Nassin Wasiyya A Hadisan Imam Ali Da Ahlul Baiti
Abu ne a fili ga wanda ya karanta tarihi cewa imam Ali shi ne wanda ya bayyanar da hadisai da suke nuna halifancinsa bayan Manzo da sunansa (A.S). Kuma ingancin wannan wani abu ne da ma’abota ilimi na wannan al’umma da suka fitar da son rai daga zukatansu suka tabbatar da shi, kuma sama da malami hamsin daga masu sharhin hadisansa sun yi bayanin haka suka kuma kare wannan kariya mai cike da hujjoji da dalilai da suka bayar da nutsuwa a kan hakan[21]. Ali (A.S) shi ne wanda ya dawo wa kwakwalen mutane batun hadisan halifancinsa ba tare da wata jayayya ba, bayan an hana fadin wadannan hadisai a lokacin halifofi da suka gabace shi, yayin da suka hana fadin hadisan manzon Allah sai wanda ya shafi ibada kawai:
1- Ya tara sahabban manzon Allah lokacin halifancinsa sannan ya yi musu huduba yana mai hada su da Allah cewa waye ya ji Manzo (S.A.W) a Gadir khum yana cewa; “Duk wanda nake shugabansa Ali shugabansa ne”, sai ya tashi ya shaida[22].
2- Ali shi ne ya yada wannan hadisin da ya bujuro da shi ga Abubakar da Umar da Annabi yake cewa akwai wanda a cikinku zai yi yaki a kan tawilin Kur’ani kamar yadda na yi yaki a kan saukarsa wanda Abubakar ya yi burin a ce shi ne, haka ma Umar, amma Manzo ya amsa musu da: cewa ba su ba ne. Sannan daga baya Manzo ya gaya wa mutane cewa Ali ne[23].
Wannan ruwaya duk da waninsa sun rawaito ta amma ruwayarsa tana da wani hususiyya domin ya yi ta ne a huduba a gaban mutane, ba hadisi ba ne da ya gaya wa mutum daya ko wasu jama’a, wannan kuwa yana karfafa karfin hadisi game da hakkinsa da yake da yakini da shi, kuma yake da yakini da cewa sauran sahabbai suna da yakini da hakan ba su manta ba.
3- Kuma ya ambaci da yawa daga wadannan hadisai da suke nuna hakkinsa a ranar shura ko bayanta, sai dai an yi sabani kan dalla-dallar maganar da isnadinsa, duk da a dunkule sun tabbatar da hakkinsa, mafi karancin abin da ya hada su da Allah a kansa shi ne abin da Ibn Abdulbar ya fitar a littafinsa yana mai cewa: Ali ya fada wa wadanda suke cikin shura tare: “Ina hada ku da Allah shin akwai wanda Manzo (S.A.W) ya hada shi ‘yan’uwantaka da shi tsakaninsa da shi yayin da ya sanya ‘yan’uwantaka tsakanin musulmi in ba ni ba? A bayan wannan hadisi Ibn Abdulbar ya sake rawaito wani daga Ali yana mai cewa: Imam Ali (A.S) ya kasance yana cewa: “Ni bawan Allah ne kuma dan’uwan manzonsa, ba mai fadin haka a bayana sai makaryaci”[24].
An rawaito ta a littafin Kanzul Ummal a wani hadisi mai tsawo daga Abu Dufail ya ce: Ali (A.S) ranar shura yana fadin wannan hadisi…[25]. Wanda abin da shi Ibn Abdulbar ya fitar wani yanki ne daga gareshi, sai dai sanadin Kaznul ummal a kwai jahala[26] a cikinsa, shi ya sa ma aka samu jayayya game da shi, an ce Zafir ya rawaito shi wanda shi mutum ne da ba a san shi ba, wasu kuma sun yi musun sa saboda mataninsa amma ba a la’akari da wannan saboda ya ginu ne a kan fahimta ta cewa an yi bai’a ga Abubakar a kan cewa ijma’i ce ko kusa da hakan wacce ba ta da asasi.
Amma isnadi ya kasance saboda Zafir ne kamar yadda Ibn Abdulbar ya rawaito shi a littafin Isti’ab,[27] Ibn Hajar Askalani ya ce: Zafir ba a tuhumar sa da karya, kuma idan aka same shi a hadisi to hadisinsa yana da kyau[28]. A farkon wannan hadisin, Abu Dufail yana cewa: Na kasance a bakin kofa ranar shura sai aka daga sauti sama, sai na ji Ali (A.S) yana cewa: “Mutane sun yi bai’a ga Abubakar amma na rantse da Allah ni na fi shi cancanta, amma sai na ji na bi domin tsoron kada su koma kafirai wasu suna saran wasu da takobi, sannan sai Umar ya biyo bayansa alhalin na fi shi cancanta kan wannan al’amri, amma sai na ji na bi tsoron kada mutane su koma kafirai wasu suna saran wasu, sannan sai ga ku kuna son ku yi bai’a ga Usman! Ba komai zan ji in bi”, Sannan sai ya ambaci al’amrin shura ya fara bayyana musu falalarsa da fifikonsa da darajojinsa da ya fi su da ita, daya daga cikinsu ita ce wannan bangaren da shi Ibn Abdulbar ya rawaito game da ‘yan’uwantakarsa da Manzo (S.A.W)[29]. Wannan hadisi yana da wani mai karfafarsa da zai zo nan gaba.
4- Daga abin da yake nuna cancantarsa fiye da Abubakar musamman yayin da ya fadi karbar surar bara’a daga Abubakar! Nisa’i ya rawaito da sanadi sahihi daga Ali (A.S) cewa manzon Allah (S.A.W) ya aika shi da bara’a zuwa ga mutanen Makka tare da Abubakar, sannan sai ya sa Ali ya bi shi ya ce da shi: “Ka karbi littafin ka tafi zuwa Makka ya ce: Sai ya cim masa a hanya, sai Abubakar ya koma Madina yana mai bakin ciki, sai ya ce: An saukar da wani abu game da ni ne? Sai Manzo ya ce: A’a, sai dai ni an umarce ni da in isar da wannan ko ni ko wani mutum daga gidana”[30]. A dukkan wannan hadisai akwai raddi ga wanda yake cwa Ali bai ambaci wani abu ba da yake nuna shi ya fi cancanta da halifanci, wannan kenan balle mu shiga Nahajul Balaga.
5- Daga mafi shaharar maganarsa bayan labarin Sakifa ya zo masa da kuma mubaya’ar da mutane suka yi wa Abubakar:
ya ce: Me kuraishawa suka ce?
Suka ce: Sun kafa hujja da cewa su ne bishiyar Manzo.
Sai ya ce; Sun kafa hujja da bishiya amma sun tozarta ‘ya’yan itaciyar[31].
6- Kafa hujja da sakamakon Sakifa a fadinsa:
Idan ka shugabance su sakamakon shura
Yaya haka alhalin masu shawara ba sa nan
Idan kuma ka kafa hujja garesu da kusanci ne
To waninka shi ne ya fi cancanta, ya fi kusanci[32]
7- Hudubar shakshakiyya wacce take da karfafuwa daga malamai[33] daban-daban kuma take da ma’ana da take nuni ga hakan a fili dalla-dalla: “Amma wallahi! Hakika wane ya sanya ta (rigar halifanci) alhalin kuma ya san cewa misalin matsayina game da ita kamar matsayin kan inji ne na nika da dutsensa, kwararar ambaliyar ruwa daga gare ni yake gangarowa kuma tsuntsu ba ya iya kaiwa wajena (duk tashinsa), amma sai na sakaya tufafi na kau da kai[34] na kuma cije na kawar da kai, na zama ina mai kai-kawon ko in tafi da yankakken (shanyayyen) hannu ko kuma in yi hakuri cikin makahon duhu…! Sai na ga hakuri a kan wannan ya fi lizimtuwa, sai na yi hakuri amma a cikin idanu akwai kwantsa, akwai kuma shakewa (ala-ka-kai) a cikin makogaro, ina ganin gadona abin kwacewa! har sai da na farko ya wuce, sai ya mika ta zuwa ga wane bayansa…
Abin mamaki! Yayin da ya kasance yana neman ya sance ta daga wuyansa[35] a rayuwarsa sai ga shi ya kulla (mika) ta ga wani bayan wafatinsa, ya mamakin tsananin yadda suka yi kashe mu raba na abin da yake cikin hantsarta…![36] Sai na yi hakuri tsawon lokaci, da tsananin jarabawa, har sai da ya wuce shi ma sai ya sanya al’amarin halifanci a hannun wasu jama’a da ya raya cewa (wai) ni daya ne daga cikinsu, Kaicon al’amarin shura!, yaushe ne kokwanton fifikon al’amarina a kan na farkonsu ya faru har da zan zama ana sanya ni tsaran makamantan wadannan!…”[37].
Daga wannan magana ta imam Ali (A.S) zamu sani cewa; ashe kenan Abubakar ya san matsayin imam Ali na halifanci da daukakarsa kamar yadda kan dutsen markade da nika yake da daukaka a kan jikin dutsen ne.
Saoba haka ne yake a fili cewa matsayinsa ba boyayye ba ne sai dai mun ga tarihi yana neman ya farar da wani abu na jayayya domin ya yi daidai da abin da ya faru a tarihi, kamar yadda muka samu wasu suna neman musun maganarsa a game da halifanci, wanda da can sun yi musu ga hadisan Manzo (S.A.W). Amma gaskiya tana nan, sai dai abin takaici da tarihi bai karkata zuwa ga Ali ba! Tarihin da ya riga ya tabbatar da cewa imam Ali bai yi bai’a ga Abubakar sai bayan wata shida, sai ya nemi toshe kunnensa game da wannan jinkiri da imam Ali ya yi!
8- Maganarsa bayan shura, yayin da suka yi wa Usman bai’a yana mai cewa: “Wallahi kun sani ni na fi cancanta fiye da wanina, wallahi zan yi hakuri matukar al’amarin musulmi ya kubuta zalunci ya kasance a kaina ne ni kadai, domin neman ladan Allah da falalarsa, da kuma nisantar abin da yake kuna goggoriyonsa na kawa da adonsa”[38]. Ibn Abil Hadid ya samu wannan kalma cikin karshen abin da Ali ya fada a wannan lokaci a maganar da ya nakalto ta a nan bayan ya kawar da duk wani kokwanto game da ingancinta, sai ya ce: Mu muna ambaton wannan abu da ya zo na ruwayoyi masu yawa na imam Ali da ya hada ma’abota shura da Allah, kuma mutane da dama sun rawaito wannan da yawa, amma abin da ya inganta bai kasance da tsawo ba kamar yadda aka rawaito, sai dai bayan sun yi bai’a ga Usman shi ya ki bai’a ya ce: “Mu muna da hakki da in an ba mu sai mu karba, amma idan aka hana mu shi sai mu hau bayan rakuma komai nisan tafiya”. Sannan sai ya ce da su: “Ina hada ku da Allah shin a cikinku akwai wanda Manzo ya sanya shi dan’uwa tsakaninsa da shi in ba ni ba?
Suka ce: A’a.
Ya ce: A cikinku akwai wanda Manzo ya ce: Duk wanda nake shugabansa wannan shugabansa ne in ba ni ba?
Suka ce: A’a.
Ya ce: A cikinku akwai wanda Manzo (S.A.W) ya ce: Kai a wajena kamar matsayin Haruna ne gun Musa, in ba ni ba?
Suka ce: A’a.
Ya ce: Shin a cikinku akwai wanda aka amincewa ya isar da surar bara’a kuma Manzo ya ce: Kuma ba wanda zai isar daga gare ni sai ni ko wani mutum daga gareni, in ba ni ba?
Suka ce: A’a.
Ya ce: Shin ba ku sani ba cewa sahabban Manzo sun gudu sun bar shi a filin daga[39] ba wanda ya rage tare da shi in ba ni ba, ban taba guduwa ba?
Suka ce: E.
Ya ce: Shin kun sani cewa ni ne farkon musulunta?
Suka ce: E.
Sai ya ce: Waye ya fi kusanci da Manzo?
Suka ce: Kai ne.
Sai Abdurrahman dan Auf ya katse maganarsa ya ce: Ya Ali! mutane ne suka zabi Usman, kada ka dora wa kanka laifi (ka damu kanka).
Sannan sai Abdurrahman ya kalli Abu Dalha Al’ansari[40] ya ce da shi: Ya Aba Dalha da menene Umar ya umarce ka?
Sai ya ce: In kashe duk wanda ya saba wa al’umma!
Sai Abdurrahaman dan Auf ya ce da imam Ali: Ka yi bai’a tun da haka ne, in ba haka ba sai ka zama wanda bai bi tafarkin musulmi ba! Kuma mu zartar da umarnin da aka umarce mu da shi a kanka!!
Sai Ali (A.S) ya ce: “Kun sani ni ne mai wannan hakki ba wani ba, wallahi zan yi hakuri matukar al’amarin musulmi ya tafi daidai zalunci ya zamanto a kaina ne kawai…”[41]. Wannan kuma hadisi jama’a da yawa suka rawaito shi, ba ya cikin raunanansu ko wadanda ake kokwanto.
9- Wani ya taba cewa da imam Ali ya dan Abi Dalib kai ka kasance mai kwadayin wanna shugabanci, sai ya ce: Ku ne kuka fi ni kwadayinsa kuma ku ne mafi nisa, amma ni na fi kusanci, kuma ina neman hakkina ne, ku kuma kuna hana ni, kuna juyar da fuskata daga gareshi, yayin da ya kafa masa hujja a cikin mutane sai ya juya yana dimuwa bai san me zai amsa ba”[42].
Ahlussunna sun ce wanda ya fadi haka shi ne Sa’ad dan Abi Wakkas ranar shura, Shi’a kuma sun tafi a kan Abu ubaida ne bayan Sakifa, kowanne ne gaskiya dai muhimmin abu ne wanda ya shahara da kowa Sunna da Shi’a suke rawaito wa kamar yadda Ibn Abil Hadid wanda yake Sunna kuma Bamu’utazili yake rawaitowa[43].
10- Fadinsa: “Ya Ubangiji! ni ina hada ka da kuraishawa da wanda ya taimaka musu, sun yanke zumuncina sun karanta matsayina, sun hadu a kan kwace mini abin da yake nawa ne, sannan suka ce: Ka karba da gaskiya ko ka bari da gaskiya[44],
11- Fadinsa: “Amma bayan haka… Yayin da Allah ya karbi ran annabinsa (S.A.W) sai muka ce mu ne ahlinsa masu gadonsa zuriyarsa majibinta al’amarinsa ba wani ba, ba mai yi mana jayayya kan shugancin Muhammad, kuma kada wani ya yi kwadayin hakkinmu, sai mutanenmu suka mike suka kwace mana hakkinmu na shugabanci, sai ga shugabancin a hannun waninmu…”.
Wannan duk yana daga hudubobin da imam Ali ya yi a Madina a farkon shugabancinsa a lokacin bai fi watanni da karbar halifanci ba[45].
12- Fadinsa: “Amma kwace mana wannan matsayi wannan wani abu ne da kwadayin mutane ya jawo shi, wasu kuma suka yi bakin ciki kan matsayinmu, alhali hukunci na Allah ne, kuma makoma a ranar kiyama tana nan gareshi”. Ya fadi wannan a jawabin wanda ya tambaye shi: Yaya mutane suka ture ku daga wannan matsayi alhali ku kuka fi cancanta da shi.
Sannan sai imam Ali ya cigaba da magana kan wani abin da ya fi ban mamaki na wannan zamani da kamar Mu’awiya zai zo yana jayayya da shi, yana mai cewa “Zamani ya kai munzalin da yanzu ya ba shi dariya bayan ya sa shi kuka”[46].