Na Biyu: Nassin Halifanci Ya Zo Daga Manzo
Farra’u a littafin Ahkamus suldaniyya yana cewa: Babu jayayya a kan tabbacin hakkin halifa a kan wasiyya ga wanda zai maye gurbinsa, kuma babu kokwanto a kan zartuwar wannan wasiyya, domin imami shi ne ya fi cacanta ta da ita, zabinsa yana ga abin da ya zartar kuwa wannan ba ya dogara da ma’abota ra’ayi da fada aji na al’umma[15], wannan yana zama na halifa ne saboda tsoron faruwar fitina da kuma rashin zaman lafiyar al’umma[16] saboda haka wasu daga sahabbai suka rika koma wa Umar dan Khaddabi suna tambayarsa ya yi wasiyya ga wanda zai maye gurbinsa[17]. Ibn Hazam ya karfafi wannan ya ce: Mun samu cewa nada jagoranci yana inganta ta wasu fuskoki:
Na farko kuma mafi inganci mafifici shi ne shugaba mai mutuwa ya yi wasiyya zuwa ga wani mutum da yake zaba shugaba bayan mutuwarsa, shin ya yi hakan a lokacin lafiyarsa ko lokacin mutuwarsa ne, kamar yadda Manzo ya yi ga Abubakar, ko kuma Abubakar ya yi ga Umar, ko kuma Sulaiman dan Abdulmalik ga Umar dan Abdul’Aziz. Ya ce: Wannan fuska da muka zaba waninmu ya yi musunta, kuma mun zabe ta ne saboda abin da yake cikinta ne na cigaban saduwar jagoranci ba katsewa, da kuma tsaruwar al’amarin musulunci da ahlinsa, da kuma dauke abin da ake tsoro na sabani da rikici da ake zaton faruwarsa na daga rashin zaman lafiya, da kuma tsoron kada sirri ya yadu kuma kwadayin wasu ya tashi[18], Sai dai nassi da aka yi da’awrsa ga Abubakar daga Manzo bai tabbata ba, domin babu nassi ga Abubakar shi a kan kansa da cewa shi ne shugaba bayan Manzo (S.A.W), kai ba ma wanda ya taba cewa akwai shi, kai al’umma sun hadu a kan ma babu shi, domin duk wanda yake son ya tabbatar da nassi ga Abubakar to dole ya kore al’amarin da ya faru a Sakifa a dunkule da kuma a rarrabe, kuma ya karyata duk abin da ya zo a sihah na maganar Abubakar, da Umar, da Ali, da dan Abbas, da Zubair, game da halifanci. Saboda haka dole ya rusa dukkan abin da a zo na daga nazarin Ahlussunna game da Manzo (S.A.W) da imamanci, wannan nazari ba a gina shi a kan asasi daya, wato bai’a ga Abubakar ta wannan hanya da ta faru a Sakifa da kuma abin da ya biyo baya! Amma daga faruwar wannan abu ne nazarin shura ya samo asali tsakanin manyan al’umma, saboda haka babu wani ijma’i da ya tabbata, ijma’i a kan nassi game da Abubakar korarre ne[19]”. A nan ne Gazali ya kawo wata magana mai daidai da wannan ijma’i yana mai rushe maganar Ibn Hazam, Gazali yana fadi da alamar tambaya cewa: Don me ya sa ba ku ce nassi wajibi ne ya zo daga Annabi ko kuma daga halifa ba domin ku yanke cibiyar sabanin da ake yi? Sannan sai ya amsa da cewa: Da wasiyya ta kasance wajibi da Manzo (S.A.W) ya yi, alhalin bai yi wasiyya ba, Umar ma bai yi ba[20].
Yayin da Ibn Hazam ya ci gaba da kawo nazarinsa sai ga shi yana kore asalin nazarin shura da kuma kore maganar hakkin zabar shugaba ta hannun manyan al’umma, yana mai dogaro da zabar halifa ta hanyar nassi! Saboda ya nutsu da wajabcin nassi, sai dai shi yana nufin nassin da ya yi daidai da abin da ya faru, koda yake babu wani dalili a kan hakan. Hakika nassi bai saba da asalin nazarin shura ba har abada, shura a nan ba al’amari ne da ba shi da abin da ya kebance shi da wani yanayi ba, kuma dattijan al’umma ba su da hakkin su zabi wanda suka so haka nan kawai ba wani dalili, domin shura tana da iyaka, wannan kuma iyakar nassi ne ya zana mata ita. Suka ce: Daga sharadin shugaba ya kasance bakuraishe, imamanci ba zai yiwu ba sai da shi, suna masu kafa dalili da nassi tabbatacce a kan haka, hakika ya tabbata daga Annabi (S.A.W) ya ce: “Imamai daga Kuraish ne”. A wata ruwaya yana cewa: “Ku gabatar da Kuraish kada ku shiga gabanta” tare da samun wadannan nassosi da kowa ya sallama a kansu babu wata shubuha ta mai jayayya[21], ko zancen mai sabawa da za a yi la’akari da shi. Suka kuma shardanta wa wannan bakuraishe ya zama na ainihi daga kabilar Bani nadar dan Kinanata, domin ya yi daidai da nassi[22].
Ahmad dan Hanbal ya ce: “Ba yadda za a yi wani daga wanin kuraishawa ya zama halifa[23]”. Yana mai kafa dalili da wannan hadisi da tawaturinsa, da kuma fasawar da Ansar suka yi suna masu mika wuya ga muhajirai kuraishawa yayin da suka kafa musu dalili da wannan hadisi a Sakifa[24]. Ibn Khaldon ya ce: Jamhur sun tafi a kan sharadin kuraishanci da kuma ingantuwar halifanci ga bakuraishe koda kuwa ba zai iya daukar nauyin aikin tafiyar da al’amuran musulmi ba[25]. Haka nan nassin shari’a ya tabbatar da tawaturin magana a kan ingancinsa kuma ijma’i a kansa ya tabbata. Abu ne bayyananne cewa wannan ya faru ne yayin da nasara ta tabbata ga nassi a kan asasin shura, yayin da halifa na biyu ya ga wajabcin samuwar nassi a kan wanda zai maye gurbinsa. Sai wannan nassi ya zama ya hade da tsarin siyasa, duk da yana jefar da ka’idar shura gaba daya. Hada da cewa nassin hadisin Annabi mai daraja da daukaka yana cewa: “Shugabanni daga kuraishawa ne” yana mai rushe tunanin shura gaba daya! Sai ya zama wanda ya yi galaba a kan al’umma ya kuma kwace halifanci da takobinsa ya zama bakuraishe halifancinsa ya inganta domin bai fita daga nassin da ya gabata ba. Haka nan ba a la’akari da sharuddan wajibi da suke dole a same su ga halifa kamar ijtihadi, da adalci, da takawa, domin idan halifa ya zama bakuraishe to halifancin sa ya inganta koda kuwa ya zama mai rauni ko azzalumi. Ashe kenan al’amarin shura ya kamata ya zama ya fita daga wajen nassi, kuma ba zai yiwu a zabi wani ba sai bakuraishe na asali.
A takaice
wannan mas’ala tana tabbatar mana da samuwar nassi ingantacce a wannan nazari ta wannan hadisi: “Shugabanni daga kuraishi ne” hakika Buhari da Muslim da ma’abota Sunnan da Siyar sun rawaito da lafazi mabanbanta, sai dai wannan nassi yana bukatar abin da zai kebance shi saboda wasu dalilai:
1-Nassin da ya gabata “Shugabanni daga kuraish ne”, shi kadai ba ya iya tabbatar da hadafin da ake nema na tabbatar da shugabanci, wannan ya kasance domin kare addini da al’umma, ta yadda sahabbai da kansu sun fahimci wannan al’amari tun karewar zamanin halifanci na gari. A cikin sahihul Buhari ya zo cewa: Yayin da aka yi jayayya tsakanin Marwan dan Hakam yana Sham, da Abdullahi dan Zubair yana Makka, sai wasu jama’a suka tafi wajen sahabi Abi barzatal aslami suka ce: Ya Aba barza! ba ka ganin abin da mutane suka fada cikinsa? Sai ya ce: Ina neman ladan Allah domin na wayi gari ina mai fushi da kuraishawa, domin wanda yake a Sham wallahi ba yana yaki ba ne sai domin duniya, wanda yake yaki a Makka ba yana yaki ba ne sai domin duniya[26].
2-Akwai wasu nassosi ingantattu da suka kebance hadisin da ya gabata, kamar haka: Hakika Annabi ya tsoratar a kan alfahari da nasaba ta kuraish, ya kuma yi gargadin cewa wannan al’umma zata halaka, kuma al’amarinta zai daidaice. Ya zo a cikin Sahilul Buhari, daga gare shi (S.A.W) ya ce: “Halakar wannan al’umma zata kasance a hannun wasu samari na kuraishawa ne”[27]. Yaya kenan za a iya hada wannan nassosi guda biyu mai cewa: “Shugabanni daga kuraish ne” da kuma “Halakar wannan al’umman zata kasance a hannun wasu samari na kuraishawa ne”. Ba makawa a kebance wannan hadisin da abin da ya zo na hadisai game da kuraishawa, wannan kuma kebancewar iri biyu ce:
A-Ta korewa: Akwai hadisai da suka toge wasu mutane daga kuraishawa kuma suka nisantar da su daga fagen girmamawa.
Ibn Hajar Alhaisami a wani hadisi mai sanadi ingantacce cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Mafi sharrin kabilun larabawa: Banu Umayya, da Banu Hanifa, da Sakif”. Ya ce: A wani hadisi ingantace Hakim ya ce: A bisa sharadin shaihaini daga Abi Barzata ya ce: “Mafi kin jama’a ko mutane a wajan manzon Allah su ne Banu Umayya[28]”. Abin da ya zo game da sukan alayen Hakam baban Marwan yana da yawa kuma mash’huri ne, shin ya inganta shugabancin al’umma ya dogara da mafi sharrin kabilun larabawa wanda sune ma fi kin mutane a wajan manzon Allah (S.A.W)! Idan wadannan suka zama masu hukunci a sarari to dole mu shaida da cewa lallai al’umma ta halaka ta karkace ga barin gaskiya, kuma kamata ya yi al’umma ta dawo zuwa ga bin shiriyar manzon Allah (S.A.W) da nassin da ya kawo daga Allah na wasiyyarsa da Ahlin gidansa (A.S) maimakon ta koma tana neman samar wa abin da ya faru mafita da kuma tawilinsa da nassi.
B-Ta tabbatarwa:
Hadisin da yazo yana mai nuna fifikon kuraishawa da zabi a kan sauran kabilu bai tsaya ga nuna da’irai kuraishawa ba kawai, sai dai ya kebance wannan da cewa wasu jama’a daga cikinsu ake nufi sai ya ce: “Allah ya zabi Kinana daga ‘ya’yan Isma’il, ya zabi Kuraish daga Kinana, ya zabi Bani Hashim daga Kuraish, ya zabe ni daga Bani Hashim”[29]. Wannan fifita wa da daukaka ga Bani Hashim a kan sauran kuraish ne.
Ibn Taimiyya yana mai karin bayani game da wannan hadisi yana mai cewa: “Ya zo a cikin Sunna cewa; Abbas ya kai karar wasu kuraishawa da suke wulakanta shi, sai Manzo (S.A.W) ya ce: Na rantse da wanda raina take ga hannunsa! Ba wanda zai shiga aljanna sai ya so ku don Allah da kuma kusancina”. Idan sun kasance su ne mafifitan halitta to ba makawa ayyukansu su ne mafifita ayyuka, mafificinsu shi ne mafificin kowane mafifici na sauran kabilun kuraishawa da larabawa, har da Bani Isra’il da waninsu[30]. Matsayi a nan ba matsayi ne na fifita wa ba shi ke nan, sai dai abin nufi kuraish imaninta ba ya inganta sai ta so su Bani Hashim so biyu; Saboda Allah da kuma domin kusanci da Manzo (S.A.W).
Shin ya inganta kuraish gaba dayanta ta zama daidai a wajan gabtarwa a shugabanci da imamanci, kuma akwai Banu Hashim da nassi ya daukaka su zuwa mafi daukakar matsayi, da akwai kuma Banu Umayya da nassi ya kaskantar da su zuwa mafi kaskancin martaba?! Idan abin da ya wakana ya kai mu zuwa ga wannan halin, to shi kenan sai mu shaida da cewa abin da ya faru kauce wa daga hanya ta gari ne, ba mu yi kokarin gyara shi ba.
A takaice yana iya bayyana a fili cewa, a nan mu mun yi duba sosai don gane da abin da ya shafi bahasin maudu’in imamanci, sai muka ga cewa dalilin da ya sa aka samu wannan cece-kuce dangane da wadannan sabani da ake ta fama da su shi ne, bin wannan al’amari da ya faru, da kuma kokarin gyara shi da kuma sanya shi doka da madogara na asasi a tsarin siyasa da tafiyar da shugabancin al’umma har ya zama doka. Maganganu masu rusa juna da ake samu a lokuta daban-daban sun bayyana a zahiri a wadannan ra’ayoyi, abin da ya sa suka rasa kimarsu a matsayinsu na nazarin musulunci da zai iya warware daya daga manyan al’amuran musulunci masu girma.
Sai ga magana game da nassi na shari’a ba ta tsaya ga shi nassin ba, ba ta kuma lizimtu da aiwatar da sharuddansa ba da iyakokinsa. Shura kuma an nuna cewa abu ne rusasshe da aikin da halifa da ya gabata ya yi na nassi ga mai bi masa, da kuma ra’ayin shura da ra’ayin kwace da rinjaye da karfi da kuma sa karfin takobi. Amma mahangar tsarin shawarar manyan gari (shura) shi ya fi kowanne daga wadannan mahangai shiga duhu. Wani lokaci sai ta zama hannun mutum daya da zai kafa kansa halifa mutum biyu su bi shi kamar yadda ake daura aure, ko mutum hudu su bi shi, ko kuma su zama shida da halifa da ya rigaya zai ayyana ba tare da al’umma tana so ba, kai har abin ya wuce hakan, kai har malami kamar Ibn Khaldon ya sanya makusantan sarki da na gefensa -komai kuwa rashin takawarsu da iliminsu - a matsayin ma’abota kulla shugabanci da warwarewa wadanda irinsu ne suka sabawa halifa Ma’amun kan sanya halifanci zuwa ga Ali Arrida (A.S) bayansa[31].
Wannan al’amari ya faru a rabi na biyu na halifancin Usman, ta yadda ya zamana an samu shugaban masu bayar da shawara wani ne daga makusantansa na Banu Umayya a kebance, wanda ba su da wani fifiko, da daukaka, da kokari, da rigo na addini, tare da yawan wadanda suke da wadannan dabi’u a wannan lokaci! Sai manyan shura suka zama su ne Abdullahi dan Amir, da Abdullah dan Sa’ad dan Abi Sarh[32], da Sa’id dan Asi, da Mu’awiya dan Abi Sufyan, da Marwan dan Hakam.
Dabari ya rawaito cewa Usman ya aikawa Mu’awiya da Abdullahi dan Sa’ad dan Abi Sarh, da Sa’id dan Asi, da Amru dan Asi, da Abdullahi dan Amir, sai ya tara su domin ya yi shawara kan al’amrinsa, sai ya ce da su: Kowane mutum yana da wazirai da masu ba shi nasiha, kuma ku ne waziraina masu ba ni nasiha kuma aminaina, kuma kuna ganin abin da mutane suka gani na in kawar da gwamnonina, in kuma mayar da dukkan abin da da suke ki zuwa ga abin da suke so, ku yi kokarin dubawa ku ba ni shawara. Yayin da suka ba shi shawara sai ya yi aiki da duk shawararsu; ya kuma mayar da su a kan ayyukansu, ya kuma umarce su da tsanantawa ta fuskacinsu, da kuma korar mutane kan iyakoki[33] da kuma hana su komawa wajan iyalansu, ya kuma yi niyyar hana su albashinsu domin su bi shi su bukace shi[34].
Wannan irin al’amura masu karo da juna mustahili ne a same su a nazari daya, ta yadda zai zama nazari mai dacewa da al’amuran tafiyar da sha’anin al’umma da yake da doka da ake iya fahimta. Kuma daidai gwargwadon kokawanto game da ingancin wannan nazari daidai yadda yake kai wa ga rinjayar da dogaro da ingancin nassin shari’a da ya zo daga Annabi (S.A.W) wajan ayyana halifansa. Wannan ita ce irin natijar da Dr. Ahmad Mahmudu Subhi ya cimma yana mai duba nazarin imamanci yayin da ya ce: “Amma ta nahiyar tunani Ahlussunna ba su kawo wani nazari mai karfi ba game da siyasa da zai iyakance ma’anar bai’a da shura da ma’abota nada shugabanci da warwarewa daga manyan al’umma, balle a samu wani abu mai iya bambance mana tsakanin mahanga da abin da ya faru a aikace a zahiri, ko tsakanin abin da yake na shari’a da kuma abin da ya gudana a tarihi a aikace.
Sai ga nazarin Ahlussunna a siyasa ya bayyana a wannan zamanin karshe bayan daula ta tsayu a kan wanda ya fi karfi ya yi mulki kamar yadda ya zo a mafi yawancin wannan ra’ayoyi sun zo ne domin raddi ga nazarin Shi’a mabiya Ahlul Baiti (A.S), Kuma wasu daga wadannan ra’ayoyi aka sanya su a matsayin dalilai na hukuncin shari’a saboda dogaro da usulubin da halifofi uku na farko suka yi shugabanci. Wannan kuma ci baya da faduwa da rashin makama tsakanin shari’a da kuma abin da ya faru game da halifanci ne, balle kuma ga maganganu masu karo da juna na wadannan ra’ayoyi da abin takaici daga karshe suka sanya su a cikin dokokin fitar da hukuncin shari’a. Ba komai ne hadafinsu na yin haka ba sai samar da wani ra’ayi mai kishiyantar mahangar Ahlul Bait (A.S) na samun tabbatar nassi a game da halifanci[35].
Na uku: Muhimmancin da shari’a ta bayar ga abin da shawara ta zartar da kuma alakarsa da halifancin da yake da nassi. Zamu ga mafi muhimmanci madogarar shari’a da wannan nazari na shura ya dogara da shi ita ce wannan aya mai girma ta: “Ka yi shawara da su kan al’amari”. Wannan aya tana lizimta wa shugaba wajabcin shawara a kan wani ra’aryi gun wadanda suke ganin ana magana da Manzo ne da umartarsa da yin shawara, kuma umarni yana nuna wajabci, wannan kuwa yana nuna wajabcin shawara da musulmi, kuma tunda ba za a iya shawartar dukkan musulmi ba gaba daya to wannan yana nuna shawara da ma’abota ra’ayi da tunani na wannan al’umma ne[36]. Da wannan ma’anar zamu iya tambaya cewa; Shin shawara tana nufin ana neman yin ta a kan kanta, ko kuma ita hanya ce da za a cimma wasu hadafofi da ita? Suka ce: Ba makawa shawara ba a nemanta a kan kanta kuma ba tana zaman kanta ba ne, ita shawara hanya ce ta tabbatar da wasu abubuwan da mafi muhimmancinsu sanin ra’ayin wasu da kuma tunaninsu da tattaunawa, Domin idan tunani ya zo daga mahanga daban-daban aka tara shi waje daya sai ya sami kima mai girma wajan sanin makamar siyasa, da hukunci, da kuma tafiyar da al’amura, da tattalin arziki, da aminci, da yaki, a wannan kasa, wannan kuwa yana tabbata ba tare da ma’asumi ba daga ma’abota shugabanci.
A nan hadafin sanya shawara zai bayyana, sai dai menene matsayin shura a shari’a? Kuma shin natijar da za a samu ta hanyar shawara da ijma’i ra’ayin duka ake bukata ko kuma ra’ayin mafi yawa za a dauka? Kuma shin ya zama dole ga shugaba ya yi riko da wannan ko kuwa?. Malaman Ahlussunna suna bayar da amsa kala biyu ne a kan hakan:
Na farko: Masu ganin sakamakon shawara ya zama dole ne ga shugaba ya yi riko da shi. Daga cikin wadannan akwai Muhammad Abduh da yake fada a bayanin ma’anar Ulul’amri da yake cewa: Ulul’amri su ne masu shugabantar al’umma a hukunci, kuma wannan su ne aka yi nuni da su a fadin Allah madaukaki: “Al’amarinsu shawara ne tsakaninsu” ba kuma zai yiwu ba shawara ta samu tsakanin dukkan al’umma, don haka ya zama dole a samu wasu jam’a masu wakiltar al’umma, da ba kowa ne ba su sai ma’abota girma da daukaka na wannan al’umma da aka yawaita ambatonsu, yana mai karawa da cewa: Wajibi ne a kan shugabanni su yi hukunci da abin da manyan al’umma suka zartar”[37].
Na biyu: Ra’ayin da yake ganin shawara a matsayin fuskantarwa kawai, babu wani kima da take da shi na shari’a a wajan tilasta shugaba ya yi riko da ita wajan zartar da abin aka hadu a kansa, ko kuma abin da mafi yawa suka tafi a kai.
Daga cikin wadannan akwai Kurdabi, yayin da yake cewa a tafsirinsa “Shawara ta ginu ne a kan sabanin ra’ayoyi, mai shawara yana duba wadannan sabani ne, ya kuma duba wanda ya fi kusa da littafi da sunna in zai yiwu, idan Allah ya shiryar da shi zuwa ga abin da ya so sai ya yi niyyar aiki a kansa ya kuma zartar yana mai dogara gareshi”[38].
Amma malaman Shi'a sun tafi a kan ra’ayi na biyu a tafsirin ayar shura, Muhammad Jawad Balagi yana cewa: “Ka shawarce su a kan al’amari” ai ka nemi gyaransu, da kuma karkato zukatansu da shawara, ba wai domin zasu sanar da kai ilimin daidai ba ko sanar da kai ingantaccen ra’ayi ba, yaya kuwa zasu iya hakan alhali Allah (S.W.T) yana cewa: “Ba ya magana ta son rai, shi (al’amarin) ba komai ba ne face dai wahayi ne da aka yi” saboda haka idan ka yi niyya a kan abin da Allah ya umarce ka da hasken annabta ya kuma datar da kai a cikinsa sai ka aikata kana mai “ka dogara ga Allah”[39].
Shura a nazarin koyarwar Ahlul Baiti (A.S) tana nuna cewa ra’ayin musulmi ba ya lizimtar Annabi (S.A.W) yayin da madaukaki yake cewa: “Idan ka yi niyyar aiwatarwa sai ka dogara ga Allah”. Ashe kenan tsayuwa da aiki yana zama a bisa asasin niyyar Manzo (S.A.W) ba bisa abin da muminai suka yarda ba. Sannan shawararsa (S.A.W) ta kasance domin gane ra’ayin musulmi ne ga yadda za a zartar da hukunce-hukuncen musulunci, ita shawarar ba a matsayin fitar da hukuncin shari’a take ba, hada da cewa Ubangiji madaukaki ya ce: “Bai kamata ba ga mumini ko mimina idan Allah ya hukunta wani al’amari ya zama suna da zabi a al’amarinsu, duk wanda ya saba wa Allah da manzonsa hakika ya bace bata bayyananne”[40],
Ashe kenan rinjayar da shawara yana takaita da wajan da Allah da manzonsa ba su yi wani hukunci ba ne, amma abin da suka yi hukunci a ciki, shawara a nan sabo ce ga Allah da manzonsa da kuma bata bayyananne[41].
Saboda haka shura tana da kima ne idan ta amfana wajan daukar dokokin zartarwa na musulunci a dukkan fagagen rayuwa da makamancinta, kuma ba ta zama dole ga imami ma’asumi ba, domin ita ba ta iya shar’anta hukunci sabanin magana da zance da tabbatarwar ma’sumi, tana kebanta ne da wajan da Allah da manzonsa ba su da hukunci.
Amma ta bangaren tarihi kamar yadda muka ambata shura ba ta zama wani tsari na siyasa na shari’a na hukunci ba, domin an kirkiri ra’ayinta ne domin gyara barna da kuskure na tarihi da kuma sanya wannan a matsayin madogarar asasi ta tarihi a tsarin shugabanci na wannan lokaci, kuma mu sani halifanci ba ya tabbata sai da nassi daga Annabi ga halifan da zai zo bayansa.