Takaitaccen Tarihin Manzo
Da Ahlin Gidansa Manzo Muhammad Dan Abdullahi Al-Habib: Sunansa da Nasabarsa: Muhammad dan Abdullahi dan Abdul mudallibi dan Hashimi dan Abdu manafi dan Kusayyi dan Kilabi, nasabarsa madaukakiya tana tukewa zuwa ga Annabi Ibrahim (A.S).
Mahaifiyarsa:Ita
ce Aminatu ‘yar wahabi dan Abdu Manafi dan Zuhrata dan Kilabi.
Alkunyarsa: Abul Kasim, Abu Ibrahim.
Lakabinsa: Almusdafa yana da sunaye da suka zo a cikin Kur’ani mai girma kamar, Khataman nabiyyin, da Al’ummi da Almuzzammil da Almuddassir da Annazir da Almubin da Alkarim da Annur da Anni’ima da Arrahma da Al’abdu da Arra’uf da Arrahim da Asshahid da Almubasshir da Annazir da Ad’da’i da sauransu.
Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi’ul Auwal Shekarar Giwa (571m) bisa mash’hurin zance gun Ahlul Baiti (A.S), an ce, 12 ga watan da aka ambata.
Wurin haihuwarsa: Makka.
Aikoshi: An aiko shi a Makka 27 Rajabyana
dan shekara arba’in.
Koyarwarsa: ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da ‘yan’uwantaka da rangwamena
gaba daya ga wanda ya shiga musulunci, sa’annan ya kafa shari’a madaukakiya da dokoki na adalci da ya karbo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karba daga gare shi.
Mu’ujizozinsa: Mu’ujizarsa madauwamiyaita
ce Kur’ani amma wadanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.
Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a boye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma. Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi’ul Auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa.
Yakokinsa: Allah ya yi wa Manzo izinin yakar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi dauki ba dadi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune: Badar- Uhud- Al-khandak (Ahzab)-
Khaibar- Hunaini.
Matansa: KHadija ‘yar Khuwailid (A.S) ita ce matarsa ta farko, amma sauran su ne: Saudatu ‘yar Zami’a da A’isha ‘yar Abubakar da Gaziyya ‘yar Dudan (Ummu Sharik) da Hafsa yar Umar da Ramla ‘yar Abu Sufyan (Ummu Habibia) da Ummu Salama ‘yar Abu Umayya da Zainab ‘yar Jahash da Zainab ‘yar Huzaima da Maimuna ‘yar Al-Haris da Juwairiyya ‘yar Al-Haris da Safiyya ‘yar Huyayyi dan Akhdabl.
‘Ya’yansa: 1-Abdullah 2-Al-Kasim 3-Ibrahim 4-Fadima (A.S) a wani kaulin da Zainab da Rukayya da Ummu Kulsum.
Ammominsa: Tara ne, su ‘ya’yan AbdulMudallib ne: Al-haris da Zubair da Abu Dalib da Hamza da Al-Gaidak da Dirar Al-mukawwam da Abu Lahab da Abbas.
Ammominsa mata: Su shida ne daga iyaye mata daban-daban su ne: Amima da Ummu Hakima da Barra da Atika da Safiyya da Arwa.
Wasiyyansa goma sha biyu ne, su ne: Amirulmuminina Ali dan Abi Dalib (A.S) da Hasan dan Ali da Husain dan Ali da Aliyyu dan Husaini da Muhammad dan Ali da Ja’afar dan Muhammad da Musa dan Ja’afar da Ali dan Musa da Muhammad dan Ali da Ali dan Muhammad da Alhasan dan Ali da Muhammad dan Hasan Mahadi (A.S).
Mai tsaron kofarsa: Anas dan Malik.
Mawakinsa: Hassan dan Sabit, da Abdullahi dan Rawahata, da Ka’abu dan Malik.
Mai kiran sallarsa: Bilal Al-Habashi da Abdullahi dan Ummu Maktum da Sa’ad Al-kirdi.
Tambarin zobensa: Muhammadur Rasulullah!
Tsawon rayuwarsa: shekaru 63.
Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23.
Tarihin wafatinsa: 28 Safar 11 H.
Wajan da ya yi wafati: Madina.
Inda aka binne shi: Madina a Masallaci Madaukaki Mai alfarma.