|
Mu'assasar Al-Balagh
Kur’ani Mai Daraja:
"Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .
Ayoyin Wilaya
Hakika ayoyin Alkur'ani masu yawa sun sauka da batun Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s.) wanda aka yi tarbiyyarsa cikin gidan Manzon Allah (s.a.w.a.) tun yana karami( ). Ya tashi karkashin kiyayewarsa (s.a.w.a) don haka ya kwaikwayi halayensa. Ya yi imani da shi, gaskanta shi da kuma binsa tun yana dan shekara goma. Sannan kuma Imam Ali (a.s.) ya kasance mai daukar tutar Manzon Allah (s.a.w.a.) kuma shi ne jarumin sojansa wanda ya kere kowa a dukkan yake-yakensa, da suka hada da Badar, Uhud, Hunain, Ahzab, Khaibar, Zatu Silasil da dai sauransu. A saboda irin jaruntar da ya nuna a irin wadannan yakuna, ya sa Manzon Allah (s.a.w.a.) da kansa ya jinjina masa da bayyanar da wasu kalmomi dawwamammu da suka kasance ado ga littatta-fan tarihi sannan kuma abin koyi na koli cikin sadaukar-wa da kuma jihadi.
Idan muka yi bincike kan asbabun Nuzul (dalilan saukar ayoyi), za mu samu cewa abin da ya sauka dangane da Amirul Muminina, Aliyu bn Abi Talib (a.s.) - ban da abin da muka ambata na Ahlulbaiti (a.s) - suna bayani ne:
1. Kan jaruntar Aliyu (a.s.) gwarzontaka da kuma sadaukarwarsa a kan tafarkin Allah.
2. Kan hakurinsa bisa cutarwa da izgili.
3. Kan gudun duniya, takawa ilimi da kuma kaunarsa ga muminai.
Bari mu ambato wasu misalai kamar haka:
Ayar Wilaya
إنَّما وليُّكُمُ اللهُ ورَسولُهُ والَّذينَ آمَنوا الَّذينَ يُقيمونَ الصَّلاةَ ويُؤتُونَ الزَّكاةَ وهُمْ راكِعونَ # ومَنْ يَتَوَلَّ اللهَ ورَسُولَهُ والَّذينَ آمَنُوا فإنَّ حِزْبَ اللهِ هُمُ الغالِبُونَ
"Abin sani kawai, majibincinku Allah ne da ManzonSa da wadanda suka yi imani, wadanda suke tsayar da salla, kuma suna bayar da zakka alhali suna masu ruku'i. Kuma wanda ya jibinci Allah da ManzonSa da wadanda suka yi imani, to, kungiyar Allah su ne masu rinjaye". (Surar Ma'ida, 5: 55-56)
Zamakhshari cikin tafsirinsa ya bayyana cewa: "Wannan aya ta sauka ne dangane da Aliyu (Allah Ya karrama fuskarsa) lokacin da wani ya roke shi alhaliyana cikin ruku'in salla, sai ya sake masa zobensa wanda yake loko-loko a dan kuriyarsa, wanda cire shi baya bukatar aiki mai yawa da ka iya bata salla. Idan ka ce ta ya ya za a ce da Ali ake alhali lafazin na jam'i ne? sai in ce maka: An zo da shi akan lafazin jam'i ne ko da yake dalilin saukar ayar a kan mutum guda ne domin a kwadaitar da mutane wajen yin tamkar aikinsa, sai su sami tamkar ladansa. Domin kuma tambihi cewa halayen muminai wajibi ne su kasance da wannan koluwa wajen kwadayin aikin alheri da bibiyar lamarin mabukata ta yadda idan wani abin da ba ya son jinkiri ya lizimce su suna cikin salla, ba sa jinkirta shi sai an idar da sallar( )".
Al-Wahidi ya ambata cewa al-Kalbi ya fadi cikin dalilin saukar wannan aya, cewa: "Lalle karshen wannan aya a kan Aliyu dan Abi Talib (r.a.) take domin ya ba da zobensa ga wani mai bara alhali yana cikin ruku'un salla( )".
Littattafan tafsiri da hadisi masu yawa sun ambato cewa wannan aya mai albarka ta sauka ne dangane da Imam Ali (a.s.). Akwai cikakken bayani kan hakan cikin wadannan littattafa ga mai karin bayani( ).
Ayar Tabligh (Isar da Sako)
يا أيُّهَا الرَّسُولُ بَلِّغْ مَآ أُنْزِلَ إلَيْكَ مِنْ رَبِّكَ وَإنْ لمْ تَفْعَلْ فَمَا بَلَّغْتَ رِسَالَتَهُ واللهُ بَعْصِمُكَ مِنَ النَّاسِ.. "
Ya kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar maka daga Ubagijinka. Kuma idan baka aikata ba, to, ba ka iyar da sakonSa ba kenan, kuma Allah Zai tsare ka daga mutane( )" (Surar Ma'ida: 5:67.
An saukar da wannan aya ne a wani kwari da ake ce ma Ghadir Khum. Ga bayanin akan abin da ya faru:
An ruwaito cewa, yayin da Manzon Allah (s.a.w.a.) yake dawowa daga Hajjin Ban Kwana( ) sai wannan aya (da muke magana a kanta) ta sauka a gare shi a rana ta goma sha takwas ga watan Zul Hajji( ).
To sai ya yada zango a Ghadir Khum daga Juhfa( ), inda a nan ne kuma hanyoyi suka rarrabu zuwa birnin Madina, Masar da kuma Sham. Sai ya tsaya a nan har wadanda suke bayansa suka iso, wadanda suke gaba kuwa suka komo inda yake( ). Akwai wasu itatuwan kaya a rarrabe, sai aka hana Sahabbai sauka a karkashinsu. Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sa aka sare wadannan itatuwa na kaya( ), sai ya sa aka yi kiran salla( ), ya sallaci azahar tare da jama'a cikin garjin rana( ). Daga nan sai ya mike ya gudanar da huduba bayan ya yi godiya ga Allah da kuma tsarkake Shi da kuma yin wa'azi ga al'umma, sai ya ce: "Hakika an kusa a kira ni kuma in amsa, ni kuma abin tambaya ne ku ma abin tambaya ne, to me za ku ce?
Sai suka amsa: "Za mu ba da shaidar cewa kai ka isar da sako, ka yi nasiha, to Allah Ya saka maka da alheri".
Sai Annabi (s.a.w.a) ya ce: "Shin ba kwa shaidar cewa babu abin bauta da gaskiya face Allah ba, kuma Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, da cewa aljanna gaskiya ce, wuta ma gaskiya ce"?
Sai suka ce: "Haka ne, mun shaida hakan".
Sai ya ce: "Ya Allah Ka shaida", sai ya ci gaba da cewa: "Shin ba kwa ji".
Sai suka ce: "Na'am" (watau suna ji).
Sai ya ce: "Ya ku mutane! Ni mai gabata ne ku kuma masu iske ni ne a bakin tabki, fadinsa tamkar tafiyar tsakanin garin Basra da San'a'( ) ne, akwai kofuna na azurfa, yawansu kamr adadin taurari, ni kuma mai tamabayarku ne batun abubuwa biyu masu nauyi (Sakalaini), to ku kula da yadda za ku kasance game da su a bayana".
Sai wani ya yi kira ya ce: "Mene ne wadannan nauyaya biyu, Ya Manzon Allah?
Sai ya ce masa: "Littafin Allah, gefe yana hannun Allah, gefe kuma yana hannunku, to ku yi riko da shi, ba za ku bata ba, ba za ku canjba ba, da kuma iyalina, mutanen gidana. Hakika Mai Tausayawa, Masani, Ya sanar da ni cewa su biyun ba za su rabu da juna ba har sai sun iske ni a bakin tafki. Na roka musu wannan wajen Ubagijina, saboda haka kada ku gabace su sai ku halaka, kada ku takaita (ga barinsu), sai ku halaka, kada ku sanar da su domin sun fi ku sani( ).
Sannan sai ya ce: "ashe ba ni ne nafi cancanta ga kowane mumini a kan kansa ba"?
Sai suka ce: "Haka ne, Ya Manzon Allah( )".
Daga nan sai ya kama hannun Aliyu bn Abi Talib (a.s.) ya daga sama har mutane suka ga farin hammatarsa( ), ya ce: Ya ku mutane! Allah Shi ne Majibincina, ni kuma ni ne majibincinku( ). To duk wanda na ke majibincinsa, wannan Aliyun majibincinsa ne. Ya Allah! Ka jibinci wanda ya jibince shi, Ka yi gaba da wanda ya yi gaba da shi( ), Ka taimaki wanda ya taimake shi, Ka wulakanta wanda ya wulakanta shi( ), Ka so mai son sa, Ka ki wanda ya ki shi( )".
Sannan sai ya ce: "Ya Allah Ka shaida( )".
Ba su (Manzon Allah da Aliyu) rabu ba har sai da Allah Ya saukar da wannan aya: (اليَومَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُم وأَتْمَمْتُ عَلَيْكُم نِعْمَتي وَرَضِيتُ لَكُمُ الإسْلاَمَ دِينًا )
"A yau Na kammala muku addininku, kuma na cika muku ni'imaTa a kanku, kuma Na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku". (Surar Ma'ida, 5:3)
Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Allahu Akbar! Bisa kammalar addini da cikar ni'ima da yardar Ubangiji da Manzancina da walittakan Aliyu( )".
Akwai ayoyi masu yawa, wadanda wannan karamin littafi ba zai iya tattaro su ba, da suke magana a kan matsayin Ahlulbaiti (a.s) da karamar su da girman mutanen ciki, wadanda wasu daga cikinsu sun kebanta ne ga Uban wannan itace mai tsarki, wato Imam Ali (a.s.). Mai karatu zai iya samun wadannan ayoyi cikin littattafan tafsiri, hadisi, tarihi da kuma masu bayani kan falalolin wadannan taurari da kuma wadanda suka yi magana kan Asbabun Nuzul na wadannan ayoyi. To amma bari mu kawo kadan daga cikin irin wadannan ayoyi, su ne kuwa: (1). Fadin Allah Madaukakin Sarki: )إنَّمَا أنْتَ مُنْذِرٌ ولِكُلِّ قَوْمٍ هَادٍ)
"Abin sani kawai kai mai gargadi ne kuma a cikin kowadanne mutane akwai mai shiryarwa". (Surar Ra'ad, 13:7)
Hadisi ya zo cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sanya hannunsa bisa kirjinsa, ya ce: "Ni mai gargadi ne, ko wadanne mutane kuma suna da mai shiryarwa", sai ya yi nuni da hannunsa zuwa Ali
(a.s.), sai ya ce kai ne mai shiriyarwan, Ya Aliyu, da kai masu shiryuwa za su shiryu a bayana( )".
(2). Fadar Allah Madaukakin Sarki: أفَمَنْ كَانَ مُؤمِنًا كَمَنْ كَانَ فَاسِقًا لا يَسْتَوُونَ
"Shin wanda ya zama mumini yana kamar wanda ya zama fasiki? Ba za su yi daidai ba". (Surar Sajada, 36: 18)
Wannan mumini kuwa shi ne Aliyu (a.s.), fasikin kuma shi ne Walid bn Ukba( ).
(3). Fadar Allah Madaukakin Sarki: أفَمَنْ كَانَ على بَبِّنَةٍ مِنْ رَبِّهِ ويَتْلوهُ شَاهدٌ مِنْهُ
"Shin wanda ya kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijinsa, kuma shaida na binsa daga gare shi..." (Surar Hudu, 11:17)
Manzon Allah (s.a.w.a.) shi ne yake bisa hujja bayyananna a al'amarinsa, shaidan kuwa shi ne Imam Ali (a.s.) ( ).
(4). Fadar Allah Madaukakin Sarki: (فإنَّ اللهَ هُوَ مَوْلاهُ وجِبْريلُ وصَالحُ المؤمِنين)
"...to lalle Allah Shi ne Mataimakinsa da Jibrilu da Salihin muminai..." (Surar Tahrim, 66: 4)
Salihin muminai a nan shi ne Aliyu bn Abi Dalib (a.s.) ( ).
(5). Fadar Allah Madaukakin Sarki: (وتَعِيَها أُذُنٌ واعِيَةٌ) "...kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye". (Surar Alhakkatu, 69: 12)
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya karanta wannan aya, sai ya juya ga Ali (a.s.), ya ce: "Na roki Allah da ya sanya shi shi ne kunnenka".
Sai Ali (a.s.) ya ce: "Babu wani abu da na ji daga Manzon Allah (s.a.w.a.) na manta shi( )".
Al-Wahidi ya nakalto cikin Asbabun Nuzul daga maruwaita daga Buraida, cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce wa Aliyu (a.s.) cewa: "Allah Ya umurce ni da in kusato da kai, kada kuma in nisantar da kai, cewa kuma in ilmantar da kai, don ka kiyaye, kuma Allah Ya yi alkawarin Zai sa ka kiyaye din. Sai aya ta sauka: "Kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye".
(6). FadinSa Madaukakin Sarki cewa: (إنَّ الَّذينَ آمَنوا وعَمِلوا الصَّالِحَاتِ سَيَجْعَلُ لمُمُ الرَّحْمنُ وُدًّا)
"Hakika wadanda suka ba da gaskiya suka kuma yi aiki na nagari, to (Allah) Mai rahama Zai sanya soyayya a tsakaninsu". (Surar Maryam, 19: 96)
Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce wa Aliyu (a.s.) cewa: "Ya Aliyu ka ce: "Ya Allah Ka sanya mini wani alkawari, kuma Ka sanya mini soyayya cikin zukatan muminai". Sai Allah Ya saukar da wannan ayar dangane da Aliyu (a.s.) ( ).
(7). Fadar Allah Ta'ala cewa: (إنَّ الَّذينَ آمَنوا وعَمِلوا الصَّالِحَاتِ أُولئكَ هُمْ خَيْرُ البَرِيَّة)
"Lalle ne wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan kwarai, wadannan su ne mafifita alherin halitta" (Surar Bayyina, 98:7)
Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: "Ya Aliyu, mafifita alherin halitta (a cikin wannan aya) su ne, kai da 'yan shi'arka( )".
(8). Fadar Allah Madaukakin Sarki cewa: ( أجَعَلْتُم سِقايَةَ الحاجِّ وعِمَارَةَ المَسْجِدِ الحَرامِ كَمَنْ آمَنَ باللهِ واليَومِ الآخِر)
"Yanzu kwa mayar da shayar da alhazai da raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya ba da gaskiya da Allah da ranar lahira kuma ya yi jihadi domin Allah?..." (Surar Tauba, 9: 19)
Lalle wadannan su ne Abbas da Dalha, wanda ya yi imani kuwa shi ne Aliyu (a.s.).
Akwai wasu ayoyi da dama a kan wannan lamari da muke magana a kansa, amma za mu takaita saboda takaitawa. |
|