• Farawa
  • Na Baya
  • 20 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 11367 / Gurzawa: 3073
Girma Girma Girma
Jagorancin Imam Sadik

Jagorancin Imam Sadik

Mawallafi:
Hausa

Jagorancin Imam Sadik (a.s)

Imam Sadik (a.s) ya dauki nauyin cigaba da wannan tafiya a cikin yanayi mai tsananin sarkakiya da wahala. Bore ya kunno kai ako ina a daular musulunci, hakimai sun shagaltu da tara kazamar dukiya alhali ga annoba da fari sun aukawa yanki mai yawa wanda ya hada da Kurasan da Irak. Masu mulki kuwa suna tursasawa da zalunci ba tare da rahama bako kankani, da haka suke jefa mutane cikin halin kaskanci da mika wuya. Kumagalibi hadarin masu shagaltuwa da ilmomin musulunci kamar fikihu da hadisi da tafsiri bai kasa na ‘yan siyasa da mahukunta ba.Alhali kuwa su ake tsammanin zamansu mafaka ga mutane. Yawa yawan wadannan malamaina kawata fatawowi saboda dadada wa sarki da hakimansa. Da yawa daga cikinsu suna shagaltar dakansu da ma mutane da mas’alolin da basu taka kara sun karya ba, suna ta da jayayyar da ba bakin komai take ba cikin mas’alolin ilmul kalam kuma babu abin da ya danganta ta da musulunci ko wahalhalun da al’umma ke ciki.

Nauyin da ya rataya a wuyan Imam Sadik (a.s) a wannan yanayi mai duhu shi ne abin da muka ambata kan sha’anin nauyin imamanci.A takaice shi ne bijiro da ingantaccen tunanin musulunci, watau bayyana musulunci kamar yanda ya zo cikin Alkur’anidasunnarMa’aiki( s.a.w.a) gami da yaki da dukkanin baude-baude da gurbatarwar jahiliyya mai bin son rai. Hakanan kuma da shirya dabarun kafa tsarin adalcin musulunci da kuma kare wannan tsarin yayin kafa shi.Duk wannan nauye-nauye guda biyu watau nauyin wanzar da tsarin tunani da nauyin tsarin siyasa suna matsayin wani hadari mai girma ne ga tsarin da yake mulki. Ba nauyin siyasa kadai yake tunzura fushin sarauta ba, a’a shi ma nauyin tsarin tunaniwanda yake jifa da baudaddun tunane-tunane da manufofin da sarki da masu wa’azinsa ke gabatar wa al’umma da sunan addini, yana fusata ta. Wannan ya nuna cewa aikin kyautata tunani abin fifitawa ne dominyana kawar da karkatarwa da sunan addini wacce tsarin sarauta ke dogaro da ita wajen wanzarda zaluncin da yake yi wa jama’a. Ta wata fuska kuma yanayin da ake cikinsa a shirye yake ya saurari tunanin shi’a maineman sauyi, domin yaki da talauci da danniya sabubba ne masu habaka ruhin sauyi, ga kuma share fage da ayyukan Imam Bakir (a.s) suka yi a yankuna dabam-dabam. Dabarar cimma manufar Imamanci a gameita ce yunkurin sauyin tauhidi irin na Imam Ali. Bukatunta su ne:-Na farko: Samarda wata jama’a wacce za ta dauki tunanin imamanci, ta yanda zai saje daita , sannan ta zama mai begen aiwatar da shi.

Na biyu: Samar da wata jama’a tsararriya mai jihadi da sadaukarwa. Shikansa cimma wadannan bukatu yana bukatar yada kiran gaskiya a sassan duniya da shirya zukata domin karbar tunanin musulunci mai ra’ayin sauyi a dukkanin wurare. Harila yau yana bukatar wani kiran daban wanda zai tanadi daidaiku masu sadaukarwa da fana’i, wadanda za su zama mambobin shirin tsare-tsaren kiran na sirri.Wannan shi ne sirrin wahalar kira bisa tafarkin imamancin gaskiya. Saboda kira mai dauke da sako, mai zimmar kawar da dagutu da fir’aunanci da jabberanci da dagawa da zalunci a cikin al’umma tare da cewa tana riko da ma’aunan musulunci wajen ayyukanta dole ne ta yi dogaro da zabin (irada) talakawa da karfinsu da imaninsu da nunarsu. Sabanin kiraye-kirayen da suke dauke da taken yaki da masu dagawa alhali su ma suna aikata irin ayyukan dagutai da azzalumai, basu lura da dokokin kyawawan dabi’u dana halin zaman jama’a. Irin wadannan kiraye-kiraye basu fuskantar wahalhalun da kira mai dauke da sako, mai manufa, take fuskanta. Wannan shine sirrin rashin tabbatar manufofin harakar Imamanci cikin gaggawa, shi ne kuma sirrin samun nasaranan take na harakokin da suka yi hannun riga da harakar imamanci, kamar ta Banu Abbas.

Yanayin da ake ciki da shirin da ayyukan imamin da ya gabata (Imam Bakir) bai shafi takwabi ba. A’a shiyana tsayawa ne ta hanyar suka mai tsanani, sawa’un da salon aikin gyaran tunani ko na tsare-tsare ko kuma ta wata fuskar dabam, da nufin kwankwasar azzalumai da yakar su. Anan Imam Bakir (a.s) yana karfafawa kan ma’anar yukurin da Imam Sadik zai yi saboda aiwatar da babban nauyi wajen fuskantar mulki mai ci, kuma ba ya karfafawa kan sakamakon da ka iya biyowa baya. Kai a wata riwayar ma maganarsa kusan tana yanke kaunar samun nasarar harakar imamanci ne a cikin wannan yanayin siyasar da ake ciki.Daga cikin riwayoyin da a cikin su Imam Bakir (a.s) yake karfafawa kan rawar da Imam Sadik (a.s) zai taka akwai abin da Abu Sabah Alkinani ya ruwaito, ya ce: “Abu Ja’afar ya dubi dansa Abu Abdillah sai ya ce: ‘Kana ganin wannan? Wannan yana cikin wadanda Allah Ta’ala ya ce (game dasu :Kuma muna nufin Mu yi falala ga wadanda aka raunanar a cikin kasa kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magada.[26]

La’alla wadannan fayyace-fayyacen Imam Bakir su ne suka yada tunanin yunkurin Imam Sadik (a.s) da halifancinsa a tsakanin ‘yan shi’a, ya kuma sanya sahabban Imam Bakir da Imamsadik( a.s) sauraron wata faraga daga lokaci zuwa lokaci. Akwai wata riwaya cikin Rijalna Shaikh Kashshi wacce a cikinta ana iya fahimtar wannan yanayi mai wanzuwa a tsakanin mabiya Ahlulbaiti a wancan lokacin. Ibn Miskan ya ruwaito daga Zurara cewa ya tambayi Abu Abdillah (a.s) batun wani mutum cikin abokanmuwanda yake buya saboda gudun tara. Yace : Allah ya kiyaye ka! Akwai wani mutum cikin abokanmu yana buya saboda gudun tara, idan wannan al’amari kusa yake zai hakura har ya fito tare da mai tsayawa, Idan kuma akwai jinkiri zai yi sulhu( da mahukunta ) saboda gudun tara. Sai Abu Abdillah (a.s) yace : Zai kasance. Sai Zurara yace : Zai kasance nan da shekara? Sai Abu Abdillah yace : Zai kasance insha’allahu. Sai Zurara yace : Zai kasance nan da shekara biyu? Sai Abu abdillah yace : Zai kasance insha’allahu. Sai Zurara ya fita, sai ya kwallafa ransakan cewa zai kasance nan da shekara biyu.Amma bai faru ba. Sai yace : Ban kasance ina ganin Jafar ba face ya fi haka sani.[27]

Kalamar ‘wannan al’amari’ a sanin mabiya Ahlulbaiti kinayace kan zamani mai zuwa wanda aka yi musu alkawarinsa, watau karbar ragamar mulki ko kuma tabbatar da abin da zai kusanta su da wannan, kamar juyin juya hali ta hanyar daukan makami.Kuma ‘Mai Tsayawa’ shi ne zai jagoranci wannan aikin.

A wata riwaya Hisham Ibn Salimwanda shi ma wani babba ne kuma sananne daga cikin shi’a, ya ambaci cewa Zurara ya ce da shi: “Ba zaka ga wani kan karagar shugabanci ba face Ja’afar.” Yace : Yayinda Abu Abdillah ya yi wafati sai na zo na ce masa (Zurara): Kana tuna labarin da ka bani? Na ambata masa shi,ina mai tsoron kada ya yi musun cewa ya fada mini. Sai ya ce: “Wallahi ni ban fadi waccar maganar ba face dama nawa ra’ayinne( watau dama ba ya ruwaito maganar Imam ba ne)”.

Daga jumlar abin da ya gabata muna fahimtar cewa a ra’ayin babansa dana jama’a Imam Sadik (a.s) shi ne mai tabbatar da burin imamanci da shi’anci. Kuma silsilar imamanci ta riga ta yi tanadinsa domin tabbatarda kokarin Imam Sajjad da ImamBakir( a.s) Kamar dai shi ne ya wajaba a kansa ya dawo da ginin hukumar Alawiyya da tsari irin na tauhidi,watau ya wajaba ya aiwatar da wani sabon yunkurin musulunci. Imamannan biyu da sauka gabata sun riga sun ci zango-zango masu wahala da kunci a kan wannan gwadabe, shi kuma sai ya ji da zangon karshe. Kamar yanda muka ambata, yanayi ya daidaita ga Imamkuma ya yi amfani da wannan dama wajen yukurin gabatar da sakonsa mai girma.

Tun lokacin da ya karbi nauyin shugabaci har zuwa wafatinsa, Imam ya dauki shekara talatin da ukuyana jihadi maras yankewa. Cikin wadannan shekarun yanayi ya kasance yana sa kyakkyawar fata, wani lokacin kuma matsin lamba yana hawa da kuma sauka;wani zubi ya dace da maslahar mazhabin Ahlulbaiti, wani zubin kuwa yanayin ya juya akasin hakan. Wani lokaci halinyana sa kyakkyawar fata, wani lokacin kuma matsin lamba yana tsanani, har sahabban Imam su zaci cewa dukkan buri ya tarwatse. A duk wadannan halaye ImamSadik( a.s) yana rike da ragamar jagoranci kyam tare da azama da jajircewa. Yana keta fagennan mai rudani, mai tattare da tsammani da kuma yanke kauna, ba ya damuwa da komai sai tafiyar da ke gaba yana wanzar da kokari da karfin gwiwa da imani wa mabiyansa domin kaiwa ga tsira.

A nan ya zama wajibi mu yi nuni da wani al’amari mai ban takaici wanda dukkan masu bincike kan rayuwar ImamSadik( a.s) suke fuskanta .

Wannan kuwa shi ne halin rashin tabbas wanda ya lullube shekarun farkon imamanciSadik( a.s) wadanda suka yi muni daidai da karshen zamanin Banu Umayya. A lokacin rayuwa ba ta san natsuwa ba tana kuma cike da aukuwar manya-manyan al’amura,muna iya fahimtar alamunsu cikin daruruwan riwayoyi. Saidai malaman tarihi da hadisi basu kawo mana labarin wannan lokacin a jere tare da sajewa da daganta wannan bayani da wancan ba. Saboda haka ya zama dole ga mai bincike ya yi dogaro da kuma lura da al’amura da suke baiyana cikin abinda yake karantawa (kara’in), ya lura da kungiyoyi da ra’ayoyi a game na wancan zamani sannan ya kwatanta ko wace riwaya da bayanan da ya riga ya sani domin ya ga abinfahimtar( mafhumi) abinda riwayar ta kunsa da rabe-raben ta.

La’alla daya daga dalilan wannan rikitarwa shi ne kasancewa harakar Imam da mabiyansa an yi ta cikin sirri, domin shirina siri wanda ya kafu bisa ingantattun ginshikai dole ne bayanan da suka dangance shi su wanzu cikin sirri da boyewa, kuma wajibi ne kada wanda yake waje da wannan shiri ya tsinkaye su.Wadannan bayanai ba su watsuwa sai bayan tabbatar harakar da kuma nasararta. Saboda haka ne muke samun cikakkun bayanai dalla-dallakan sadarwa ta sirri a harakar Abbasiyawa domin harakarsu ta yi nasara. Babu shakka da an kaddarawa harakar Ahlulbaiti kaiwa ga nasara da karbar ragamar mulki da a yau mun riski sirrin tsare-tsarenta masu fadi.

Akwai wani dalilin daban wanda zai iya janyo wannan rashin baiyana dangane da harakar Ahlulbaiti, cewa murubuta tarihi, bisa al’ada suna rubuta abin da yake dadada wa sarakuna ne. Domin haka muke ganin bayanai filla-filla kan rayuwar halifofi da wasanninsu da hirarrakinsu da wuraren holewarsu amma bamu ganin bayanan kirki kan masu neman juyi da wadanda aka zalunta da wadanda aka murkushe. Domin samun irin wadannan bayanan mai bin diddigina bukatar dogon bincike da kirkado da tsananin biyawa. Amma rayuwar halifofi bayani ne tanadadde, tsuntsu dagasama gasashshe, yana kawo yardarsu da tarin kyaututtuka.

Marubuta tarihi masu rusnawa ga halifofin Abbasiyawa sun cigaba da rubutu bisa wannan hanya na tsawon shekara dari biyar bayan rayuwar Imam Sadik (a.s). Saboda haka ba za mu yi tsammanin samun wani abin kirkina bayanai kan rayuwar Imam Sadik (a.s) ba, da ma na ko wani imamin shi’a cikin wadannan littafai.

Hanyar kadai da za ta iya shiryar da mukan layin da rayuwar Imam Sadik ta duka ita ce gano muhimman alamu na rayuwar Imam ta hanyar ka’idoji, a game, na salon tunanin Imam da dabi’unsa. Kana mu yi bincikekan abubuwan tarihi da suka danganci wannan rayuwa da hujjojin tarihi da suke warwatse da kuma irin wadancan abubuwa masu dangantaka da rayuwar Imam wadanda ba na tarihi ba har mu kai ga rarrabewar al’amarin filla-filla.