6- Wasu Ruwayoyi Na Daban
Kamar dai yadda muka bayyana, hadisai da ruwayoyi daga Manzon Allah (s.a.w.a.) game da Ahlulbaitinsa (a.s.) suna da yawan gaske, kuma ba za su kidayu ba a wannan karamin littafin. Malamai da masu hadisi sun kebance musu litattafai, ko kuma fasulla a littattafan hadisai, ko kuma sun ambata a wuraren da suka dace cikin litattafan tafsiri da ruwaya. Ga kadan daga ciki: "Mu Ahlulbaiti ba a gwada mu da kowa
".
A cikin wannan hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.) yana bayyana mukamin Ahlulbaiti (a.s) ne, da kuma matsa-yinsu madayanci, domin ya sanar da al'umma mahal-linsu, ya kuma shiryar da ita zuwa ga riko da su da lizimtar hanyar su a bayansa, domin a auna su da wasu wadanda ba su ba, don a gani.
A cikin wani hadisi na daban kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana magana ne kan Ahlulbaitisa (a.s.), inda yake cewa: "Mu Ahlulbaiti, Allah Ya zaba mana lahira bisa ga duniya, kuma lalle Ahlulbaitina za a nuna musu son kai da tsanani da kora cikin garuruwa, har wasu mutane za su zo ta nan - sai ya yi nuni da hannunsa ta gabas - ma'abutan bakar tuta, za su tambayi hakki, ba za a ba su ba, za su yi yaki kuma su yi nasara. Za a ba su abin da suka so kuma ba za su karbe shi ba har su mika ta (tutar) ga wani mutum daga Ahlulbaitina, har sai ya cika duniya da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci. To duk wanda ya riski wannan ya taho musu ko da da jan ciki ne a kan kankara
.
"(Dailami ya kawo hadisi daga Abu Sa'id (r.a.) cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Fushin Allah ya tsananta kan wanda ya cutar da ni dangane da Ahlulbaitina
". (Daga Aliyu (r.a.) ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Ku yi wa 'ya'yanku tarbiyya kan halaye guda uku: son Annabinku da son Ahlulbaitinsa da kuma karatun Alkur'ani, domin mahaddatan Alkur'ani na cikin inuwar Allah a ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa, tare da AnnabawanSa da ZababbunSa
"). (Dabarani ya ruwaito daga Ibn Abbas (r.a.) yana cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Digadigan bawa ba za su gushe ba har sai an tambaye shi abubuwa hudu: Kan rayuwarsa, yadda ya karar da ita; da jikinsa, yadda ya tsufar da shi, da dukiyarsa, yadda ya kashe ta da inda ya same ta da kuma soyayyarmu, Ahlulbaiti
").
A wata ruwayar kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana shiryar da al'ummarsa zuwa ga Ahlulbaitinsa, yana kuma bayyana matsayinsu na ilmi, da kuma fuskantar da al'ummar zuwa gare su yayin da fitinu suka tsananta, ra'ayoyi kuma suka sassaba. Yana gwama su da Littafin Allah, domin su ne malamai masu bayyana abin da Alkur'ani ya kunsa, masana hakikaninsa da abubuwan da ya tattara.
(Dabarani ya fitar da hadisi daga Al-Mudallabi bn Abdullahi bn Handabi daga babansa, ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi mana huduba a Juhfa, ya ce: "Ashe ban fi ku cancanta ba a kan kanku", sai suka ce: "Haka nan ne Ya Manzon Allah". Sai ya ce: "To ni mai tambayar ku ne kan abubuwa biyu: kan Alkur'ani da Ahlulbaitina
").
Alkur'ani Mai Girma A Wajen Malaman Mazhabar Ahlulbaiti (a.s)
"Lalle Mu ne, Muka saukar da Ambato (Alkur'ani), kuma lalle Mu, hakika masu kiyayewa ne gare shi". (Surar Hijr, 15: 9)
Alkur'ani littafin Allah ne da wahayinSa abin saukarwa a kan AnnabinSa mai daraja, Muhammadu dan Abdullahi (s.a.w.a). Littafin da Allah Ya kiyaye shi daga jirkita da gurbata. Wannan wahayin Allah tsarkakakke, wanda hannun mai jirkitawa bai taba shi ba, duk wata barna bata samunsa, ko ta baya ko ta gaba. Shi a yau yana nan kamar yadda ya sauko wa Manzo Amintacce (s.a.w.a), ba tare da wata tawaya ko kari ba. Shi ne mabubbugar shari'a, daga gare shi ake fitar da hukumce-hukumce, shi ne ma'auni sunna, magwajin fahimta da tunani, shi ne mabubbugar wayewar ilmomin Musulunci kana kuma tushen alherin dan'Adam da tsirarsa.
Hakika musulmi sun zazzaga da Alkur'ani tsakanin-su, daga tsara zuwa wata tsarar, suna nakaltar sa da kiyayewa da kula da shi kamar yadda Jibrilu (a.s.) ya saukar da shi ga Manzon Allah (s.a.w.a.). Wannan kuwa shi ne abin da musulmi suka dace a kai, kamar yadda suka hadu a kan karyata ruwayoyi raunana na karya wadanda suka sabawa wannan ijma'i na malamai kan rashin gurbatan Alkur'ani ta kowane bangare.
Babban malamin tafsirin nan wanda ya rubuta shahararren littafin tafsirin nan na Majma'ul Bayan fi Tafsiril Kur'an, Allama Shaikh Abu Ali al-Fadhl bn Hasan Dabrisi
(Allah Ya daukaka mukaminsa), wanda ake daukar tafsirinsa a matsayin mabubbuga kana abin komawa ga malamai da masu tafsiri, ya ce:
"Akwai irin wadannan maganganu (marasa tushe) kan kari ko ragi cikin Alkur'ani, da ba sa ma bukatan magana a kansu. To amma dangane da kari, an hadu kan cewa rashin ingancin hakan, amma batun ragi, wasu jama'a daga cikin abokanmu da wasu mutane daga cikin 'yan Sunna sun ruwaito cewa akwai canji ko tawaya a cikin Alkur'ani. To amma ingantacciyar magana a gurinmu ita ce sabanin hakan (wato babu wata tawaya ko ragi a cikin Alkur'ani), hakan kuwa shi ne abin da Murtadha([88]) (Allah Ya tsarkake ruhinsa) ya bayyana ya kuma yi bayani a kai. A wurare da dama ya ambata cewa ilimin da ake da shi kan ingancin nakalto Alkur'ani kamar ilmin da ake da shi kan garuruwa, manyan abubuwan da suka faru, shahararrun littattafa da rubutattun wakokin larabawa, lallai an sami kula mai tsanani, bukata kuwa ta tabbata kan nakaltar Alkur'ani da kiyaye shi. Bukatar da kular sun kai matsayin da nakalto shahararrun littattafa da wakokin da muka ambata ba su samu ba, domin Alkur'ani mu'ujizar annabta ne, a nan ake daukar ilmomin shari'a da hukumce-hukumcen addini. Malaman Musulunci sun kai matuka wajen kiyaye shi da kare shi har sukan san duk abin da a ka saba cikinsa game da li'irabinsa, kira'arsa, haruffa da kuma ayoyoyinsa, to ya ya zai yiwu a ce an jirkita shi ko kuma an tauye shi duk da wannan kula mai tsanani da kuma tsarewa matsananciya..."
Ya kuma kara da cewa: "Lalle ilmi a kan tafsirin Alkur'ani da sassaninsa da kuma ingancin nakalto shi kamar ilmi ne a kan jumlarsa, kuma hakan yana bisa tafarkin abubuwan da aka sani ne bisa larura cikin littat-tafai wallafaffu, kamar littafin Sibawaihi da Al-Mazanni. Masu kula da wannan sha'ani (nahawu) sun san littattafan nan a fasalce tamkar sanin da suka yi musu a jumlace, ta yadda da wani zai shigar da wani babi na nahawu cikin littafin Sibawaihi, wanda da baya ciki, to da sun gane da kuma fahimtar cewa an sanya shi ne cikin littafin daga baya, ba daga cikin asalin littafin yake ba, haka nan ma yake game da littafin Al-Mazanni. Kuma sananne abu ne cewa kula da nakalin Alkur'ani da tsare shi, yafi gaskata bisa kula da tsare littafin Sibawaihi da kuma Diwanin mawaka".
Ya kuma sake cewa: "Shi Alkur'ani ya kasance a zamanin Manzon Allah (s.a.w.a.) a tare yake a wallafe kamar yadda yake a yau. Ya kafa hujja da cewa Alkur'ani ya kasance ana darasinsa ana kuma haddace shi a wancan zamani har aka ayyana wata jama'a cikin sahabbai da cewa sun haddace shi, da kuma cewa ana bijiro da shi ga Manzon Allah (s.a.w.a.) ana karanta masa, sannan kuma wata jama'a daga cikin sahabbai kamar su Abdullahi bn Mas'ud da Ubayyu bn Ka'ab da sauransu, sun sauke Alkur'ani gaba ga Annabi (s.a.w.a) sau da yawa. Duk wannan yana nunawa cewa shi Alkur'ani ya kasance tararre ne jerarre, ba yankakke ba, ba kuma a watse yake ba. Ana riskar wannan hakika kuwa ba tare da bukatar wani dogon tunani ba.
Sayyid Murtadha ya ci gaba da cewa wanda ya saba wa wannan ra'ayi daga cikin Imamiyya da Hashawiyya, to ba a dogaro da wannan sabawa ta su domin sabawa da wannan ra'ayi abin dangantawa ne ga wasu mutane daga cikin ma'abuta hadisi wadanda suka nakalto hadisai masu rauni, amma suna zaton ingantattu ne. Kuma ba a barin abin da aka tabbatar da ingancinsa domin irin wadannan raunanan hadisai
". Sannan kuma sai ya ce: "Abin da ya shahara a wajen malaman Shi'a da masu bincikensu, kai ba ma kawai shahara ba har ma babu jayayya a cikinsa, shi ne rashin ragi ko kari cikin Alkur'ani
".
Shaihin malaman hadisi Muhammad bn Ali bn Husain bn Babawaihi al-Kummi, wanda ake wa lakabi da "Saduk" (ya rasu a shekara ta 381), kuma mawallafin littafin Man La Yahdhuruhul Fakih da kuma dimbin muhimmman littattafai, ya fada cikin littafinsa mai suna I'itikadatul Saduk cewa:
"Akidarmu game da Alkur'ani mai girma wanda Allah Ya saukar wa AnnabinSa Muhammadu (s.a.w.a) shi ne abin da yake cikin bangwayen nan biyu, shi ne wanda yake hannun mutane bai wuce wannan ba - har ya zuwa inda yake cewa - kuma duk wanda ya danganta gare mu cewa muna fadin wai Alkur'ani ya fi haka to shi makaryaci ne". Sannan ya shiga kawo hujjoji kan hakan, mai son karin bayani yana iya duba cikamakin maganan tasa
.
Shugaban jama'ar Shi'a, Abu Ja'afar Muhammad bn Husain al-Dusi (wanda ya rasu a shekara ta 460 hijiriyya), mawallafin littafin Al-Khilaf da Al-Mabsud da Al-Tahzib da Al-Istibsar da sauransu, ya fada cikin littafinsa na tafsiri mai suna Al-Tibyan cewa
:
"Amma zancen kari (cikin Alkur'ani) da tawaya, suna daga cikin abubuwan da su ma ba su dacewa da shi domin kari cikinsa, abu ne wanda aka yi ijima'i kan batacce ne. Tawaya kuwa, bisa zahirin ra'ayin musulmi, babu shi, hakan kuwa shi yafi dacewa da abin da ya inganta a mazhabarmu, shi ne kuwa abin da Al-Murtadha ya goyawa baya, shi ne kuma zahirin ruwayoyi, - har zuwa inda yake cewa - ruwayoyinmu kuma suna karfafa juna kan kwadaitar da karanta shi da riko da abin da yake ciki, da dawowa da duk wata sassabawar hadisai masu magana kan rassa (furu'a) zuwa ga Alkur'ani. Hakika an ruwaito wani hadisi da ba wanda yake musa shi, daga Annabi (s.a.w.a) cewa, Annabi (s.a.w.a) ya ce:
"Ni mai barin Nauyayan Abubuwa guda Biyu ne tare da ku, wadanda idan kuka yi riko da su ba za ku bata a baya na ba: (su ne) Littafin Allah da Zuriyata, Ahlulbaiti, don ba za su rabu da juna ba har sai sun riske ni a bakin tafki".
Wannan yana nuni da cewa shi Alkur'ani samamme ne a dukkan zamani, domin ba zai yiwu ya yi umurni da riko da abin da ba za mu iya riko da shi ba, kamar yadda Ahlulbaiti (a.s) da wanda bin fadarsa yake wajibi samammu ne a duk lokaci. To idan wanda yake tare da mu an hadu a kan ingancinsa to ya kamata mu shagaltu da tafsirinsa da bayyana ma'anoninsa, mu bar komawa bayan wannan).
Allama Shaikh Muhammad Jawad al-Balagi ya tabbatar da wannan hakika cikin tafsirinsa Ala'ur Rahaman fi Tafsiril Kur'an, wato dawwamar Alkur'ani da kubutarsa daga jirkita da gurbata, inda yace:
"Haka Alkur'ani ya ci gaba a kan wannan gagarumin tafarki daga wannan al'umma zuwa wancan, kana iya ganin duban dubata na littattafa da mahaddatansa, kuma haka aka ci gaba da buga wasu Kur'anan daga wasu, wasu daga cikin musulmi suna ji da karanta shi daga wasunsu……ko da yake muna cewa dubbai ne kawai, amma fa daruruwan dubbai ne ko ma a ce dubban dubbai. Babu shakka, babu wani al'amari na tarihi da ya sami irin wannan inganci da wanzuwa wacce take a sarari tamkar abin da Alkur'ani ya samu, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya yi alkawari cikin Surar Hijr:
"Lalle Mu ne Muka saukar da Ambato (Alkur'ani), kuma lalle Mu, hakika, Masu kiyayewa ne a gare shi". Da kuma fadinSa Ta'ala cikin Surar Kiyamati: "Lalle ne wajibi ne a gare Mu, Mu tara shi, Mu (tsare maka) karatunsa".
To idan ka ji wani abu kan jirkitar Alkur'ani da bacewar sashensa, daga bakaken ruwayoyi, kada ka ko kula su sannan ka fadi duk abin da ilmi yake yarda da fadinsa na daga sassabawar su da rauninsu da raunin masu ruwaitosu da sabawarsu wa musulmi, da kuma raunin da abin ruwaitowarsu - rusashshe - ya zo da shi
".
Shehin malamin ya ci gaba da cewa cikin tafsirinsa karkashin fasalin: "Maganar Imamiyya Kan Cewa Babu Tawaya Cikin Alkur'ani", inda yace: "Ba a boye yake ba cewa Shaihin masu hadisi wanda aka san shi da kula da abin da yake ruwaitowa, wato Shaikh Saduk (Allah Ya kyautata makwancinsa) ya fada cikin littafinsa al-I'itikad cewa: "Akidarmu ita ce cewa Alkur'anin nan da Allah Ya saukar wa AnnabinSa (s.a.w.a) shi ne dai wanda yake cikin bangwayen nan biyu (wanda kowa ya sani) bai kuma wuce haka ba, wanda kuwa ya danganta mana cewa mun ce ya fi haka, to shi makaryaci ne".
Shaikh al-Mufid a littafinsa na al-Makalat ya kawo cewa wasu jama'a daga cikin Imamiyya sun ce shi Alkur'ani ba a tauye ko da kalma ko aya ko sura daga cikinsa ba, amma an shafe abin da yake tabbatacce cikin Mus'hafin Amirul Muminina (a.s) na tawili da tafsirin ma'anoninsa bisa hakikanin saukarwa.
A cikin littafin Kashful Gida'i fi Kitabil Kur'an, a fasali na takwas, kan tawayar Alkur'ani an ce: Babu shakka cewa an kiyaye shi daga tawaya da kiyayewar Sarki Mai sakamako, kamar yadda Alkur'ani ya yi nuni da hakan a sarari, kuma malamai suka hadu a kai.
Shaikh Baha'i yana cewa: "Kuma haka nan an yi sabani kan aukuwar kari da tawaya cikinsa, abin da ya inganta shi ne shi Alkur'ani mai girma kiyayayye ne daga hakan, kari yake ko ragi, kuma lalle fadin Allah Madaukakin Sarki cewa: "Kuma lalle Mu, hakika Masu kiyayewa ne gare shi" yana nuni da kuma tabbatar da hakan. Al-Mukaddas al-Bagdadi cikin Sharhin al-Wafiya yana cewa:
"Hakika sanannen zancen Imamiyya kan ragi a cikin Alkur'ani shi ne rashin hakan a cikinsa", har ila yau ya ce an samu daga Shaikh Ali bn Abdul Ali cewa shi ya wallafa littafi na musamman kan kore tawaya cikin Alkur'ani daga hadisai, inda ya ce idan hadisi ya zo bisa sabanin dalili na Littafin Allah da Sunna ingantacciyar ko kuma ijma' (abin da malamai suka hadu a kai amma da sharadin akwai wani Imami a cikinsu), kuma ba zai yiyu a yi masa wani tawili ba ko kuma daukansa da wasu ma'anoni ta wasu fuskoki ba, to wajibi ne a jefar da shi
".
Marigayi Allama kana Mujahidin zamani Shaikh Muhammad Husain Kashif al-Ghida ya fada cikin littafinsa mai suna Aslul Shi'a wa Usuluha cewa:
"Lalle wannan Littafin da yake hannu musulmi shi ne Littafin da Allah Ya saukar masa (Annabi) domin gajiyarwa da kalubale, da kuma cewa babu nakasi a ciki, babu jirkita, babu kuma kari, a kan hakan ne (malamai) suka hadu a kai".
Sharifi mai kira zuwa ga gyara, Sayyid Abdul Husain Sharafuddin ya fada cikin littafinsa Fusulul Muhimma fi Talifil Umma cewa: "Alkur'ani mai hikima, barna bata zuwa masa a zamaninsa ko a bayansa. Abin sani dai shi ne a cikin bangwaye biyun nan, shi ne kuma a hannun mutane, ba a kara ko da harafi ko kuma a rage wani ba, babu musayyar kalma da wata, ko harafi da wanin harafin. Kuma ko wani harafi cikin haruffan Alkur'ani tabbatacce ne a kowani zamani tun daga zamanin da aka saukar da shi. Sannan ya kasance a tare a wancan zamani mafi tsarkaka, yana rubuce kamar yadda yake a yau. Mala'ika Jibrilu (a.s.) ya kasance yana kawo shi ga Manzon Allah (s.a.w.a.) sau da yawa, dukkan wannan yana cikin al'amurra sanannu wajen masu bin diddigi cikin malaman Imamiyya. Don haka ba a dogara da maganan 'yan Hashawiyya, domin su ba su da fahimta".
Haka nan kuma malamin nan mai yawan bincike, babban mutum, Sayyid Muhsin Amin Husaini Amili ya fadi cikin littafinsa A'ayanu al-Shi'a cewa:
"Babu wani daga cikin 'yan Imamiyya, dadadde ko na yanzu da yake cewa akwai kari, babba ne ko karami, cikin Alkur'ani, face ma dai dukkansu sun hadu a kan rashin kari, hakika wadanda ake dogaro da maganarsu daga cikin masu bin diddigi sun hadu a kan cewa babu abin da ya ragu daga cikin Alkur'ani".
To wannan dai shi ne Alkur'ani mai girma da kuma ra'ayin Imamiyya dangane da shi, shi ne kuma dai a yanzu yake hannu musulmi, kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya zo da shi. Kuma shi mai wanzuwa ne da wanzuwar dan'Adam a kan doron kasa, yana haskaka wa dan'Adam hanyar rayuwa, ya kuma rike hannun al'umma zuwa ga shiriya.
Malamai da masu bincike da masu bin diddigi, suna ganin cewar abin da ke yawo tsakanin wasu mutane na ruwayoyi da zantattuka (marasa tushe) da suke maganar tawayar Alkur'ani, cikin da'irar Ahlussunna da Shi'a, ba kome ba ne face sanyawa ce ta makaryata, wacce babu makawa dole a yi jifa da su.
Haka nan ana samun wasu ruwayoyi wadanda ana yiwa zahirinsu wata fahimta ba tare da zurfafa nazari wajen karanta su da fahimtar su ba, wacce kuma ta sa ake cewa da akwai tawaya cikin Alkur'ani ko kuma samuwar wani Mus'hafi daban kamar yadda al'amarin ya rikitar da wasu mutane, masu muzanta Musulunci kuma suka dauki hakan wata dama ce gare su ta musguwa wa Musuluncin da kuma musulmai da kuma kokarin kawo rarrabuwa tsakaninsu. Kamar abin da aka ruwaito daga Imam Ja'afar bn Muhammad al-Sadik (a.s.), ba tare da kula da ingancin ruwayar ko rashin sa ba. Ga abin da ya ce:
"...amma wallahi - sai ya mika hannunsa zuwa kirjinsa - akwai makamin Manzon Allah (s.a.w.a.) tare da mu, takobinsa da sulkensa, kuma wallahi, muna da Mus'hafin Fadima tare da mu, babu wata ayar Littafin Allah a cikinsa, shi dai shifta ce daga shiftar Manzon Allah (s.a.w.a.) Aliyu kuwa shi ne ya rubuta shi da hannunsa
".
Hakika wasu sun shiga wahami kan cewa Imam Sadik (a.s.) - wal iyazu billahi - yana ba da labarin samuwar wani Alkur'ani ne ban da wannan Alkur'anin da ke hannunmu, sai wadansu suka dauki wannan waha-mi a matsayin wata hujjar shuka barna tsakanin mutane.
To amma abin da hadisin nan yake nufi a sarari yake, ga mafi raunin mutane, wanda dai ya san harshen larabci. Domin shi Imam Sadik (a.s.) yana cewa ne: "Wallahi muna da Mus'hafin Fadima". Idan muka koma ga kalma Mus'haf cikin harshen larabci zai sa mu fahimci ma'anar wannan magana ta Imam (a.s.).
Ragib al-Isfahani yana cewa: "Sahifa ita ce duk wani abu shimfidadde, kamar shimfidar kunci, ganye ko wani shafi da ake rubutu a kansa, jam'inta kuwa shi ne Saha'if ko kuma Suhuf. Allah Ta'ala Yana cewa: "Suhufin Ibrahima da Musa", "Suna karanta Suhufai tsarkakakku, cikinsu akwai litattafai masu kima".
An ce abin da ake nufi da Suhufan shi ne Alkur'ani, sai Ya sanya su takardu da litattafai a cikinsa domin tara wani abu bayan abin da yake cikin sauran littattafan Allah. Shi kuwa Mus'hafi shi ne abin da aka yi shi mai tattara takardu rubutattu, jam'insa kuwa shi ne Masahif
).
Saboda haka kalmar Mus'haf, a ma'anonin da muke amfani da su a yau, tana nufin littafi ba suna ne wanda ya kebanta da Littafin Allah (Alkur'ani) ba. Shi suna ne na kowane littafi da ya tattara takardu ko fatu (kamar yadda ake rubutu a jikin fata a zamanin da). Ana kiran Alkur'ani da sunan Mus'haf ne domin shi mai tattare ne da takardu.
Alkur'ani mai girma yana da sunaye daban-daban kamar haka: Alkur'ani, al-Zikr, al-Furkan da kuma al-Kitab
, wahayi dai bai kira shi (Alkur'ani) da sunan Mus'haf ba, kai dai musulmi su suka ba shi wannan suna yayin da suka tara shi, don bayan tarawan ya zamanto wani tari ne na (suhuf) wato takardu.
Saboda haka, lallai tushen rudanin shi ne batun isdilahi (yadda ake amfani da kalmomi) da ma'ana ta lugga a wancan zamanin, wadda ma'anar da mutane suke dauka a cikinsa, yanzu ba a daukar ta a wannan zamanin.
Sannan kuma Imam ya bayyana ma'anar wannan Mus'haf din domin ya kau da rikitarwar da ka iya faruwa, inda ya ce: "Babu wata aya ta Littafin Allah a cikinsa".
Ma'ana, shi ba Alkur'ani ba ne, ba kuma daga Alkur'ani yake ba, ba kuma wahayi ne ba, (shi dai shifta ce ta Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma (rubutun Imam Ali).
Wasu malumma suna cewa wannan Mus'hafin wasu tarin addu'oi da shiryarwa ne wadanda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi shiftar su ga Fadima al-Zahra (a.s.) domin tarbiyyarta da kuma ilmantar da ita.
To wannan yana bayyana mana kuskure, rudani da jirkitarwa da wasu daga cikin musulmi suka yarda da shi a dalilin mummunar fahimta da mugun nufi. Alkur'ani Mai Girma A Ruwayoyin Ahlulbaiti (a.s)
Wanda duk ya yi bitar ruwayoyi da hadisan da suka zo ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) ya kuma karanci tarihin rayuwarsu da alakarsu da Littafin Allah, ba zai sami muhimmanci da kulan da Ahlulbaiti (a.s) suke bayarwa fiye da wanda suke bai wa Littafin Allah, Mai Girma da Daukaka ba, ko a yanayin rayuwarsu ko cikin abin da suka ruwaito da maganganunsu ko cikin abin da suka yi wasiyya ko suka tarbiyyantar ko suka fuskantar da mabiyansu da almajiransu da daukacin 'ya'yan musulmi.
Imam Ja'afar Sadik (a.s.) ya ruwaito daga kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ya ku mutane, lalle kuna gidan dako ne, kuma kuna kan tafiya, tafiyar kuwa tana sauri da ku, kun ko ga dare da yini da rana da wata suna tsufar da kowane sabon abu, suna kuwa kusanto da kowane manisanci suna kawo kowane abin alkawartawa, to ku tanadi shiri wa tafiyar nan mai tsawo". Ya ce: sai Mikdad bn Aswad ya mike, ya ce: Ya Manzon Allah! Mene ne gidan dako?, sai ya ce masa:
"Gidan isarwa da yankewa, to idan fitinu kamar yankin dare mai duhu sun rikitar da al'amurra a kanku, na hore ku da Alkur'ani, domin shi, mai ceto ne abin karbawa ceto, mai jayayya abin gaskatawa. Duk wanda ya sanya shi gabansa zai ja-gorance shi zuwa aljanna, wanda ko ya sanya shi a bayansa zai iza shi zuwa wuta. Shi kuwa ja-gora ne mai shiryarwa zuwa mafi alherin hanya. Kuma shi littafi ne wanda a cikinsa akwai rarrabewa da bayani da riba (ko karuwa) shi ne rarrabewa kuma ba kakaci ba ne, yana da baya da ciki. Bayansa hukumci ne, cikinsa kuwa ilmi ne, bayan nasa gwanin kyau ne da shi, cikin nasa kuwa zurfi ne da shi. Yana da taurari, bisa taurarinsa ma akwai wasu taurarin. Ba a iya kididdigar ababen ban mamakinsa, abubuwan ban sha'awarsa kuma ba sa tsufa. Akwai fitilun shiriya da hikima cikinsa, kuma mai shiryarwa ne zuwa ga masaniya ga wanda ya san sifa. To mai yawo ya yi yawo (cikin Alkur'ani) da ganinsa, kuma dubinsa ya riski sifar domin ya tsira daga halaka ya kuma kubuta daga tsanani. Domin kuwa tunani rayuwar zuciya mai gani ne, kamar yadda mai tafiya cikin duhu yake haskaka hanya da haske. To na hore ku da kubuta mai kyau da karancin dako
". Imam Sadik (a.s.) yana cewa: "Mahaddacin Alkur'ani, mai aiki da shi yana tare da Mala'iku Marubuta, Masu daraja, Masu da'a ga Allah Ta'ala
".
Imam Aliyu bn Husain (a.s.) yana cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda Allah Ya ba shi Alkur'ani, sai ya ga cewa an bai wa wani mutum fiye da abin da aka ba shi, to hakika ya rena babban abu, ya kuma girmama karami
".
Ya zo kuma daga wajen Imam Muhammadu Bakir (a.s.) cewa ya ce Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ya ku jama'a makarata Alkur'ani! Ku ji tsoron Allah Mai Girma da Daukaka cikin abin da Ya dora muku na LittafinSa domin ni abin tambaye ne, ku ma abin tambaya ne. Ni za a tambaye ni kan isar da sako, ku kuma za a tambaye ku ne kan abin da aka dora muku na Littafin Allah da Sunnata
".
Sannan kuma Imam Sadik (a.s.) yana cewa: "Ya kamata mumini kada ya mutu har sai ya koyi Alkur'ani, ko kuwa yazama cikin koyonsa([102])".
Imam Sadik (a.s.) kuma yana cewa: "Alkur'ani alkawarin Allah ne da bayinSa, to hakika ya kamaci mutum musulmi ya yi dubi cikin alkawarinsa, ya kuma karanta ayoyi hamsin daga ciki a kullum
".
Imam Sadik din dai yana cewa: "Abubuwa uku za su kai kuka zuwa ga Allah Madau-kakin Sarki: masallacin da aka kaurace masa ba a salla a cikinsa, malamin da ke tsakanin jahilai da kuma Alkur'anin da aka rataye shi kura tana hawa kansa don ba a karanta shi
".
Imam Sadik (a.s.) yana cewa: "Lalle Alkur'ani rayayye ne ba matacce ba, kuma yana gudana kamar yadda dare da yini suke gudana, kuma kamar yadda rana da wata suke tafiya. Yana kuma tafe ne kan na karshenmu, kamar yadda yake tafe a kan na farkonmu".
Amirul Muminina (a.s) ya ce: "Sannan Allah Ya saukar masa da Littafi, haske ne fitilunsa, ba su mutuwa, fitila ce da haskenta ba ya bishewa, kogi ne da ba a risko zurfinsa; tafarki ne wanda salonsa ba ya bacewa; haske ne wanda ba ya yin duhu, mai rarrabewa wanda karfin hujjarsa ba ya raguwa, bayani ne wanda ba a rusa ginshikinsa, waraka ce wadda ba a tsoron cuta a tare da ita, daukaka ce wacce ba a rinjayar masu taimakon ta; gaskiya ce wadda ba a tabar da masu taya ta. Shi ne taskar imani, kuma tsakiyar shi, shi ne mabubbugan ilmi da kogunan shi; shi ne koraman adalci da tabkunan shi; shi ne murhun Musulunci da ginin shi; shi ne kwazazzabon gaskiya da mafakarta; shi tekun ne da masu kwarfa ba sa iya kwarfe shi; idanuwar ruwa ne masu kwarfa ba su iya karar da shi; wuraren sha ne masu taho masa ba sa kafar da shi; masaukai ne da matafiya ba sa bacewa da hanyarsa, alamu ne wadanda matafiya ba sa makance masa; tsaunuka ne da wanda ya nufe su ba zai wuce su ba. Allah Ya sanya shi mai kashe kishin ruwan malamai; bazaar (mai rayawa) ga zukatan fukaha'u (masana ilmin fikihu); gwadabe mai tara hanyoyin mutanen kwarai; waraka wadda babu wata cuta bayanta; hasken da babu wani duhu tare da shi; igiya ce mai karfi; mafaka ce wadda kololuwarta karerriya ce; daukaka ga wanda ya jibince shi; aminci ga wanda ya shige shi; shiriya ga wanda ya yi koyi da shi; uzuri ga wanda ya yi riko da shi; hujja ga wanda ya yi magana da shi; shaida ga wanda ya yi amfani da shi wajen jayayya; nasara ga wanda ya kafa hujja da shi; mai daukar duk wanda dauke shi; abin hawa ga wanda ya yi aiki da shi; alama (aya) ce ga wanda ya sa lura; garkuwa ga wanda ya nemi kariya da shi; ilmi ga mai kiyayewa; abin fadi ga mai ruwaya; kuma hukumci ne ga mai hukumtawa
".
Haka nan dai muke fahimtar kimar Alkur'ani da darajarsa a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da kuma tafarkinsu. Ita ce kuwa kima ta hakika wacce Alkur'ani ya yi furuci da ita, wahayi kuma ya siffanta shi da ita "Hakika wannan Alkur'ani yana shiryarwa zuwa hanya da tafi daidai". (Surar Isra'i, 17: 9)
Alkur'ani shi ne hanyar rayuwar al'umma, mabubbu-gar ilmi da shiriya, taskar ma'arifa da wayewa, tafarkin fahimta da tunani, ma'aunin ci gaba da halaye na kwarai, shi ne doka ta ilmi wajen tsara rayuwar dan'Adamtaka, kuma shi ne ma'aji mai tattara al'adun rayuwar mutumtaka da dokokinta.