Tafarkin Ahlulbaiti (a.s) Kan Ayyukan Siyasa
Duk wanda ya bibiyo salon siyasar Ahlulbaiti (a.s) da gwagwarmayarsu ta bayyane da ta boye a tsawon karno-ni biyu da rabi zai iya gano cewa aikin da suka yi na siyasa yana bisa ginshikai kamar haka:
(1). Tarbiyyantar da al'umma kan kin zalunci da tabbatar da manufar adalci da bayyana fikirar imamanci da siyasa da fayyace rukunan hukumci da shugabanci cikin addinin Musulunci. Sun yi haka ne domin karfafa fahimtar siyasa ga al'umma da karfafa kulawarta da kiyayyarta ga azzalumai, da farkar da ita daga barci. Wanda ya yi bitar abin da Ahlulbaiti (a.s) suka ruwaito suka watsa daga Manzon Allah (s.a.w.a.) dangane da wannan al'amari, zai gane muhimmancin wannan mataki wajen farfado da ruhin siyasa da kiyayewa ta Musulunci. A nan za mu ambaci wasu daga cikin ruwayoyin da suke magana dangane da shugabanci da kuma nauyin da suka hau kan shugaba musulmi, da kuma kyamar da Musulun-ci yake wa zalunci da kuma kira zuwa ga adalci, don mu fahimci fikira da tunanin Ahlulbaiti (a.s) wajen fada da zalunci da kuma kwadaitar da al'umma zuwa ga canji da kuma motsi na siyasa.
An ruwaito daga Imam Muhammad Bakir (a.s.) cewa wani dattijo daga kabilar Nakh'a ya ce: "Na ce wa Abu Ja'afar (a.s.) cewa: Ni na kasance gwamna ne tun zamanin Hajjaj har yau din nan, shin za a karbi tuba ta? Sai na yi shiru, sannan na sake maimaita wannan tambayar, sai yace min: "A a; har sai ka mai da wa duk wani mai hakki, hakkinsa
".
Abu Hamza al-Thumali ya ruwaito daga Imam Abu Ja'afar al-Bakir (a.s.) cewa: "Yayin da Aliyu bn Husaini (a.s.) ya zo cikawa sai ya rungume ni ya zuwa kirginsa sannan ya ce: "Ya dana, ina maka wasicci da abin da babana (a.s.) ya mini wasicci yayin da cikawa ta zo masa, kuma da abin da ya ambata cewa babansa ya yi masa wasicci. Ya ce: Ya dana, na hane ka zaluntar wanda ba shi da mai taimako kanka sai Allah Ta'ala
".
Imam Sadik (a.s.) ya ce: "Babu zaluncin da yafi zaluncin da wanda aka zaluntan ba shi da mai taimakonsa a kan shi sai Allah Mai Girma da Daukaka
".
Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito daga kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Ku tsoraci zalunci domin shi duhu ne a ranar lahira
".
Imam Sadik (a.s.) ya ce: "Allah Mai Girma da Daukaka Ya yi wasicci ga wani Annabi da cikin Annabawansa wanda yake cikin masarautar wani jabbarin sarki cewa: 'Ka je wajen wannan azzalumin ka ce da shi; Ni ban shugabantar da kai domin zubar da jini da tara dukiya ba, sai dai kawai na shugabantar da kai ne domin ka raba Ni da sautin (karar) wadanda aka zalunta. Domin Ni ba zan bar zaluncin da aka yi masu ba ko da kafirai ne
".
Imam Sadik (a.s.) ya ce: "Da wanda ya aikata zalunci da mai taimakonsa da kuma wanda ya yarda da shi, to dukkansu ukun masu tarayya ne (cikin zaluncin)
".
Imam Sadik (a.s.) din dai ya ce: "Duk wanda ya yi uzuri wa zaluncin azzalumi, Allah zai dora masa wani azzalumi da zai zalunce shi, kuma idan ya yi addu'a ba za a amsa masa ba, kuma Allah ba zai ba shi ladar zaluncin da aka masa ba
".
Abu Basir ya ruwaito cewa: "Mutane biyu sun zo wajen Imam Sadik (a.s.) a kan wani lamari na mu'amala tsakaninsu. Yayin da Imam (a.s.) ya ji zancen kowannensu, sai ya ce: "Hakika wanda ya cimma bukatarsa da zalunci bai cimma kome ba. Lallai za a biya wanda aka zalunta da addinin azzalumin fiye da abin da shi ya dauka daga dukiyar wanda aka zalunta", daga nan sai ya ce: "Duk wanda yake aikata wa mutane sharri kada ya yi kyama idan aka yi masa. Hakika babu abin da dan Adam zai girba face abin da ya shuka. Babu wanda zai girbi abu mai dadi baicin ya shuka mai daci, babu kuma wanda zai girbi mai daci baicin ya shuka mai dadi". Sai mutane biyun nan suka yi sulhu kafin ma su tashi daga gare shi
".
A'imman Ahlulbaiti (a.s) sun ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Duk wanda ya tafi tare da azzalumi domin ya taimake shi, alhalin ya san cewa shi azzalumi ne, to, hakika ya fice daga Musulunci
".
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Adalci na sa'a guda ya fi ibadar shekaru saba'in na sallar dararensu da azumtar yininsu. Zalunci a hukumci na sa'a guda kuma ya fi tsanani da girma wajen Allah a kan sabon shekara sittin
".
Jabir bn Abdullah al-Ansari (r.a.) ya ce: 'Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda ya nemi yardar wani sarki da abin da yake fusata Allah, to ya fita daga addinin Allah
".
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda ya shugabanci mutum goma sannan bai yi adalci a tsakaninsu ba, zai zo ranar lahira hannayensa da kafafunsa da kansa na cikin ramin gatari
".
Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk mutumin da ya shugabanci wani al'amari na musulmi, sannan ya rufe kofa (ya ki sauraronsu) to yana cikin azabar Allah Mai Girma da Daukaka da la'anarSa har sai ya bude kofarsa ga mai wata bukata da mai (karar) wani zalunci, sun shigo
".
Kamar haka A'imma (a.s.) suke tarbiyyar mabiyansu da karkato da ra'ayin jama'a zuwa ga canji da gyara da shiga fagen siyasa ta hanyarta ta asali.
(2). Yankewa daga Azzalumai: Bayan shiryarwa da tarbiyya kan munin zalunci, Ahlulbaiti (a.s) sun kara da umurni da yanke hulda da azzalumai, kamar yadda ya zo cikin hadisi cewa:
"Duk wanda ya yi tafiya tare da azzalumai, alhali yana sane da cewa azzaluman ne, to hakika ya fice daga Musulunci" da kuma cewa: "Mai aikata zalunci da mai taimaka masa da mai yarda da shi dukkansu masu tarayya da juna ne".
Haka nan suke kira da yanke hulda da azzalumai da rashin taimaka masu. An ruwaito cikin hadisi cewa: "Idan ranar alkiyama ta zo mai kira zai yi kira: Ina azzalumai da mataimakansu; wanda ya shirya masu kurtun tawada ko ya daure musu wata jaka ko ya fere musu kan alkalami, ku tara su tare da azzalumai
".
Kyakkyawan misalin yankewa azzalumai shi ne abin da A'imma (a.s.) suka yi da matakan da suka dauka dangane da zalunci da azzaluman mahukuntan Umayyawa da Abbasiyawa a zamanin Imam Sajad, Imam Bakir, Imam Sadik, Imam Kazim, Imam Ridha
(*), Imam Jawad
(**), Imam Hadi da kuma Imam Hasan Askari (a.s.).
A wannan lokacin A'imma (a.s.) sun gamu da wahalhalu daban-daban daga mahukunta, kamar cutarwa da kora da sa ido da shiga kurkuku da matsi da tsoratarwa, za mu kawo kadan daga cikin irin wadannan abubuwa a cikin wannan littafi.
A matsayin misali na irin wannan yankewa, shi ne matsayin da Imam Sadik (a.s.) ya dauka dangane da halifan Abbasiyawa Abu Ja'afar Mansur wanda ya shahara da mugun hali da zubar da jini da zalunci ga zuriyar Imam Ali (a.s.). Malaman tarihi sun rubuta cewa, wata rana Mansur ya rubuta wasika zuwa ga Imam Sadik (a.s.) yana neman zama da shi don kokarin sanya shi cikin malaman hukuma. Sai Imam yaki duk kuwa da halin tsoratarwa da kaushin halin da mahukuntan suke nunawa.
Ga abin da Mansur ya rubuta: "Me zai hana ka ziyarce mu kamar yadda mutane suke ziyartarmu"?, sai Imam (a.s.) ya rubuta masa cewa: "Babu abin da muke tsoronka dominsa, babu wani abu daga sha'anin lahira a gare ka wanda zai sa mu kaunaci (saduwa da) kai dominsa. Ba ka kuma cikin wata ni'ima ballantana mu yi maka murna, ba ma kuma ganinsa a matsayin azaba ballantana mu yi maka jaje". Sai Mansur ya rubuto amsa ya ce: "Ka zauna da mu saboda ka yi mana nasiha". Sai Imam (a.s.) ya amsa masa da cewa:"Mai nufin samun duniya ba ya maka nasiha, wanda kuwa yake nufin lahira ba ya zama da kai
". Haka nan dai matsayar A'imma (a.s.) da raddinsu ya kasance ga mahukuntan da ba sa tsai da shari'a, ba su lizimtar ginshikanta.
To haka nan ma malaman fikihun mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suka bi tafarkin Imamansu wajen yanke hulda da azzaluman mahukunta ta hanyar fatawoyinsu masu haramta taimakawa azzalumai ko karbar aikin hukumominsu. Suna kawo wannan ne galibi a babin makasib wato hanyoyin neman abin masarufi. Bari mu kawo maganar Shahid Muhammad bn Jamal (*) Makki al-Amuli wanda aka fi sani da Shahidul Awwal (Allah Ya rahamshe shi) yayin da yake kawo sana'oi haramtattu cewa: "Da taimakon azzalumai cikin zalunci" (yana daga cikin haramtattun sana'oi), shi kuma mai sharhin littafin ya ce: "Kamar yi musu rubutu da kawo musu wanda suke zaluntarsa da dai makamantansu
".
Malaman sun hana karbar duk wani aiki a hukumar azzalumai sai dai da nufin yi wa Musulunci hidima da tunkude zalunci ga barin bayin Allah, ta yadda dai za a samu wani gyara ko wani amfani ga al'umma.
(3). Gwargwarmaya da abin da ya shafi amfani da karfi: Wajibcin umurni da aiki mai kyau da hana mummuna wani ginshiki ne wanda ya tabbatar da gwagwarmaya domin kawar da zalunci, kuma an lizimta da shi ga musulmi.
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Shugaban shahidai shi ne Hamza da kuma mutumin da ya mike ya umarci sarki azzalumi (da kyakkyawan aiki) ya hana shi (mummuna) sannan sarki ya kashe shi".
Duk wanda ya bibiyi tsarin rayuwar Ahlulbaiti (a.s) a fagen siyasa da sabawa zaluncin da suka yi, zai ga cewa hanya ce guda wajen sabawa zalunci da kira zuwa ga gyara da gwagwarmaya. Gwagwarmaya ta faro ne a zamanin mulkin Mu'awiyyah dan Abu Sufyan, yayin da ya dora dansa Yazid a kan wuyar al'ummar musulmi duk da cewa bai cancanci shugabanci ba kuma ya rasa dukkan sharuddansa. Wannan ta'asa ta janyo fasadi da kaucewar al'umma, abin da ya sanya Imam Husaini (a.s.) yin shelar jihadi. Imam (a.s.) ya zauna a Makka na tsawon wata hudu bayan barowarsa birnin Madina, daga bisani sai ya fuskanci kasar Iraki. Can a Karbala ne aka yi gumurzu tsakanin rundunar Yazid da jama'ar Imam Husaini (a.s.) 'yan kalilan, a can tsarkakken jini ya zuba, Imam (a.s.) ya yi shahada. Zubar da jinin Imam Husaini (a.s.) tare da Ahlulbaitinsa da kuma mabiyansa ya girgiza al'umma ya tashe ta daga barcin da take ciki. Wannan kuwa shi ne farkon tawaye wa azzaluman mahukunta masu fakewa da Musulunci don cimma burinsu da warware mubaya'ar jabu da shelar kawar da hukumcin bata-gari mai sabawa rukunan Musulunci. Wannan tawaye wa azzalumai shi ya yaye zanin malaman da suke kiran mutane zuwa kaskanci da mika kai bori ya hau, da gurbata ra'ayin ilahirin jama'a da karfafa cewa sai an lizimci mubaya'ar azzalumi an cika masa alkawari komin lalacewarsa. Wadannan muggan malamai dangin Bal'ama dan Ba'ura sun yi kunnen uwar shegu da fadar Manzon Allah (s.a.w.a.) ce wa: "Ba a karbar rantsuwar mai sabo", Da kuma fadinsa (s.a.w.a) cewa: "Babu biyayya ga halitta cikin sabon Mahalicci".
Suna yin biris da fadin Allah Ta'ala cewa: "Kuma kada ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku". (Surar Hud, 11:113).
Shi Shugaban shahidai, Imam Husaini bn Ali (a.s.) ya kaddamar da gwagwarmayarsa ne a shekara ta sittin da daya bayan hijira, kuma a wannan shekarar ne ya yi shahada a can yankin Karbala na kasar Iraki. Da wannan ne kuma ya rushe dukkan kiraye-kirayen muggan malamai na rauni gaban hukumomin zalunci da yarda da su. Hakika sautin shahada da jini ya rinjayi na kwadayi da kaskanci.
Imam Husaini (a.s.) ya bayyana wa mutane dalilan fitowarsa da tsarin da yake tafe bisansa da cewa:
"Ni ban fito domin girman kai ko alfahari ba, ba kuma domin barna a bayan kasa ko zalunci ba. Abin da kawai ya fito da ni shi ne neman gyara a cikin al'ummar kakana, Manzon Allah (s.a.w.a.). Ina nufin yin umurni da kyakkyawan aiki da hana mummuna, in kuma bi irin rayuwar kakana da babana
".
Sannan ya ayyana wa mutane siffofin shugaba wanda shi ne ja-gora mai jan ragamar musulmi, da wajibcin tsayuwa don gwagwarmayar sauya mai hukumci a yayin da ya karkace ya bar wadannan ginshikin. Ga abin da Imam Husaini (a.s.) ya rubuta wa mutanen Kufa:
"Ina rantsuwa da cewa ba wani ne shugaba ba face mai hukumcin da ya tsayar da adalci, mai riko da addinin gaskiya, mai tsare kansa bisa (umurnin) Zatin Allah
".
Daga cikin abin da ya rubuta wa manyan mutanen garin Basra kuwa, cewa ya yi: "Ni ina kiranku zuwa ga Littafin Allah da Sunnar AnnabiSa (s.a.w.a), domin an riga an kashe sunna an raya bidi'a. To idan kun saurari fadina kuka bi umurnina zan shiryar da ku tafarkin shiriya. Aminci ya tabbata a gare ku da rahamar Allah
".
Hakan nan Imam Husaini (a.s.) ya tabbatar wa al'umma yadda shari'a ta yi umarni da sabawa azzalumin shugaba, ya kuma yi shelar rukunan jihadi mai tsarki, domin sauya hukumcin azzalumai.
Bayan jihadin Imam Husaini (a.s.) mai albarka, Ahlulbaiti (a.s) sun taimaka wa yunkuri daban-daban da Alawiyyawa suka yi tsawon sama da karni biyu, a fadin kasashen musulmi.
Zaid bn Ali bn Husaini, wato dan Imam Zainul Abidin kuma jikan Imam Husaini (a.s.) ya yi yunkuri a shekara ta 121 bayan hijira. Wannan kuwa ya faru ne a zamanin Imam Sadik (a.s.) wanda kuwa ya goyi bayansa ya kuma yi juyayin shahadar Zaid (*).
Fudhail Rassan ya ce: "Na shigo wajen Abu Abdullah (a.s.) bayan an kashe Zaid bn Ali, sai aka shigar da ni cikin uwar daki, sai ya ce da ni: "Ya kai Fudhail, an kashe baffana? Sai na ce 'fansar ka nake (e an yi haka), sai ya ce:"Allah Ya jikansa, lallai shi ya kasance mumini mai sani, mai ilmi, mai yawan gaskiya. Lallai da ya yi nasara da ya cika alkawari. Lallai da ya sami mulki da ya san inda zai sanya shi
". Haka aka yi ta samun taimakawar Ahlulbaiti (a.s) wa masu yunkurin kawo gyara cikin Alawiyyawa.
Daya daga cikin bayyanannen misalin irin wannan mataki na siyasa kuwa, shi ne matakin da Imam Kazim (a.s.) ya nuna dangane da yunkurin da Husaini bn Ali ya yi a shekara ta 169 a birnin Madina, yunkurin da aka fi sani da Yunkurin Fakh
(*) wanda aka yi shi a watan Zulkida na wannan shekarar.
Duk da cewa Imam Kazim (a.s.) ya ga alamun rashin nasarar yunkurin a wancan lokacin, babu shakka magan-ganun da ya yi sun nuna cewa yana goyon bayan ra'ayin jihadi. Ga abin da ya fadi wa shi Husainin yayin da ya ga yayi niyyar fita wannan arangama:
"Za a kashe ka, saboda haka ka tsananta yaki domin mutanen fasikai ne, suna bayyana imani suna boye munafunci da shirka. Lalle ne mu daga Allah muke kuma wajenSa za mu koma! Ga Allah nake neman ladan rashinku
".
Yayin da Husain ya yi shahada aka kawo kawukan wadanda suka yi shahada tare da shi wajen mahukuntan Abbasiyawa, sai aka tambayi Imam Kazim cewa wannan kan Husaini ne? sai ya ce:
"E, lalle ne mu ga Allah muke, kuma lalle ne mu zuwa gare Shi za mu koma. Na rantse da Allah, ya mutu musulmi ne salihi, mai yawan azumi, mai umurni da kyakkyawa, mai kuma hana mummuna, babu tamkarsa cikin mutanen gidansa
".
Shi dai Husain ya kasance ne yana kiran mutane da cewa: "Ina kiranku ne zuwa ga abin da Alu Muhammadu suka yarda da shi, da aiki da Littafin Allah da sunnar Annabi (s.a.w.a) a tsakaninku, da kuma tsayar da adalci a tsakanin jama'a
". Kiran da Husain ya yi, kira ne zuwa ga biyayya ga mutumin da ya cancanci shugabanci, wanda yake daga Alu Muhammadu, kuma shi ne Imam Kazim (a.s.), kamar yadda Zaid ya yi nufin mai da shugabanci ga Imam Sadik (a.s.) da ya yi nasara. Hakika halifan Abbasiyawa ya fahimci goyon bayan da Imam Kazim (a.s.) yake yi wa yunkurin Husain a yakin Fakh.
Allamah Majilisi ya ruwaito cewa: "Sai ya (halifan Abbasiyawa) ci gaba da zagin Dalibiyawa (jikokin Ali bn Abi Talib) har ya ambaci Musa bn Ja'afar (a.s.), sai ya zage shi yana cewa: 'Wallahi Husaini bai yunkura ba sai da umarninsa (Musa bn Ja'afar), ba abin da ya bi face abin da yake so domin shi (Imam Kazim) ne ma'abucin wasiyya a cikin mutanen wannan gidan. Idan na bar shi, Allah Ya kashe ni
".
Imam Jawad, jikan Imam Kazim (a.s.) shi ma ya bayyana tasa matsayar dangane da masu gwagwarmar, inda ya ce: "Bayan Dif (Karbala), ba a cutar da mu kamar cutarwar Fakh ba
".
Akwai misalai masu yawa na yunkuri da goyon bayan Ahlulbaiti (a.s) gare su, har wannan (yunkurin) ya zama tafarki da salo na aikin siyasa wanda yake da goyon bayan shari'a.
(4). Gwagwarmaya ta Siyasa: Wannan yana da muhimmancin gaske a rayuwar siyasar al'umma a duk lokacin da azzalumin shugaba ya bayyana ba ya gudanar da hukumce-hukumcen Allah Ta'ala, ba ya kuma tsaifa adalci a tsakanin mutane. Kowane Imami na Ahlulbaiti (a.s) ya shugabanci al'umma a fagen siyasa a zamaninsa, kuma ya kasance shi ne alamar bijirewa azzalumai a zukatan jama'ar musulmi. Wannan kuwa shi ne ya bai wa yunkure-yunkuren da aka yi siffar dacewa da shari'a. Halifofin Banu Umayya da Banu Abbas wadanda tarihi ya yi wa shaidar rashin lizimtar addini da barin adalci sun san irin kimar Ahlulbaiti (a.s) a zukatan musulmi, saboda haka suka bi hanyoyi daban-daban domin su nisantar da kaunar Ahlulbaiti (a.s) daga mutane, hanyoyi kamar su tsoratarwa da kai su kurkuku da kisa da rashawa da mukamai da sauransu. A matsayin misali, Mu'awiyya ya yi tawaye ga Imam Ali (a.s.) ya yake shi duk da cewa shi ne halaltaccen halifa.
Baya ga haka kuma, bai tsaya ba sai da ya yaki Imam Hasan (a.s.) ya yi tawaye wa halifancinsa, ya kashe shi da guba a shekara ta hamsin, bayan hijira. Yazid dan Mu'awiyya, shi ma ya dauki mataki irin na ubansa akan Imam Husain (a.s.), ya kashe shi tare da mutanen gidansa, ya ribaci zuriyar Manzon Allah (s.a.w.a.) yayin da Imam Husaini (a.s.) ya jagoranci yunkurin bijirewa hukumar Banu Umayya ta zalunci da aka tilasta ta a kan al'umman musulmi.
Bayan Imam Husaini (a.s.) ya yi shahada, musulmi sun karkata hankalinsu ga Imam Ali bn Husain, Zainul Abidin (a.s.), suna ganinsa a matsayin wata alama kana kuma makoma gare su, don haka ne masu yunkuri
Gwagwarmaya suke neman izininsa. Don haka ne ma a zamaninsa an sami masu jihadi domin kare Ahlulbaiti (a.s) da yawa, kamar yunkurin Madina da Makka da na Mukhtar Al-Thakafi da na Tawwabun, dukkansu suna yaki domin daukar fansa kan wadanda suka kashe Imam Husaini (a.s.). A wancan lokacin mutane suna ganin Imam Zainul Abidin a matsayin kololuwar bijirewa azzalumai duk da cewa bai motsa ba. Matsayin da ya dauka kan Yazid bn Mu'awiyya da Marwan bn Hakam da Abdul Malik bn Marwan da sauran azzaluman mahukunta, matsayi ne na mai bijirewa a asirce da taimakon masu yunkuri ba tare da shelar hakan ba. har ma Imam (a.s.) ya roki rahamar Allah ga Mukhtar, wanda ya dauki fansa kan wadanda suka kashe Imam Husaini (a.s.) ya kuma yaba da jihadin Mukhtar. Sannan kuma Imam (a.s.) ya yi amfani da makamin addu'a
(*) mai bayyana irin ra'ayinsa na siyasa da akida, mai sabawa da ra'ayin su Yazid.
Imam Bakir (a.s.) dan Imam Zainul Abidin (a.s.) shi ma ya nuna matsayin da yake kai na bijirewar siyasa daga Banu Umayya. Imam ya sha wahala kwarai a hannunsu, musamman ma Hisham bn Abdul Malik mai bayyana kiyayya da gaba ga Alawiyyawa. A zamaninsa ne Zaid bn Ali dan uwan Imam Bakir (a.s.) ya fito jihadi.
Shi dai wannan halifa na Banu Umayya ya tabbatar cewa tushen wannan yunkuri na Zaid daga Imam Bakir da dansa Ja'afar Sadik (a.s.) yake. Don haka sai ya kira su daga Madina zuwa ga helkwatarsa da ke Sham, yayin da Imam Bakir (a.s.) ya shiga fadar Hisham sai ya yi sallama yana nuni zuwa ga mahalarta majalisar, amma bai yi gaisuwar sarauta ga halifan ba. Sai Imam ya zauna ba tare da da wani izinin sarki ba, hakan ya kara wa Hisham kiyayyarsa ga Imam har ma ya kama sukansa da cewa:
"Ya Muhammad bn Ali, ko yaushe sai an sami wani mutum daga cikinku yana raba kan musulmi, da kiran jama'a don su bi shi, domin wauta da karancin ilmi".
Sai Hisham ya ci gaba da suka, jama'ar da ke fada su ma suka fara sukar Imam din bayan Hisham ya yi shiru. Da ganin wannan ka san cewa an umurce su da hakan ne kafin ma Imam din ya shigo tare da dansa, Imam Sadik (a.s.). Ganin haka ke da wuya, sai Imam Bakir (a.s.) ya mike tsakiyar majalisar yana mai raddi ga sarki da cewa:
"Ya ku mutane! Ina kuke zuwa ne? Ina aka nufa da ku ne? Da mu Allah Ya shiryar da farkonku, da mu kuma Zai cika (shiryar) da na karshenku. Idan kuna da mulki abin gaggautarwa, to mu muna da mulki da aka jikirta, kuma babu wani mulki bayan namu, domin mu ne masu mulkin karshe".
Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Kuma kyakkyawan karshe tana tabbata ga masu tsoron Allah". (Surar A'araf, 7: 128). Jin haka, ya sa Hisham ya tsare shi
.
To a cikin kurkukun ma Imam Bakir (a.s.) bai yi shiru ba, ya wayar da kan fursunoni kan batutuwan siyasa da jihadi har fursunonin suka sami tasirin wa'azinsa, inda suka tayar da hargowa a cikin kurkukun. Ganin haka, sai shugaban kurkukun ya isar da lamarin zuwa ga Hisham, inda shi kuma ya yi umarni da a fitar da Imam (a.s.) daga kurkukun a mai da shi birnin Madina, a hannun wani dan aiken sarki
.
Muhammad bn Jarir Tabari ya rubuta cewa dalilin da ya sa aka mai da Imam Bakir (a.s.) zuwa Madina shi ne bazuwar tasirinsa kan tunanin mutanen Sham sakamakon wata muhawara da ta gudana tsakaninsa da wani shugaban kiristoci
.
A wata muhawara da ta gudana tsakanin Hisham bn Abdul Malik da Zaid, a lokacin da labarin yunkurin Zaid din ya isa kunnen Hisham, Hisham ya ce da Zaid: "Na sami labarin kana ambaton halifanci kuma kana burinsa, alhali kai ba ka cikin mazowansa, kuma kai dan baiwa ne".
Sai Zaid ya mayar masa da martani da cewa, Annabi Isma'il dan baiwa ne kuma Allah Ta'ala Ya ba shi annabta. Sannan Hisham ya dora ambaton Imam (a.s.) da zagi, yana mai tambayan Zaid da cewa:
"Dan'uwanka Bakara kuwa...", sai Zaid ya amsa masa da cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ambace shi da Al-Bakir
(*) kai kuma ka kira shi da Bakara (wato saniya), lalle sabaninka da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi yawa kuma za ka saba da shi a ranar lahira kamar yadda ka saba da shi a nan duniya, domin Annabi (s.a.w.a) zai shiga aljanna kai kuwa za ka shiga wuta". To wannan shi ne matakin da Imam Bakir (a.s.) ya dauka da kuma yunkurinsa na siyasa, har lokacin da ya yi shahada.
To daga nan sai zamanin dansa Imam Ja'afar Sadik (a.s.), a wannan lokaci na Imam Sadik (a.s.) kuwa bala'i ya yawaita kan al'ummar Annabi (s.a.w.a), ya kuma fi tsanani kan Alayensa (s.a.w.a). Imam Sadik (a.s.) ya kasance shi ne jagoran bijirewa azzalumai ta hanyar siyasa duk da yake bai yi magana bayyananniya kan masu iko ba. Masu yunkuri suna neman shawararsa da goyon bayansa, kai har da neman ya karbi jagorancin harkar, kamar yadda Abu Muslim Khorasani ya bukata yayin da ya mika mubaya'arsa ga Imam. Imam Sadik (a.s.) ya ki karbar wannan mubaya'a saboda rashin cikar sharudda da kasantuwar yanayi bai dace ba, kamar dai yadda ya yi lokacin yunkurin Zaid a zamanin Hisham bn Abdul Malik Ba'umayye.
Abul Abbas Saffah ya yi kokarin kashe Imam domin saninsa da mukaminsa na jagoranci da goyon bayansa ga bijirewa mahukunta. To amma Allah Ya kare shi daga sharrinsa, duk kuwa da cewa ya taba kiran Imam din daga Madina zuwa garin Hira da ke kasar Iraki, inda ya tsananta masa da kuma sanya shi karkashin 'yan leken asiri.
Yayin da Abu Ja'afar Mansur ya gaji Al-Saffah, shi ma ya ji tsoron matsayin Imam Sadik (a.s.) kamar yadda magabatansa suka ji, sau da yawa ya kan kira Imam (a.s.) daga Madina zuwa Iraki.
Ga yadda yake siffanta karfin Imam a fagen siyasa da tasirinsa kan masu gwagwarmaya, inda ya ke cewa: "Wannan bakin cikin (yana nufin Imam Sadik) da rike makoshin halifofi, korarsa ba ta halalta, kisan sa ba ya halalta. Ba don mun hadu da shi a bishiya mai kyakkyawan tushe, mai rassan da suka gabata, mai dadadan 'ya'ya, an kuma albarkaci zuriyarta aka tsarkake ta cikin Littattafai ba, da an sanya shi cikin mummunan karshe, saboda labarin da muka samu na tsananin aibantamu da mummunan magana da yake fada game da mu
". Wannan shi ne matsayin Imam Sadik (a.s.) da aikin da ya yi na bijirewa azzaluman mahukunta, da goyon bayan masu yunkurin kawo gyara.
Daga nan sai zamanin Imam Musa bn Ja'afar Kazim (a.s), dan Imam Sadik (a.s.), a lokacinsa cutar da musulmi da karkata addini da kwadaitar da mutane da dukiya sun tsananta a hannun Abbasiyawa. Don haka ne Imam (a.s.) ya kasance jogora wajen gyaran al'amarin Musulunci.
An sanya Imam (a.s.) karkashin leken asiri a zamanin Mansur wanda shi ya kai matuka wajen zaluntar Alawiyyawa da kwace dukiyoyinsu, da gina turakun gadoji da kadarkai da soraye a kansu da ransu, da azabtar da su cikin kurkuku.
To amma bayan da Muhammad Al-Mahdi ya gaji sarautar Abbasiyyawa sai tsoransa ga Imam Kazim ya yi tsanani, don haka sai ya kirayi Imam (a.s.) daga Madina zuwa Bagadaza domin ya hukunta shi. Al-Mahdi ya sa aka rufe Imam Kazim (a.s.) a kurkuku har zuwa wata rana da halifan ya ga Imam Ali bn Abi Talib (a.s.) a mafarko yana ce da shi: "To, shin, kuna fatan idan kun juya za ku yi barna a cikin kasa, kuma ku yanyanke zumuntarku?" (Surar Muhammadu, 47: 22). Wannan sai ya tsoratar da Mahdi ya fitar da Imam Kazim (a.s.) daga kurkuku.
A mulkin Al-Hadi, sarkin Abbasiyawa, ne bala'i ya tsananta kan Imam (a.s.) da kuma Alu Ali (a.s.). Ya ci gaba da korarsu da kashe su da neman batar da su gaba daya musamman ma bayan yunkurin Husain bn Ali wanda aka fi sani da waki'ar Fakh. Imam Kazim (a.s.) ya gamu da tsanantarwa da matsarwa har sai da ta kai Al-Hadi din ya hukumta Imam (a.s.) da hukumcin kisa ya kuma tasanma aiwatar da hakan. Malaman tarihi sun ruwaito cewa alkali Abu Yusuf almajirin Imam Abu Hanifa shi ne ya shiga tsakanin Al-Hadi da wannan kuduri da ya dauka na kashe Imam Kazim (a.s.), don Al-Hadin ya zaku kan kashe Imam (a.s.) har cewa ya yi: "Allah ya kashe ni idan na yi wa Musa ibn Ja'afar afuwa".
Daga nan sai Al-Hadi ya sanya Imam Kazim (a.s.) a kurkuku da hana shi damar gudanar da aikinsa na ilmantarwa da jagoranci a bayyane. Amma mutuwa ba ta bar shi ya aikata mummunan nufinsa, don kuwa ta kawo karshen wannan azzalumi jabberi.
Daga nan sai lokacin Haruna Rashid wanda aka sami jayayya mai tsananin gaske tsakaninsa da Imam Kazim (a.s.). Haruna Rashid ya yi kiran Imam da ya taho daga birnin Madina zuwa Iraki, inda ya ci gaba da tozarta shi da sanya shi a kurkuku da azabtarwa nau'i daban-daban, wadanda suka hada da daure shi da karfe yana daukansa daga wannan kurkukun zuwa wancan. Imam (a.s.) ya zauna a kurkuku tsawon shekaru, daga karshe Haruna Rashid ya ci da shi guba ta hannun shugaban dogarawan-sa mai suna Al-Sandi bn Shahik. Imam (a.s.) ya yi shaha-da ne a ranar 25 ga watan Rajab a shekara ta 183 bayan hijira.
Daga nan sai zamanin Imam Ridha, Aliyu bn Musa bn Ja'afar (a.s.), wanda shugabancinsa na siyasa ya wajabtawa Abbasiyawa la'akari da shi a sakamakon karfin alkadarin Imam (a.s.) da kaunar al'umma gare shi ga kuma tsanantar bijirewa ga Abbasiyawa. Wannan yanayi ya tilastawa halifan Abbasiyawa Ma'amun sanya Imam (a.s.) a matsayin magajinsa. Imam Ridha (a.s.) ya karbi wannan matsayi ba don sonsa ba, kana kuma da sharadin cewa shi ba zai shiga harkokin shugabanci ba, sannan idan Ma'amun ya mutu, halifanci zai koma hannunsa. To amma Imam Ridha (a.s.) ya yi shahada yayin da Ma'amun ya ba shi guba a shekara ta dari biyu da uku bayan hijira.
To bayan shahadar Imam Ridha (a.s.), wanda ya karbi jagoranci al'umma da lamarin Imamanci shi ne dansa Imam Muhammad Jawad (a.s.) wanda ya yi zamani da Ma'amun na dan lokaci. Ma'amun ya yi mu'amala da shi da girmamawa a munafunce, ya aurar masa da 'yarsa Ummul Fadhl domin ya sami soyayyar al'umma, yayi hakan ne kuwa domin ya juya hankulan mutane ya karkata ra'ayin masu gaba da shi, wadanda suke ganin Imam (a.s.) a matsayin jagora. Sai dai fa Ma'amun bai tsinana komai ba domin Imam Jawad (a.s.) ya bar Bagadaza ya koma birnin Kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.) saboda ci gaba da aikinsa na ilmantarwa da jagorancin al'umma a can.
To bayan da Ma'amun ya mutu sai dansa Al-Mutasim ya hau karagar mulkin Abbasiyawa, sai dai kuma shi Al-Mutasim bai jima a kan mulkin ba, to amma dai shi ma ya kasance yana jin tsoron Imam Jawad (a.s.) da kuma hadarin zamansa a Madina. To shi ma Al-Mutasim bai yi wata-wata ba sai ya kama tafarkin iyayensa yayin da ya dauko Imam daga Madina ya kawo shi helkwatarsa domin ya sanya ido a kansa. Marubuta tarihi sun ce Imam Jawad (a.s.) ya yi shahada ne a hannun Mutasim ta hanyar guban da ya sa masa cikin abinci a shekarar da ya kawo shi Bagadaza a lokacin kuwa hijira tana da shekara dari biyu da ashirin da biyar.
To bayan shahadar Imam Jawad (a.s.) dansa Imam Ali Hadi shi ne ya gaji jagorancin al'umma da Imamanci daga mahaifin nasa. A zamanin Mutawakkil Abbasi ne Imam Hadi (a.s.) ya fuskanci keta da cutarwar Abbasiya-wa. Mutawakkil da ma sananne ne da son wasa da kuma gaba da Alayen Manzon Allah (s.a.w.a.) da kashe su da korar su da yanke abincinsu da hana mutane taimakonsu. Imam Hadi (a.s.) ya kasance yana tsorata halifa Mutawakkil saboda haka sai ya dauko shi daga Madina ya kai shi garin Samarra ya sa ido sosai a kansa, ya kuma tilasta masa zama a can. To lokacin da al'amurra suka yi zafi wa Mutawakkil, sai ya fara barazanar kisa ga Imam Hadi (a.s.) baya ga daure shi da ya sha yi. A wasu lokuta ya kan sa a binciki gidan Imam Hadi (a.s.) da kai hari wa gidan, bugu da kari kan tsananta sanya ido a kansa saboda tsoron irin tasirin da Imam (a.s.) yake da shi a idon al'umma.
Marubuta tarihi sun ambaci dalilan da suka sa Mutawakkil ya ta da Imam Hadi (a.s.) daga Madina. Sibt Al-Jawziyya ya ce: "Malaman tarihi sun ce: Ya fito da shi daga Madinar Manzon Allah (s.a.w.a.) zuwa Bagadaza ne don yana tsananin kin Aliyu da zuriyarsa sai kuma ya sami labarin irin matsayin Aliyu Hadi a Madina da karkatar mutane zuwa gare shi. Wannan ya sa shi tsoronsa
".
Bayan shahadar Imam Hadi (a.s.) garin Samarra a shekara ta 254 bayan hijira, sai dansa Imam Abu Muhammad Hasan Askari (a.s.) ya kasance Imami mai kula da harkar al'umma da kuma shiryar da su. To shi ma dai matsayinsa kan Abbasiyawa tamkar na iyayensa ne, wajen fito-na-fito a fagen siyasa. To shi ma dai mahu-kumtan ba su bar shi don kuwa sun cutar da shi kamar yadda suka cutar da mahaifansa. Al-Muhtadi bn Al-Wasik sarkin Abbasiyawa ya sanya shi a kurkuku a garin Samarra, inda ya mika shi ga hannun gandurobobin kurkukun wadanda suka shahara da mugun hali da zalunci don azabtar da shi, amma Imam (a.s.) ya yi tasiri kansu har suka shiryu suka zamo mutanen kwarai.
Malaman tarihi sun kiyaye abubuwan da suka sami Imam Hasan Askari (a.s.) na matsanancin bala'i, kamar abin da Ahmad bn Muhammad ya ruwaito, inda ya ce:
"Yayin da Al-Muhtadi da fara kashe magoya bayan Ahlulbaiti (a.s) sai na rubuta wa Abu Muhammad Hasan Askari (a.s.) na ce masa: Ya shugabana, godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya shagaltar da shi (Muhtadi) daga barinka. Hakika na sami labari cewa yana maka barazana da cewa: "Wallahi sai na kore su daga duk sababbin kasashe", sai Abu Muhammad (a.s.) ya rubuta da hannunsa cewa: "Wannan shi zai takaita rayuwarsa
".
An ruwaito cewa, Imam Askari (a.s.) ya kasance cikin kurkuku a zamanin Al-Mutamad har lokacin da ya kira shi don warware wata matsala da ta faru tsakanin musulmi da wani malamin Nasara, a kan shayarwa (ruwan sama). Sai Imam (a.s.) ya warware ta, to a saboda haka Al-Mutamad ya fito da shi daga kurkukun kuma ya nemi a saki mabiyansa da ke tare da shi a kurkuku, hakan kuwa aka yi, wato a ka sake su.
Wannan shi ne kadan daga tarihin Ahlulbaiti (a.s) a fagen siyasa da fito-na-fiton da suka yi da hukumomin zalunci na lokacinsu wadanda suka doru a kan al'umma. Idan an duba da kyau za a ga cewa, silsilar Imamai goma sha daya mai albarka ta Ahlulbaiti (a.s) ta kasance wani fage ne na jagorantar al'umma da kuma shiryar da su. Don kuwa kowane Imami za a ga shi ne jagorar al'um-mar da ya kasance a cikinta, wanda kuma ya fi kowa ilmi da sanin ya kamata. Irin wannan tsari ba zai yiyu a same shi ba sai da shiri gabatacce daga Allah Ta'ala. Kuma babu makawa wannan bibiya ta jagorancin Ahlulbaiti (a.s) yana sanar da mu mukaminsu da fagensu na shugabancin akida da siyasa a rayuwar wannan al'umma.