce: "Ya Allah! Wadannan su ne mutanen gidana, make-bantana, to Ka tafiyar da kazamta daga gare su kuma Ka tsarkake su, tsarkakewa".
Ya fadi hakan har sau uku. Ummu Salma ta ce: "sai na shigar da kaina cikin mayafin na ce: "Ina tare da ku Ya Manzon Allah? Sai ya ce: "ke kina tare da wani alheri", ya fadi hakan har sau biyu ( ).
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ci gaba da bayyana wa al'ummarsa ma'anar wannan aya mai girma, yana tsarkake fahimtarta ga wannan aya domin al'umma ta haskaka da ita ta kuma rayu a kan shiryuwarta. An ruwaito shi yana cewa: "Wannan aya ta sauka ne a kan mutane biyar: Ni kaina, Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini…."…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa( )".
Kamar yadda kuma aka ruwaito daga Ummul Muminina A'isha, tafsirin ayar da bayanin mutanen da ake nufi a ciki, kamar haka: (Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fito wata safiya yana sanye da wani mayafi mai zane, wanda aka yi da bakin gashi, sai Hasan dan Ali ya zo, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya shigar da shi (cikin mayafin), sannan sai Husaini ya zo, ya shigar da shi, sannan Ali ya zo ya shigar da shi, sa'an nan sai ya ce: "…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa( )".
A wata ruwayar kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana wucewa ta kofar Fadima (a.s.) yayin da ya fito sallar asuba yana cewa: "Salla! Ya mutanen babban gida (Ahlulbaiti), salla! "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa "( ).
Hakan nan Alkur'ani yake magana a kan Ahlulbaiti (a.s) yana iyakance mutanen da suke ciki, tsarkaka manisanta daga dukkan dauda da sabo da zunubi da kuma son zuciya. Saboda haka halayen su abin koyi ne haka nan su kansu. Alkur'ani bai sanar mana da su irin wannan sanarwa ba, sai domin ya jaddada matsayi da mukaminsu ga al'umma, ya kuma ja hankulanmu zuwa ga koyi da su da komawa gare su domin fahimtar shari'a da karbar hukumce-hukumcenta daga wurinsu. Ta wannan hanyar, Alkur'ani ya ayyana mana mizani na aikace (wato ayyukan Ahlulbaiti) da ma'aunin da za mu koma gare shi yayin da ra'ayoyi suka sassaba, aka kuma sami bambancin fahimta da I'itikadi (wato abin da mutum ya yarda da shi).
Wannan kuwa a sarari yake idan muka duba yadda Alkur'ani ya jaddada cikin ayoyi da yawa ya kuma bijiro da Ahlulbaiti (a.s) a matsayin ja-gorori ga al'umman musulmi bayan Manzon Allah (s.a.w.a.).
Dogewar da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi, wata da watanni bisa tsayuwa a bakin kofar Aliyu da Fadima (a.s.) yana kiransu da asuba zuwa salla, yana kiransu da Ahlulbaiti ba kome ba ne face sanar da al'umma mutanen da ake nufi da Ahlulbaiti, kana kuma yana fassara wa musulmi ayar tsarkakewa, yana sanar da su matsayin Ahlulbaiti (a.s) tare da jan hankulansu zuwa gare su da kuma wajabta musu kaunarsu da yi musu biyayya da jibinta al'amari gare su.
Dabarani ya ruwaito daga Abu Hamra' cewa: "Na ga Manzon Allah (s.a.w.a.) yana zuwa kofar Aliyu da Fadima tsawon wata shida yana cewa: "Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa( )".
Fakhru al-Razi ya ambata a cikin tafsirinsa, Tafsir al Kabir, cewa bayan saukar ayar: "Kuma ka umurci iyalanka da salla, kuma ka yi hakuri a kanta", (Surar Daha, 20: 132), Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kan je (kofar) Aliyu da Fadima kowace safiya yana mai cewa: (lokacin) salla (ya yi), ya aikata hakan har na tsawon watanni.
Sannan kuma ya kawo hadisin Hammad bn Salma, daga Aliyu bn Zaid daga Anas cewa: "Annabi (s.a.w.a) ya kasance yana wucewa ta dakin Fadima koyaushe ya fito zuwa ga salla har na tsawon wata shida, yana mai cewa: "Salla! Ahlulbaiti! "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa( )".
A cikin wannan akwai bayani da kuma nuni zuwa ga muhimmancin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya riki Ahlulbaiti (a.s) da shi, da kuma karfafawarsa wa musulmi cewa su (Aliyu, Fadima da 'ya'yansu) su ne mutanen gidansa (Ahlulbaiti), wadanda Allah Ya tafiyar da dukkan dauda ga barinsu, Ya kuma tsarkake su tsarkakewa. Wannan muhimmancin an nuna shi ne bayan Allah Ya yi magana da ManzonSa cewa: "...kuma ka umurci iyalanka da salla, kuma ka yi hakuri a kanta".
Sannan a sarari yake cewa daga abin da ayar: "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa", take nuni da shi da kuma amfani da lafazin maza ba lafazin mata ba da aka yi, wato (عنكم) da kuma (يطهِّركم), akwai nuni zuwa ga wadanda ake nufi, su ne wadannan mutane biyar din. Bayani ya zo a cikin Tafsirai cewa da Allah Yana nufin matan Annabi (s.a.w.) ne da Yayi amfani da kalmar (عنكنّ) da ta (يطهِّركنّ) da magana irin wacce ake yi wa mata.
A baya mun riga da mun ga Hadisin Mayafi lokacin da aka saukar da wannan aya ta tsarkakewa yayin da Ummu Salama taso shiga cikin wannan mayafi amma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce mata ke dai kina a matsayinka, kuma kina a kan alheri.
Hakan yana nuna mana rashin shigar matayen Annabi (s.a.w.a) cikin wannan aya ta tsarkakewa, kana kuma babu daya daga cikinsu da ta yi ikirarin saukar wannan aya a kansu, duk kuwa da cewa ayar ta falaloli da kuma matsayi mai girma ce.
Wannan ayar ta fitar da wata hanya wacce abin da take nuni da shi da abin da ta tattara suna da yalwar gaske. Tana jan hankulanmu zuwa ga batutuwa na asasi a rayuwar Musulunci domin kada mu sami rikitarwar fahimta balle ma manufofin Littafin Allah na gaskiya su tawaya. Allah Ya yi nufin gina al'umma bisa ginshikin tsarki da nisantar dauda da abin kunya sai Ya sanya Ahlulbaiti (a.s) a matsayin wani tushe abin dogara da kuma haske mai haskakawa. Lalle babu wani mutum da Alkur'ani mai girma ya siffanta shi da wannan siffa daga cikin musulmi, babu kuma wanda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya siffanta shi da wannan siffar (siffar tsarki maras iyaka) face Ahlulbaiti (a.s).
 

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)