Jazirar Larabawa Kafin Musulunci
Idan muna son fahimtar musulunci da sanin girman annabin rahama mai shiryarwa Muhammad (S.A.W) Wanda da ikon Allah ya iya tseratar da dan Adam, ya sanya shi akan
tafarkin cigaba da daidaituwa a ayyuka, yana mai farawa da wadanda suke gefensa na larabawa. To yana kanmu da farko mu san wane hali ne larabawa suka kasance kafin musulunci domin mu san yanayin da, daga nan ne da’awa zuwa ga musulunci ta fara, daga cikin mafi kyawun magana a kan wannan al’amari ita ce maganar Sayyid Allama Tiba’tiba’i (K.S) da yake cewa:
“Hakika wannan kur’ani yana ambaton lokacin zamanin larabawa da yake tukewa har zuwa bayyyanar musulunci a lokacin jahiliyya, ba komai ba ne sai nuni daga gareshi zuwa cewa; abinda yake hukunci a cikinsu a wannan zamani shi ne jahilci ba ilimi ba, kuma abin da ya mamaye su a cikin kowane al’amari nasu ba komai ba ne sai barna ba gaskiya ba
, sun kasance a kan hakan kamar yadda kur’ani ya ke ba mu labarinsu yana mai cewa: “Suna tsammani ga Allah abin da yake ba gaskiya ba zato na jahiliyya suna masu cewa shin mu na da wani makami na wani abu”. Ali imran: 154.
Madaukakin sarki yace
: “Shin hukuncin jahliyya suke so waye yafi kyautata hunkunci fiye da Allah ga mutane masu yakini”. Al-ma’ida: 50.
Yace
: “Yayin da wadanda suka kafirta suka sanya gaba a zuciyarsu irin gaban nan ta jahiliyya, sai Allah ya saukar da nutsuwarsa a kan manzonsa da kuma a kan muminai ya kuma lizimta musu kalmar takawa, kuma da man sun kasance su ne mafi cancanta da ita kuma su ne ma’abotanta, kuma Allah ya kasance masani da kowane abu”. Al-fath:26
.
Yace
: “Ku tabbata a gidajenku kada ku yi fita irin fitar jahiliyya ta farko, ku tsayar da salla, ku bayar da zakka, ku bi Allah da manzonsa”. Ahzab: 33.
Wannan ayoyi su ne mafificin madubi da yake nuna halin da larabawa da yanayinsu ya kasance, al’ummar larabawa musamman yankin hijaz ba ta da wata wayewa, kuma babu wani abuna
wayewa da cigaba da ya rage a cikinta kafin bayyanar musulunci, kuma ga al’adu iri-iri da koyi da iyaye da ya yadu a cikinta da mafi shahararsu su ne:
1- Shirka da Allaha
ibada, ta hanyar bauta ga gumaka da taurari.
2- Musun tashin kiyama, wato komawar mutum zuwa rayuwa a wata duniyar bayan mutuwarsa.
3- Yaduwar surkulle da kauce wa tafarki madaidaci da camfi, abubuwan da suke dakushe hankulan mutane, wadannan al’adu ne da suka yi karfi a suka kafu a cikinsu, kuma suka kasance dalili mai karfi na ci bayansu, kuma suka zama hani mai karfi a tafarkin cigaban da’war musulunci daga baya, abin da ya sanya annabi (S.A.W) yake aiki da dukkan karfinsa da kokarinsa wajan kawar da wadannan al’adu na jahiliyya, da gurbatattun akidu.
4- Fasadi da lalacewar dabi’a, kamar yaduwar caca, da giya, da zina, da luwadi, da karuwanci.
5- Binne ‘ya’ya mata, wannan wata al’adace mai muni da kur’ani ya yi magana game daita
a matsayin laifi mai muni da ba zai bari haka nan ba a lahira ba tare da ya yi hisabi a kai ba.
Yace
: “Idan aka yi wa dayansu albishir da mace sai fuskarsa ta zama baka yana mai bakin ciki, yana boye kansa daga mutane daga munin aibin da aka yi masa albishir da shi, shin zai rike shi ne a wulakance ko kuma ya turbude shi a turbaya, hakika abin da suke hukumtawa ya munana”. Nahal: 58-59.
Yace
: “Idan wacce aka binne ta aka tambaye ta.Da wane laifi ne aka kashe ta”.
Takwir: 8-9.
Saboda haka ne mace ta zama an haramta mata dukkan hakkokin zamantakewar al’ umma har da gado, namiji ya zama yana auren matar babansa idan ya sake ta ko bayan wafatinsa, da yawa daga ‘ya’ya suka yi fasin-fasin da matar babansu daya bayan daya, kamar yadda namiji yake gadon matar dan’uwansa idan ya mutu ya bar ta tamkar yadda yake gadon kayan gida, hada da cewa su ba sa ba wa ‘ya’ya mata gado kamar yadda suke ba wa ‘ya’ya maza.
6- Shan jini, da cin mushe, da cin naman alade, da cin naman sauran dabbobi da suke kashewa ta hanyar rashin tausayi.
7- Cin riba, wannan kumayana
zaman kashin bayan cinikayya a tattalin arzikinsu.
8- Kwace da karfi, kwace abin da yake hannun mutane da kai hari, da kisa, da kashewa,yana
daga al’adu masu karfi a wajansu, har ma ya zama yana daga abubuwan alfahari gun maza.
9- Amma a janibin ilimi da wayewa, mutanen hijaz sun siffantu da rashin iya rubutu da karatu, wadanda suka san karatu da rubutu a Makkagaba
dayanta adadinsu bai wuce mutane goma sha bakwai ba daga kuraishawa kafin zuwan musulunci.
10- Daga cikin munanan al’adunsu a wancan zamani akwai abin da Ja’afar Dan Abi Talib (A.S) ya fada yayin da ya yi huduba a gaban Najashi sarkin Habashayana
mai cewa: “Ya kai sarki! Mu mun kasane mutane ne na jahiliyya, muna bauta wa gumaka, muna cin mushe, muna zo wa alfasha, muna yanke zumunci, muna munana wa makwabci, mai karfi a cikinmu yana cin mai rauni, mun kasance a haka…”
. Wannanita
ce hakikar larabawa kafin musulunci.