Ahlul Baiti

Ahlul Baiti0%

Ahlul Baiti Mawallafi:
: Mu'assasar Al-Balagh
: Ammar Kumo
Gungu: Kala-kala

  • Farawa
  • Na Baya
  • 9 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 16489 / Gurzawa: 3792
Girma Girma Girma
Ahlul Baiti

Ahlul Baiti

Mawallafi:
Hausa

Abin lura dangane da wannan littafin

Wanda ya tsara ya buga kuma ya yada

Muassasar Hasanain don yada al’adun Musulunci

Da fatan Allah Ta'ala ya datar da mu wajen kara gyara shi da fitar da shi bisa mafi kyawun sura

www.alhassanain.org/hausa

AHLUL BAITI (ZURIYAR MANZON ALLAH)

Mukaminsu Halinsu Da Tafarkinsu

Wallafar: Mu'assasar Al-Balagh

Fassarar: Ammar Kumo

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI

Ahlul Baiti a Kur’ani da Hadisai:

“Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku Ahlul Baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa”

“Ni na bar muku nauyaya biyu; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su”.

Gabatarwar Mu'assasa

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ni mai bari muku nauyaya biyu ne tare da ku, littafin Allah da dangina, mutanen gidana (ahlulbaiti) wadanda in kun yi riko da su ba za ku taba bata ba a bayana har abada, kuma lalle ne su biyun ba za su rabu da juna ba har su riske ni a bakin tafki".

Ahlulbaiti (a.s) makaranta ce mai haske kuma taurari ne a sararin samaniyar addinin Musulunci madaukaki. Su ne ja-goranci cikakke mai koyi da Manzon Allah (s.a.w.a.), sun sha daga ilminsa a gidansa suka tashi, sannan suka rayu bisa tafarkinsa. Suna masu kira zuwa ga Littafin Allah da kuma riko da sunnar AnnabinSa (s.a.w.a). Suna nuna misalai madaukaka ta hanyar halayensu, suna kira zuwa ga gaskiya, ba sa karkace mata ko da kamar dan yatsa. Kamar yadda hadisin Manzon tsira ya bayyana mana su (Ahlulbaiti) tagwaye ne na Alkur'ani mai girma, ba sa rabuwa domin su ne hakikanin tamka na Alkur'ani da duk abin da yake tattare da shi na ilminsa da tarbiyyarsa. Domin haka Alkur'ani ya ambace su a sarari:

"...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen Babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" (Surar Ahzab, 33:33)

Domin yawan ayoyin da suka sauka game da Ahlulbaiti (a.s) da kuma hadisai bayyanannu wadanda aka yi furuci da su, lallai Ahlulbaiti (a.s) sun zama abin kauna ga zukatan musulmi na kasashe da zamunna daban-daban, suna kwarara zuwa gare su domin su sha daga tabkin ilminsu kuma su nemi karuwa daga hasken masaniyyarsu.

Duk wanda ya kyautata karatun tarihin Ahlulbaiti (a.s) da aikin da suka yi na ilmi, zai san rawar da suka taka, wacce ita ce ta kan gaba, zai kuma san aiki mai girma da suka yi. Lallai sun yi matukar dagewa wajen kiyaye tsarkakar shari'a da kuma tsare asalin akidar Musulunci har ma suka sadaukar da kansu da yin jihadi domin tabbatar da ka'idojin nan madaukaka a aikace da ja-gorancin al'umma bisa shiriyar wadannan ka'idojin. A kullum tarihin Ahlulbaiti (a.s) madaukaka yana bayyana a matsayin rayayyiyar baiwa wadda take da tasiri ga tunanin al'umma da kiyayewarta, tana wadatar da rayuwarta tana kuma daukaka wayewarta. Babu shakka, Ahlulbaiti (a.s) su ne kudubin al'umma, su ne rumfa matattara mai hada kan al'umma don gyara.

A cikin wannan matakaicin littafin, mun yi kokarin bayyana sashin abubuwan da rayuwar Ahlulbaiti (a.s) ya kunsa da kuma abin da ya ta'allaka da martabarsu da rawar da suka taka a tarihi. Game da gabatar da wannan littafin, muna kwadaitar da 'yan'uwa musulmi da su samu fa'idantuwa da shiryarwa ta Ahlulbaiti (a.s) da aiki da ita da komawa wajen wannan ja-gaban da kuma koyi da shi da tsayawa sahu guda don fuskantar 'yan rahoton nan masu kokarin raba kan musulmi da wargaza hadin kansu, a dai-dai lokacin da al'ummarmu ta Musulunci take shiga gumurzu mai tsanani tsakaninta da 'yan mulkin mallaka da 'yan gurguzu da yahudawan sahayoniyya, wannan gumurzun kuwa sakamako ne na tabbatar da sakon Musulunci da kuma (kokarin) rayuwa karkashin inuwar adalcin Ubangiji.

Muna kuma kira ga al'ummar musulmi da su fuskantar da dukkan karfinsu wajen kira zuwa ga Musulunci da kare tsarkakan abubuwansa da tauye damar wadanda suka saba shuka sabani da watsa gubar banga-ranci tsakanin al'ummar musulmi.

Ya ku al'ummar Annabi Muhammadu mai girma! Ya masoya Ahlulbaiti! Ya zama wajibi a gare ku da ku hada kai da kuma karfinku waje guda, domin kuwa wannan al'umma, al'umma ce guda, kuma daukakarku da kara-marku ba sa tabbata sai da riko da sakon Musulunci da kuma aiki da Littafin Allah da Sunnar AnnabinSa (s.a.w.a). "Kuma ka ce: ku yi aiki, sa'an nan Allah Zai ga aikinku da ManzonSa da kuma muminai". (Surar Tauba, 9:105)

Mu'assasar

Iran

Gabatarwa

Ahlulbaiti (a.s.) suna ne mai haskakawa, kuma daukaka ce madawwamiya, sannan suna ne da yake abin kauna ne ga duk rai mai kaunar Manzon Allah (s.a.w.a.) kuma ya yi imani da shi, kuma yake rayuwa bisa shiriyarsa (s.a.w.a). Hakika musulmi sun san wannan madaukakin suna cikin tarihi da kuma cikin martabar nan da take rataye da Alkur'ani mai girma, tun lokacin da Alkur'anin ya yi furuci da wannan sunan mai albarka, kuma ya sanyawa wannan tauraruwan (Ahlulbaiti) lakabin da babu irinsa a duniyar dan Adam:

"...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" (Surar Ahzab, 33:33)

Da saukar wannan aya mai albarka wani tafarki ya ayyana a matsayin wani abin dogaro da mafuskanta a rayuwar Musulunci. Alkur'ani ya juya fuskoki zuwa ga wannan tafarki tare da tabbatar da dukkan haske a bisa wannan a kan gaba wajen ja-goranci. Har ila yau ya bayyana rawar da Ahlulbaiti (a.s) za su taka a rayuwar al'ummar musulmi, ya kuma kebance su da nufin tsarkakewa, abin karfafawa daga Gwani, Masani.

Lalle wannan aukuwa mai girma tana da wata kebantacciyar ma'ana a rayuwar al'umma da gina tarihinta da wayewarta. Wannan ma'ana kuwa dukkan masu bincike da tahkikin Musulunci da kuma fagen rayuwar siyasar wannan al'umma sun san da ita.

Hakika wadannan ayoyin sun ayyana wata cibiyar harkar tarihi bayan Manzon Allah (s.a.w.a.), harkar da ta dace da al'ada da tsarin hujjar da Musulunci ke dogara da shi. Wannan ya biyo bayan baiwar da Allah Ya yi wa tatattun nan masu albarka (Ahlulbaiti), baiwa ta tsarka-kewa daga zunubai da sabo da kuma laifi. Hakika Alkur'ani mai girma ya tabbatar musu da mafificiyar darajar falala da kuma mafi girman martabobin cancanta, da'a da shugabanci a rayuwa ta Musulunci wacce falsafarta a rayuwa ita ce:

"Lalle mafificinku daraja a wurin Allah shi ne wanda yake mafificinku a takawa". (Surar Hujurat, 349:13)

Babu shakka duk wanda ya bibiyi Alkur'ani mai girma da sunnar Annabi (s.a.w.a) tsarkakkiya zai samu cewa mutanen gidan Annabi mai daraja (s.a.w.a) suna da matsayi kebantacce da muhalli mabayyani. Za a ga cewa shugabannin wannan al'umma da malamanta da masu fassara da masu ruwaya da ma'abuta tarihi da malaman fikihu da masu yawan ibada duk suna ba da labarin wannan matsayi na Ahlulbaiti (a.s) ta dukkan fuskoki da hanyoyi. Lallai littattafan hadisi, tarihi, tafsiri da na adabi da wake da darajoji wadanda musulmi daga mazhabobi da hanyoyin ilmi daban-daban suka wallafa, sun bayyana kebantaccen matsayin da muhalli muhimmi na Ahlulbaiti (a.s). Wadannan littattafai suna magana a kan daukakar wannan itaciya mai albarka. Ana auna imanin mumini ne da kaunar Annabi (s.a.w.a) da Ahlubaitinsa da rige-rigen sanar da al'umma darajojin Alayen Manzo masu daraja da nutsar da kaunarsu cikin rayuka, da bayyana gajin hakuri da jin ciwon halayyar wadanda suka yi gaba da mutanen gidan Annabi mai daraja, kuma suka cutar da su da ababen kunya da kuma bala'u.

Lallai mutanen wannan gida tamkar tauraruwa ce wacce babu kamarta, domin ilmin da suke dauke da shi da kuma takawa da halayen kwarai da darajoji madau-kaka da kare Musulunci da ilminsu da kuma daukar takobi da yaki da zalunci da keta haddi. Domin haka ne musulmi suka dace a kan cewa babu wani daga cikin wannan al'ummar da ya mallaki mukami da daukaka da daraja irin wanda Allah Ya kebance Ahlulbaiti da su…su kadai Allah Ya kebance da tsarkakewa daga dauda da zunubi:

"...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa"

Kuma su kadai ne Allah Ya kebance da wajabta kaunarsu a kan wannan al'ummar Ya kuma sanya kaunar ta su wani hakki na Annabi (s.a.w.a) a kan al'umma:

"...Ka ce: "Ban tambayar ku wata lada a kansa, face dai soyayya ga makusanta...". (Surar Shura, 42:23)

Kuma su kadai ne Allah Madaukakin Sarki Ya wajabta yi musu salati a cikin salloli biyar, Yana gwama ambatonsu da ambaton ManzonSa (s.a.w.a):

"Lalle Allah da Mala'ikunSa suna yin salati wa Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi". (Surar Ahzab, 33:56)

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya riga ya koyawa al'um-marsa yadda za ta yi salati a gare shi da alayensa yayin da suka tambaye shi: Ya ya za mu yi salati a gare ka Ya Rasulallah? Sai ya ce da su:

"Ku ce: Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu da Alayen Muhammadu kamar yadda Ka yi salati ga Ibrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai ne Abin godiya, Mai girma"

To babu wanda yake da wadannan darajoji da siffofi cikin wanna al'umma face su. Wannan shi ya sanar da mu daukakar Ahlulbaiti (a.s) da matsayinsu, da wajibcin kaunarsu da koyi da su da kuma tafiya bisa turbarsu. Ba don kome ne Alkur'ani ya jaddada a kan mutanen wannan gida, ya kuma bayyana matsayi da mukaminsu ba, sai domin a yi koyi da su bayan Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma riko da sonsu da karbar (dukkan ilmi da shiriya) daga gare su.

Babu abin da yasa Alkur'ani ya sanar mana da Ahlulbaiti (a.s) ta hanyar da ya nuna mana su face domin wasu dalilai na akida da abin da ya danganci sakon Musulunci kaco-kam, dalilan da suke sa dukkan wani musulmi ya dora tunani mai zurfi da lura da kuma kokarin riskar da kwakwalwarsa hakikanin wannan jama'a (Ahlulbaiti) da take a kan gaba wajen karbar sako. Wannan jama'a kuwa ita ce Allah Ya yi wa baiwar matsayi na shugabanci a cikin al'umma, bayan Alkur'ani da Manzo (s.a.w.a) sun yi masu wannan gabatarwa. A nan gaba za mu bijiro da gabatarwar da Alkur'ani mai girma da Sunna mai tsarki da shuwagabannin musulmi da malamansu da masu adabi suka yi wa wannan itaciya mai albarka, zuriyar mai tsarki, wacce ita ce madugun al'umma.

Ahlul-baiti (a.s) Cikin Kur'ani Mai Girma

Alkur'ani mai girma shi ne tushen dukkan tunani, shi ne mabubbugar shari'a da ka'idoji. Duk abin da Alkur'-ani ya zo da shi wahayi ne abin saukarwa, kuma magana ce tsarkakkiya daga Allah, yana furuci da tsarin rayuwa yana kuma ayyana dokokin rayuwar. Duk wani musulmi ya san cewa abin da Alkur'ani ya zo da shi shi ne shari'a da sakon da zai bi a rayuwarsa, sannan kuma an wajabta masa aiki da shi da yin tafiya bisa shiriyarsa. Abin lura kuma shi ne Alkur'anin nan ya yi magana a kan Ahlulbaiti (a.s) da yanayi da tsari kamar haka:

1. Amfani da sunansu na isdilahi wanda shi Alkur'-anin ya sanya musu. Wani lokaci yakan ambace su da Ahlulbaiti kamar yadda ya zo cikin Ayar Tsarkakewa, wani lokaci kuma yana ambatonsu da al-Kurba kamar yadda ya zo cikin ayat al-Muwadda (ayar kauna). Ayoyi masu yawa sun sauka da wadannan ma'anoni sannan Sunna ta yi bayaninsu ga al'umma a lokacin da ayoyin suke sauka daga bisani kuma masu fassara da masu ruwaya suka nakalto bayanin cikin littattafansu manya da kanana.

Kiyaye da kuma rubuta dukkan ababen da suka kebanta ga Ahlulbaiti (a.s) bugu da kari kan saukan ayoyi da dama da suke ambaton falalar Ahlulbaiti (a.s), matsayinsu, yabo da fuskantar da al'umma zuwa gare su; wani zubin a ambaci darajojin a hade, kamar yadda ya zo cikin Ayar Mubahala (Surar Ali Imrana, 3: 61) da Ayar Ciyarwa cikin Surar Dahri da sauransu. Wani zubin kuwa a rarrabe kamar yadda ya zo cikin Ayar Wilaya (Surar Ma'ida, 5: 55).

Bari mu bijiro da sashen wadannan ayoyi - suna kuwa da yawa - wadanda suka yi magana a kan Ahlulbaiti (a.s), domin bayani a kan falalarsu da matsayinsu, gami da kuma sharhi:

Ta Farko:Ayar Tsarkakewa

"...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa". (Surar Ahzabi, 33:33)

Hakika tafsirai da ruwayoyi sun hadu a kan cewa abin da ake nufi da Ahlulbaiti shi ne mutanen gidan Annabi (s.a.w.a) wadanda kuma su ne, Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.). Bayani ya zo cikin littafin Durrul Mansur na Imam As-Suyudi cewa: (Al-Dabarani ya fitar da hadisi daga Ummu Salma cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce da Nana Fadimatu cewa: "Taho min da mijinki da 'ya'yansa biyu", sai ta taho da su sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya lullube su da wani mayafi, sa'an nan ya sanya hannunsa bisansu ya ce:

"Ya Allah! Wadannan su ne Ahlulbaitin Muhammadu (a wani lafazin zuriyar Muhammadu) to Ka sanya tsirarKa da albarkarKa wa zuriyar Muhammadu kamar yadda Ka sanya wa zuriyar Ibrahima, lalle Kai ne Abin godiya, Mai girma".

Sai Ummu Salma ta ce: "Sai na daga mayafin domin in shiga in kasance tare da su, sai Annabi (s.a.w.a) ya janye shi daga hannuna ya ce: "Lallai ke kina tare da wani alheri"([1]).

An ruwaito hadisi daga Ummu Salma, matar Annabi (s.a.w.a) cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance a dakinta bisa wurin kwanciyarsa yana rufe da wani mayafi sakar Khaibara, sai Fadima ta zo da wata tukunya da abinci a cikinta. Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ki kira mijinki da 'ya'yansa Hasan da Husaini". Sai ta kira su. Yayin da suke cin abincin sai aya ta sauko wa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa:

"…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkake-ku tsarkakewa".

Sai Annabi (s.a.w.a) ya kama gefen ragowar sashen mayafinsa ya rufe su da shi, sannan ya fitar da hannunsa daga mayafin ya nuna sama ya ce:

"Ya Allah! Wadannan su ne mutanen gidana, make-bantana, to Ka tafiyar da kazamta daga gare su kuma Ka tsarkake su, tsarkakewa".

Ya fadi hakan har sau uku. Ummu Salma ta ce: "sai na shigar da kaina cikin mayafin na ce: "Ina tare da ku Ya Manzon Allah? Sai ya ce: "ke kina tare da wani alheri", ya fadi hakan har sau biyu([2]) .

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ci gaba da bayyana wa al'ummarsa ma'anar wannan aya mai girma, yana tsarkake fahimtarta ga wannan aya domin al'umma ta haskaka da ita ta kuma rayu a kan shiryuwarta. An ruwaito shi yana cewa:

"Wannan aya ta sauka ne a kan mutane biyar: Ni kaina, Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini…."…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa([3]) ".

Kamar yadda kuma aka ruwaito daga Ummul Muminina A'isha, tafsirin ayar da bayanin mutanen da ake nufi a ciki, kamar haka:

(Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fito wata safiya yana sanye da wani mayafi mai zane, wanda aka yi da bakin gashi, sai Hasan dan Ali ya zo, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya shigar da shi (cikin mayafin), sannan sai Husaini ya zo, ya shigar da shi, sannan Ali ya zo ya shigar da shi, sa'an nan sai ya ce:

"…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa([4]) ".

A wata ruwayar kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana wucewa ta kofar Fadima (a.s.) yayin da ya fito sallar asuba yana cewa:

"Salla! Ya mutanen babban gida (Ahlulbaiti), salla! "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa "([5]) .

Hakan nan Alkur'ani yake magana a kan Ahlulbaiti (a.s) yana iyakance mutanen da suke ciki, tsarkaka manisanta daga dukkan dauda da sabo da zunubi da kuma son zuciya. Saboda haka halayen su abin koyi ne haka nan su kansu. Alkur'ani bai sanar mana da su irin wannan sanarwa ba, sai domin ya jaddada matsayi da mukaminsu ga al'umma, ya kuma ja hankulanmu zuwa ga koyi da su da komawa gare su domin fahimtar shari'a da karbar hukumce-hukumcenta daga wurinsu. Ta wannan hanyar, Alkur'ani ya ayyana mana mizani na aikace (wato ayyukan Ahlulbaiti) da ma'aunin da za mu koma gare shi yayin da ra'ayoyi suka sassaba, aka kuma sami bambancin fahimta da I'itikadi (wato abin da mutum ya yarda da shi).

Wannan kuwa a sarari yake idan muka duba yadda Alkur'ani ya jaddada cikin ayoyi da yawa ya kuma bijiro da Ahlulbaiti (a.s) a matsayin ja-gorori ga al'umman musulmi bayan Manzon Allah (s.a.w.a.).

Dogewar da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi, wata da watanni bisa tsayuwa a bakin kofar Aliyu da Fadima (a.s.) yana kiransu da asuba zuwa salla, yana kiransu da Ahlulbaiti ba kome ba ne face sanar da al'umma mutanen da ake nufi da Ahlulbaiti, kana kuma yana fassara wa musulmi ayar tsarkakewa, yana sanar da su matsayin Ahlulbaiti (a.s) tare da jan hankulansu zuwa gare su da kuma wajabta musu kaunarsu da yi musu biyayya da jibinta al'amari gare su. Dabarani ya ruwaito daga Abu Hamra' cewa:

"Na ga Manzon Allah (s.a.w.a.) yana zuwa kofar Aliyu da Fadima tsawon wata shida yana cewa: "Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa([6]) ".

Fakhru al-Razi ya ambata a cikin tafsirinsa, Tafsir al Kabir, cewa bayan saukar ayar: "Kuma ka umurci iyalanka da salla, kuma ka yi hakuri a kanta", (Surar Daha, 20: 132), Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kan je (kofar) Aliyu da Fadima kowace safiya yana mai cewa: (lokacin) salla (ya yi), ya aikata hakan har na tsawon watanni.

Sannan kuma ya kawo hadisin Hammad bn Salma, daga Aliyu bn Zaid daga Anas cewa: "Annabi (s.a.w.a) ya kasance yana wucewa ta dakin Fadima koyaushe ya fito zuwa ga salla har na tsawon wata shida, yana mai cewa: "Salla! Ahlulbaiti! "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa([7]) ".

A cikin wannan akwai bayani da kuma nuni zuwa ga muhimmancin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya riki Ahlulbaiti (a.s) da shi, da kuma karfafawarsa wa musulmi cewa su (Aliyu, Fadima da 'ya'yansu) su ne mutanen gidansa (Ahlulbaiti), wadanda Allah Ya tafiyar da dukkan dauda ga barinsu, Ya kuma tsarkake su tsarkakewa. Wannan muhimmancin an nuna shi ne bayan Allah Ya yi magana da ManzonSa cewa: "...kuma ka umurci iyalanka da salla, kuma ka yi hakuri a kanta".

Sannan a sarari yake cewa daga abin da ayar: "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa", take nuni da shi da kuma amfani da lafazin maza ba lafazin mata ba da aka yi, wato (عنکم ) da kuma (ویطهرکم ), akwai nuni zuwa ga wadanda ake nufi, su ne wadannan mutane biyar din. Bayani ya zo a cikin Tafsirai cewa da Allah Yana nufin matan Annabi (s.a.w.) ne da Yayi amfani da kalmar (عنکم ) da ta (ویطهرکم ) da magana irin wacce ake yi wa mata.

A baya mun riga da mun ga Hadisin Mayafi lokacin da aka saukar da wannan aya ta tsarkakewa yayin da Ummu Salama taso shiga cikin wannan mayafi amma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce mata ke dai kina a matsayinka, kuma kina a kan alheri.

Hakan yana nuna mana rashin shigar matayen Annabi (s.a.w.a) cikin wannan aya ta tsarkakewa, kana kuma babu daya daga cikinsu da ta yi ikirarin saukar wannan aya a kansu, duk kuwa da cewa ayar ta falaloli da kuma matsayi mai girma ce.

Wannan ayar ta fitar da wata hanya wacce abin da take nuni da shi da abin da ta tattara suna da yalwar gaske. Tana jan hankulanmu zuwa ga batutuwa na asasi a rayuwar Musulunci domin kada mu sami rikitarwar fahimta balle ma manufofin Littafin Allah na gaskiya su tawaya. Allah Ya yi nufin gina al'umma bisa ginshikin tsarki da nisantar dauda da abin kunya sai Ya sanya Ahlulbaiti (a.s) a matsayin wani tushe abin dogara da kuma haske mai haskakawa. Lalle babu wani mutum da Alkur'ani mai girma ya siffanta shi da wannan siffa daga cikin musulmi, babu kuma wanda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya siffanta shi da wannan siffar (siffar tsarki maras iyaka) face Ahlulbaiti (a.s).

Ta Biyu: Ayar Soyayya

"Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta. Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, za Mu kara masa kyau a cikinsa, lallae Allah Mai gafara ne, Mai godiya". (Surar Shura, 42:23)

Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya bayyana ko wane ne ake nufi da wannan aya mai albarka, kuma ko su waye kaunarsu da biyayya gare su da rayuwa bisa tafarkinsu ya wajabta ga musulmi. Malaman tafsiri da hadisi da tarihi sun ruwaito cewa "Makusantar Annabi" wadanda ake nufi a wannan ayar su ne Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.).

Zamakhshari ya fada a cikin tafsirinsa al-Kashshaf cewa: "An ruwaito cewa mushrikai sun taru a wurin taronsu sai sashinsu ya ce wa sashi: "shin kuna ganin Muhammadu zai nemi wani lada a kan abin da yake kira gare shi? Sai aya ta sauka cewa: "Ka ce: "Ba ni tambaya ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta([8]) ".

Sai Zamakhshari ya ce: "Kuma an ruwaito cewa yayin da wannan aya ta sauka sahabbai sun tambayi Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya Manzon Allah su waye danginka wadanda sonsu ya wajabta a kanmu". Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu".

A cikin Musnad na Imam Ahmad bin Hambal - da isnadinsa ambatacce -, daga Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas (r.a.) ya ce: "Yayin da zance Allah Ta'ala cewa: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ya sauka, sai mutane suka tambayi Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya Rasulallah! Su waye danginka wadanda sonsu ya wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'yayansu biyu([9]) ".

Fakhrurrazi ya tabbatar da wannan zancen cikin Tafsirul Kabir bayan ya ambaci maganar Zamakhshari dangane da Alu Muhammad (dangin Muhammadu). Ga abin da yake cewa:

"Ni ina cewa dangin Muhammadu su ne wadanda al'amuransu suke tare da na shi (Annabi), to kuma duk wadanda kusancinsu yafi kusa da shi da kuma cika, to su ne aalu (dangin Annabi). Babu shakka cewa Fadima da Ali da Hasan da Husaini suna da mafi tsananin alaka da Manzon Allah (s.a.w.a.), wannan kuwa an nakalto ta hanyoyi daban. A saboda haka ya wajaba su kasance su ne Aalu".

Har ila yau an sassaba a kan ma'anar aalu, wasu sun ce su ne danginsa, wasu kuma sun ce su ne al'ummarsa. To idan mun dauke shi da ma'anar dangi, to su din dai su ne aalu din, idan kuma muka dauke shi da ma'anar al'umma([10]) wadanda suka karbi kiransa to nan ma dai su ne aalu din. Don haka a bisa dukkan yanayi dai su aalu din ne dai.

To amma shigar waninsu cikin kalmar aal, a nan kan an samu sabani kan hakan. Marubucin al-Kashshaf ya ruwaito cewa yayin da wannan aya ta sauka, mutane sun ce: "Ya Manzon Allah su waye danginka wadanda kaunarsu ta wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu, Fadima da 'ya'yansu biyu", sai ya tabbatar da cewa wadannan hudun su ne dangin Annabi (s.a.w.a), to idan kuwa hakan ya tabbata to ya wajaba su zama abin kebancewa da karin girmamawa. Ana iya tabbatar da hakan ta fuskoki kamar haka:

1. Fadin Allah (S.W.T) cewa: "face dai soyayya ga makusanta", kuma fuskar kafa hujja da ayar ya gabata.

2. Babu shakka cewa Annabi (s.a.w.a) ya kasance yana kaunar Fadima. An ruwaito shi yana cewa:

"Fadima yanki ne daga gare ni, abin da yake cutar da ita yana cutar da ni ".

Kamar yadda ingantaccen hadisi ya tabbatar cewa Annabi Muhammadu (s.a.w.a) ya kasance yana kaunar Aliyu, Hasan da Husaini (a.s.). To idan wannan ya tabbata, lallai kaunarsu ta zama wajibi a kan dukkan al'umma domin fadin Allah (S.W.T.) cewa:

"Ka ce: Idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, Allah Ya so ku...". (Surar Ali Imrana, 3:31)

"...ku bi shi, don ku shiryu". (Surar A'arafi, 7: 158)

Da kuma fadinSa cewa: "...to, wadanda suke sabawa umurninSa, su kiyayi abkuwar wata fitina...". (Surar Nur, 24: 63)

"Lalle abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah..." (Surar Ahzabi, 33: 21)

3. Addu'a ga dangin Manzo tana da wani matsayi mai girma, domin haka ne aka sanya wannan addu'ar ta zama cikamakin tahiya a cikin salla, wato: "Ya Allah! Ka yi tsira ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kuma Ka yi jin kai ga Muhammadu da Alayen Muhammadu".

Ba a samun wannan girmamawa ga wani wanda ba su dangin ba. To duk wannan yana nuni da cewa kaunar alayen Muhammadu wajiba ce.

Imam Shafi'i yana cewa:

Ya kai mahayi tsaya a wannan kwari na Mina,

Ka kira mazaunin al-Nahidhi

Da daddare yayin da alhazai suka wuce zuwa Mina,

Tamkar kogin Furatu mai yalwa da yawan ruwa

Idan Rafdhu([11]) shi ne son Zuriyar Muhammadu,

To mutane da aljannu su shaida ni Rafidhi ne([12])

Ibn Munzir da ibn Abi Hatam da ibn Mardawihi da Dabarani cikin Mu'ujamul Kabir daga Ibn Abbas sun ce: "Yayin da ayar: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ta sauka sai mutane suka ce: "Ya Manzon Allah su wane ne makusantanka wadanda kaunarsu ta wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu([13]) ".

A cikin Mu'ujam din dai ya inganta daga Imam Hasan dan Ali (a.s.) cewa wata rana yayin da yake huduba wa mutane ya ce:

"Ni ina daga cikin Ahlulbaitin da Allah Ya farlanta kaunarsu a kan kowane musulmi, inda Ya ce: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta".

(Ibn Abi Hatam ya fitar daga Ibn Abbas cewa: (lokacin da aka karanta wannan aya): (…ومن يقترف حسنة نزد له فيها حسنا ) "…kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau…) (Surar Shura, 42: 23), sai ya ce: "(hakan) shi ne kaunar Ahlulbaiti([14]) ".

Alkur'ani mai girma ya tabbatar da tsarkin Ahlulbaiti (a.s) da ayar tsarkakewa kuma ya fahimtar da al'umma matsayinsu da rawar da suka taka dangane da daukaka sakon Musulunci a cikin rayuwar al'umma. Da wannan ne kuma suka cancanci soyayya da riko zuciya daya wanda Alkur'ani ya yi umurni da shi a wannan ayar.

Abin da Alkur'ani yake nufi da wannan soyayya ba wai bege da doki da soyayya ta zuci kawai ba ne, domin babu wata fa'ida ga soyayya da kaunar da take cikin rai da zuciya, amma ba ta da wata bayyana a waje (a fili). Lallai tabbatar kauna da soyayya ga makusantan Manzon Allah (s.a.w.a.) yana samuwa wajen koyi da su da kuma rayuwa bisa turbarsu da lizimtar mazhabarsu da abin da ya fito daga gare su, da kuma daukar matsayinsu a al'umma matsayin shugaba kuma ja-gora.

Yayin da Alkur'ani yake sanya wannan ayar a bisa harshen Manzon Allah (s.a.w.a.) kuma Yake umurtansa da cewa ya sanar da al'ummarsa da mutane bai daya cewa ba ya nufin samun wani lada ko sakayya daga gare su domin isar da sako da jure wahalhalun kira zuwa ga Allah da kuma shiryar da su, face soyayya ga makusantansa (s.a.w.a) da tsarkake zuciya gare su da rayuwa bisa tafarkinsu, abin da kurum Alkur'ani yake nufi shi ne kiyaye tafarkin al'umma da tsare hanyarta ta akida da shari'a, domin al'umma ta fuskanci Ahlulbaiti bayan da Alkur'ani ya fuskantar da ita zuwa gare su.

Ba don lamuncewar da ake samu daga Ahlulbaiti (a.s) ba, da kuma ikon ja-gorancin al'umma a kan hanyar shiriya da lamunce hakan ba, da Alkur'ani bai saukar da soyayyar ba, kuma da ba a umurci Manzon Allah (s.a.w.a.) da ya sanya hakkinsa (ladansa) a kan al'umma shi ne kaunar Ahlulbaiti (a.s) ba.

Wannan tarin bayanai da muka kawo na maganganun malaman tafsiri da hadisi sun nakalto mana fassarar da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi wa wannan aya mai albarka, da sanya kaunar Ahlulbaiti (a.s) cikin zukata kuma ya sanya kaunar ta hakika ce mai tabbata cikin zuciyar ko wane musulmi, tana bayyana a cikin halayensa, tunaninsa da kuma begensa. Soyayyar nan tana kuma ayyana matsayarsa a kan Ahlulbaiti (a.s) da makiyansu da masoyansu da kuma bin tafarki da kuma abin da ya tabbata daga gare su na hadisi, fikihu, tafsiri, tunani, akida, shari'a da kuma tsarin aiki na jagoranci da siyasa.

Wannan lambar girma da daukaka tana da manufa da abin da take nuni da shi a kebance, wanda ya kamata musulmi su kiyaye shi kuma su riski zurfinsa.

Ta Uku: Ayar Mubahala

"To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirayi 'ya'yanmu da 'ya'yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, sa'an nan kuma mu kankantar da kai, sa'an nan kuma mu sanya la'anar Allah a kan makaryata". (Surar Ali Imrana, 3: 61)

Wani abu mai madauwamin tarihi wanda malaman tarihi da tafsiri sun ruwaito shi ya auku, wanda kuma yake nunawa al'umma irin girma da daukakan Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a.), su ne kuwa: Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.) a wajen Allah (S.W.T.) da kuma matsayinsu a cikin wannan al'umma.

Wannan abin kuwa kamar yadda su malaman tafsiri da tarihin suka kawo shi ne cewa wata tawaga([15]) ta kiristocin Najran ta zo domin ta yi jayayya da Manzon Allah (s.a.w.a.) don a gane waye yake kan gaskiya. Nan take sai Allah Ya umurce shi cikin wannan aya mai albarka da ya kira Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.) ya fita da su zuwa wani kwazazzabo, ya kuma kira Kiristocin da 'ya'yansu da matansu su fito sannan a yi addu'ar Allah Ya saukar da azaba kan makaryata. Zamakhshari a cikin Al-Kashshaf yana cewa:

"Yayin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kiraye su zuwa ga Mubahala([16]) , sai suka ce: sai mun koma mun yi nazari. Da suka kebanta sai suka ce wa shugabansu; "Ya Abdul Masih! Me ka ke gani? Sai ya ce: "Wallahi, Ya ku jama'ar Nasara, kun sani cewa Muhammadu Annabi ne wanda aka aiko shi kuma hakika ya zo muku da bayani mai rarrabewa game da al'amarin sahibinku. Wallahi babu wata al'umma da ta taba yin mubahala da wani Annabi face babbansu ya halaka, karaminsu kuma ya gagara girma, to idan ko kun aikata hakan to lallai za mu halaka. Idan kun zabi riko da adddininku da zama bisa abin da kuke kansa to ku yi bankwana da mutumin na ku koma garinku.

Ko da gari ya waye sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fito yana mai sammako, yana rungume da Husaini (a.s.) yana rike da hannun Imam Hasan (a.s.), Fadima (a.s.) kuwa tana biye da shi sannan shi kuma Aliyu (a.s.) yana bayanta, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce musu: "Idan na yi addu'a ku ce amin".

Ko da Kiristocin nan suka hango Manzon Allah (s.a.w.a.) yana zuwa da tasa tawagar, sai wannan Fadan da ke cikinsu ya ce musu: "Ya jama'ar Nasara! Wallahi ni ina ganin wasu fuskokin da idan Allah Ya so gusar da wani tsauni daga muhallinsa domin alhurmansu sai Ya yi. Don haka (ina shawartarku) da kada ku yi Mubahala da su don za ku halaka ya zamo babu wani kiristan da zai wanzu a bayan kasa har tashin kiyama".

To daga nan sai suka ce wa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya Abal Kasim! Mun yi shawara ba za mu yi mubahala da kai ba, mu bar ka a kan addininka, mu kuma mu tabbata a bisa addininmu". Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce musu:

"Idan kun ki yarda da mubahala, to ku musulunta duk hakkin da musulmai ke da shi kuma kuna da shi, duk kuwa abin da yake kansu yana kanku". Amma sai suka ki, don haka sai ya ce musu: "To ni zan yake ku".

Sai suka ce : "Ba mu da karfin yaki da Larabawa, amma za mu yi sulhu da kai cewa ba za ka kai mana hari ba, ba za ka tsoratamu ba, ba za ka fitar da mu daga addininmu ba. Mu kuma za mu kawo riguna dubu biyu duk shekara, dubu daya cikin watan Safar dubu dayan kuwa cikin watan Rajab, da kuma sulken karfe guda talatin". Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi sulhu da su akan hakan, sa'an nan ya ce: "Na rantse da Wanda raina yake HannunSa, hakika

halaka ta yi reto kan mutanen Najran, da sun yi mubahala (da mu) da anshafe su an mai da su birrai da aladu, da kuma kwazazzabon nan ya kama da wuta a kansu da kuma Allah Ya tuge Najran da mutanenta har tsuntsayen da ke bisa bishiyoyi, kuma da ba za a shekara ba face Nasara sun hallaka dukkansu".

Sannan Zamakhshari ya ci gaba da bayani kan tafsirin Ayar Mubahala da matsayin Ahlulbaiti (a.s) bayan da ya ba da shaidar matsayinsu mai girma da hadisin Ummul Muminina A'isha, ya ce:

"(Annabi) Ya gabatar da su (Ahlulbaiti) a kan kansa ne wajen ambato domin ya yi mana tambihi a kan taushin matsayinsu da kusancinsu (ga Allah), don ya nuna cewa su abin gabatarwa ne a kan kai kuma abin fansa da su. Wannan kuwa shi ne mafi karfin dalili a kan falalar Ashabul Kisa'i([17]) .

Tafsirul Kashshaf na Zamakhshari yayin tafsirin Surar Ali Imrana aya ta 61, haka nan kuma ya zo cikin Tafsirin Tha'alabi daga Mujahid da Kalbi([18]) .

Wannan yanayi (na fitowa domin Mubahala) yana nuna mana fitowar rundunar imani ne tana fuskantar rundunar shirka, sannan kuma wadanda suka fito (a sashin imani) su ne 'yan kan gaba wajen karbar shiriya, su ne magabatan al'umma kuma mafi tsarkin cikinsu, rayuka ne wadanda Allah Ya tafiyar da dauda ga barinsu kuma Ya tsarkake su matukar tsarkakewa. Ba a mayar masu da addu'a, ba a kuma karyata wata maganarsu. Daga nan za mu fahimci cewa dukkan abin da ya zo mana daga Ahlulbaiti (a.s) yana gudana ne bisa wannan matsaya (ta tsarki da fifiko) sawa'un wani tunani ne ko shari'a ko ruwaya ko tafsiri ko shiryarwa da fuskantarwa. Domin su ne magaskanta cikin maganarsu da harkar rayuwarsu da kuma tafarkinsu.

Da Ahlulbaiti (a.s) ne Alkur'ani ya kalubalanci abokan gaba Musulunci, ya sanya masu jayayya da su su ne makaryata abubuwan bijirowar tsinuwa da azaba; "…sa'an nan kuma mu sanya la'anar Allah a kan makaryata".

Shakka babu da ba don an lamunce mana tabbatuwa da kuma gaskiya cikin abin da yake fitowa daga gare su ba, da Allah bai ba su wannan daukaka ba kuma da Alkur'ani bai yi furuci da wannan ba.

Fakhrurrazi ya kawo cikin tafsirinsa Alkabir kwaton-kwacin abin da Zamakhshari ya ruwaito, inda tafsirinsu suka dace da juna a wannan matsayin. Sannan ya yi karin bayani a kan zancen Zamakhshari da cewa: "Ka sani cewa wannan ruwaya daidai take da abin da aka daidaita a kan ingancinsa tsakanin ma'abuta tafsiri da hadisi([19]) ".

Allama Tabataba'i ya ce wadanda ake nufi a wannan aya kuma wadanda Allah Ya yi nufin (amfani da su wajen) tsinewa abokan gabarsu, su ne Manzon Allah (s.a.w.a.), Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.). Ga abin da Allama Tabataba'in ya ce:

"Malaman hadisi sun hadu a kan ruwaito wannan ruwaya da samun karbuwarta, kuma ma'abuta manyan littattafai kamar su Muslim a cikin Sahihinsa da Tirmizi a nasa Sahihin, sun tabbatar da wannan ruwaya, sannan malaman tarihi sun karfafa ta. Kana kuma malaman tafsiri sun hadu a kan kawo wannan ruwaya cikin tafsiransu ba tare da wata suka ba, ba kuma kokwanto. Haka nan kuma akwai malaman hadisi da tarihi kamar su Dabari da Abul Fida da Ibn Kathir da Suyudi da sauransu". A cikin wannan aya mai albarka, Allah da ManzonSa

Sun yi amfani da Ahlulbaiti (a.s) wajen yin Mubahala da abokan gaban Allah, to hakan kuwa yana sanar da al'umma matsayi da daukakan da suke da shi. Hakika ba don wannan kebantacciyar daukaka da suke da ita a wajen Allah ba, da kuma tsarki na musamman ma ba, da Manzon Allah (s.a.w.a.) bai kira wadannan taurari tsarkaka domin yin barazana ga makiya Allah da saukar da azaba da kuma lamunce amsa addu'arsu ba.

A cikin ayar akwai ma'anoni masu zurfi na harshen da aka yi amfani da shi cikin maganar wadanda lallai ne a yi la'akari da su, hakan kuwa shi ne danganta wadannan Taurari (Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini) da Annabi (s.a.w.a.), wato cewan da aka yi "'ya'yanmu" da "matanmu" da "kanmu".

Ba don faruwar wannan lamari da fitar da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi da wadannan Taurari tare da shi ba, da mai yiyuwa zukata su koma ga matan Annabi (s.a.w.a) wajen kalmar "matanmu", wajen kalmar "'ya'yanmu" kuwa zuwa ga Fadima da sauran 'ya'yan Ma'aiki (s.a.w.a.), sannan wajen kalmar "kanmu" kuwa zuwa ga zatin Annabi (s.a.w.a) mai tsarki shi kadai.

Amma fita da wadannan mutanen hudu da Annabi ya yi tare da shi koma bayan wasunsu, ya fassara mana cewa mafificiyar macen wannan al'umma kuma abin koyi gare ta ita ce Nana Fadima (a.s.), zababbun 'ya'yan musulmi kuwa su ne Hasan da Husaini (a.s.), don kuwa Alkur'ani ya dangantasu ga Annabi (s.a.w.a.) sai suka zama 'ya'yansa, kamar yadda aya ta nuna. Kana kuma Alkur'ani ya dauki Aliyu (a.s.) tamkar ran Manzo (s.a.w.a).

Ta Hudu: Ayar Salati

"Lalle, Allah da Mala'ikunSa suna salati ga Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi". (Surar Ahzab, 33:56)

A cikin ayoyin da suka gabata, Alkur'ani mai girma ya yi magana a kan tsarkin Ahlulbaiti (a.s) da kaunarsu da kuma cewa su ne mutanen gidan Manzon Allah (s.a.w.a.). Masu fassara kuma sun iyakance wadannan mutane da sunayensu cewa su ne Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.).

To wannan ayar kuwa ta kawo umurni ne na wajibcin yin salati ga Annabi (s.a.w.a) da alayensa madaukaka da kuma kebancesu, koma bayan wasunsu da kuma girmama mukaminsu da karamarsu domin al'umma ta san matsayinsu wajen sakon Musulunci a cikin rayuwar al'umma.

Fakhrurrazi ya kawo cikin Tafsirinsa abin da aka ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a.) kan tafsirin wannan aya mai albarka, inda ya ce: "An tambayi Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya ya za mu yi salati a gare ka Ya Manzon Allah? Sai ya ce:

"Ku ce: Ya Allah Ka yi tsira ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kamar yadda Ka yi tsira ga Ibrahim da Alayen Ibrahim, Ka yi albarka ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kamar yadda Ka yi albarka ga Ibrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai Abin godiya ne, Mai girma". Kafin ya kawo wannan nassin, sai da ya bijiro da tafsirin ayar sannan ya ce: "Wannan dalili ne kan mazhabar Shafi'i domin umurnin na wajibci ne([20]) saboda haka salati ga Annabi yana wajabta. Kuma salatin ba ya wajaba in ba a tahiya ba, saboda haka yana wajaba ne a cikin tahiya([21]) ".

Fakhrurrazi ya karkare da cewa: "Idan Allah da Mala'ikunSa sun yi wa Manzon Allah (s.a.w.a.) salati, to wata bukata kuma yake da shi ga salatinmu?

To muna iya cewa yi masa salati ba wai don yana bukatuwa ga salatin ba ne, don kuwa idan ba haka ba ne, to ai babu bukatar salatin Mala'iku bayan salatin Allah a gare shi. Amma ba kome ba ne yasa muke masa salati face bayyana girmamawarmu gare shi, da tausayawarSa gare mu domin Ya saka mana domin salatin. Don haka ne Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda ya yi mini salati sau guda, Allah Zai masa goma").

A ciki Durrul Mansur na Imam Suyudi, Abdurrazak da Ibn Abi Shaiba da Ahmad da Abd bn Humaid da Bukhari da Muslim da Abu Dauda da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ibn Mardawihi, daga Ka'ab bn Ujrah, ya ce wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, mun san yadda ake maka sallama, to ya ya ake maka salati? Sai ya ce: "Ka ce: Ya Allah Ka yi tsira a kan Muhammadu da Alayen Muhammadu kamar yadda Ka yi tsira kan Ibrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai ne Abin godiya, Mai girma".

Malamin ya kawo hadisai goma sha takwas ban da wannan hadisin dukkan su suna nuni ga tarayyar Alayen Manzon Allah (s.a.w.a.) da shi cikin salati. Ma'abuta littattafan hadisi sun ruwaito su daga sahabbai daban-daban. Ga wasu daga cikinsu: Ibn Abbas da Dalha da Abu Sa'id al-Khudri da Abu Huraira da Abu Mas'ud al-Ansari da Buraida da Ibn Mas'ud da Ka'ab bn Umrah da Ali (a.s.).

Sannan kuma a cikinsa Imam Ahmad da Tirmizi sun fitar da hadisi daga Hasan bn Ali (a.s.) cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a gurinsa bai mini salati ba([22]) ".

Kamar haka ne malaman fikihu suka ruwaito wajibcin salati ga Annabi Muhammadu da Alayensa (a.s.) cikin tahiyar salla([23]) da wajibcin kawo ambaton Alayen Muhammadu cikin salla.

Duk wanda ya sa ido a kan wannan aya zai fahimci cewa manufar shar'anta salatin da lizimtar da shi shi ne girmama Alayen Manzon Allah (s.a.w.a.), wadanda Allah Ya tafiyar da dauda daga gare su kuma Ya tsarkake su matukar tsarkakewa, domin al'umma ta yi koyi da su, ta bi tafarkinsu, kuma ta fake a gare su lokacin fitinu da sassabawa.

To wadannan da salla ba ta inganta sai gami da an masu salati, su ne Shuwagabannin al'umma, su ne a ka yi nuni da su kuma aka lamunce a yi koyi da su. Ba don tabbata da lamuncewar tsayuwarsu da kubutar abin da ya fito daga gare su ba, da Allah bai umurci musulmi a dukkan zamunna da su rataya da su da yi musu salati cikin kowace salla ba.

Hakika cikin wannan maimaitawa - maimaita salati ga Annabi da Alayensa, da kuma farlanta hakan a kowace salla - akwai jaddadawa da jan hankulan musulmi cikin kowace salla saboda muhimmanci Ahlulbaiti (a.s) da matsayinsu, da kuma koyi da su da rayuwa bisa tafarki da hanyarsu.

Ta Biyar: Surar Insan

"Hakika mutane na gari suna sha daga wani kofin (giya) da mahadinta ya kasance mai kamshin kafur ne.

(Shi kafur din) wani marmaro ne da bayin Allah suke sha daga gare shi suna bubbugo shi bubbugowa ta hakika. (Don ko) suna cika alkawari na bakance suna kuma tsoron ranar da sharrinta ya kasance mai tartsatsi ne. Suna kuma ciyar da abinci tare da kuma suna son sa; ga miskini da maraya da kuma ribatacce a yaki. (Suna cewa): "Mu kawai muna ciyar da ku ne saboda Allah, ba ma nufin sakamako ko godiya daga wurinku. Hakika mu muna jin tsoron rana mai sa daure fuska matsananciya daga Ubangijinmu". Sai Allah Ya kare su (daga) sharrin wannan ranar Ya kuma hada su da haske da kuma farin ciki. Ya kuma saka musu da Aljanna da alhariri saboda hakurin da suka yi. Suna masu kishingida a cikinta a kan gadaje ba sa samun zafin rana ko sanyi a cikinta. Inuwowinta suna kusa da su, an kuma yiwo kasa-kasa da 'ya'yan itacenta kasa sosai. Ana kuma kai-ka-wo da korai na azurfa da kofuna wadanda suka kasance na karau. Karau din na azurfa ne, sun auna su, aunawa daidai da bukata. Ana kuma shayar da su wata giya a cikinta wadda mahadinta ya kasnce mai kanshin zanjabilu ne (watau citta mai yatsu). (Shi zanjabilu) wani marmaro ne a cikinta da ake kiran sa Salsabilu. Samarin hadimai dawwamammu da ba sa tsufa kuma suna kai-ka-wo tsakaninsu, idan ka gan su sai ka yi tsammanin su wani lu'u-lu'u ne wanda aka baza. Idan kuma ka yi kallo a canza ka ga ni'ima da kuma mulki kasaitacce. A samansu akwai tufafi sakar alhariri koraye da kuma abawarsa, aka kuma yi musu ado da warawarai na azurfa, Ubangijinsu kuma Ya shayar da su abin sha mai tsafta. Hakika wannan ya kasance sakamako ne a gare ku, kuma aikinku ya kasance abin godewa.

A cikin wadannan ayoyi masu albarka, Alkur'ani ya yi zancen Ahlulbaiti (a.s) ya kuma sanya su su ne koluluwar masu gabatar da wani bisa kansu wajen ciyarwa da kuma takawa. Alku'ani ya sanya su misali da ja-gora ga dan'Adam, domin sauran mutane su yi koyi da su da kuma rayuwa bisa tafarkinsu.

Abin da ya faru har ya sa aka saukar da wadannan ayoyi dominsa yana nuni ne da matsayin Ahlulbaiti (a.s) da kaiwarsu matuka wajen aikatawa da lizimtar shari'a da kuma fuskantar Allah cikakkiya. Kuma su ne mutanen kirkin da aka yi musu albishir da aljanna, to duk wanda ya yi koyi da su, ya yi tafiya a kan tafarkinsu, to za a tashe shi tare da su. Zamakhshari ya kawo bayani kan wannan aya cikin tafsirinsa. Ga abin da ya ce:

(Daga Ibn Abbas (r.a.): Wata rana Hasan da Husaini (a.s.) sun yi rashin lafiya, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) tare da wasu mutane suka ziyarce su don gai da su, sai ya ce wa Imam Ali (a.s.): Ya Abal Hasan, da dai ka yi bakance kan rashin lafiyar 'ya'yanka. Sai Aliyu da Fadima da baiwarsu Fiddha suka ce idan suka sami sauki daga wannan ciwo nasu, za su yi azumin kwanaki uku. Sai kuwa suka warke, alhalin kuwa a wannan gida mai albarka babu wani abu na daga abinci. Sai Aliyu (a.s.) ya yi bashin sa'i uku na Sha'ir daga wani Bayahude mai suna Sham'un Alkhaibari, daga nan sai Fadima ta nika sa'i guda ta yi gurasa biyar, adadin mutanen gidan. Sai ta sanya gurasar a gabansu domin su yi buda baki, bayan lokacin shan ruwa ya yi. Sun shirya za su ci kenan sai ga wani almajiri ya tsaya a kofa ya ce: Assalamu Alaikum, mutanen gidan Muhammadu (s.a.w.a), ni miskini ne daga miskinan musulmi, ku ciyar da ni, Allah Ya ciyar da ku daga abincin aljanna. Sai suka fifita shi (wajen cin abincin) wato suka dauka suka ba shi, su kuwa suka kwana ba su dandani kome ba, sai ruwa, sannan kuma

suka wayi gari da azumi a bakinsu. Da suka kai maraice, suka sake shirya abincin buda baki, sai ga wani maraya ya tsaya a kofa ya yi bara, nan take suka dauki abincin suka ba shi, suka kwana haka. A rana ta uku ma suka ci gaba da azumi, shi ma da lokacin buda baki ya yi suka shirya dan abin da ya sawwaka, a nan ma sai ga wani kamamme ya zo shi ma yana neman abin da zai ci. Sai suka dauki abin da suka tanada suka ba shi.

Da suka wayi gari sai Aliyu (r.a.) ya kama hannun Hasan da Husaini suka nufi gurin Manzon Allah (s.a.w.a.). Yayin da Annabi (s.a.w.a) ya gansu suna karkarwa kamar 'ya'yan tsaki saboda tsananin yunwa, sai ya ce: "Babu abin da zai bakanta mini rai fiye da halin da na ganku a ciki". Sai ya tashi ya tafi tare da su sai ya ga Fadima (a.s.) tana wurin sallarta alhali bayanta ya mannu da cikinta, idanunta sun fada. Ganinta cikin irin wannan hali ya bakanta wa Manzon Allah (s.a.w.a.) rai, sai ga Jibrilu (a.s.) ya sauko ya ce: "Karbi ya Muhammadu, Allah Na tayaka murna batun Ahlulbaitinka", sai ya karanta masa wannan surar([24]) .

Ta Shida: Ayoyi

Hakika ayoyin Alkur'ani masu yawa sun sauka da batun Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s.) wanda aka yi tarbiyyarsa cikin gidan Manzon Allah (s.a.w.a.) tun yana karami([25]) .

Ya tashi karkashin kiyayewarsa (s.a.w.a) don haka ya kwaikwayi halayensa. Ya yi imani da shi, gaskanta shi da kuma binsa tun yana dan shekara goma. Sannan kuma Imam Ali (a.s.) ya kasance mai daukar tutar Manzon Allah (s.a.w.a.) kuma shi ne jarumin sojansa wanda ya kere kowa a dukkan yake-yakensa, da suka hada da Badar, Uhud, Hunain, Ahzab, Khaibar, Zatu Silasil da dai sauransu. A saboda irin jaruntar da ya nuna a irin wadannan yakuna, ya sa Manzon Allah (s.a.w.a.) da kansa ya jinjina masa da bayyanar da wasu kalmomi dawwamammu da suka kasance ado ga littatta-fan tarihi sannan kuma abin koyi na koli cikin sadaukar-wa da kuma jihadi.

Idan muka yi bincike kan asbabun Nuzul (dalilan saukar ayoyi), za mu samu cewa abin da ya sauka dangane da Amirul Muminina, Aliyu bn Abi Talib (a.s.) - ban da abin da muka ambata na Ahlulbaiti (a.s) - suna bayani ne:

1. Kan jaruntar Aliyu (a.s.) gwarzontaka da kuma sadaukarwarsa a kan tafarkin Allah.

2. Kan hakurinsa bisa cutarwa da izgili.

3. Kan gudun duniya, takawa ilimi da kuma kaunarsa ga muminai.

Bari mu ambato wasu misalai kamar haka:

Ayar Wilaya

"Abin sani kawai, majibincinku Allah ne da ManzonSa da wadanda suka yi imani, wadanda suke tsayar da salla, kuma suna bayar da zakka alhali suna masu ruku'i. Kuma wanda ya jibinci Allah da ManzonSa da wadanda suka yi imani, to, kungiyar Allah su ne masu rinjaye". (Surar Ma'ida, 5: 55-56)

Zamakhshari cikin tafsirinsa ya bayyana cewa: "Wannan aya ta sauka ne dangane da Aliyu (Allah Ya karrama fuskarsa) lokacin da wani ya roke shi alhaliyana cikin ruku'in salla, sai ya sake masa zobensa wanda yake loko-loko a dan kuriyarsa, wanda cire shi baya bukatar aiki mai yawa da ka iya bata salla. Idan ka ce ta ya ya za a ce da Ali ake alhali lafazin na jam'i ne? sai in ce maka: An zo da shi akan lafazin jam'i ne ko da yake dalilin saukar ayar a kan mutum guda ne domin a kwadaitar da mutane wajen yin tamkar aikinsa, sai su sami tamkar ladansa. Domin kuma tambihi cewa halayen muminai wajibi ne su kasance da wannan koluwa wajen kwadayin aikin alheri da bibiyar lamarin mabukata ta yadda idan wani abin da ba ya son jinkiri ya lizimce su suna cikin salla, ba sa jinkirta shi sai an idar da sallar([26])

Al-Wahidi ya ambata cewa al-Kalbi ya fadi cikin dalilin saukar wannan aya, cewa: "Lalle karshen wannan aya a kan Aliyu dan Abi Talib (r.a.) take domin ya ba da zobensa ga wani mai bara alhali yana cikin ruku'un salla([27]) ".

Littattafan tafsiri da hadisi masu yawa sun ambato cewa wannan aya mai albarka ta sauka ne dangane da Imam Ali (a.s.). Akwai cikakken bayani kan hakan cikin wadannan littattafa ga mai karin bayani([28]) .

Ayar Tablig (Isar da Sako)

Ya kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar maka daga Ubagijinka. Kuma idan baka aikata ba, to, ba ka iyar da sakonSa ba kenan, kuma Allah Zai tsare ka daga mutane([29]) ” (Surar Ma'ida: 5:67.

An saukar da wannan aya ne a wani kwari da ake ce ma Ghadir Khum. Ga bayanin akan abin da ya faru:

An ruwaito cewa, yayin da Manzon Allah (s.a.w.a.) yake dawowa daga Hajjin Ban Kwana([30]) sai wannan aya (da muke magana a kanta) ta sauka a gare shi a rana ta goma sha takwas ga watan Zul Hajji([31]) .

To sai ya yada zango a Ghadir Khum daga Juhfa([32]) , inda a nan ne kuma hanyoyi suka rarrabu zuwa birnin Madina, Masar da kuma Sham. Sai ya tsaya a nan har wadanda suke bayansa suka iso, wadanda suke gaba kuwa suka komo inda yake([33]) . Akwai wasu itatuwan kaya a rarrabe, sai aka hana Sahabbai sauka a karkashinsu. Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sa aka sare wadannan itatuwa na kaya([34]) , sai ya sa aka yi kiran salla([35]) , ya sallaci azahar tare da jama'a cikin garjin rana([36])

Daga nan sai ya mike ya gudanar da huduba bayan ya yi godiya ga Allah da kuma tsarkake Shi da kuma yin wa'azi ga al'umma, sai ya ce: "Hakika an kusa a kira ni kuma in amsa, ni kuma abin tambaya ne ku ma abin tambaya ne, to me za ku ce?

Sai suka amsa: "Za mu ba da shaidar cewa kai ka isar da sako, ka yi nasiha, to Allah Ya saka maka da alheri".

Sai Annabi (s.a.w.a) ya ce: "Shin ba kwa shaidar cewa babu abin bauta da gaskiya face Allah ba, kuma Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, da cewa aljanna gaskiya ce, wuta ma gaskiya ce"?

Sai suka ce: "Haka ne, mun shaida hakan".

Sai ya ce: "Ya Allah Ka shaida", sai ya ci gaba da cewa: "Shin ba kwa ji".

Sai suka ce: "Na'am" (watau suna ji).

Sai ya ce: "Ya ku mutane! Ni mai gabata ne ku kuma masu iske ni ne a bakin tabki, fadinsa tamkar tafiyar tsakanin garin Basra da San'a'([37]) ne, akwai kofuna na azurfa, yawansu kamr adadin taurari, ni kuma mai tamabayarku ne batun abubuwa biyu masu nauyi (Sakalaini), to ku kula da yadda za ku kasance game da su a bayana".

Sai wani ya yi kira ya ce: "Mene ne wadannan nauyaya biyu, Ya Manzon Allah?

Sai ya ce masa: "Littafin Allah, gefe yana hannun Allah, gefe kuma yana hannunku, to ku yi riko da shi, ba za ku bata ba, ba za ku canjba ba, da kuma iyalina, mutanen gidana. Hakika Mai Tausayawa, Masani, Ya sanar da ni cewa su biyun ba za su rabu da juna ba har sai sun iske ni a bakin tafki. Na roka musu wannan wajen Ubagijina, saboda haka kada ku gabace su sai ku halaka, kada ku takaita (ga barinsu), sai ku halaka, kada ku sanar da su domin sun fi ku sani([38]) .

Sannan sai ya ce: "ashe ba ni ne nafi cancanta ga kowane mumini a kan kansa ba"?

Sai suka ce: "Haka ne, Ya Manzon Allah([39]) ".

Daga nan sai ya kama hannun Aliyu bn Abi Talib (a.s.) ya daga sama har mutane suka ga farin hammatarsa([40]) , ya ce:

Ya ku mutane! Allah Shi ne Majibincina, ni kuma ni ne majibincinku([41]) . To duk wanda na ke majibincinsa, wannan Aliyun majibincinsa ne. Ya Allah! Ka jibinci wanda ya jibince shi, Ka yi gaba da wanda ya yi gaba da shi([42]) , Ka taimaki wanda ya taimake shi, Ka wulakanta wanda ya wulakanta shi([43]) , Ka so mai son sa, Ka ki wanda ya ki shi([44]) ". Sannan sai ya ce: "Ya Allah Ka shaida([45]) ".

Ba su (Manzon Allah da Aliyu) rabu ba har sai da Allah Ya saukar da wannan aya: "A yau Na kammala muku addininku, kuma na cika muku ni'imaTa a kanku, kuma Na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku". (Surar Ma'ida, 5:3)

Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Allahu Akbar! Bisa kammalar addini da cikar ni'ima da yardar Ubangiji da Manzancina da walittakan Aliyu([46]) ".

Akwai ayoyi masu yawa, wadanda wannan karamin littafi ba zai iya tattaro su ba, da suke magana a kan matsayin Ahlulbaiti (a.s) da karamar su da girman mutanen ciki, wadanda wasu daga cikinsu sun kebanta ne ga Uban wannan itace mai tsarki, wato Imam Ali (a.s.). Mai karatu zai iya samun wadannan ayoyi cikin littattafan tafsiri, hadisi, tarihi da kuma masu bayani kan falalolin wadannan taurari da kuma wadanda suka yi magana kan Asbabun Nuzul na wadannan ayoyi. To amma bari mu kawo kadan daga cikin irin wadannan ayoyi, su ne kuwa:

(1). Fadin Allah Madaukakin Sarki: "Abin sani kawai kai mai gargadi ne kuma a cikin kowadanne mutane akwai mai shiryarwa". (Surar Ra'ad, 13:7)

Hadisi ya zo cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sanya hannunsa bisa kirjinsa, ya ce: "Ni mai gargadi ne, ko wadanne mutane kuma suna da mai shiryarwa", sai ya yi nuni da hannunsa zuwa Ali (a.s.), sai ya ce kai ne mai shiriyarwan, Ya Aliyu, da kai masu shiryuwa za su shiryu a bayana([47]) ".

(2). Fadar Allah Madaukakin Sarki: "Shin wanda ya zama mumini yana kamar wanda ya zama fasiki? Ba za su yi daidai ba". (Surar Sajada, 36: 18)

Wannan mumini kuwa shi ne Aliyu (a.s.), fasikin kuma shi ne Walid bn Ukba([48]) .

(3). Fadar Allah Madaukakin Sarki:

"Shin wanda ya kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijinsa, kuma shaida na binsa daga gare shi..." (Surar Hudu, 11:17)

Manzon Allah (s.a.w.a.) shi ne yake bisa hujja bayyananna a al'amarinsa, shaidan kuwa shi ne Imam Ali (a.s.)([49]) .

(4). Fadar Allah Madaukakin Sarki:

"...to lalle Allah Shi ne Mataimakinsa da Jibrilu da Salihin muminai..." (Surar Tahrim, 66: 4) Salihin muminai a nan shi ne Aliyu bn Abi Dalib (a.s.)([50]) .

(5). Fadar Allah Madaukakin Sarki:

"...kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye". (Surar Alhakkatu, 69: 12)

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya karanta wannan aya, sai ya juya ga Ali (a.s.), ya ce: "Na roki Allah da ya sanya shi shi ne kunnenka". Sai Ali (a.s.) ya ce: "Babu wani abu da na ji daga Manzon Allah (s.a.w.a.) na manta shi([51]) ".

Al-Wahidi ya nakalto cikin Asbabun Nuzul daga maruwaita daga Buraida, cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce wa Aliyu (a.s.) cewa: "Allah Ya umurce ni da in kusato da kai, kada kuma in nisantar da kai, cewa kuma in ilmantar da kai, don ka kiyaye, kuma Allah Ya yi alkawarin Zai sa ka kiyaye din. Sai aya ta sauka: "Kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye".

(6). FadinSa Madaukakin Sarki cewa: "Hakika wadanda suka ba da gaskiya suka kuma yi aiki na nagari, to (Allah) Mai rahama Zai sanya soyayya a tsakaninsu". (Surar Maryam, 19: 96)

Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce wa Aliyu (a.s.) cewa: "Ya Aliyu ka ce: "Ya Allah Ka sanya mini wani alkawari, kuma Ka sanya mini soyayya cikin zukatan muminai". Sai Allah Ya saukar da wannan ayar dangane da Aliyu (a.s.)([52]) .

(7). Fadar Allah Ta'ala cewa: "Lalle ne wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan kwarai, wadannan su ne mafifita alherin halitta" (Surar Bayyina, 98:7)

Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: "Ya Aliyu, mafifita alherin halitta (a cikin wannan aya) su ne, kai da 'yan shi'arka([53]) ".

(8). Fadar Allah Madaukakin Sarki cewa: "Yanzu kwa mayar da shayar da alhazai da raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya ba da gaskiya da Allah da ranar lahira kuma ya yi jihadi domin Allah?..." (Surar Tauba, 9: 19) Lalle wadannan su ne Abbas da Dalha, wanda ya yi imani kuwa shi ne Aliyu (a.s.). Akwai wasu ayoyi da dama a kan wannan lamari da muke magana a kansa, amma za mu takaita saboda takaitawa.

Ahlulbaiti (a.s) Cikin Sunnar Annabi

Dukkan wanda ya bibiyi sunnar Manzon Allah (s) da tarihinsa na aikace da kuma alakarsa da mutanen gidansa wadanda nassin Alkur'ani ya kawo, sannan shi (Manzo) kuma ayyanasu (Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu), zai san cewa mutanen wannan gida suna da wata rawar da za su taka a bangaren nauyin rike sako da kuma wayewar wannan al'umma. Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance mai tsare-tsare domin al'ummar tasa da kuma shirya da ita domin ta karbi wannan ni'ima ta Ahlulbaiti (a.s), da umarnin Allah (S.W.T.).

Hakika wannan yanki mai haske na tsare-tsaren Annabi (s.a.w.a), wadanda ya yi da umurnin Allah, ya soma ne da aurar da Fadima (a.s.) ga Imam Ali (a.s.), da dasa wannan itaciya mai albarka, domin rassanta su mamaye sansanin wannan al'umma, tsawon rayuwarta.

An ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce wa Aliyu (a.s.) yayin da ya aurar masa da Fadima (a.s.) cewa: "Lalle Allah Madaukakin Sarki Ya umurce ni da in aurar maka da Fadima bisa sadaki gwargwadon nauyin miskalin azurfa dari hudu, shin ka yarda da hakan". Sai Aliyu (a.s.) ya ce: "Lalle na yarda da hakan, Ya Manzon Allah". Anas bin Malik ya ce: Sai Annabi (s.a.w.a) ya ce: "Allah Ya hada kanku, Ya arzurta kokarinku, Ya albakace ku, Ya kuma fitar da zuriya mai albarka". Sai Anas ya ce: "Wallahi, hakika kuwa Allah Ya fitar da zuriya mai albarka daga gare su"([54]) .

An ruwaito cewa yayin da Annabi (s.a.w.a) ya aurar da Fadima ga Aliyu (a.s.), sai ya shiga wajenta ya kira ta sai Ummu Aiman ta kawo kasko da ruwa a ciki, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi tofi a ciki sannan ya yayyafa a kanta da tsakanin nononta, sannan ya ce: "Ya Allah! Ni ina nema mata tsarinKa da zuriyarta daga shaidan jefaffe". Sai kuma ya ce wa Ali (a.s.): "Miko min ruwa", sai Aliyu (a.s.) ya kawo masa, sai ya zuba a kansa da kuma tsakanin kafadunsa (a.s.), sai ya ce: "Ya Allah! Ina nema masa tsarinKa da zuriyarsa daga shaidan jefaffe".

A wata ruwayar kuma cewa aka yi, sai ya bukaci a kawo masa ruwa, bayan ya yi alwala da shi sai ya zuba a kan Aliyu da Fadima (a.s.), sai ya ce: "Ya Allah! Ka albarkace su cikin zuriyarsu([55]) ".

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana neman uzuri ga duk wani daga cikin sahabbai da ya zo neman a ba shi Fadima (a.s.), yana mai cewa: "Hukumci bai sauko ba tukunna([56]) ".

Hakika wannan kula ta Ubangiji da AnnabinSa ta aurar da Fadima (a.s.) ga Aliyu (a.s.) ta sanya aurar da ita bai faru ba face da umurni daga Allah (S.W.T.) domin wannan ya yi nuni ga matsayin Ahlulbaiti (a.s) da kuma alherin al'umma da Manzon Allah (s.a.w.a.) yake nufi da alakarsa da su. Wannan matsayi na su kuwa shi ne Alkur'ani mai girma ya fassara, haka nan ma sunnar Annabi (s.a.w.a) mai daraja.

Watakila hasken da muke tsinkaya daga ruwayoyi da hadisai Manzon Allah (s.a.w.a.) da Ahlulbaiti (a.s) (wadanda kuwa masu yawa ne) suna riskar da mu ne irin zurfaffar kula ta Allah da ManzonSa (s.a.w.a) wajen gina wannan gida, da yawaita soyayya da albarka da kula gare shi. Domin mutanen wannan gida su zama ja-gororin al'umma cikin rayuwarsu da kuma hanyoyin tsirarsu daga bala'u da kuma kasancewa tsari da makoma ta hadin kanta yayin da ta rarraba, kamar yadda ruwayoyi da hadisai suka yi nuni da hakan.

Manzon Allah (s.a.w.a.) yana danganta zuriyar Aliyu da Fadima (a.s.) da kansa, yana cewa: "Lalle su zuriyata ne 'ya'ya ne, kamar yadda Alkur'ani ya bayyana hakan da cewa: "To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirayi 'ya'yanmu da 'ya'yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku". (Surar Ali Imrana, 3: 61)

Abin nufi da 'ya'yansa a wannan aya su ne Hasan da Husaini (a.s.), kamar yadda maganganun malaman tafsiri da ma'abuta tarihi suka sanar da mu.

Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya karfafa wannan ma'anar wa al'ummarsa sau da yawa, bari mu ambaci kadan daga cikinsu. Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:

"Allah Ya sanya zuriyar kowane Annabi daga tsatsonsa, (ni kuma) Ya sanya zuriyata cikin tsatson wannan", yana nufin Aliyu (a.s.)([57]) .

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana rungumar Hasan da Husaini (a.s.), yana cewa: "Dukkan 'ya'yan wani uba dangantakarsu ta ubansu ce, ban da 'ya'yan Fadima, ni ne ubansu, da ni ake dangantasu". Imam Ahmad ya fito da wannan hadisin cikin al-Manakib([58]) .

Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) yana karfafa matsa-yin Ahlulbaiti (a.s) a kowani muhimmin lokaci, domin al'umma ta koma gare su, ta lizimci tafarkinsu, ta kuma yi riko da soyayyarsu. A ruwayoyi da dama, muna samun cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya nuna mana su a matsayin tudun tsira ga wannan al'umma, yana gwama su da Alkur'ani, yana kuma sanya rawar da za su taka a fagen akida da rike sakon Musulunci, mai lizimtar Littafin Allah ne, ba sa rabuwa da shi. Hakan kuwa don al'umma ta fuskanto su wajen fahimtar Alkur'ani mai girma, da ciro ma'anoninsa da hukumce-hukumcensa.

Littattafan hadisi da tarihi sun taru bisa kawo hadisin Annabi (s.a.w.a) da ake kira da Hadisin Nauyaya Biyu (Hadith al-Thakalain). Musulmi sun ruwaito wannan hadisi duk da bambance-bambancen mazhabobinsu na siyasa da fikihu. Za mu ambace shi a nan tare da sashin isnadinsa (maruwaitan da suka ruwaito shi), kamar yadda masu ruwaya da malaman hadisi suka nakalto.

1- Hadisus Sakalain (Nauyaya Biyu)

Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Na kusata da a kira ni in kuma amsa, amma ni mai bari muku abubuwa masu nauyi guda biyu ne, su ne kuwa: Littafin Allah Mai girma da Daukaka, da kuma zuriyata. Littafin Allah wata igiya ce da aka sako ta daga sama zuwa kasa, zuriyata kuwa su ne mutanen gidana (Ahlulbaiti). Allah Mai tausasawa Ya ba ni labari cewa su biyun ba za su taba rabuwa ba har abada har sai sun iske ni a bakin tafki. To ku lura da yadda za ku rike su a bayana([59]) ".

Al-Shibrawi al-Shafi'i ya nakalto cikin littafinsa mai suna al-Ithafu bi hubbil Ashraf, cewa: "Muslim da Tirmizi sun kyautata shi (hadisin), haka ma Hakim shi ma ya ruwaito shi, lafazin Muslim kuwa daga Zaid bn Arkam cewa ya yi: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya mike a cikinmu domin ya yi mana huduba sai ya yi godiya ga Allah ya yi yabo gare Shi, sannan ya ce:

"Bayan haka, Ya ku mutane, ni dai mai mutuwa ne, kuma zan amsa kiran manzon Ubangijina. To amma na bar muku wasu nauyayan abubuwa guda biyu tare da ku; na farkonsu Littafin Allah, shiriya da haske na cikinsa, to ku kama Littafin Allah ku yi riko da shi". Sannan sai ya ce: "Da Ahlulbaitina, ina gama ku da Allah dangane da Ahlulbaitina([60]) ".

Al-Shibrawi din kuma ya nakalto cewa: "A wata ruwayar kuma Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa ya yi: "Ni mai bari muku al'amurra guda biyu , ba za ku bata ba idan har kun bi su, su ne kuwa; Littafin Allah da Ahlulbaitina". A wata ruwayar kuma (aka cika da cewa) "ba za su rabu ba har sai sun iske ni a bakin tafki, to ku kula da yadda za ku rike su a bayana([61]) ". Ya kara da cewa: "Ibn Hajar ya fada cikin Sawa'ikul Muhrika cewa: "Annabi (s.a.w.a) ya ambaci Alkur'ani da zuriyarsa da cewa "Nauyaya Biyu" ne saboda nauyin dukkan wani mutum shi ne abu mafi muhimmanci a gare shi, kuma wadannan guda biyu haka suke. Domin kuwa kowane daga cikinsu taska ce ta ilmummukan addini da sirrorin hankali irin na shari'a, domin haka ne ma aka kwadaitar da koyi da su. Wani kaulin kuma ya ce an ambace su da "Nauyaya Biyu" ne domin wajibcin kiyaye hakkokinsu. Sannan kuma wanda kwadaitarwar ta tabbata a gare su, su ne masana Littafin Allah masu riko da sunnar ManzonSa (s.a.w.a), domin su ne wadanda ba su rabuwa da Littafin har zuwa tabki([62]) ".

Allama Shaikh Muhammad Jawad al-Balagi ya nakalto cikin tafsirinsa Ala'u al-Rahman fi tafsiril Kur'an cewa: "Haka nan ma kamar hadisin Sakalain wanda yake an tabbatar da ingancinsa kamar yadda 'yan'uwanmu Ahlul Sunna suka ambace shi cikin littattafansu suka kawo ruwayarsa daga sahabbai wadanda suka ji shi daga wajen Manzon Allah (s.a.w.a.):

"Ni mai bari muku Nauyaya guda biyu ko kuma halifofi guda biyu, Littafin Allah da zuriyata, Ahlulbaitina, wadanda idan kun yi riko da su ba za ku bata ba har abada, su ba za su rabu da juna ba har sai sun riske ni a bakin tafki".

(1). Imam Ali bn Abi Talib (a.s)

(2). Abdullahi bn Abbas.

(3). Abu Zar Giffari

(4). Jabir al-Ansari.

(5). Abdullahi bn Umar

(6). Hudhaifa bn Usaid.

(7). Zaid bn Arkam.

(8). Abdurrahman bn Awf.

(9). Dhamratul Aslami.

(10). Amir bn Laili.

(11). Abu Ra'fi'.

(12). Abu Huraira.

(13). Abdullah bn Handab

(14). Zaid bn Thabit.

(15). Ummu Salama.

(16). Ummu Hani.

(17). Khazima bn Thabit.

(18). Sahl bn Sa'ad.

(19). Adi bn Hatam.

(20). Ukba bn Amir.

(21). Abu Ayyub Ansari.

(22). Abu Sai'd al-Khudri.

(23). Abu Shuraih Khuza'i.

(24). Abu Kadama Ansari.

(25). Abu Laili.

(26). Abu Haitham bn Al-Tayhan.

Allama al-Balagi ya ci gaba da cewa: Wadannan su ne muka riga muka ambaci sunayensu bayan Ummu Hani. Kowannensu ya ruwaito shi, shi kadai, kamar wadanda suka gabace shi, sun tsaya a dandalin Kufa tare da mutum bakwai Kuraishawa, suka tabbatar da cewa sun ji wannan hadisi daga Manzon Allah (s.a.w.a.), adadinsu kuwa shi ne talatin da uku.

Kuma abu Nu'aim Al-Isfahani ya ruwaito shi cikin littafin Munkabatu al-Mudahharin da isnadi daga Jabir bn Mad'am da kuma wani isnadin daga Anas bn Malik da Al-Barra'u bn Azib, haka nan Muwaffak bn Ahmad ya ruwaito shi daga Amr bn al-As.

Da wuya a sami wani littafin hadisi babba ko karami ko littafin falaloli da Ahlussunna suka rubuta wanda bai kawo wannan hadisin ba, daga farkon wadanda suka kawo hadisin daga hadda da kuma zukatan mahaddata har zuwa takardun malaman hadisi. Kuma bai gushe ba ana ruwaito shi daga sahabbai guda ko masu yawa. Ta yiwu ma a ruwaito shi daga sama da sahabbai ashirin a littafi guda, ko dai a game kamar yadda ya zo cikin littafin Sawa'ikul Muhrika, ko kuma da isnadi rarrabe kamar yadda ya zo cikin littattafan al-Sakhawi da Suyudi da Samhudi da dai sauransu".

Sannan sai ya ce: "Malaman Imamiyya sun ruwaito shi cikin litattafan-su da isnadinsu masu maimaita juna daga Imam Bakir, Ridha da Kazim da Sadik (a.s.) daga iyayensu (a.s.) daga Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma wadansu isnadan na daban daga Amirul Muminina (a.s) da Umar da Ubayyu da Jabir da Abu Sa'id da Zaid bn Arkam da Zaid bn Thabit da Huzaifa bn Usaid da Abu Huraira da sauransu, dukkanninsu sun ji daga Manzon Allah (s.a.w.a.)([63]) .

A cikin Musnad na Ahmad bn Hambal, ya ruwaito ta hanyar Abi Sa'id al-Khudri daga Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:

"Ni na kusanta da a kira ni in amsa, ni kuma mai barin nauyayan abubuwa ne guda biyu tare da ku, Littafin Allah Mai Girma da Daukaka da kuma Ahlulbaitna, shi Littafin Allah igiya ce da aka sako daga sama zuwa kasa. Kuma lalle Mai Tausasawa Masani, Ya ba ni labarin cewa baza su taba rabuwa da juna ba har sai sun iske ni a bakin tafki, don haka ku kula da yadda za ku rike su a bayana([64]) ".

Haka nan kuma idan muka duba za mu ga kusan dukkan maruwaita sun ruwaito wannan hadisi da ke gwama Ahlulbaiti (a.s) da Littafin Allah Mai Tsarki. Daga wannan ne musulmi za su fahimci cewa Ahlulbaiti (a.s) su ne makoma baicin Littafin Allah kuma su ne aka bar wa amanar Littafin har su isa ga tabki.

2- Hadisus Safina (Hadisin Jirgin Ruwa)

Yayin da Hadisus Sakalain yake gwama Ahlulbaiti (a.s) da Alkur'ani waje guda domin nauyin da aka dora musu na bayyana Alkur'anin da kwaranye boyayyun abubuwansa da asirorinsa da abubuwan da ke kewaye da shi, to wannan hadisi na Safina kuwa yana bayyana wa al'umma ne cewa su Ahlulbaiti (a.s) su ne jirgin tsira, kuma hanyar kubutar wannan al'umma bayan Manzon Allah (s.a.w.a.). Domin haka, lallai rashin riskan wannan jirgin da rashin hawansa, zai ja wadanda suka ki shiga jirgin zuwa ga nutsewa da halaka. Domin kin binsu, kin bin ja-gora zuwa gabar shiriya da tsira ne.

Al-Shibrawi al-Shafi'i ya nakalto daga Rafi Maulan Abu Zarri, ya ce: "(Wata rana) Abu Zar (r.a.) ya hau dokin kofar Ka'aba, ya kama marikin kofar ya dogara da shi, sai ya ce: "Ya ku mutane, wanda ya sanni to ya sanni, wanda kuma bai sanni ba, to ni ne Abu Zar, na ji Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:

"Ahlulbaitina tamkar jirgin Nuhu suke, wanda ya hau shi ya tsira wanda kuwa ya ki hawa ya fada wuta". Na kuma ji Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Ku sanya Alayena (agareku) matsayin da kai yake da shi a jiki, kuma matsayin idanu ga kai. Domin shi jiki baya shiryuwa sai da kai, shi kuma kai ba ya shiryuwa sai da idanu([65]) ".

Abu Nu'aim([66]) ya ruwaito ta hanyar Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas, ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:

"Misalin Ahlulbaitina a cikinku, tamkar jirgin (Annabi) Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya ki hawa ya nutse (ya halaka)([67]) ".

An ruwaito ta hanyar Anas bn Malik, cewa, ya ce Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Abin sani kawai shi ne cewa, misalin Ahlulbaitina a cikinku, kamar jirgin Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya ki hawansa ya halaka([68]) ".

Suyudi ma ya ruwaito wannan hadisin cikin littafinsa Durrul Mansur karkashin tafsirin fadin Allah Madauka-kin Sarki cewa: "Kuma lokacin da Muka ce: "Ku shiga wannan alkarya, sa'an nan ku ci daga gare ta, inda kuka so, bisa wadata, kuma ku shiga kofa kuna masu tawali'u, kuma ku ce: "Kayar da zunubai" Mu gafarta muku laifukanku". Inda ya ce: "Ibn Abi Shaiba ya fitar da hadisi daga Aliyu bn Abi Talib (a.s.) ya ce: "Abin sani dai, misalinmu (Ahlulbaiti) cikin wannan al'umma kamar misalin jirgin Nuhu ne, kuma kamar Kofar Yafuwa (Hidda) ce([69]) ".

Al-Muttaki ya ruwaito shi cikin littafin Kanzul Ummal (juzu'i na 6 shafi na 216) cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Misalin Ahlulbaitina a cikinku, tamkar jirgin Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya ki hawansa ya halaka, kuma tamkar kofar Hidda ne ta Bani Isra'ila". Sannan ya ce Dabarani ma ya ruwaito wannan hadisi daga Abuzarri([70]) .

3- Hadisin Aminta Daga Sassabawa

A cikin wannan hadisin, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana bayyana rawar da Ahlulbaiti (a.s) ke takawa a fagen akida da siyasa. Domin mafi hadarin abin da yake samun al'umma shi ne rarraba da sabawa cikin ra'ayi da akida da kuma fuskantarwa ta siyasa. Don haka ne ya sa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana tsoratar da al'ummarsa wannan fitinar, ya kasance yana tsare-tsare saboda hadin kanta da riko da juna ta bangaren tunani da siyasa. Kana kuma yake fuskantar da al'ummar tasa zuwa ga lizimta da riko da Ahlulbaitinsa da komawa gare su. A saboda hakan ne kuma, ya siffanta su da cewa su masu lizimtar Alkur'ani da kiransa ne, kuma ba za su rabu da juna ba har ranar tashin kiyama. Ya kuma siffanta su da cewa su jirgin tsira ne, kuma kofar yafuwar zunubbai. To a nan kuma yana siffanta su ne da cewa su ne mattara, kuma su ne madogara mai hada kan wannan al'umma ta musulmi ne, da kuma cewa riko da su da rayuwa bisa tafarkinsu lamuni ne daga rarraba da sabawa.

Al-Dabarani ya kawo hadisi daga Ibn Abbas (r.a.) cew, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Taurari aminci ne ga mazauna kasa daga nutsewa (halaka), Ahlulbaitina kuwa aminci ne ga mazauna kasa daga sassabawa (rarrabuwa)([71]) ".

Muhibbuddin Dabari ya ruwaito daga Aliyu (a.s.) yana cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Taurari aminci ne ga mazowa sama, idan taurari suka tafi, mazowa sama sai su tafi, Ahlulbaitina kuwa aminci ne ga mazowa kasa, idan Ahlulbaitina sun tafi, mazowa kasa sai su tafi". Sai al-Dabarani ya ce: "Ahmad bn Hambal ya ruwaito wannan hadisi cikin al-Manakib([72]) .

4- Hadisul Kisa'i (Hadisin Mayafi)

Hadisin Mayafi shi ne hadisin da ya zo daga Manzon Allah (s.a.w.a.) dangane da Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.) yayin da Ayar Tsarkakewa ta sauka. Mun riga da dai mun gabatar da wannan hadisi kuma mun yi magana a kan shi tare da kawo ra'ayuyyukan wasu malaman tafsiri, da kuma ruwayoyin da suka yi batun wadannan wadanda aka tsarkake a cikin babin "Ahlulbaiti (a.s) Cikin Alkur'ani". To amma a nan za mu kawo wasu ruwayoyi ne daban domin karfafa wannan fikirar da kuma kafa wannan manufar da Manzon Allah (s.a.w.a.) yake da ita wajen yin hakan (wato lullube su da mayafinsa da kuma yi musu addu'a).

Hanyoyin da wannan hadisi ya zo suna da yawan gaske cikin littattafan hadisi da ruwaya da tafsiri, to amma za mu ambaci wasu daga cikinsu ne kawai:

"Dangane da abin da aka ruwaito daga Ummu Salama, matar Annabi (s.a.w.a), Imam Ahmad ya ruwaito shi cikin Musnad dinsa har ya zuwa ga Ummu Salama, inda ta ce: "Wata rana Manzon Allah (s.a.w.a.) yana dakina, sai wani hadimi ya zo ya ce: 'Aliyu da Fadima na nan bakin kofa', sai ta ce: sai Annabi (s.a.w.a) ya ce da ni: "Ki tashi ki kauce wa Ahlulbaitina". "Sai na tashi na kauce gefe guda. Sai Aliyu da Fadima da Hasan da Husaini suka shigo. A yayin nan Hasan da Husaini suna yara kanana, sai Annabi (s.a.w.a) ya dauke su ya dora su a kan cinyarsa, ya sumbace su, ya rungume Aliyu da hannunsa, Fadima kuma da dayan, sannan ya lullube su da wani bakin mayafi, ya ce:

"Ya Allah! Zuwa gare Ka ba zuwa wuta ba, ni da Ahlulbaitina". Sai Ummu Salama ta ce: 'Da ni ya Manzon Allah', sai ya ce: "Na'am da ke([73]) ".

Al-Wahidi ya ruwaito cikin littafinsa Asbabun Nuzul marfu'i ta hanyar Ummu Salama (r.a.) ta ce: (Wata rana Annabi (s.a.w.a) ya kasance a dakinta sai Fadima (a.s.) ta zo da tukunya da wani abinci na alkama a ciki, sai ta shiga da shi. Sai yace da ita: "Ki kira mini mijinki da 'ya'yanki biyu". Sai Ali da Hasan da Husaini suka zo, suka shiga suka zauna suna cin abincin, Annabi (s.a.w.a) kuma yana zaune a kan wani benci, a kan wani mayafi wanda aka saka a Khaibara. Sai Ummu Salama ta ce: Ni kuma ina cikin dakin, kusa da su, sai Annabi (s.a.w.a) ya kama mayafin ya lullube su da shi, sannan ya ce: "Ya Allah! Mutanen gidana, kebantattuna (kenan), to Ka tafiyar da kazanta daga gare su Ka tsarkake su, tsarkakewa".

Sai ta ce: Sai na shigar da kaina, na ce: "Ni ma ina tare da ku, Ya Manzon Allah". Sai ya ce: "Ke kina tare da alheri, ke kina tare da alheri". Sai Allah Mai girma da Daukaka Ya saukar da ayar:

"...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa([74]) ". (Surar Ahzabi, 33:33)

5- Hadisin Soyayya

Mun riga da mun yi magana kan Hadisin Soyayya wajen tafsirin Ayar Soyayya, kuma mun ambaci wasu masu ruwaya da suka ruwaito shi da kuma daga wajen wadanda suka ruwaito shi. A nan za mu sake ambaton hadisin ta hanyoyin daban ne, kuma zai kasance mai amfani mu ambaci sashin abin da ya taho daga Annabi (s.a.w.a) a kan son Ahlulbaiti (a.s) da kaunarsu a wasu ruwayoyin na daban.

(Imam Ahmad da Dabarani duk sun ruwaito daga Ibn Abbas (r.a.) ya ce: "Yayin da Ayar Soyayya, wato "Ka ce: "Bana tambayarku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ta sauka, sai mutane suka ce: Ya Manzon Allah, su wane ne makusanta wadanda soyay-yarsu ta wajaba a kanmu?, sai yace: "Aliyu da Fadima da 'ya'yansu guda biyu".

Al-Bazzaz da Dabarani sun ruwaito cewa Hasan dan Aliyu (a.s.) yayi huduba wata rana yana cewa: "Wanda ya sanni to ya sanni, wanda kuwa bai sanni ba, to ni ne Hasan dan Muhammadu (s.a.w.a). Ni ne dan Mai albishir, ni ne dan Mai gargadi, ni ne dan mutanen gida wadanda Allah Ya farlanta son su a kan kowane musulmi, Ya kuma saukar a kansu (da ayar), "Ka ce: Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta. Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, Za mu kara masa kyau a cikinsa". To aikata kyawawan shi ne soyayyarmu, Ahlulbaiti([75]) ".

Al-Saddi ya ruwaito daga Abi Malik daga ibn Abbas (r.a.) dangane da fadin Allah Madaukaki cewa: "...wanda ya aikata wani abu mai kyau, Za mu kara masa kyau a cikinsa".

Al-Saddi ya ruwaito daga Abi Malik daga ibn Abbas (r.a.) dangane da fadin Allah Madaukaki cewa: "...wanda ya aikata wani abu mai kyau, Za mu kara masa kyau a cikinsa". Inda ya ce: "Soyayyar ta Alayen Muhammadu (s.a.w.a) ce([76]) ". Hadisan da suka zo game da so da kaunar Ahlulbaiti (a.s) da kuma yin musu da'a da lizimtarsu, ba za su kirgu ba cikin wannan dan karamin littafi, sai dai mun zabi sashi ne daga cikinsu kawai, don kuwa kowanne daya daga cikinsu (Ahlulbaiti) (a.s.) rana ce mai haske a cikin littattafan hadisi da ruwayoyi.

To amma domin a kara arzurta mai karatu da kara karfafa abin da zai kara masa sanin Ahlulbaiti (a.s) da kuma karfafa dangantaka da su, da mai da shi mai ta'allaka da su, mai rayuwa bisa tafarkinsu, don ya samu nasarar samun cetonsu, bari mu sake ambaton wasu daga cikin hadisan da suka zo game da su:

(Dabarani ya fitar da hadisi cikin littafin al-Awsad daga ibn Hajar (r.a.) cewa; "Karshen abin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya furta shi ne: "Ku wakilce ni cikin Ahlulbaitina([77]) ").

(Dabarani ya fitar da hadisi cikin littafin Al-Awsad daga Jabir bn Abdullah (r.a.) ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi mana huduba, na ji yana cewa: "Ya ku mutane! (Duk) wanda ya fusata mu, mu Ahlulbaiti, Allah Zai tashe shi ranar kiyama yana bayahude([78]) ".

(Muslim da Tirmizi da Nasa'i duka sun ruwaito daga Zaid bn Arkam cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ina tunatar da ku Allah game da Ahlulbaitina([79]) ".

Alkhatib ya fitar a cikin littafin Tarihinsa daga Aliyu (r.a.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Cetona ga al'ummata, na ga wanda ya so Ahlulbaitina([80]) ".

6- Wasu Ruwayoyi Na Daban

Kamar dai yadda muka bayyana, hadisai da ruwayoyi daga Manzon Allah (s.a.w.a.) game da Ahlulbaitinsa (a.s.) suna da yawan gaske, kuma ba za su kidayu ba a wannan karamin littafin. Malamai da masu hadisi sun kebance musu litattafai, ko kuma fasulla a littattafan hadisai, ko kuma sun ambata a wuraren da suka dace cikin litattafan tafsiri da ruwaya. Ga kadan daga ciki: "Mu Ahlulbaiti ba a gwada mu da kowa([81]) ".

A cikin wannan hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.) yana bayyana mukamin Ahlulbaiti (a.s) ne, da kuma matsa-yinsu madayanci, domin ya sanar da al'umma mahal-linsu, ya kuma shiryar da ita zuwa ga riko da su da lizimtar hanyar su a bayansa, domin a auna su da wasu wadanda ba su ba, don a gani.

A cikin wani hadisi na daban kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana magana ne kan Ahlulbaitisa (a.s.), inda yake cewa: "Mu Ahlulbaiti, Allah Ya zaba mana lahira bisa ga duniya, kuma lalle Ahlulbaitina za a nuna musu son kai da tsanani da kora cikin garuruwa, har wasu mutane za su zo ta nan - sai ya yi nuni da hannunsa ta gabas - ma'abutan bakar tuta, za su tambayi hakki, ba za a ba su ba, za su yi yaki kuma su yi nasara. Za a ba su abin da suka so kuma ba za su karbe shi ba har su mika ta (tutar) ga wani mutum daga Ahlulbaitina, har sai ya cika duniya da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci. To duk wanda ya riski wannan ya taho musu ko da da jan ciki ne a kan kankara([82]) .

".

(Dailami ya kawo hadisi daga Abu Sa'id (r.a.) cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Fushin Allah ya tsananta kan wanda ya cutar da ni dangane da Ahlulbaitina([83]) ". (Daga Aliyu (r.a.) ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:

"Ku yi wa 'ya'yanku tarbiyya kan halaye guda uku: son Annabinku da son Ahlulbaitinsa da kuma karatun Alkur'ani, domin mahaddatan Alkur'ani na cikin inuwar Allah a ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa, tare da AnnabawanSa da ZababbunSa([84]) "). (Dabarani ya ruwaito daga Ibn Abbas (r.a.) yana cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:

"Digadigan bawa ba za su gushe ba har sai an tambaye shi abubuwa hudu: Kan rayuwarsa, yadda ya karar da ita; da jikinsa, yadda ya tsufar da shi, da dukiyarsa, yadda ya kashe ta da inda ya same ta da kuma soyayyarmu, Ahlulbaiti([85]) ").

A wata ruwayar kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana shiryar da al'ummarsa zuwa ga Ahlulbaitinsa, yana kuma bayyana matsayinsu na ilmi, da kuma fuskantar da al'ummar zuwa gare su yayin da fitinu suka tsananta, ra'ayoyi kuma suka sassaba. Yana gwama su da Littafin Allah, domin su ne malamai masu bayyana abin da Alkur'ani ya kunsa, masana hakikaninsa da abubuwan da ya tattara.

(Dabarani ya fitar da hadisi daga Al-Mudallabi bn Abdullahi bn Handabi daga babansa, ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi mana huduba a Juhfa, ya ce: "Ashe ban fi ku cancanta ba a kan kanku", sai suka ce: "Haka nan ne Ya Manzon Allah". Sai ya ce: "To ni mai tambayar ku ne kan abubuwa biyu: kan Alkur'ani da Ahlulbaitina([86]) ").

Alkur'ani Mai Girma A Wajen Malaman Mazhabar Ahlulbaiti (a.s)

"Lalle Mu ne, Muka saukar da Ambato (Alkur'ani), kuma lalle Mu, hakika masu kiyayewa ne gare shi". (Surar Hijr, 15: 9)

Alkur'ani littafin Allah ne da wahayinSa abin saukarwa a kan AnnabinSa mai daraja, Muhammadu dan Abdullahi (s.a.w.a). Littafin da Allah Ya kiyaye shi daga jirkita da gurbata. Wannan wahayin Allah tsarkakakke, wanda hannun mai jirkitawa bai taba shi ba, duk wata barna bata samunsa, ko ta baya ko ta gaba. Shi a yau yana nan kamar yadda ya sauko wa Manzo Amintacce (s.a.w.a), ba tare da wata tawaya ko kari ba. Shi ne mabubbugar shari'a, daga gare shi ake fitar da hukumce-hukumce, shi ne ma'auni sunna, magwajin fahimta da tunani, shi ne mabubbugar wayewar ilmomin Musulunci kana kuma tushen alherin dan'Adam da tsirarsa.

Hakika musulmi sun zazzaga da Alkur'ani tsakanin-su, daga tsara zuwa wata tsarar, suna nakaltar sa da kiyayewa da kula da shi kamar yadda Jibrilu (a.s.) ya saukar da shi ga Manzon Allah (s.a.w.a.). Wannan kuwa shi ne abin da musulmi suka dace a kai, kamar yadda suka hadu a kan karyata ruwayoyi raunana na karya wadanda suka sabawa wannan ijma'i na malamai kan rashin gurbatan Alkur'ani ta kowane bangare.

Babban malamin tafsirin nan wanda ya rubuta shahararren littafin tafsirin nan na Majma'ul Bayan fi Tafsiril Kur'an, Allama Shaikh Abu Ali al-Fadhl bn Hasan Dabrisi([87]) (Allah Ya daukaka mukaminsa), wanda ake daukar tafsirinsa a matsayin mabubbuga kana abin komawa ga malamai da masu tafsiri, ya ce:

"Akwai irin wadannan maganganu (marasa tushe) kan kari ko ragi cikin Alkur'ani, da ba sa ma bukatan magana a kansu. To amma dangane da kari, an hadu kan cewa rashin ingancin hakan, amma batun ragi, wasu jama'a daga cikin abokanmu da wasu mutane daga cikin 'yan Sunna sun ruwaito cewa akwai canji ko tawaya a cikin Alkur'ani. To amma ingantacciyar magana a gurinmu ita ce sabanin hakan (wato babu wata tawaya ko ragi a cikin Alkur'ani), hakan kuwa shi ne abin da Murtadha([88]) (Allah Ya tsarkake ruhinsa) ya bayyana ya kuma yi bayani a kai. A wurare da dama ya ambata cewa ilimin da ake da shi kan ingancin nakalto Alkur'ani kamar ilmin da ake da shi kan garuruwa, manyan abubuwan da suka faru, shahararrun littattafa da rubutattun wakokin larabawa, lallai an sami kula mai tsanani, bukata kuwa ta tabbata kan nakaltar Alkur'ani da kiyaye shi. Bukatar da kular sun kai matsayin da nakalto shahararrun littattafa da wakokin da muka ambata ba su samu ba, domin Alkur'ani mu'ujizar annabta ne, a nan ake daukar ilmomin shari'a da hukumce-hukumcen addini. Malaman Musulunci sun kai matuka wajen kiyaye shi da kare shi har sukan san duk abin da a ka saba cikinsa game da li'irabinsa, kira'arsa, haruffa da kuma ayoyoyinsa, to ya ya zai yiwu a ce an jirkita shi ko kuma an tauye shi duk da wannan kula mai tsanani da kuma tsarewa matsananciya..."

Ya kuma kara da cewa: "Lalle ilmi a kan tafsirin Alkur'ani da sassaninsa da kuma ingancin nakalto shi kamar ilmi ne a kan jumlarsa, kuma hakan yana bisa tafarkin abubuwan da aka sani ne bisa larura cikin littat-tafai wallafaffu, kamar littafin Sibawaihi da Al-Mazanni. Masu kula da wannan sha'ani (nahawu) sun san littattafan nan a fasalce tamkar sanin da suka yi musu a jumlace, ta yadda da wani zai shigar da wani babi na nahawu cikin littafin Sibawaihi, wanda da baya ciki, to da sun gane da kuma fahimtar cewa an sanya shi ne cikin littafin daga baya, ba daga cikin asalin littafin yake ba, haka nan ma yake game da littafin Al-Mazanni. Kuma sananne abu ne cewa kula da nakalin Alkur'ani da tsare shi, yafi gaskata bisa kula da tsare littafin Sibawaihi da kuma Diwanin mawaka".

Ya kuma sake cewa: "Shi Alkur'ani ya kasance a zamanin Manzon Allah (s.a.w.a.) a tare yake a wallafe kamar yadda yake a yau. Ya kafa hujja da cewa Alkur'ani ya kasance ana darasinsa ana kuma haddace shi a wancan zamani har aka ayyana wata jama'a cikin sahabbai da cewa sun haddace shi, da kuma cewa ana bijiro da shi ga Manzon Allah (s.a.w.a.) ana karanta masa, sannan kuma wata jama'a daga cikin sahabbai kamar su Abdullahi bn Mas'ud da Ubayyu bn Ka'ab da sauransu, sun sauke Alkur'ani gaba ga Annabi (s.a.w.a) sau da yawa. Duk wannan yana nunawa cewa shi Alkur'ani ya kasance tararre ne jerarre, ba yankakke ba, ba kuma a watse yake ba. Ana riskar wannan hakika kuwa ba tare da bukatar wani dogon tunani ba.

Sayyid Murtadha ya ci gaba da cewa wanda ya saba wa wannan ra'ayi daga cikin Imamiyya da Hashawiyya, to ba a dogaro da wannan sabawa ta su domin sabawa da wannan ra'ayi abin dangantawa ne ga wasu mutane daga cikin ma'abuta hadisi wadanda suka nakalto hadisai masu rauni, amma suna zaton ingantattu ne. Kuma ba a barin abin da aka tabbatar da ingancinsa domin irin wadannan raunanan hadisai([89]) ". Sannan kuma sai ya ce: "Abin da ya shahara a wajen malaman Shi'a da masu bincikensu, kai ba ma kawai shahara ba har ma babu jayayya a cikinsa, shi ne rashin ragi ko kari cikin Alkur'ani([90]) ".

Shaihin malaman hadisi Muhammad bn Ali bn Husain bn Babawaihi al-Kummi, wanda ake wa lakabi da "Saduk" (ya rasu a shekara ta 381), kuma mawallafin littafin Man La Yahdhuruhul Fakih da kuma dimbin muhimmman littattafai, ya fada cikin littafinsa mai suna I'itikadatul Saduk cewa:

"Akidarmu game da Alkur'ani mai girma wanda Allah Ya saukar wa AnnabinSa Muhammadu (s.a.w.a) shi ne abin da yake cikin bangwayen nan biyu, shi ne wanda yake hannun mutane bai wuce wannan ba - har ya zuwa inda yake cewa - kuma duk wanda ya danganta gare mu cewa muna fadin wai Alkur'ani ya fi haka to shi makaryaci ne". Sannan ya shiga kawo hujjoji kan hakan, mai son karin bayani yana iya duba cikamakin maganan tasa([91]) .

Shugaban jama'ar Shi'a, Abu Ja'afar Muhammad bn Husain al-Dusi (wanda ya rasu a shekara ta 460 hijiriyya), mawallafin littafin Al-Khilaf da Al-Mabsud da Al-Tahzib da Al-Istibsar da sauransu, ya fada cikin littafinsa na tafsiri mai suna Al-Tibyan cewa([92]) :

"Amma zancen kari (cikin Alkur'ani) da tawaya, suna daga cikin abubuwan da su ma ba su dacewa da shi domin kari cikinsa, abu ne wanda aka yi ijima'i kan batacce ne. Tawaya kuwa, bisa zahirin ra'ayin musulmi, babu shi, hakan kuwa shi yafi dacewa da abin da ya inganta a mazhabarmu, shi ne kuwa abin da Al-Murtadha ya goyawa baya, shi ne kuma zahirin ruwayoyi, - har zuwa inda yake cewa - ruwayoyinmu kuma suna karfafa juna kan kwadaitar da karanta shi da riko da abin da yake ciki, da dawowa da duk wata sassabawar hadisai masu magana kan rassa (furu'a) zuwa ga Alkur'ani. Hakika an ruwaito wani hadisi da ba wanda yake musa shi, daga Annabi (s.a.w.a) cewa, Annabi (s.a.w.a) ya ce:

"Ni mai barin Nauyayan Abubuwa guda Biyu ne tare da ku, wadanda idan kuka yi riko da su ba za ku bata a baya na ba: (su ne) Littafin Allah da Zuriyata, Ahlulbaiti, don ba za su rabu da juna ba har sai sun riske ni a bakin tafki".

Wannan yana nuni da cewa shi Alkur'ani samamme ne a dukkan zamani, domin ba zai yiwu ya yi umurni da riko da abin da ba za mu iya riko da shi ba, kamar yadda Ahlulbaiti (a.s) da wanda bin fadarsa yake wajibi samammu ne a duk lokaci. To idan wanda yake tare da mu an hadu a kan ingancinsa to ya kamata mu shagaltu da tafsirinsa da bayyana ma'anoninsa, mu bar komawa bayan wannan).

Allama Shaikh Muhammad Jawad al-Balagi ya tabbatar da wannan hakika cikin tafsirinsa Ala'ur Rahaman fi Tafsiril Kur'an, wato dawwamar Alkur'ani da kubutarsa daga jirkita da gurbata, inda yace:

"Haka Alkur'ani ya ci gaba a kan wannan gagarumin tafarki daga wannan al'umma zuwa wancan, kana iya ganin duban dubata na littattafa da mahaddatansa, kuma haka aka ci gaba da buga wasu Kur'anan daga wasu, wasu daga cikin musulmi suna ji da karanta shi daga wasunsu……ko da yake muna cewa dubbai ne kawai, amma fa daruruwan dubbai ne ko ma a ce dubban dubbai. Babu shakka, babu wani al'amari na tarihi da ya sami irin wannan inganci da wanzuwa wacce take a sarari tamkar abin da Alkur'ani ya samu, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya yi alkawari cikin Surar Hijr:

"Lalle Mu ne Muka saukar da Ambato (Alkur'ani), kuma lalle Mu, hakika, Masu kiyayewa ne a gare shi". Da kuma fadinSa Ta'ala cikin Surar Kiyamati: "Lalle ne wajibi ne a gare Mu, Mu tara shi, Mu (tsare maka) karatunsa".

To idan ka ji wani abu kan jirkitar Alkur'ani da bacewar sashensa, daga bakaken ruwayoyi, kada ka ko kula su sannan ka fadi duk abin da ilmi yake yarda da fadinsa na daga sassabawar su da rauninsu da raunin masu ruwaitosu da sabawarsu wa musulmi, da kuma raunin da abin ruwaitowarsu - rusashshe - ya zo da shi([93]) ".

Shehin malamin ya ci gaba da cewa cikin tafsirinsa karkashin fasalin: "Maganar Imamiyya Kan Cewa Babu Tawaya Cikin Alkur'ani", inda yace: "Ba a boye yake ba cewa Shaihin masu hadisi wanda aka san shi da kula da abin da yake ruwaitowa, wato Shaikh Saduk (Allah Ya kyautata makwancinsa) ya fada cikin littafinsa al-I'itikad cewa: "Akidarmu ita ce cewa Alkur'anin nan da Allah Ya saukar wa AnnabinSa (s.a.w.a) shi ne dai wanda yake cikin bangwayen nan biyu (wanda kowa ya sani) bai kuma wuce haka ba, wanda kuwa ya danganta mana cewa mun ce ya fi haka, to shi makaryaci ne".

Shaikh al-Mufid a littafinsa na al-Makalat ya kawo cewa wasu jama'a daga cikin Imamiyya sun ce shi Alkur'ani ba a tauye ko da kalma ko aya ko sura daga cikinsa ba, amma an shafe abin da yake tabbatacce cikin Mus'hafin Amirul Muminina (a.s) na tawili da tafsirin ma'anoninsa bisa hakikanin saukarwa.

A cikin littafin Kashful Gida'i fi Kitabil Kur'an, a fasali na takwas, kan tawayar Alkur'ani an ce: Babu shakka cewa an kiyaye shi daga tawaya da kiyayewar Sarki Mai sakamako, kamar yadda Alkur'ani ya yi nuni da hakan a sarari, kuma malamai suka hadu a kai.

Shaikh Baha'i yana cewa: "Kuma haka nan an yi sabani kan aukuwar kari da tawaya cikinsa, abin da ya inganta shi ne shi Alkur'ani mai girma kiyayayye ne daga hakan, kari yake ko ragi, kuma lalle fadin Allah Madaukakin Sarki cewa: "Kuma lalle Mu, hakika Masu kiyayewa ne gare shi" yana nuni da kuma tabbatar da hakan. Al-Mukaddas al-Bagdadi cikin Sharhin al-Wafiya yana cewa:

"Hakika sanannen zancen Imamiyya kan ragi a cikin Alkur'ani shi ne rashin hakan a cikinsa", har ila yau ya ce an samu daga Shaikh Ali bn Abdul Ali cewa shi ya wallafa littafi na musamman kan kore tawaya cikin Alkur'ani daga hadisai, inda ya ce idan hadisi ya zo bisa sabanin dalili na Littafin Allah da Sunna ingantacciyar ko kuma ijma' (abin da malamai suka hadu a kai amma da sharadin akwai wani Imami a cikinsu), kuma ba zai yiyu a yi masa wani tawili ba ko kuma daukansa da wasu ma'anoni ta wasu fuskoki ba, to wajibi ne a jefar da shi([94]) ".

Marigayi Allama kana Mujahidin zamani Shaikh Muhammad Husain Kashif al-Ghida ya fada cikin littafinsa mai suna Aslul Shi'a wa Usuluha cewa:

"Lalle wannan Littafin da yake hannu musulmi shi ne Littafin da Allah Ya saukar masa (Annabi) domin gajiyarwa da kalubale, da kuma cewa babu nakasi a ciki, babu jirkita, babu kuma kari, a kan hakan ne (malamai) suka hadu a kai".

Sharifi mai kira zuwa ga gyara, Sayyid Abdul Husain Sharafuddin ya fada cikin littafinsa Fusulul Muhimma fi Talifil Umma cewa: "Alkur'ani mai hikima, barna bata zuwa masa a zamaninsa ko a bayansa. Abin sani dai shi ne a cikin bangwaye biyun nan, shi ne kuma a hannun mutane, ba a kara ko da harafi ko kuma a rage wani ba, babu musayyar kalma da wata, ko harafi da wanin harafin. Kuma ko wani harafi cikin haruffan Alkur'ani tabbatacce ne a kowani zamani tun daga zamanin da aka saukar da shi. Sannan ya kasance a tare a wancan zamani mafi tsarkaka, yana rubuce kamar yadda yake a yau. Mala'ika Jibrilu (a.s.) ya kasance yana kawo shi ga Manzon Allah (s.a.w.a.) sau da yawa, dukkan wannan yana cikin al'amurra sanannu wajen masu bin diddigi cikin malaman Imamiyya. Don haka ba a dogara da maganan 'yan Hashawiyya, domin su ba su da fahimta".

Haka nan kuma malamin nan mai yawan bincike, babban mutum, Sayyid Muhsin Amin Husaini Amili ya fadi cikin littafinsa A'ayanu al-Shi'a cewa:

"Babu wani daga cikin 'yan Imamiyya, dadadde ko na yanzu da yake cewa akwai kari, babba ne ko karami, cikin Alkur'ani, face ma dai dukkansu sun hadu a kan rashin kari, hakika wadanda ake dogaro da maganarsu daga cikin masu bin diddigi sun hadu a kan cewa babu abin da ya ragu daga cikin Alkur'ani".

To wannan dai shi ne Alkur'ani mai girma da kuma ra'ayin Imamiyya dangane da shi, shi ne kuma dai a yanzu yake hannu musulmi, kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya zo da shi. Kuma shi mai wanzuwa ne da wanzuwar dan'Adam a kan doron kasa, yana haskaka wa dan'Adam hanyar rayuwa, ya kuma rike hannun al'umma zuwa ga shiriya.

Malamai da masu bincike da masu bin diddigi, suna ganin cewar abin da ke yawo tsakanin wasu mutane na ruwayoyi da zantattuka (marasa tushe) da suke maganar tawayar Alkur'ani, cikin da'irar Ahlussunna da Shi'a, ba kome ba ne face sanyawa ce ta makaryata, wacce babu makawa dole a yi jifa da su.

Haka nan ana samun wasu ruwayoyi wadanda ana yiwa zahirinsu wata fahimta ba tare da zurfafa nazari wajen karanta su da fahimtar su ba, wacce kuma ta sa ake cewa da akwai tawaya cikin Alkur'ani ko kuma samuwar wani Mus'hafi daban kamar yadda al'amarin ya rikitar da wasu mutane, masu muzanta Musulunci kuma suka dauki hakan wata dama ce gare su ta musguwa wa Musuluncin da kuma musulmai da kuma kokarin kawo rarrabuwa tsakaninsu. Kamar abin da aka ruwaito daga Imam Ja'afar bn Muhammad al-Sadik (a.s.), ba tare da kula da ingancin ruwayar ko rashin sa ba. Ga abin da ya ce:

"...amma wallahi - sai ya mika hannunsa zuwa kirjinsa - akwai makamin Manzon Allah (s.a.w.a.) tare da mu, takobinsa da sulkensa, kuma wallahi, muna da Mus'hafin Fadima tare da mu, babu wata ayar Littafin Allah a cikinsa, shi dai shifta ce daga shiftar Manzon Allah (s.a.w.a.) Aliyu kuwa shi ne ya rubuta shi da hannunsa([95]) ".

Hakika wasu sun shiga wahami kan cewa Imam Sadik (a.s.) - wal iyazu billahi - yana ba da labarin samuwar wani Alkur'ani ne ban da wannan Alkur'anin da ke hannunmu, sai wadansu suka dauki wannan waha-mi a matsayin wata hujjar shuka barna tsakanin mutane.

To amma abin da hadisin nan yake nufi a sarari yake, ga mafi raunin mutane, wanda dai ya san harshen larabci. Domin shi Imam Sadik (a.s.) yana cewa ne: "Wallahi muna da Mus'hafin Fadima". Idan muka koma ga kalma Mus'haf cikin harshen larabci zai sa mu fahimci ma'anar wannan magana ta Imam (a.s.).

Ragib al-Isfahani yana cewa: "Sahifa ita ce duk wani abu shimfidadde, kamar shimfidar kunci, ganye ko wani shafi da ake rubutu a kansa, jam'inta kuwa shi ne Saha'if ko kuma Suhuf. Allah Ta'ala Yana cewa: "Suhufin Ibrahima da Musa", "Suna karanta Suhufai tsarkakakku, cikinsu akwai litattafai masu kima".

An ce abin da ake nufi da Suhufan shi ne Alkur'ani, sai Ya sanya su takardu da litattafai a cikinsa domin tara wani abu bayan abin da yake cikin sauran littattafan Allah. Shi kuwa Mus'hafi shi ne abin da aka yi shi mai tattara takardu rubutattu, jam'insa kuwa shi ne Masahif([96]) ).

Saboda haka kalmar Mus'haf, a ma'anonin da muke amfani da su a yau, tana nufin littafi ba suna ne wanda ya kebanta da Littafin Allah (Alkur'ani) ba. Shi suna ne na kowane littafi da ya tattara takardu ko fatu (kamar yadda ake rubutu a jikin fata a zamanin da). Ana kiran Alkur'ani da sunan Mus'haf ne domin shi mai tattare ne da takardu.

Alkur'ani mai girma yana da sunaye daban-daban kamar haka: Alkur'ani, al-Zikr, al-Furkan da kuma al-Kitab([97]) , wahayi dai bai kira shi (Alkur'ani) da sunan Mus'haf ba, kai dai musulmi su suka ba shi wannan suna yayin da suka tara shi, don bayan tarawan ya zamanto wani tari ne na (suhuf) wato takardu.

Saboda haka, lallai tushen rudanin shi ne batun isdilahi (yadda ake amfani da kalmomi) da ma'ana ta lugga a wancan zamanin, wadda ma'anar da mutane suke dauka a cikinsa, yanzu ba a daukar ta a wannan zamanin.

Sannan kuma Imam ya bayyana ma'anar wannan Mus'haf din domin ya kau da rikitarwar da ka iya faruwa, inda ya ce: "Babu wata aya ta Littafin Allah a cikinsa".

Ma'ana, shi ba Alkur'ani ba ne, ba kuma daga Alkur'ani yake ba, ba kuma wahayi ne ba, (shi dai shifta ce ta Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma (rubutun Imam Ali).

Wasu malumma suna cewa wannan Mus'hafin wasu tarin addu'oi da shiryarwa ne wadanda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi shiftar su ga Fadima al-Zahra (a.s.) domin tarbiyyarta da kuma ilmantar da ita.

To wannan yana bayyana mana kuskure, rudani da jirkitarwa da wasu daga cikin musulmi suka yarda da shi a dalilin mummunar fahimta da mugun nufi. Alkur'ani Mai Girma A Ruwayoyin Ahlulbaiti (a.s)

Wanda duk ya yi bitar ruwayoyi da hadisan da suka zo ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) ya kuma karanci tarihin rayuwarsu da alakarsu da Littafin Allah, ba zai sami muhimmanci da kulan da Ahlulbaiti (a.s) suke bayarwa fiye da wanda suke bai wa Littafin Allah, Mai Girma da Daukaka ba, ko a yanayin rayuwarsu ko cikin abin da suka ruwaito da maganganunsu ko cikin abin da suka yi wasiyya ko suka tarbiyyantar ko suka fuskantar da mabiyansu da almajiransu da daukacin 'ya'yan musulmi.

Imam Ja'afar Sadik (a.s.) ya ruwaito daga kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ya ku mutane, lalle kuna gidan dako ne, kuma kuna kan tafiya, tafiyar kuwa tana sauri da ku, kun ko ga dare da yini da rana da wata suna tsufar da kowane sabon abu, suna kuwa kusanto da kowane manisanci suna kawo kowane abin alkawartawa, to ku tanadi shiri wa tafiyar nan mai tsawo". Ya ce: sai Mikdad bn Aswad ya mike, ya ce: Ya Manzon Allah! Mene ne gidan dako?, sai ya ce masa:

"Gidan isarwa da yankewa, to idan fitinu kamar yankin dare mai duhu sun rikitar da al'amurra a kanku, na hore ku da Alkur'ani, domin shi, mai ceto ne abin karbawa ceto, mai jayayya abin gaskatawa. Duk wanda ya sanya shi gabansa zai ja-gorance shi zuwa aljanna, wanda ko ya sanya shi a bayansa zai iza shi zuwa wuta. Shi kuwa ja-gora ne mai shiryarwa zuwa mafi alherin hanya. Kuma shi littafi ne wanda a cikinsa akwai rarrabewa da bayani da riba (ko karuwa) shi ne rarrabewa kuma ba kakaci ba ne, yana da baya da ciki. Bayansa hukumci ne, cikinsa kuwa ilmi ne, bayan nasa gwanin kyau ne da shi, cikin nasa kuwa zurfi ne da shi. Yana da taurari, bisa taurarinsa ma akwai wasu taurarin. Ba a iya kididdigar ababen ban mamakinsa, abubuwan ban sha'awarsa kuma ba sa tsufa. Akwai fitilun shiriya da hikima cikinsa, kuma mai shiryarwa ne zuwa ga masaniya ga wanda ya san sifa. To mai yawo ya yi yawo (cikin Alkur'ani) da ganinsa, kuma dubinsa ya riski sifar domin ya tsira daga halaka ya kuma kubuta daga tsanani. Domin kuwa tunani rayuwar zuciya mai gani ne, kamar yadda mai tafiya cikin duhu yake haskaka hanya da haske. To na hore ku da kubuta mai kyau da karancin dako([98]) ". Imam Sadik (a.s.) yana cewa: "Mahaddacin Alkur'ani, mai aiki da shi yana tare da Mala'iku Marubuta, Masu daraja, Masu da'a ga Allah Ta'ala([99]) ".

Imam Aliyu bn Husain (a.s.) yana cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda Allah Ya ba shi Alkur'ani, sai ya ga cewa an bai wa wani mutum fiye da abin da aka ba shi, to hakika ya rena babban abu, ya kuma girmama karami([100]) ".

Ya zo kuma daga wajen Imam Muhammadu Bakir (a.s.) cewa ya ce Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ya ku jama'a makarata Alkur'ani! Ku ji tsoron Allah Mai Girma da Daukaka cikin abin da Ya dora muku na LittafinSa domin ni abin tambaye ne, ku ma abin tambaya ne. Ni za a tambaye ni kan isar da sako, ku kuma za a tambaye ku ne kan abin da aka dora muku na Littafin Allah da Sunnata([101]) ".

Sannan kuma Imam Sadik (a.s.) yana cewa: "Ya kamata mumini kada ya mutu har sai ya koyi Alkur'ani, ko kuwa yazama cikin koyonsa([102])".

Imam Sadik (a.s.) kuma yana cewa: "Alkur'ani alkawarin Allah ne da bayinSa, to hakika ya kamaci mutum musulmi ya yi dubi cikin alkawarinsa, ya kuma karanta ayoyi hamsin daga ciki a kullum([103]) ".

Imam Sadik din dai yana cewa: "Abubuwa uku za su kai kuka zuwa ga Allah Madau-kakin Sarki: masallacin da aka kaurace masa ba a salla a cikinsa, malamin da ke tsakanin jahilai da kuma Alkur'anin da aka rataye shi kura tana hawa kansa don ba a karanta shi([104]) ".

Imam Sadik (a.s.) yana cewa: "Lalle Alkur'ani rayayye ne ba matacce ba, kuma yana gudana kamar yadda dare da yini suke gudana, kuma kamar yadda rana da wata suke tafiya. Yana kuma tafe ne kan na karshenmu, kamar yadda yake tafe a kan na farkonmu".

Amirul Muminina (a.s) ya ce: "Sannan Allah Ya saukar masa da Littafi, haske ne fitilunsa, ba su mutuwa, fitila ce da haskenta ba ya bishewa, kogi ne da ba a risko zurfinsa; tafarki ne wanda salonsa ba ya bacewa; haske ne wanda ba ya yin duhu, mai rarrabewa wanda karfin hujjarsa ba ya raguwa, bayani ne wanda ba a rusa ginshikinsa, waraka ce wadda ba a tsoron cuta a tare da ita, daukaka ce wacce ba a rinjayar masu taimakon ta; gaskiya ce wadda ba a tabar da masu taya ta. Shi ne taskar imani, kuma tsakiyar shi, shi ne mabubbugan ilmi da kogunan shi; shi ne koraman adalci da tabkunan shi; shi ne murhun Musulunci da ginin shi; shi ne kwazazzabon gaskiya da mafakarta; shi tekun ne da masu kwarfa ba sa iya kwarfe shi; idanuwar ruwa ne masu kwarfa ba su iya karar da shi; wuraren sha ne masu taho masa ba sa kafar da shi; masaukai ne da matafiya ba sa bacewa da hanyarsa, alamu ne wadanda matafiya ba sa makance masa; tsaunuka ne da wanda ya nufe su ba zai wuce su ba. Allah Ya sanya shi mai kashe kishin ruwan malamai; bazaar (mai rayawa) ga zukatan fukaha'u (masana ilmin fikihu); gwadabe mai tara hanyoyin mutanen kwarai; waraka wadda babu wata cuta bayanta; hasken da babu wani duhu tare da shi; igiya ce mai karfi; mafaka ce wadda kololuwarta karerriya ce; daukaka ga wanda ya jibince shi; aminci ga wanda ya shige shi; shiriya ga wanda ya yi koyi da shi; uzuri ga wanda ya yi riko da shi; hujja ga wanda ya yi magana da shi; shaida ga wanda ya yi amfani da shi wajen jayayya; nasara ga wanda ya kafa hujja da shi; mai daukar duk wanda dauke shi; abin hawa ga wanda ya yi aiki da shi; alama (aya) ce ga wanda ya sa lura; garkuwa ga wanda ya nemi kariya da shi; ilmi ga mai kiyayewa; abin fadi ga mai ruwaya; kuma hukumci ne ga mai hukumtawa([105]) ".

Haka nan dai muke fahimtar kimar Alkur'ani da darajarsa a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da kuma tafarkinsu. Ita ce kuwa kima ta hakika wacce Alkur'ani ya yi furuci da ita, wahayi kuma ya siffanta shi da ita "Hakika wannan Alkur'ani yana shiryarwa zuwa hanya da tafi daidai". (Surar Isra'i, 17: 9)

Alkur'ani shi ne hanyar rayuwar al'umma, mabubbu-gar ilmi da shiriya, taskar ma'arifa da wayewa, tafarkin fahimta da tunani, ma'aunin ci gaba da halaye na kwarai, shi ne doka ta ilmi wajen tsara rayuwar dan'Adamtaka, kuma shi ne ma'aji mai tattara al'adun rayuwar mutumtaka da dokokinta.

Ka'idojin Fahimtar Alkur'ani Da Tafsirinsa

A cikin abin da ya gabata, mun ambaci yadda tafar-kin Ahlulbaiti (a.s) da mazhabarsu suka tabbatar mana da cewa Littafin Allah madawwami ne, ba jirkitarwar da ta same shi, shi ne kuma kundin dokokin Ubangiji dawwa-mammu, shi ne tushen shari'a, shi ne ma'auni mai hukumci kan ingancin ruwayoyi da hadisai, shi ne kuma hujja wajen tabbatar da kuskure ko dacewar kowane abu. Hadisi ya zo daga Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa:

"Idan wani hadisi ya zo muku daga gare ni, ku gwada shi da Littafin Allah, abin da ya dace da shi ku karba, abin da ya saba masa kuwa ku yi jifa da shi([106]) ".

Bayan tabbatar wannan da soke dukkan raunanan maganganu na barna, za mu gane cewa tafarkin musulun-ci na asali ya nuna wa musulmi da ma'abuta ilmi da sani hanyar fahimtar Alkur'ani da tafsirinsa da mu'amala da nassin Alkur'ani, ya kuma kayyade mana hanyar. Wannan batu na fahimtar Alkur'ani da tafsirinsa da kuma tawilinsa, batu ne mai tushe, wanda kubutar tunani a Musulunce da ingancin akida da shari'a da masaniyar Musulunci duk sun dogara a kansa ne. Domin duk wani karkata ko takaita ko takaitawa wajen fahimtar Alkur'ani da binciken taskar shari'a da akida da fitar da hukumce-hukumcensa da riskar iliminsa da dokokinsa na zamanta-kewar al'umma da na siyasa, tattalin arziki, tarbiyya, zartar da hukumci da dai sauransu, duk suna kai wa ga karkata da rarrabar musulmi, da kuma yin tawaye ga tsarin asalin addinin Musulunci da tsabtarsa. Wajibi ne a farkon magana kan wannan batu mai tushe da muhimmanci, mu rarrabe tsakanin tafsiri da tawili.

Tafsiri dai a wajen malaman lugga, shi ne: "Gano ma'anar lafazi da kuma fito da ita([107]) ". Tawili kuwa shi ne: "Mai da dayan ma'anoni biyu da lafazi ke iya dauka ya zuwa dacewa da zahirin al'amari([108]) ".

Ahmad Ridha ya ce: "Kalmar tafsiri an dauko ta ne daga kalmar "fassara" wacce aka ciro ta daga "assifru", shi ne kuwa fitarwa da bayyanarwa. Ana cewa "asfaras subhu" wato asubahi ya bayyana, ana kuma cewa "asfaratil mar'atu an wajhiha" wato mace ta fito da fuskarta, an yi amfani da kalmar "asfara" wajen fitowa.

Ko kuma ace kalmar tafsiri an dauko ta ne daga "fasara-yafsiru" kamar "daraba-yadribu" ko "nasara-yansuru" "fasara-yafsiru-fasran. Fasru tana nufin bayyana da fito da rufaffen abu. Mutum ya kan ce "fasartu" ga abu idan ya bayyana shi([109]) ".

Shaikh Tabrisi (Allah Ya daukaki mukaminsa) ya fadi cikin gabatarwar tafsirinsa mai daraja wato Majma'ul Bayan fi Tafsiril Kur'an cewa:

"Tafsiri shi ne fito da manufar lafazi mai rikitarwa, tawili kuwa shi ne maidowa da dayan ma'anoni biyu da lafazi ke iya dauka, ya zuwa ga dacewa da zahiri. Tafsiri shi ne bayani".

Abul Abbas Mubarrid ya ce: "Tafsiri da tawili da ma'ana duk daya suke. An ce 'fasru' shi ne fitowa da rufaffe, tawili kuwa shi ne karshen abu da makomarsa, da abin da al'amarinsa yake komawa gare shi...([110]) ".

Hanyar Da Ake Bi Wajen Tafsirin Kur'ani

Yayin da tafsiri yake bayanin ma'anar kalmomin Alkur'ani da jumlolinsu da kuma fito da ma'anoni a sarari, sannan kuma sashen kalmomin Alkur'ani da jumlolinsa ana iya fassara su da tafsirin zahiri wanda mai yiyuwa ne ya kasance ya yi nisa da manufa ta hakika ga Alkur'ani, shi kuwa tawili shi ne aikin fito da ma'anar da ake nufi, hakan kuwa ta hanyar mayar da ma'anoni da ke ajiye cikin ayar - bayan jujjuya su tsakanin fuskoki biyu ko fiye([111]) - ya zuwa ga makomarsa. Burin da muke so mu cimma a nan shi ne daidaiton tawili da tafsiri a matsayin sakamako. Shi ne kuwa fayyace ma'anonin Alkur'ani da bayanin abin da Allah Madaukakin Sarki Yake nufin bayaninsa ga bayinSa.

Duk wanda ya yi bitar littattafan tafsiri da tafarkin masu tafsiri, zai samu cewa akwai tazara mai fadi da ramuka masu hadari, wadanda sashin masu fassara suka fada, sai suka karkace daga manufar tafsiri domin hanyoyin tafsirin wadanda suka bi da bayanin tawilin da suka yi wa ayoyin Alkur'ani. Wani lokacin a samu sun dogara da raunanan ruwayoyi da aka sossoka, wani loton kuwa a samu sun bi son zuciya sai su tankwarar da Alkur'ani zuwa ra'ayoyin kungiyoyin da suke bi, da kuma son zuciyarsu kebantacciya. Sai ka ga suna kokarin sa ayoyin Alkur'ani su dace da abubuwan da suka auku a tarihi kuma danganta su ga wadansu daidai-kun mutanen da Alkur'anin ba su yake nufi ba. Kai sun ma nemi su sa ayoyin Alkur'ani su dace da girmama ra'ayoyinsu da karkatar su kebantattu.

Misalin karkata cikin tawili shi ne fuskartar da ayoyin Alkur'ani da sashen masu falsafa da ilimin kalami suka yi bayan sun riga sun yi imani da tunani da mazhabobin kalami da falsafa sannan suka tankwara ma'anonin ayoyin zuwa wadannan mazhabobin.

Misali kuma shi ne cewa akwai abin da sashen marubuta da masu tafsiri ke yi na fuskantar da ayoyin Alkur'ani domin su dace da nazarce-nazarcensu na ilimin kimiyya da tunaninsu na tattalin arziki da zamantakewa da siyasa wadanda marubuta da amsu nazari suka bijiro da su suka kuma yadu a zamanin wadannan masu fassara. Suna bin fadar masu nazarce-nazarcen nan ba tare da akwai wata dangantaka ta hakika ko dacewa ta gaskiya ba. Haka nan muke samun yadda ake murda ayoyi zuwa son zuciya, ko ka ga mai tafsiri ya yarda da wasu ra'ayoyi sannan daga baya ya karkata ayoyin Alkur'ani zuwa ra'ayoyi da halaye da dama, tun da can da kuma ma yanzu.

Hakika masu tafsiri da yawa sun fada cikin wannan kuskuren, kuma daga mazhabobi daban-daban, na Ahlussunna ne ko na Shi'a ko kuma waninsu. Bayan sun yi wannan kuskuren sai su dora kawo hujjoji da dalilai don kare wadannan ra'ayoyi nasu.

Idan muka koma ga tafarkin Musulunci na asali wajen tafsiri za mu ga cewa ya yi watsi da wannan tafarki da muka fadi a baya da kuma tabbatar da asasai ingantattu na tafsiri.

Don kuwa tafsiri kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fadi, kuma tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da duk wanda ya bi tafarkinsu ba tare da karkata ba da malaman tafsiri masu lizimta, yana da asasai da ginshikansa wadanda suke shiryar da mai tafsiri da mai bincike zuwa dacewa mayalwaciya.

Bari mu kawo bayanin da ya zo daga Manzon Allah (s.a.w.a.) da Imamai Masu shiryarwa (a.s.) da malaman al'umma kan batun sanya ginshikai wadanda ba su da wata karkata, domin tafsiri da tabbatar da ma'aunai da kuma dokoki masu kiyaye wannan ilmi mai daraja, domin shi ilmi ya ba da gudummawarsa tare da cikakkiyar kula da kubuta daga karkatarwa. Kuma domin wannan ilmi ya wadatar da duniyar dan'Adamtaka da ma'anoni da tunani da fahimce-fahimcen da za a iya riska da kuma hukumce-hukumce, ba tare da wata tawaya ko kirdado ko jidali ko bin ra'ayi ko kuma tankwara tafsirin domin ya bi son zuciya ba.

Allama Dabrisi ya ambata cewa: "Ya inganta daga Annabi (s.a.w.a), ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) cewa: "Tafsirin Alkur'ani ba ya halatta sai da asari (wato hadisi) ingantacce da kuma nassi bayyananne([112]) ".

Lalle Ahlulbaiti (a.s) sun kasance suna bin wannan hanyar, suna kuma watsi da yi wa Alkur'ani tafsirin da ya yi nisa daga wadannan ginshikai guda biyu, wato:

1. Tafsirin Alkur'ani da Alkur'anin, wato wasu ayoyi su yi wa wasu tafsiri.

2. Tafsirin Alkur'ani da ruwayoyi da kuma hadisai ingantattu.

Don haka ne ya wajaba cewa dole tafsirin ya lizimci wadannan ginshikai biyu, cikakkiyar lizimta. Sannan kuma wajibi ne kada mu gafala kan cewa hankali yana da fagensa na asasi da ja-goranci wajen fahimtar Alkur'ani da tafsirin ma'anoninsa da fuskantar da zahirinsa, bisa sharadin cewa shi hankali zai lizimci iyakokin Littafin Allah da Sunnan Ma'aiki (s.a.w.a.), ba zai kuma sabawa tsarinsu ba. Hakika Manzo Mai girma ya ba wa hankali fage fitacce wajen tafsirin Alkur'ani, inda ya ce: "Alkur'ani mai saukin korawa ne, mai fuskoki da yawa; to ku dauki fassarar da ta fi kyau([113]) ". Har ila yau ya ce: "Ku bayyana Alkur'ani kuma ku nemi kebantattun abubuwansa([114]) ".

Alkur'ani mai girma ya bayyana irin rawar da hankali zai taka cikin tafsiri, ya kuma yaba wa ma'abota hankula masu fitar da hukumce-hukumce daga Alkur'ani, yayin da yake cewa: "Da masu istinbadinsa daga cikinsu sun san shi". (Surar Nisa'i, 4: 83)

Alkur'ani ya yi suka ga wadanda suka bar tunani da lurar hankali cikin ayoyin Alkur'ani mai girma, da gano ma'anoninsa da abubuwa da ya kunsa, da cewa: "Shin ba su lura da Alkur'ani ne, ko kuwa da kemare ne bisa zukata" (Surar Muhammadu, 47:24). Daga nan za mu san cewa a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) tafsiri yana dogara ne da asasai uku:

1. Tafsirin Alkur'ani da Alkur'ani.

2. Tafsirin Alkur'ani da Sunna.

3. Tafsirin Alkur'ani da hankali mai lizimtar Alkur'ani da Sunna.

Haka nan muke samun cewa tafsiri yana da asasai da dokoki, kuma abin da ya tafo na tafsirai wanda za a cewa ra'ayin mutum ya shige shi, ko kuwa an dauki wasu nazarce-nazarcen ilmi wadanda mai tafsirin ya yi zamani da su, ko ra'ayoyin falsafa da ilmin akida, ko abin da aka danganta shi da ruwayoyi raunana ko ma wadanda sanadinsu yashashshe ne, ko kuwa masu karo da ayoyin Alkur'anin da suke a sarari ko kuma sunna tabbatatta, ko kuwa tafsirin da mai tafsirin ya daidaita shi da ra'ayinsa da karkatarsa da kuma sauran irin wadannan, dukkansu ababan yarfarwa ne a tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da kuma malamai da masu tafsiri wadanda suka bi shiriyarsu. Sau da yawa kuma ana samun cikin tafsiran musulmi, sunna da shi'a, ra'ayoyi da tafsirai wadanda ba su lizimci wannan hanyar ta Musulunci ba, wadanda kuma ba su bayyana ruhin Alkur'ani.

Don haka, ba wa irin wadannan tafsiran kima ba ya inganta, ba za mu kuma rike su mu yi aiki da su ba, sai dai wanda ya tabbatar wa kansa da ingancinsu.

Mai tafsiri kuwa ko wane ne shi, Alkur'ani hujja ce akansa, ba shi ne hujja a kansa ba. Kuma ba zai zamo hujja kan musulmi ba face da gwargwadon abin da ya dace da katari da abin da ya gano na hakika kawai.

Hakika hani ya zo daga wajen Imamai (a.s.) kan magana ba da wani ilimi ko hujja ba. An ruwaito Imam Bakir (a.s.) yana cewa:

"Abin da kuka san shi to ku fade shi, abin da kuwa ba ku sani ba to ku ce "Allah Shi Ya fi sani". Lalle mutum yana tuzgo aya daga Alkur'ani ya fadi cikin tuzgowar da ya yi, faduwar mai nisan fiye da tsakanin sama da kasa([115]) ".

Imam Sadik (a.s.) ya ce: "Ko wane abu ana komar da shi zuwa ga Littafin Allah da Sunna([116]) ".

Sunnar Annabi (s.a.w.a) A Mazhabar Ahlulbaiti (a.s)

"Allah Ya ni'imta bawan da ya ji maganata sannan ya haddace ta ya kiyaye ta ya kuma bayar da ita (ga wasu) kamar yadda ya ji ta. Sau da yawa ana samun mai daukar ilmi, amma ba malami ba, sannan kuma sau da yawa ana samun mai daukar ilmi ya zuwa wanda ya fi shi sani([117]) ".

Baicin Littafin Allah, Sunna ita ce mabubbuga ta biyu daga mabubbugan shari'a, wadanda musulmi suke dogara da su wajen fitar da hukumce-hukumce da dokoki da ka'idojin Musulunci. Ita Sunna tana daukar nauyin bayani da faiyacewa da kuma tafsirin Littafin Allah da furuci da abubuwan da ya kunsa da kuma abubuwan da ya tattara na shari'a da tunani da kuma tarbiyya. Shi nassi na Alkur'ani yana dauke da wata wadata da arziki na tunani da shari'a, mai girma kuma dauwamammiya, ita sunna kuwa ta dauki nauyin bayyana wannan arziki da gamar da shi. Lalle hankula ba za su iya riskar Littafin Allah tamkar yadda Sunna take riskar shi tana bayyana shi ba. Manzon Allah (s.a.w.a.) shi aka yi wa zance da wahayi, shi ne kuwa masanin abin da ke cikin Littafin Allah mai girma na daga abin da suka shafi hukumce-hukumce da ababen fahimta daga ciki da kuma manufofin da yake da su.

Don haka ne ita Sunna mabubbuga ce wacce ba ta kafewa, kuma gaskiya ce wacce barna bata taho mata a bayanta ko a gabanta. Sunna ita ce amintacciya mai ayyana dokokin rayuwa da kuma tsarin jin dadin dan'Adam, kuma ita madawwamiya ce dawwama irin ta Alkur'ani mai girma. Allah Ta'ala Ya ce: Abin da Manzo ya zo muku da shi, ku karba, abin da kuma ya hane ku, to ku hanu...". (Surar Hashr, 59: 7)

"Hakika abin koyi mai kyau ya kasance muku daga Manzon Allah, da duk wanda yake kaunar Allah da kuma ranar lahira...". (Surar Ahzab, 33: 21) "Idan kuka yi jayayya a wani abu to ku mai da (hukumcinsa) ga Allah da Manzo...". (Surar Nisa'i, 4:59)

Babu shakka, Ahlulbaiti (a.s) da wadanda suka dauki tafarkinsu wajen tafsiri da hadisi da fikhu da shari'a da akida, sun lizimci wannan hanyar, sun kuma yi gwagwarmaya, sadaukarwa, daurewa cutarwa, shiga kurkuku, kisa, azabtarwa da kuma kora duk a dalilin kare sunna mai tsarki da kira zuwa ga dacewarta da Littafin Allah mai girma.

Hakika an bijirar da Sunna tsarkakakkiya ga coge da karkatarwa da jirkitarwa wanda masu yi wa Musulunci dasisa, karya da kiyayya suke yi domin muzanta wannan dawwamammen sako na Ubangiji, domin kuma su karkatar da tafarkin al'ummar Musulunci.

Ahlulbaiti (a.s) sun kasance suna fagen kan gaba wajen kiyaye Sunna tsarkakakkiya da daukar ta da kuma isar da ita da gaskiya da amana, da kuma bayyana abubuwan da ta tattara na bayani mai zurfi.

Don aka ne suka yaki bidi'oi da bata, suka yi kira da a lizimci Littafin Allah da Sunna da sanya Littafin Allah ya zama shi ne ma'aunin Sunnar Annabi (s.a.w.a). Sun yi hakan ne domin Littafin Allah abin kiyayewa ne daga karkatarwa da jirkita - Alhamdu lillahi - kiyayye ne kamar yadda Jibrilu (a.s.) ya isar da shi ga Annabi Amintacce Muhammadu (s.a.w.a). "Lalle Mu muka saukar da Ambato (Alkur'ani) kuma lalle Mu Masu kiyaye shi ne".

Saboda haka, babu hannun jirkitawa ko coge ko wasa da ya taba shi. Domin haka ne ma muke samun Amirul Muminina (a.s) yana cewa: "Ya ku mutane! Farkon aukuwar fitinu (na daga) son zuciya wadanda ake bi da hukumce-hukumce fararru (wato na bidi'a) wadanda ake sabawa Littafin Allah wajen binsu, mutane suna jibintar wasu mutane wajen bin wadannan hukumce-hukumce. Da dai ita bata tsantsarta take, da ba ta buya ba ga mai hankali, da kuma gaskiya tsantsarta take, da sabani bai samu ba. Amma ana daukar wani abu a nan, a dauki wani a can, sai a cudanya su, sannan su zo tare. A nan ne Shaidan ya rinjaye majibantansa, wadanda kuwa kariya ta gabata gare su daga Allah suka tsira([118]) ".

Abu Basir, daya daga cikin sahabban Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito cewa: "Na ce da Abu Abdullahi (a.s.) cewa: Wadansu abubuwa suna taho mana, mu ba mu san su cikin Littafin Allah ko Sunna ba, to za mu dube su? Sai ya ce: "A'a, amma kai ko ka dace ba za a sakanta maka ba, idan kuwa ka yi kuskure to ka yi wa Allah Mai Girma da Daukaka karya([119]) ". Sannan ya ce (a.s.): Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata cikin wuta take".

Abdullah bn Abi Ya'afur ya ce: "Wata rana na tambayi Abu Abdullah (a.s.) game da sassabawar hadisai, wadanda muke amincewa da wadanda ma ba mu amince musu suna ruwaitowa", sai ya ce:

"Idan hadisi ya zo muku kuma kuka sama masa wata shaida daga Littafin Allah ko wata magana ta Manzon Allah (s.a.w.a.), (to ku karba) idan kuwa ba haka ba to wanda ya kawo muku hadisin ya fi cancanta da shi([120]) ".

An samu daga Ayyub bn Al-Hurr ya ce: "Na ji Abu Abdullah (a.s.) yana cewa: "Duk wani abu ana iya masa raddi in ban da Littafin Allah da Sunna, to duk hadisin da bai dace da Littafin Allah ba, to kyalkyali ne kawai([121]) ".

An samu daga Ayyub bn Rashid daga Abu Abdullah al-Sadik (a.s.) ya ce: "Abin da bai dace da Alkur'ani ba daga cikin hadisai kyalkyali ne kawai([122]) ".

An samu daga Imam Sadik (a.s.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda ya yi riko da Sunnata yayin sassabawar al'umma, yana da ladan shahidai dari([123]) ".

Wani mutum ya taho wa Amirul Muminina (a.s) ya ce: "Ka ba ni labari (mece ce) Sunna da bidi'a da jama'a da kuma rarraba", sai Amirul Muminina (a.s) ya ce da shi:

"Sunna ita ce abin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sunnanta, bidi'a kuma ita ce abin da aka fare shi a bayansa. Jama'a ita ce wadanda suke tare da gaskiya ko da su kadan ne, rarraba kuwa ita ce wadanda suke tare da bata, ko da kuwa suna da yawa([124]) ". Har ila yau, Imam Ali (a.s) yana cewa:

"Sunna biyu ce: Sunna ta wajibci, riko da ita shiriya ce, barinta kuwa bata ce. Da kuma Sunna cikin abin da ba wajibi ba, riko da ita falala ce, barinta kuwa kure ne([125]) ". Imam Bakir (a.s.) yana cewa:

"Ita Sunna ba a yi mata kiyasi, to ya ya za a yi kiyasin Sunna alhali mace mai haila tana rama azumi, amma ba ta rama salla([126]) ".

An samu daga Abu Abdullah, Imam Sadik (a.s.) daga Mahaifansa, daga Imam Ali (a.s.) cewa: "Kowace gaskiya tana tare da wata hakika, kuma kowace dacewa tana tare da wani haske. To abin da ya dace da Littafin Allah ku karbe shi, abin da kuwa ya saba da Sunnar Manzon Allah, to ku bar shi([127]) ". Sannan kuma yana cewa: "Allah Ya ji kan mutumin da ya kawo hadisi daga Manzon Allah (s.a.w.a.) ba tare da ya yi masa karya ba, ko da kuwa mutane sun guje shi([128]) ".

Sannan Amirul Muminina Ali (a.s) ya ce: "Na ji Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Idan hadisi ya taho muku (sashinsa) yana daidaita, (sashi kuma) yana sassabawa, to abin da sashinsa yake karyata sashe ba daga gare ni yake ba, kuma ban fade shi ba, ko da an ce na fada. Idan kuma hadisi ya taho muku, sashensa yana gaskata sashe, to shi daga gare ni yake, kuma ni na fade shi. Wamda kuwa ya ganni bayan rasuwata, kamar wanda ya ganni a raye ne, wanda kuwa ya ziyarce ni to zan kasance masa mai shaida a ranar kiyama([129]) ".

An samu daga gare shi (a.s.) ya ce wa Muhammad bn Muslim cewa: "Ya Muhammad! Abin da ya taho maka na wata ruwaya daga mutumin kwarai ko na banza, idan ya dace da Alkur'ani to ka dauke shi, abin da kuwa ya taho maka na ruwaya daga mutumin kwarai ko na banza, idan ya saba da Alkur'ani to kada ka karbe shi([130]) ".

Haka nan ake sanya iyakoki wa abin da ake daukarsa Sunnar Manzon Allah (s.a.w.a.) ne a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da tafarkinsu da kuma alakar wannan Sunna mai tsarki da Littafin Allah, da kuma rawar da take takawa cikin shari'a da sanya dokoki da gina rayuwar zamantakewa da ta ibada, wa al'ummar Musulmi. Muna iya tsamo wadansu abubuwa daga wannan tsarin mazhabi kamar haka:

1. Cewa kowane fadi ko aiki ko tabbatarwar da aka danganta ga Manzon Allah (s.a.w.a.), to wajibi ne a gwada su da Alkur'ani, a tabbatar da ingancinsu bisa hasken Alkur'ani, abin da ya dace da Littafin Allah, to daga Sunnar Manzo (s.a.w.a) yake, abin da kuwa ya saba da shi to ba kome yake ba wajen Sunna.

2. Alkur'ani da Sunna su ne tushen shari'a da doka, su ne ma'aunin hukumce-hukumce da halaye da tsarin rayuwa. Abin da duk muka samu na hukumce-hukumce na fikihu ko ma'anonin da ake riska na akida, to wajibi ne mu tabbata sun dace da Littafin Allah da Sunna. Duk abin da muka samu daga cikinsu ya dogara bisa asasin Littafin Allah da Sunna da shari'a, to doka ce ta Allah, mu yi aiki da shi, mu rike shi da karfi. Abin da kuwa ya saba da Littafin Allah da Sunna to shi bidi'a ce, bata ce.

3. Idan aka samu Sunna tabbatacciya, wacce an tabbatar da fitowarta daga Manzon Allah (s.a.w.a.) tana kuwa yin daidai da Litttafin Allah, to wajibi ne mu dauke ta a matsayin ma'auni kuma abin da za a yi amfani da ita wajen ruwayoyi da hadisan da muke shakkar su, ko muka sami rikitarwa wajen ingancinsu. Sai mu tabbatar da abin da ya dace da Littafin Allah da tabbatacciyar Sunna, mu yarfar da abin da ya saba da su. Ta wannan hanyar ne mazhabar Ahlulbaiti (a.s) ta ke iyakance tafarkin da za a bi wajen mu'amala da Sunnar Ma'aiki (s.a.w.a.).

Rabe-Raben Sunnar Annabi (s.a.w.a)

Malamai suna raba Sunnar Annabi (s.a.w.a) zuwa gida uku:

1. Maganganu: Su ne dukkan abin da suka taho daga Manzon Allah (s.a.w.a.) na daga zantattuka, hudubobi, wasiyyoyi, wasiku da dai sauransu.

2. Ayyuka: Abin nufi shi ne duk wani aiki da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi wajen mu'amalarsa da mutane, ko wajen yin ibadoji, ko wanin wannan daga abin da yake bayyana halalci. Duk aikin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya aikata to za mu gane halalcinsa a tushen al'amarin domin Ma'aiki (s.a.w.a.) abin tsarakake-wa ne daga aikata haramun.

Saboda haka muna iya cewa abin da ya fito daga Ma'aiki (s.a.w.a.) na aiki ya kasu kashi biyu:

· Wajibci: Sashin abin da ya fito daga Manzo (s.a.w.a) kamar salla, hajji, adalci tsakanin mutane da dai sauransu, yana bayyana wajibcin wannan aiki, da kuma cewa shi takalifi ne kuma farilla ne, wadda lizimtar su yana wajaba a kanmu, kuma dole ne mu gudanar da hukumce-hukumcensu.

· Akwai wasu ayyukan Manzon Allah (s.a.w.a.) wadanda ba su nuna wajibci, suna nuna halalci ne. Dukkan wannan yana karkashin halal, wanda aikatasu ja'izi (ya halalta) ne.

Don haka, aikin Manzo (s.a.w.a.) yana bukatar tafsiri domin mu gane wajibi da mustahabi da kuma ja'izi. Malamai wadanda suka kebanta da wannan fannin suna rarrabewa cikin fahimta da tafsirin 'aiki' a cikin Sunna, ta hanyar hujjoji da alamomi da tafarkin bincike na ilmin Usulu.

3. Yarda (Takriri): Shi ne yin shirun Manzo (s.a.w.a) kan wani aikin da sahabbansa suka aikata, ya gani kuma bai hana su ba, kamar mu'amalolin zamantakewa da aikin mutum shi kadansa. To hakan ikirari ne da kuma yarda daga wajen Manzon Allah (s.a.w.a.), yana kuma shiga karkashin Sunna.

To kamar haka ne mazhabar Ahlulbaiti (a.s) ta iyakance yadda ake mu'amala da Sunna mai tsarki da tafarkin tabbatar da ingancinta da tafsirinta.

Tafarkin Bincike da Tabbatarwa

Malaman mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suna da hanyar bincike da tabbatar da Sunnar Annabi (s.a.w.a) wacce Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka iyakance kuma suka bayyana tushenta da alamominta. Mun riga mun yi nuni ya zuwa ga ruwayoyin da suka zo kan hakan a baya.

Bisa wannan tushen malaman fikhun mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suka kafa tafarkin gyara (nakdi) cikin aikin bincike na ilmi. Babu wata sunna da suke mika wuya wajen ingancinta tun farko, sai dai su dauki matakin shakka kan ingancin sunnar, sannan su ci gaba da kokkofi da binciken ruwayar da tabbatar da ingancinta, idan har ingancinta ya tabbata sai su yi riko da ita da kuma daukanta a matsayin hujja da kuma fitar da hukumce-hukumce daga cikinta. Idan kuwa rashin ingancinta ya tabbata musu, sai su yi jifa da ita, ba za su yi aiki da ita ba. To kamar haka ne tafarkin binciken ruwayoyi da tabbatar da ingancin Sunna yake.

Bisa ga wannan bayani, malaman mazhabar Ahlul-baiti (a.s) ba su yi ikrari da samuwar wasu littattafan hadisai masu inganci, sake ba tare da wani kaidi ba. Sai dai kowane littafi dole ya rusuna wa bincike da gwaji kafin a tabbatar da ingancinsa. Misalin littattafai mashahurai a ruwaya wadanda suka tattara abin da ya taho ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) su ne:

1. Al-Kafi na Shaikh Kulayni.

2. Al-Istibsar na Shaikh Dusi.

3. Al-Tahzib na Shaikh Dusi.

4. Man la Yahdhuruhul Fakih na Shaikh Saduk.

5. Wasa'il al-Shi'a na Hur al-Amuli.

6. Biharul Anwar na Allama Majlisi.

Da dai sauran littattafan hadisi.

Babu shakka malaman Imamiyya wadanda kuma suke lizimtar tafarkin Ahlulbaiti (a.s) a fikihu da shar'antawa da ilmomin Musulunci sun sanya hadisan da suka zo cikin wadannan littattafa a bisa ma'aunin bincike wanda ya kubuta daga son rai, inda bayan binciken suka zubar da adadi mai yawa na hadisan saboda rashin ingancinsu.

Kamar yadda wadannan malumma suka binciki wadannan littattafa na hadisi, haka kuma suka gudanar da bincike kan wasu littattafan kuma, kamar su Sahih Bukhari, Sahih Muslim, Sunan Abi Dawud, Kanzul Ummal da dai makamantansu daga cikin littattafan hadisai da ruwayoyi, suka kuma auna su da wannan ma'auni na ilmi, kamar dai yadda suka gudanar akan wadancan, suka dauki na dauka da kuma zubar da ba zubarwa. Su wadannan malamai kuwa, su kan yi wannan bincike nasu ne a bisa wadannan asasai:

(A). Bincike Kan Isnadi: Abin nufi da isnadi kuwa shi ne silsilar maruwaita wadanda suke ruwaito hadisi. A nan malaman su kan tsaya tsayin daka wajen tabbatar da gaskiyar maruwaitan, suna masu dogaro da ilmul Rijal, wanda yake gabatar musu da sanarwar abin da ya jibinci mutanen da suke maruwaita ne, yana shaidar gaskiya ko rashin gaskiyarsu, ba tare da la'akari da mazhabar da maruwaicin ya fito ba. Idan ya zama abin dogaro kuma gaskiya, sai su karbi ruwayarsa, idan kuwa an yi suka cikin al'amarinsa sai su ture ruwayar tasa. Su ba sa duba kome sai gaskiyar mai ruwaya da kubutarsa a bisa ginshikai tabbatattu.

(B). Binciken Matani: Abin nufi da matani shi ne asalin nassi. A nan malamai suna bincike ne kan luggar matani da ma'anarta, kuma suna bincike domin su tabbatar da cewa abin da ya taho a hadisin bai sabawa Littafin Allah ko tabbatacciyar Sunna ko wata hakika tabbatacciya wacce Mai shar'antawa Matsarkaki (Allah) Ya tabbatar da ita a matsayin tabbatacciyar hakika a hankalce ba.

Yayin da ingancin isnadi da na matani suka tabbata wajen malamai sai su karbi ruwayar, idan kuwa ba haka ba sai su ture ta, ba ruwansu da cewa a wani littafi daga cikin littattafan hadisi ta zo.

Saboda haka a tafarkin malaman fikihu da malaman mazhabar Ahlulbaiti (a.s) Imamiyya ba a samun:

1. Rikon wani littafi na hadisi a matsayin sahihi daga dayansa ko kuma kore shi gaba dayansa.

2. Su suna karbar ruwayar maruwaici ne bisa sharadin gaskiyarsa da amincinsa ba tare da lura da mazhabarsa ko bangaren da ya fito ba. Wanda duk yake bitar littattafan Usulu da fikihu da Ilmul Rijal , zai samu wannan hakikar a bayyane.

Da haka ne wannan hanyar bin diddigi ta ilmi ta kiyaye asalin shari'a da tsarkin ta, da kuma hadin kan musulmi da nisantar nuna bangaranci, jahilci da ganin girman wani tun da ba a ba da dama wa wadannan abubuwa a tafarkin bincike, don kuwa a yayin bincike kowa daya ne.

Kuma da wannan tafarkin bincike da ilmin bin diddigi, wanda ya kafu a bisa asasin neman gaskiya da bincike a aikace, da rashin mika wuya da yarda da ingancin kowace ruwaya ba tare da lura da kowane ne maruwaicin ta ba, ko littafin da aka ruwaito ta ba, ne ake gudanar da binciken hadisi.

Imaman Ahlulbaiti (a.s) Maruwaita Manzon Allah (s.a.w.a)

Imaman Ahlulbaiti (a.s) ba su kasance masu Ijtihadi ko fitar da hukumci ba, sai dai sun kasance masu ruwayar Sunna ne, don haka, duk abin da ya fito daga gare su Sunna ce. Su kan ruwaito Sunnar ce da daga mahaifinsa, daga kakansa….daga Manzon Allah (s.a.w.a.). A saboda haka ne Imam Sadik (a.s.) ya ke cewa: "Hadisina hadisin babana ne, hadisin babana hadisin kakana ne, hadisin kakana hadisin babansa ne, hadisin babansa kuwa hadisin Aliyu bn Abi Talib ne, hadisin Aliyu kuwa hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.) ne, hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.) kuwa fadar Allah ce Mai girma da Daukaka([131]) ".

Daga Kutaiba, ya ce: "Wani mutum ya tambayi Abu Abdullah al-Sadik (a.s.) wata mas'ala, sai ya ba shi amsarta, sai mutumin ya ce: mene ne ra'ayinka in ya kasance kaza da kaza, mene ne hukumcinsa? Sai Imam ya ce masa: "Saurara! Abin da na baka jawabinsa, to daga Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ke, mu ba mu daga cikin wadanda a ke ce da su mene ne ra'ayinka a kowane abu([132]) ".

A saboda haka ne Shaikh al-Baha'i yake cewa: "Dukkan hadisanmu idan ba 'yan kadan ba suna komawa ga Imamanmu goma sha biyu (a.s.), daga nan kuma suna komawa zuwa ga Annabi (s.a.w.a). Domin ilminsu abin haskaka ne daga waccar fitilar([133]) ".

Da wannan ne Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka zama mabubbugar hadisi da ruwaya da bayanin hukumce-hukumcen shari'a da kuma bude boyayyun al'amurranta.

Lalle rayuwarsu mai albarka, rayuwa ce da ke danfare da juna, babu rabewa a cikinta, babu wani bako wanda ba sananne ba da ya shamakance saduwarsu da Manzon Allah (s.a.w.a.), to wannan rayuwa tana zaman wata makaranta ce da kuma gwaji rayayye mai nuna Musulunci da tabbatar da hukumce-hukumcensa da kiyaye tushensa. Dukkan wannan yana karfafa mana amincewa da tsarkin mabubbugar da tsabtar baiwar da kuma cewa abin da ya taho daga gare su (a.s.) mai asali ne.

Yayin da muka san dukkan hakan, za mu iya gane yanayin da mazhabar ilmi wanda mabiyan Ahlulbaiti (a.s) suka taso daga ciki suka kuma dauki iliminsu, sannan za mu gane cewa mazhabarsu na hadisi da tafsiri da ilmin akida da tauhidi da dai sauransu suna da aminci kuma hanya ce tsabtacciya mai sadarwa zuwa ga masaniyar annabci da tsarkin shari'a da asalin tushen Musulunci.

Daga nan ya dace mu fito da daidaikun silsilar nan mai albarka ta Imaman Ahlulbaiti (a.s) maruwaita daga Manzon Allah (s.a.w.a.) sannan kuma mu sanar da al'ummarmu matsayinsu na ilmi a shariance. Su Ahlulbaiti (a.s) yayin da suke zancen silsilarsu ta maruwaita hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.), suna zancen wannan silsilar ne, ga ta nan kuwa:

1. Aliyu bn Abi Talib (a.s.), an haife shi shekara ta 30 bayan Shekarar Giwaye, ya kuma yi shahada ne a shekara ta 40 bayan hijira.

2. Hasan bn Ali (a.s.), an haife shi shekara ta 3 bayan hijira, ya yi shahada kuma a shekara ta 50 bayan hijira.

3. Husaini bn Ali (a.s.), an haife shi a shekara ta 4 bayan hijira, ya yi kuma shahada ne a shekara ta 61 bayan hijira.

4. Imam Ali bn Husain (Zainul Abidin) (a.s.), an haife shi a shekara ta 38 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 95 bayan hijira.

5. Imam Muhammad bn Ali al-Bakir (a.s.), an haife shi a shekara ta 57 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 114 bayan hijira.

6. Imam Ja'afar bn Muhammad Sadik (a.s.), wanda ake danganta mazhabar Ja'afariyya Imamiyya gare shi, an haife shi a shekara ta 83 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 148 bayan hijira.

7. Imam Musa bn Ja'afar al-Kazim (a.s.), an haife shi a shekara ta 128 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 183 bayan hijira.

8. Imam Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.), an haife shi a shekara ta 148 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 203 bayan hijira.

9. Imam Muhammad bn Ali al-Jawad (a.s.), an haife shi a shekara ta 195 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 220 bayan hijira.

10. Imam Aliyu bn Muhammad al-Hadi (a.s.), an haife shi a shekara ta 212 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 254 bayan hijira.

11. Imam Hasan bn Ali al-Askari (a.s.), an haife shi a shekara ta 232 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 260 bayan hijira.

12. Imam Muhammad bn Hasan al-Mahdi (a.s.), an haife shi a shekara ta 255 bayan hijira, yana kuma raye a boye gwargwadon abin da ruwayoyi suka kawo.

Mun riga da mun yi magana kan guda uku na farko (wato Aliyu, Hasan da Husaini), mun san matsayi da mukaminsu cikin Alkur'ani da Sunnar Annabi (s.a.w.a), wadanda suke nuni da wajibcin yin musu da'a da kuma karba daga gare su.

To yanzu kuma bari mu yi bibiyar zantuttukan malamai dangane da sauran da suka saura daga cikin wadannan taurari masu albarka na gidan Annabci.

4- Imam Aliyu bn Husain (Zainul Abidin) (a.s.):

Shaikh Mufid ya nakalto cikin littafinsa Al-Irshad daga Zuhri cewa: "Ban riski wani mutum daga mutanen wannan gida - wato gidan Annabi (s.a.w.a) - wanda ya fi Aliyu bn Husaini (a.s.) ba([134]) ".

An nakalto daga Sa'id bn Musayyab, dangane da Imam Aliyu bn Husain (a.s.) yana cewa: "Wannan Shugaban masu ibada, Aliyu dan Husain dan Aliyu dan Abi Talib (a.s.) ne([135]) ".

Ibn Hajar cikin littafinsa Sawa'ikul Muhrika ya siffanta Imam Aliyu bn Husain (a.s.) da cewa: "Zainul Abidin shi ne halifan babansa (Imam Husain) wajen ilimi da zuhudu da ibada([136]) ".

An samu daga Abi Hazim da Sufyan bn Uyaina, ko wani dayansu yana cewa: "Ban taba ganin wani Bahashime wanda ya fi Aliyu bn Husain daraja ko ilmi ba([137]) ".

Hakika irin wadannan mutane daidaiku masu daraja wadanda suke kan mukamin Imamanci su ne malaman al'umma kuma su ne mafifita wajen ilmi, to lallai sun cancanca da malamai su siffantasu da irin wadannan siffofi, kuma sun cancanci karkatowar musulmi zuwa gare su wajen karbar hadisi da fikihu da tafsiri da akida da dai sauran ilmomin shari'a matsarkaki.

Hakika Imam Husaini bn Ali (a.s.) ya yi wa dansa Imam Ali Zainul Abidin alamar imamanci, ya kuma bayyanar da Imamanci da shugabancin addini ga dan nasa. Akwai dalili mafi bayyana, cikin yin hakan, dalilin da ya nuna mukamin wannan Imamin (Zainul Abidin) da karbar abin da ya fito daga gare shi na ilmomi da masaniyya da ruwayoyi da sauransu.

An ruwaito hadisi daga Imam Ja'afar Sadik (a.s.) cewa: "Lallai yayin da Husaini (a.s.) ya yi tafiya zuwa Iraki ya yi ajiyar littattafai da wasiyya wajen Ummu Salama (r.a.). Da Aliyu bn Husaini ya dawo (daga Iraki bayan shahadar babansa) sai Ummu Salama ta mayar da ajiyar zuwa gare shi([138]) ".

5- Imam Muhammad bn Aliyu al-Bakir (a.s.):

Amma dansa, Muhammad bn Ali, wanda ake masa lakabi da al-Bakir saboda fadadawarsa cikin ilmomi da masaniyya, to shi kamar mahaifinsa yake, shi ne mafi shahara da musulmi suka sani da tsantsaini da zuhudu da ilmi da masaniyya, malamai da maruwaita da malaman hadisi sun shaida hakan. Sahabin nan mai daraja Jabir bn Abdullah al-Ansari ya ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ba da labarin cewa shi (Jabir) zai riski dansa Muhammad al-Bakir ya kuma umurce shi da ya isar masa da gaisuwarsa.

Wannan sahabin ya ruwaito cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce da shi: "Za ka rayu har ka hadu da wani da nawa daga Husaini, ana ce da shi Muhammadu, yana tsaga ilimi tsagawa. To idan ka hadu da shi ka isar masa da gaisuwa daga gare ni([139]) ".

Wannan sahabi kuwa ya riski Imam Bakir (a.s.) alhali yana yaro, sannan kuma ya isar da wannan gaisuwa ta Manzon Allah (s.a.w.a.) gare shi.

Lallai a cikin wannan shaida ta annabta da wannan sanarwa, akwai wadatarwa wajen bayyanar da mukamin wannan Imami da dogaro da shi da komawa zuwa gare shi da karbar hukumce-hukumce daga gare shi. Lokacin rayuwarsa, Imam Bakir (a.s.) da dansa Imam Sadik (a.s.) su ne yanki mafi wadata daga dukkan tarihin Musulunci wajen hadisi da ruwaya da kuma sanar da ilmummukan Musulunci.

Hakika malamai da maruwaita da malaman tafsiri da masu neman ilmummukan Musulunci daban-daban a wancan yanki zamanin suna yi wa Imam Bakir kallon kololuwar da tafi kowacce, kuma ilmin da ba wani ilmin da daukakarsa ta kusaci nasa.

Ibn Ahmad al-Hanbali ya siffanta shi da cewa: "Abu Ja'afar, Muhammadu al-Bakir ya kasance daga malaman Madina kuma ana ce da shi bakir ne domin ya tsaga ilmi wato ya tsaga shi ya sanar da asalinsa ya kuma fadada cikinsa([140]) ".

Ibn Jawzi ya nakalto daga wani shugaban Tabi'ai, Ada, wata maganar da ya yi kan Imam Muhammad al-Bakir (a.s.) cewa: "Ban taba ganin malamai suna kaskantar da kai cikin ilminsu kamar yadda na gani a gaban Abu Ja'afar al-Bakir ba([141]) ".

6- Imam Ja'afar bn Muhammad al-Sadik (a.s.):

To batun dansa, Ja'afar al-Sadik (a.s.) kuwa, hakika malamai sun yawaita yabo gare shi da kuma mahaifansa da kuma girmama matsayinsu. Za mu ambaci kadan daga cikin wadannan maganganu, kamar haka:

Allama Muhakkik Sayyid Muhsin Amin ya nakalto cewa: "Lallai Hafiz bn Akd al-Zaidi a cikin littafinsa na Rijalu, ya kawo mutum dubu arba'in daga magaskatan da suka ruwaito daga Ja'afar bn Muhammad (a.s.), ban da kuma wadanda ba a tabbatar da gaskiyarsu ba. Ya kuma ambaci rubuce-rubucensu([142]) ". Ibn Shahr Ashub ya kawo a cikin littafinsa, Manakib Aali Abi Dalib daga littafin Hilyatul Awliya' na Abu Nu'aim cewa: "Hakika manyan malamai da shuwagabanni sun karbi hadisi daga Ja'afar al-Sadik, cikinsu har da: Malik bn Anas, Shu'ba bn Hajjaj, Sufyan al-Thawri, Ibn Jarih, Abdullah bn Amru, Ruh bn Kasim, Sufyan bn Uyaina, Sulaiman bn Bilal, Isma'il bn Ja'afar, Hatim bn Isma'il, AbdulAziz bn Mukhtar, Wahb bn Khalid, Ibrahim bn Dahhan da dai sauransu. Ya ce: Muslim ya fitar da hadisi cikin Sahihinsa yana mai kafa hujja da hadisinsa (Imam Sadik). Wasu kuma suka ce: Wadanda suka ruwaito daga gare shi sun hada da Malik, Shafi'i, Hasan bn Salih, Abu Ayyub al-Sajistani, Umar bn Dinar da Ahmad bn Hambal. Malik bn Anas ya ce: Ido bai ga ba, kunne bai jiba, kuma bai fado wa zuciyar wani mutum wanda ya fi Ja'afar Sadik a falala da ilmi da ibada da tsantsaini([143]) ".

Uztaz Shaikh Mahmud Abu Zuhra, shaihin malami a Jami'ar Azhar ta kasar Masar ya yi magana kan Imam Sadik (a.s.) a cikin gabatarwar littafinsa mai suna Imam Sadik, ya ce:

"Bayan haka; hakika mun yi niyyar mu yi rubutu kan Imam Ja'afar Sadik, da taimakon Allah da gamo da katar daga gare Shi. Hakika mun yi rubutu kan bakwai daga shuwagabanni masu daraja, ba mu jinkirta rubutu kansa domin ya kasa wani daga garesu ba, a'a, shi yana da fifikon gabatuwa bisa mafiya yawansu. Yana kuma da fifiko makebanci bisa manya-manya daga cikinsu domin Abu Hanifa ya kasance yana ruwaitowa daga gare shi yana kuma daukarsa a matsayin mafi sanin abin da mutane suka sassaba a kansa, kuma mafi kewayewa da ilmi cikin dukkan fukaha'u. Imam Malik ya kasance mai halartarsa domin karatu da ruwaya. Imam Ja'afar Sadik yana da falalar malanta kan Abu Hanifa da Malik, wannan kuwa ya isa daraja. Saboda wannan, jinkirtawa ba ta yiyuwa domin nakasinsa kuma ba a gabatar da waninsa domin fifiko. Kuma bayan haka ma shi jikan Aliyu Zainul Abidin ne, wanda ya kasance shugaban mutanen Madina a zamaninsa wajen falala da daraja da addini da ilmi, kuma mutane kamarsu Ibn Shihab al-Zuhri da kuma da dama daga cikin tabi'ai sun yi dalibta a hannunsa. Shi ne dan Muhammad Bakir wanda ya tsaga ilmi ya kai ga ainihinsa. Shi yana daga wadanda Allah Ya tattara musu daraja a zatinsu da daraja ta girman asalinsu na dangin Hashimi da kusanci da Annabi (s.a.w.a)([144]) ".

Amru bn Mukdam ya kasance yana cewa: "Idan na dubi Ja'afar bn Muhammad na kan gane cewa shi daga tsatson Annabawa ya fito".

Shahararren malamin tarihin nan Ya'akubi ya siffanta Imam Sadik (a.s.) da cewa: "Ya kasance mafificin mutane, mafi ilmin addinin Allah. Mazowa ilmi wadanda suka ji daga gare shi sun kasance idan za su ruwaici wani abu daga gare shi su kance; 'Malam ya ba mu labari([145]) '.

Wannan dan haske ne kadan daga sanarwar malamai da maruwaita da masu hadisi da kuma shaidarsu mai bayyana matsayin Ahlulbaiti (a.s) da bigirensun nan na ilmi da imani madaukaki.

7- Imam Musa bn Ja'afar al-Kazim (a.s.):

Batun kuma Imam Musa bn Ja'afar (a.s.) kuwa, shi ne dan Imam Ja'afar Sadik (a.s.). Ya sami tarbiyya cikin kulawan babansa wanda daga gare shi ne Imam Musa Kazim ya dibi ilmi da tsantsaini da kyawawan dabi'u. Saboda haka ne ma babansa ya masa shaida da cewa mai girman alkadari da madaukakin matsayi, da kuma cewa dansa Musa shi ne shugaban Ahlulbaiti (a.s), shi ne Imami wanda za a koma gare shi domin karbar ilmomi da masaniya.

Hadisi ya zo daga gare Imam Sadik din yana fadawa wani sahabinsa cewa: "Lallai wannan da nawa da ka gani, da za ka tambaye shi abin da yake tsakanin bangwayen Littafi guda biyu (Alkur'ani) da ya ba ka amsa da ilmi cikakke([146]) .

Malaman Ilmul Rijal da na tarihi sun siffanta shi da cewa shi malami ne mai gaskiya kuma mai ibada ne wanda ya shahara da tsantsaini da takawa da girman al'amari da madaukakin halin kwarai. Za mu ambaci abin da Hafiz al-Razi ya fadi cikin littafinsa na Ilmul Rijal kan irin wannan shaidar, inda yake cewa:

"Musa dan Ja'afar dan Muhammad dan Ali dan Husain dan Ali dan Abu Dalib ya yi ruwaya ne daga babansa, shi kuma dansa Ali bn Musa da dan'uwansa Ali bn Ja'afar sun ruwaito daga gare shi, ya ce; Na ji babana yana fadawa Abdurrahman cewa: An tambayi babana game da shi sai ya ce: Mai gaskiya ne, mai yawan gaskiya, shugaba daga shuwagabannin musulmi([147]) ".

Muhammad bn Ahmad al-Zahabi ya fadi game da shi cewa: "Musa ya kasance daga masu (gwanayen) hikima kuma daga bayin Allah masu tsoron Allah Ta'ala([148]) ".

Kamaluddin Muhammad bn Dalha al-Shafi'i ya ce: "Shi ne shugaba mai girman alkadari, mai madauka-kin al'amari, babban mujtahidi mai kyautata ijtihadi, wanda ya shahara da ibada, mai dogewa bisa biyayyar Allah, wanda ya shahara da karamomi. Yana kwana yana sujjada da tsayuwa, cikin yini kuwa yana mai sadaka da azumi. Saboda tsananin afuwarsa da kauda kai ga barin masu zaluntarsa aka yi masa lakabi da Kazimu (mai hadiye fushi)([149]) ".

Mu'umin Shabalanji ya ce: "Musa al-Kazim (r.a.) ya kasance mafi yawan ibada a zamaninsa kuma mafi ilmi([150]) ".

8- Imam Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.):

Amma batun dansa wato Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.) kuwa, to hakika ya kasance tamkar mahaifinsa wajen ilmi da tsantsaini da cikar kyawawan halaye. Ya karbi ragamar shugabancin addini da nauyin Imamanci a bayan babansa. Ya kai matsayi mai daukaka da daraja wanda ya tilastawa halifan Abbasiyawa Ma'amun ya nada shi magajinsa a bayansa, duk da gaba da fito-na-fito da ke tsakanin Alawiyyawa da Abbasiyawa.

Hakika malamai sun ba da shaida a majalisun ilmi da muhawara, kan matsayin Imam Ali Ridha wajen ilmi da karimci da siffantuwarsa da tsantsaini da takawa.

Ga wasu daga cikin wadannan maganganu:

Al-Wakidi ya ce: "Ya kasance mai gaskiya, yana ba da fatawa a masallacin Manzon Allah (s.a.w.a.) alhali yana dan shekara ashirin da 'yan kai. Yana daga dabaka ta takwas ta tabi'ai na mutanen Madina([151]) ".

Amma babansa Musa bn Ja'afar (a.s.) wanda muka riga da muka san matsayinsa na ilmi da tsantsaini da tsoron Allah, shi ma ya ba da shaidar ilmin Aliyu bn Musa al-Ridha da kuma shiryarwa zuwa ga karbar addini da shiriya daga gare shi, inda yake cewa:

"Wannan dan'uwannaku Ali bn Musa, shi ne mafi sani a duk mutanen gidan Muhammadu, don haka ku tambaye shi batun addininku, kuma ku kiyaye abin da yake fada muku([152]) ".

9- Imam Muhammad bn Aliyu al-Jawad (a.s.):

Amma Imam Jawad (a.s.), shi ma tamkar mahaifa da magabatansa tsarkaka yake wajen ilmi da zuhudu da kuma tsoron Allah.

Sibd bn Al-Jawzi yana cewa: "Muhammad al-Jawad shi ne Muhammad bn Ali bn Musa bn Ja'afar bn Muhammad bn Ali bn Husain bn Ali bn Abi Dalib. Sunan kunyarsa shi ne Abu Abdullah, wasu kuma su kan ce masa Abu Ja'afar. An haife shi ne a shekara ta 165 bayan hijira, ya yi shahada kuma a shekara ta 220, ya kasance bisa tafarkin babansa wajen ilmi da takawa da zuhudu da kyauta([153]) ".

Muhammad bn Ammar ya ruwaito cewa: "Na kasance wajen Ali bn Ja'afar (*) bn Muhammad a Madina, na kasance a wajensa har na tsawon shekara biyu ina rubuta abin da na ji daga wajen dan'uwansa (Imam Musa bn Ja'afar Kazim) sai Abu Ja'afar Muhammad bn Ali Ridha ya shiga masallacin Manzon Allah (s.a.w.a.), sai Ali bn Ja'afar ya yunkura ya mike ba takalmi ba abaya, sai ya sumbanci hannunsa ya girmama shi.

Sai Abu Ja'afar ya ce da shi: "Ya baffana, zauna mana, Allah Ya yi maka rahama".

Sai ya ce: "Ya shugabana, ya ya zan zauna alhalin kana tsaye?! Yayin da Ali bn Ja'afar ya dawo gurin zamansa sai abokansa suka dora sukarsa, suna cewa: 'Kai baffan babansa ne kuma ka ke yi masa haka!!

Sai ya ce: "Ku saurara - sai ya kama gemunsa - idan Allah Mai girma da Daukaka bai nufi wannan furfurar da cancantar shugabanci ba amma Ya nufi wannan saurayin, Ya kuma ajiye shi inda Ya ajiye shi, shin zan yi inkarin falalarsa ne? Muna neman tsarin Allah daga abin da kuke fadi, kai bari dai ni bawansa ne ma([154]) !".

Mahmud bn Wuhaib al-Bagdadi al-Hanafi ya ce: "Muhammad al-Jawad bn Ali al-Ridha, sunan kunyarsa shi ne Abu Ja'afar", daga nan sai ya ce: "shi ne magajin babansa wajen ilmi da fifiko, ya fi duk 'yan'uwansa daraja da kamala([155]) ".

10- Imam Aliyu bn Muhammad al-Hadi (a.s.):

Amma Imam Ali al-Hadi (a.s.) dan Imam Muhammad al-Jawad (a.s.) lallai yana da falala mai girma da daukakar al'amari wajen ilmi da tsantsaini, tamkar abin da Mahaifansa masu kyauta suke da shi. Ana masa alkunya da Abul Hasan.

Mu'min al-Shabalanji ya ce: "Ya kasance mai yawan munajati (addu'a), an fadi cikin al-Sawa'ik cewa: Abul Hasan ya kasance magajin babansa wajen ilmi da kyautattaki([156]) ".

Abdulhayy bn al-Ammad al-Hambali ya ce: "Abul Hasan, Ali bn Muhammad bn Ali al-Ridha bn al-Kazim, Musa bn Ja'afar al-Sadik, ba'alawiyye, bahusainiyye, wanda aka fi sani al-Hadi, ya kasance fakihi ne kuma shugaba mai yawan ibada([157]) ".

Alhafiz Imaduddin Abul Fida, Isma'il bn Umar bn Kathir yana cewa: "Shi Abul Hasan, Ali al-Hadi, shi ne dan Muhammadal-Jawad dan Ali al-Ridha dan Musa al-Kazim dan Ja'afar al-Sadik dan Muhammad al-Bakir dan Ali Zainul Abidin dan Husain al-Shahid dan Ali dan Abi Dalib, daya daga Imamai goma sha biyu. Shi ne baban Hasan bn Ali al-Askari. Ya kasance mai yawan ibada mai zuhudu. Mutawakkil al-Abbasi ya mai da shi garin Samarra, inda ya zauna a can sama da shekaru ashirin da watanni, ya kuma yi shahada ne a can a shekara ta 254 bayan hijira([158]) ".

An ruwaito daga Yahya bn Harthama wanda Mutawakkil, sarkin Abbasiyawa, ya aika domin taho da Imam Hadi (a.s.) daga Madina zuwa Samarra, ya ce:

"Sai na tafi Madina, da na shiga garin sai mutanenta suka yi kuwwa mai tsanani wanda ba a taba jin irin ta ba, su na masu tsoron wani abu zai faru da Ali. Suna nuna wannan damuwa ce saboda ya kasance mai kyautata musu, mai lizimtar masallaci, ba ya wata karkata zuwa ga duniya. Sai na fara kwantar musu da hankali, ina rantse musu cewa ba a umurce ni da munana masa ba kuma na zo cutar da shi ba ne. Daga nan sai na binciki gidansa, ban sami kome bai sai Kur'ani da addu'oi da littattafan ilmi, a saboda haka sai na ga girmansa ya daukaka a idanuwana([159]) ".

11- Imam Hasan bn Aliyu al-Askari (a.s.):

Imam Hasan al-Askari kuwa shi ne dan Imam Ali al-Hadi (a.s.), shi ma tamkar mahaifansa masu kyautatawa yake wajen ilmi, masaniya, tsantsaini da jihadi. Malamai da ma'abuta tarihi sun ba da shaidar hakan. Za mu ambaci kadan daga cikin wadannan maganganu na masana, kamar haka:

Shamsuddin Abu Muzaffar, Yusuf bn Faragili, jikan bn Al-Jawziyya, yace: "Ya kasance malami mai gaskiya, ya ruwaito hadisi daga babansa da kakansa([160]) ".

1. Ali bn Sabbag al-Maliki ya ce:

"Darajojin shugabanmu Abu Muhammad Hasan al-Askari suna nuni da cewa shi mai daraja ne dan mai daraja, babu wanda ke shakka ko kokwanton imaman-cinsa. Kuma na san cewa da ana sayar da karimci da waninsa ne mai saye shi kuwa mai sayarwa. Shi tilo ne a zamaninsa ba shi da na biyu, ba a kwatanta shi da kowa, ba shi da kishiya. Shi ne shugaban mutanen lokacinsa, shi ne kuma Imaminsu. Zantuttukansa daidaitattu ne, ayyukansa kuwa abin yabo([161]) ".

12- Imam Muhammad bn Hasan al-Mahdi (a.s.):

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ranaku da darare ba za su kare ba har sai Allah Ya tasar da wani mutum cikin Ahlulbaitina sunansa kamar sunana, zai cika kasa da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci da danniya([162]) ".

An karbo daga Ali bn Abi Dalib (a.s.) daga Annabi (s.a.w.a) cewa ya ce: "Da a ce babu abin da ya saura na lokaci face yini guda, to da Allah Ya tasar da wani mutum daga cikin Ahlulbaitina ya cika kasa da adalci bayan an cika ta da zalunci".

Haka Abu Dawud ya kawo hadisin cikin Musnad dinsa. Kuma Abu Dawud din da Tirmizi sun ruwaito shi cikin Sunan dinsu, kowannensu daga Abu Sa'id Khudri (r.a.) ya ce: "Na ji Ma'aiki (s.a.w.a.) yana cewa: "Mahdi daga gare ni yake, goshinsa mai fadi, mai dogon hanci, zai cika kasa da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci".

Abu Dawud ya kara da cewa: "Zai yi mulkin shekaru bakwai, ya kara da cewa hadisi ne tabbatacce mai inganci([163]) .

Hadisan da suka zo ta hanyoyin malaman hadisi da ruwaya daga mazhabobin musulmi daban-daban, suna da yawa ainun, dukkansu sun tafi a kan cewa sunan Mahdi shi ne Muhammadu, kuma shi cikin Ahlulbaitin Annabi (s.a.w.a) yake. Sai dai sun saba kan ko waye shi. Abin da ya tabbata wajen mabiya Ahlulbaiti (a.s) da ma wasu ban da su shi ne; shi Mahdi shi ne Imam Muhammad bn Hasan al-Askari bn Ali Hadi bn Muhammad al-Jawad bn Ali Ridha bn Musa al-Kazim bn Ja'afar Sadik bn Muhammad Bakir bn Ali Zainul Abidin bn Husain bn Ali bn Abi Dalib (a.s.). Kuma an haife shi a tsakiyar watan Sha'aban shekara ta 255 bayan hijira, a garin Samarra. Kuma da ikon Allah, bai gushe ba yana nan a fake, zai bayyana a wani lokaci da kasa za ta cika da zalunci da danniya domin ya cika ta da adalci, kamar yadda hadisai suka nuna. Da kuma cewa Annabi Isa (a.s.) zai yi salla a bayansa. Wannan shi ne takaitaccen bayani kan Imaman Ahlulbaiti (a.s) da mukaminsu da kuma matsayinsu.

Daga gare su ne aka karbi ilmi fikihu da hadisi da tafsiri da ilmummukan akida da shari'a da dai sauransu.

Tauhidi A Tafarkin Ahlulbaiti (a.s)

"Farkon addini sanin Allah, cikar saninSa kuwa kadaita Shi, cikar kadaita Shi kuwa tsarkake niyya gare Shi([164]) ".

"Allah ba Ya karbar aiki ba tare da an sanShi ba, babu kuma yadda za a sanShi sai da aiki. To wanda ya sani sanin zai shiryar da shi zuwa aiki, wanda kuwa bai yi aiki ba, to ba sani a gare shi. Ku saurara! Lallai shi imani sashinsa daga sashe yake([165]) ".

Tauhidi ka'ida ce ta Musulunci, shi ne kuma ginshikin fahimta da tunani, kuma shi ne matattarar ilmi da aiki. Shi ne matakin farko da kuma ka'idar sauya shari'a da ka'idoji da halaye kwarai da kuma tafarkin tunani.

Manufar Tauhidi tana matsayin ginshiki wajen gina wayewa ta Musulunci wacce ta kebanta da rininta na tauhidi; Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Rinin Allah! Kuma wane ne mafi kyau ga rini daga Allah? Kuma mu, a gare Shi, masu bautawa ne". (Surar Bakara, 2: 138)

Rinin nan na tauhidi wanda ya banbanta wayewa irin ta Musulunci daga wata wacce ba ita ba, kuma wanda shi ya ba ta siffofi iyakantattu na aike (daga Allah) shi ya sanya wa rayuwar musulmi da tunaninsa wani zubi kebantacce.

Lallai Alkur'ani mai girma da Sunna mai tsarki su ne tushen tunani na matsalolin akida. Hakika sun ba mu bayani cikakke kan akidar tauhidi, sun bayyana mana samuwar Allah Mahalicci, Mai Girma da Daukaka, sun kebance mana bayanin siffofinSa na kamala tare da tabbatar masa da cikakkiyar tsarkaka daga dukkanin nakasa. Ginshikan wannan akidar ta tauhidi sun cika, musulmin farko kuwa sun yi imani da su, kamar yadda suka ji su daga Manzon Allah (s.a.w.a.) suka kuma karanta su cikin Littafin Allah Mai Daukaka.

Addinin Musulunci ya watsu yayin da aka ci kasashe da yaki, al'ummai masu wayewa da falsafar jahiliyya kamar su Farisa da Hindu da Sin, sun shigo Musulunci. Haka nan mutane mabiya karkatattun addinan Kiristanci da Yahudanci wadanda kuma sun sami tasirin falsafa da akidojin Kiristanci da Yahudanci su ma sun shigo Musulunci. A hada da abin da aka debo daga tunani da falsafar Yunaniyawa da masu kama da su. Duk wannan ya tsirar da jayayya da shakku, sannan karairayi da bakin manufofi suka shigo akidar tauhidi, yayin da wannan wayewar mai rusawa ta kutsa kai, sai aka samu cewa akidar tauhidi ta kada ta yi rauni a wajen wadanda suka shagalta da bahasi kan akida da ilmin falsafa. Matsaloli da suka shafi rawar da dan'Adam yake takawa a ayyukansa kamar su Jabr (watau tilastawa) da tafwidh (ba da ikon zabi) da kuma Guluwi (masu wuce gona da iri) da tajsim (kudurta cewa Allah jiki ne) da bayani kan Isra'i da Mi'iraji, duk irin wadannan suka taso, da rudani cikin tunanin mutane. Sakamakon haka sai aka sami mazhabobi da kungiyoyi daban-daban suka tsiro tare da akidoji karkatattu, manisanta daga akidar asali ta tauhidi. Wannan ya sa Imaman Ahlulbaiti (a.s) da malamai masu tunani irin na Musulunci sun shiga fagen fama da masu wadannan karkatattun akidu. Jayayyar da har a wannan zamanin gurbinta bai gushe ba, duk da cewa sashin karkatattun kungiyoyin ya bace. Wannan fama da jayay-ya tsakanin wasu kungiyoyi daban-daban ya wanzar da gurabansa masu kyau da kuma munana, ana iya ganinsu cikin tunanin musulmi na akida da mafuskantar bayanin matsalolin akida.

Saboda abin da Allah (S.W.T.) Ya yi baiwa da shi ga Ahlulbaiti (a.s) na tsarkakar fahimta da kewayewa ga dukkan ilmomin shari'a da sanin Allah da kiyayewarsu da ilmin Littafin Allah da na Sunnar Annabi (s.a.w.a), lallai su da mazhabarsu sun taka rawar gani wajen warware rikice-rikice da rusa karkatattun ra'ayuyyuka da kuma kare manufar tauhidi da tsare tsarkinta. Muna da muhawarorin Imaman Ahlulbaiti (a.s) da hadisansu da tafsiran ayoyin tauhidi da bayanansu masu gusar da rudani domin fahimtar Musulunci ta gudana bisa tafarkinta na asali ba tare da karkata ba ko mummunan fahimta wa ayoyin da yi musu tafsiri na son zuciya ko bin wata batacciyar falsafa, karkatacciya. Wannan bayani na Imamai kan fahimtar Littafin Allah da saninsu da Allah (S.W.T.) ya haifar da wani tunani hadadde mai riko da akidar tauhidi.

Idan mutum ya yi nazarin al'amarin akidar tauhidi da rassanta da matsalolinta bisa tafarkin Ahlulbaiti (a.s) zai riski tsarkaka da zurfin sha'anin tauhidi, kuma zai gane cewa ginshikin akida da duk wata wayewa shi ne kadaita Allah (S.W.T.). Daga nan za a gane cewa akidar tauhidi ta ginu ne bisa tushen; "Tabbatar da cikakken kamala ga Allah (S.W.T.) da tsarkake Shi daga dukkan tawaya da kuma kore duk wani abokin tarayya ko makamanci ko tamka ko kuma kishiya".

Imam Ali (a.s.) ya kafa tushen wannan mahanga ta tauhidi da cewa: "Tauhidi shi ne kada ka takaita Allah cikin rayawarka takaitacciya, adalci kuwa shi ne kada ka dora wa Allah tuhuma([166]) ". A cikin hadisai da muhawarori masu yawa, Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun tabbatar da akidar tauhidi tare da raddi kan rudanin da mabarnata da zindikai kamar su Aldaisani da Ibn Abi Al-Awja'a da ibn Almukaffa da mulhidai da 'yan gullatu da 'yan jabru da tafwid da makamantarsu, suka shigar.

A nan za mu kawo wani sashe na wadannan asasai na tauhidi wadanda suke nuna akidar Alkur'ani da kuma ayyana tushen ilmi, tunani na tauhidi, tsabtansa da kuma asalinsa.

Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito Amirul Muminina (a.s) yana cewa: "Ku nemi sanin Allah ta hanyar Allah, Manzon Allah kuma ta hanyar sakon (Musulunci), wadanda aka ba su shugabanci (Ulul Amri) kuwa ta wajen umurninsu da kyakkyawa da haninsu ga mummunan aiki da adalci da kyautatawa([167]) ".

Alfath bn Yazid ya ruwaito daga Imam Ali bn Musa Ridha (a.s.) cewa: "Na tambaye shi kan mafi kankantar sanin Allah, sai ya amsa min da cewa:"shi ne yarda da kuma furuci da cewa babu abin bauta koma bayan Allah, babu makamancinSa, babu tamkarSa kuma Shi Dawwamam-me ne ba mai gushewa ba, da kuma cewa babu wani abu tamkarSa([168]) ".

Nafi'u bn Al-Azrak ya tambayi Imam Abu Ja'afar, Muhammad Bakir (a.s.) cewa: "Ka ba ni labari yaushe ne Allah Ya kasance?, sai ya ce: "Yaushe ne bai kasance ba har zan ba ka labarin lokacin da Ya kasance? Tsarki ya tabbata wa Wanda bai gushe kuma ba zai gushe ba, Makadaici, Wanda ake nufinSa da bukata, bai riki abokiyar zama ba ko kuma da([169]) ".

Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito cewa wani malamin yahudawa ya taho ma Imam Ali (a.s.) yana tambayarsa cewa: "Ya Amirul Muminina! Yaushe Ubangijinka Ya kasance? Sai ya ce masa:"Tir da kai, ana 'yaushe ya kasance' ga Wanda ba samamme ba ne? Amma wanda samamme ne ba da wani ba, ba a ce wa 'yaushe ya samu'. Shi Allah samamme ne gaban gabani ba tare da wani 'gabani' ba kuma samamme ne bayan 'baya' ba tare da wani 'baya' ba, kuma babu wai iyakar karshe da za a ce karshenSa ya kai iyaka". Sai malamin ya ce da Imam: "Kai Annabi ne?", Sai Imam (a.s.) ya amsa da cewa: "Kaitonka, ni ba kowa ba ne face bawa cikin bayin Manzon Allah (s.a.w.a.)([170]) ".

Imam Bakir (a.s.) ya ce: "Na hane ku yin tunani kan Allah, sai dai duk yayin da kuke nufin duban buwayar Allah to ku dubi girman halittun Allah Ta'ala([171]) ".

Imam Sadik (a.s.) ya yi wasiyya ga wani sahabbinsa (Muhammad bn Muslim) da cewa: "Ya Muhammad! Su mutane, magana ba za ta gushe gare su ba har sai sun yi magana kan (zatin) Allah. To idan kun ji ana hakan ku ce: 'Babu abin bauta face Allah Makadaici, Wanda babu wani abu tamkarsa([172]) '".

Imam Bakir (a.s.) yana cewa: "Ku yi magana kan kome, kada ku yi magana kan batun zatin Allah Ta'ala([173]) ".

Yayin da wani ya tambayi Imam Ali (a.s.) cewa: 'Ina Allah Yake gabannin Ya halicci halitta', sai Imam ya yi masa bayani cewa Allah ba Shi da bukatar bigire, Ya karfafa tsarkakar Mahalicci Madaukaki ga barin wannan, haka nan tsarkakke Ya ke ga barin bukatuwa ya zuwa ga zamani. Wani mai tambayan kuma ya tambaye shi cewa: 'Ina Ubangijinmu Yake kafin Ya halicci sama da kasa?, Sai Imam (a.s.) ya amsa da cewa: "Ina tambaya ce kan bijire, Allah kuwa Samamme ne yayin da ba a samar da bigire ba([174]) ".

Yayin da kuma aka tambaye shi kan ganin Allah (S.W.T.) sai ya tsarkake Allah ga barin ganuwa. Ga tambayar: "Ya Amirul Muminina! Shin ka ga Ubangijinka lokacin da kake bauta masa? Sai ya ce: "Kaitonka! Bana bautar Ubangijin da ban ganshi ba", sai ya ce masa to yaya ka gan shi?, sai Imam (a.s.) ya amsa masa da cewa: "Tir da kai, idanu ba sa riskar Allah da gani irin na ido, sai dai zukata sun gan Shi da matabbatan imani([175]) ".

Muhammad bn Hakim ya ce: "Abul Hasan Musa bn Ja'afar (a.s.) ya yi rubutu ya aike wa babana cewa: "Allah (S.W.T.) Ya daukaka, girmanSa ya buwaya ga barin riskar ainihin siffarsa. Ku siffanta Shi da abin da Ya siffanta kanSa da shi, ku kuma kame ga barin koma-ba-yanSa([176]) ".

Al-Mufaddal ya ce: 'Na tambayi Abul Hasan wani abu kan sifa, sai ya ce: "Kada ku ketare abin da ya ke cikin Alkur'ani([177]) ".

Abdur Rahman bn Atik Alkasir ya ce: 'Na rubuta tambaya zuwa Abu Abdullah al-Sadik (a.s.) ta hannun Abdul Malik bn A'yun cewa: "Wasu mutane a Iraki suna siffanta Allah da wani yanayi da kuma kama, to idan ka yarda, Allah Ya sanya ni fansarka, ina so ka rubuto min da bayani kan ingantac-cen matsayi kan tauhidi. Sai ya rubuto mini da cewa: "Ka yi tambaya - Allah Ya jikanka - kan tauhidi da kuma abin da wadannan mutane suke fadi. Daukaka ta tabbata ga Allah Wanda babu wani abu tamkarSa, Shi ne Mai ji, Mai gani. Allah Ya daukaka ga barin siffantawar masu siffantawa, wadanda suke kamata Allah da halittarSa, masu kage wa Allah. To ka sani -Allah Ya rahamshe ka- cewa ingantacce tafarki wajen tauhidi shi ne abin da Alkur'ani ya saukar da shi na siffofin Allah Mai Girma da Daukaka. To ka kore ga barin Allah (S.W.T.) dukkan korewa da kamantawa, domin babu korewa ba kuma kamantawa. Shi ne Allah Tabbatacce Ya daukaka ga barin siffantarwar masu siffantawa. Kada ku ketare Alkur'ani ku bata bayan (cikakken) bayani([178]) ".

Batun dayantuwar zatin da tsarkake shi ga barin kama da halitta kuwa, Hamza bn Muhammad ya ce: 'Na rubuta tambaya ga Abul Hasan Al-Kazim (a.s.) kan jiki da kama (da ake danganawa ga Allah), sai ya rubuto min cewa: "Tsarki ya tabbata ga Wanda babu wani abu tamkarSa, ba jiki babu kama([179]) ".

Haka nan muke karanta tauhidi tsarkakakke, kubutacce na Allah (S.W.T.) a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da karantarwarsu da ke nuna ainihin ruhin Alkur'ani da abubuwan da yake tattare da su, da abin da ayoyinsa suka kunsa. Da wannan ne suka tabbatar da akidar tauhidi, suka kore barnace-barnace da shubuhohi da bata wadanda aka jarrabi tunanin Musulunci a wancan lokacin. Haka kuma wannan bayani yake raddi kan batattu da karkatattun 'yan gulatu (*) (masu wuce gona da iri wajen soyayya), 'yan Mufawwida (masu cewa an bar dan'Adam haka kawai a sake komai yayi daga gare shi ne), 'yan Mujassima (masu siffanta Allah da jiki), 'yan Hululi (masu akidar cewa Allah Yana shiga wasu halittu) da kuma masu akidar haduwa, wato Allah Ya hadu da halittanSa suka zama abu guda.

Haka kuma bayanan Ahlulbaiti (a.s) sun fayyace al'amurra wa wadanda suka shiga rudani suka cudanya tafarkin Ahlulbaiti (a.s), tsarkakakke na gaskiya, wanda bai yarda da karairakin 'yan gulatu da 'yan mufawwida da 'yan hululi ba wadanda suka yi da'awar suna bin Ahlulbaiti (a.s), da wadancan kungiyoyi na bata.

Sau da yawa masu neman raba kan musulmi suna cudanya gaskiya da karairayi, suna karkatar da gaskiya, suna kage da kuma gafalantar da jahilai domin shuka gaba da raba kan al'umma da taimaka wa abokan gaba.

Adalcin Allah Da Sharhi Kan Halayyar Dan'adam

"Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18)

Adalci siffa ce, cikin siffofin Allah (S.W.T.). Muna iya ganin gurabun adalcinSa a dukkan bangarorin samammu, kamar fagen halitta da samarwa da fagen dabi'a da halittar mutum da dabba da tsiro, haka kuma muna ganin wannan adalcin cikin shari'a da dokokin Ubangiji. "Lalle Allah Na yin umurni da adalci da kyautatawa". (Surar Nahli, 16: 90)

Haka ma adalcin Ubangiji ya bayyana cikin abin da Yake hukumtawa da kaddarawa kan halittunSa na hukumci da kaddara, da cikin abin da Ya shar'anta na shari'u da sakonni. Kamar yadda yake bayyana a fagen lahira, ranar hisabi da sakamako. Zai sakantawa mai kyautatawa da kyautatawar, mai mummunan aiki kuwa da irin aikinsa. "Kuma Ubangijinka ba Ya zaluntar kowa". (Surar Kahf, 18: 49) "Sa'an nan kuma a cika wa kowane rai abin da ya sana'anta". (Surar Bakara, 2: 281)

"Allah ba Ya kallafawa rai face ikon yinsa, yana da ladan abin da ya aikata, kuma a kansa akwai zunubin abin da ya yi ta aikatawa...". (Surar Bakara, 2: 286)

Bisa wannan tsarin ne musulmin farko suka tafi wajen fahimtar alakarsu da Allah (S.W.T.) da fahimtar halayyar 'yan Adam da ayyukansu. Daga bisani sai falsafa ta shigo ga kuma ra'ayoyin ilmin tauhidi dukkansu masu sassabawa juna. Hakika wadannan sun tsirar da ra'ayoyi uku kan fassarar ayyukan mutane da alakarsu da iradar (nufi) Allah Madaukakin Sarki. Wadannan ra'ayoyi kuwa su ne:

1. Jabru (Tilastawa).

2. Tafwidhu (Sakarwa).

3. Babu Jabru ballantana Tafwidhu.

Hakika wadansu kungiyoyi da mazhabobi sun yi mummunan fahimta wa zahirin wadansu ayoyin Alkur'ani, kamar fadinSa (S.W.T.) cewa: "Zahirinsu ya sanya irin wannan kungiya suka yarda da Jabru. Abin da wannan ra'ayi yake nufi shi ne dan'Adam ba ya mallakar nufi kuma ba shi da zabi, shi ba kome ba ne face bigire da gurin saukar kaddararrun abubuwa daga Allah (S.W.T.). A bisa wannan ra'ayi, mutum abin tilastawa ne, ba shi da wani zabi cikin al'amurransa. Masu irin wannan ra'ayi ana kiransu da sunan Mujabbira.

Ra'ayi na biyu kuwa shi ne mai cewa an sakar wa dan'Adam ikon zabi wajen ayyukansa, da kuma nufinsa babu nufin Allah a cikin ayyukansa. Kai suna ganin ma cewa Allah ba Ya iya hana mutum yin abin da ya yi nufin yi ko sabo ne kamar kisan kai, zalunci, shan giya, ko kuwa ayyukan biyayya ne kamar su adalci, kyautatawa, salla da dai sauransu. To da wannan, dan'Adam yana da 'yanci ga barin Allah (S.W.T.), wannan kuwa shi ne ra'ayin Mu'utalizawa.

To Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun yi raddi wa wadannan ra'ayoyi guda biyu, sun nuna bacinsu gaba daya. Kowanne daga ra'ayoyin nan biyu sun saba da abin da Alkur'ani ya zo da shi, akidar tauhidi kuwa ta kafu kan tushensa ne. su Imamai (a.s.) sun fayyace mana cewa akwai bayyananniyar alaka tsakanin irin yadda ake fahimtar halayyar mutum da imani da adalcin Allah. Suka ce lallai abin da ra'ayin cewa mutum ba ya mallakar wani nufi ko zabi sai dai shi abin tilastawa ne kurum, yana janyo tuhumtar Mahalicci Mai girma da Daukaka da zalunci da kore adalci daga gare Shi, lallai kuwa Ya girmama daga hakan. Saboda ma'anar wannan shi ne Allah Ya tilastawa mutum aikata sharri sannan kuma Ya yi masa ukuba dominsa, haka nan Ya tilasta masa aikata alheri sannan kuma Ya hana shi ladansa. Domin haka ne Imamai (a.s.) suka kakkabe wannan mumunan fassara wanda da yawan musulmi suka fada ciki a dalilin gurguwar fahimtar da suka yi wa zahirin wadansu ayoyi kamar cewa: "Yana batar da wanda Ya so, Yana kuma shiryar da wanda Ya so".

Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun yi wa matsalolin shiryarwa da batarwa tafsiri bayyananne mai dacewa da adalcin Allah (S.W.T.). Bayanin wannan yana tafe.

Haka nan kuma Imamai (a.s.) sun yi watsi da ra'ayin masu cewa an sakarwa mutum akala sai yadda ya ga dama zai yi, ba tare da Allah Yana iya hana shi ba. Sun bayyana cewa wannan ra'ayi karkatacce da cewa tuhumar Allah ne da rashin cikakken iko kan bayinSa da gajiyawarSa kan hakan. Alhali kuwa Allah (S.W.T.) Mai cikakken iko ne, kuma Mamallakin dukkan halittunSa.

Imamai (a.s.) suna da matsaya matsakaiciya dangane da al'amarin da ya shafi adalcin Ubangiji. Wannan matsaya tana kore Tilastawa da Sakarwa, tana cewa: (Nufin mutum baya iya rabuwa da nufin Allah). Sun bayyana wannan alakar da take tsakanin nufin mutum da nufin Ubangiji bayani cikakke a akidance. Nan gaba za mu kawo ruwayoyinsu masu nuna wannan ra'ayi.

Kafin mu kawo wadannan ruwayoyi, bari mu yi dan sharhi kan batutuwan da mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suka bambanta da masu ra'ayoyi kan mas'alar adalcin Allah, bisa abubuwa guda uku na asasi:

Dan'Adam yana da nufi da ikon zabin duk aikin da zai yi, ko na alheri ko na sharri, haka kuma kin aikata shi. Mutum yana iya kisan kai ko sata ko zalunci ko karya, da wannan nufin da ikon da yake da shi. Haka kuma yana da daman tsai da adalci da aikata aikin kwarai da yin salla da barin haramtattun abubuwa, da wannan nufi nasa da iko.

Hakika Allah (S.W.T.) Yana da ikon hana mutum kowane aiki, kamar yadda yake da ikon sa mutum aikata kowane aiki ba tare da zabin mutum ya sami tasiri ba. Sai dai Allah ba Ya tilastawa kowa aikata alheri ko sharri.

Amma Shi Allah, domin tausayinSa da jin kanSa, Yana shiga tsakanin bawan da ya cancanci taimakonSa wajen aikata mummunan aiki, domin jin kai. Haka ma Yana taimaka masa wajen aikata alheri idan ya cancanci taimakon.

1. Wani abin da yake da dangantaka da adalcin Ubangiji kuma shi ne: Allah Yana sakantawa kowane mutum ranar kiyama da abin da ya aikata, alheri ko sharri. Sai dai kuma wata kungiyar ta musulmi tana ganin cewa mai yiyuwa ne Allah Ya shigar da mai kyautata aiki cikin wuta, mai mummunan aiki kuma aljanna, suna kuma dogara ne, bisa kuskure da mummunan fahimta, kan wannan aya mai girma: "Ba a tambayarSa ga abin da Yake aikatawa, alhali kuwa su ana tambayarsu". (Surar Anbiya, 21: 23)

Wasu jama'a daga cikin musulmi sun dogara da wannan ayar ne bisa tafsiri na kuskure, suka ce ba ya wajaba kan Allah (S.W.T.) Ya cika alkawarin sakayya da Ya yi a ranar kiyama. Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun mai da martani kan wannan zance da cewa, wannan ya sabawa gaskiyar Allah Ta'ala da adalcinSa.

Wancan ra'ayin yana daidaita mai kyautatawa da mai mummunan aiki, hakan kuwa yana rusa kimar kallafawa bayi da kuma sanya shari'a. Ingantaccen zance dai shi ne babu wani aikin da ba shi da sakamako, ko kuma mai daukar laifin yinsa, kamar yadda aya ta ce:

"To wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai ganshi. Kuma Wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi". (Surar Zalzala, 99: 7-8)

2. Ra'ayoyin sashin musulmi sun tafi a kan cewar ya dace ga Allah (S.W.T.) Ya kallafawa bayi abin da yafi karfinsu, wannan kuwa sun fade shi ne domin dogara kan fahimta ta kuskure da suka yi wa wannan aya mai girma: "Ya Ubangijinmu Kada Ka sanya mu daukar abin da babu iko gare mu da shi". (Surar Bakara, 2: 286)

Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun kore wannan fahimta suna masu bayanin cewa ta saba da adalcin Allah da kuma bayyanannen fadi na Alkur'ani mai girma, cewa: "Allah ba Ya kallafa wa rai face abin da zai iya dauka". (Surar Bakara, 2: 286)

To yanzu za mu kawo sashen ruwayoyi da tattauna-war Ahlulbaiti (a.s), masu mana sharhin wadannan ginshikai na asali da fassara halayyar mutum da alakar da ke akwai tsakanin nufin mutum da ta Allah (S.W.T.). Wadannan ruwayoyi suna kulla tafsiri da sharhin halay-yar mutum da tushen adalcin Allah domin su karfafa mana dayantaka (ta Ubangiji) fahimta da tunani da kuma i'itikadi cikin sakon Musulunci. A lokaci guda sun bata ra'ayin Jabru da Tafwidhu da ma dukkan sauran tunace-tunace da kirdado wadanda suka fice daga tafarkin Alkur'ani.

Imam Sadik (a.s.) ya ce: "Allah Ya halicci halittu Ya kuma san makomarsu. Ya umarce su (da ayyukan biyayya) Ya hane su (ayyukan sabo). Kuma bai umarce su da abu ba face Ya sanya musu hanyar barin abin. Ba su zamowa masu riko (da umarnin) ko masu bari face da izinin Allah Ta'ala([180]) ".

Yayin da Imam Ali bn Abi Dalib (a.s.) ya tafi kasar Sham (Syria), domin yakar Mu'awiyya a Siffin, wani daga sahabbansa ya tambaye shi cewa:

"Ya Amirul Muminina! Ka ba mu labarin wannan tafiya tamu, shin da hukumcin Allah ne ko da kaddararSa?" sai ya amsa masa da cewa: "Saurara dattijo, na rantse da Allah ba kwa hawan wani tudu ko ku gangara cikin wani kwari face bisa hukumcin Allah da kaddararSa".Sai Dattijon ya ce: 'Ga Allah nake neman ladar wahalata, Ya Amirul Muminina'. Sai Imam Ali (a.s.) ya ce da shi:"Kaiconka! Ta yiyu kana zaton hukumci lizimtacce da kaddara yankakkiya! Da haka al'amarin yake da sakamako da horo sun baci, kuma da alkawari da narko sun warware. Allah (S.W.T.) Ya umarci bayinSa bisa zabinsu, Ya hana su domin gargadi, Ya kallafa musu sassauka bai kallafa musu mai tsanani ba, Yana biyan kadan da mai yawa. Ba a saba masa domin rinjaya, ba a tilastawa don a yi maSa biyayya. Bai aiko Annabawa don wasa ba, kuma bai sauko da Littafi wa bayi haka a banza ba. Bai kuwa halicci sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu a banza ba; "Wannan shi ne zaton wadanda suka kafirta. To, bone ya tabbata ga wadanda suka kafirta daga wuta([181]) ".

An ruwaito daga Imam Ali bn Musa al-Ridha (a.s.) cewa an ambaci Jabru da Tafwidhu a gabansa, sai ya ce: "Shin ba zan sanar da ku wata ka'idar da ba za ku sassaba a cikinta, kuma duk wanda ya yi jayayya da ku sai kun rinjaye shi ba?Sai muka ce: 'E, a sanar da mu', sai ya ce:"Allah Mai Girma da Daukaka ba a biyayya gare Shi domin tilastawa, ba a saba masa don rinjaya, ba ya sake da bayinSa cikin mulkinSa. Shi ne Mamallakin abin da Ya mallakar masu, Mai iko kan abin da Ya ba su ikonSa. Idan bayinSa sun yi biyayya gare Shi, ba zai tare ko Ya hana su ba. Idan kuwa suka zabi su saba masa, in Ya ga damar tare su sai Ya yi, idan kuwa bai tare su ba suka aikata sabon, to ba kuwa Shi Ya jefa su ciki ba". Daga nan sai ya ce: "Wanda duk ya kiyaye wannan maganar, to lallai zai rinjayi mai sabawa da shi([182]) ".

A cikin littafin Sharh al-Aka'id na Shaikh Mufid an ce: "An ruwaito daga Abul Hasan na Uku (a.s.) yayin da aka tambaye shi batun ayyukan bayi; shin halittattu ne daga Allah Ta'ala? Sai ya amsa da cewa: "Da Shi Ya halitta su da bai barranta da su ba, alhali Yana cewa: 'Lalle ne Allah Barrantacce ne daga masu shirka'. Barrantan nan ba ta shafar zatinsu, Ya dai barranta ne daga shirkarsu da munanan ayyukansu([183]) ".

A cikin littafin Kitabul Tauhid na Muhammad bn Ajlan, ya ce: "Na tambayi Abu Abdullah (a.s.) cewa: 'Shin Allah Ya sakar wa bayi al'amarinsu ne?', sai ya ce: "Karimcin Allah ya wuce gaban Ya saki al'amurransu gare su", sai nace: 'To kenan Allah Ya tilasta wa bayi aikata ayyukansu kenan?, sai ya ce: "Adalcin Allah Ya wuce gaban tilastawa bawa yin wani aiki sannan kuma Ya azabta shi a kan wannan aiki([184]) ".

A ruwaito cikin Uyunul Akhbar al-Ridha (a.s.) wajen fadar Allah Ta'ala cewa: "Kuma Ya (Allah) bar su a cikin duffai, ba su gani". (Surar Bakara, 2: 17)

Abu Abdullah (a.s.) ya ce: "Ba a siffanta Allah da bari kamar yadda ake siffanta halittunSa, sai dai yayin da Ya san cewa ba su dawowa ga barin kafirci da bata ba, sai Ya hana su taimako da ludufi (tausayi), Ya bar su da zabinsu([185]) ".

Har ila yau ya zo cikin wannan littafin wajen tafsirin Imam Ridha (a.s.) kan fadin Allah (S.W.T.) cewa: "Allah Ya sa rufi a kan zukatansu". Sai ya ce: "Abin da ake nufi da 'Khatam' shi ne 'al-Dab'u' watau rufi a kan zukatan kafirai domin yi musu ukuba kan kafircinsu, kamar yadda Allah (S.W.T.) ya ce:

"A'a Allah ne Ya rufe a kansu (zukatansu) saboda kafircinsu, saboda haka ba za su yi imani ba face kadan([186]) ". (Surar Nisa', 4: 155)

To haka ne tafarkin Ahlulbaiti (a.s) yake fayyace manufar shiriya da bata da kuma cewa Allah (S.W.T.) bai halicci mutane suna batattu ko shiryayyu ba. Sai dai Ya bar musu zabi, Ya ba su nufi, Ya kuma bayyana musu hanyar alheri tare da gargadi kan hanyar sharri da halaka, Allah Ta'ala Yana cewa: "Lalle ne Mu, Mun shiryar da shi (mutum) ga hanyar kwarai, ko ya zama mai godiya, ko kuma ya zama mai kafirci". (Surar Insan, 76: 3)

Kuma Yana cewa: "Kuma Muka shiryar da shi ga hanyoyi biyu". (Surar Balad, 90: 10) Watau Mun sanar da shi hanyar alheri da ta sharri, zabi kuma na gare shi.

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fassara ayar da cewa: "Su dai hanyoyi ne guda biyu, hanyar alheri da hanyar sharri. Kada hanyar sharri ta fi soyuwa gare ku bisa hanyar alheri([187]) ".

Tafarkin Ahlulbaiti (a.s) ya zabi ra'ayi tsarkakakke na bayani kan halayyar dan'Adam na alheri ko sharri, da wata ka'ida: "Babu Jabru ba tafwidhu, sai dai al'amari ne tsakanin al'amurra biyu, watau mataki tsakanin matakai biyu". Yayin da aka tambayi daya daga cikin Imaman Ahlulbaiti (a.s), shin akwai wani mataki tsakanin tilasta-wa (jabru) da sajarwa (tafwidh)? Sai ya amsa da cewa: "Abin da yake tsakaninsu ya kai fadin tsakanin sama da kasa".

Wannan shi ne takaitaccen bayanin tafarkin Ahlul-baiti (a.s) kan batun Jabru da Tafwidh, haka ne kuma akidar musulmin da suka yi koyi da tafarkinsu take.

Ra'ayin Ahlulbaiti (a.s) Dangane da Batattun Kungiyoyi

Babu shakka makiya Musulunci sun san cewa Ahlul-baiti (a.s) su ne mabubbuga ta asali da tsarkakar addini mai kwaranye wa musulmi dukkan wahalhalu da bala'u. Su masu daraja ne a zukatan musulmi bai daya.

Kowa yana ganin girman alkadarinsu, yana tsarkake duk abin da ya fito daga gare su ko ya karkare zuwa gare su. Don haka ne masu neman rushe addini da shuka masa dasisa suke fuskantar wannan tushe na Musulunci domin su sami damar shuka barna alhali suna karkashin inuwar Ahlulbaiti (a.s). Suna daukar tutar Ahlulbaiti (a.s) da sunan goyon bayansu domin su sami damar kaidi da rushe akidar tauhidi, alhali Ahlulbaiti (a.s) sun barranta daga gare su da kuma tsine musu albarka. Wadannan irin jama'a sun kirkiri akidun bata da karkatacciyar falsafa mai cewa Allah Yana hululi (wato Ya shiga jikin wata halitta daga cikin halittunSa) cikin Imamai - Allah Ya daukaka ga barin hakan- da cewa Allah Ya sakar wa Imamai (a.s.) al'amurran arzurtawa da tasiri cikin halittar aljanna da wuta.

Ba su tsaya nan ba sai da sashinsu ya dangantawa Imamai (a.s.) allantaka. Duk hakan kuwa sun yi shi ne domin kaidi wa Musulunci da musulmi da rusa akidar tauhidi. Hakika masu wannan aiki sun sami asali ne daga kungiyoyi irin na Majusawa, Manawiyya da Mazdakawa wadanda suka shiga Musulunci a munafurce, ba tare da sun yi imani ba. Haka nan, akwai tunanin kiristoci da yahudawa a cikin wannan yunkurin rusawa([188]) (*).

Wadannan mabarnata sun bi wancan hanyar suka rudar da hankula da shuka rikici da kirkirar ruwayoyi da ra'ayoyi fandararru, suka danganta su ga Ahlulbaiti (a.s) bisa karya. Saboda haka manyan malami suka rubuta littattafai kan masu ruwaya wato Ilmul Rijal domin tona asirin makaryata da masu kirkira da masu munanan akida tun zamanin Manzon Allah (s.a.w.a.) har ya zuwa karshen jerin Imamai (a.s.), amintattun maruwaita daga Manzon Allah (s.a.w.a.). Ta hanyar ne suka jefar da duk wata ruwaya ta karya da kuma duk wani maruwaici mai kirkira ake gane shi, kamar yadda Najashi ya yi cikin sanannen littafinsa nan na Rijalul Najashi da Shaikh Dusi cikin littattafansa na Al-Fihrist da kuma Rijalul Dusi da dai sauransu.

Tarihi yana sanar mana samuwar wasu kungiyoyi fandararru wadanda suka danganta kansu da Ahlulbaiti (a.s) kamar 'yan Gullatu da 'yan Mufawwidha, alhali kuwa Ahlulbaiti (a.s) sun barranta da su, sun la'ane su da kuma koransu. Baya ga haka ma, malaman mazhabar Imamiyya (Shi'a) suna hukumta su da cewa su najasa ne.

Al-Nawbakhti([189]) (*) cikin littafinsa mai suna Firakush Shi'a ya ambato kungiyoyi daban-daban na 'yan Gullatu da 'yan Mufawwidha, da kuma ambaton matsayar Imaman Ahlulbaiti (a.s) dangane da su, ga kadan daga cikin abin da yake cewa:

"Amma batun sahabban Abul Khaddab Muhammad bn Abi Zainab al-Ajda al-Asadi da duk wanda yake da ra'ayi irin nasa, to lallai sun watse lokacin da suka ji cewa Imam Sadik (a.s.) ya la'anci Abul Khaddab, ya kuma barranta daga gare shi da sahabbansa". Har zuwa inda yake cewa: "Wata kungiya daga cikinsu ta ce Abu Abdullah Ja'afar bn Muhammad Sadik shi ne Allah - Allah Ya daukaka ga barin haka daukaka mai girma - sannan Abul Khaddab kuma Annabi ne mursali.

Wata kungiyar kuwa cewa ta yi: "Ja'afar bn Muhammad shi ne Allah - Wal iyazu billah- kuma Shi Allah (S.W.T.) wani haske ne mai shiga jikkunan wasiyyai ya kuma zauna a cikinsu. Wannan haske sai ya kasance shi ne Ja'afar bn Muhammad Sadik, sannan ya fita daga jikinsa ya shiga jikin Abul Khaddab([190]) ". Bayan al-Nawbakhti ya bijiro da wadannan batattun akidu sai ya ce:

"Wadannan kungiyoyin 'yan Gullatu masu da'awar Shi'a, sun sami asali ne daga addinan Kharmadaniyya(**) da Mazdakiyya([191]) (*)da Zindikiyya([192]) (**) da Dahriyya([193]) (***) duk madaurinsu guda ne, Allah Ya la'ancesu. Dukkansu sun tafi a kan kore rububiyyar Allah Mahalicci (Allah Ya daukaka ga barin hakan), sun kuma tabbatar da ita wa jikkuna ababen halitta da nufin wai jikkunan su ne bigiren da Allah Yake zama, sannan kuma shi Allah Ta'ala wani haske ne da ruhi mai ciratuwa daga wannan jikin zuwa wani. Face dai su sun sassaba ne kurum wajen shugabannin da suke bi, sashinsu yana barranta daga sashi yana kuma la'antarsa([194]) .

Al-Nawbakhti ya kara da nakalto fandararrun kungiyoyin da suka riga suka mace, masu fakewa da jingina kansu ga Ahlulbaiti (a.s) kamar haka:

"Wata kungiya ta ce wai Muhammad bn Hanafiyya dan Imam Ali (a.s.) 'shi ne Mahdi, Imam Ali ya kira shi da Mahdi, bai mutu ba kuma ba zai mutu ba, wannan ba ya halatta, sai dai kawai shi ya faku ne, ba a kuma san inda yake ba. Zai dawo ya mallaki kasa, babu wani Imami bayan fakuwarsa har zuwa dawowarsa wajen sahabbansa, su ne kuma sahabban Ibn Karb([195]) ". Sannan ya ce:

"Hamza bn Ammara al-Barbari cikinsu yake kuma shi mutumin Madina ne, sai ya rabu da su ya yi ikirarin cewa shi Annabi ne, shi kuma Muhammad bn Hanafiyya shi ne Allah - wal iyazu billahi -. Ya kuma ce shi ne Imam sannan kuma wasu abubuwa guda bakwai za su sauko masa daga sama, da su ne zai cinye dukkan kasa ya mallake ta. Ya kuma sami mutane daga Madina da Kufa da suka bi shi kan hakan. Imam Bakir (a.s.) ya tsine masa ya barranta daga gare shi, ya karyata shi, a sanadiyyar hakan ne kuma ya sa 'yan Shi'a suka barranta daga gare shi([196]) ".

Haka nan ma Imam Sadik (a.s.) ya la'anci Sa'id al-Nahdi wanda wadannan fandararrun kungiyoyin nan suke bi. Imam din ya kira shi shaidan, wanda ya yi wa Imam karya([197]) ".

Ga wasu ruwayoyin malaman Shi'a kan matsayin da Imam Sadik (a.s.) ya dauka dangane da wadannan 'yan Gullatu da kuma fandararrun ra'ayoyinsu. Misalin hakan shi ne abin da Imam din ya ce kan Abul Jarud da mabiyansa kamar yadda Ibnu Nadim ya nakalto cikin Alfihrist. "Imam Sadik (a.s.) ya la'ance shi ya ce: 'shi makahon zuciya ne da idanu([198]) '.

Kamar yadda kuma Imam din ya la'anci Abu Mansur al-Ajli, daya daga cikin 'yan Gullatu, an ruwaito cewa: 'Al-Kishshi ya kawo cikin Rijal dinsa shafi na 300 cewa Imam Sadik ya la'ance shi sau uku. Sannan kuma Yusuf bn Umar al-Thakafi, gwamnan Iraki, ya tsire shi a zamanin Hisham bn Abdul Malik([199]) '.

Hakika Imam Sadik (a.s.) ya bayyana matsaya kan wadannan 'yan gullatu, daga nan ya ambaci wasu daga cikinsu, su ne: Mughira bn Sa'id, Bazi, Sirri, Abul Khaddab Muhammad bn Abi Zainab al-Ajda', Mu'ammar, Bashshar Sha'iri, Hamza Barbari da Sa'id Nahadi, sai ya ce: "Allah Ya la'ance su, mu dai ba mu rabuwa da makaryata msu yi mana karya ko kuma wani mai gurgun tunani. Allah Ya isar mana ga dukkan makaryaci, Ya kuma dandana musu zafin karfe([200]) ".

A wani hadisin kuma Imam Sadik (a.s.) ya barranta daga 'yan Gullatu, inda yake cewa: "Ya ku jama'ar Shi'a - shi'ar Alu Muhammadu- ku kasance matsakaita, wadanda suka wuce gona da iri (masu guluwi) su dawo gare ku, wadanda kuwa suka yi nawa su risko ku". Sai wani mai suna Sa'id ya ce: 'Allah Ya sanya ni fansarka! Wane ne mai guluwi? Sai Imam ya ce masa:"Wasu mutane ne masu fadi game da mu, abin da mu ba mu fada ba, wadannan ba su daga gare mu, mu ma ba mu daga gare su". Sai mutumin ya ce: 'To wane ne mai nawa? Sai ya amsa masa da cewa: "Shi ne mai bidar (gaskiya) yana nufin alheri, alherin zai same shi kuma za a sakanta masa da shi([201]) ".

Daya daga cikin sahabban Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito cewa yayin da Imam din ya sami labarin cewa Abul Khaddab na wuce gona da iri sai idanunsa suka cika da hawaye yana cewa:

"Ya Ubangiji, na barranta ya zuwa gareKa, daga abin da Al-Ajda yake ikirari a kaina, gashina da fatar jikina sun ji tsoronKa. Ni bawa ne a gare Ka dan bawanKa, makaskanci mai tawali'u".Daga nan sai ya sunku'i da kai na dan lokaci kamar yana ganawa da wani abu, sai ya daga kansa yana cewa:"Haka yake, haka yake! Bawa mai tsoro, makaskanci gaba ga Ubangijinsa, kankani, mai tsananin tsoro. Wallahi ina da Ubangijin da nake bautarSa, bana yi masa tarayya da kome. Me ya same shi (Abul Khaddab)? Allah ya kunyata shi, Ya zuba masa tsoro. Kada kuma Ya ba shi aminta daga firgici a ranar kiyama…..ba haka amsawar Annabawa take ba, ko ta mursalai, ba kuma amsawa ta ba. Amsawa ta kam ita ce fadar cewa: Ya Allah na amsa maKa, na amsa maKa Ya Allah ba Ka da abokin tarayya([202]) ".

Sadir ya ce: 'Na ce da Abu Abdullah (a.s.) cewa wasu mutane suna ikirarin cewa ku alloli ne, suna kuma kafa hujja da fadar Allah (S.W.T.) cewa:"Kuma Shi ne Wanda ke abin bautawa a sama, kuma bautawa a kasa"", (Surar Zukhruf aya ta 84),sai ya ce:"Ya kai Sadir! (Ka sani) jina da ganina da fatata da namana da gashina duk sun barranta daga wadannan mutane, Allah ma Ya barranta da ga gare su. Ba kan addinina wadannan suke ba, ba kuma kan na iyayena ba. Na rantse da Allah ba zai tara ni da su ba ranar lahira, kuma ba su zo a wannan rana ba face Allah Na fushi da su([203]) ".

Kamar yadda suka yi wa Imam Bakir da Sadik (a.s.) karairayi kuma suka barranta daga gare su, haka nan ma suka yi wa Imam Musa Kazim (a.s.) bayan shahadarsa. Suka ce bai mutu ba, sai dai kawai an daukake shi ne kamar yadda aka daukaki Annabi Isa (a.s.) kuma nan gaba zai dawo. Imam Ridha (a.s.) dan Imam Kazim (a.s.) sai ya barranta daga gare su, ya kuma la'ance su.

Kamar yadda Imam Sadik (a.s.) ya ce ba za a rabu da masu yi wa Ahlulbaiti (a.s) karya ba, domin su rikita tafarkinsu, domin kaidi ga Musulunci, haka nan Ahlulbaiti (a.s) suka bayyana matsayinsu dangane da wadannan masu niyyar ruguza Musulunci.

Yana daga ni'imomin Allah ga Musulunci da musulmi cewa wadannan kungiyoyi sun gushe, babu abin da ya rage sai ambatonsu cikin littattafan tarihi. Sai dai abin ban mamaki da takaici shi ne wasu masu mugun nufi suna danganta tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da tatsuniyo-yi da barnace-barnace domin bakanta tafarkin Ahlulbaiti (a.s). Duk wani mai nufin alheri ba zai yarda da wannan ba bayan kuwa su Ahlulbaiti (a.s) da kansu sun barranta daga duk abin da ya saba wa tafarki madaidaici, kamar yadda muka ambata a baya. Babu shakka babu abin da masu sukar mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) suke yi face barazana ga hadin kan musulmi.

A daya gefen kuma, duk masu bincike suna iya ganin abubuwan da ake danganta su da sauran mazhabobin musulmi na akida, kamar su jabru da cewa Allah jiki ne kuma Yana zama a bisa kujera da cewa fadin kujerarSa taki bakwai ne, da cewa Allah zai shigar da kafarSa cikin wuta a ranar lahira sai Ya bice zafinta, da cewa Shi Yana saukowa nan duniya bisa wani farin jaki da dai sauransu.

Hakika a sarari yake cewa duk wadannan zantuttuka, kamar tatsuniyoyin Gulatu, suna warware akidar tauhidi, addinin Musulunci kuwa yana barranta daga gare su.

Tafarkin Ahlulbaiti (a.s) Wajen Tarbiyyar Mabiyansu

Imam Ja'afar Sadik (a.s.) ya ce: "Ni ina kin a ce mutum ya mutu alhali akwai wata ta'adar Manzon Allah (s.a.w.a.) da ta rage bai aikata ba([204])".

Babu shakka Ahlulbaiti (a.s) sun ba da muhimmanci kwarai wajen ilmantarwa da tarbiyyar mabiya da sahab-bansu da kuma shiryar da su zuwa hanya sahihiya ta tabbatar da rayuwa irin ta mai akida da halayen kwarai da biyayya ga hukumce-hukumcen Musulunci. Sun karfafa kan gina tarbiyyar musulmi bisa dacewa da Littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (s.a.w.a.) domin samar da gwarzaye masu daukar hasken Musulunci da kira zuwa gare shi ta yadda hasken zai watsu kan sauran jama'a su amfana da ilmi da kuma aiki. Ahlulbaiti (a.s) sun yi hakan ne saboda tabbatar da haraka ta Musulunci cikin al'ummar duniya bayan da muggan manufofin masu neman ruguza addini suka bayyana ko ina. Muna iya ganin wannan kokarin nasu a fili cikin halayensu da wasiyyoyinsu da tarbiyyarsu ga mabiyansu. Daga cikin maganganun Imam Bakir (a.s.) akwai raddi kan masu cewa duk wanda ya kaunaci Ahlulbaiti (a.s) ba ya bukatar lizimtar farilloli Musulunci. Imam ya bayyana musu tafarkin Musulunci na gaskiya wanda Ahlulbaiti (a.s) suke kai, kuma suke kaunar dukkan musulmi ya yi riko da shi. Idan ba ka san shi ba, to shi ne tafarkin ilmi da akida ta gaskiya da aiki da duk abin da Alkur'ani ya zo da shi, Annabi (s.a.w.a) kuma ya iyar da shi ya kuma rayu a kansa. Imam din ya ce:

"Wallahi ba mu da wata kubuta daga Allah, babu wata dangantaka tsakaninmu da Allah, ba mu da wata hujja a kan Allah, kuma ba a kusantar Allah sai da biyayya. Wanda ya zama mai biyayya daga cikinku to jibintarmu za ta amfane shi, wanda kuwa yake mai sabo daga cikinku, jibintarmu ba za ta amfane shi ba([205]) ".

Amru bn Sa'id bn Hilal ya ce da Abu Ja'afar (a.s.): 'Allah Ya sanya ni fansar ka! Ni da kyar nake saduwa da kai, sai dai bayan shekaru, to ka yi mini wasicci da wani abin da zan rika', sai ya ce masa:"Ina maka wasicci da tsoron Allah da tsantsaini da kokari, ka sani cewa tsantseni ba ya amfani sai tare da kokari([206]) ".

Daga cikin abin da Imam Sadik (a.s.) ya yi wasicci da shi ga wani mabiyinsa, Abu Usama ya kuma umurce shi da ya isar da shi ga sauran mabiyansa, shi ne cewa:

"Ku ji tsoron Allah ku kasance ado a gare mu, kada ku zamo abin kyama. Ku janyo mana dukkan soyayya, ku ije mana duk wani mugun abu, domin mu ba kamar yadda aka fada dangane da mu muke ba. Muna da hakki cikin Littafin Allah da dangantaka da Manzon Allah (s.a.w.a.) da tsarkakewa daga Allah, da haifayya tsarkakakkiya, ba mai ikirarin hakan, koma bayanmu, face makaryaci*. Ku yawaita ambaton Allah da tuna mutuwa da karatun Alkur'ani da salatin Annabi (s.a.w.a) domin akwai (ladan) kyawawan aiki goma ga ko wane salati a gare shi([207]) ".

Imam Sadik (a.s.) ya yi wasicci wa Isma'il bn Ammar, daya daga cikin sahabbansa, da cewa: "Ina ma wasicci da tsoron Allah da tsantseni da gaskiya cikin magana da mai da amana da kyautatawa makwabta da yawan sujada, don da wannan ne Annabi (s.a.w.a) ya umurcemu([208]) ".

Hisham bn Salim ya ce: 'Na ji Abu Abdullah (a.s.) yana fada wa Hamran cewa: "Ka dubi wanda ya kasa ka, kada ka dubi wanda ya fi ka, domin haka ya fi (tabbatar da) wadar zuci ga abin da aka yanka maka, kuma za ka fi cancantar kari daga Allah. Ka sani cewa kadan na dawwamammen aiki wanda aka yi yakini, a wajen Allah, ya fi mai yawa dawwamamme amma babu yakini a cikinsa. Ka sani cewa babu tsantsenin da ya fi nisantar ababen da Allah Ya haramta, da kuma kamewa ga barin cutar da musulmai da yi da su. Babu kuma abin da ya fi kyan hali faranta rai. Kuma babu dukiyar da tafi amfani daga wadatuwa da kadan mai biyan bukata. Babu jahilcin da ya fi jiji da kai daci([209]) ".

Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a.) kan siffofin muminai cewa: "Wanda ya yi bakin cikin mummunan aikinsa, ya yi farin ciki da kyakkyawan aikinsa, to mumini ne([210]) ".

Wadannan bayanai suna nuna siffar mumini mai riko da addini irin wanda Ahlulbaiti (a.s) suka yi kokarin samarwa kuma wannan shi ne tafarkinsu na tarbiyyar al'ummar musulmi. Shi ne kuma kiran da suka yi wa al'ummar Annabi (s.a.w.a) na lizimtar Littafin Allah da Sunnar Ma'aiki (s.a.w.a.) da gina rayuwa bisa wannan shiriya da tafarki mai karfi. Babu abin da ya fi dacewa ga musulmi sai bin shiryarwarsu da wasiccinsu da kuma wa'azinsu.

Gudummawar Ahlulbaiti (a.s) A Fagen Siyasa

Babu shakka al'ummar musulmi ta san matsayin Ahlulbaiti (a.s) da hakkinsu a kan wannan al'umma na shugabantarta. Domin haka ne za a iya ganin cewa Ahlulbaiti (a.s) suna matakin kololuwa a fagen siyasa da shugabancin Musulunci, domin su shiryar da al'umma, su tabbatar da gyara da aiwatar da hukumce-hukumcen addini da tsayar da adalci.

Duk wanda ya karanci tarihin Musulunci zai gani a sarari cewa shugabantar al'umma bayan zamanin Khulafa'u al-Rashiduna ta koma mulukiyya mai dora kanta bisa bayin Allah da jan hankulansu da dukiya da mukamai da kuma dankwafe hukumce-hukumcen shari'a da wasa da su. Wannan wasa da shari'a da makomar al'umma ya janyo sassabawa da juyin-juya-hali da jayayya mai tsanani da zubar da jinin kungiyoyi masu sabanin ra'ayoyi da tunace-tunace masu warware juna sun zama sakamakon wannan. Wasunsu suna goya wa sarakuna baya kan zaluncinsu da kuma horar da mutane su mika wuya da hana su bijirewa da warware mubaya'arsu ga azzalumai. Wasu kuma sun yi amfani da wannan damar (ta jayayya tsakanin musulmi) wajen tabbatar da mugun nufinsu na ruguza addini yayin da suka dora kira da halalta dukkan haram da dukiyoyi da mata da rusa wajibai, kungiyoyi irinsu 'yan Karamida, Mazdakiyya da Kharmiyya da dai sauransu. Wasu kuma suka dora kira zuwa ga rudani da rusa dukiyar hukuma da zubar da jini da kafirta kowa da kowa kamar su Khawarijawa.

Da wannan fantsamar ra'ayoyin siyasa masu sassabawa da fitinu da yake-yake na cikin gida, al'umma ta fuskanci hadari mai munin gaske. Ahlulbaiti (a.s), a matsayinsu na jagororin al'umma, sun kasance mafus-kanta da tushen sakon Musulunci wanda duk wata mishkila ta akida da tunani wacce ta kalubalanci musulmi ana iya warware ta a hannunsu. Domin wannan matsayi nasu na matabbacin tafarkin gaskiya, musulmi suna bin ra'ayinsu da riko da matsayin da suka dauka kan al'amurra. Face wadanda suka damfaru da masu iko, masu kare ayyukansu domin biyan bukatar kansa. A nan za mu yi dubi cikin tafarkin Ahlulbaiti (a.s) akan abubuwan da suka shafi ayyukan siyasa.

Tafarkin Ahlulbaiti (a.s) Kan Ayyukan Siyasa

Duk wanda ya bibiyo salon siyasar Ahlulbaiti (a.s) da gwagwarmayarsu ta bayyane da ta boye a tsawon karno-ni biyu da rabi zai iya gano cewa aikin da suka yi na siyasa yana bisa ginshikai kamar haka:

(1). Tarbiyyantar da al'umma kan kin zalunci da tabbatar da manufar adalci da bayyana fikirar imamanci da siyasa da fayyace rukunan hukumci da shugabanci cikin addinin Musulunci. Sun yi haka ne domin karfafa fahimtar siyasa ga al'umma da karfafa kulawarta da kiyayyarta ga azzalumai, da farkar da ita daga barci. Wanda ya yi bitar abin da Ahlulbaiti (a.s) suka ruwaito suka watsa daga Manzon Allah (s.a.w.a.) dangane da wannan al'amari, zai gane muhimmancin wannan mataki wajen farfado da ruhin siyasa da kiyayewa ta Musulunci. A nan za mu ambaci wasu daga cikin ruwayoyin da suke magana dangane da shugabanci da kuma nauyin da suka hau kan shugaba musulmi, da kuma kyamar da Musulun-ci yake wa zalunci da kuma kira zuwa ga adalci, don mu fahimci fikira da tunanin Ahlulbaiti (a.s) wajen fada da zalunci da kuma kwadaitar da al'umma zuwa ga canji da kuma motsi na siyasa.

An ruwaito daga Imam Muhammad Bakir (a.s.) cewa wani dattijo daga kabilar Nakh'a ya ce: "Na ce wa Abu Ja'afar (a.s.) cewa: Ni na kasance gwamna ne tun zamanin Hajjaj har yau din nan, shin za a karbi tuba ta? Sai na yi shiru, sannan na sake maimaita wannan tambayar, sai yace min: "A a; har sai ka mai da wa duk wani mai hakki, hakkinsa([211]) ".

Abu Hamza al-Thumali ya ruwaito daga Imam Abu Ja'afar al-Bakir (a.s.) cewa: "Yayin da Aliyu bn Husaini (a.s.) ya zo cikawa sai ya rungume ni ya zuwa kirginsa sannan ya ce: "Ya dana, ina maka wasicci da abin da babana (a.s.) ya mini wasicci yayin da cikawa ta zo masa, kuma da abin da ya ambata cewa babansa ya yi masa wasicci. Ya ce: Ya dana, na hane ka zaluntar wanda ba shi da mai taimako kanka sai Allah Ta'ala([212]) ".

Imam Sadik (a.s.) ya ce: "Babu zaluncin da yafi zaluncin da wanda aka zaluntan ba shi da mai taimakonsa a kan shi sai Allah Mai Girma da Daukaka([213]) ".

Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito daga kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Ku tsoraci zalunci domin shi duhu ne a ranar lahira([214]) ".

Imam Sadik (a.s.) ya ce: "Allah Mai Girma da Daukaka Ya yi wasicci ga wani Annabi da cikin Annabawansa wanda yake cikin masarautar wani jabbarin sarki cewa: 'Ka je wajen wannan azzalumin ka ce da shi; Ni ban shugabantar da kai domin zubar da jini da tara dukiya ba, sai dai kawai na shugabantar da kai ne domin ka raba Ni da sautin (karar) wadanda aka zalunta. Domin Ni ba zan bar zaluncin da aka yi masu ba ko da kafirai ne([215]) ".

Imam Sadik (a.s.) ya ce: "Da wanda ya aikata zalunci da mai taimakonsa da kuma wanda ya yarda da shi, to dukkansu ukun masu tarayya ne (cikin zaluncin)([216]) ".

Imam Sadik (a.s.) din dai ya ce: "Duk wanda ya yi uzuri wa zaluncin azzalumi, Allah zai dora masa wani azzalumi da zai zalunce shi, kuma idan ya yi addu'a ba za a amsa masa ba, kuma Allah ba zai ba shi ladar zaluncin da aka masa ba([217]) ".

Abu Basir ya ruwaito cewa: "Mutane biyu sun zo wajen Imam Sadik (a.s.) a kan wani lamari na mu'amala tsakaninsu. Yayin da Imam (a.s.) ya ji zancen kowannensu, sai ya ce: "Hakika wanda ya cimma bukatarsa da zalunci bai cimma kome ba. Lallai za a biya wanda aka zalunta da addinin azzalumin fiye da abin da shi ya dauka daga dukiyar wanda aka zalunta", daga nan sai ya ce: "Duk wanda yake aikata wa mutane sharri kada ya yi kyama idan aka yi masa. Hakika babu abin da dan Adam zai girba face abin da ya shuka. Babu wanda zai girbi abu mai dadi baicin ya shuka mai daci, babu kuma wanda zai girbi mai daci baicin ya shuka mai dadi". Sai mutane biyun nan suka yi sulhu kafin ma su tashi daga gare shi([218]) ".

A'imman Ahlulbaiti (a.s) sun ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Duk wanda ya tafi tare da azzalumi domin ya taimake shi, alhalin ya san cewa shi azzalumi ne, to, hakika ya fice daga Musulunci([219]) ".

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Adalci na sa'a guda ya fi ibadar shekaru saba'in na sallar dararensu da azumtar yininsu. Zalunci a hukumci na sa'a guda kuma ya fi tsanani da girma wajen Allah a kan sabon shekara sittin([220]) ".

Jabir bn Abdullah al-Ansari (r.a.) ya ce: 'Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda ya nemi yardar wani sarki da abin da yake fusata Allah, to ya fita daga addinin Allah([221]) ".

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda ya shugabanci mutum goma sannan bai yi adalci a tsakaninsu ba, zai zo ranar lahira hannayensa da kafafunsa da kansa na cikin ramin gatari([222]) ".

Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk mutumin da ya shugabanci wani al'amari na musulmi, sannan ya rufe kofa (ya ki sauraronsu) to yana cikin azabar Allah Mai Girma da Daukaka da la'anarSa har sai ya bude kofarsa ga mai wata bukata da mai (karar) wani zalunci, sun shigo([223]) ".

Kamar haka A'imma (a.s.) suke tarbiyyar mabiyansu da karkato da ra'ayin jama'a zuwa ga canji da gyara da shiga fagen siyasa ta hanyarta ta asali.

(2). Yankewa daga Azzalumai: Bayan shiryarwa da tarbiyya kan munin zalunci, Ahlulbaiti (a.s) sun kara da umurni da yanke hulda da azzalumai, kamar yadda ya zo cikin hadisi cewa:

"Duk wanda ya yi tafiya tare da azzalumai, alhali yana sane da cewa azzaluman ne, to hakika ya fice daga Musulunci" da kuma cewa: "Mai aikata zalunci da mai taimaka masa da mai yarda da shi dukkansu masu tarayya da juna ne".

Haka nan suke kira da yanke hulda da azzalumai da rashin taimaka masu. An ruwaito cikin hadisi cewa: "Idan ranar alkiyama ta zo mai kira zai yi kira: Ina azzalumai da mataimakansu; wanda ya shirya masu kurtun tawada ko ya daure musu wata jaka ko ya fere musu kan alkalami, ku tara su tare da azzalumai([224]) ".

Kyakkyawan misalin yankewa azzalumai shi ne abin da A'imma (a.s.) suka yi da matakan da suka dauka dangane da zalunci da azzaluman mahukuntan Umayyawa da Abbasiyawa a zamanin Imam Sajad, Imam Bakir, Imam Sadik, Imam Kazim, Imam Ridha([225]) (*), Imam Jawad([226]) (**), Imam Hadi da kuma Imam Hasan Askari (a.s.).

A wannan lokacin A'imma (a.s.) sun gamu da wahalhalu daban-daban daga mahukunta, kamar cutarwa da kora da sa ido da shiga kurkuku da matsi da tsoratarwa, za mu kawo kadan daga cikin irin wadannan abubuwa a cikin wannan littafi.

A matsayin misali na irin wannan yankewa, shi ne matsayin da Imam Sadik (a.s.) ya dauka dangane da halifan Abbasiyawa Abu Ja'afar Mansur wanda ya shahara da mugun hali da zubar da jini da zalunci ga zuriyar Imam Ali (a.s.). Malaman tarihi sun rubuta cewa, wata rana Mansur ya rubuta wasika zuwa ga Imam Sadik (a.s.) yana neman zama da shi don kokarin sanya shi cikin malaman hukuma. Sai Imam yaki duk kuwa da halin tsoratarwa da kaushin halin da mahukuntan suke nunawa.

Ga abin da Mansur ya rubuta: "Me zai hana ka ziyarce mu kamar yadda mutane suke ziyartarmu"?, sai Imam (a.s.) ya rubuta masa cewa: "Babu abin da muke tsoronka dominsa, babu wani abu daga sha'anin lahira a gare ka wanda zai sa mu kaunaci (saduwa da) kai dominsa. Ba ka kuma cikin wata ni'ima ballantana mu yi maka murna, ba ma kuma ganinsa a matsayin azaba ballantana mu yi maka jaje". Sai Mansur ya rubuto amsa ya ce: "Ka zauna da mu saboda ka yi mana nasiha". Sai Imam (a.s.) ya amsa masa da cewa:"Mai nufin samun duniya ba ya maka nasiha, wanda kuwa yake nufin lahira ba ya zama da kai([227]) ". Haka nan dai matsayar A'imma (a.s.) da raddinsu ya kasance ga mahukuntan da ba sa tsai da shari'a, ba su lizimtar ginshikanta.

To haka nan ma malaman fikihun mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suka bi tafarkin Imamansu wajen yanke hulda da azzaluman mahukunta ta hanyar fatawoyinsu masu haramta taimakawa azzalumai ko karbar aikin hukumominsu. Suna kawo wannan ne galibi a babin makasib wato hanyoyin neman abin masarufi. Bari mu kawo maganar Shahid Muhammad bn Jamal (*) Makki al-Amuli wanda aka fi sani da Shahidul Awwal (Allah Ya rahamshe shi) yayin da yake kawo sana'oi haramtattu cewa: "Da taimakon azzalumai cikin zalunci" (yana daga cikin haramtattun sana'oi), shi kuma mai sharhin littafin ya ce: "Kamar yi musu rubutu da kawo musu wanda suke zaluntarsa da dai makamantansu([228]) ".

Malaman sun hana karbar duk wani aiki a hukumar azzalumai sai dai da nufin yi wa Musulunci hidima da tunkude zalunci ga barin bayin Allah, ta yadda dai za a samu wani gyara ko wani amfani ga al'umma.

(3). Gwargwarmaya da abin da ya shafi amfani da karfi: Wajibcin umurni da aiki mai kyau da hana mummuna wani ginshiki ne wanda ya tabbatar da gwagwarmaya domin kawar da zalunci, kuma an lizimta da shi ga musulmi.

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Shugaban shahidai shi ne Hamza da kuma mutumin da ya mike ya umarci sarki azzalumi (da kyakkyawan aiki) ya hana shi (mummuna) sannan sarki ya kashe shi".

Duk wanda ya bibiyi tsarin rayuwar Ahlulbaiti (a.s) a fagen siyasa da sabawa zaluncin da suka yi, zai ga cewa hanya ce guda wajen sabawa zalunci da kira zuwa ga gyara da gwagwarmaya. Gwagwarmaya ta faro ne a zamanin mulkin Mu'awiyyah dan Abu Sufyan, yayin da ya dora dansa Yazid a kan wuyar al'ummar musulmi duk da cewa bai cancanci shugabanci ba kuma ya rasa dukkan sharuddansa. Wannan ta'asa ta janyo fasadi da kaucewar al'umma, abin da ya sanya Imam Husaini (a.s.) yin shelar jihadi. Imam (a.s.) ya zauna a Makka na tsawon wata hudu bayan barowarsa birnin Madina, daga bisani sai ya fuskanci kasar Iraki. Can a Karbala ne aka yi gumurzu tsakanin rundunar Yazid da jama'ar Imam Husaini (a.s.) 'yan kalilan, a can tsarkakken jini ya zuba, Imam (a.s.) ya yi shahada. Zubar da jinin Imam Husaini (a.s.) tare da Ahlulbaitinsa da kuma mabiyansa ya girgiza al'umma ya tashe ta daga barcin da take ciki. Wannan kuwa shi ne farkon tawaye wa azzaluman mahukunta masu fakewa da Musulunci don cimma burinsu da warware mubaya'ar jabu da shelar kawar da hukumcin bata-gari mai sabawa rukunan Musulunci. Wannan tawaye wa azzalumai shi ya yaye zanin malaman da suke kiran mutane zuwa kaskanci da mika kai bori ya hau, da gurbata ra'ayin ilahirin jama'a da karfafa cewa sai an lizimci mubaya'ar azzalumi an cika masa alkawari komin lalacewarsa. Wadannan muggan malamai dangin Bal'ama dan Ba'ura sun yi kunnen uwar shegu da fadar Manzon Allah (s.a.w.a.) ce wa: "Ba a karbar rantsuwar mai sabo", Da kuma fadinsa (s.a.w.a) cewa: "Babu biyayya ga halitta cikin sabon Mahalicci".

Suna yin biris da fadin Allah Ta'ala cewa: "Kuma kada ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku". (Surar Hud, 11:113).

Shi Shugaban shahidai, Imam Husaini bn Ali (a.s.) ya kaddamar da gwagwarmayarsa ne a shekara ta sittin da daya bayan hijira, kuma a wannan shekarar ne ya yi shahada a can yankin Karbala na kasar Iraki. Da wannan ne kuma ya rushe dukkan kiraye-kirayen muggan malamai na rauni gaban hukumomin zalunci da yarda da su. Hakika sautin shahada da jini ya rinjayi na kwadayi da kaskanci.

Imam Husaini (a.s.) ya bayyana wa mutane dalilan fitowarsa da tsarin da yake tafe bisansa da cewa:

"Ni ban fito domin girman kai ko alfahari ba, ba kuma domin barna a bayan kasa ko zalunci ba. Abin da kawai ya fito da ni shi ne neman gyara a cikin al'ummar kakana, Manzon Allah (s.a.w.a.). Ina nufin yin umurni da kyakkyawan aiki da hana mummuna, in kuma bi irin rayuwar kakana da babana([229]) ".

Sannan ya ayyana wa mutane siffofin shugaba wanda shi ne ja-gora mai jan ragamar musulmi, da wajibcin tsayuwa don gwagwarmayar sauya mai hukumci a yayin da ya karkace ya bar wadannan ginshikin. Ga abin da Imam Husaini (a.s.) ya rubuta wa mutanen Kufa:

"Ina rantsuwa da cewa ba wani ne shugaba ba face mai hukumcin da ya tsayar da adalci, mai riko da addinin gaskiya, mai tsare kansa bisa (umurnin) Zatin Allah([230]) ".

Daga cikin abin da ya rubuta wa manyan mutanen garin Basra kuwa, cewa ya yi: "Ni ina kiranku zuwa ga Littafin Allah da Sunnar AnnabiSa (s.a.w.a), domin an riga an kashe sunna an raya bidi'a. To idan kun saurari fadina kuka bi umurnina zan shiryar da ku tafarkin shiriya. Aminci ya tabbata a gare ku da rahamar Allah([231]) ".

Hakan nan Imam Husaini (a.s.) ya tabbatar wa al'umma yadda shari'a ta yi umarni da sabawa azzalumin shugaba, ya kuma yi shelar rukunan jihadi mai tsarki, domin sauya hukumcin azzalumai.

Bayan jihadin Imam Husaini (a.s.) mai albarka, Ahlulbaiti (a.s) sun taimaka wa yunkuri daban-daban da Alawiyyawa suka yi tsawon sama da karni biyu, a fadin kasashen musulmi.

Zaid bn Ali bn Husaini, wato dan Imam Zainul Abidin kuma jikan Imam Husaini (a.s.) ya yi yunkuri a shekara ta 121 bayan hijira. Wannan kuwa ya faru ne a zamanin Imam Sadik (a.s.) wanda kuwa ya goyi bayansa ya kuma yi juyayin shahadar Zaid (*).

Fudhail Rassan ya ce: "Na shigo wajen Abu Abdullah (a.s.) bayan an kashe Zaid bn Ali, sai aka shigar da ni cikin uwar daki, sai ya ce da ni: "Ya kai Fudhail, an kashe baffana? Sai na ce 'fansar ka nake (e an yi haka), sai ya ce:"Allah Ya jikansa, lallai shi ya kasance mumini mai sani, mai ilmi, mai yawan gaskiya. Lallai da ya yi nasara da ya cika alkawari. Lallai da ya sami mulki da ya san inda zai sanya shi([232]) ". Haka aka yi ta samun taimakawar Ahlulbaiti (a.s) wa masu yunkurin kawo gyara cikin Alawiyyawa.

Daya daga cikin bayyanannen misalin irin wannan mataki na siyasa kuwa, shi ne matakin da Imam Kazim (a.s.) ya nuna dangane da yunkurin da Husaini bn Ali ya yi a shekara ta 169 a birnin Madina, yunkurin da aka fi sani da Yunkurin Fakh([233]) (*) wanda aka yi shi a watan Zulkida na wannan shekarar.

Duk da cewa Imam Kazim (a.s.) ya ga alamun rashin nasarar yunkurin a wancan lokacin, babu shakka magan-ganun da ya yi sun nuna cewa yana goyon bayan ra'ayin jihadi. Ga abin da ya fadi wa shi Husainin yayin da ya ga yayi niyyar fita wannan arangama:

"Za a kashe ka, saboda haka ka tsananta yaki domin mutanen fasikai ne, suna bayyana imani suna boye munafunci da shirka. Lalle ne mu daga Allah muke kuma wajenSa za mu koma! Ga Allah nake neman ladan rashinku([234]) ".

Yayin da Husain ya yi shahada aka kawo kawukan wadanda suka yi shahada tare da shi wajen mahukuntan Abbasiyawa, sai aka tambayi Imam Kazim cewa wannan kan Husaini ne? sai ya ce:

"E, lalle ne mu ga Allah muke, kuma lalle ne mu zuwa gare Shi za mu koma. Na rantse da Allah, ya mutu musulmi ne salihi, mai yawan azumi, mai umurni da kyakkyawa, mai kuma hana mummuna, babu tamkarsa cikin mutanen gidansa([235]) ".

Shi dai Husain ya kasance ne yana kiran mutane da cewa: "Ina kiranku ne zuwa ga abin da Alu Muhammadu suka yarda da shi, da aiki da Littafin Allah da sunnar Annabi (s.a.w.a) a tsakaninku, da kuma tsayar da adalci a tsakanin jama'a([236]) ". Kiran da Husain ya yi, kira ne zuwa ga biyayya ga mutumin da ya cancanci shugabanci, wanda yake daga Alu Muhammadu, kuma shi ne Imam Kazim (a.s.), kamar yadda Zaid ya yi nufin mai da shugabanci ga Imam Sadik (a.s.) da ya yi nasara. Hakika halifan Abbasiyawa ya fahimci goyon bayan da Imam Kazim (a.s.) yake yi wa yunkurin Husain a yakin Fakh.

Allamah Majilisi ya ruwaito cewa: "Sai ya (halifan Abbasiyawa) ci gaba da zagin Dalibiyawa (jikokin Ali bn Abi Talib) har ya ambaci Musa bn Ja'afar (a.s.), sai ya zage shi yana cewa: 'Wallahi Husaini bai yunkura ba sai da umarninsa (Musa bn Ja'afar), ba abin da ya bi face abin da yake so domin shi (Imam Kazim) ne ma'abucin wasiyya a cikin mutanen wannan gidan. Idan na bar shi, Allah Ya kashe ni([237]) ".

Imam Jawad, jikan Imam Kazim (a.s.) shi ma ya bayyana tasa matsayar dangane da masu gwagwarmar, inda ya ce: "Bayan Dif (Karbala), ba a cutar da mu kamar cutarwar Fakh ba([238]) ".

Akwai misalai masu yawa na yunkuri da goyon bayan Ahlulbaiti (a.s) gare su, har wannan (yunkurin) ya zama tafarki da salo na aikin siyasa wanda yake da goyon bayan shari'a.

(4). Gwagwarmaya ta Siyasa: Wannan yana da muhimmancin gaske a rayuwar siyasar al'umma a duk lokacin da azzalumin shugaba ya bayyana ba ya gudanar da hukumce-hukumcen Allah Ta'ala, ba ya kuma tsaifa adalci a tsakanin mutane. Kowane Imami na Ahlulbaiti (a.s) ya shugabanci al'umma a fagen siyasa a zamaninsa, kuma ya kasance shi ne alamar bijirewa azzalumai a zukatan jama'ar musulmi. Wannan kuwa shi ne ya bai wa yunkure-yunkuren da aka yi siffar dacewa da shari'a. Halifofin Banu Umayya da Banu Abbas wadanda tarihi ya yi wa shaidar rashin lizimtar addini da barin adalci sun san irin kimar Ahlulbaiti (a.s) a zukatan musulmi, saboda haka suka bi hanyoyi daban-daban domin su nisantar da kaunar Ahlulbaiti (a.s) daga mutane, hanyoyi kamar su tsoratarwa da kai su kurkuku da kisa da rashawa da mukamai da sauransu. A matsayin misali, Mu'awiyya ya yi tawaye ga Imam Ali (a.s.) ya yake shi duk da cewa shi ne halaltaccen halifa.

Baya ga haka kuma, bai tsaya ba sai da ya yaki Imam Hasan (a.s.) ya yi tawaye wa halifancinsa, ya kashe shi da guba a shekara ta hamsin, bayan hijira. Yazid dan Mu'awiyya, shi ma ya dauki mataki irin na ubansa akan Imam Husain (a.s.), ya kashe shi tare da mutanen gidansa, ya ribaci zuriyar Manzon Allah (s.a.w.a.) yayin da Imam Husaini (a.s.) ya jagoranci yunkurin bijirewa hukumar Banu Umayya ta zalunci da aka tilasta ta a kan al'umman musulmi.

Bayan Imam Husaini (a.s.) ya yi shahada, musulmi sun karkata hankalinsu ga Imam Ali bn Husain, Zainul Abidin (a.s.), suna ganinsa a matsayin wata alama kana kuma makoma gare su, don haka ne masu yunkuri

Gwagwarmaya suke neman izininsa. Don haka ne ma a zamaninsa an sami masu jihadi domin kare Ahlulbaiti (a.s) da yawa, kamar yunkurin Madina da Makka da na Mukhtar Al-Thakafi da na Tawwabun, dukkansu suna yaki domin daukar fansa kan wadanda suka kashe Imam Husaini (a.s.). A wancan lokacin mutane suna ganin Imam Zainul Abidin a matsayin kololuwar bijirewa azzalumai duk da cewa bai motsa ba. Matsayin da ya dauka kan Yazid bn Mu'awiyya da Marwan bn Hakam da Abdul Malik bn Marwan da sauran azzaluman mahukunta, matsayi ne na mai bijirewa a asirce da taimakon masu yunkuri ba tare da shelar hakan ba. har ma Imam (a.s.) ya roki rahamar Allah ga Mukhtar, wanda ya dauki fansa kan wadanda suka kashe Imam Husaini (a.s.) ya kuma yaba da jihadin Mukhtar. Sannan kuma Imam (a.s.) ya yi amfani da makamin addu'a([239]) (*) mai bayyana irin ra'ayinsa na siyasa da akida, mai sabawa da ra'ayin su Yazid.

Imam Bakir (a.s.) dan Imam Zainul Abidin (a.s.) shi ma ya nuna matsayin da yake kai na bijirewar siyasa daga Banu Umayya. Imam ya sha wahala kwarai a hannunsu, musamman ma Hisham bn Abdul Malik mai bayyana kiyayya da gaba ga Alawiyyawa. A zamaninsa ne Zaid bn Ali dan uwan Imam Bakir (a.s.) ya fito jihadi.

Shi dai wannan halifa na Banu Umayya ya tabbatar cewa tushen wannan yunkuri na Zaid daga Imam Bakir da dansa Ja'afar Sadik (a.s.) yake. Don haka sai ya kira su daga Madina zuwa ga helkwatarsa da ke Sham, yayin da Imam Bakir (a.s.) ya shiga fadar Hisham sai ya yi sallama yana nuni zuwa ga mahalarta majalisar, amma bai yi gaisuwar sarauta ga halifan ba. Sai Imam ya zauna ba tare da da wani izinin sarki ba, hakan ya kara wa Hisham kiyayyarsa ga Imam har ma ya kama sukansa da cewa:

"Ya Muhammad bn Ali, ko yaushe sai an sami wani mutum daga cikinku yana raba kan musulmi, da kiran jama'a don su bi shi, domin wauta da karancin ilmi".

Sai Hisham ya ci gaba da suka, jama'ar da ke fada su ma suka fara sukar Imam din bayan Hisham ya yi shiru. Da ganin wannan ka san cewa an umurce su da hakan ne kafin ma Imam din ya shigo tare da dansa, Imam Sadik (a.s.). Ganin haka ke da wuya, sai Imam Bakir (a.s.) ya mike tsakiyar majalisar yana mai raddi ga sarki da cewa:

"Ya ku mutane! Ina kuke zuwa ne? Ina aka nufa da ku ne? Da mu Allah Ya shiryar da farkonku, da mu kuma Zai cika (shiryar) da na karshenku. Idan kuna da mulki abin gaggautarwa, to mu muna da mulki da aka jikirta, kuma babu wani mulki bayan namu, domin mu ne masu mulkin karshe".

Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Kuma kyakkyawan karshe tana tabbata ga masu tsoron Allah". (Surar A'araf, 7: 128). Jin haka, ya sa Hisham ya tsare shi([240]) .

To a cikin kurkukun ma Imam Bakir (a.s.) bai yi shiru ba, ya wayar da kan fursunoni kan batutuwan siyasa da jihadi har fursunonin suka sami tasirin wa'azinsa, inda suka tayar da hargowa a cikin kurkukun. Ganin haka, sai shugaban kurkukun ya isar da lamarin zuwa ga Hisham, inda shi kuma ya yi umarni da a fitar da Imam (a.s.) daga kurkukun a mai da shi birnin Madina, a hannun wani dan aiken sarki([241]) .

Muhammad bn Jarir Tabari ya rubuta cewa dalilin da ya sa aka mai da Imam Bakir (a.s.) zuwa Madina shi ne bazuwar tasirinsa kan tunanin mutanen Sham sakamakon wata muhawara da ta gudana tsakaninsa da wani shugaban kiristoci([242]) .

A wata muhawara da ta gudana tsakanin Hisham bn Abdul Malik da Zaid, a lokacin da labarin yunkurin Zaid din ya isa kunnen Hisham, Hisham ya ce da Zaid: "Na sami labarin kana ambaton halifanci kuma kana burinsa, alhali kai ba ka cikin mazowansa, kuma kai dan baiwa ne".

Sai Zaid ya mayar masa da martani da cewa, Annabi Isma'il dan baiwa ne kuma Allah Ta'ala Ya ba shi annabta. Sannan Hisham ya dora ambaton Imam (a.s.) da zagi, yana mai tambayan Zaid da cewa:

"Dan'uwanka Bakara kuwa...", sai Zaid ya amsa masa da cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ambace shi da Al-Bakir([243]) (*) kai kuma ka kira shi da Bakara (wato saniya), lalle sabaninka da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi yawa kuma za ka saba da shi a ranar lahira kamar yadda ka saba da shi a nan duniya, domin Annabi (s.a.w.a) zai shiga aljanna kai kuwa za ka shiga wuta". To wannan shi ne matakin da Imam Bakir (a.s.) ya dauka da kuma yunkurinsa na siyasa, har lokacin da ya yi shahada.

To daga nan sai zamanin dansa Imam Ja'afar Sadik (a.s.), a wannan lokaci na Imam Sadik (a.s.) kuwa bala'i ya yawaita kan al'ummar Annabi (s.a.w.a), ya kuma fi tsanani kan Alayensa (s.a.w.a). Imam Sadik (a.s.) ya kasance shi ne jagoran bijirewa azzalumai ta hanyar siyasa duk da yake bai yi magana bayyananniya kan masu iko ba. Masu yunkuri suna neman shawararsa da goyon bayansa, kai har da neman ya karbi jagorancin harkar, kamar yadda Abu Muslim Khorasani ya bukata yayin da ya mika mubaya'arsa ga Imam. Imam Sadik (a.s.) ya ki karbar wannan mubaya'a saboda rashin cikar sharudda da kasantuwar yanayi bai dace ba, kamar dai yadda ya yi lokacin yunkurin Zaid a zamanin Hisham bn Abdul Malik Ba'umayye.

Abul Abbas Saffah ya yi kokarin kashe Imam domin saninsa da mukaminsa na jagoranci da goyon bayansa ga bijirewa mahukunta. To amma Allah Ya kare shi daga sharrinsa, duk kuwa da cewa ya taba kiran Imam din daga Madina zuwa garin Hira da ke kasar Iraki, inda ya tsananta masa da kuma sanya shi karkashin 'yan leken asiri.

Yayin da Abu Ja'afar Mansur ya gaji Al-Saffah, shi ma ya ji tsoron matsayin Imam Sadik (a.s.) kamar yadda magabatansa suka ji, sau da yawa ya kan kira Imam (a.s.) daga Madina zuwa Iraki.

Ga yadda yake siffanta karfin Imam a fagen siyasa da tasirinsa kan masu gwagwarmaya, inda ya ke cewa: "Wannan bakin cikin (yana nufin Imam Sadik) da rike makoshin halifofi, korarsa ba ta halalta, kisan sa ba ya halalta. Ba don mun hadu da shi a bishiya mai kyakkyawan tushe, mai rassan da suka gabata, mai dadadan 'ya'ya, an kuma albarkaci zuriyarta aka tsarkake ta cikin Littattafai ba, da an sanya shi cikin mummunan karshe, saboda labarin da muka samu na tsananin aibantamu da mummunan magana da yake fada game da mu([244]) ". Wannan shi ne matsayin Imam Sadik (a.s.) da aikin da ya yi na bijirewa azzaluman mahukunta, da goyon bayan masu yunkurin kawo gyara.

Daga nan sai zamanin Imam Musa bn Ja'afar Kazim (a.s), dan Imam Sadik (a.s.), a lokacinsa cutar da musulmi da karkata addini da kwadaitar da mutane da dukiya sun tsananta a hannun Abbasiyawa. Don haka ne Imam (a.s.) ya kasance jogora wajen gyaran al'amarin Musulunci.

An sanya Imam (a.s.) karkashin leken asiri a zamanin Mansur wanda shi ya kai matuka wajen zaluntar Alawiyyawa da kwace dukiyoyinsu, da gina turakun gadoji da kadarkai da soraye a kansu da ransu, da azabtar da su cikin kurkuku.

To amma bayan da Muhammad Al-Mahdi ya gaji sarautar Abbasiyyawa sai tsoransa ga Imam Kazim ya yi tsanani, don haka sai ya kirayi Imam (a.s.) daga Madina zuwa Bagadaza domin ya hukunta shi. Al-Mahdi ya sa aka rufe Imam Kazim (a.s.) a kurkuku har zuwa wata rana da halifan ya ga Imam Ali bn Abi Talib (a.s.) a mafarko yana ce da shi: "To, shin, kuna fatan idan kun juya za ku yi barna a cikin kasa, kuma ku yanyanke zumuntarku?" (Surar Muhammadu, 47: 22). Wannan sai ya tsoratar da Mahdi ya fitar da Imam Kazim (a.s.) daga kurkuku.

A mulkin Al-Hadi, sarkin Abbasiyawa, ne bala'i ya tsananta kan Imam (a.s.) da kuma Alu Ali (a.s.). Ya ci gaba da korarsu da kashe su da neman batar da su gaba daya musamman ma bayan yunkurin Husain bn Ali wanda aka fi sani da waki'ar Fakh. Imam Kazim (a.s.) ya gamu da tsanantarwa da matsarwa har sai da ta kai Al-Hadi din ya hukumta Imam (a.s.) da hukumcin kisa ya kuma tasanma aiwatar da hakan. Malaman tarihi sun ruwaito cewa alkali Abu Yusuf almajirin Imam Abu Hanifa shi ne ya shiga tsakanin Al-Hadi da wannan kuduri da ya dauka na kashe Imam Kazim (a.s.), don Al-Hadin ya zaku kan kashe Imam (a.s.) har cewa ya yi: "Allah ya kashe ni idan na yi wa Musa ibn Ja'afar afuwa".

Daga nan sai Al-Hadi ya sanya Imam Kazim (a.s.) a kurkuku da hana shi damar gudanar da aikinsa na ilmantarwa da jagoranci a bayyane. Amma mutuwa ba ta bar shi ya aikata mummunan nufinsa, don kuwa ta kawo karshen wannan azzalumi jabberi.

Daga nan sai lokacin Haruna Rashid wanda aka sami jayayya mai tsananin gaske tsakaninsa da Imam Kazim (a.s.). Haruna Rashid ya yi kiran Imam da ya taho daga birnin Madina zuwa Iraki, inda ya ci gaba da tozarta shi da sanya shi a kurkuku da azabtarwa nau'i daban-daban, wadanda suka hada da daure shi da karfe yana daukansa daga wannan kurkukun zuwa wancan. Imam (a.s.) ya zauna a kurkuku tsawon shekaru, daga karshe Haruna Rashid ya ci da shi guba ta hannun shugaban dogarawan-sa mai suna Al-Sandi bn Shahik. Imam (a.s.) ya yi shaha-da ne a ranar 25 ga watan Rajab a shekara ta 183 bayan hijira.

Daga nan sai zamanin Imam Ridha, Aliyu bn Musa bn Ja'afar (a.s.), wanda shugabancinsa na siyasa ya wajabtawa Abbasiyawa la'akari da shi a sakamakon karfin alkadarin Imam (a.s.) da kaunar al'umma gare shi ga kuma tsanantar bijirewa ga Abbasiyawa. Wannan yanayi ya tilastawa halifan Abbasiyawa Ma'amun sanya Imam (a.s.) a matsayin magajinsa. Imam Ridha (a.s.) ya karbi wannan matsayi ba don sonsa ba, kana kuma da sharadin cewa shi ba zai shiga harkokin shugabanci ba, sannan idan Ma'amun ya mutu, halifanci zai koma hannunsa. To amma Imam Ridha (a.s.) ya yi shahada yayin da Ma'amun ya ba shi guba a shekara ta dari biyu da uku bayan hijira.

To bayan shahadar Imam Ridha (a.s.), wanda ya karbi jagoranci al'umma da lamarin Imamanci shi ne dansa Imam Muhammad Jawad (a.s.) wanda ya yi zamani da Ma'amun na dan lokaci. Ma'amun ya yi mu'amala da shi da girmamawa a munafunce, ya aurar masa da 'yarsa Ummul Fadhl domin ya sami soyayyar al'umma, yayi hakan ne kuwa domin ya juya hankulan mutane ya karkata ra'ayin masu gaba da shi, wadanda suke ganin Imam (a.s.) a matsayin jagora. Sai dai fa Ma'amun bai tsinana komai ba domin Imam Jawad (a.s.) ya bar Bagadaza ya koma birnin Kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.) saboda ci gaba da aikinsa na ilmantarwa da jagorancin al'umma a can.

To bayan da Ma'amun ya mutu sai dansa Al-Mutasim ya hau karagar mulkin Abbasiyawa, sai dai kuma shi Al-Mutasim bai jima a kan mulkin ba, to amma dai shi ma ya kasance yana jin tsoron Imam Jawad (a.s.) da kuma hadarin zamansa a Madina. To shi ma Al-Mutasim bai yi wata-wata ba sai ya kama tafarkin iyayensa yayin da ya dauko Imam daga Madina ya kawo shi helkwatarsa domin ya sanya ido a kansa. Marubuta tarihi sun ce Imam Jawad (a.s.) ya yi shahada ne a hannun Mutasim ta hanyar guban da ya sa masa cikin abinci a shekarar da ya kawo shi Bagadaza a lokacin kuwa hijira tana da shekara dari biyu da ashirin da biyar.

To bayan shahadar Imam Jawad (a.s.) dansa Imam Ali Hadi shi ne ya gaji jagorancin al'umma da Imamanci daga mahaifin nasa. A zamanin Mutawakkil Abbasi ne Imam Hadi (a.s.) ya fuskanci keta da cutarwar Abbasiya-wa. Mutawakkil da ma sananne ne da son wasa da kuma gaba da Alayen Manzon Allah (s.a.w.a.) da kashe su da korar su da yanke abincinsu da hana mutane taimakonsu. Imam Hadi (a.s.) ya kasance yana tsorata halifa Mutawakkil saboda haka sai ya dauko shi daga Madina ya kai shi garin Samarra ya sa ido sosai a kansa, ya kuma tilasta masa zama a can. To lokacin da al'amurra suka yi zafi wa Mutawakkil, sai ya fara barazanar kisa ga Imam Hadi (a.s.) baya ga daure shi da ya sha yi. A wasu lokuta ya kan sa a binciki gidan Imam Hadi (a.s.) da kai hari wa gidan, bugu da kari kan tsananta sanya ido a kansa saboda tsoron irin tasirin da Imam (a.s.) yake da shi a idon al'umma.

Marubuta tarihi sun ambaci dalilan da suka sa Mutawakkil ya ta da Imam Hadi (a.s.) daga Madina. Sibt Al-Jawziyya ya ce: "Malaman tarihi sun ce: Ya fito da shi daga Madinar Manzon Allah (s.a.w.a.) zuwa Bagadaza ne don yana tsananin kin Aliyu da zuriyarsa sai kuma ya sami labarin irin matsayin Aliyu Hadi a Madina da karkatar mutane zuwa gare shi. Wannan ya sa shi tsoronsa([245]) ".

Bayan shahadar Imam Hadi (a.s.) garin Samarra a shekara ta 254 bayan hijira, sai dansa Imam Abu Muhammad Hasan Askari (a.s.) ya kasance Imami mai kula da harkar al'umma da kuma shiryar da su. To shi ma dai matsayinsa kan Abbasiyawa tamkar na iyayensa ne, wajen fito-na-fito a fagen siyasa. To shi ma dai mahu-kumtan ba su bar shi don kuwa sun cutar da shi kamar yadda suka cutar da mahaifansa. Al-Muhtadi bn Al-Wasik sarkin Abbasiyawa ya sanya shi a kurkuku a garin Samarra, inda ya mika shi ga hannun gandurobobin kurkukun wadanda suka shahara da mugun hali da zalunci don azabtar da shi, amma Imam (a.s.) ya yi tasiri kansu har suka shiryu suka zamo mutanen kwarai.

Malaman tarihi sun kiyaye abubuwan da suka sami Imam Hasan Askari (a.s.) na matsanancin bala'i, kamar abin da Ahmad bn Muhammad ya ruwaito, inda ya ce:

"Yayin da Al-Muhtadi da fara kashe magoya bayan Ahlulbaiti (a.s) sai na rubuta wa Abu Muhammad Hasan Askari (a.s.) na ce masa: Ya shugabana, godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya shagaltar da shi (Muhtadi) daga barinka. Hakika na sami labari cewa yana maka barazana da cewa: "Wallahi sai na kore su daga duk sababbin kasashe", sai Abu Muhammad (a.s.) ya rubuta da hannunsa cewa: "Wannan shi zai takaita rayuwarsa([246]) ".

An ruwaito cewa, Imam Askari (a.s.) ya kasance cikin kurkuku a zamanin Al-Mutamad har lokacin da ya kira shi don warware wata matsala da ta faru tsakanin musulmi da wani malamin Nasara, a kan shayarwa (ruwan sama). Sai Imam (a.s.) ya warware ta, to a saboda haka Al-Mutamad ya fito da shi daga kurkukun kuma ya nemi a saki mabiyansa da ke tare da shi a kurkuku, hakan kuwa aka yi, wato a ka sake su.

Wannan shi ne kadan daga tarihin Ahlulbaiti (a.s) a fagen siyasa da fito-na-fiton da suka yi da hukumomin zalunci na lokacinsu wadanda suka doru a kan al'umma. Idan an duba da kyau za a ga cewa, silsilar Imamai goma sha daya mai albarka ta Ahlulbaiti (a.s) ta kasance wani fage ne na jagorantar al'umma da kuma shiryar da su. Don kuwa kowane Imami za a ga shi ne jagorar al'um-mar da ya kasance a cikinta, wanda kuma ya fi kowa ilmi da sanin ya kamata. Irin wannan tsari ba zai yiyu a same shi ba sai da shiri gabatacce daga Allah Ta'ala. Kuma babu makawa wannan bibiya ta jagorancin Ahlulbaiti (a.s) yana sanar da mu mukaminsu da fagensu na shugabancin akida da siyasa a rayuwar wannan al'umma.

Dubi Cikin Mazhabobin Fikihu

A zamanin Manzon Allah (s.a.w.a.) musulmi suna samun hukumce-hukumce da dokoki masu tsara al'amurransu na zamantakewa da ibada, kamar su salla, rabon gado, zaman iyali, kasuwanci, jihadi, aikin hajji da abin da ya shafi kasa da filaye da shari'u da sauransu ne kai tsaye daga Annabi (s.a.w.a), domin shi ne mai isar da sako, mai kira zuwa ga shiriya ta hanyar wahayi.

Bayan da ya koma ga Ubangijinsa Mahalicci, al'ummar musulmi sun koma ga Littafin Allah da Sunnar Ma'aiki (s.a.w.a.), suna daukar dokoki da sanin ra'ayin shari'a kan dukkan abubuwan da suka shafe su ta hanyar sahabbai da Ahlulbaiti (a.s), wadanda suka kiyaye Sunna da kuma Littafin Allah. Daga nan al'ummar musulmi ta sami ci gaba cikin salon rayuwa, saboda faruwar sabbin abubuwa cikin rayuwar mutane. Babu shakka wadannan sabbin abubuwa suna bukatar hukumcin Musulunci da sanin dokokin shari'a domin daidaitasu. Wannan fadada-wa cikin shari'a ya fara samuwa kusan a karshen karnin farko a zamanin Imam Muhammad Bakir (a.s.), wanda shi ne malamin Madina, kuma mokamar dukkan malaman zamaninsa. Malaman tarihi da na fikihu sun ruwaito cewa saboda hakan ne ma ake kiransa da Al-Bakir, domin fadadawarsa wajen ilmomi da yada su. A zamanin dansa Imam Ja'afar Sadik (a.s.) ne fannonin ilmi da fikihu da shari'a suka yi fure, yayin da shugabannin mazhabobi suka yi karatu a wajen Imam Sadik (a.s.) din. Da shi babansa Imam Bakir (a.s.) sun kasance masu ruwaito Sunna ne da kuma bayanin abin da Littafin Allah da sunnar suka kunsa, ba wai masu ijtihadi ba ne su.

A zamanin Imam Sadik ne aka fara samun mazhabobin fikihu kamar masu bin ra'ayi da kiyasi, wato mazhabar Imam Abu Hanifa, wanda ya yi karatu na wani lokacin a wajen Imam Sadik (a.s.) da sauran mazhabobi, wadanda daga baya suka takaitu cikin mazhabobi guda hudu, wato: Mazhabobin Malikiyya, Hannifiyya, Shafi'iyya da kuma Hambaliyya. Wadanda su ma wadannan mazhabobi sun rarrabu a tsakaninsu a wajen tafarkin Ijtihadi da yarda da wata ruwaya, a gefe guda kuma ga mazhabar nassi wacce Imam Sadik (a.s.) yake jagoranta, wacce ta dogara da Littafin Allah da Sunnar Annabi (s.a.w.a) wajen fitar da hukumce-hukumcen Musulunci, sannan kuma take watsi da ra'ayi da kiyasi. A daidai lokacin da kuma sauran mazhabobin suka sanya wasu hanyoyi da gano shari'a bayan Littafin Allah da Sunna, kamar su:

1. Kiyasi.

2. Istihsan (ganin dacewar ko kyaun abu)

3. Masalihul Mursala (maslahar al'amari)

4. Fathul Zara'i'i wa sadduha (bude kofar hanzari da rufe ta)

Mazhabobin Ahlussunnan nan guda hudu, Hanafiyya, Malikiyya, Hambaliyya da Shafi'iyya sun sassaba kan karbar wadannan hujjoji, ba su hadu gaba daya akansu ba. Za ka ga wasunsu suna tabbatar da wannan su yi watsi da wancan daga cikin hujjojin (hanyoyin samun hukumci).

A dalilin sassabawa wajen dauka ko watsi da wasu hujjoji mazhabobin fikihu guda hudun nan suka sami sabani tsakaninsu kuma suka saba da mazhabar nassi wacce A'imman Ahlulbaiti (a.s) suke jagoranta. Kuma a dalilin hakan ne mazhabobin nan biyar suka sassaba ka bayanan hukumce-hukumcen filla-filla. Wannan sabanin yana komawa ne ga abubuwa na tushe guda biyu, su ne:

1. Rikon wasu hujjojin (na fitar da hukumcin shari'a) daban tare da Alkur'ani da Sunna da sashen mazhabobin suka yi da kuma rashin riko da su a wajen wani sashen.

2. Sassabawa wajen karbar sashen ruwayoyi (hadisai) ko watsi da su domin dogaro da sharuddan karbar hadisi da gaskata sashen maruwaita ko a'a.

A sarari yake cewa sabanin da ke tsakanin mazha-bobin Musulunci, sabani ne na ilmi wanda bai kamata ya raba musulmi ba, ko ya nisanta tsakaninsu. Domin abin lura shi ne ana iya magance irin wannan sassabawa ta hanyar muhawara da bincike mai tsabta wanda babu son zuciya ciki. Wajibi ne irin wannan bincike a yi shi karkashin ginshikin ilimi yardaddu ga dukkan musulmi, tare da bude kofar ijtihadi wacce take rufe a wurin wasu mazhabobi. Yana da muhimmanci a gane cewa wannan sabani ba tsakanin Sunna da Shi'a yake ba, sai dai ya wanzu ne tsakanin mazhabobin fikihu kamar guda shida: Hanafiyya, Malikiyya, Shafi'iyya, Hambaliyya, Ja'afariyya da Zaidiyya, a kara kuma da ra'ayoyi da ijtihadin sashin malaman fikihu ko cikin wadannan mazhabobi ambatattu ko waje da su.

Yayin da aka bude kofar ijtihadi wa dukkan sassan musulmi, malaman fikihu kuma suka karbi aikinsu da aka sansu da shi, to za a iya iyakance ginshikan istinbadi (tsamo hukumci daga Alkur'ani da hadisi ko dai wani tushe na shari'a) da ayyana ko mene ne mabubbugan shari'a da kuma hanyar ciro hukumce-hukumce daga mabubbugar nan na tushe (wato Alkur'ani da Sunna). Domin ta hanyar komawa garesu su biyun da kokkofin ruwayoyi da hadisai da zubar da wadanda ba su inganta ba daga cikinsu, ba tare da son kai ko karkata ga wani ra'ayi ba, to musulmi za su iya yin watsi da mafi yawan sabanin da yake tsakaninsu, kuma za su iya gane abin da yake shi ne dai-dai, kuma su iya hade kansu waje guda. Duk da haka, irin ra'ayoyi da mahanga na ilmi da malaman fikihu suke da su za su wanzu, kamar yadda yake tsakanin malaman fikihu na ko wacce mazhaba ta Musulunci, kuma wannan wata dabi'a ce ta ilimi a duk wani fagen ilmi da ka sani a rayuwar dan'Adam. Saboda ba makawa a sami ra'ayoyin malamai a fagen ijtihadi da istinbadi domin malaman fikihu ba za su iya gano ainihin hukumce-hukumcen Ubangiji dukkansu gaba daya ba. Dole a samu mujtahidi (mai yin ijtihadi) yana dacewa yana kuskure kuma shi abin yi wa uzuri ne da kuma sakantawa da lada matukar ya yi bincikensa bisa tushen ilmi da ingantacciyar hanya ta shari'a.

Ga wasu misalan yadda ra'ayoyin malaman fikihu suke dacewa ko sassabawa, ba kuma tare da la'akari da ko daga Shi'a ko Sunna suke ba:

Imamiyya da Hambaliyya sun ce: Tahiyar farko wajiba ce a salla, amma Hanafiyya da shafi'iyya da Malikiyya sun ce mustahabi take ba wajiba ba. Amma tahiya ta karshe kuwa wajiba ce a ganin Shafi'iyya da Imamiyya da Hambaliyya, amma Malikiyya da Hanafiyya sun ce mustahabi ce .

Batun sallama kuwa, Shafi'awa da Malikawa da Hanbalawa sun ce wajiba ce, Hanafawa kuma suka ce ba wajiba ba ce. To amma Imamiyya kuma sun saba, wasu suna cewa wajiba ce, saura kuwa suka ce mustahabi ce. Daga cikin masu cewa mustahabi ce kawai har da Shaikh Mufid, Shaikh Tusi da Allama Hilli([247]) .

Dangane da sallar jam'i kuwa, Hanbalawa sun ce wajiba ce, wajibcin kuwa kan kowane mukallafi ne idan har zai iya, amma idan ya bar jam'i ya yi salla shi kadai, to ya yi zunubi, amma sallar tasa ta inganta. Imamiyya da Hanafiyya da Malikiyya da mafiya yawa cikin Shafi'awa sun ce ba ta wajaba wajibci na aini (wanda dole kowa ya yi) ko ma na kifaya (wanda wani yake dauke wa wani) ba, sai dai mustahabi ce mai karfi.

Kan cancantar zakka kuwa, shafi'awa da Hanbalawa sun tafi a kana cewa wanda ya mallaki rabin abin da zai ishe shi, ba a sa shi cikin fakirai, ba ya halalta a ba shi zakka. Imamiyya da Malikiyya suka ce fakiri a shar'ance shi ne wanda bai mallaki abin da zai biya bukatunsa da na iyalansa a shekara ba. Saboda haka duk wanda ke da wata gona ko kaddara ko dabbobi amma ba za su biya bukatun iyalansa tsawon shekara ba, to ya halalta a ba shi Zakka.

Imamiyya da Shafi'iyya da Hambaliyya sun ce wanda yake da ikon nema ba ya halalta ya karbi zakka. Hanafawa da Malikawa kuma suka ce ya halalta kuma ana iya ba shi.

Kan kwana a Muzdalifa a yayin aikin hajji kuwa, Hanafiyya da Shafi'iyya da Hanbaliyya sun ce wajibi ne a kwana a can, wanda ya bar shi sai ya yi yanka (haka Al-Mugni ya kawo). Imamiyya da Malikiyya kuwa suka ce bai wajaba ba, amma shi ya fi.

Wajen jifa a Jamratul Akba kuwa, Malikiyya da Hanafiyya da Hambaliyya da Imamiyya suka ce bai halalta a yi jifa gabannin alfijir ba, idan kuwa aka yi hakan ba da wani uzuri ba, sai an sake. Sai dai sun halalta gabatarwar domin uzurai kamar gajiyawa ko rashin lafiya ko tsoro. Shafi'awa kuwa suka ce babu laifi a yi jifa gabannin alfijir domin lokacin da aka ambata na mustahabbanci ne ba wajibci ba (Al-Tazkira da Bidaya na Ibn Rushdi).­­­

Kan daurin aure Imamiyya da Hambalawa da Shafi-'awa cewa suka yi ba ya halalta a daura aure da rubutu, watau dole ne a yi da baki. Hanafawa suka ce yana inganta idan mai neman aure da wacce ake nema ba sa guri guda.

Shafi'awa da Malikawa suka ce: waliyi na iya aurar da baliga shiryayya idan budurwa ce ko ba da yardarta ba. Idan kuwa bazawara ce, to sai da yardar ta, ba zai gudanar da daura mata aure shi kadai ba, ita ma haka. Ko da yake wajibi ne shi zai yi siga, ita ba za ta iya siga ba.

Hannafawa kuwa suka ce baliga mai hankali tana iya zabin miji da siga da kanta, budurwa take ko bazawara, ba wanda yake da walicci a kanta ko hakkin sabawa zabinta da sharadin ta zabi mutumin da ya yi daidai da ita, kuma kada ta yi aure da mafi karanci daga sadakin tamkarta.

Mafi yawan malaman Imamiyya sun ce baliga shiryayya tana da mallakar dukkan lamurran da suka shafi kulla wata yarjejeniya har da na aure, budurwa take ko bazawara, hakan kuwa saboda balaga da kuma shiryuwarta ne. Tana iya daura aure wa kanta ko waninta, ko ta yi da kanta ko da wakili, ko ta bayar ko karba. Ita kamar namiji take ba tare da wani bambanci ba.

Batun sakin aure kuwa, Abu Zuhra ya fada cikin littafinsa Ahwalul Shaksiyya shafi na 283 cewa: "A mazhabar Hanafiyya saki yana aukuwa ne daga kowani mutum idan ba yaro ko mahaukaci ko mai raunin hankali ba, saboda haka saki yana aukuwa daga mai wasa ko mai maye daga abin da yake haram, ko wanda aka tilasta". A shafi na 286 ya ce: "Tabbatacce yake a mazhabar Hanafiyya cewa sakin wanda ya yi kuskure ko mantuwa yana aukuwa"([248]) .

A shafi na 284 kuma ya ce: "Malik da Shafi'i sun dace da Abu Hanifa da mutanensa kan batun sakin mai wasa, Ahmad ya saba da shi, yana ganin rashin aukuwar sakin". Imamiyya sun ruwaito daga Ahlulbaiti (a.s) cewa: "Babu saki sai ga wanda ya nufi sakin".

Dangane da iddar macen da ta yi zina kuwa: Hanafawa da Shafi'awa da mafiya yawa daga Imamiyya sun ce: Idda ba ta wajaba domin zina, domin ruwan (maniyyin) mazinaci ba shi da wata alhurma (girmama-wa). Saboda haka ya halalta a daura aure wa macen da ta yi zina, da kuma ingancin takar ta ko da tana da ciki. Amma Hanafawa sun haramta takar mai ciki sai ta haihu duk da yake ana iya daura mata aure.

Malikawa kuwa sun ce: Wanda ya yi zina da mace tamkar takan ta ne cikin rashin sani, dole ne ta yi istibra'i gwargwadon idda sai fa idan ana nufin tsayar da haddi kanta ne, a nan kam sai ta yi istibra'i da haila guda. Hanbalawa kuwa suka ce: Idda wajiba ce kan mazinaciya kamar yadda take kan sakakka (AlMugni, juzu'i na 6 da kuma Majma'ul Anhar)

Kan batun wasiyya ga ciki (wato dan da ke cikin ciki) kuwa, malaman fikihu sun saba kan cewa shin dole ne a samu cikin yayin wasiyyar ko kuma a'a.

Imamiyya da Hanafiyya da Hambaliyya da Shafi'iyya bisa mafi ingancin zantuttukansu sun ce ana shardanta hakan, kuma cikin ba ya gado sai idan an san cewa samamme ne yayin wasiyyar. Ana tabbatar da hakan ne, idan matar ta haihu kafin wata shida bayan an yi wasiyyar idan tana da miji mai iya saduwa da ita. Idan kuwa ta haihu bayan wata shida ko fiye, to ba a bai wa ciki kome daga cikin wasiyyar saboda yiyuwar samuwar sabon ciki. Tushe shi ne rashin samuwar ciki yayin da aka yi wasiyyar. Wannan kauli kuwa ya ginu ne kan rashin halalcin wasiyya wa wanda ba samamme ba.

Malikawa kuwa sun ce: Wasiyya tana inganta wa cikin da yake samamme ne da wanda zai samu nan gaba, domin suna ganin halalcin wasiyya wa wanda ba samamme ba. (Dubi Tazkiratul Hilli da Fikihu ala Mazahib Al-Arba' da litattafan fikihu na Hanbaliyya da dama a babin wasiyya).

Wadannan misalai ne 'yan kadan daga fikihu idan an kwatanta mazhabobin Musulunci da junansu. Muna iya ganin yadda wasu mazhabobi suka dace ko suka saba da juna a mas'alolin hukumce-hukumce. Za a ga Malikiyya da Shafi'iyya sun dace da Imamiyya, su saba da Hanafiyya da Hambaliyya, ko Hanafiyya ko Hambaliyya su dace da Imamiyya, su saba da sauran mazhabobi Ahlussunna, da dai sauran irin wannan. Saboda haka sassabawa ba ta dogara da kasancewa cikin Sunna ko Shi'a, sassabawar ta ilimi da tunani, ba sabawar Sunna da Shi'a ba ce, ko kusa, sai dai sabawa ce ta tsarin ilmin ciro hukumce-hukumce na mazhabobin nan biyar. Saboda haka ya zama wajibi a kan mu mu tantance dalilai na shari'a ta hanyar tattaunawa ta ilmi domin isa ga dacewa, sabili da hukumcin Allah dai daya ne akan kowace mas'ala.

Masu kokarin nuna cewa sabanin da ke akwai tsakanin Sunna da Shi'a tamkar ya mai da su kishiyoyi masu jayayya tsakanin juna, ba abin da suke yi sai karkata gaskiya da nisantar tsarin kubutaccen tattaunawa ta ilmi. Babu abin da suke yi sai aiki wa abokan gaban musulmi ta hanyar wargaza hadin kan musulmi.

Musulmi Al'umma Ce Guda

"Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku, a lokacin da kuka kasance makiya, sai Ya sanya soyayya a tsakanin zukatanku, saboda haka kuka wayi gari, da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance a kan gabar rami na wuta, sai Ya tsamar da ku daga gare ta. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa, tsammaninku, za ku shiryu # Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umurni da alheri, kuma su na hani daga abin da ake ki. Kuma wadannan su ne masu cin nasara # Kuma kada ku kasance kamar wadanda suka rarrabu, kuma suka saba wa juna, bayan hujjoji bayyanannu sun je musu, kuma wadannan suna da azaba mai girma". (Surar Aali Imrana, 3: 103-105)

"Saboda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini, kana mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutane a kanta. Babu musanyawa ga halittar Allah, wannan shi ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba # Kuma masu mai da al'amari gare Shi kuma ku bi Shi da takawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai # Watau wadanda suka rarrabe addininsu, kuma suka kasance kungiya-kungiya, kowace kungiya tana mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai. (Surar Rum, 30: 30-32)

"Kuma abin da kuka saba wa juna a cikinsa, ko mene ne, to hukumcinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan Shi ne Allah Ubangijina, a gare Shi na dogara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarina. (Surar Shura, 42: 10)

"Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga ManzonSa da ma'abota al'amari daga cikinku. Idan kun yi jayayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kuna imani da Allah da Ranar Lahira. Wannan ne mafi alheri, kuma mafi kyau ga fassara". (Surar Nisa'i, 4: 59) "Kuma lalle ne wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Ni, Ubangijinku ce, sai ku bi Ni da takawa". (Surar Mu'uminun, 23: 52)

"Kuma ku yi da'a ga Allah da MazonSa, kuma kada ku yi jayayya har ku raunana kuma karfinku ya kau, kuma ku yi hakuri, lalle ne Allah Yana tare da masu hakuri". (Surar Anfal, 8: 46)

Tun al'ummar musulmi tana jaririya a hannun Manzon Shiriya, Muhammadu (s.a.w.a), abokan gaban musulmi daga masu bautar gumaka da yahudawa da nasara da munafukai da masu neman fadanci domin arzurta kansu, suke kokarin kekketa al'ummar da hura wutar sabani da rarraba. Hakika da'awar Musulunci a karkashin jagorancin Manzon Allah (s.a.w.a.) ta fuskanci wannan kaidin ta kuma yi nasara kan yahudawa da mushrikai da munafukai, albarkacin jagoranci Annabi (s.a.w.a) da kuma lizimtar sahabbansa, zababbu.

Tarihin yadda Musulunci ya sha kokawa da wadan-nan magabta a zamanin Annabi (s.a.w.a) yana cike da abubuwa masu bayyana mana yadda masu jayayya da Musulunci, magabtan al'umma suka yi aiki da makamin rarrabawa da shuka sabani. Duk wanda ya bibiyi Alkur'ani Mai Girma da Sunnar Annabi (s.a.w.a) da dalilan saukar ayoyin Alkur'anin, sannan kuma ya dubi tarihin farkon sakon Musulunci zai lura da cewa sakon ya yaki wannan ciwon mai neman rusa addini, yakin da ba kakkautawa. Ya kuma gargadi musulmi kan kada su fada cikin sabani da rarraba kamar yadda al'ummar da suka shude suka fada. Alkur'ani ya hori musulmi da hadin kai da riko da juna, ya kuma yi gargadi kan rarraba da sassabawa da jayayya, yana mai suranta irin makomar masu yin hakan da cewa: "...Kuma kada ku yi jayayya har ku raunana, karfinku kuma ya tafi...".

Hakika Alkur'ani ya yi gargadi kan jayayya da sabani wanda shi yake kai mutane da makoma mai muni da rauni da ragwanci da kasawa da gushewar karfi da daula. Haka nan kuma ya gargade mu kan zamowa kungiyoyi masu gaba da neman halaka juna, sashi na dukan sashi, sashi na la'antar wani sashin tamkar yadda mushirikai da batattun al'ummai masu keta kalmar Allah da wasa da shari'o'inSa suka kasance. Alkur'ani mai girma yana fuskantar da wannan al'umma da ta hada kai bisa kalmar tauhidi:

"...Saboda haka ka tsayar da fuskarka ga addini... wannan shi ne addini madaidaici".

Da kuma kira zuwa ga riko da igiyar Allah: "Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba...".

Da kuma cewa wannan al'umma guda ce: "Kuma lalle ne wannan al'ummar ku ce, al'umma guda daya, kuma Ni Ubangijinku ne, sai ku biNi da takawa". "Kuma lalle ne wannan al'ummarku ce, al'umma guda daya, kuma Ni Ubangijinku ne, sai ku bauta Mini".

Kamar haka ne Alkur'ani ya sanya matakan hada kan al'umma kamar haka:

1. Wanda ake wa bauta Shi kadai ne, kuma abin nema shi ne kadaita Shi da bauta masa.

2. Manufar addini ita ce tsayin daka da kuma muwafaka da halittar da Allah Ya yi mutane a bisa kanta.

3. Cewa wajibi ne kan al'umma ta tara karfinta wurin kira zuwa ga Musulunci da tabbatar da al'umma mai kira zuwa ga alheri da umurni da kyakkyawa da hana mummunan aiki, da daukar sakon Allah (S.W.T.) zuwa ga 'yan'Adam baki daya:

"Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umurni da alheri da kuma hani daga abin da ake ki".

An umurci musulmi da wannan aikin a madadin rarraba da sabani da jayayya domin kada su halakar da karfinsu kan kokawan cikin gida har ma su raunana su zamo abin hadiyewa ga abokan gaba. Alkur'ani mai girma yana kiran hankulanmu domin mu gane dalilan sabani da kuma tabbatar da tushen hanyoyin warware shi:

(a). Sabani kan shari'a da tunani irin na Musulunci wajibi ne a mai da shi ga Alkur'ani da Sunna.

"Idan kun yi jayayya cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa...".

"Kuma abin da kuka saba wa juna a cikinsa, ko mene ne, to hukumcinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah".

Alkur'ani yana hana mu mayar da jayayya ta ilimi da shar'antawa zuwa wata matsala ta rarraba da sabani da gaba da keta al'ummar musulmi, ya ce: "Kuma kada ku yi jayayya har ku raunan, karfinku ya kau....".

(b). Mas'alolin da suke da alaka da siyasa ko zamantakewa wadanda shugaban al'umma, na shari'a, shi yake tsara su da gudanar da su, to wajibi ne a yi masa biyayya domin kada ra'ayoyi su yawaita a sassaba. Domin dole ne al'ummar musulmi ta zama tana da matsaya guda kan sha'anin siyasa da zamantakewar al'umma. "...Ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga Manzon Allah da ma'abuta al'amari daga cikinku".

Hakan kuwa matukar su ma'abuta al'amari sun lizimci hukumce-hukumcen shari'a, kuma suna tabbatar da maslahar al'umma. Musulmi a yau - alhamdu lillahi - suna tare da Littafin Allah, wanda barna ba ta shigo masa ko a farko ko a karshe, duk wani mai jirkitarwa bai iso shi, yana nan kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kawo shi: "Hakika Mu ne Muka saukar da ambato (Alkur'ani), kuma hakika Mu masu kiyayewa ne a gare shi". (Surar Hijiri, 15: 9)

Na biyu kuma, Musulmi sun hadu kan kubutar Alkur'ani daga dukkan wani ragi ko kari, kana kuma sun yi imani da shi da kuma Wanda Ya saukar da shi, Allah Madaukakin Sarki, Abin nufi da bukata, kamar yadda ya siffanta kanSa cikin wannan Littafi Nasa.

Na uku, musulmi sun hadu kan gaskata Annabi (s.a.w.a), suna da Alkibla guda, sun yarda da farillolin Musulunci kamar su salla, zakka, azumi, hajji, jihadi, umurni da mai kyau da kuma hani da mummuna da dai sauransu.

Musulmi sun hadu kan haramcin manyan laifuffuka, kamar su zina, shan giya, luwadi, sata, kisan kai, karya, cin rashawa da dai makamantansu.

Babu wani sabani tsakanin musulmi cikin ginshikai da tushen imani wadanda suke sanya al'umma ta zama musulma, sun yi ittifaki akan dukkan wadannan gishikai. Saboda haka, wajibi ne a warware mas'alolin ijtihadi da ra'ayoyin ilmi ta hanyar mai da su ga Littafin Allah da tabbatacciyar Sunnar Annabi (s.a.w.a) domin kuwa Annabi (s.a.w.a) ya bar al'ummarsa bisa hanya ma'abu-ciyar haske. Annabi (s.a.w.a) ya ce: "Na bar ku kan hanya mai haske, darenta tamkar yininta. Babu mai karkace mata a bayana sai halakakke".

Al'ummar musulmi a yau tana cikin wani matsayi na tarihinta mai bukatar lura da yanayi na ci gaba mai hadari domin tun da dadewa makiya Musulunci suka yi ta kai hare-hare gare su, kama tun daga yakukuwan Salibiyya (wadanda kiristocin Turai suka yi da musulmi), kawo ya zuwa yau din da muke ciki.

Su wadannan makiya, kama tun daga su wadannan kiristoci na salibiyya da kuma yahudawan sahyoniya da 'yan korensu, sun fuskanci akidoji da maslahohin musulmi da ruguzawa da kuma makirci, kuma ba su gushe ba tsawon karni na goma sha tara da na ashirin suna babbata wannan al'umma, suna yada rarraba da sabani na siyasa da tunani da bangaranci da jinsi da nahiyanci, ga kuma yakinsu na tunani da kokarin halaka addinin Musulunci. Baya ga haka kuma, ga yada akidojin son duniya kawai da karyata addinai, kamar akidojin jari hujja na Turawan Yamma da gurguzu da dai sauransu. Ga kuma kirkirar jam'iyyu da hukumomi da mahukunta 'yan korensu wadanda suka riki wadannan akidu domin su yaki Musulunci da masu kira da kokarin daukaka shi da shiryar da 'yan'Adam zuwa ga tafarki madaidaici da kuma kubutar da su daga zalunci da bauta wa azzaluman duniya. A waje guda kuma, malaman kwarai suna kiran al'ummar musulmi zuwa ga hadin kai da dawo da martabar musulmi da tabbatar da hukumce-hukumce da tsarin addini, a wani gefen kuwa 'yan koren kafirci, masu sanye da tufafin malamai suna shuka sabani da rarraba da gurbata fuskar Musulunci domin su tabba-tar da hukumcin 'yan koren Turai da sauran makiya Musulunci, masu tsotse arzikin kasashen musulmi da shinfida ikon sahayoniyawa da 'yan jari hujja da 'yan gurguzu.

Ya wajaba kan 'yan'uwa musulmi da su kiyaye tare da sanin hakikanin masu yada dafin rarraba da sabani cikin musulmi ta hanyar dasisa da karya da kage-kage ko ta hanyar riko da raunana da kagaggun ruwayoyi da suke cikin littattafan hadisai. Irin wadannan hadisai za a samu cewa malamai da masu bincike sun riga da sun fitar da su daga da'irar ilmi, suna ganin sauya su aka yi. Duk musulmi sun san da hakan kamar yadda Manzon Tsira (s.a.w.a) ya gargadi musulmi a hajjinsa na bankwana da cewa:

"Hakika makaryata sun mini yawa kuma za su yawaita. To duk wanda ya yi min karya da gangan ya tanadi mazauninsa a wuta. Idan hadisi ya zo muku, ku gwada shi da Littafin Allah da Sunnata, abin da ya dace da Littafin Allah, to ku rike shi, abin da kuwa ya saba da Littafin Allah da Sunnata, to kada ku yi riko da shi([249]) ".

To idan dukkanmu muna sane da wannan, saboda maslahar waye masu neman rusa addini suke rubuta littattafai da mujallu masu yada rarraba da sabani tsakanin musulmi da kafirta juna da shuka gaba cikin zukata? - domin maslahar wa suke wannan mugun aiki, musamman ma a wannan lokacin mai hadari? Alhali Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:

"Ba za ku shiga aljanna ba sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba sai kun so juna. Shin in shiryar da ku ga wani abu idan kun yi za ku so juna? Ku yada sallama tsakaninku([250]) ".

Irin wadannan kulle-kulle babu shakka aikin manyan azzaluman duniya ne, masu rawar jiki duk san da aka ambaci hadin kan musulmi da gangamin al'ummar Annabi (s.a.w.a), saboda tsantsar karfin ta na mutane da albarkatu da akida mai karfin gaske.

Abin da ya dace da malamai da masu tunani da marubuta da masu wa'azi da duk masu daukan nauyin kula da makomar addinin Musulunci masu kyakyawar niyya shi ne su karkata akalar da'awarsu zuwa kalubalantar barnar masu mugun nufi, su kira al'umma zuwa ga hadin kai da warware matsalolinsu na shari'a da tunani bisa dalilai na ilmi.

An nakalto daga Ibn Shar Ashub cikin littafinsa Munakib Ali Abi Talib cewa: "Wata mace ta yi wasicci da sulusin dukiyarta don a yi mata sadaka, aikin hajji, a kuma 'yanta bawa, to amma dukiyar ba ta isa dukkan wadannan ayyukan ba. Sai aka tambayi Abu Hanifa da Sufyan Al-Sauri kan hakan, sai kowanensu ya ce: A nemi mutumin da ya yi aikin hajji amma bai cika ba sai a ba shi kudi ya karasa da wanda yake kokarin 'yanta wuya, amma bai gama biya ba sai a cika masa, sannan a yi sadaka da sauran. Sai Mu'awiyya bn Ammar (yana daga cikin sahabban Imam Sadik) ya tambayi Imam Sadik (a.s.) kan wannan matsala, sai ya ce da shi: "Ka soma da hajjin domin hajji farilla ne, sauran kuma a aikata nafilolin". Sai Abu Hanifa ya yi wannan ya yi wannan fatawar ya sauya ra'ayinsa([251]) ".

Abu Kasim Al-Baggar ya kawo cikin Musnad na Abu Hanifa, cewa Hasan bn Ziyad ya ce: Na ji Abu Hanifa yana ba da amsar wannan tambayar: Wane ne mafi sani cikin wadanda ka gani?

Sai ya ce: Ja'afar bn Muhammad. Yayin da al-Mansur ya kawo shi sai ya kira ni, ya ce: Ya Abu Hanifa, mutane sun fitinu da Ja'afar bn Muhammad, saboda haka ka shirya masa tambayoyi masu tsanani. Sai na shirya masa tambayoyi guda arba'in. Daga nan sai ya kira ni alhali kuwa a lokacin yana Hira ta kasar Iraki, sai na amsa masa wannan kira tasa na isa wajensa a lokacin kuwa Ja'afar bn Muhammad yana zaune a damansa. Yayin da na kalli Ja'afar, sai kwarjininsa ya shige ni, tamkar wannan kwarjinin bai shiga Mansur ba. Sai na yi masa sallama, ya amsa mini, sai na zauna. Sai Mansur ya ce: Ya Aba Abdillah, wannan Abu Hanifa ne, sai ya ce: "E, na san shi", sannan sai ya juya gare ni ya ce: "Ya Aba Hanifa, jefa tambayoyinka ga Abu Abdullah". Sai na rika jefa masa tambaya yana amsa mini, yana cewa: "Ku kuna cewa kaza, mutanen Madina suna cewa kaza, mu kuma muna cewa kaza. Ta yiyu mu dace da ku, ta yiwu kuma mu dace da su, wani lokaci kuma mu saba duka. Haka aka yi sai da na gama tambayoyin nan arba'in. Babu abin da ya gaza daga ciki. Sannan Abu Hanifa ya ce; "Lalle mafi sani cikin mutane shi ne wanda ya fi su sanin sassabawarsu([252]) ".

Wadannan abubuwa biyu da suka faru a tarihi suna nuna yadda ake muhawara ta ilmi bisa tafarki mai tsari, yadda ake bijiro da mas'aloli da binciken hakika da gudanar da muhawara da fito da amsa.

Irin yadda Abu Hanifa ya yi muhawara da Imam Sadik (a.s.) da tafarkin da suka bi wanda Musulunci ya tabbatar shi ya cancanta malamai da masu bincike su bi domin hakan Musulunci ya sanya ya zama ginshikin isa zuwa ga hakikanin gaskiya.

Muna iya ganin misalin bin wannan hanya ta ilmi da tunani kubutacce a guri Shaikh al-Azhar, Shaikh Mahmud Shaltut yayin da ya fitar da fatawa cewa ya halalta wa musulmi masu bin mazhabobin Hanafiyya, Malikiyya, Shafi'iyya da Hambaliya, su bi mazhabar Shi'a Imamiyya kamar yadda ya halalta a bi sauran mazhabobin Musulunci, kuma aikinsu ingantacce ne karbabbe. Baya ga haka kuma Dokta Muhammad Muha-mmad Fahham, daya daga cikin Shehunan Azhar din shi ma yayi amanna da wannan fatawar. Don dada tabbatarwa, bari mu kawo dukkan wadannan fatawoyi don amfaninmu gaba daya:

Fatawar mai girma Shaikhul Azhar kan halaccin aiki da Mazhbar Shi'a Ithna Ashariyya

An tambaye shi cewa: "Wasu mutane suna ganin wajibi ne kan musulmi ya yi taklidi (koyi) da mazhabobin nan guda hudu sanannu, kuma babu mazhabar Shi'a Imamiyya ko Shi'a Zaidiyya a cikinsu, domin aikinsa na ibada da mu'amala ya zama ingantacce, karbabbe. Shin Malam yana muwafaka da wannan ra'ayi, misali yana hana aiki da mazhabar Shi'a Imamiyya, ga misali?"

Sai Mai girma ya amsa da cewa: 1. Lalle addinin Musulunci ba ya wajabtawa wani daga mabiyansa da ya bi wata mazhaba kebabbiya. Kai kowani musulmi yana da hakkin, tun daga farko, na ya bi kowace mazhaba wacce aka nakalto ta nakaltowa sahihiya wacce aka rubuta hukumce-hukumcenta cikin littattafanta kebantattu. Kuma duk wanda yake bin wata mazhaba daga wadannan mazhabobi yana da damar ya koma wata mazhabar, kowace ce kuwa. Kuma ba shi da laifi kan kome daga wannan.

2. Lalle mazhabar Ja'afariyya wacce aka fi sani da Mazhabar Shi'a Imamiyya Ithna Ashariyya, mazhaba ce wacce ta halalta a yi ibada da ita bisa shari'a kamar sauran mazhabobin Ahlussunna. Ya kamata musulmi su san wannan, kuma su kubuta daga 'yan garanci wajen son wata mazhaba ayyananna. Addinin Allah da shari'ar-Sa (S.W.T.) ba su takaita da wata mazhaba ba. Duk (ma'abuta mazhabobin) ma'abuta ijtihadi ne karbabbu wajen Allah Ta'ala, ya halalta ga wanda bai cancanci bincike da ijtihadi ba ya yi taklidi da su da aiki da abin da suka tabbatar da shi cikin fikihunsu. Kuma babu bambanci tsakanin ibada da mu'amala a wannan".

(Mahmud Shaltut)

"Allah Ya jikan Shaikh Shaltut wanda ya waiwaici wannan ma'ana mai girma ya dawwamar da ita cikin fatawarsa mabayyaniya mai gwarzantaka, yayin da ya yi furuci da halalcin aiki da mazhabar Shi'a Imamiyya yana mai daukar ta a matsayin mazhabar fikihu a Musulunci, mai dogara kan Littafin Allah da Sunna da dalili. Allah na ke roko Ya ba da dacewa wa masu aiki bisa wannan tafarki mai girma na gane juna cikin 'yan'uwa masu bin akidar gaskiya ta Musulunci". "Kuma ka ce: Ku yi aiki, sa'an nan Allah Zai ga aikinku, da ManzonSa da kuma muminai". Kuma karshen kiranmu Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai".

(Muhammad Muhammad Fahham) In an duba za a ga cewa hanyar hada kan al'umma bude take ga duk mai ikhlasi daga 'yan'uwa musulmi, wajibi ne su hada sahu guda, su jefar da sassabawa da 'yan garanci, su tuge dalilan rarraba, su gurfanar da ra'ayoyin ilmi gaban bincike da tattaunawa domin a gano gaskiya.

Mu muna kiran al'ummar musulmi ko ina suke da su fahimci irin halin kunci da musulmi suke ciki na siyasa da zamantakewar jama'a, su kuma yi aiki kan hada kan musulmi da watsar da rarrabuwa, kuma su gano wanda yake rura wutar sabani da 'yan garanci, domin su nesance shi. Domin ya wajaba mu sani cewa muna fama da kulle-kullen Yahudawa Sahyoniya da 'yan mulkin mallaka na Gabashi da Yammaci da 'yan barandansu.

Daga karshe, muna rokon Allah Mai Daukaka, Mai iko da Ya hada kan al'ummar musulmi, Ya nisantar da masu dasisa da masu rura wutar fitina tsakanin al'ummar musulmi da tozarta masu aikin tabbatar da shari'ar Allah da masu kira zuwa gare Shi. Domin akwai taimakawa abokan gaban Allah da hidima ga azzaluman duniya cikin raunana hadin kan musulmi da yada rarraba tsakanin rundunonin masu jihadi da kira zuwa ga Allah.

"Kuma ka ce: "Ku yi aiki, sa'an nan Allah Zai ga aikinku, da ManzonSa da kuma muminai". (Surar Tauba, 9: 105). v Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai.

_____________________

[1] Tirmizi juzu'i na 2 cikin "Manakib Ahlulbaiti" shafi na 308 daga Umar ibn Abi Salama, wanda ya ce: an saukar da ayar "…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" a gidan Ummu Salma. Daga nan sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya kira Fadima, Hasan, Husaini da Ali ya rufe su da mayafi, ya ce: "Ya Allah! Wadannan su ne Ahlulbaiti, don haka Ka tafiyar da kazamta daga gare su Ka tsarkake su tsarkakewa". Sai Ummu Salma ta ce: "Ya Manzon Allah shin ni ma ina daga cikinsu ne?, sai ya ce mata: "Ke dai kina a matsayinki, ke kina a kan alheri".

[2] An ruwaito wannan hadisi cikin littafin Ghayat al-Maram daga Abdullah ibn Ahmad ibn Hambal ta hanyoyi uku daga Ummu Salama, haka nan ma cikin Tafsirin Tha'alabi…haka nan ma Ibn Mardawihi da Khadib daga Abi Sa'id Khudri da wannan ma'ana sai dai kawai 'yan canje-canje na lafazi. Haka nan kuma an ruwaito shi cikin Ghayat al-Maram daga Abdullahi bn Ahmad bn Hambal daga babansa da isinadinsa zuwa ga Ummu Salama, dubi Al-Mizan fi Tafsiril Kur'an na Allama Tabataba'i kan Ayar Tsarkakewa. Wanda kuma ya ke son karin bayani kan wasu masdarori na musamman kan tafsirin wannan aya da kuma gabatarwa kan Ahlulbaiti guda biyar (a.s.) to sai ya karin bayani da ke karshen wannan littafi.

[3] Ibn Jarir da Ibn Abi Hatam da Dabarani sun ruwaito wannan hadisi daga Abi Sa'id Khudri, kamar yadda kuma aka ruwaito shi cikin Ghayat al-Maram da Tha'alabi cikin tafsirinsa, a cikinsa Tirmizi ya ruwaito shi kuma ya ingantar da shi, da kuma Ibn Jarir da Ibn Munzir da Hakim, kuma duk sun ingantar da shi. Haka nan ma Ibn Mardawihi da Baihaki cikin Sunan dinsa ta hanyar Ummu Salma. Dubi Al-Mizan fi Tafsiril Kur'an na Allama Tabataba'i.

[4] Buhari da Muslim duk sun ruwaito ta hanyar A'isha/ Ghayat al-Maram, haka nan kuma Zamakhshari ya ambato shi cikin tafsirin al-Kashshaf ya yin da yake tafsirin Ayar Mubahala.

[5] Ibn Mardawihi daga ibn Abi Shaibah da Ahmad da kuma Tirmizi sun ruwaito kuma sun inganta shi, sannan kuma Ibn Jarir da Ibn Munzir da Dabarani da Hakim, kuma sun inganta shi, da kuma ibn Mardawihi daga Anas. Mai son karin bayani sai ya duba Al- Mizan na Tabataba'i yayin da yake magana a kan Ayar Tsarkakewa.

[6] Jami al Usul, juzu'i na 9, shafi na 156 ya nakalto daga Sahih Tirmizi, haka nan ma Hakim ya ruwaito shi cikin Mustadrak juzu'i na 3 shafi na 158, kuma ya inganta shi.

[7]Fadhl Aalulbaiti na Takiyuddin Ahmad bn Aliyu al Makrizi (wanda ya rasu a shekara ta 845 bayan hijira), shafi na 21.

[8] Fakhrurrazi cikin Tafsirul Kabir yayin tafsirin Surar Shura aya ta 23.

[9] Ghayat Maram yayin tafsirin ayar.

[10] Sanannen al'amari ga mai karatu cewa wannan fassara ta yi nisa ga hakikanin ma'anar kalmar, don kuwa ma'anar kalmar aal a cikin harshen Larabci a fili yake, babu yadda za a fassara kalmar aal da al'umma.

[11] Rafdhu a wajen malaman Ahlussunna shi ne yarda da cewa Imam Ali bn Abi Talib (a.s.) shi ne halifan Manzon Allah (s.a.w.a.) na farko bayan rasuwarsa. Kuma Rafidhi shi ne wanda ya yarda da hakan.

[12] Fakhrurrazi cikin Tafsirul Kabir, yayin tafsirin Surar Shura aya ta 23.

[13] Ihya'ul Mait bi fadha'il Ahlilbaiti na Suyudi shafi na 8, kuma Suyudin ya ruwaito shi cikin Durrul Mansur , juzu'i na 6 shafi na 7 ta hanyar Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas, sannan kuma Dabarani ma ya fitar da shi cikin Mu'ujamul Kabir, juzu'i na 1 shafi na 125. Haka ma Tabari ya ruwaito shi cikin Zakha'ir shafi na 25, yana cewa: "Ahmad ya fitar da shi cikin Munakib. Kamar yadda kuma Ibn Sabbag al-Maliki ya ruwaito shi daga Nabawiy daga Ibn Abbas, shafi na 29. Hakan nan kuma Kurdabi ya fitar da shi cikinsa Jami' al-Ahkam al-Kur'an da ruwayar Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas, juzu'i na 16, shafi na 21-22.

[14] Tabataba'i daga Sheik Tusi.

[15] Wannan tawaga ta kumshi manya-manyan shuwagabannin kiristocin Larabawa kamar haka: Abdul Masih, wanda ya kasance shugabansu, da kuma al-Ayhma, wanda ya kasance mai kula da al'amurran gudanarwa da ayyukan ibada, da kuma Abu Hatam ibn Alkama, wanda ya kasance bishof ne kana kuma kula da makarantunsu. Dubi Fusul al-Muhimma na Ibn Sabbag al-Maliki a sashin gabatarwar marubuci.

[16] Yin 'yar kure tsakanin vangare biyu kan Allah Ya saukar da azaba a kan vangaren da ba ya kan gaskiya. A takaice dai yin la'ananneniya tsakanin vangarori biyu don gano wani vangare ne ya ke kan gaskiya.

[17] Ashabul Kisa' (ma'abuta mayafi), suna ne da ake kiran mutanen da suka kasance tare da Manzon Allah (s.a.w.a.) cikin mayafinsa inda daga baya aka saukar da Ayar Tsarkakewa a gare su. Su ne kuwa: Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.), kamar yadda aka ambata a baya.

[18] Tafsirul Kashshaf na Zamakhshari yayin tafsirin Surar Ali Imrana aya ta 61, haka nan kuma ya zo cikin Tafsirin Tha'alabi daga Mujahid da Kalbi.

[19] Tafsirul Kabir na Fakhrurrazi a kan Ayar Mubahala.

[20] Jumlar "....ku yi salati a gare shi.." wacce ta zo cikin ayar tana nuni da wajibci ne, don malaman Usul al-Fikh sun bayyana fi'ilin umurni a matsayin yana nuni ga wajibci ne, wasu ma suna ganin cewa a duk lokacin da fi'ilin umurni ya zo cikin Alkur'ani ko hadisi yana nuni ga wajibci ne sai dai idan akwai wani abin da yake nuni da cewa wajibcin ya koma zuwa ga mustahabi.

[21] Tafsirul Kabir na Fakhrurrazi a tafsirin Surar Ahzab aya ta 56.

[22] Almizan fi Tafsiril Kur'an na Allamah Tabataba'i, juzu'i na 16, shafi na 344.

[23] Allamah Hilli wanda ya kasance daga cikin manyan malaman fikihun mazhabar Ahlulbaiti (a.s), kuma yana daga cikin sanannun karni na bakwai bayan hijira, yayin da yake ambaton wajiban salla yana cewa: (Na bakwai) tahiya, wajaba ce a dukkan salla mai raka'o'i biyu sau guda, sannan kuma sau biyu a salloli masu raka'o'i uku da hudu, da mutum zai bar ta da gangan, to salla ta vaci. Akwai abubuwa guda biyar a cikin ko wane daya daga cikinsu da suka kasance wajibai, su ne kuwa: zama gwargwadon tahiya, yin shahadojin nan guda biyu da salati ga Annabi da Alayensa (a.s.). Dubi Shara'ii Islam, juzu'i na 1, babin salla.

[24] Zamakhshari cikin littafin al-Kashshaf, yayin tafsirin Surar Insan, haka nan kuma Fakhrurrazi shi ma ya kawo wannan ruwaya cikin littafinsa na Tafsir al-Kabir Haka ma Tabrisi cikin Majma'ul Bayan.

[25] Birnin Makka ya fuskanci fari mai tsananin gaske kafin aiko Ma'aiki (s.a.w.a.), don haka sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya dauko Imam Ali (a.s.) daga wajen mahaifinsa Abu Talib (a.s.) zuwa gidansa don yi masa tarbiyya da kuma saukaka wa Baffansa (Abu Talib) wanda ya kasance fakiri ne.

[26] Zamakshari cikin al-Kashshaf yayin tafsirin Surar Ma'ida aya ta 55.

[27] Al-Wahidi cikin Asbabun Nuzul / Surar Ma'ida aya ta 55.

[28] Mai son karin bayani sai ya koma ga.....

[29] Hakim al-Haskani cikin littafin Shawahid al-Tanzil juzu'i na 1 shafi na 190 ya ruwaito cewa: "Daga Abdulla bn Abi Aufa, yana cewa: Na ji Manzon Allah (s.a.w.a.) ya karanto wannan aya (sai ya karanto ayar Tabligh) a Ranar Ghadir Khum, sai ya daga hannayensa har ana ganin farin hammatansa, ya ce: "Ku sani duk wanda ya zamanto shugabansa, to Aliyu shugabansa ne". Haka nan ma Al-Wahidi cikin Asbabun Nuzul shafi na 135, da kuma Suyudi cikin Durrul Mansur juzu'i na 2 shafi na 198, daga Abi Sa'id al-Khudri cewa: Wannan aya ta sauka ne dangane da sha'anin Aliyu bn Abi Talib.

[30] Majma' al-Zawa'id, juzu'i na 9, shafi na 163-165.

[31] Hakim al-Haskani ya ruwaito shi cikin juzu'i na 1, shafi na 192-193.

[32] Majma' al-Zawa'id, juzu'i na 9 shafi na 163-165, da kuma Ibn Kathir juzu'i na 5 shafi na 209-213.

[33] Tarikh ibn Kathir, juzu'i na 5 shafi na 213.

[34] Majma' al-Zawa'id.

[35] Musnad Ahmad juzu'i na 4 shafi na 281, Sunan ibn Maja babin falalar Ali, ta Tarikh ibn Kathir, juzu'i na 5, shafi na 209 da 210.

[36] Musnad Ahmad, juzu'i na 4, shafi na 281, Sunan Ibn Majah, babin falalar Ali, da kuma ibn Kathir, juzu'i na 5, shafi na 212.

[37] Basra sunan wata alkarya ce da ke kusa da Damaskus, San'a' kuma tana kusa da garin Bagadaza.

[38] Majma' al-Zawa'id da wasu kalmominsa daga ruwayar Hakim, juzu'i na 3, shafi na 109-110, da kuma Ibn Kathir, juzu'i na 5, shafi na 209.

[39] Musnad Ahmad, juzu'i na 1, shafi na 118 da 119, da kuma juzu'i na 4 shafi na 281, da Sunan Ibn Majah, juzu'i na1, shafi na 372, da Ibn Kathir, juzu'i na 5 shafi na 209.

[40] A cikin ruwayar Hakim al-Haskani, juzu'i na 1 shafi na 190, cewa ya yi: sai ya daga hannunsa har aka ga farin hammatarsa, sannan a cikin shafi na 93 kuma cewa ya yi: har farin hammatarsa ya fito.

[41] Hakim al-Haskani cikin Shawahid al-Tanzil, juzu'i na 1, shafi na 191, da kuma wurin Ibn Kathir, juzu'i na 5, shafi na 209 cewa ya yi: ni kuma ni ne majivincin kowane mumini.

[42] Musnad Ahmad juzu'i na 1 shafi na 118 da 119 da juzu'i na 4 shafi na 281 da 370 da 372 da 373 da juzu'i na 5 shafi na 347 da 370, da al-Mustadrak na Hakim, juzu'i na 3, shafi na 109, Sunan Ibn Majah da Hakim al-Haskani, juzu'i na 1 shafi na 190 da 191, da Tarikh ibn Kathir, juzu'i na 5 shafi na 209 da 210-213, inda ibn Kathir cikin juzu'i na 5 shafi na 209 ya ce: nace wa Zaid, shin ka ji hakan daga Manzon Allah (s.a.w.a.)? sai yace: Babu wani wanda yake gurin face ya gan shi ko kuma ya ji da kunnuwansa, sai Ibn Kathir ya ce: Malaminmu Abu Abdullah al-Zahabi ya ce: wannan hadisi ingantacce ne.

[43] Musnad Ahmad, juzu'i na 1 shafi na 118 da 119, Majma' al-Zawa'id juzu'i na 9 shafi na 104 da 105 da 107, da Shawahid al-Tanzil juzu'i na 1 shafi na 193, da Tarikh Ibn Kathir juzu'i na 5 shafi na 210 da 211.

[44] Shawahid al-Tanzil juzu'i na 1 shafi na 191, da Tarikh Ibn Kathir juzu'i na 5 shafi na 210.

[45] Shawahid al-Tanzil, juzu'i na 1 shafi na 190.

[46] Hakim al-Haskani ya ruwaito shi daga Abu Sa'id al-Khudri, juzu'i na 1 shafi na 157-158, hadisi 211-212, daga Abu Huraira shafi na 158 hadisi na 212, da kuma cikin Tarikh na Ibn Kathir juzu'i na 5 shafi na 214.

[47] Al-Mustadrak, juzu'i na 3, shafi na 129, Kanzul Ummal, juzu'i na 6, shafi na 157, Dabari ma ya ambaci haka cikin tafsirinsa da Fakhrurrazi cikin tafsirinsa na Al-Kabir, da kuma Suyudi cikin Durrul Mansur yayin da yake tafsirin wannan aya.

[48] Ibn jarir Tabari ya ambaci hakan, da kuma Suyudi cikin Durrul Mansur , da Zamakhshari cikin Al-Kashshaf yayin da yake tafsirin ayar, da kuma Wahidi cikin Asbabun Nuzul shafi na 200, da kuma Tarikh Bagdad da kuma Riyadhun Nadhrah.

[49] Suyudi cikin Durrul Mansur, Fakhrurrazi cikin tafsirinsa yayin tafsririn wannan aya, kamar yadda Al-Muntaki Al-Hindi cikin Kanzul Ummal juzu'i na 1 shafi na 251.

[50] Suyudi cikin Durrul Mansur karkashin tafsirin wannan aya, Kanzul Ummal juzu'i na 1 shafi na 237, Askalani cikin Fathul Bari juzu'i na 13 shafi na 27 da kuma Haithami cikin Majma'a juzu'i na 9 shafi na 194.

[51] Ibn Jarir Dabari ya ruwaito shi cikin tafsirin ayar, da kuma Zamakhshari cikin Al-Kashshaf yayin tafsirin ayar, Suyudi cikin Durrul Mansur yayin tafsirin ayar, haka nan ma Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 408, da kuma Wahidi cikin Asbabun Nuzul.

[52] Zamakhshari cikin tafsirin Al-Kashshaf, Suyudi cikin Durrul Mansur yayin tafsirin ayar, Riyadhun Nadhrah juzu'i na 2, shafi na 207 da kuma Ibn Hajar cikin Al-Sawa'ik al-Muhrika shafi na 102.

[53] Ibn Jarir Dabari cikin tafsirinsa, Suyudi cikin Durrul Mansur ta vangarori daban-daban, ya kara da cewa, a duk lokacin da Aliyu (a.s.) ya nufo wajen sahabban Manzon Allah (s.a.w.a.) sukan ce: Ga mafifitan alherin halitta (Khairul Bariya) ya iso. Haka ma an ruwaito wanda hadisi cikin Sawa'ikul Muhrika shafi na 96 da kuma cikin Nurul Absar na Shabalanji, shafi na 70 da kuma na 101.

[54] Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'ir al-Ukba fi Manakib Zawil Kurba, shafi na 30.

[55] Al-Ithafu bi hubbil Ashraf na Abdullah bn Muhammad bn Amir al-Shabrawi al-Shafi'i, shafi na 21.

[56] Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'ir al-Ukba fi Manakib Zawil Kurba, shafi na 30.

[57] Zakha'irul Ukba na Dabari, shafi na 67.

[58] Dabari ya ruwaito wannan hadisi da dan bambancin lafazi cikin Mu'ujamul Kabir, juzu'i na 1 shafi na 24, haka nan cikin Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 220, Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'irul Ukba shafi na 121, da Suyudi cikin Ihya'ul Mayyiti shafi na 29, da wannan lafazi" "Dabarani ya fitar da shi daga Umar, cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Dukkan wani mutum, to danganta-karsa tana komawa ne ga mahaifinsa, in ban da 'ya'yan Fadima, don dangantakarsu tana komawa ne gare ni, ni ne mahaifinsu".

[59] Tirmizi ya ruwaito shi cikin Sahihinsa juzu'i na 2, shafi na 380 da isnadinsa daga Zaid bn Arkam, haka ma Hakim ya ruwaito shi cikin Al-Mustadrak juzu'i na 3 shafi na 109, shi ma daga Zaid bn Arkam, haka nan ma Ahmad bn Hambal ya ruwaito shi cikin Musnad dinsa daga Abu Sa'id al-Khudri, juzu'i na 3 shafi na 17, kamar yadda kuma Dabarani cikin Mu'ujamul Kabir juzu'i na 1 shafi 129 ya ruwaito, haka ma Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'irul Ukba daga Ahmad shafi na 16.

[60] Al-Ithafu bi hubbil Ashraf, shafi na 22.

[61] Kamar na sama.

[62] Kamar na sama, shafi na 22-23.

[63]Al-Balagi cikin Ala'ur Rahman shafi na 44. Allama Faiz Abadi ya nakalto cewa: " Muslim ya ruwaito Hadisus Sakalain cikin sahihinsa, haka ma Ahmad bn Hambal cikin Musnad dinsa, juzu'i na 4 shafi na 366, da Baihaki cikin Sunan dinsa, juzu'i na 2 shafi na 148, juzu'i na 7 shafi na 30, haka ma Darimi ya ruwaito shi Sunan dinsa, juzu'i na 2 shafi na 431, Al-Muttaki cikin Kanzul Ummal, juzu'i na 1 shafi na 45, da juzu'i na 7 shafi na 102, haka ma Dahawi cikin Mishkilul Athar juzu'i na 4 shafi na 368, Tirmizi ma ya ruwaito shi cikin Sahihinsa, juzu'i na 3 shafi na 109, haka Nisa'I cikin Khasa'is shafi na 21. Haka nan ma cikin al-Mustadrak na Hakim, juzu'i na 3 shafi na 148.

[64] Musnad Ahmad bn Hambal, juzu'i na 3 shafi na 17.

[65] Shabrawi al-Shafi'I cikin littafinsa na al-Ittihaf bi hubbil Ashraf, mukaddimar mawallafi, shafi na 26.

[66] Abu Nu'aim cikin littafin Hilliyat al-Awliya juzu'i na 4 shafi na 306, ya nakalto daga Firuz Abadi cikin littafin Fadha'il al-Khamsa min al-Sihah al-Sitta juzu'i na 2 shafi na 64, Ibn Hajar ma ya ambato shi cikin Zawa'id babin Ahlulbaiti wal Azwaj shafi na 277, haka ma Haithami ya nakalto shi.. ..daga Ibn al-Bazzar cikin Majma' al-Zawa'id juzu'i na 9 shafi na 163, kamar yadda kuma Dabarani ya kawo cikin Mu'ujamul Kabir juzu'i na 1 shafi na 125, haka ma Dabari cin Zaka'ir shafi na 20, haka ma Hakim cikin al-Mustadrak tare da karin lafuzza, juzu'i na 2 shafi na 343, haka ma cikin Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 216.

[67] Hakim cikin al-Mustadrak ya ruwaito wannan hadisi a juzu'i na 2 shafi na 343, inda ya ce: wannan hadisi ne ingantacce a bisa sharadin Muslim, haka ma Al-Muttaki ya ruwaito shi cikin Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 216, da kuma Haithami cikin Majma'ansa, juzu'i na 9 shafi na 168, haka ma Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'ir dinsa shafi na 20, haka ma Khadib al-Bagdadi cikin Tarihinsa, juzu'i na 12 shafi na 19.

[68] 4- Fadha'il al-Khasa na Firuz Abadi, juzu'i na 2 shafi na 65.

[69] Kamar na sama.

[70] Kamar na sama.

[71] Al-Ittihaf bi Hubbil Ashraf na Al-Shabrawi shafi na 20, Hakim ma ya fitar da shi cikin al-Mustadrak, juzu'i na 3 shafi na 149, inda ya ce wannan hadisi ne ingantacce sai dai kuma bai (Muslim) ruwaito shi ba, kamar kuma al-Muttaki ya fitar da shi cikin littafinsa Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 217, haka ma Ibn Hajar ya kawo shi cikin littafinsa Sawa'ikul Muhrika shafi na 140.

[72] Fadha'il Khamsa, juzu'i na 2 shafi na 68. An kira wannan hadisi da sunan Hadisin Mayafi ne saboda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tara Ahlulbaitinsa guda hudu (Aliyu, Fatima, Hasan da Husaini) ya rufe su da mayafi.

[73] Ma'ana E kema ba kya zuwa wuta.

[74] Al-Fusulul Muhimma fi Ahawalul A'imma na Ibn Sabbag al-Maliki, shafi na 25-26.

[75] Al-Ithafu bi hubbil Ashraf na Shaikh Shabrawi, shafi na 17-18.

[76] Al-Fusulul Muhimma fi Ahawalul A'imma na Ibn Sabbag al-Maliki, shafi na 29.

[77] Suyudi ya ruwaito shi cikin littafin Ihya'ul Mayyiti daga Dabarani daga Umar, shafi na 20, kamar yadda Haithami kuma ya fitar da shi cikin littafin Majma'ul Zawa'id juzu'i na 9 shafi na 163, kamar yadda kuma Ibn Hajar ya kawo shi cikin littafinsa Sawa'ikul Muhrika shafi na 90.

[78] 4- Suyudi ya ruwaito shi cikin littafin Ihya'ul Mayyiti daga Dabarani daga Jabir bn Abdullah, shafi na 22, kamar yadda Haithami kuma ya fitar da shi cikin littafin Majma'ul Zawa'id juzu'i na 9 shafi na 172.

[79] Muslim ya ruwaito shi cikin littafin Fadha'il al-Sahaba (Falalar Sahabbai) cikin babin falalar Aliyu bn Abi Talib daga Yazid bn Hayyan, juzu'i na 4 shafi na1873, haka ma Ahmad bn Hambal ya ruwaito shi cikin Musnad dinsa ya yi kuma daidai da abin da Muslim ya ruwaito, juzu'i na 4 shafi na 366-367, kamar yadda kuma Muttaki ya ruwaito cikin Kanzul Ummal juzu'i na farko shafi na 158, da kuma cikin juzu'i na bakwai shafi na 102, haka ma Suyudi ya ruwaito shi cikin tafsirinsa Durrul Mansur juzu'i na 6 shafi na 7, ya ce daga gare shi: Muslim, Tirmizi da Nasa'i sun ruwaito shi daga Zaid bn Arkam, haka ma Suyudi ya ruwaito shi cikin littafinsa Ihya'ul Mayyit shafi na 11.

[80] Khadib ya ruwaito shi cikin tarihinsa, juzu'i na 2 shafi na 146 da kari cikin matanin, kamar yadda kuma Al-Muttaki ya kawo hadisin cikin Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 217 karkashin lamba ta 3800, sannan Suyudi ma ya ruwaito shi cikin Ihya'ul Mayyiti bi Fadha'il Ahlulbaiti, shafi na 37.

[81] Tabari cikin Zakha'irul Ukba shafi na 17.

[82] Kamar na sama.

[83] Suyudi ya fitar da shi cikin Ihya'ul Mayyit daga Dailami daga Abi Sa'id, shafi na 43, haka ma Al-Manawi ya ambace shi cikin Faizul Kabir juzu'i na 1 shafi na 515, ya ce: Dailami ya fitar da shi cikin Firdausi.

[84] Suyudi ya ruwaito shi cikin Ihya'ul Mayyiti shafi na 40-41, yana cewa: "Dailmai ya fitar da shi daga Aliyu, kamar yadda kuma Al-Muttaki ya ambato shi cikin Kanzul Ummal juzu'i na 8, shafi na 278, kamar yadda kuma Ibn Hajar ya ambato shi cikin Sawa'ikul Muhrika, shafi na 103.

[85] Suyudi ya ruwaito shi cikin Ihya'ul Mayyiti shafi na 39, daga Dabarani daga Ibn Abbas, haka ma Al-Muttaki ya ambato shi cikin Kanzul Ummal juzu'i na 8, shafi na 212, yana cewa: "Dabarani ya nakalto shi daga Ibn Abbas, sannan kuma Haithami ma ya ambace shi cikin Majma'ul Zawa'id juzu'i na 10 shafi na 346, ya ce: "Dabarani ya ruwaito shi cikin Al-Kabir da Al-Awsad.

[86] Ihya'ul Mayyiti na Suyudi shafi na 38, Majma'ul Zawa'id na Haithami juzu'i na 5 shafi na 195, Usudul Gaba na Ibn Athir juzu'i na 3 shafi na 137, Hilyatul Awliya na Abu Na'im juzu'i na 9 shafi na64 daga Aliyu (a.s.).

[87] (*)- Shaikh Tabrisi yana daga cikin shahararru kana manyan malaman mazhabar Shi'a Imamiyya a qarni na shida hijiriyya.

[88] (**)- Sayyid Murtadha: shi ne Aliyu bn Husain, yana daga cikin manya-manyan malaman Shi'a Imamiyya na qarni na hudu hijiriyya, kuma yana daga cikin daliban Shaikh al-Mufid kuma malamin Shaikh al-Tusi, Mu'assasin Jami'ar birnin Najaf al-Ashraf, ya rasu a shekara ta 437 Hijiriyya.

[89] Majma'ul Bayan fi Tafsiril Kur'an na Shaikh Dabarasi a mukaddimar tafsirin.

[90] Kama na sama.

[91] Ma'al Khatib fi Khututihi al-Aridha na Shaikh Lutufullah Safi, shafi na 42.

[92] Tafsirul Tibyan Shaikh Dusi juzu'i na 1shafi na3.

[93] Ala'ur Rahaman na Shaikh Al-Balagi, juzu'i na 1 shafi na 18.

[94] Kamar na sama, Mukaddima.

[95] Biharul Anwar na Allama Majlisi juzu'i na 47, shafi na 271.

[96] Mu'ujam Mufradat Alfaz al-Kur'an na Ragib Isfahani, wajen kalmar Suhuf.

[97] Majma'ul Bayan fi Tafsiril Kur'an na Allama Dabrisi, a mukaddimar littafin.

[98] Usul Kafi na Shaikh Kulayni juzu'i na 2 shafi na 598.

[99] Kamar na sama, shafi na 603.

[100] Kamar na sama, shafi na 605.

[101] Kamar na sama, shafi na 606.

[102] Usul Kafi na Shaikh Kulayni juzu'i na 2 shafi na 607.

[103] Kamar na sama, shafi na 609.

[104] Kamar na sama, shafi na 613.

[105] Nahjul Balagah, huduba ta 198.

[106] Majma'ul Bayan na Dabrisi, Mukaddima, juzu'i na 1, shafi na 13.

[107] Majma'ul Bahrain na Duraihi, kalmar fassara.

[108] Majma'ul Bayan na Dabrisi, Mukaddima, juzu'i na 1, shafi na 13.

[109] Ahmad Ridha cikin Mukaddimar Majma'ul Bayan, juzu'i na 1, shafi na 13.

[110] Gabatarwar Majma'ul Bayan juzu'i na 1 shafi na 13.

[111] Daga cikin misalin tawili, shi ne tawilin da ake yi wa wannan aya: "KujerarSa ta yalwaci sammai da kasa", anan ana yi wa kujera tawili da ilmi da mulki…da dai sauransu, ba wai kujera wacce ake zama a kanta ba kamar yadda aka sani.

[112] Gabatarwar Majma'ul Bayan na Tabrisi, juzu'i na 1, shafi na 13.

[113] Kamar na sama.

[114] Kamar na sama.

[115] Sahihul Kafi na Bahbudi, juzu'i na 1, shafi na 5.

[116] Kamar na sama, shafi na 11.

[117] Al-Diraya na Zainuddin al-Amuli, shafi na 113.

[118] Sahihul Kafi na Muhammad Bakir Bahbudi, juzu'i na 1 shafi na 8.

[119] Kamar na sama, shafi na 9.

[120] Sahihul Kafi na Muhammad Bakir Bahbudi, juzu'i na 1 shafi na 11.

[121] Kamar na sama.

[122] Kamar na sama.

[123] Mishkatul Anwar na Tabrisi, babin riki da sunna.

[124] Mishkatul Anwar na Tabrisi, babin riki da sunna.

[125] Kamar na sama.

[126] Kamar na sama.

[127] Kamar na sama.

[128] Kamar na sama.

[129] Kamar na sama.

[130] Mishkatul Anwar na Tabrisi, babin riki da sunna.

[131] A'ayanu al-Shi'a na Allama Sayyid Muhsin Amin juzu'i na 3 shafi na 34.

[132] Usulul Kafi na Shaikh Kulayni, juzu'i na 3, shafi na 34.

[133] Mubadi Amma fi Ilmil Hadith na Shaikh Baha'i shafi na 22.

[134] Kitabul Irshad na Shaikh Mufid babin falalar Imam Aliyu bn Husain (a.s.).

[135] Kamar na sama, shafi na 257.

[136] Ahlulbaiti na Abu Ilmi.

[137] Tazkiratul Khawas na Ibn Jawzi.

[138] A'alamul Wara bi A'alamul Huda na Allama Dabrisi/ Nassosin da suke nuni da Imamancinsa/ shafi 252 da kuma Manakib Aali Abi Dalib/ juzu'i na 3.

[139] Kitabul Irshad na Shaikh al-Mufid, Fusulul Muhimma na Ibn Sabbag al-Maliki, Ya'akubi cikin Tarihinsa da Sabalanji cikin Nurul Absar da kuma Ibn Jawzi cikin Tazkiratul Khawas.

[140] Imam Sadik wal Mazahibul Arba' na Asdar Haidar, juzu'i na 2, ya nakalto daga Shazratul Zahab juzu'i na 1, shafi na 149.

[141] Siratul A'imma Ithna Ashr na Hashim Ma'aruf al-Hasani, juzu'i na 2, shafi na 198.

[142] Allama Muhsin Amin ya nakalto shi cikin littafinsa na A'ayanu al-Shi'a, juzu'i na 3, shafi na 34.

[143] Manakib Aali Abi Dalib na Ibn Shahr Ashub, juzu'i na 4, shafi na 248.

[144] Imam Sadik na Muhammad Abu Zuhra, shafi na 3.

[145] Tarikh Ya'akubi, juzu'i na 2, shafi na 381.

[146] Kurbul Asnad, shafi na 193, da kuma Al-Manakib na Shahr Ashub, juzu'i na 3, shafi na 411.

[147] AlJurhu wa al-Ta'adil na Razi, juzu'i na 8, babin Jim, shafi na 139.

[148] Mizanul I'itidal na Zahabi, juzu'i na 3, shafi na 209.

[149] Madalibul Su'ul na Kamaluddin al-Shafi'i, shafi na 18.

[150] Nurul Absar na Mumin Shabalanji, shafi na 218.

[151] Tazkiratul Khawas na Ibn Jawzi, shafi na 198.

[152] Kitabul Irshad na Shaikh al-Mufid.

[153] Tazkiratul Khawas na Ibn Jawzi, shafi na 202. (*) Aliyyu bn Ja'afar Sadiq shi ne baffan baban Imam Jawad (a.s.), kuma yana daga cikin maruwaita masu gaskiya abin dogara a wajen maruwaitan hadisan musulmi.

[154] Madinatul Ma'ajiz, shafi na 450.

[155] Jawharul Kalam , shafi na 147.

[156] Nurul Absar, shafi na 149.

[157] Shazaratul Zahabi, juzu'i na 2, shafi na 129.

[158] Al-Bidaya wan Nihaya, juzu'i na 11, shafi na 15.

[159] Tazkiratul Khawas na Ibn Jawzi, shafi na 202.

[160] Tazkiratul Khawas na Ibn Jawzi, shafi na 203.

[161] AlFusulul Mihimma fi Ahawalil A'imma na Ibn Sabbag al-Maliki, shafi na 290.

[162] Abu Dawud ya ruwaito cikin Sunan dinsa, juzu'i na 4, shafi na 104, hadisi na 4282, Fusulul Muhimma na Ibn Sabbag al-Maliki.

[163] Sunan Abi Dawud na Abu Dawud juzu'i na 4, shafi na 104.

[164] Imam Ali (a.s.) cikin littafin Nahjul Balagah, huduba ta 1.

[165] Hadisi mai tsarki daga Imam Sadik (a.s.).

[166] Imam Ali cikin Nahjul Balagah bangaren kalmomin hikima, hikima ta 470.

[167] Usulul Kafi na Kulayni, juzu'i na 1, babin tauhidi, shafi na 85.

[168] Usulul Kafi na Kulayni, juzu'i na 1, babin tauhidi, shafi na 86.

[169] Kamar na sama, shafi na 88.

[170] Kamar na sama, shafi na 90.

[171] Kamar na sama, shafi na 93.

[172] Kamar na sama, shafi na 92.

[173] Kamar na sama, shafi na 90.

[174]Usulul Kafi na Kulayni, juzu'i na 1, babin tauhidi, shafi na 90.

[175] Kamar na sama, shafi na 98.

[176] Kamar na sama, shafi na 102.

[177] Kamar na sama.

[178] Usulul Kafi na Kulayni, juzu'i na 1, babin tauhidi, shafi na 100.

[179]Kamar na sama, shafi na 104. (*). Da yardar Allah a nan gaba za mu yi bayani dangane akidar wannan batacciyar kungiya, wacce ta ke siffanta Imaman Ahlulbaiti (a.s) da siffar Ubangiji, Imamai sun la'ance su da kuma barranta daga gare su.

[180] Sahihul Kafi na Bahbudi, juzu'i na , babin Jabru da Kadr.

[181] Nahjul Balagah, hikima ta 78.

[182] Kitab al-Tauhid da Uyun Akhbar al-Ridha na Sheikh Saduk da kuma Al-Mizan na Sayyid Tabataba'i, juzu'i na 1, bahasin al-Jabru wat Tafwidh.

[183] Al-Mizan na Sayyid Tabataba'i, juzu'i na 1, bahasin al-Jabru wat Tafwidh.

[184] Kamar na sama.

[185] Al-Mizan na Sayyid Tabataba'i, juzu'i na 1, bahasin al-Jabru wat Tafwidh.

[186] Kamar na sama.

[187] Majma'ul Bayan fi Tafsir al-Kur'an na Tabrisi, yayin tafsirin wannnan aya.

[188] (*) Hakika rawar da wannan aiki na ruguzawa da wadannan batattun tunanunnuka na shafa wa Ahlulbaiti (a.s) kashin kaza suka taka, ba su takaita kawai gare su ba, face ma dai sun yi kokarin shigar da su ga sauran kungiyoyi da al'ummomin musulmi. A saboda haka ne ma malamai da masana na sauran mazhabobin musulmi suka yi iyakacin kokarinsu wajen kubuta daga gare su, amma duk da haka har ya zuwa yanzu muna ganin da.. ..yawa daga cikin irin wadannan dasisi da batattun akidoji cikin littattafan musulmi da abubuwan da suke dogaro da su.

[189] (*)Al-Nawbakhti: shi ne Abu Muhammad al-Hasan bn Musa al-Nawbakhti, yana daga cikin manyan malaman shi'a Imamiyya a karni na uku bayan hijira.

[190] Firakhul Shi'a na al-Nawbakhti, shafi na 59. (**). Kharmadaniyya: Kungiya ce wacce ta fito a karni na biyu bayan.. ..kashe Abi Muslim Khorasani da da'awar Jawidan bn Sahl, ta kasance daga cikin sauran kungiyoyin da suke Iran tun kafin Musulunci. Sun halalta dukkan abubuwan haramun da kuma halalta matayensu a tsakaninsu. Dubi al-Firakul Khurmadiniyya na Dr. Shahin Kamiran Mukaddam, shafi na 3.

[191] (*)Mazdakiyya: Su ne mabiyan Mazdak wanda ya bayyana a lokacin babban sarkin Farisawa Kubbad mahaifin Anushiran. Sunan littafin da ya yi ikirarin cewa an saukar masa da shi, shi ne Distaw. Maganganunsu yana kama da tsohon addinin Farisawan nan na Maniwiyya, wajen imani da tushen addininsu na Haske da Duhu. Mazdakawa sun halatta haramtattun abubuwa da kuma cewa mutane suna tarayya cikin dukiya da mata. Dubi karin bayanin da Sayyid Muhammad Sadik Bahrul Ulum yayi wa littafin Nawbakhti na Firakul Shi'a.

[192] (**)Zindikai: Su ne masu kore dukka sha'anin addinin Ubangiji, masu ikirarin 'yancin tunani.

[193] (***)Dahriyya: su ne masu cewa duniya tana nan tun fil azal, ba ta gushewa, kuma babu wani Mahalicci, suna daga cikin kungiyoyin kafirai da mulhidai.

[194] Firakhul Shi'a na al-Nawbakhti, shafi na 60.

[195] Kamar na sama, shafi na 44.

[196] Firakhul Shi'a na al-Nawbakhti, shafi na 45.

[197] Kamar na sama.

[198] Alfehrist na al-Nadim, shafi na 227.

[199] Almukalat wal firak na Sa'ad bn Abdullah al-Ash'ari , shafi na 47.

[200] Rijal al-Kishshi, shafi na 305.

[201] Mishkatul Anwar fi Guraril Akhbar na Dabrisi, shafi na 66.

[202] Biharul Anwar na Allama Majlisi, juzu'i na 47, shafi na 378.

[203] Usulul Kafi na Kulayni, juzu'i na 1, shafi na 269.

[204] Makarimul Akhlak na Tabrisi, shafi na 39.

[205] Makarimul Akhlak na Tabrisi, shafi na 67.

[206] Kamar na sama, shafi na 66.

[207] Kamar na sama. (* ) A nan Imam yana nuni da darajar dangantaka da Manzon Allah (s.a.w.a.) da suka samu ta hanyar mahaifiyarsu Nana Fadima (a.s.).

[208] Makarimul Akhlak na Tabrisi, shafi na 66.

[209] Biharul Anwar na Allama Majlisi, juzu'i na 78, shafi na 198, da kuma Furu'ul Kafi na Kulayni, juzu'i na 8, shafi na 244.

[210] Makarimul Akhlak na Dabrisi, shafi na 77.

[211] Usulul Kafi na Kulayni, juzu'i na 2, babin zalunci.

[212] Kamar na sama.

[213] Kamar na sama.

[214] Kamar na sama.

[215] Kamar na sama.

[216] Kamar na sama.

[217] Usulul Kafi na Kulayni, juzu'i na 2, babin zalunci.

[218] Kamar na sama.

[219] Mishkatul Anwar na Dabrisi, fasalin Zalunci, shafi na 315.

[220] Kamar na sama, shafi na 316.

[221] Kamar na sama, shafi na 318.

[222] Mishkatul Anwar na Dabrisi, fasalin Zalunci, shafi na 316.

[223] Kamar na sama.

[224] Biharul Anwar na Allamah Majlisi, juzu'i na 75, shafi na 372.

[225] (*) Hakika Imam Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.) ya yanke wa sarakunan da suka yi zamani da shi face dai sai saboda wani yanayi na musamman da ya sa shi ya karbi wazircin Ma'amun a bisa wasu sharudda da Imam din ya kafa masa.

[226] (**) Amma Imam Jawad (a.s.) rayuwarsa ba ta yi tsayi ba, duk da cewa kuma Ma'amun ya aurar masa da 'yarsa don samun goyon bayan mabiya Ahlulbaiti (a.s), to amma duk da hakan bai taimaka wa Ma'amun cikin komai ba haka nan kuma bai hada hulda da shi ba.

[227] Imam Sadik (a.s) na Mahmud Abu Zuhra, shafi na 139. (*)Yana daga cikin manyan malaman mazhabar Ahlulbaiti (a.s) , ya rayu ne tsakanin shekara ta 734 - 786 bayan hijira.

[228] Rawdhatul Bahiya fi sharhil Lum'at al-Damashkiyya lil Shahidil Awwal na Shahidus Thani, juzu'i na 3, shafi na 213.

[229] Maktal al-Husain na Khawarizmi, juzu'i na 1, shafi 88.

[230] Kitabul Irshad na Shiekh Mufid, shafi na 204.

[231] Maktal al-Husain na Abdurrazak al-Mukarram, shafi na 141- 142. (*) Yana da kyau mu ambaci cewa Abu Hanifa, shugaban mazhabar hannafiyya, ya taimaka wa yunkurin Zaid kuma ya yi fatawar a ba shi zakka, domin wannan yunkuri nasa.

[232] Biharul Anwar na Allamah Majlisi, juzu'i na 47, shafi na 325, daga littafin Rijal al-Kishshi.

[233] (*) Shi dai wannan yunkuri an yi shi karkashin jagorancin Husain bn Ali bn Hasan bn Hasan bn Imam Hasan bn Imam Ali bn Abi Talib, kuma an yi don fuskantar halifan Abbasiyawa Al-Hadi a Madina, bayan da shi Husain.. ..din ya dauki alkawari a kabarin Kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.). A yayin wannan yunkurin, Husain ya yi shahada a hannun Abbasiyawan a kusa da garin Makka. Hakika ana daukan wannan yunkuri na Fakh a matsayin bala'i na biyu da ya fada wa Ahlulbaiti bayan waki'ar Karbala.

[234] Makatilul Talibiyyin na Abul Faraj, shafi na 447.

[235] Makatilul Talibiyyin na Abul Faraj, shafi na 445.

[236] Kamar na sama, shafi na 450.

[237] Bihar al-Anwar na Allamah Majlisi, juzu'i na 48, shafi na 151.

[238] Kamar na sama, shafi na 165.

[239] (*) An tara wadannan adduo'i na Imam Zainul Abidin a cikin wani littafi da ake kira Sahifatus Sajjadiyya.

[240] Al-Manakib na Ibn Shahru Ashub, juzu'i na 4, mas'alar mai da Imam Bakir (a.s.) zuwa Sham.

[241] Kamar na sama.

[242] Dala'il al-Imamah na Muhammad bn Jarir Tabari, vangaren rayuwar Imam Bakir (a.s.).

[243] (*) A nan yana nuni da fadin Manzon Allah (s.a.w.a.) ga sahabinsa Jabir Abdullah al-Ansari ne cewa: Lalle kai za ka riski daya daga cikin 'ya'yan Husaini, shi zai tsaga ilmi, don haka ka isar da gaisuwa ta gare shi". To a saboda haka ne aka kiran Imam Bakir (a.s.) da wannan suna na Bakir , wato mai tsatstsaga ilmi.

[244] Imam Sadik na Abu Zuhra, shafi na 138.

[245] Tazkiratul Khawas na Ibn Jawziyya, shafi na 359.

[246] Al-Fusulul Muhimma na Ibn Sabbag Al-Maliki, babin rayuwar Imam Hasan Askari (a.s.).

[247] Al-Fikhu ala mazahibil Khamsa na Shaikh Muhammad Jawad Mugniyya, shafi na 114.

[248] Al-Fikhu ala mazahibil Khamsa na Shaikh Muhammad Jawad Mugniyya, shafi na 466.

[249] Safinatul Bihar na Shaikh Abbas Kummi, babin karya, shafi na 484.

[250] Sunan Abi Dawud na Abu Dawud, juzu'i na 4, babin yada sallama, shafi na 350.

[251] AlManakib na Khawarizmi, juzu'i na 5, shafi na 44.

[252] AlManakib na Khawarizmi, juzu'i na 5, shafi na 122.

Abin da littafi ya kunsa

AHLUL BAITI (ZURIYAR MANZON ALLAH) 1

Mukaminsu Halinsu Da Tafarkinsu 1

Wallafar: Mu'assasar Al-Balagh 1

Fassarar: Ammar Kumo 1

Ahlul Baiti a Kur’ani da Hadisai: 2

Gabatarwar Mu'assasa 2

Gabatarwa 3

Ahlul-baiti (a.s) Cikin Kur'ani Mai Girma 5

Ta Farko:Ayar Tsarkakewa 5

Ta Biyu: Ayar Soyayya 8

Ta Uku: Ayar Mubahala 11

Ta Hudu: Ayar Salati 14

Ta Biyar: Surar Insan 16

Ta Shida: Ayoyi 18

Ayar Wilaya 18

Ayar Tablig (Isar da Sako) 19

Ahlulbaiti (a.s) Cikin Sunnar Annabi 21

1- Hadisus Sakalain (Nauyaya Biyu) 23

2- Hadisus Safina (Hadisin Jirgin Ruwa) 25

3- Hadisin Aminta Daga Sassabawa 26

4- Hadisul Kisa'i (Hadisin Mayafi) 27

5- Hadisin Soyayya 27

6- Wasu Ruwayoyi Na Daban 28

Alkur'ani Mai Girma A Wajen Malaman Mazhabar Ahlulbaiti (a.s) 30

Ka'idojin Fahimtar Alkur'ani Da Tafsirinsa 37

Hanyar Da Ake Bi Wajen Tafsirin Kur'ani 38

Sunnar Annabi (s.a.w.a) A Mazhabar Ahlulbaiti (a.s) 40

Rabe-Raben Sunnar Annabi (s.a.w.a) 43

Tafarkin Bincike da Tabbatarwa 44

Imaman Ahlulbaiti (a.s) Maruwaita Manzon Allah (s.a.w.a) 45

Tauhidi A Tafarkin Ahlulbaiti (a.s) 53

Adalcin Allah Da Sharhi Kan Halayyar Dan'adam 57

Tafarkin Ahlulbaiti (a.s) Wajen Tarbiyyar Mabiyansu 65

Gudummawar Ahlulbaiti (a.s) A Fagen Siyasa 66

Tafarkin Ahlulbaiti (a.s) Kan Ayyukan Siyasa 67

Dubi Cikin Mazhabobin Fikihu 77

Musulmi Al'umma Ce Guda 81

Fatawar mai girma Shaikhul Azhar kan halaccin aiki da Mazhbar Shi'a Ithna Ashariyya 86