• Farawa
  • Na Baya
  • 20 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 11364 / Gurzawa: 3073
Girma Girma Girma
Jagorancin Imam Sadik

Jagorancin Imam Sadik

Mawallafi:
Hausa

Matsayin Imam Sajjad (a.s)

Bayan waki’ar Ashura Imam Zainul Abidin Ali bin Hussain (a.s) yana da zabi biyu,su ne:- Imma dai ya sa sahabbansa shiga wata harka sakamakon motsawar rai da tausayi ya jefa su cikin wani garaje wanda wutarsa ba badewa ruruwarta zai yi sanyi, ya bice (saboda ba su da sifofin masu jihadi), sannan daga bisani a bar wa Banu Umayya filin ci gaba da danniya da babakere kan makomar al’umma wajen tunani da siyasa, ko kuma ya rinjayi tausayi da biri---bokon fushi da tunzura, kana ya tanadi share fage wa wani babban aiki wanda zai kai ga dawo da rayuwa irin ta musulunci. Bukatun share fagen su ne tunani mai jagorantan aiki da samar da wata salihar jama’a domin ta zama iri ga juyi da sauyi nan gaba, ya kuma nisanci idanun Banu Umayya, ya ci gaba da aiki haikan wanda manufarsa ita ce gina tunani da kuma dai-daikun matane. Da haka ne zai yi tafiya mai yawakan manufar kira, Imamin da zai gaje shi kuwa zai zama ya kara kusanto cimma manufar.

To wani zabiko hanya zai fifita?Ko shaka babu, hanyar farko ita ce ta sadaukarwa da daukar fansa, sai dai jagoran da yake shiri saboda harakar tarihi da kuma zamanin da tsawonsa ya zarce tsawon rayuwar Imam nesa ba kusa ba, sadaukar da rayuwarsa kawai ba ta isa. Dole ne yazama mai zurfin tunani, mai yalwar zuciya, mai hangen nesa mai dabara da hikima cikin al’amuransa. Wadannan sharrudda sun wajabtawa Imamzabar hanya ta biyun.

Imam Ali bin Hussain (a.s) ya zabi ta biyun duk da dauriya da wahal-halu da juriya da kuncin da ke tattare da wannan hanya. Ya ba da rayuwarsakan wannan tafarki (a shekara ta 95 bayan hijira).

Imam Sadik (a.s) ya sifanta mana yanayin da imami na hudu ya rayu a kai da kuma rawar da ya taka ta jagaba, ya ce:-“Bayan Imam Hussain (a.s) mutane sun juya baya banda mutum uku, Khalid Alkabuli da Yahya ibn Ummi Dawil da Jubair bin Mud’im.Daga bisani sai mutane suka dawo suka yawaita. Yahaya Ibn Ummi Dawil ya kan shiga masallacin Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce:- “Mun fita batunku kuma kiyayya da jiyewa juna sun bayyana a tsakaninmu …..”(Mumtahina aya 4.)

Wannan riwaya tana nuna halin da al’ummar musulmi take ciki bayanan kashe Imam Hussaini (a.s). yanayi ne mai ban tsoro, na fatattaka da raunin zuciya wanda ya game al’ummar musulunci a lokacin da waccan waki’ar ta faru, abin takaicinda ya auku a Karbala al’ummar har ma shi’ar Ahlulbaiti, ya fadi warwas. Wadannan ‘yan shi’an da suka gamsu da alaka da Imamai a zuci kawai amma a aikace sun karkatawa duniya da jin dadinta da kelkelinta. Irin wadannan sunanan tsawon tarihi hatta a zamanin nan namu, ba kuma kadan suke ba.

Daga cikin dubban masu da’awar shi’a a zamanin Imam Sajjad (a.s) mutum uku kadai suka rage bisa tafarki, mutum uku ne razanarwar Ummayawa da kamun da hukuma ke yiwa mutane bai sa su firgita ba, kuma son kubuta daga neman zaman lafiya bai girgiza azamarsu ba. Sun cigaba da amsa kira da fama bisa wannan tafarki da cikakkiyar azama da tabbata.Guguwar da ta kwashi al’umma tamkar wasu zauna gari-banza suka kuma bi manufar azzalumar hukuma, ba ta kwashi wadannan mutanen ba. Dayansu watau Yahya ibn Ummi Dawil ya kan mike a masallacin Madina ya yi huduba wa masu da’awar wilaya ga Ahlulbaiti yana mai baiyana bara’a gare su, kamar yanda ya gabata, yana kafa hujja da abin da Annabi Ibrahim (a.s) da mabiyansa suka fada wa masu bijirewan zamaninsa“ Mun fita batunku kuma kiyayya da jiyewa juna sun bayyana a tsakaninmu.” Ibn Ummi Dawil ya karanta wannan aya mai girma gaba ga masu da’awar wilaya ga Ahlulbaiti ne domin ya baiyana cikakken rabewa tsakanin sassan guda biyu:sashen ma’abota sako masu lizimta da kuma sashen masu zaman dirshan da sassautowa zuwa burace-buracen da basu taka kara sun karya ba da kuma rudi da abin duniya mara kima. Wannan rabewa tana tare da dukkanin kiraye-kirayen addini. Imam Sadik ya sifanta wannan rabewa na sassan biyu da cewa:- (Wanda ba ya tare da mu, to yana adawa da mu). Watauwanda duk ba ya sashen tauhidi to yana bangaren dagutu, babu wata ma’ana ga zama dan ba ruwanmu domin kuwa ba wani yankin tsaka-tsaki.

Wannan musulmi mai wilayar gaskiya ga Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a) watau Yahaya bn Ummi Dawil, da wannan kiran nasa ya baiyana rabewa tsakanin masu gamsuwa da wilayar da ta takaita ga motsin rai alhali suna kwanto cikin abubuwan amfanin kansu, suna nitse cikin dattin kuntataccen zatinsu,da masu lizimtar Imam a tunani da kuma aiki.Bisa dabi’a wannan rabewa tana nufin wuce gaban cewa batattun masu rinjaye su janye mutum, amma ba tana nufin watsi da batattun ba. Da wannan fikira ne wannan salihar jama’a ta fuskanci aikin tsamar da duk wani mai iya ‘yantuwa daga wahala da kangi. Sannu a hankali, sai wannan jama’a mai jihadi da dauriya ta yawaita, kuma da wannan ne Imam Sadik (a.s) yake ishara yayin da yace : “…… daga bisani sai mutane suka dawo suka yi yawa” Ta haka ne Imam Sajjad ya ci gaba da ba da himma kan aikinsa. Wannan aikin da wadansu matsayin da Imam ya dauka, wadanda za muambato nan gaba yana daga cikin abubuwan da suka janyo shahadarsa da ta wasu daga mukarrabansa.

Ban ga wani bayyanannen sa-in-sa da hukuma a rayuwar Imam Sajjad (a.s) ba.Kamar yanda muka ambata, hakan shi ne abin da ya dace da hikima. Domin da ya dauki irin matsayin da muke gani a rayuwar Imam Musa ibn Ja’afar (a.s) da imaman da suka biyo bayansa dangane da mahukuntan zamaninsa da bai iya ciyar da aikin sauyigaba har ya samar wa Imam Baqir (a.s) damar mayalwacin aiki ba. Da yayi haka daan hallaka shi da salihar jama’ar da take tare da shi.

Ba mu iya tsinkayar ra’ayin Imamna hakika dangane da masu iko illa nadiran, ko a nan ma bai kai matsayin fito-na fito ba. Iyakadai yana tabbatar da wani matsayi wa tahiri yana kuma fadakar da jama’ar da take kusa da shi kan abin da ya shafi aikinsa da harakarsa gwargwado. Irin wadancan matsayi sun hada da takardar suka mai tsanani da Imam da aikewa wani malami mai alakar kut-da-kut da Banu Umayya watau Muhammad bin Shihab Azzuhri. Muna iya fahimta a takardar cewa Imam yana magana ne da tsararraki masu zuwa tsawon zamani, ba da Azzuhri ba saboda Azzuhri ba mutumin da zai iya yantuwa daga kangin liyafar Banu Umayya da wasanninsu da mukamansu da al’farmarsu ba ne.Tahiri ya tabbatar da hakan, domin kuwa Azzuhri ya gama rayuwarsa ne cikinsa hidimarsu tare da rubuta littafi da kuma kirkirar hadisai saboda neman kusanci da su [9]

Saboda haka takardar Imam tana bayyana matsayinsa kan yanayin zamaninsa ne. Nassin wannan wasika yana nan cikin littafin Tuhaful Ukul.[ 10]

Akwai kuma wasikar da Imam ya aikewa Abdulmalik ibn Marwan a matsayin jawabikan wata wasikarsa wacce take dauke da aibantawa ga Imam saboda ya auri wata baiwar da ya yanta. Abin da Abdulmalik yake son baiyanawa Imam (a.s .) shi ne yana sane da duk abin da yake aikatarwa hatta al’amuran da suka kebance shi. Kazalikayana nufin tunatar da Imam (a.s) da dangantakarsa da shi da zimmar jan hankalinsa.

A jawabin da ya rubuta, Imam ya baiyana ra’ayin musulunci akan wannan mas’ala yana mai takidin cewa fifikon imani da musulunci ya kore kowani fifiko. Sannan ta hanyar kinaya, mai gwanin kyau, imam yayi ishara da hali rinna jahiliyya wanda iyayen halifa suka rayu a kai, la’alla ya hada har da rayuwar halifan shi kan shi. Ya ce:“ Babu karanta ga musulmi, karantar jahiliyya ce kawai karanta”.

Da halifa ya karanta kalmomin Imam (a.s) ya fahimci ma’narsu,cikakkiyar famta,kamar yanda dansa Sulaiman ya tsinkayi ma’anar yayin da ya ce da mahaifinsa: “Ya Shugaban Muminai alfaharin da Ali bn Hussaini ya yi hakika ya yi tsanani!” Saboda gogewarsa ta siyasa,halifa sai ya amsa wa dansa da abin da zai nuna masa cewa ya fi shi sanin abin da karo da imamin shi’a zai hafar. Ya ce da shi: “Da na kada ka fadi haka,domin wadannan harsunan Bani Hashim ne masu tsaga dutse, masu kamfata daga teku. Da ma ai Ali ibn Hussainiyana bayyana daukakarsa a yanayin da sauran mutane suke fankamar mika wuya.”

Wani misali mai nuna matsayin da Imam ya dauka shi ne yin watsi da wata bukatar Abdulmalik bin Marwan. Abdulmalik yasami labarin cewa akwai takwabin Manzon Allah (s.a.w.a) wurin Imam sai ya aiko yana neman ya ba shi kyautarsa ya kuma yi barazanar yanke abin da ake baiwa Imam daga baitul mali.Sai Imam (a.s) ya rubuto masa:-

((Bayan haka, Lallai Allah ya lamuncewa masu tsoronsa mafita ta inda suke ki, da arziki ta inda basu tsammani. Mai girman ambato ya ce (Lallai Allah ba ya son duk wani mai tsananin ha’inci mai yawan kafirci), sai ka duba ka gani wane ne daga cikinmu ya dace da wannan aya?[ 11]))

A wasu wurare muna ganin Imam Sajjad (a.s)yana motsawa cikin natsuwa da kuma garkuwa da tarbiyar dai-daiku da gina mutumtaka ta musulunci bisa karantarwar mazhabin Ahlulbaiti da yaki da baude-baude da sauransu. Da wannan aikin ne bisa hakika, ya dauki matakin asasina farko a kan tafarkin tabbatar da manufar mazhabin Ahlulbaiti wanda ita ce kafa jama’ar musulunci karkashin inuwar salihar hukumar musulunci bisa misalin hukumar Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali bin Abi Talib (a.s).Kuma kamar yanda muka ambata Imam (a.s) da mabiyansa basu nemi daidaitawa da hukuma mai kamu da azabtarwa ba duk da cewa sun bi hanyar da a zahiri tana daidaitawa da hukuma.

Daga cikin mabiyansa akwai wadanda aka kashe ta kazamar hanya, wasuan daure wasu kuwa an kore su nesa da mutanensu da gidajensu. Imam da kansa a kalla sau daya an tusa keyarsa a cikin kangi a cikin halin torartawa da wahala daga Madina zuwa Sham, sau da yawa kuma ya fada cikin nau ‘o’ in cutarwa da azabatarwa.Daga karshe halifan banu Umayya, Walid bin Abdulmalik ya ciyar da shi guba. Imam (a.s) ya yi shahada a shekara ta 95 bayan hijira.

Rayuwar Imam Bakir (a.s) Zarcewar Irin Rayuwar

Imam Sajjad An wayi gari mabiya Ahlulbaiti sun zama wata jama’a fitacciya mai dogaro da kai, kirar Ahlulbhaiti kuwa wacce ta dan tsaya ta kuma boye bayan shamaki mai kauri a dalilin waki’ar Karbala da waki’o’in da aka zubar da jini da suka biyo bayanta kamar waki’ar Harra da tawayen Tawwabun wadanda fir’aunancin Umayyawa ya haifar ta zama samamma ce mai yaduwa ta kuma bayyana cikin da yawa daga yankunan daular musulunci, musamman a Iraki da Hijaz da Kurasan. Tare da wannan samuwa, ta haifar da tsarina tunani da kuma aiki. Kwanakin da Imam Sajjad (a.s) ya sifanta da cewa : “ mabiyansa ba su wuce ashirin ba” sun kau sai ga Imam Bakir (a.s) yana shigo masallacin Ma’aiki (s.a.w.) a Madina jama’a mai yawa daga mutanen Kurasan da sauran lardunan duniyar musulmi suna kewaye shi, suna tambayarsa hukuncin musulunci kan al’amuran rayuwa dabam-dabam. Mutane kamarsu Dawus Yamani da Katada ibn Da’ama da Abu Hanifa da wadansu daga shugabannin mazhabobin fikihu suna tahowa domin su sha daga ilmin Imam ko kuma su yi jayayya da shi kan al’amura dabam-dabam.

A wannan zamaninan sami mawaka masu kare mazhabin Ahlulbaiti da bayyana manufofinsa. Daga cikinsu akwai Kumaitwanda ya sauwara mafi kyan surar da kwararru ke zaiyanawa a kan wilaya ta tunani da kauna ga mutanen gidan Manzon Allah (s.a.w.a) cikin kasidarsa mai suna hashimiyya. Hakika harsuna basu gushe ba suna nakaltar wadannan gwalagwalan wake yayin da zukata suke kiyaye su.

Ta wata fuska kuwa halifofin Banu Marwana cikin wannan dan lokacin, sun sami wata natsuwa da tabbatar mulki bayan Abdulimalik ibn Marwan (m.86H) cikin shekara ashirin da ya yi mulki, ya murkushe dukkan masu ja da mulkinsu, kuma yiwuwa cewa sansancewar aminci da natsuwa da halifofin Marwaniyawa na wannan lokacin ya samo asali ne daga kasancewar sun sami mulki tamkar wata ganima, sabanin magabatansu wadanda suka yi jan aiki kafin su kai ga mulki. Wannan natsuwa tasa halifofin baya shagaltuwa da wasanni da jin dadin duniya, tadodin da galibi suke tare da mai jin iko da alfarma da kuma girma.Ko mene ne ma dai, damuwar halifofin Banu Marwan da lamarin mazhabin Ahlulbaiti ta ragu a wancan lokacin, sai ga Imam da mabiyansa suna rayuwa kusan a ce cikin aminci daga farautar hukuma. Bisa dabi’a, Imam zai ci tafiya mai yawakan tafarkin tabbatar da manufofin mazhabin Ahlulbaiti a irin wannan yanayi ya kuma kai shi’anci wani sabon zango.Wannan kuwa shi ne ya bambanta rayuwar Imam Bakir (a.s) da ta saura. Ana iya takaita abin da rayuwar Imam, cikin shekaru goma shatara na imamancinsa (95-144H) ta kunsa kamar haka:-

Yayin da mahaifinsa Imam Sajjad (a.s) ya zo cikawa ya yi wasici da cewa dansa Muhammadu yazama Imami bayansa, gaba ga sauran ‘ya’yansa da danginsa, ya kuma ba shi wani akwati. Riwayoyi sunce akwatin cike yake da ilmi, sun kuma ce akwai makamin Manzon Allah (s.a.w.a) a ciki. Imam Sajjad (a.s) ya ce:- “Ya kai Muhammadu wannana akwati ka tafi da shi gidanka” Sannan ya ce:- “Hakika babu dinari ko dirhami a ciki, sai dai cike yake da ilmi”[12]

La’alla wannan akwati wata alamace mai muna cewa Imam Sajjad ya mikawa dansa jagorancin tunani da ilmi (tunda yana cike da ilmi) ya kuma mika masa nauyin jagorancin juyi (tun da yana kunshe da makamin Annabi (s.a.w.a)).

Gami da farawar Imam da mabiyansa faffadan aikinsuna yada koyarwar Ahlubaiti (a.s) farfajiyar yaduwar kiran ta kara fadi, ta sami sababbin fuskoki wadanda suka zarce fagenta daya gabata a Madina da Kufa.Sai ga ta tana yaduwa cikin larduna manisanta daga cibiyar mulkin Umayyawa. Lardin Kurasan na daga cikin wadancan wurare kamar yanda riwayoyin tahiri suka nuna.[ 13]

Yanayin tunani da zamantakewa mai kaskanta mutane ya zaburar da Imam da mabiyansa wajen haraka mai dorewa ba tare da gajiya ko kosawa ba domin sauya wannan mummunan yanayi da tabbatar da abinda Ubangiji ya wajabta na kawar da wannan baudiyar.

Suna ganin mafiya yawan mutane sun rusna wa gurbatanccen yanayin da Banu Umayya suka yada, suka nitse cikin kazantar abin duniya iya wuya har suka wayi gari tamkar mahukuntan nasu,basu fahimtar zance, kunnensu bai jin nasiha. “Idan mum kira su ba sa amsa mana”.[ 14]

Ta wata fuska kuwa, Imam da jama’arsa suna ganin bincike-binciken fikihu da ilmul kalam da hadisi da tafsirina karkata ne wajen dadada wa fir’aunancin Umayyawa da bin sonransu. Saboda haka duk hanyoyin dawowar jama’a kan katari da sun toshe, ba don zaburar mazhabin Ahlulbaiti wajen bayar da wajibinsa ba idan kuwa muka kyale su ba za su shiriya ta hanyar waninmuba[ 15]

Mazhabin Ahlulbaiti ya yi Allah wadai da malamai da mawaka da suka sayardakansu .An yi wannan sukan ne saboda kokarin farkarda zukatan wadancan malaman ko kuma zukatan mabiyansu. Imam yana fadawa Kumait, sha’irin Ahlulbaiti, da lafazin suka:- yabon Abdulmalik kayi?

Ya ce:- Ban ce da shi ‘ya shugaban shiriya’ ba, abin da na ce shi ne ‘ya zaki’ zaki kuma kare ne, ‘ya rana’ rana kuwa jamadatu ce, ‘ya kogi’ kogi kuwa mataccen abu ne, ‘ya maciji’ maciji kuwa kwaro ne mai wari, ‘ya tsauni’ tsauni kuwa kurman dutse ne. Sai Imam ya yi murmushi. Kumait sai ya rera wannan baitin gaban Imam:- Zuciyar da so ya tsare ya aure? Ban da yaranta tasa har da guri, Wannan mimiyar ta kafa mararraba tsakanin alkiblar Alawiyya da ta Umawiyya a daraja da kuma halaye ta hanyar dawwamammar zaiyanawa mai kyan gaske.

Wata rana Ikrima almajirin ibn Abbaswanda yake sananne ne, mai matsayin ilmi a cikin al’ummar wancan zamanin ya je yin mukabala da Imam sai haibarsa da natsuwarsa da ruhinsa da tunaninsa suka kama Ikrima. Abin da kadai ya iya fada shi ne:- “Ya dan Manzon Allah hakika na zauna gaban Ibn Abbas da waninsa sau da yawa amma irin abin da ya same ni yanzu bai taba samu na ba”. Sai Imam ya amsa masa da cewa:- “(Kai kana gaba ga gidaje wadanda Allah ya yi wa daukaka kuma ake ambaton sunansa a cikinsu)[16]

Ta wandansu fuskoki daban na ayyukan mazhabin Ahlulbaiti a wannan zangon kuwa, akwai jerin zalunci da fir’aunanci da kisa da azabtarwa da kora, da suka kewaye Ahlulbaitin Manzon Allah da mabiyansu ba don komai ba sai domin kokarin da suke yi na iza matacciyar zuciyar mutane da girgiza rayukansu wadanda suka yi sanyi da zaburar da kwantacciyar azamarsu da shiryar da su zuwa harakar juyi.

Alminhal bin Umar ya ruwaito cewa:- “Na kasance ina zaune tare da Muhammad bn Ali Albakir (a.s) sai wani mutum ya taho ya ce da shi: Yaya kuke? Sai ImamBakir( a.s) ya ce:- “Lokaci bai yi ba da za ku san yanda muke? Misalinmu a wannan al’umma tamkar Bani Isr’a’ila ne a da,ana yanka ‘ya‘ya maza ana barin (raya )mata. Ka saurara!Lallai wadannan suna yanka ‘ya‘yanmu maza suna barin ‘ya ‘yanmu mata. Larabawa sun yi da’awar fifiko bisa baibayi. Sai baibayin sukace : ‘Mene ne dalilin haka?’ Sai sukace : “Muhammadu balarare ne daga gare mu” Sai suka ce da su: “Kun yi gaskiya.”Kuraishawa kuwa suka yi da’awar cewa suna da wani fifiko bisa sauran larabawa. Sai sauran larabawa sukace “Mene ne dalili?” Sai suka amsa da cewa: ‘Muhammadu bakuraishe ne’. Sukace da su: ‘Kun yi gaskiya’. Idan mutanen nan sun yi gaskiya, to muna da fifiko bisa mutane domin mu zuriyar Muhammadu ne, mutanen gidansa kuma makusantansa masu kebanta da shi, waninmu ba ya tarayya da mu a wannan” Sai mutumin ya ce da Imam; “Wallahi ni ina son ku, ku Ahlulbait”. Sai yace da shi: “To ka dauki bala’i a matsayin riga, domin kuwa wallahi shi (bala’i) ya fi kusa da mu da kuma shi’armu bisa ga gudanar igiyar ruwa a cikin kwari. Da mu bala’i zai fara sanan ku”[ 17]

Da ganin alamar cewa mutumin ya girgiza saboda zaburarwar da ya ji sai Imam ya yi maza ya zana masa tafarkin kiran, ya fayyace.Shidai tafarki ne wanda aka shimfida shi da jini da kwalla, Imam kuwa shi ne madugun tafiyar, bala’i yana samunsa da farko kafin ya kai ga shia’rsa.

A tsakanin shi’arsa alakar Imamtana da wadansu sifofi kebantattu. Za ka gan shi cikin mabiyansa tamkar yanda kwakwalwa take a tsakanin gabban jikiyana ciyar da ruhinsu yana karfafa masu haraka da himma ba tare da yankewa ba. Akwai hujjoji a hannunmu wadanda suke bayyana wannan alaka mai bawa mabiya manufofi da karantarwa mabayyana da kuma tsara al’amuransu bisa tafarki hadadde, lasaftacce.

Misali; A farkon haduwar Jabir Alju’fi da ImamBakir( a.s) sai ya masa wasiyya da kada ya fada wa kowa cewa daga Kufa yake ya kuma yi fita irin ta mutanen Madina .Da wannan Imam yake koyar da darasin rike sirri ga wannan sabon dalibi wanda ya ga alamun iya rike sirri tattare da shi. Wannan dalibi mai cancanta sai yazama ma’abocin sirrin Imam. Tsakaninsa da hukuma kuwa lamarin ya kai ga abin da Nu’man bin Bashir yace :-

“Ina mai lizimtar Jabir bin Yazid Alju’fi yayin da muke Madina sai ya shiga wurin Abu’far (a.s) ya yi masa bankwana ya fitoyana farin ciki. (Mukakama hanya) har muka isa Al’ukairaja, daga kewayen Madina, a ranar Juma’a.Muka yi salla. Munkama tafiya kenan sai ga wani mutum dogo mai duhun fatar jiki da wasika a hannunsa. Sai Jabir ya karbe ta ya sunbace ta yasanya takan idanunsa. Sai ga shi arubuce( ( Daga Muhammad bin Ali ( Bakir) zuwa ga Jabir bin Yazid)), ga kuma danyen bakin yumbu a kanta. Sai yace da shi: ‘Yaushe rabonka da shugabana?’ Sai mutumin yace : ‘Dazun nan; sai ya ce: ‘kafin salla, ko bayan salla? Sai yace : ‘Bayan salla.’ Sai ya warware hatimin ya cigaba da karantawa, yana daure fuska har ya kai karshenta, sannan ya nade ta. Daga nan ban sake ganinsa yana dariya ko farin ciki ba har muka isa Kufa”.

Numan ya cigaba da cewa: “Mun isa kufa cikin dare, kashegari sai na tafi wajen Jabir Alju’fi saboda girmama shi, sai gashi ya fito bisa dokin kara yana rataye da wadansu kulle-kulle, tamkar yanda mahaukata ke yi, yana rerawa kamar haka: ‘Na san Mansur mutumin mutane; Mai umurni ba’a umurtansa’ da wasu baitoci irin wannan. Sai ya kalli fuskatana kalli tasa amma bai ce da ni komai ba, ni ma ban ce masa komai ba. Saina juya ina kuka saboda abin da na gani.Sai jama’a, babba da yaro, suka kewaye mu. Sai ya tafo har ya shigo dandali, yakama zagawa tare da yara mutane na cewa Jabir bin Yazid ya haukace. Wallahi bayan ‘yan kwanaki sai ga takardar Hisham Ibn Abdulmalik an aiko ta gareni kan batun shi. Tana cewa: ‘Ka binciki wani mutun mai suna Ja’bir Ibn YazidAlju’fi ?’sai mutane suka ce: ‘Allah ya kiyaye ka’.Da mutun ne mai ilmi da daraja da sanin hadisi, ya yi aikin haji sai ya haukace. Shi ne wancan a dandali bisa dokinkara yana wasa da yara. Sai na ce: “Godiya ta tabbatar ga Allah wanda ya hutar da ni kisansa’.[ 18]

Wannan misali nena alaka tsakanin Imam da mabiyansa na kusa. Yana bayyana tsananin tsarisa alaka kazalika yana nuna wani misali na matsayin hukuma kan mabiyan Imam. Wannan yana tabbatar mana cewa, masu iko ba cikin cikakkiyar gafala dangane da alakar Imam da mabiyansa na kusa suke ba, a’a, suna sa ido kan wadannan alakoki, suna kokarin gano su da kuma yin fito-na-fito da su.[19]

Sannu a hankali bangaren fito-na fito a rayuwar Imam Bakir (a.s) da ta shi’ayana tabbatar da wani fasali na rayuwar Ahlulbaiti (a.s).

Nassoshin tarihi da riwayoyin hadisi wadanda suke hannunmu basu faiyace samuwar wata matsananciyar harakar fama a siyasance wacce Imamyake aiwatarwa ba. Wannan rashin bayyanannar famayana da dalilai, kamar su wanzuwar wani yanayi na jabberanci da azabtarwa mai mamaye da rayuwar al’umma, abin da ya tisalta wa mabiyan Imam wadanda su kadai ne masu masaniya kan rayuwarsa ta fuskar siyasa da su yi riko da takkiya. Saidai martani matsananci wanda magabta (hukuma) suke mayarwa yana nuni da aikin jihadi mai zurfin tasiri da ake yi. Yayin da karfin mulki iri na Abdulmalik Ibn Marwan,wanda ake daukarsa a matsayin mafi karfin sarakunan Umayyawa, yayin da yake daukar mafi tsanani da tsaurin mataki kan Imam Bakir, ba wata tantama, wannan yana nuna cewa halifan yana jin tsoron hadarin da harakar da Imam da mabiyansa ke gudanarwa take tattare da shi ne. Da a ce Imam ya shagaltu ne da aiyukan ilmantarwa kadai ba tare da ya ba da himma kan gina tunani da tsare-tsare ba, to da sai mu ce ba maslaha ce ga masu mulki ba su matsawa Imam din lamba domin wannan mataki yana iya sa wa shi da mabiyansa su dauki matsayin fushi matsananci tamkar wanda mai tawayen nan ba’alawe Shahidin Fakh, watau Hussain bin Ali ya dauka.

A takaice, ana iya fahimtar matsanancin matsayin da hukuma ta dauka dangane da Imam Bakir (a.s) ta fuskar mayar da martanin da take yikan aiyukan Imam masu sabawa da ra’ayin masu iko.

Daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a karshen rayuwar Imam Bakir (a.s) akwai kiransa da aka yi zuwa hedkwatar halifancin Umayyawa watau Sham (Dimashka). Halifofin Umayyawa sun yi niyyar bincikar matsayin Imamkan hukuma. Wannan yasa suka yi umurni da kama shi da kuma kai shi Sham cikin cikakken tsaro. A wasu riwayoyi ance wannan umurni ya hada har da dansa matashi watau Ja’far Sadik.

An kawo Imam fadar halifa. Kafin haka Hisham ya yiwa jama’arsa shiftar yanda za su fuskanci Imam yayin da yake shiga. Abin da ya shirya shi ne, shi halifa zai fara bijiro da tuhumce-tuhumcekan Imam sannan jama’a su ci gaba.

Abubuwa biyu yake da niyyar cimmawa:na farko shi ne raunana azamar Imam da sanya masa rashin yarda da kai. Na biyu: Kokarin sukar Imam a cikin taron da ya hada jagaban jama’ar halifanci da kumana Imamanci a waje guda, sannan daga bisani a yada wannan cin zarfin ta hanyar kakakin fada kamar masu jawabi da masu wa’azin sarki da kuma ‘yan laken asiri, kuma da haka ne Hisham yake fatar samawa kansa nasara kan abokin hamayyarsa.

Da Imam ya shigo fadar halifa, sabanin yanda masu shigowa sukasaba da yin gaisuwa ga halifa da sunan shugaban muminai, sai ya fuskanci dukkan mahalarta yana mai nuni ga ilahirinsu, ya ce: assalamu alaikum. Sannan ba tare da jiran izininzama ba sai ya yi zamansa.

Wannan abin da Imam ya aikata ya cinna wutar hasada da kufe a zuciyar Hisham. Nan take sai ya fara jefa muggan maganganu yana cewa: ‘ Ya Muhammad Ibn Ali ba’a gushe ba wani daga cikinku yana rarraba kan musulmi, yana kiran mutane da su bi shi, yana kuma da’awar shi ne Imami (shugaba ) saboda wauta da karancin sani ………[20]Ya dai ci gaba da sukar sa.

Bayan Hisham yagama sai jama’a suka karba, suka ci gaba da maimata wadannan tuhumce-tuhumce da soke-soke. A tsawon wannan lokaci Imam uffan baice ba, yana sunkuye da kai cikin natsuwa, yana jiran damar ba da amsa. Yayin da mutanennan suka kare duk abin da ke gare su, wuri ya yi tsit, sai Imam ya mike ya fuskanci jama’a, ya yi yabo ga Ubangiji ya yi salati ga Manzonsa (s.a.w.a) kana ya yi jawabi.

Wannan jawabin ya kunshi kalmomi ne matakaita masu kwankwasa tare da bayyana rauni da kuma sakar akala tamkar kumakiwanda wadancan ‘yan amshin Shatan suka yi. Kazalika ya nuna matsayi da daukaka da Ahlulbaiti suke da shi, kamar yanda ma’aunan musulunci suka tabbatar, ya kuma wulakanta duk abin da halifa da jama’arsa suka mallakana kazamar dukiya da kuma iko. Ya ce:- ‘Ya ku mutane ina kuke tafe ne?Ina aka nufa da ku? Da mu Allah ya shiryina farkonku kuma da mu ne zai cikata (shiryar da) na karshenku. Idan abin gaggautawa na mulki naku ne to (ku sanicewa ) abin da aka jinkirtar na mulki namu ne sannan kuma babu wani mulki bayan namu saboda mu ne ma’abota kyankkyawan karshe. Allah mai girma da daukaka yana cewa: “Kuma kyakkyawan karshe ya tabbata ga masu takawa”[ 21].

Wadannan kalmomi matakaita wadanda suka kunshi wawaitarwa da kokowa da zalunci, da albishiri da bazarana, da tabbatarwa da kuma raddi duk a lokaci guda, ba shakka masu girgizawa ne tare da sa mai sauraro yin imani da cewa mai fadarsu shi ne ma’abocin hakki.Sakamakon haka, Hisham sai ya ga babu abin da zai yi face umarni da a jefa Imam kurkuku. Imam Bakir( a.s ) ya ci gaba da aikinsa na gyara hatta a cikin gidan kaso, al’amarin da ya yi tasiri matuka kan fursunoni. Da labari ya kai ga Hisham,sai ya ji tsoron cewa irin wannan farkawa za ta faru a hedkwatarsa wacce aka kiyaye daga tasirin Alawiyyawa. Sai ya yi umarni da fitar da wannan fursunan (Imam Bakir) tare da wadanda suka dauki ra’ayinsa da kuma aika su da daggawa zuwa Madinawanda shi ne mazaunninsa. Umarnin ya hada da cewa idan sunkama hanya kada kowa ya yi wata hulda da wannan ayari wanda halifa yake fushi da shi. Kada a ba su guzurin abinciko ruwan sha.

Bayan kwana uku ana tafiya ba kakkautawa abinci da ruwan da yake tare da su sai ya kare, a wani birni da ake kira Madin. Saboda umarnin Hisham, mutanen sun kulle kofifin birnin suka kuma ki sayarwa wadannan bayin Allah da komai. Yunwa da kishi suka yiwa mabiya Imam tsanani. Sai Imam ya haura kan wani tudu wanda daga bisan shi ana iya hangar cikin birnin ya daga murya da kyau ya ce:- “Ya ku mutan garin da mutanensa suka yi zalunci! Ni ne falalar Allah mai wanzuwa Allah yana cewa”:- Falalar Allah mai wanzuwa (bakiyyatullahi ) ita ce mafi alheri a gare ku idan kun kasance muminai, kuma ni ba mai tsaro ne a kanku ba”.

Mai riwaya ya ci gaba da cewa: Akwai wani tsoho tukuf a wannan birni, wanda ya ce da su: ‘Mutanena, wallahi wannan kira ne irin na Annabi Shu’aibu( a.s ). Na rantse da Allah idan ba ku fita kuka sayarwa wannan mutumin (abin da yake bukata) ba za’a kama ku daga birbishinku da kuma karkashinku. To lallai ku gaskata ni kuma ku bi maganta, dominni mai nasiha ne a gare ku’.

Mutanen garin sai suka amsa kiran dattijon nan, suka fita da gaggawa suka sayar wa Abu Ja’afar (Imam Bakir (a.s)) da sahabbansa da abin da suke bukata.[ 22]

Karshen wannan ruwayayana nuna mana irin dirar da halifan Abbasiyawa yake yi kan mutane da kuma jabberancinsa. Bayan mutanen birnin sun budewa Imam da sahabbansa kofofin gari sai aka rubuta dukkan abin da ya faru aka aikewa Hisham. Sai ya aiko da takarda zuwa hakimin Madin da umarnin cewa yakama wancan dattijon ya kashe. Allah ya ji kansa da rahama![ 23]

Tare da wannan hali, Imamyana nisantar duk wani matsanancin fito-na-fito da yin gaba da masu mulki. Ba ya daukar takobi ba ya kuma yardarwa masu garaje zare tokobi,yana dai shiryar da su ta hanyar hikima. Takobin harshe ma Imam ba ya zarewa idan ba aikinsana gyara da sauyi daga tushe ya bukaci hakan ba. Kuma bai yardarwa dan uwansa Zaid, wanda fushi da motsin rai ya kai masa iya wuya, yin tawaye ba. A ‘a, shidai aikinsa yana ba da karfi ne wajen shiryarwar da wayar da kai da tunani, hakan kuma gina tushen manufa (aidiyoloji) ne tare da kula da takiyya a siyasance.

Saidai wannan salon bai hana Imam ya bayyana wa mabiyansa “harakar imamanci” ba, kamar dai yanda muka yi nuni da shi, bai kuma hana shi karfafa musu babban burin shi’an nan na kafa sahihin tsarin siyasa mai bin tafakarkin Imam Ali (a.s) ba. Wani lokaci mayana tunzura zukatansu gwargwadon bukata saboda raya wannan burin.

Daya daga hanyoyin da Imam Bakir (a.s) yake kwadaitar da mabiyansaita ce ishara ga zamanin mai haske wanda zai zo nan gaba. Wannan kumayana nuna yanda Imam (a.s) ya kwatanta zangon da yake raye a harakar imamanci. Hakam ibn Uyainayana cewa: wata rana ina tare da Abu Ja’far (a.s) alhali gidan na cike makil da mutanen gidansa sai ga wani dattijo ya tafo yana tokarawa da mashinsa har ya tsaya bakin kofa ya ce:

Aminci da rahamar Allah da albarkarsa su tabbatar gare ka ya dan Manzon Allah (watau ya yi sallama). Sannan ya yi shiru. Sai Abu Ja’far ya amsa masa: Aminci ya tabbata gare ka da rahamar Allah da albarkarsa. Sai dattijo ya fuskanci mutanen gidan yace : assalam alaikum, sannan ya saurara har jama’a suka amsa sallama gaba dayansu. Sai ya fuskanci Imam yace : “Ya dan Manzon Allah ka kusantar da ni gareka, Allah Ya sanya ni fansarka. Wallahini ina kaunarku, ina kuma kaunar mai kaunarku. Kuma wallahi bana son ku tare da son mai son ku saboda kwadayin abin duniya. Kumani ina kin mai gaba da ku ina kubuta (bara’a) daga gare shi. Kuma wallahi bana kin shi ina kubuta daga gare shi domin wata kullalliya da ke tsakaninmu. Wallahini ina halatta abin da kuka halatta shi, ina haramta abin da kuka haramta shi ina sauraron umarninku. To shin kana mini tsammanin (alheri ) ,Allah ya sanya ni fansar ka? Sai Imam ya ce:“ Taho nan, taho nan” ya zaunar da shi gangarsa sannan yace:-

‘Dattijo! Lallai wani mutum ya zo wa babana Ali bin Hussain (a.s) ya tambaye shi tamkar abin da ka tambaye ni sai babana (a.s) ya ce da shi:- Idan ka mutu za ka zo ga Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali da Hassan da Hussain da Ali ibn Hussaini, kuma za’a sanyaya zuciyarka, za ka ga farin ciki, za’a tarbe ka da hutawa da kyakkyawan abinci tare da Masu daraja, Marubuta ( kiramun katibuna ). Idan kuma ka rayu za ka ga abin farun cikin da Allah zai sanya ka ciki za ka kasance tare da mu cikin kololuwar daukaka”.

Cikin gigicewa saboda girman wannan albishiri,dattijo sai ya ce:`Ta yaya,ya kai Abu ja’far?Sai Imam ya maimaita masa maganar da ya yi. Sai tsohon nan ya ce:Allahu akbar! Ya Abu Ja’far idan na mutu zan zo wa Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali da Hassan da Hussain da Ali ibn Hussaini, kuma zan ga abin farin ciki, a kuma sanyaya min zunciya, a tarbe ni da hutawa da kyakkyawan abinci tare da Masu daraja, Marubuta idan na cika? Idan kuma na rayu zan ga abin da zai faranta mini rai, kuma in zama tare da ku a kokoluwar daukaka?” Sai tsoho yakama kuka sai da ya kai kasa. Yayin da mutanen gidan Imam suka ga yanayin da dattijonnan ya shiga sai su ma suka kama kuka.Sai dattijo ya daga kai ya nemi Imam ya mika masa hannunsa. Sai ya sumbanci hannun ya sanya shikan idanu da kumatunsa sanan ya yi ban kwana ya fita. Imam yana kallonsa yana cewa:- Wanda ya so ganin wani mutum daga mutanen aljanna to ya dubi wannan (mutumin).[24]

Irin wannan fayyacewa tana karfafa ruhin buri a zukatan da suke rayuwa cikin yanayin zalunci da danniya, takan wanzar da tunkudawa zuwa ga manufar da ake bida wacce ita ce kafa adalin tsari na musulunci.

Shekara goma shatara na imamanci Imam Bakir (a.s) aka yi aiki na gudana bisa wannan mikakken layi mabayyani. Shekara goma shatara na koyarwa kan manufar gini da dabarun kare kai da tsare-tsare da kare haraka da takiyya da karfafa ruhin sa-rai da sauransu.

Shekara goma shatara ana gudanar da wannan tafiya mai tattare da kaya da munin hanya wanda yake bukatar kokari da ijtihadi mai yawa. Lokacin da wadannan shekaru suka kawo karshe, ranar rayuwarsa mai albarka ta zo faduwa, sai abokan gabansa suka yi ajiyar zuciya domin a zatonsu idan wannan jagora mai shiryarwa ya tafi za su huta da tushen farkarwa da izawawanda ya dade yana hana su hutu da barci.

Amma hakan bai yiwu ba domin Imam ya tabar da burinsu ya kumasa wannan dama ta kubuce musu saboda ya sanya wafatinsa ya zama tushen shiryarwa, musabbabin farkawa sannan kuma hanyar wayar da kai mai dorewa. Imam ya umarci dan saSadik( a.s) a karshen rayuwarsa, ya umarce shi da wani aiki wanda samfuri ne mai gwanin ban sha’awa daga samfur-samfur na takiyya da kuma salon kira wadanda Imam Bakir (a.s) ya yi amfani da su a zangon zamani wanda ya kebance shi A cikin ruwaya daga Abu Abdillah Sadik (a.s) ya ce: ‘Babana ya ce da ni: Ka ware abu kaza daga dukiyata saboda a mini zaman makoki na tsawon shekara goma a Mina a ranakun Minan”.[ 25] ..Ita wannanruwaya , wadanda suka yi bincike kan rayuwar Imam Bakir basu dube ta da kyau ba kuma sun gafala ga barin ma`anoni masu girma wadanda ta kunsa. Imam ya rasu ya bar dirhami dari takwas, yayi umarni da aware wani abu daga ciki a baiwa masu kukan mutuwarsa a Mina. Yin kukan rasuwar Imam a Mina ya kunshi ma`ana mai girma .Lallai shi aiki nena raya tushen nan da ya kasance a ko yaushe yana watsa hasken wayar da kai da farkarwa da kuma sanya ruhin kamuji da gwagwarmaya.

Zaben Mina kuwayana nufin wanzar da aikin a tsakiyar taron jama`a masu tahowa daga dukkanin sassan duniyar musulunci a dai dai lokaci guda daya tak da ake zaune wuri guda yayin aikin haji. Saboda dukkan ayyukan haji ana gabatar da su ne cikin halin motsawa ba tare da sararawa ba idan ba a Mina ba, inda ake kwana biyu ko uku, saboda haka alhazai suna samun isashshen lokaci domin sauraro da ganin kukan rasuwar Imam a wannan wuri zai kuma sa a yi tambaya kan ko wane ne wannan mamacin? Za’a kumasami jawabi wajen mutanen Madina wadanda suka yi zamani da shi. Za suce shi daya daga ‘ya’yan Manzon Allah ne, kuma shi ne malamin fukaha`u da masana hadisi. Za’a kuma tambayi dalilin da yasa ake makokinsa a wannan guri, shin mutuwarsa ta bambanta da ta saura ne? To wane ne ya kashe shiko ya sanya masa guba? Shin ya kasance wata barazana ga mulkin Umayyawa ne? Dadai sauran su.Gomonin tambayoyi aka yi ta jefowa yayin da ake kukan rasuwar Imam a wannan wuri, sannan masu tambaya suna samun amsa. Kuma labarin ya yi ta watsuwa cikin garuruwa, sako sako, bayan komawar alhazai kasashensu. Akwai kuma masu zuwa daga Kufa da Madina takanas saboda amsa wadannan tambayoyi da yada ruhin shi’a suna daukar damar taron musulmi, damar da ba’a samun tamkar ta a wancan lokacin.

Haka Imam ya rayu, haka kuma ya tsara al’amura domin abin da zai zo bayan wafatinsa. Tsira ta tabbata gare shi ranar da aka haife shi da ranar da ya yi jihadi da ranar da ya yi shahada a tafarkin Allah da kuma ranar da za’a tashe shi rayayye.

Imam Bakir (a.s) ya rasu yana da shekara hamsin da bakwai a duniya, a zamanin Hisham bin Abdulmalik, wanda yake daya ne daga sarakunan Banu Umayya wadanda suka fi iko. Duk da matsaloli da wahalhalun da suka addabi sarautar Banu Umayya a wancan zamanin wannan bai hana su aikata makida ga zuciyar shi’annan mai bugawa, watau Imam Bakir, ba. Hisham ya yi ishara ga barorinsa cewa su sanyawa Imam guba, da haka ne kuma ya cimma burinsa na hallaka mafi hadarin abokan gabansa.