Alamomi a Rayuwar Imam Sadik (a.s)
Muhimman alamomi wadanda suke fitattu a rayuwar Imam Sadik (a.s) idan muka lura da mahangar bahasinmu, suna iya tattaruwa cikin wadannan:-
1. Bayyana sha’anin imamanci da kira zuwa gare shi.
2. Sharhikan
hukunce-hukunce da tafsirin Alkur’ani dai-dai da abin da mazhabin Ahlulbaiti ya gada daga Manzon Allah (s.a.w.a)
3.kafa
tsari na sirri kan manufa da kuma siyasa.
Hanyar da bahasinmu zai daukaita
ce yin bincike kan kowani daya daga wadannan alamomi sannan daga karshe mu sanya wani jadawalin ayyukan Imam (a.s) Duk wannan zai kasance da salon masu tarihi ba na masu hadisi ba, gwargwadon iyawarmu.
1. Bayyana sha’anin imamanci da kuma yin kira zuwa gare shi.
Wannan maudu’iyana
daukar masayin mafi bayyanan alamomin kiran imaman Ahlulbaiti (a.s) tun shekarun farko bayan kaurar Annabin rahama (s.a.w.a). Mas’alar tabbatar da imamancin Ahlulbaitiita
ce al’amari na kan gaba wajen kira a dukkan zamunnan imamanci.Muna iya ganin wannan mas’alar a yunkurin Imam Hussain ibn Ali (a.s) da kuma yunkurin ‘ya‘yan imaman Ahlulbaiti kamar Zaid ibn Ali.
Kirar Imam Sadikita
ma ba ta fita daga wanna fagen ba.
Kafin mu bijiro da hujjojikan
wannan maudu’i ya zama wajibi tukun mu fara da bayanin ma’anar (imama) ‘imamanci’ a tunanin musulunci.Kuma mene ne kira zuwa ga imamanci?
Kalmar imamancia
asalinta tana nufin jagoranci sake ba kaidi. A tunanin musulunci kuwagalibi
ana amfani da ita ne a kebance. Wannan wurin kuwa shi ne jagoranci a sha’anin halin zaman jama’a walau wajen tsarin tunani neko
kuwa tsarin siyasa.
Kalmomin da aka tsago daga ita kalmar ‘imama’kamar su ‘imam’ da ‘a’imma,’ duk inda suke a cikin Alkur’ani abin da ake nufi da su shi ne kebantaciyar ma’anarsu watau jagorancin al’umma. A wadansu wurare abin da ake nufi daita
shi ne jagorancin tunani a wadansu kuwa jagorancin siyasa ko kuma biyun gaba daya.
Bayan kaurar Ma’aiki da bayyanar rarrabuwar salon tunani da siyasa tsakanin jama’ar musulmi,kalmar
imamanci, da imama, ta dauki wani kebantaccen masayi, saboda mas’alar jagorancin siyasa ita ce jigon sassabawar musulmi. Da farko,kalmar
tana da manufar siyasa fiye da kowace manufa wacce ba ta siyasa ba. Daga bisani wadansu ma’anonin sun riske ta sannu a hankali, har aka wayi gari a karnina
biyu mas’alar ‘imama’ ta zamo mas’ala mafi muhimmanci wajen makarantan ilmul kalam masu baiyana ra’ayoyinsu kan sha’anin sharuddan imam da sifofinsa, watau sharuddan mai hukunci a al’ummnar musulunci; wannan kuwa shi ne ma’anar imamanci a siyasance.
A kan imami kuma cewa ya yi:-
“(Shi) tauraruwa mai shiryarwa ne, ruwan dadi ne, matsera daga halaka ne, girgije mai kawo ruwa ne, mafakar bayi a lokacin bala’i ne, amintaccen Allah kan halitarsa ne, hujjarsa bisa bayinsa ne, halifansa a kasashe ne, mai kira zuwa ga Allah, mai tsare hurumin Allah ne, daidaiton addini ne, daukakar musulmi ne, fushin munafukai ne, kuma halakan kafirai ne”[29]
Duk nauye-nauye da mas’uliyyar da Annabi ya gudanar, Ali (a.s) da imamai daga ‘ya’yansa suna daukarsu.[
30]
A wata riwaya daga Imam Sadik (a.s) akwai ta’kidikan
biyayya ga ‘wasiyyai’. Riwayar ta fayyace cewa wasiyyan su ne wadanda Alkur’ani ya kira da lakabin ululamri .[
31]
Daruruwan riwayoyi da ke rarrabe cikin babi daban-daban suna fayyace mana cewa manufar imam da imamanci a tunanin shi’a ba komai bace
face jagoranci da gudanarwa na al’amuran musulmar al’umma kuma imaman Ahlulabaiti (a.s) basu takaita wajen da’awar imamanci kan abin da ya shafi tunani da ma’nawiyya kadai ba, a’a suna kira da cewa hukuma ita ma tasu ce. Kiransu mai fadi kamar haka mai kuma tattara dukkan sassa hakika kirace
ta wata harakar siyasa da kuma soji wadda take da zimmar karbar shugabanci.
Wannan batu ya cigaba
da zama boyayye ga masu bincike a zamunnan da suka biyo baya amma a fahimtar sahabban imamai da wadanda suka yi zamani da su batun yana daga mafi bayyanannun al’amura. A cikin daya daga kasidunsa na Hashimiyyat, Kumait yana sifanta imaman Ahlulbaiti da cewa su ne shugabanni masu jagorantar mutane ta wata hanya wacce ta saba gaba daya da hanyar da azzaluman mahukunta suka bi, inda suke mu’amala da mutane tamkar dabbobi.[
32]
Mu koma ga maudu’in asali cewa kashin baya a kiran Imam Sadik (a.s) da sauran imaman Ahlulbaiti (a.s) shi ne batun imamanci.
A tare da mu akwai riwayoyi masu karfafa juna wadanda suke tabbatar da wannan batuna
tarihi.Ana nakalto su a bayyane tare kuma da wannan fayyacewa daga Imam Sadik (a.s) inda ya yi da’awar imamanci.
Za mu bayyana nan gaba cewa lokacin da Imam yake bayar da sanarwar wannan kiran nasa, yana ganin kansa cikin wani mataki na jihadi mai bukatar ya yi watsi da mahukuntan zamaninsa, ta hanya bayyananna kuma kai tsaye, sannan kuma ya sanar cewa shi ne ma’abocin hakki na hakika, ma’abocin shugabanci (wilaya) da kuma imamanci. Irin wannan fitowa, bisa al’ada, tana nufinan
ketare sauran matakan jihadi wadanda suke gabatarta tare da nasara. Dole ne ya kasance farkawa a siyasance da yanayin zaman jama’a ta zama tuni ta sami goyon baya mai fadi, ana jin shirin mutane ya yi karfi a ko wani wuri, shimfida kan manufa ta kankama ga wani adadin mutane mai dama, sannan jama’a masu yawa sun yi imani da wajibcin kafa hukumar gaskiya da adalci, sannan daga karshe, jagoran ya zama ya riga ya dauki kuduri mai karfi akan wannan fito-na-fito mai tsanani. Idan wadannan sharuddan basu cika ba,sanarda
imamancin wani mutum ayyananne da jagorancin sa na gaskiya ga al’umma abu ne mai tattare da ujula ba kuma cimma manufa tare da shi.
Wata mas’alar da ba makawa ga karfafawa game da ita a wannan bayanin ita ce, a wadansu lokutan Imam Sadik (a.s) ba ya takaita kan tabbatar da imamancinsa kadai, yana ma ambaton sunayen imaman gaskiya magabatansa tare da ambaton nasa sunan, watau, bisa hakika, yana gabatar da silsilar imaman Ahlulbaiti tare da sadarwa, daya bayan daya, ta yanda yayyankewa ko rarrabewa ba ya yiwu wa.
Wannna matsayinyana
nuni da dangantakar da ke akwai tsakanin jihadin imaman Ahlulbaiti (a.s) da dorewarsa tun daga zamunnan da suka gabata har zuwa lokacin Imam Sadik (a.s). Imam Sadik (a.s) yana bada sanarwar imamancinsa a matsayin shi na wani sakamakon da ba makawa zai biyo bayan imamancin magabatansa, kuma da wannan yake bayyana tushen wanna kiran da zurfin kafuwarta a tarihin sakon musulunci, da dangantakarta da ma’abocin kiran, Manzon mai girma, mafificin tsira da aminci ya tabbata gare shi. Bari mu kawo wasu samfurin kiran Imam:-
Riwayar Amru ibn Abi Mikdamita
ce mafi ban-sha’awa a wannan babin, tana kuma sauwara wani yanayi mai ban mamaki.
A ranartara
ga watan Zulhijja, yayin da mahajjata suka taru a Arfa domin tsayuwa gashi sun riga sun hallara a wannan wuri daga ko ina: kamar daga karshen kasar Kurasan har zuwa gabar tekun Atlantika, a wannan wuri mai hadarin gaske, inda kira a cikinsa tana iya aika amon ta zuwa nisan duniyar musulunci.Imam ya hadu da wannan taron jama’u masu yawa saboda ya isar musu da kalmarsa.
Mai ruwaya yace:-
na ga Imam ya tsaya cikin jama’an nan, ya daga murya da kyau domin ya isa kunnuwar mahalarta sannan daga bisani ya kai ga kunnuwan talikai, yana kira kamar haka:-“Ya ku mutane ! Lallai Manzon Allah ya kasance shi ne shugaba (imam), sannan Ali ibn Abi Talib, sannan Hassan, sannan Hussaini, sannan Ali ibn Hussain, sannan Muhammad Ibn Ali, sannan ……..” Yana wannan kiran sau uku ga wadanda suke gabansa, da gefensa na dama, da gefensa na hagu da kuma bayansa, kira goma-sha biyu ke nan”[
33]
A wata riwayar daga Abu Sabah Alkinani cewa Imam Sadik (a.s) ya sifantakansa
da kuma imaman shi’a da cewa ganima (anfal) da zababben dukiya tasu ce.
Daga Abi Sabah ya ce:-
Abu Abdillah ( a.s) ya ce da ni: “Ya Aba Sabah, mu mutane ne wadanda Allah ya farlanta biyayya gare mu. Ganima tamu ce, zababben dukiya namu ne, mu ne matabbata cikin sani kuma mu ne wadanda aka yi wa hasada wadannan da Allah ya fade su cikin littafinsa”[
34]
Safwulmali
, zababbar dukiya, shi ne kayayyakin da suke da kima matuka daga cikin ganimar yaki. Da ba’a rabawa
mayaka irin wadannan kayayyakin kamar yanda ake raba musu sauran dukiyar ganima saboda kada a fifita wani da zababben abu, gudun kada wannan ya zamewa wani wata daraja ta karya. Maimakon haka ana barin irin wadannan kayayyaki ne a hannun shugaban musulunci ya yi amfani da su wajen abin da zai tabbabtar da maslahar musulmigaba
daya. Azzaluman mahukunta su kan dauki irin wannan dukiya su kebanta da ita ta hanyarkwace(
gasabi). Imamyana
fayyacewa kan cewa zababbar dukiya, wajibi ta zama tasu, haka nan ganima. Wannanyana
nufin cewa Imam yana bayyana kansa a sarari a matsayin shugaban musulmi a ganin shari’a, wanda nauyin jujjuya wadannan dukiyoyi dai-dai da abin da yake ganin zai tabbatar da maslahar al’umma a kansa yake.
A wani hadisin Imam Sadik (a.s)yana
ambaton sunayen imamai magabatansa daya bayan daya, yana ba da shaidar imamancinsu da wajib cin biyayya gare su. Yayin da ya isokan
sunansa sai ya yi shiru, masu saurare kuma sun sani sarai cewa gadon ilmi da hikima bayan Imam Bakir (a.s) a wajen Imam Sadik (a.s) yake. Kuma da wannan Imam (a.s) yake bayyan hakkinsana
jagorantar al’umma, yana bayyana shi da wani salo mai danganta hakkin nasa da kakansa Ali ibn Abi Talib (a.s). Cikin wadansu babi-babina
littafin Alhujja cikin Alkafi da ma cikin juz’i na arba’in da bakwai na Biharul Anwar akwai irin wadannan hadisai da yawa, suna fayyacewa, wani zubin kuwa suna kinaya kan da’awar imamanci da kuma kira gare ta.
Domin tabbatar da wannan batuna
tarihi, akwai hujjoji ko shaidu da suke tabbatar da samuwar wani tsararren shirin sadarwa da yake gudanar da kiran Imam (a.s) a ko ina cikin sassan duniyar musulunci. Mayawaitan hujjoji da ke akwai akan
wannan batu sun sa samuwar wannan shirin sadarwa wani al’amari ne yankakke ba wani shakka a kansa. Wadannan shaidun sun yi yawa da karfin da ana iya kafa hujja da su akan
wannan maudu’i namu, hujja tabbatatta, ko da ba’a sami sahihin hadisi ko guda ba kan wannan batu. Mu dubi wadannan tabbatattun al’amuran tarihin:-
1.Akwai
wata tsararrar alaka ta tunani da ta abin da ya shafi dukiya tsakanin imamai (a.s) da mabiyansu, kuma an kasance ana daukar dukiyoyi daga sassa dabam dabam na duniya ana kaiwa Madina kazalika da tambayoyin addini mayawaita.
2.Fadadar
fagen da ke wilaya ga mutanen gidan Manzo (s.a.w.a) musamman a yankunan duniyar musulunci wadanda suke masu saurin daukar dumi.
3.Tattaruwar
jama’a masana hadisi da maruwaita Kurasanawa da Sistanawa da Kufawa da Basarawa da Yamanawa da Misrawa gaban Imam (a.s).
Shin wannan al’amariwanda
sashensa yake munasaba da sajewa da sashe ya faru ne kwatsam ba tare da an shirya shi ba?
Wajibi ne mu yikari
da cewa wannan al’amari ya tabbata ne karkashin ikon siyasa wanda ya yi da gaske wajen watsi hatta da sunan Ali (a.s) kai da ma zagin Ali a kan mimbarori da wanzar da nau’o’in dira da razanarwa kan mabiyansa. To a irin wannan halin, yaya aka iya samar da mabiya mayawaita masu wilaya ga Ahlulbaiti daga cikin talakawa suna taka dubban milamilai saboda su kai kasar Hijaz da birnin Madina da zimmar daukar karatu gaban imaman Ahlulbaiti (a.s) da kuma koyon tunanin musulunci a kan rayuwar dai-daiku da ta jama’a da kuma tattaunawa da su kan batutuwa mayawaita da kuma mas’alolin tawaye wa yanayin barna da fasadi, ko kuma kamar yanda riwayoyi suke kiran al’amarin-mas’alolin ‘tsayawa’ da ‘ficewa’ daga da’a ga azzalumai )?!!
Idan da ace masu kiran Ahlulbaiti suna takaita bayanansu nekan
ilmin imamai (a.s) da zuhudunsu, to me ya sa tattaunawar wadannan mabiyan a kullum take kan batun tawaye ta hanyar daukar makami? Shin wannan baya nuni da samuwar wani tsararren shirin sadarwa saboda kira zuwa imamancin Ahlulbaiti (a.s) da cikakkiyar ma’anar imamanci, watau tsrin tunani dana
siyasa?
Anan
tambaya za ta zo kan cewa dalilin kawaicin tarihi dangane da samuwar irin wannan tsararren shirin sadarwa a kiran Ahlulbaiti (a.s). Shin mene ne yasa
tarihi bai ambaci komai kan wannan batu a fayyace ba? Amsaita
ce abin nan da muka yi nuni da shi a baya. Ta yiwu sahabban imamai sun lizimci ka’idarnan
ta hikima wajen haraka wanda aka sani da takiyya, wanda take ba ta bada duk wani bare a tsarin imama damar kutsa kai. Haka kuma mai yiwuwa ne tarihi baice
komai ba saboda rashin kaiwa harakar jihadi ta shi’a ga tabbatar da manufofinta da karbar ragamar mulki. Da ace
Banu Abbas basu hau karagar mulki ba da kuwa, ba shakka duk bayanen aikace-aikacensu na sirri da muhimman batutuwan kiransu mai dadi da mara dadi da ya takaita ga zukatansu kadai, ba tare da wani ya san su ba kuma da tarihi bai rubuta komai a kansu ba.
Duk da haka riwayoyin da suke fayyacewa gwargwadokan
samuwar mayalwacin kira zuwa ga imamancin Ahlulbaiti (a.s) ba kadan suke ba. Za mu hakura da guda daya mai cewa:-
Wani mutum daga mutanen Kufa ya zo Kurasan, sai ya kira mutane zuwa wilayar Jafar ibn Muhammad (a.s).
Wata jama’a sai ta bi shi ta amsa kiransa.
wata
kuma ta musa masa ta yi inkari wata kuma ta dakata ta yi tsantseni. Sannan riyawar tace
: Sai mutum daya daga kowace jama’a ya tafo wa Imam Abu Abdillahi (a.s).Mai magana daga cikinsu shi ne wannan da ya dakata ya yi tsantsenin.
Sai yace :
Allah ya kiyaye ka, wani mutum ya zo mana daga mutanen Kufa ya kira mutane zuwa biyayya da wilaya gare ka sai wasu mutane suka amsa masa, wasu suka yi inkari wasu kuma suka ya tsantseni suka dakata. Imam (a.s) ya ce:-
“Daga cikin ukun wacce kake ciki? “Ya ce:-
Daga jama’ar da ta yi tsantseni ta dakata. Yace
: To ina tsantsenin ka yake daren kaza da kaza? (sai
ya tunatar da shi kasawarsa a wani hali na sha’awa) sai mutumin ya yi shakka. [35]
Kamar yanda ka ji, mai kiran daga mutane Kufa yake, kirannasa
kuwa zuwa imamancin Ja’afar ibn Muhammad Al Sadik (a.s) da wilayarsa da kuma biyayya gare shi ne.
Akwai wadansu hujjoji daban masu bayyana abin da kiran imaman Ahlulbaiti (a.s) da shi’arsukan
imamanci ya kunsa. Jayayya tsakaninsu da abokan hamayyarsuna
siyasa (Umayyawa da Abbasiyawa) ta bijiro da shi. Wani lokaci ana wannan jayayya ne ta hanyar kafa hujja a fagen addini da ilmul kalam a wasu lokatan kuma tana daukar salon adabi mai zurfi ta hanyar wake. Duk jayayyar ana yin ta nekan
tabbatar da cancantar imamanci a siyasance da shugabanci ga imaman Ahlulbaiti (a.s) da gwagwarmaya da masu kankamewa kan karagar hukumar musulmi bisa zalunci da kwace.Saboda yin zamani daya da harakar Abbasiyawa da samun nasararta, lokacin Imam Sadik (a.s) ya kasance a cike yake da irin wannan jayayya da mujadala.
Mawakan Abbasiyawa suna kokarin tabbatar da cancantar shugabanci ga Abbasiyawa suna dogaro da hujjojinda, bisa al’ada, masu kwadayin mulki da kuma masu kankamo da karagar sarauta suke gabatarwa.
Mawakan shi’a kuwa sukan fuskance su suna gugar wadancan hujjojin suna masu kafa hujja kan fandarar da mulkin Abbasiyawa ya yi daga mandikin musulunci( dalilan
da ya dogara a kansu ) wanda yana kafe ne bisa yarfar da zalunci da aikata laifi da ha’intar hakkokin al’ummar musulunci.
Mukabala ta hanyar wake tsakanin Abbasiyawa da Alawiyyawa tana da muhimmanci anan
saboda irin muhimmiyar rawar da wake ke takawa a wancan lokacin wajen bayyana abin da rai ya kunsa da tunane-tunane saboda kuma irin tsarin da yake da shi kan mabiya cikin talakawa. Ma’abocin littafin “Abbasiyawan Farko”yana
ambatar rawar da adabi ya taka a karnin farko da na biyu. Yace
:-
“Adabi ya kasance yana tasiri a zukata yana kokarin samun goyon bayan jama’a da karkatarsu ga wannan kungiya ko waccar, mawaka da masu jawabi matsayinsu irin wanda jaridu suke da shi ne ayau .
Ko wannensu yana bayyana wani ra’ayin siyasa ne yana kuma kare wata kungiya ayyananna, yana bijiro da dalilin ingancikin kirar da yake yi daya bayan daya yana rushe ra’ayoyin abokan hamayya da magana maiu tasiri da salo mai fasaha”[
36]
Mawakan fadar Abbasiyawa sun kasance suna kokarin tabbatar da cancantar Abbasiyawa ga halifanci da hujjar alakarsu da Annabi ta hanyar ‘ya’yan baffa, sun kafa hujjakan
hakan da cewa gado ba ya riskar ‘ya’yan diya tare da samuwar baffanu. Saboda haka halifanci a bayan Annabi hakkin Abbas, baffan Annabi ne, a bayansa kuma,na
‘ya’yansa ne, watau yayan Abbas. Marwan ibn Abi Hafsa ya ce:- Kaka zai yiwu, ai bai yiwuwa, Gadon baffanu a hannun dan diya Abban ibn Abdilhamid Lahiki ya ce:- Ya’yan Abbas su ke da gado nai, Baffa ga dan baffa ai hijjabi ne Mabiya Ahlulabaiti sai suka zabura saboda ji a jika cewa wannan furuci zalunci ne, suka yi raddi kan wadancan hujjoji da irin tunanin (mandiki) da aka yi amfani da shi a wani lokaci, a wani zubin kuma su kan dauki wani mandikin dabam, daboda kafa hujja kan hakkin imaman Ahlulbaiti na imamanci. Daga wannan akwai kafa hujja da hadisin Gadir kummi kamar zancen Sayyid Himyari, inda ya ce:- Wanda nake a gare shi shugaba, Wannan tabbas a gare shi shugaba Amma sun ki yarda sun ki gamsuwa Muhammad ibn Yahya ibn Abi Murra Taglibi ya yi raddi kan hujjar mawakin Abbasiyawa wanda ya yi magana kan gadon baffanu, ya ce:- Me zai hana, kai hakika hakku ne, Rabon baffa a tattara shi wa dan diya Rabi daga dukiya na diyarsa ne, Shi baffa ya tai gida ba ko daya Kai sakakke me ya kai ka batunta ne? Ba don kisa ba bai ruku’i ko daya Du’bal yana ganin cewa duk ma masifun da suka auka wa Ahlulbaiti (a.s) ba don komai ba ne sai domin sun gaji Annabi, sai masu hadama suka yi rub da ciki kan wannan gadon kuma suka cutar da wanda shi ke da hakkin imamancin. Gadon Ma’aiki ya lahanta madaukaka, Mutuwa, tsoro wawasonsu suke Kurayen Umayya su kira su azazzala, Tuttudar kunci, da masifu kansu ne Banu Abbasin dinu su barnata, Ha’inci, zalunci, halinsu ne Wai shi Rashidu saboda shiriya tasa Mamun, Amin ka ga fa nasu ne Shiriya! Wanga bai tsare hakki ko daya Amincin biyun zagon ga Islama ne Ba abu ne mawuyaci ba ga mai bincike a kan farkon zamanin Abbasiyawa samun daruruwan misalai kan muhawarori da mukabalar siyasa wadanda suka kai yawan wake-waken da aka yi kan wannan batu. Mawakan shi’a da abokan hamayyarsu sukan
kafa hujjoji ne kan kiran da kowannensu yake yi.Ba shi da muhimanci mu san ingancin hujjojin da ake kafawa a wannan jayayya, abin da yake da muhimmanci shi ne mu gane ginshikin jayayyar da ake yi da kuma hakkin da sassan biyun ke da’awarsa.
Akwai wani hakkin dako
wani sashe yake da’awa wannan kuwa shi ne gadar Manzon Allah (s.w.a) wajen mulki da jagorancin musulmi.
Jayayyar tsakanin sashen Alawiyawa dana
Abbasiyawa ba kan gadar tadodi da dabi’u na gari da ma’nawiyya ko tsarin tunani irin na Annabi (s.a.w.a) ba ne. Ba wai ana sassabawa kan wane ne ya cancanci gadon wata tada ba ne, domin wadannan tadodi ba wani hakki ne da bangare biyun za su yi sa-in-sa a kai ba. Jayayyardai
a kan wani hakki ne wanda sassan biyu suke da’awarsa. Kuma mun ji yanda mawaka a zamanin Imam Sadik (a.s) suke kare hakkin imamina
jagorancin musulmar al’umman nan ma na mulkar jama’ar musulunci.Suna kuma kutsawa cikin yaki da wadanda basu da cancantar mulkar musulmi.
Akwai shaidu masu yawakan
wannan batu a wake-waken karni na biyu bayan hijjira.
Kafin mu rufe wannan fasali ya dace mu yi nuni da wani salon kafa hujjan dabanwanda
kuwa shi ne salon wasika.Wadannan wasikun kafa hujja, a wani gefen, suna kunshe da bayanan manufofin kungiyoyi a sarari ba da wata rikitarwa ba.
Ta wani gefen kuwa sunajan
hankalin talakawa bayan yaduwar manufar bayanan. Kazalika ana samun tasiri mai karfikan
mataimaka da kuma abokan hamayya.Za mu ambaci wasikar da Muhammad ibn Abdillah ibn Hassan, Nafsi Zakiyya, ya aikewa Mansur sarkin Abbasiyawa.
Wannan Ba’alawe mai neman juyi yana fayyacewa gaba gadi cewa yana fafutukar kwabe halifanci daga hannun abokin hamayyarsa domin ya kasanse a hannun ‘ya’yan Ali (a.s), ya ce:-
“Lallai mahaifinmu Ali ya kasance shi ne wasiyyi kuma shi ne imami, to ta yaya kuka gaji shugabancinsa alhali ‘yayansa suna raye?”[37]
Ga alama Ba’alawen ya kawo wannan hujjan ne saboda raddikan
kafa hujja da Abbasiyawa suka yi kan gadar halifanci, domin banu Abbas ba su mallaki wata hujja ba face wannan da’awar gadon.Nafsi zakkiya ya yi haka ne domin ya toshe musu duk wata kafa da irin nasu mandikin (salon hujja).
Ana iya lura a kalmominsa yanda yake karfafawakan
imammanci kana ya karfafa kan yanayin kiran Gidan Ali wanda wannan mai neman juyin yake wakilta a wannan jayayya.
2. Sharhikan
hukunce-hukunce da tafsirin Alkur’ani dai-dai da abin da mazhabin Ahlulbaiti (a.s) ya gada daga Manzon Allah (s.a.w.a).
Wannan aikin shi ma ana iya ganinsa a rayuwar Imam Sadik (a.s) fiye da yanda ake iya ganinsa
a rayuwar sauran imaman Ahlulbaiti (a.s) abin da ma ya sanya ake kiran fikihun shi’a da sunan Fikhun Ja’fari kenan. Hatta masu rintsa idokan
ayyukan Imam Sadik na siyasa sun hadu kan cewa Imam ya kasance yana gudanar da daya daga cikin mafi girman makarantun fikihu a zamaninsa, idan ma ba mafi girmansu ba. Abin da bai gushe bayana
lullube ga barin idanun mafi yawan masu bincike kan rayuwar Imam shi ne ma’ana ta siyasa da ta gwagwarmaya wadanda irin wadannan ayyukan Imam suke dauke da shi.Wannan shi za mu kawo a yanzu.
Da farko yazama
wajibi mu ambata cewa mukamin halifanci a musulunci yana da wadansu sifofin da suke sanya shugaba ya banbanta da shugabanni a wadansu tsare-tsaren shugabanci na daban. Shi halifanci ba wai tsarin siyasa ne kadai ba a’a, shi tsari nena
siyasa da addini a gwame. Baiwa shugaban musulunci lakabin halifayana
karkafa wannan batu: shi halifan Manzon Allah (s.a.w.a) ne a duk wani aikin da Manzo yake aiwatarwa ga jama’a wa lau nauyin da ya shafi addini ne ko kuwa na jagorancin siyasa.
Shi halifa a musulunci yanan dauke da mas’u’liyyar siyasa da ta addinigaba
daya. Wannan tabbataccen al’amari yasa
halifofin da suka zo bayan na farko, wadanda rabonsu a cikin ilmomi addini ya yi karanci ainun, ko kuwa basu da wani rabo sam, ya sanya su rufe wannan nakasu ta hanyar malaman addini masu aikata musu abin da suke so. Sai suka baiwa fukaha’u da malaman tafsiri dana
hadisi aiki a fada saboda tsarinsu na shugabanci ya tara sassan nan biyu: na addini da na siyasa.
Wata fa’idar samuwar masu wa’azin sarki a tsarin shugabanci,ita
ce: azzalumin shugaba mai kama karya, a duk lokacin da ya so, yana iya canja wa hukunce-hukuncen addini fuska ko kuma ya musanya su dai-dai da bukatunsa. Wadancan ma’aikata, malaman fada, su suke aiwatar da wannan domin dadadawa
masu azurta su.Suna yin haka ne karkashin rigar istinbadi da ijtihadi mai rudin jama’a.
Mawallafa da marubuta tarihi daga magabata sunambato
mana misalan da kare ba zai ci ba kan kirkirar hadisai da tafsiri da ra’ayi inda ake ganin hannun ikon siyasa a sarari. Za mu yi nuni da wani abu akai anan
gaba. Wannan al’amari wanda dafarko(
har zuwa karshen karnin farko bayan hijira) ya dauki salon kirkirar riwaya ko hadisi, sannu a hankali ya dauki matsayin fatawa. Daboda haka ne a karshen zamanin Banu Umayya da farkonna
Banu Abbas muke ganin bayyanar fukaha’u masu yawa suna amfani da hanyoyin ka’idojin istinbadi masu rauni domin su kafa dokoki dai-dai da zabinsu wanda a kashin gaskiya zabin tsarin da yake shugabanci ne.A fagen tafsirin Alkur’an ma, dai-dai wannan aiki aka zartar.
Tafsiri da ra’ayi,galibi
, ya sa gaba wajen bayar da fahimce-fahimce wa musulunci, wadanda basu dogara da komai ba face zabin mai fassara da son ransa, wanda ba kome na ne illa son ran tsarin da yake shugabanci.
Wannan shi ne musabbabin rabuwar ilmomin musulunci:na
fkihy da hadisi da tafsiri, tun zamunan na farko, zuwa ra’ayoyi biyu.
Ra’ayin Farko:-
Ra’ayin da ke da alaka da tsarin azzulumar hukuma mai kwace. Yana bambata dadayan
wajen sadaukar da gaskiya domin tabbatar da ‘maslaha’ wacee bisa hakika maslahar tsarin da ke shugabanci ne. Daga sifofin wannan ra’ayin har wala yau akwai baudar da hukunce-hukuncen Allah domin, ladan ‘yan dirhamomi.
Ra’ayin na Biyu:-
Ra’ayi dan asali amintacce wanda ba ya ganin akwai wata maslaha mai daraja da daukaka da ta wuce bayyana ingantattun hukunce-hukuncen Ubangiji. Wannan ra’ayi ya kasance,ko
an ki ko an so, yana cin karo da tsarin da yake shugabanci da kuma masu wa’azin fada, a duk wani taku da ya yi. Saboda haka tun farkon al’amari ya dauki mafuskanta irin ta talakawa tare da taka tsan- tsan da kiyayewa.
Fahimtar wannan zaisa
mu gane da kyau cewa sabawan Fikihun Ja’afar da fukaha’un sarauta a zamanin Imam Sadik ba wai sabawa ce ta tunani da akida kadai ba, a’a ta hada har da abin da ya kunsa na hari irin wanda abokin hamayya yake yi.
Mafi muhimmanci daga kusurwowin wannan abin da ya kunsa shi ne tabbatar da cewa tsarin da ke shugabanci fanko ne kawaiwanda
ya rasa dukkan ma’anonin addini, ga kuma gajiyawarsa wajen gudanar da al’amuran tunani ga al’umma.Ko
kuma mu ce rashin cancantarsa hawa mukamin “halifanci”. Wata kusurwaita
ce ayyana wuraren da aka baude cikin fikihun sarauta, wadannan baude-baude da aka gina kan tunanin “maslaha” wajen bayanin hukunce-hukuncen fikihu da sassautarwar malaman fikihu ga tsarin da ke shugabanci. Imam Sadik (a.s), da ayyukansana
karantarwa da kuma sabar nauyin bayyana hukunce-hukuncen fikihu da ilmomin musulunci da tafsirin Alkur’ani ta hanyar da ta saba da ta masu wa’azin fada, hakika, a’aikace, ya dauki matsayin hamayya da tsarin da ke mulki. Da wannan aikin, Imam ya iya watsi da duk tsarin sarauta a addini da fikihuwanda
wani bangare ne na hukumar halifofi, ya kuma tube wa tsarin da ke mulki duk wata rigar addini.
Ba mu da wani tabbataceen isnadi mai bayyana lurar tsarin Umayyawa da wannan janibin hamayya,wanda
Imam Sadik (a.s) ya aiwatar a fagen ilmi da fikihu. Saidai
abin da aka fi tsammani shi ne tsarin Abbasiyawa mai mulki-----musamman lokacin Mansur wanda yake mai wayo da gogewa da fahimtar halayyar duniya, abubuwan da ya koya a lokacin dambarwar siyasa mai tsawo sakaninsa da mulkin Umayyawa kafin shi kansa ya sami mulkin--wannan tsarin nasu yana kiyaye mas’alolin masu wuyar fahimta da ke tattare da ayyukan gidan Ali. Kuma tsarin Abbasiyawa mai mulkiyana
fahimtar muhimmiyar rawar da wancan aikin ulmi zai iya takawa ta bayan fage.
Barazana da kuntatawa da matsin lamba wadanda suke tattare da ayyukan Imam Sadik (a.s)na
ilmantarwa wadanda kuma riwayoyi masu yawa na tarihi ke nakalto mana, sakamakon wannan luran ne da kasancewar mas’alar mai hadari ce. Kazalika muhimmancin da Mansur yabayar
wajen tara mashahuran fukaha’u daga Hijaz da Irak a helikwatarsa, kamar dai yanda nassoshin tarihi mayawaita suke nunawa, shi ma ya samo asali ne daga wancan lurar da ya yi.
A magarsa da koyarwarsa ga sahabbansa da mukarrabansa, Imam (a.s)yana
kafa hujja da “yanayin holoko da jahilci na halifofi” kan cewa a ra’ayin musulunci basu cancantar shugabanci. Ana iya ganin wannan sigar sukakan
tsari mai mulki a sarari da fayyacewa a darusansa na fikihu.
An ruwaito zancensa (a.s):- “Mu mutane ne wadanda Allah ua farlanta biyayya gare mu, kuma kuna koyi da wanda ba’a yi wa mutane hanzari saboda jahilcinsa”[
38]
Abin nufi shi ne mutane sun baude saboda jahilcin mahukuntansu da shugabanninsu, sun dauki hata wanya bata Allah ba.
Wadannan ba abin yi wa hanzari ba ne wajen Allah domin biyayyarsu ga wadannan mahukunta aiki ne na baudiya saboda haka ba zai wanke abin da ke biyo bayansa na abkawa cikin baude-baude ba.[
39]
A koyarwar imamai (a.s) kafin imam Sadik da bayansa kuna ganin karfafawakan
wajibcin gwama jagorancin siyasa da tunani da manufa (aidiyolojiyya). A wata riwaya daga Imam Ali ibn Musa Al Rida (a.s) daga kakansa Imam Muhammad Bakir (a.s) ya ce: Makami a gare mu tamkar akwati ne ga Bani Isra’ila, duk inda akwati ya juya, sai mulki ya juya, (ka yi tunani da kyau kan ma’ana irin ta alama (ramzu) da ke cikin maganar) duk kuwa inda makami ya juya a cikinmu ilmi can zai juya.A wata riwayar kuma duk inda makami ya juya a cikinmu, to can al’amarin (hukuncin) yake.
[40] Sai mai riwaya ya tambayi Imam ya ce:-
Shin makamin yana rabuwa da ilmi?
Imam ya ce:-
A’a (watau jagorantar al’ummar musulmi wajibine ta zama a hannun wanda yake rike da makami da kuma ilmi gaba daya). Saboda haka Imam (a.s) yana ganin cewa ilmin addini da fahimtar Alkur’ani ingantacciyar fahimta daya daga sharudan imamanci ne. Ta wata fuska kuma ta hanyar aikinsa na ilmi da tara adadi mai yawa na masu kishirwa da begen ilmomin addini a gangarsa, da koyar da addini yanda ya saba cikakkiyar sabawa da hanyar da aka saba wajen malamai da masana hadisi da masana tafsiri masu alaka da tsarin halifanci. Wannanyana
tabbatarwa, a aikace, da cewa janibin addini sifa ce ta asali a makarantarsa, da kuma cewa rigar addinin da tsarin halifanci da malaman fada masu daka rawarsu ke da shi ta boge ce. Da wannan hanyar hari mai tsanani mara yankewa kuma cikin tsanaki Imamyake
baiwa jihadinsa wata sabuwar kusurwa.
Kamar yanda muka ambata a baya, mahukuntan Abbasiyawana
farko wandanda suka sami shekaru da dama kafin su karbi mulki, suna tare da jihadin Alawiyawa kuma mataimakansu suna da masaniya kan da yawa daga hanyoyi da sako-sakon kirar.Sun riski rawar da hari da fama da wannan aikin fikihu da hadisi da tafsiri ke takawa fiye da magabatansu, Umayawa.
Hala wannan dalilin shi ya sanya Mansur, saboda tinkarar Imam Sadik (a.s) ya hana shizama
a halakar koyarwa na wani lokaci da hana mutane zuwa gare shi. Har Mufaddal ibn Umar yana cewa:- “ Hakika Mansur ya daura aniyar kashe Abu Abdillah ba ma sau daya ba ko yaushe ya aika a kira shi domin ya kashe shi, idan ya dube shi sai haibar Imam ta rufe shi kana ya bar shi-sai dai fa ya hana mutane zuwa gare shi, ya kuma hana shi zama saboda mutane, ya bincike shi bincike mai tsanani, har al’amar ya kai ga cewa waninsu zai bukaci samun haske a wata mas’alar addini kan batun aure ko shika ko wani abin daban, gashi basu da sanin ta, kuma basu iya isa gare shi. Sai mutum ya kauracewa
iyalinsa. Wannan abu ya kuntata wa shi’arsa ya kuma yi musu tsananin”[
41]
3. Kafa tsarina
sirri kan manufa da kuma siyasa
Ya gabata cewa Imam Sadik (a.s) a karshen zamanin Umayyawa ya jagoranci wani shirin sadarwa da sanarwa mai fadiwanda
kuma manufarsa ita ce kira zuwa imamanci irin na Ali (a.s) da bayyana sha’anin imamanci a kan sahihiyar ma’anarsa.Wannan shirin sadarwa ya yi yunkurin tabbatar da aikin yada ma’anonin imamanci.
Wannan yunkuri ya yi alfanu saboda irin tasirinsa a sassan duniyar musulunci masu nisa masammana
Irak da Kurasan.
Anan
za mu yi ishara ga kadan daga wannan al’amari. Sha’anin tsaren-tsaren sirri a rayuwar siyasa ta Imam Sadik (a.s) da sauran imamaiyana
daga cikin al’amura wadanda suka fi muhimmanci kuma suka fi tsanani ko hadari a lokaci guda kuma shi ya fi komai zama dishi-dishi da rashin bayyana a rayuwarsu. Kamar yanda muka ambata ba zai yiwu musami
bayani wannani al’amari a fayyace ba tun da ba mu tsammanin Imam ko wani daga sahabbansa zai yi furuci da cewa akwai wadannan tsare-tsaren siyasa da tunani a fili.
Wannan abu newanda
ba za’a iya gano shi ba. Abin da hankali zaikama
shi ne Imam ya tabbatar da rashin samuwar irin wannan tsari na sirri, tare da musantawa mai tsanani, haka nan ma sahabbansa, kuma sun dauka wannan wata tuhuma ce da mugun zato da tsarin hukuma zai nemi su ba da bayani kan wannan lamari. Wannanita
ce sifar da aikin sirri ya kebanta da ita, kuma shi ma mai bincike yana da damar rashin gamsuwa da samuwar irin wanna tsarin idan ba da dalili mai gamsarwa ba. Idan haka ne to yazama
wajibi mu bincika da shaidu da abubuwan da suka auku wadanda ga alama ba bakin komai suke ba kuma basu daukar hankalin mai karatu mara lura, saboda mu yi binciken manuniyar da suke da ita a kan wannan batu. Da irin wannan bin diddigi a rayuwa imamai (a.s) cikin karni biyu darabi
, mai bincike zai iya natsuwa da samuwar irin wadannan tsare-tsare masu aiki karkashin jagorancin imamai (a.s).
Me ake nufi da tsari?
Ba fa tsari anan
yana nufin wata jam’iyya tsararra bisa irin manufar da take da ita a yau ba.Ba kuma samuwar wasu dakaru tararru masu jagorantar larduna, masu dangantaka tamkar tsarin dala ba.
Babuwannan
, kuma bai yiwuwa a same shi. Abin nufi da tsari shi ne samuwar wata jama’a ta bil Adama mai tarayyakan
wata manufa, masu aikace-aikace daban-daban wadanda cimma waccan manufa shi suka sa gaba, masu alaka da matattara daya da zuciya mai bugawa guda daya da kwakwalwa mai tunani guda daya, sannan daidaikunta suna tarayya a alakar soyayya.
Wannan jama’a, a zamanin Imam Ali (a.s) (watau cikin shekara ishirin da biyar tsakanin wafatin Manzon tsira da mubaya’ar Ali a matsayin halifa) ta kasance imani da hakkin Imam Alina
halifanci yana hada ta. Takan
bayyana cika alkawarinta ga Imam ta hanyar tunani da ta siyasa, sai dai ita tana koyi da Imam Ali (a.s) kan rashin ta da abin da zai girgiza jaririyar al’ummar musulunci. Haka kuma suna yunkurawakan
abin da a wadancan shekaru Imam Ali yake yunkuri saboda shi kamar nauye-nauyen sako da zimmar kare musulunci da yada shi da kokarin takaita baude-baude.Saboda wilayar ta wannan jama’a ta dauki sunan ‘Shi’ar Ali’.
Wadanda suka shahara daga cikinsu akwai Salman da Ammar da Abu Zarri da Ubayy ibn Ka’ab da Mikdadi da Huzaifa da sauransu, daga manyan sahabbai.
Muna da shaidun tarihi masu tabbatar da cewa wadannan suna yada tananinsukan
al’amarin imamancin Ali (a.s) cikin mutane tare da hikima. Wannan aiki nasu yazama
gabatarwa ga dafifin da mutane suka yi kan Imam Ali (a.s) da kafa hukumarsa.
Bayan Imam Ali (a.s) ya karbi ragamar mulki shekara ta talatin da biyar bayan hijira mutane iri biyu suke tare da shi.Na farko sun san Imam da matsayinsa, sun fahimci ma’anar imamancin sun kuma gaskata shi.
Wadannan su ne shi’arsa wadanda suka yi tarbiyya a gabansako
dai kai tsaye ko kuma ta hanyar wadansu. Kashina
biyu ya kunshi jama’a baki daya wadanda suka rayu cikin yanayin tarbiyyar Imam da tafarkinsa amma basu da alaka ta tunani ko ta ruhi da jama’ar da Imam ya yi wa tarbiyya ta musamman.
Saboda haka ne za kasami
mabiya Imam iri biyu ne na mutane, tsakaninsu da fifiko mai yawa.Kashi guda ya hada da Ammar da Malik Ashtar da Hujr ibn Adiy da Sahl ibn Hunaif da Kais ibn Sa’ad da tamkarsu.
Daya kashin kuwa ya hada da Abu Musa AlAsh’ari da Ziyad ibn Abih da ire-irensu.
Bayan sulhin Imam Hassan (a.s) muhimmin matakin da Imam ya dauka shi ne yada tunanin mazhabin Ahlulbaiti da daidaita tsakanin masu wilaya da wannan tunanin, tun da ansami
faragar motsawa mafi yalwa sabili da danniyar mulkin Umayyawa. Da’iman haka al’amarin yake, danniya tana kawo hadinkan
wadanda ake dannewa ya sa su sajewa da kafuwa a maimakon watsewa da rarraba. Dabarun Imam Hassan sun fuskancitara
karfi mai wilaya dan asali waje guda da kare shi daga rabkar tsarin Umayyawa, da kuma yada tunanin musulunci dan asali a tsakanin wata takaitacciyar kungiya, sai dai an zurfafa koyar da su wannan tunanin. Sauran ayyuka sun hada daneman
masu shigowa safun wilaya da dakon damar da ta dace da yin tawaye wa tsarin zalunci: da yin bindiga da ginshikansa da kuma aza hukumar Alawiyya a gubinsa. Wannan dabarar aikiita
ta bar Imam Hassan (a.s) da zabi daya kadai, wanda shi ne sulhu.
Wannan shi yasa
muke ganin wani gungun ‘yan shi’a karkashin jagorancin Musayyib ibn Najiyya da Sulaiman ibn Sard Alkhuzai, ya tafo gurin Imam Hassan (a.s) a Madina bayan sulhu, yayin da ya dauki birnin ya zama sansanin aikinsa na tunani da siyasa bayan dawowarsa daga Kufa. Wadannan mutane suna gabatarwa Imam da shawarar sabonta karfinsu da tsare-tsarensuna
soji da mamayar Kufa da yin tafo-mu-gama da rundunar Sham. Imam ya yi kiran wadannan mutane biyu daga cikin gungun, ya kebance da su, ya kuma tattauna da sukan
abin da ba mu san me ya kunsa ba. Mutanennan
biyu sun fito a karshen wannan tattaunawa tare da cikakken gamsuwa da rashin alfanun daukar wannan mataki. Yayin da wadannan biyun suka koma ga wadanda suka zo tare da su sai suka fahimtar da su a takaice cewa an yi watsi da batun tawaye ta hanyar daukar makami, kuma dole ne a koma Kufa domin a sake sabon aiki a can.[
42]
Wannan muhimmin al’amari ya kunshi ma’anoni masu girma wadanda sukasa
sashen malaman tarihi na wannan zamani daukar wancan zama a matsayin tushen da aka kafa tsare-tsaren shi’a a kansa.
Hakikan al’amari shi ne idan dai matakin farko na tsare-tsaren shi’a an dauke shi ne a wancan zama tsakanin Imam Hassan (a.s) da mutane nan biyu wadanda suka tafi daga Irak to ai Imam Ali (a.s) ya yi wasici da irin wannan matakin a lokacin da ya yi wasici ga sahabbansa mukarrabai da cewa:- “Idan kun rasa ni lallai za ku ga a bayana abubuwan da dayanku zai yi burin mutuwa saboda zalunci da gaba da son kai da rikon sakainar kashi da za’a yi wa hakkin Allah da kuma tsoron abin da zai sami ransa. Idan haka yafaru :
-
-Ku yi riko da igiyar Allahgaba
dayanku, kuma kada ku rarraba…..
-Na hore ku da dauriya da kuma salla.
-Da kuma takiyya.
Kuma ku sani Allah Mai girma da daukakayana
kin bayinsa su zama masu fuska biyu. Kada ku gusa daga gaskiya da mutanenta domin duk wanda ya musanya mu da wani ya halaka, kuma duniya ta kubuce masa, zai kuma fita daga cikin ta yana mai sabo)[
43]
Wannan nassi mai zana yanayin bala’i da ya wanzi a zamanin Umayyawa a fayyace, mai fuskantar da muminaikan
wajibcin taimakekeniya da daidaitawa da sajewa da juna yana furuci da mafi hasken shaida kan shirin tsare-tsare a harkar Ahlulbaiti (a.s). Wannan shirin tsare-tsare ya fito fili da siffarsa ta aikace a zamannan
da Imam Hassan (a.s) ya yi da biyu daga cikin shi’arsa makusanta. Kuma babu shakka cewa ba duka mabiyan Ahlulbaiti suke da masaniyakan
wannan shiri mai zurfi ba. La’alla wannanyana
iya zama wani hanzari kan abin da yake fitowa daga sahabbansa wanda ya danganci suka. Masu sukan kuwa sun kasance suna fiskantar maganar Imamsa’ar
da ya yi masu bayani. Ga abin da ta kunsa: “……wa
ya sani, ko wannan jarrabawa ce a gare ku, kuma amfani mai gushewa ga abokan gabarku……” A cikin wannan amsa akwai wata ishara boyayya ga siyasa da tsare-tsarenImam[
44]
A tsawon shekaru ishirin wadanda Mu’awiya ya yi mulki, farfaganda mai tsanani wanda ake gudanarwa da zimmar muzanta gidan Ali, wanda ya kai ma ana tsine wa Amirul Muminina Ali bisa mimbarorin musulmi da kuma janyewar Imam Hassan da Imam Hussain (a.s) daga fagen bayyannanar haraka wacce ake iya ganinta a fili, wannan yanayi ya sa babu wani musabbabin yaduwar tunanin Ahlubaiti da fadadar farfajiyar shi’a a Hijaz da Irak da za’a iya gani face samuwar wannan shirin tsare-tsare.Bari mu leka mu ga yanayin da fagen tunani ya ke ciki a wadannan wurare shekar ishirin bayan sulhun Imam Hassan (a.s).
A Kufa za ka samu cewa mazajen shi’a suna daga cikin mashahuran mutane.
A Makka da Madina, kai da ma larduna masu nisa za ka ga mabiuya Ahlulbaiti tamkar wata sarka, sashintayana
sane da abin da yake samun daya sashen.
Bayan wasu shekaru, da daya daga mazajen shi’a watau Hujr ibn Adiy ya yi shahada sai ka ji suka da nuna rashin yarda a wurare da damana
kasashen musulunci duk da razanarwar da aka kakaba a ko ina.
Bakin ciki da takaicin ya kai ma wani sanannen mutum a Kurasan ya mutu saboda tsananin bakin ciki bayan ya bayyana suka cikin fushi.[
45]
Bayan mutuwar Mu’awiya dubban wasiku suka zowa
Imam Hussaini (a.s) suna kiran sa da ya taho Kufa ya jagoranci juyi. Bayan shahadar Imam gomomin dubbai suka shiga kungiyar“ Tawwabun
” ko suka shiga safun rundunar Muktar da Ibrahim ibn Malik masu adawa da mulkin Umayyawa.
Wajibi ne mai binciken tarinin musulunci ya yi tambayakan
musabbabin yaduwar wilaya ga Ahlulbaiti (a.s). Shinyana
yiyuwa hakan ta tabbata ba tare da samuwar wani aiki mai yawa da tsari, wanda aka auna shi, wanda kuma hadadde ne wajen tafarki da manufa ba?
Amsa a’a, bisa dabi’a wannan ba zai yiwu ba.
Gagarumar farfa-gandar da mulkin Umayyawa sukadana
ta hanyar daruruwan alkalai da hakimai da masu huduba ba za ta rushe kuma ta ci tura ba idan ba wani zayyanannar farfaganda mai hamayya da waccar, wacce wani tsari hadadde, daidaitacce, boyayye ya yunkura da ita ba. Dab da mutuwar Mu’awiya aikace-aikacen wanna shirin Alawiyyawan ya cigaba
, saurinsa kuma ya karu. Lamarin ya kai ga hakimin Madina ya rubuta wa Mu’awiya abin da ya kunshi wannan: “Bayan haka, Umar ibn Usman (dan leken asirin hakimin Madina wanda ya sa ido kan Imam Hussain (a.s)) ya ba mu labarni cewa wadansu mazaje daga Irak da sashen manyan mutanen Hijaz suna yawan zuwa wajen Hussain Ibn Ali, suna kuma tattauna batun daga tutar tawaye …….ku rubuto mana ra’ayin ku.”[46]
Bayan waki’ar Karbala da shahahar Imam Hussain (a.s) aikin tsare-tsarena
shi’a a Iraki ya karu sakamakon girgizar da ta sami zukatansu saboda kisan Imam Hussain (a.s) inda wannan babban laifi wanda ya kwace musu daman shiga ayarin Hussain da mutanen gidansa a Karbala ya zo musu ba zata. Wannan motsawa tasu tana kewaye dajin
zafi da tabewa da takaici.
Dabari yace :
Mutanen ba su rabu da tara kayan yaki da shirya masa da kiran jama’ar shi’a da ma waninsu, a asirce, kan daukar fansar jinin Hussain ba. Mutane sun amsa kiransu jama’a na bin jama’a, birni na bin birni, ba su rabu da haka ba har Yazid ibn Mu’awiya ya mutu.[
47] Abin da littafin Jihadu Shi’a yake fadi gaskiya ne, inda ya yi taliki wa zancen Dabari da cewa:-
“Bayan kashe Imam Hussaini, jama’ar shi’a ta bayyana a matsayin wata jama’a mai tsari, ra ayoyin addini da alakar siyasa suna dinke ta, tana gudanar da tarraki tana da shugabanni, kana tana da karfin soji.
Jama’ar “Tawwabun”ita
ce farkon mai bayyana dukkan wanna.
Bincikekan
al’amuran da suka auku a tarihi da ra’ayin marubuta tarihin kan wancan zamani, ga alama, yana nuna cewa shi’a suna daukar nauyin jagoranci da shirye-shirye, sai dai farajiyar fusata da sukar Banu Umayya ta fi tsararriyar jama’ar shi’an nan fadi. Wannan farfajiyar tana haduwa da kowace haraka mai rininshi’a .
Za mu gane cewa masu motsawa da hamayya kan Banu Umayya ko da sun yi amfani da taken shi’a ba dai dai ne mu dauka cewa dukkansu suna cikin adadin shi’a ba, watau adadin tsararren shirin nan na imaman Ahlulbaiti (a.s)
Bayan bayanin da ya gabata, ina son in yi ta’akidi kan cewa bayan shahadar imam Hussaini wadanda kadai ake kiransu shi’a su ne jama’ar nan da take da alaka mai karfi da imamin gaskiya, tamkar yanda lamarin yake a zamanin Amirul Muminina (a.s). Wannan jama’a ita ce bayan sulhun Imam Hassan (a.s) ta fuskanci kafa tsarin shi’a da umarnin Imam, kuma ita ce ta yi kokarin jawo mutane zuwa wannan tsarin da kuma kange mafiya yawa wadanda basu kai matuka a tunani ba kuma basu yi kwari a fagen aiki ba balle su kai matsayin shiga tsarin, wanda yake da zimmar samar da wata babbar harakar shi’a.
Riwayar da muka kawo a farkon wannan bahasi wacce aka rawaito daga Imam Sadik (a.s) mai cewa adadin muminai bayan waki’ar Ashura bai wuce uku ko biyar ba, abin da take nufi shi ne ‘yan wannan kebantacciyar jama’a.watau
mutanen nan da suke iya rawar gani, a matsayinsu na madugu mai wayewar kai a kokarin kaiwa matuka cikin al’amarin juyin Alawiyyawa.
Sakamakon aikin da Imam Sajjad (a.s) ya yi a cikin sirri da tsanaki, turakun wannan ‘yar jama’a sun fadada kuma da wannan Imam Sadik (a.s) yake ishara a riwayar da muka ambata…… “sannan
mutane suka risko su suka yawaita”. Za mu gani cewa zamanin Imam Sajjad da Imam Bakir da Imam Sadik ya ga motsawar wannan jama’a,wanda
ta jefa tsoro da firgici a zukatan azzaluman mahukunta, al’amarin da ya sa du mai da martani mai tsanani.
A takaice, a karnin farko dana
biyu bayan hijira da ma tsawon zamanin imamai (a.s) ba’a kiran wadanda suke kaunar Ahlubaiti da imani da hakkinsu da gaskiyar kiransu kadai ba tare da yin tarayya a tafiyar harakarsu ba da sunan shi’a. Su shi’a suna bambanta da saura ne ta hanyar wani tabbatanccen sharadina
tushe, wanda shi ne alaka da Imam wajen tunani da aiki da tarayya a aikin tunani da siyasa kai da ma ta fuskar aikin soji wanda yake jagoranta saboda dawo da hakki ga mai shi da kafa tsarin Alwawiyyawa na musulunci. Wannan alakaita
ake kira “wilaya” a kamus na shi’a.
Bisa hakika jama’ar shi’a suna ne wanda ake baiwa ‘yan jam’iyyar imamanci, jama’iyyar da take motsawa karkashin jagorancin Imam (a.s) take kuma daukar boyewa da takiyya a matsayin mafaka, tamkar duk wata jam’iyya ko shiri mai rayuwar cikin tsoro da danniya. Wannan shi ne takaitaceen bayani kan dubi na hakika kan rayuwar Imamai (a.s) musamman Imam Sadik (a.s) kuma kamar dai yanda muka ambata tun farko ba zai yiwu a sami hujjoji bayyanannu kan irin wannan al’amarin ba, tun da ba za mu yi tsammanin za’a kafa wa wani gidan sirri alama mai cewa: “wannan gidan sirri ne” ba!Kazalika ba zai yiwu mu natsu da sakamakon (bincike) ba, ba tare da samuwar wasu tabbatattun shaidun yanayi ba.
Saboda haka ya kamata mu bi biddigin wadannan shaidu da isharori.
Daga cikin kalmomi masu zufafan ma’anoni wadanda suke jan hankalin mai bincike mai bin diddigi a riwayoyin da rayuwar imamai (a.s) ko kuwa wadanda ake kawowa a maganganun masu talifin karnin musulunci na farko akwai kalmomin “kofa” da “wakili” da “ma’a bocin sirri” wadannan kalmomi ne da ake kiran wasu sahabban imami da su. Alal misalim mashaurin malamin hadisi dan shi’a yana fada dangane da rayuwar Imam Sajjad (a.s)cewa :-
“ Yahya ibn Ummu Dawil shi ne kofarsa” a kan ta Imam Bakir ( a.s) kuwa ya ce: “Jabir ibn Yazid Alju’fi shi ne kofarsa”, batun rayuwar Imam Sadik (a.s) kuwa ya ce:- “Muhammad Ibn Sinan shi ne kofarsa”.A cikin littafin “Rijalul Kashshi” ana kiran Zurara da Buraid da Muhammad ibn Muslim da Abu Basir da lakabin “ma’ajin sirri”.
A cikin littafan hadisi ana ruwaitokalmar
“wakili” daga Imam Sadik (a.s) a kan batun Mu’alla ibn Kunais.Ko
wani daya daga cikin wadannan kalmomi imma dai ya fito ne daga Imam, wa imma sakamakon bincike ne mai yawa kan rayuwar imamai, wanda magabatan marubutan shi’a suka gudanar.Ko
ma yaya ta kasance zabar wadannan kalmomi masu zurfafan ma’anoni ya samo asali ne daga wadansu fitattun alamomi a rayuwar Ahlulbaiti (a.s). Idan muka yi tunani da kyaukan
wadannan kalmomi za mu tarar cewa ko wacce daga ciki tana nuni da cewa karkashin ayyukan zahiri wadanda imamayi (a.s) suke gudanarwa, akwai wani rayayyen shiri na boye.