• Farawa
  • Na Baya
  • 20 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 13275 / Gurzawa: 4208
Girma Girma Girma
Jagorancin Imam Sadik

Jagorancin Imam Sadik

Mawallafi:
Hausa

Dukkan hakkokina cibiyar Muassasar alhasanain (a.s) ne, kuma yada rubuce-rubucen tare da ambaton inda aka dauko su ba shi da matsala. Muassasar alhasanain (a.s)

JAGORANCIN IMAM SADIK (a.s)

Ayatullahi Uzma Sayyid Ali Alkhamena'i

Fassarar: Malam Umar Kumo

Dubawa: Hafiz Muhammad Sa’id

Gabatarwar Cibiyar Ahlul-bait (a.s)

Rayuwar Ahlulbaiti (a.s) ta banbanta da ta waninsu domin ita wata silsila ce kwakkwara, mara yankewa, sai dai yanayin zangon tarihin da kowane imami yake rayuwa a cikinsa, ya kan sa ya dauki wani matsayi wanda a zahiri ka ce yana sabawa da wanda imamin da ya gabace shi ko ya biyo bayan sa ya dauka, sabani mai tsanani.Muna iya ganin wannan a matsayin da Imam Hassan (a.s) da Imam Hussain (a.s) suka dauka. Amma bisa hakika wannan ba sabani ba ne, aiki ne daidai da abin da yanayi yanema , ta yanda matsayin kowane daya daga cikinsu yana cikata aikin imamin da ya gabata ne ko ya yi shimfida ga aikin da wanda zai gaje shi zai gudanar.

Sakamakon rashin fayyacewar nazari a tattare da sashen masu bahasi kan rayuwar imamai, an sami nazariyya da ra’ayoyi daban-daban wajen kokarin bayyana yanayin aikin da wani Imami ya zartar.wanda sun kasance bisa kuskure, bincike-bincike kuwa ba a zurfafa mahangarsu ba kuma ba su dogara kan tushe na imamanci da isma ba domin ba su ginu kan ingantacciyar fahimta mai iya riskar hakikanin yanayin ba.

Asalin wadannan nazarce-nazarce mara tushe ne mai cin karo, ta kowace fuska da imani da ma’asumin jagoranci wanda kowane imami yake tafiya a kai bisa abin da ya fahimta daga yanayi ko kuma dabai’ar zangon da ya sami kansa a ciki, da kuma kasancewar matsayinsa ba matsayi ne wanda son rai ko amfanin kai ko mai da martani a makance suke rinjaya ba. Matsayi newanda yake tattare da hikima da hangen nesa da dacewa da taimako daga ludufin ubangiji.

Irin wancan karkatacciyar fassara ta shafi rayuwar dukkan imamai. Sai ka ga wani lokaci ana sifanta su da daukar matakin dauki ba dadi, kamar matakin juyin juya halin da ImamHussain( a.s) ya dauka, ko kuma a ce sun karkata zuwa rayuwar tsanaki da nisantar fagen siyasa kamar yanda Imam Sajjad (a.s) ya yi.Ko kuma a buga masu tambarin masu daidatawa da azzaluman mahukunta kamar matsayin Imam Sadik (a.s).

Wannan littafin da ke gabanmu ya kunshi wata laccar da mai girma shugaban musulmi Sayyid Ali Khamene’i (Allah yaja zamaninsa) ya yi kafin juyin Islama mai albarka da aka aiwatar a kasar Iran.A cikinta ya bijiro da wadancan karkatattun nazarce-nazarce tare da rusa su ta hanyar karfafan hujjojin ilmi da tarihi.

Daga bisani, Sayyid ya gabatar da ingantaccen nazari mai fassara matsayin da kowane imami ya ba da himma akan shi domin ya yi shimfida ga imamin da zai biyo bayan shi, har al’amari ya iso hannun imam Sadik (a.s).jagorancin wannan imami bai kasance mai mika wuya ga son rai ko amfanin kai ko kuma tsoron azzalumai ba. Wannan jagorancin wani ma’sumin matsayi ne mai bin ka’idar da Allah subhanahuwa ta’ala ya bayyana, ma’asuman gabanin Imam (a.s) kuma suka shimfida masa. Imam Sadik a nasa bangaren aiwatar da wannan tafarkin ne ya yi, yana mai amfani da kwarewarsa ta siyasa da saninda Allah (s.w.t) ya karfafa shi da shi, domin ya jagoranci jirgin musulunci zuwa gabar tsira da aminci, domin kuma ya tsare wa musulmi addininsu da akidarsu bisa dacewa da ingantaccen asalinsu wanda Annabi Muhammadu (s.a.w) ya kawo, tushen da azzalumai suka yi kokarin shafe almominsa da bice haskensa, tsawon tarihi.

Cibiyar Ahlulbaiti (a.s) ta kasa da kasa, saboda sauke nauyin da ya rataya a wuyarta, ta dauki nauyin buga wannan littafi tare da watsa shi don ya kasance wata haskakawace kan tunanin musulunci da ingantaccen tarihi, domin kuma ya bayyana wa masu bincike kan Ahlubaiti fuska mafi tsabta da za’a fahimci hanyarsu mai albarka. Cibiyar Ahlulbaiti (A.S) Ta Kasa Da Kasa

Gabatarwar Mai Tarjama

Wani dan labari dangane da wannan lacca:- Wannan labari yana nuna abinda rayuwa a kasar Iran gabanin Juyin Islama take tattare da shi, na aiyukan tabbatar da musulunci da kuma kalubale da karfen kafa daga bangaren masu adawa da kiran .

Wata rana cikin watan Shawwal shekara ta 1394 H. kararrawar tarho ta buga a gidan malami mai laccan a birnin Mashhad, mai magana a wayar shi ne Shahid Dokta Muhammad Mufattih daga Tehran.

Bayan gaisuwa, Sheikh Mufattih sai ya nemi Sidi da ya taho Tehran.ran 25 ga Shawwal (watau ranar wafatin Imam Jaafar bin Muhammad Assadik (a.s) domin ya gabatar da wata lacca kan ImamSadik .

Halin da ma’abocin laccar yake ciki ya kasance mai kunci a wancan lokacin saboda yawan aiyuka da karantarwa da yawan jama’a masu zuwa daga nahiyoyi daban-dabanna Iran.Yana ba da laccoci a masallacin Imam Hassan da masallacin Alkarama a Mashhad, birnin da ke gabashin Iran, sannan ya tafi yammacin kasar domin gabatar da lacca a Hamadan da Kermanshah. A cikin Mashhad dinkansa yana koyar da tafsiri da Nahjul balaga da hadisi ga kuma darusan kwarewa a fikihu da usulu.

Duk wadannan aiyuka Sidiyana gabatar da su ne a cikin wani hali mai tsananin matsi, ga wahalar rashin kudi ga ta kuntatawar yanayin siyasa. Ya kasanceyana rayuwa cikin matsanancin talauci ba tare kowa ya sani ba. Sannan masu mulki suna matsa masa lamba sunasa ido ainun bisa duk abin da yake yi. A wannan shekaran ne suka rufe Masallacin Alkarama, abin da ya sanya Sidi ya takaita da karamin masallacinsa, watau masallacin Imam Hassan ya cigaba da aiyukansa. A cikin hunturun wanna shekarar ne masu mulki suka sakekama shi, abin da ya kai shi kurkuku a karo na biyar ke nan.

To a cikin irin wannan yanayin ne Sheikh Mufattih ya bukaci Sidi Khamene’i da ya gabatar da lacca akan Imam Sadik (a.s) a Tehran a Masallacin Javid inda shi Sheikh Mufattih yake ba da salla. Ma’abocin laccar sai ya ba da hanzari saboda dalilan da muka ambata da kuma saninsa cewa akwai malaman da za su cike gurbinsa a can Tehran, kamar su Sheikh Mufattihkansa .Amma Sheikh ya matsa, saboda haka malamin ya yarda. Bayan kwanaki Sheikh Mufattih sai ya sake buga wayayana cewa:-

“Yan sanda sun hana taron laccar” Sidi ya yi ajiyar zuciya,yana mai jin ya huta da wannan nauyin, ya kuma yi hamdala. Ba’a dade ba sai ga Sheikh ya sake bugo waya yana mai cewa:- “ Alhamdu lillahi an dauke hanin.Muna nan muna sauraronka a ranar da muka ajiye”.

Sidi ya yi iya kokarinsa domin a karbi uzurinsa amma ina Sheikh Mufattih bai gamsu ba, sai ya amsa da cewa:- “Mun riga da mun sanar da batun laccan nan cikin jami’o’ i” Sidi ya ba da dalilin cewa samun tikitin jirgi yana da wahala. Amma Sheikh sai yace a shirye yake ya saya masa tikitin, saboda haka ba makawa ga halartar Sidi!

A ranar laccar ya baro Mashhad ya kuma iso Tehran yansa ’ o’ i kafin lokacin farawa, sai ya wuce zuwa masallacin kai tsaye. Yayin da mai masaukinsa ya gan shi, ya yi farin ciki matuka, a lokacin kuwayana tare da matasa kamar dari biyu suna jiran a ta da salla.Ana cikin salla matasa sai zuwa suke yi har adadinsu ya kai dururuwa da dama. Bayan’yan mintoci sai ga dalibai gungu gungu suna ta shigowa, wannan bayan an tashi daga darasi ajami ‘o’ i kenan.

Masallacin da farfajiyarsa da loko-lokon da ke daura dashi duk suka cika makil da mutane. Sidi ya fara laccayana rike da takardu guda arba’in wadanda suke kunshe da muhimman batutuwa kan laccar. Ya cigaba da bayani wanda ya dauki hankalin masu sauraro, kai ka ce tsuntsaye ke bisa kawukansu saboda tsananin natsuwa. Laccar ta dauki tsawon sa’a uku amma sashen takardunnan kawai Sidi ya sami damar sharhinsu. Da ya zo rufewa sai ya daga wadancan takardu arba’inyana mai ishara da cewa lokaci bai ba shi damar gabatar da dukkanin abin da ya yi niyya ba.

Bayan wannanzama ba a dade ba sai aka kama Sheikh Mufattih aka hana shi salla a masallacin Javid. Bayanan sako shi sai ya koma masallacin Kuba. A nan, ya zama wajibi mu yi nuni da wani muhimmin al’amari, shine : Sidi Khamene’i (Allah ya kiyaye shi ) ya gabatar da laccan nan ne shekara ashirin da suka wuce. Kuma babu shakka ya yi nazari da bincike mai yawakan rayuwar Imaman Ahlulbaiti (a.s) saboda haka ta yiwu yana da wadansu sababbin ra’ayoyi ko kuma ya canja ra’ayi, kan wata mas’ala daga cikin mas’alolin da ya gabatar cikin jawabin. Hakika mun so mu san ra’ayinsakan wadannan mas’aloli domin mu cimma ra’ayoyinsa na baya-bayan nan kafin mu soma tarjamar wannan jawabin zuwa harshen larabci.Amma nauye-nauye da tarin ayyuka da cushewarsu ya hana hakan. Saboda haka za mu gabatar daita kamar yanda take. A cikinta akwai sabon ilmi mai yawa da kuma gadon tunane-tunanen musulunci kamar yanda ake tattauna shia Iran gabanin nasarar Juyin Islama, abubuwanda suke da muhinmanci ga duk wani mai bincike.

Ana iya lura da cewa Sidi ya yi fito-na-fito da ra’ayoyi guda biyu wadanda yake yawan sukar su a laccocinsa da darussansa. Wadannan kuwa su ne: Ra’ayin gurguzu mai sukan musulunci da alamominsa,yana sifanta mazajen musulunci da cewa ba su tabuka komai ba wajen kare hakkin matalauta da wadanda aka zalunta, dadin dadawa ma sun kasance madogarar azzalumai da masu hanu da shuni! Na biyunsu shi ne ra’ayinwanda suka yarda an rinjaye su. Saboda rinjayarsu da aka yi sai suka kasance ba su da katabus, kokari suke susami abin da wai zai zame musu hujjar rashin motsawa, a cikin tarihin rayuwar Imaman musulunci.Wadannan ra’ayoyi sun yi tasiri a kasar Iran kafin habakar Juyin Islama, sun kuma zamo karfen kafa ga masu kiran al’umma zuwa hanyar musulunci. Dokta Muhammad Ali Azarshab

Ubangiji Madaukaki yana Cewa :

Daga muminai akwai wandansu mazaje da suka gaskata abin da suka yiwa Allah Alkawari a kansa, sa'annan a cikinsu, akwai wanda ya biya bukatarsa, kuma basu musanya ba, musanyawa. Ahzab 23

Kuma muka sanya su shugabanni suna shiryarwa da umurninmu. Kuma muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alheri da tsayar da sallah dabayar da zakka.Kuma sun kasance masu bauta garemu. Anbiya 73.

Dubu Biyu Karkatattu

Godiya ta tabatta ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah da alayesa da wadanda suka yi koyi da shiriyarsu.

Akwai karkatattun dubi guda biyukan al’amrin Imam Sadik (a.s) wadanda suka samo asali daga nau’i biyu na tunani. Abin mamaki anan shi ne duk da sabawarsu da juna suna da kusaci wajen kamanni da abin da suka kunsa da kuma tushe, kai ana ma iya cewa wadannan dubi biyu suna da cikakkar tarayya a sashen ginshikansu.

Dubi Na Farko

Ra’ayiko kuma kallo irin na masu karewa watau masoya, wannan ra’ayin wasu masu zaton su mabiyan Imam Sadik (a.s) ne amma shi’arsa ne da fatar baki kawai banda aiki. Ra’ayin a takaice shi ne:-

Cewa Imam Sadik (a.s) yasami yanayin da imaman da suka gabace shi ko suka biyo bayan shi basu samu ba, yanayin da ya ba shi damar yada hukunce-hukuncen addini da kuma bude wa dalibai kofofin majlisinsa. Ya zauna gidansayana karbar masu zuwa, ya rungumi karantarwa da yada ilmomi, duk dalibi ko mai bidar gaskiyan da ya zake masa yana kashe kishinsa na ilmi. Mutum dubu hudu suka yi karatu a gabansa, kuma ta hanyar wadannan dalibai ilmomin Imam Sadik sun watsu ako ina.Daga cikinsu akwai ilmomin addini kamar su fikihu da hadisi da tafsiri, akwai kuma ilmomin dan’adamtaka kamar su tarihi da kyawawan dabi’u da ilmin zamantakewar al’umma.

Imamu ya yi mukabala da ma’abota sababbin ra’ayoyi, ya yi raddikan zindikai da yan maddiyya da mulhidai, ko dai kai tsaye ko kuma ta hanyar dalibansa.Ya yi yaki da mazowa karkatattun addinai matuka. Ako wani fagen addini Imam ya tarbiyantar da wasu fitattun dalibai da kwararru.

Ma’abota wannan mahanga suna karawa da cewa: domin burin Imam a kan ci gaban wannan gagarumin aikin ilmantarwa, dole ta sa ya guji sa baki cikin al’amuran siyasa, saboda haka bai gabatar da kowani aikin siyasa ba, bugu da kari ya ma zabi hanyar daidaitawa da irin siyasar halifofin zamaninsa domin dadada musu da nisantar duk wata rikitarwa da ka iya kusantar aikinsa.Don haka bai yi fito-na-fito da halifofin ba, ya kuma hana kowa yin hakan. Wani zubin ma yanayiyana sawa Imam ya je gaisuwa ya kuma sami kyaututtuka da goyon bayansu. Idan shugaba ya yi masa mummunan zato sakamakon faruwar wata harkar tawayeko kuma tsegunta masa wata tuhuma, Imam ya kan je gaban shugaban domin ba da baki.

Ma’abotan wannan dubin sukan jero hujjojin tarihi domin karfafa ra’ayinsu.Hujjojin sun hada da riwayar Rabi’u Alhajib da makamantansa, wadanda suke siffanta Imam da baiyana kuskure da nadamarsa a gaban Halifa Mansur. Wannan riwaya tana dangantawa Imamkalmomin yabon Mansur, wanda ko shaka babu karya ce a ce sun fito daga Imam Sadik (a.s.) dangane da azzalumai irinsu Mansur. Wadannan kalmomin suna sifanta Mansur cewa kamar Yusuf da Sulaiman da Ayyuba ya ke, suna neman ya dauki hakuri kan munana masa da Imam ko ‘ya’yan Hassan suke masa: “Hakika an baiwa Sulaiman (mulki) kuma ya yi godiya, an jarrabi Ayyuba, ya yi hakuri, kuma an zalunci Yusufu, ya yi gafara, kai kuma irinsu ne……”[ 2]

Wannan ra’ayiyana sifanta Imam da cewa shi masani ne mai bincike, Abu Hanifa da malik sun sha daga kogin ilminsa, sai dai ya yi matukar nisantar yaki da zaluntar addini da masu mulki ke yi, ya kuma nisanci bukatun umurni da kyakkyawan aiki da hana munkari yayin da sarki ya zama ja’iri. Imam ba shi da wata dangantaka da masu tawayewa zalunci ire-iren su Zaid ibn Ali da Muhammad bn Abdullah da Hassan bn Ali shahidin Fakh ko kuma rundunonin wadannan mutane. Bai kasance yana mai da martani kan abin da yake aukawa jama’ar musulmi, ko nuna damuwa kan dimbin dukiyar da Mansur yake tarawa, ko yunwar da ‘ya’yan Annabi (s.a.w.a) suke fama da ita a cikin tsaunukan Tabaristan da Mazandaran da garuruwan Irak da Iran ba, ta yanda basu da abinda zasu sa a baka ko abinda zai rufe musu al’aura idan suna son salla ajam’i !! Kuma ba ruwansa da kisa da azabtarwa da tarwatsa mabiyansa alhali suna hannu rabbana basu samunko da kwatankwancin abin da marasa galihun wancan lokaci suke mora!!!

A zaton ma’abota wannan dubin Imam Sadik sam bai nuna wata damuwakan wannan yanayi ba, a maimakon hakan ya gamsu da yin mukabala da ire-iren su Ibn Abi Awja, ya rufe masa baki da hujjoji ya kuma rinjaye shi duk da cewa ba zai ba da gaskiya ba.Wannan shi ne siffanta Imam Sadik da mazowa ra’ayin farko suka yi.

Dubi Na Biyu

Masu dauke da irin wannan dubin ba su yarda da imamancin Imam Sadik ba. Ita wannan mahanga tana ganin cewa ya nuna halin ko oho bisa zaluncin da yake aukawa al’umma. A zamamaninsa al’ummana kukan zaluncin yanayin zaman jama’a mai hawa-hawa da dagawar siyasa da babakere kan dukiyoyin jama’a [3] da hadarin da ya shafi rayuka da mutuncinsu.Dadin dadawa sarauta ta rinjayi hankula da rayuka da tunani da kuma zukatan mutane. Lamarin ya kai ga al’umma ta rasa mafi kankantan hakkokin bil Adamawanda ya hada da ikon zabe. A gefe guda kuma azzalumai suna ta wasa da makomar mutane yanda suka so, sunagina katafaran soraye kamar soron Al-hamra wanda ke makwabtaka da dubban kangwayen da matalautan al’umma ke zaune a ciki. Cikin wannan jama’ar da take dandana nau’i daban-dabanna rashin adalci da danniya wai Imam Sadik ba abin da ya yi sai fuskantar bahasinsa da bincike da tarbiyyar dalibai, yana karkata dukkan kokarinsa kan samarda fukaha’u da masana ilmul kalam!!

Hakika dukkan mahanga biyunnan sun bi son zuciya wajen hukunci kuma basu ginu kan wani tushe ba, basu kuma dogara kan wani dalili na gaskiya ba. Saidai ra’ayin farko ya fi tsanani wajen bin son zuciya da zaluntar Imam Sadik (a.s) tun da yake ya fito ne daga masu da’awar wai su shi’arsa ne kuma mabiyansa.

Anan ban yi niyar daukan salon bahasin ilmin nan da aka saba bi wajen bincike-bincike, wanda a kan bijiro da dukkanin nassoshin da suka yi magana kan rayuwar Imam Sadik (a.s) sannan a auna wannan da wancan wajen matani da isnadi har a fitar da sakamako ba. Abin da nake nufi shi ne gabatar da nazarina uku wanda ya sha bam-bam da wadancan biyun.Sannan in auna shi da hujjojin da zan tsamo daga littattafan da suke hannunku’ domin, a matsayinku na alkalai ‘yan ba-ruwan mu, ku iya hango fuskar Imam ta hakika.

Kafin in shiga cikin bahasin yazama wajibi in yi nuni da cewa dukkanin nazariyyan na biyu basu dogara kan sahihin tushe abin amincewa ba. Kamar yanda na ambata, ra’ayin farko yana dogara kan wasuriwayoyi( na bayyana yanayin isnadinsu a kasa). Wadannan riwayoyi bisa dabi’a sun dace da bukatar masuneman hutu da gudun tsangwama suna fakewa da su a matsayin yankakken hujja.Lallai kam sun isa hujja ga raunanan zukata masu saukin girgizuwa!

Wadannan riwayoyi sun sifanta Imam da cewayana mai lallamin Mansur domin kare rayuwarsa duk da cewa yana iya magance yanayin da ya sami kansa ta hanyar hikima. Idandai haka jagora yake, me zaton ka da mabiyi? Mun yi imani cewa yanayin nassin wanna riwaya ya wadatar wajen tabbatar da cewa kirkirarta aka yi. Ai Imamyana da damar tunkude sharrin Mansur ta wadansu hanyoyin daban kamar yanda amintattun riwayoyi suka nakalto abin da ya faru a wurare mayaiwata. Ashe babu dalilin da zaisa Imam ya koma wa lalama mara tushe ko yabon da ba na gaskiya ba, har ma ya baiwa Mansur halayen da ba shi da su da matsayin da bai cancance shi ba. Babu shakka matsayin imamanci ya daukakasama da wannan, daukaka mai girma, darajarsa kuwa ta wuce irin wannan kaskanci ya gurbata ta.

Ta bangaren isnadi kuwa, idan aka zurfafa bin diddigin masu ruwaya abubuwa da yawa za su baiyana a gare mu. Isnadin wasu daga cikinsuyana karewa ne kan Rabi’u Alhajib sarkin kofa.Sarkin kofan Mansur! Wannan kuwa akwai adali!Littattafai sun nuna cewa Rabi’u ya fi kowa kusanci da Mansur, ya fi kowa fada. Mansur ya yi masa waziri a shekara ta dari da hamsin da uku hijiraya watau shekaru biyar bayan wafatin Imam Sadik. Hakika Rab’u yasami daukaka a matsayin ladan karairayin da ya kirkira ya kuma danganta su ga Imam.

Irin wannan mutumwanda kusancinsa da alkawarinsa ga halifa ya tabbata ba abin mamaki ba ne ya kirkiri karairayi ya kuma jingina wa Imam Sadik lalama ko ya sake kalami mai zafi da Imam ya yi furuci da shi, ya mai da shi na kankan da kai da lallami. Wannan ba bakon abu ba ne wajen irin wannan bafaje, amma abin al’ajabin shi ne yanda mai hankali zai gaskata abokin sirrin halifa akan abin da ya shafi abokan gabarsa, har ma a ce wai shi ma shi’a ne. Wannan kaulin shi ma wani yanki ne daga kule-kullen da kaskanci ne musabbabinsu.

Shi ma ra’ayina biyun fonko ne kwatankwacin na farkon, kuma bai kafu bisa ilmi ba. Ra’ayinyana kama da irin hukuncin da mustashrikai suke yi wanda ya samo asali daga jahilci da kulli, da kuma ruhi irin na tsagwarar maddiyya wacce ba ta tafiya daidai da dabi’ar abin da yake gudana a musulunci. Mun ga irin wancan hukuncina rasar kunya da bashi da kanshin gaskiya wanda sashen mustashrikai suke yanke wa musulunci da Imaman Ahlulbaiti (a.s). Ga abin da daya daga cikin su [4] ya fadakan Imam Hassan Mujtaba: cewa ya sai da halifanci ya karbi kudi! Yagama rayuwarsa tare da turare da mata da walwala. Wani [5] kuma ya ce: Musulunci ya cirato al’umma daga matakin bauta zuwa na tsarinakda’( watau tsarinda talakawa basa mallakar filayen noma sai dai su yi aiki a filayen masu iko kana su raba amfanin)!Mahanga ta biyun tana tarayya da zantuttukan wadannan mustashrikai wajen biri-boko da garaje da kuma madogara ta maddiyya. Abin sha’awa anan shi ne hujjojin da ma’abota ra‘ayi na biyu, watau ra’ayin ‘yan gurguzu, suka dogara da su ba komai ba ne face hukunce-hukuncen da ma’abota ra’ayin farko suka kirkiro!

Sahihin Dubi: Na Uku

Bari mu fara bayanin mahanga ta ukukan lamarin Imam Sadik, ra’ayi da ko wani kaifin basira yana iya tsinkayar shi idan ya koma ga littafan riwaya. Wannan hukuncin ba ya takaita da rayuwar Imam Sadik kadai, a’ayana game dukkan Imaman Ahlulbaiti, bambancin kawai shi ne abin da aikin kowannensu ya kebanta da shi gwargwadon abin da yanayin zamani da wuri ya hukunta. Wannan sabawar kebantattun sifofin aikin ba ta cin karo da haduwar ruhin aiki da hakikaninsako kuma haduwar manufa da hanya.

Idan muna son fahimtar yanayin rayuwar Imamai ya wajaba da farko mu fahimci falsafar Imamanci. Tafiyar da aka san ta a mazhabar Ahlulbaiti da sunan Imamanci, wacce ginshikanta mutum goma sha biyu ne daya na bin daya kuma ta dauki kusan tsawon karni biyu da rabi, bisa hakika ci gaban aikin annabci ne. Shi annabi, Allah (s.w.t) yana aiko shi ne da wata sabuwar manhajar rayuwa, da sabuwar akida da wani sabon shirin alakokin dan Adam da kuma sako wanda aka dora masa, gwargwadon shekarun da aka ba shi a wannan takaitacciyar rayuwa.

Wajibi ne kira ta cigaba a bayan Annabi domin sakon ya cimma mafi daukakan matsayin da ake bukata wajen tabbatar da manufofinsa. Kazalika dole ne mutumin da ya fi kusaci da ma’abocin sakon ta dukkanin fuskoki ya dauki nauye-nauyen cigaba da kira, domin sakon ya kai amintaccen matsayi, ya sami turke mai karfi, tabbatacce mara yankewa. Wannan aiki, babu shakkayana bukatar amintattun mutane.Wadannan sune Imamai, wasiyyan Annabi. Kuma dukkanin Imamai madaukaka kuma ma’abota sako suna da wasiyyai da halifofi. Ba za mu san nauyin al’amarin Imamai ba sai mun san na Annanbi, wanda Alkur,ani mai girma ya bayyana da cewa: “Hakika, lalle, mun aiko manzanninmu da hujjoji bayyanannu, kuma muka saukar da littafi da sikeli tare da su domin mutane su tsayu da adalci……..” [6] Wannan daya daga cikin ayoyi masu baiyana dalilin aiko annabawa da kuma nauyin da akadora masu ne. An aiko su ne sabodagina wata sabuwar al’umma da tuge ginshikan fasadi da sanarwa kan aiwatar da sauyi ga jahiliyyar zamaninsu da kuma sake wa al’ummarsa fasali. Wannan shiri na kawo sauyi Imam Ali (a.s) ya bayyana shi a farkon karbar ragamar shugabancinsa dacewa : -. “ …..har sai na kasanku sun zamo su ne a sama na samanku kuwa sun zamo su ne a kasa….”[7] Wannan aiki ne na gina al’umma bisa asasin tauhidi da adalcin zamamtakewa da martaba dan Adam da yanta shi da tabbatar da daidaiton hakkoki da dokoki a tsakanin jama’u da dai-daiku da yarfar da kangi da zalunci da boye kayan masarufi; da bude kofa ga karfi da kokarin dan Adam; da kwadaitarwa kan neman ilmi, da ba da shi, da kwadaitarwa kan tunani da sauransu. Shi aiki nena kafa wata jama’a wacce a cikinta, ake habaka ilahirin hanyoyin daukakar dan Adam ta dukkanin muhimman fuskoki da kuma zaburar da shi don ya fuskanci tafiyan nan ta neman kamala a tsawon tarihinsa.

Saboda wannan nauyin ne Allah ya aiko annabawa.A matsayin Imamancina ci gaba da daukar nauye-nauyen annabci, muna iya cewa yana daukar wadancan aiyuka. Da ace Manzon Allah (s.a.w.a) ya rayu shekara 250 da wadanne ayyuka zai gabatar? Yanda ya aikata wajen kira hakanan Imamai suka aikata. Manufar Imamanciita ce ta annabci hanyar daya ce watau samar da al’umma ta musulunci adila da kokarin kare ingantaccer tafarkin musulunci. Saidai abin da zamani yake hukuntawa yana bambanta, kuma gwargwadon wannan bambancin dabaru da solon aiki na sabawa. Annabi (s.a.w.a)da kansa ya yi aiki da wani salo a farkon kira wajen tabbatar da manufofinsa bayan an kai wani zango kuma ya yi amfani da wani salon dabam.

Yayin da kirar take farkonta, tana kewaye da barazana da kalubale tana bukatar wani shirina musamman domin gudanar da aikin ida sako. Yayin da kuma ginshikan tsarin musulunci suka kafu, musulunci yasami kafuwa a Tsibirin Larabawa sai dabaru da salo suka sake.Tabbataccen al’amari na dindindin shi ne madaukakiyar manufar da sakon ya sauko saboda ita. Shi ne kuma kokarinsamar da al’ummar da a cikinta dan Adam yake iya tafiyarsa ta bidan kamala ta dukkanin fuskoki, a ciki ne kuma kwazo da karfin da ke boye cikin halittar dan Adam za su bubbugo. Anan fa kariyar wannan al’umma da tsarinta na musulunci suke.

Imaman shi’a, kamar yanda Annabi ya yi, suna faskantar ainihin wannan manufar ne watau kafa adalin tsarina musulunci mai wadannan sifofi kuma bisa wannan tafarki. Adai dai lokacin da ake kafa wannan tsarin ana kuma ba da karfi wajen kariya da tabbatar da dogewarsa.

Me kafa tsarin zaman jama’a da ci gaban gudanarsa yake bukata?. Da farkoyana bukatar wata manufa ko akida (aidiyolojiyya) mai shiryarwa wacce daga gare ta ne wancan tsarin yake bubbugowa kuma ita take zayyana shi. Na biyuyana bukatar karfin zartarwa mai iya kutsawa cikin wahalhalu da matsaloli da kangiya domin tabbatar da manufar tsarin. Mun san cewa aidiyolojiyyar (ko kuma akida) Imamai ita ce musulunci. Shi kuwa musulunci sako ne madawwami ga dan Adam, watau sakon da ke tattare da sinadarin wanzuwa da tabbatarsa.[ 8]

Idan muka lura da wadannan mas’aloli, cikin sauki za mu iya fahimtar manhajar Imamaina Ahlulbaiti kuma wasiyyan Annabin rahama (s.a.w.a). Wannan manhajar tana da sassa biyu malizimta juna:na farkon yana dangantaka da akida, na biyun kuma yana da alaka da samar da karfin zartarwa da zamantakewa. A sashen farko, Imaman suna fuskantarda kokarinsu da himomminsu ne wajen yada manufofin sako da kafa su, da tono duk wani kaucewa gaskiya da karkata wadanda masu bin son rai suke sabbabawa; da bayyana ra’ayin musulunci kan sababbin mas’aloli da raya alamomi wadanda suka rushe, sakamakon karo da amfanin ma’abota iko da masu fada a ji; da faiyace abin da ya boyu wa hankula na daga littafin Allah mai girma da sunnar Ma’aiki. Ana iya takaita zancekan nauyin sashen farko da cewa kare rayayyen sakon musulunci ne mai ginuwa, tsawon zamani.

A sashen na biyu kuwa gwargwadon abin da yanayin siyasa da zamantakewar al’ummar musulunci suke hukuntawa, suna kokarin samar da shimfida da ake bukata wajen karbar ragamar shugabancin al’umma da kansu a kusa, ko kuma shimfida domin imamin da zai ci gaba da tafiyar tasu a nan gaba ya kuma karbi shugabanci bayan zango mai tsawo.

Wannan a takaice shi ne manufar rayuwar tsarkakan Imamai, kuma wadannan su ne tsarin manufofinsu a game, saboda su suka rayu kuma dominsu suka yi shahada. Idan tarihin rayuwar Imamaiwanda ya zo mana ba ya tabbatar da ra’ayin da muka tafi a kai, to akidarmu kan Imamai ta isa ta sauwara mana rayuwarsu ta wannan fuskar kadai. Mene ne zatonka idan tarihi yana ba da shaida da take gamsar da ko wane mai bincike cewa rayuwar Imaman Ahlulbaiti tana kan wannan mafuskantar?.

Zango-zango na Tafiyar Imamanci

Tafiyar Imamanci ta fara ranar da Manzon Allah (s.a.w.a) ya bar duniya cikin watan Safar, shekara ta goma sha daya bayan hijira har zuwa wafatin Imam Hassan Askari (a.s) a watan Rabi’ul Awwal, shekara ta dari biyu da sittin bayan hijira. Cikin wadannan shekaru, tafiyar Imamaci ta ci zango hudu,wanda a kowanne Imamai sun dauki matsayi fitacce gaba ga mahukuntan al’ummar musulmi.

Zango na Farko

Wannan ya kunshi matakin kame bakiko mu ce matakin taimakawa mahukunta. A wannan zango jinjirar al’ummar musulunci ta yi fama da hadarin magabtawanda ya yi mata kawanya. Yayin da wadannan magabta suka ji barazanar da sakon musulunci yake masu, sai sukadana tarkon su daga wajen daular musulunci suna dakon wata dama domin su aukawa wannan sabuwar al’umma. A wani janibin kuwa akwai adadi mai yawana sabon-shiga musulunci wadanda hankalinsu ba zai iya daukar halin rarraba cikin al’ummar musulunci ba, saboda haka duk wata tsagar da ka iya faruwa za ta zama barazana ga tushen al’ummar da ma samuwarta. Na uku, karkatar da ta sami al’umma ba ta yi tsananin da har mutum kamar Amirul Muminina Aliyu ibn AbiTalib( a.s) wanda ya fi kowa kaunar kubutar sakon musulunci da al’ummarsa, ba zai iya jure mata ba. La’alla wanna halin da yasami jama’ar musulmi shi ne abin da Manzon tsira Muhammadu (s.a.w.a) ya yi ishara da shi lokacin da ya yi wasici ga wannan dalibinsa wanda yake farda, da ya yi juriya idan ya auku.

Wannan zangon ya dauki tsawon rayuwar Imam Ali (a.s) fara daga wafatin Manzon Allah( s.a.w.a ) har zuwa karbarsa halifanci. Imam ya yi sharhin matsayin da ya dauka cikin takardar da ya rubutawa mutanen kasar Masar yayin da ya nada masu Malik Ashtar hakimi. Ya ce:- “Sai na kame hannuna yayin da na ga masu juyawa sun juyawa musulunci baya, suna kira zuwa shafe addinin Muhamamdu (s.a.w.a). Saina ji tsoron idan ban taimaka wa musulunci da ahlinsa ba, zan ga tsagewa da rugujewa tattare da shi. Da haka zai faru, to da musibar da za ta sami musulunci ta fi tsanani a gare ni bisa ga kubucewar shugabancinku.……sai na bayar da gudumowata a abubuwan da suka faru”(1)

Yayin da shugabanci ya kauce masa sai ya hakura domin musulunci, lokacin da al’umma ta fuskanci hadura masu girma sai ya mike domin kare musulunci da al’ummarsa,yana mai shiryarwa da aiki a fagagen siyasa da soji da zamantakewa.Cikin Nahjul Balaga da sirar Imam Ali, akwai bayanai masu tabbatar da irin nau’in kokarinsa a zamanin shugabancinsa.

Zango Na Biyu

Zangon rike ragamar shugabanci. Wannan zangon ya dauki shekaru hudu da watatara na halifancin Amirul Muminina Ali (a.s) da kuma wasu watanni na halifancin dansa Hassan (a.s). Duk da wahalhalu da matsaloli da damuwa da tsanani da yake tattare da wannan zangon, kamar yadda duk wata hukuma mai ra’ayin juyi take fuskanta, mafi haske da ban sha’awan shafuffukan tarihi ne suka kunshi bayanin aikace-aikacesa, kamar su mu’amala mai cikakkiyar dan Adamtaka da adalci da tsananin lizimtar hukunce-hukuncen musulunci ta fuskoki dabam-dabam wajen gudanar da al’ummar musulunci da kuma rikon magana daya da fayyacewa da jaruntaka wajen aiwatarwa da kuma daukan matsayi.

Wannan zangona tarihin imamanci ya zama abin koyi wanda Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka yi kira domin aiwatar da shi a rayuwar siyasa da zamantakewa, tsawon karni biyu. Mabiya Ahlulbaiti suna kankame da son wancan yankina tarihin musulunci, suna neman dawo da shi, suna kuma auna tsare-tsaren da suke rayuwa cikinsu da wancan zamani mai ban sha’awa. Da wannan ma’aunin ne suke tuhumar tsare-tsaren da suka baudewa turbar musulunci. Mai ra’ayin sauyia al’ummar wacce da bidi’a da baudiya suka addaba. Wannan halin da al’umma take cikinsa ya dorawa Imaman da suka biyo baya nauyi mai tsanani da mas’uliya mai girma.

Zango Na Uku

Shi ne wanda ya dauki shekara ashirin,tsankanin sulhun Imam Hassan (a.s) a shekara ta 41 H zuwa shahadar Imam Hussain (a.s) a shekara ta 61 H. Bayan sulhun Imam Hassan (a.s) an soma wani nau’in aiki mai kama da sirri wanda kuma manufarsa ita ce maido da jagorancin musulunci wa ma’abotansa na gaskiya tun da lamarin yana bukatar dako har sai mulkin Mu’awiya ya kare. Cikin wannan gajeran lokaci an fuskantar da kokarin kyautata yanayi wajen yin shimfida ga zangona gaba.

Zango Na Hudu

Anan ya kamata mu yi bayani mai dan dama, tun da wannan zangon shi ya shafi laccarmu domin a ciki Imam Sadik (a.s) ya rayu. Cikin wannan zangon da ya dauki kusan karni biyu, tafiyar Imamanci ta cigaba kan wani dogon layi domin canja al’umma har ta dace da ra’ayin musulunci a dukkanin fagage wadanda suka hada da jagorancin siyasa. Tafiyar sashe ta yi galaba sashe kuma ta gamu da ci baya; tana tattare da nasara mai girma a fagen tunani da akida, tana cudanye da salo daban daban na dabarun gudanar da kira, abin adonta kuwa shi ne ikhlasi da sadaukarwa da fana’i da girman dan adamtaka a idon musulunci, halayen da suka kai kololuwa da kuma matukar kyau.Wannan marhala ko zango ya fara daga watan Muharam shekara ta 61 bayan hijira, bayan shahadar Imam Hussain bin Ali (a.s). Kamar yanda muka ambata, cikin wannan zangon, al’umma takara motsawa kwarai da gaske a fagen manufa (watau aidiyolojiyya) da tinkarar baude-baude ba jirkice-jirkice, wadanda matattarar iko da kuma kwakwalen jahiliyya suka wanzar.Waccar motsawa manufarta gudanar da aiyuka tsawo lokaci domin kafa hukumar musulunci mai tafiya bisa turbar Alkur’ani da sunnar Ma’aiki (s.a.w.a) kamar yanda Imam Ali (a.s) ya misalta.

A sarari yake cewa zartarda manhajar sauyi ‘yar asali a cikin al’ummar da tasami shekaru da dama cikin karkacewar tunani da aiki yana bukatar kwararan dabaru da shiri mai tushe.A wancan lokacin, al’ummar Annabi ta rayu karkashin hukumar Mu’awiya mai cike da karkata gaskiya da musanya ta da wata fuska ta jabu, halin da ya jefa jama’a cikin wani barci mai nauyi tare da nisanta tunanin mutane daga ruhin jagoranci mai bin ka’ida. Wannan baudewa ta kai har lamarin ya janyo kashe badadin Manzon Allah (s.a.w.a) a Karbala, al hali wannan al’umma tana ji tana gani, al’ummar da take fama da halin fargaba da rauni da fatattaka a hannun razanarwar banu Umayya.

Saboda haka saian yi aiki tukuru kafin a iya maido wa wannan al’umma ruhinta rasashshe da mutuntakarta wanda aka tattake, hakika aiki ne mai girma wanda al’umma take bukatarsa domin sake cancantar daukar sakon Islama da kama yunkurin ciccibar nauyin rike shi. Ba makawa ga wani sauyi tamkarwanda Manzon Allah (s.a.w.a) ya fuskanci al’ummar jahiliyya da shi, sannan daga bisani a karbi jagorancin jama’a.

Babu shakka dawo da rayuwa irin ta sauyi da sabonta ta aiki newanda bai kasa samar da ita tun farko wajen tsauri da muhimmanci ba. Tajdidi irinna juyi yana bukatar imani mai karfi da azama tabbatatta da hankali mai tsarawa da tunani farkakke, wayayye mai motsawa. To wane ne mai daukar wannan nauyin?!Waccar jama’ar da ta kasa tafiya tareda Imam Hassan (a.s) ta kuma kasa kai matsayin taimakawa Imam Hussain (a.s) lallai ba ta iya wannan aikin raya al’ummar musuluncin. Saboda haka dogaro ga wanna jama’ar babu abin da zai haifar illa cin tura da tabewa. Hakika motsin da Tawwabin suka jarraba da tawayen Mukhtar da Ibrahim bin Malik hujjace babba kan abin da muka fadi.

Matsayin Imam Sajjad (a.s)

Bayan waki’ar Ashura Imam Zainul Abidin Ali bin Hussain (a.s) yana da zabi biyu,su ne:- Imma dai ya sa sahabbansa shiga wata harka sakamakon motsawar rai da tausayi ya jefa su cikin wani garaje wanda wutarsa ba badewa ruruwarta zai yi sanyi, ya bice (saboda ba su da sifofin masu jihadi), sannan daga bisani a bar wa Banu Umayya filin ci gaba da danniya da babakere kan makomar al’umma wajen tunani da siyasa, ko kuma ya rinjayi tausayi da biri---bokon fushi da tunzura, kana ya tanadi share fage wa wani babban aiki wanda zai kai ga dawo da rayuwa irin ta musulunci. Bukatun share fagen su ne tunani mai jagorantan aiki da samar da wata salihar jama’a domin ta zama iri ga juyi da sauyi nan gaba, ya kuma nisanci idanun Banu Umayya, ya ci gaba da aiki haikan wanda manufarsa ita ce gina tunani da kuma dai-daikun matane. Da haka ne zai yi tafiya mai yawakan manufar kira, Imamin da zai gaje shi kuwa zai zama ya kara kusanto cimma manufar.

To wani zabiko hanya zai fifita?Ko shaka babu, hanyar farko ita ce ta sadaukarwa da daukar fansa, sai dai jagoran da yake shiri saboda harakar tarihi da kuma zamanin da tsawonsa ya zarce tsawon rayuwar Imam nesa ba kusa ba, sadaukar da rayuwarsa kawai ba ta isa. Dole ne yazama mai zurfin tunani, mai yalwar zuciya, mai hangen nesa mai dabara da hikima cikin al’amuransa. Wadannan sharrudda sun wajabtawa Imamzabar hanya ta biyun.

Imam Ali bin Hussain (a.s) ya zabi ta biyun duk da dauriya da wahal-halu da juriya da kuncin da ke tattare da wannan hanya. Ya ba da rayuwarsakan wannan tafarki (a shekara ta 95 bayan hijira).

Imam Sadik (a.s) ya sifanta mana yanayin da imami na hudu ya rayu a kai da kuma rawar da ya taka ta jagaba, ya ce:-“Bayan Imam Hussain (a.s) mutane sun juya baya banda mutum uku, Khalid Alkabuli da Yahya ibn Ummi Dawil da Jubair bin Mud’im.Daga bisani sai mutane suka dawo suka yawaita. Yahaya Ibn Ummi Dawil ya kan shiga masallacin Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce:- “Mun fita batunku kuma kiyayya da jiyewa juna sun bayyana a tsakaninmu …..”(Mumtahina aya 4.)

Wannan riwaya tana nuna halin da al’ummar musulmi take ciki bayanan kashe Imam Hussaini (a.s). yanayi ne mai ban tsoro, na fatattaka da raunin zuciya wanda ya game al’ummar musulunci a lokacin da waccan waki’ar ta faru, abin takaicinda ya auku a Karbala al’ummar har ma shi’ar Ahlulbaiti, ya fadi warwas. Wadannan ‘yan shi’an da suka gamsu da alaka da Imamai a zuci kawai amma a aikace sun karkatawa duniya da jin dadinta da kelkelinta. Irin wadannan sunanan tsawon tarihi hatta a zamanin nan namu, ba kuma kadan suke ba.

Daga cikin dubban masu da’awar shi’a a zamanin Imam Sajjad (a.s) mutum uku kadai suka rage bisa tafarki, mutum uku ne razanarwar Ummayawa da kamun da hukuma ke yiwa mutane bai sa su firgita ba, kuma son kubuta daga neman zaman lafiya bai girgiza azamarsu ba. Sun cigaba da amsa kira da fama bisa wannan tafarki da cikakkiyar azama da tabbata.Guguwar da ta kwashi al’umma tamkar wasu zauna gari-banza suka kuma bi manufar azzalumar hukuma, ba ta kwashi wadannan mutanen ba. Dayansu watau Yahya ibn Ummi Dawil ya kan mike a masallacin Madina ya yi huduba wa masu da’awar wilaya ga Ahlulbaiti yana mai baiyana bara’a gare su, kamar yanda ya gabata, yana kafa hujja da abin da Annabi Ibrahim (a.s) da mabiyansa suka fada wa masu bijirewan zamaninsa“ Mun fita batunku kuma kiyayya da jiyewa juna sun bayyana a tsakaninmu.” Ibn Ummi Dawil ya karanta wannan aya mai girma gaba ga masu da’awar wilaya ga Ahlulbaiti ne domin ya baiyana cikakken rabewa tsakanin sassan guda biyu:sashen ma’abota sako masu lizimta da kuma sashen masu zaman dirshan da sassautowa zuwa burace-buracen da basu taka kara sun karya ba da kuma rudi da abin duniya mara kima. Wannan rabewa tana tare da dukkanin kiraye-kirayen addini. Imam Sadik ya sifanta wannan rabewa na sassan biyu da cewa:- (Wanda ba ya tare da mu, to yana adawa da mu). Watauwanda duk ba ya sashen tauhidi to yana bangaren dagutu, babu wata ma’ana ga zama dan ba ruwanmu domin kuwa ba wani yankin tsaka-tsaki.

Wannan musulmi mai wilayar gaskiya ga Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a) watau Yahaya bn Ummi Dawil, da wannan kiran nasa ya baiyana rabewa tsakanin masu gamsuwa da wilayar da ta takaita ga motsin rai alhali suna kwanto cikin abubuwan amfanin kansu, suna nitse cikin dattin kuntataccen zatinsu,da masu lizimtar Imam a tunani da kuma aiki.Bisa dabi’a wannan rabewa tana nufin wuce gaban cewa batattun masu rinjaye su janye mutum, amma ba tana nufin watsi da batattun ba. Da wannan fikira ne wannan salihar jama’a ta fuskanci aikin tsamar da duk wani mai iya ‘yantuwa daga wahala da kangi. Sannu a hankali, sai wannan jama’a mai jihadi da dauriya ta yawaita, kuma da wannan ne Imam Sadik (a.s) yake ishara yayin da yace : “…… daga bisani sai mutane suka dawo suka yi yawa” Ta haka ne Imam Sajjad ya ci gaba da ba da himma kan aikinsa. Wannan aikin da wadansu matsayin da Imam ya dauka, wadanda za muambato nan gaba yana daga cikin abubuwan da suka janyo shahadarsa da ta wasu daga mukarrabansa.

Ban ga wani bayyanannen sa-in-sa da hukuma a rayuwar Imam Sajjad (a.s) ba.Kamar yanda muka ambata, hakan shi ne abin da ya dace da hikima. Domin da ya dauki irin matsayin da muke gani a rayuwar Imam Musa ibn Ja’afar (a.s) da imaman da suka biyo bayansa dangane da mahukuntan zamaninsa da bai iya ciyar da aikin sauyigaba har ya samar wa Imam Baqir (a.s) damar mayalwacin aiki ba. Da yayi haka daan hallaka shi da salihar jama’ar da take tare da shi.

Ba mu iya tsinkayar ra’ayin Imamna hakika dangane da masu iko illa nadiran, ko a nan ma bai kai matsayin fito-na fito ba. Iyakadai yana tabbatar da wani matsayi wa tahiri yana kuma fadakar da jama’ar da take kusa da shi kan abin da ya shafi aikinsa da harakarsa gwargwado. Irin wadancan matsayi sun hada da takardar suka mai tsanani da Imam da aikewa wani malami mai alakar kut-da-kut da Banu Umayya watau Muhammad bin Shihab Azzuhri. Muna iya fahimta a takardar cewa Imam yana magana ne da tsararraki masu zuwa tsawon zamani, ba da Azzuhri ba saboda Azzuhri ba mutumin da zai iya yantuwa daga kangin liyafar Banu Umayya da wasanninsu da mukamansu da al’farmarsu ba ne.Tahiri ya tabbatar da hakan, domin kuwa Azzuhri ya gama rayuwarsa ne cikinsa hidimarsu tare da rubuta littafi da kuma kirkirar hadisai saboda neman kusanci da su [9]

Saboda haka takardar Imam tana bayyana matsayinsa kan yanayin zamaninsa ne. Nassin wannan wasika yana nan cikin littafin Tuhaful Ukul.[ 10]

Akwai kuma wasikar da Imam ya aikewa Abdulmalik ibn Marwan a matsayin jawabikan wata wasikarsa wacce take dauke da aibantawa ga Imam saboda ya auri wata baiwar da ya yanta. Abin da Abdulmalik yake son baiyanawa Imam (a.s .) shi ne yana sane da duk abin da yake aikatarwa hatta al’amuran da suka kebance shi. Kazalikayana nufin tunatar da Imam (a.s) da dangantakarsa da shi da zimmar jan hankalinsa.

A jawabin da ya rubuta, Imam ya baiyana ra’ayin musulunci akan wannan mas’ala yana mai takidin cewa fifikon imani da musulunci ya kore kowani fifiko. Sannan ta hanyar kinaya, mai gwanin kyau, imam yayi ishara da hali rinna jahiliyya wanda iyayen halifa suka rayu a kai, la’alla ya hada har da rayuwar halifan shi kan shi. Ya ce:“ Babu karanta ga musulmi, karantar jahiliyya ce kawai karanta”.

Da halifa ya karanta kalmomin Imam (a.s) ya fahimci ma’narsu,cikakkiyar famta,kamar yanda dansa Sulaiman ya tsinkayi ma’anar yayin da ya ce da mahaifinsa: “Ya Shugaban Muminai alfaharin da Ali bn Hussaini ya yi hakika ya yi tsanani!” Saboda gogewarsa ta siyasa,halifa sai ya amsa wa dansa da abin da zai nuna masa cewa ya fi shi sanin abin da karo da imamin shi’a zai hafar. Ya ce da shi: “Da na kada ka fadi haka,domin wadannan harsunan Bani Hashim ne masu tsaga dutse, masu kamfata daga teku. Da ma ai Ali ibn Hussainiyana bayyana daukakarsa a yanayin da sauran mutane suke fankamar mika wuya.”

Wani misali mai nuna matsayin da Imam ya dauka shi ne yin watsi da wata bukatar Abdulmalik bin Marwan. Abdulmalik yasami labarin cewa akwai takwabin Manzon Allah (s.a.w.a) wurin Imam sai ya aiko yana neman ya ba shi kyautarsa ya kuma yi barazanar yanke abin da ake baiwa Imam daga baitul mali.Sai Imam (a.s) ya rubuto masa:-

((Bayan haka, Lallai Allah ya lamuncewa masu tsoronsa mafita ta inda suke ki, da arziki ta inda basu tsammani. Mai girman ambato ya ce (Lallai Allah ba ya son duk wani mai tsananin ha’inci mai yawan kafirci), sai ka duba ka gani wane ne daga cikinmu ya dace da wannan aya?[ 11]))

A wasu wurare muna ganin Imam Sajjad (a.s)yana motsawa cikin natsuwa da kuma garkuwa da tarbiyar dai-daiku da gina mutumtaka ta musulunci bisa karantarwar mazhabin Ahlulbaiti da yaki da baude-baude da sauransu. Da wannan aikin ne bisa hakika, ya dauki matakin asasina farko a kan tafarkin tabbatar da manufar mazhabin Ahlulbaiti wanda ita ce kafa jama’ar musulunci karkashin inuwar salihar hukumar musulunci bisa misalin hukumar Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali bin Abi Talib (a.s).Kuma kamar yanda muka ambata Imam (a.s) da mabiyansa basu nemi daidaitawa da hukuma mai kamu da azabtarwa ba duk da cewa sun bi hanyar da a zahiri tana daidaitawa da hukuma.

Daga cikin mabiyansa akwai wadanda aka kashe ta kazamar hanya, wasuan daure wasu kuwa an kore su nesa da mutanensu da gidajensu. Imam da kansa a kalla sau daya an tusa keyarsa a cikin kangi a cikin halin torartawa da wahala daga Madina zuwa Sham, sau da yawa kuma ya fada cikin nau ‘o’ in cutarwa da azabatarwa.Daga karshe halifan banu Umayya, Walid bin Abdulmalik ya ciyar da shi guba. Imam (a.s) ya yi shahada a shekara ta 95 bayan hijira.

Rayuwar Imam Bakir (a.s) Zarcewar Irin Rayuwar

Imam Sajjad An wayi gari mabiya Ahlulbaiti sun zama wata jama’a fitacciya mai dogaro da kai, kirar Ahlulbhaiti kuwa wacce ta dan tsaya ta kuma boye bayan shamaki mai kauri a dalilin waki’ar Karbala da waki’o’in da aka zubar da jini da suka biyo bayanta kamar waki’ar Harra da tawayen Tawwabun wadanda fir’aunancin Umayyawa ya haifar ta zama samamma ce mai yaduwa ta kuma bayyana cikin da yawa daga yankunan daular musulunci, musamman a Iraki da Hijaz da Kurasan. Tare da wannan samuwa, ta haifar da tsarina tunani da kuma aiki. Kwanakin da Imam Sajjad (a.s) ya sifanta da cewa : “ mabiyansa ba su wuce ashirin ba” sun kau sai ga Imam Bakir (a.s) yana shigo masallacin Ma’aiki (s.a.w.) a Madina jama’a mai yawa daga mutanen Kurasan da sauran lardunan duniyar musulmi suna kewaye shi, suna tambayarsa hukuncin musulunci kan al’amuran rayuwa dabam-dabam. Mutane kamarsu Dawus Yamani da Katada ibn Da’ama da Abu Hanifa da wadansu daga shugabannin mazhabobin fikihu suna tahowa domin su sha daga ilmin Imam ko kuma su yi jayayya da shi kan al’amura dabam-dabam.

A wannan zamaninan sami mawaka masu kare mazhabin Ahlulbaiti da bayyana manufofinsa. Daga cikinsu akwai Kumaitwanda ya sauwara mafi kyan surar da kwararru ke zaiyanawa a kan wilaya ta tunani da kauna ga mutanen gidan Manzon Allah (s.a.w.a) cikin kasidarsa mai suna hashimiyya. Hakika harsuna basu gushe ba suna nakaltar wadannan gwalagwalan wake yayin da zukata suke kiyaye su.

Ta wata fuska kuwa halifofin Banu Marwana cikin wannan dan lokacin, sun sami wata natsuwa da tabbatar mulki bayan Abdulimalik ibn Marwan (m.86H) cikin shekara ashirin da ya yi mulki, ya murkushe dukkan masu ja da mulkinsu, kuma yiwuwa cewa sansancewar aminci da natsuwa da halifofin Marwaniyawa na wannan lokacin ya samo asali ne daga kasancewar sun sami mulki tamkar wata ganima, sabanin magabatansu wadanda suka yi jan aiki kafin su kai ga mulki. Wannan natsuwa tasa halifofin baya shagaltuwa da wasanni da jin dadin duniya, tadodin da galibi suke tare da mai jin iko da alfarma da kuma girma.Ko mene ne ma dai, damuwar halifofin Banu Marwan da lamarin mazhabin Ahlulbaiti ta ragu a wancan lokacin, sai ga Imam da mabiyansa suna rayuwa kusan a ce cikin aminci daga farautar hukuma. Bisa dabi’a, Imam zai ci tafiya mai yawakan tafarkin tabbatar da manufofin mazhabin Ahlulbaiti a irin wannan yanayi ya kuma kai shi’anci wani sabon zango.Wannan kuwa shi ne ya bambanta rayuwar Imam Bakir (a.s) da ta saura. Ana iya takaita abin da rayuwar Imam, cikin shekaru goma shatara na imamancinsa (95-144H) ta kunsa kamar haka:-

Yayin da mahaifinsa Imam Sajjad (a.s) ya zo cikawa ya yi wasici da cewa dansa Muhammadu yazama Imami bayansa, gaba ga sauran ‘ya’yansa da danginsa, ya kuma ba shi wani akwati. Riwayoyi sunce akwatin cike yake da ilmi, sun kuma ce akwai makamin Manzon Allah (s.a.w.a) a ciki. Imam Sajjad (a.s) ya ce:- “Ya kai Muhammadu wannana akwati ka tafi da shi gidanka” Sannan ya ce:- “Hakika babu dinari ko dirhami a ciki, sai dai cike yake da ilmi”[12]

La’alla wannan akwati wata alamace mai muna cewa Imam Sajjad ya mikawa dansa jagorancin tunani da ilmi (tunda yana cike da ilmi) ya kuma mika masa nauyin jagorancin juyi (tun da yana kunshe da makamin Annabi (s.a.w.a)).

Gami da farawar Imam da mabiyansa faffadan aikinsuna yada koyarwar Ahlubaiti (a.s) farfajiyar yaduwar kiran ta kara fadi, ta sami sababbin fuskoki wadanda suka zarce fagenta daya gabata a Madina da Kufa.Sai ga ta tana yaduwa cikin larduna manisanta daga cibiyar mulkin Umayyawa. Lardin Kurasan na daga cikin wadancan wurare kamar yanda riwayoyin tahiri suka nuna.[ 13]

Yanayin tunani da zamantakewa mai kaskanta mutane ya zaburar da Imam da mabiyansa wajen haraka mai dorewa ba tare da gajiya ko kosawa ba domin sauya wannan mummunan yanayi da tabbatar da abinda Ubangiji ya wajabta na kawar da wannan baudiyar.

Suna ganin mafiya yawan mutane sun rusna wa gurbatanccen yanayin da Banu Umayya suka yada, suka nitse cikin kazantar abin duniya iya wuya har suka wayi gari tamkar mahukuntan nasu,basu fahimtar zance, kunnensu bai jin nasiha. “Idan mum kira su ba sa amsa mana”.[ 14]

Ta wata fuska kuwa, Imam da jama’arsa suna ganin bincike-binciken fikihu da ilmul kalam da hadisi da tafsirina karkata ne wajen dadada wa fir’aunancin Umayyawa da bin sonransu. Saboda haka duk hanyoyin dawowar jama’a kan katari da sun toshe, ba don zaburar mazhabin Ahlulbaiti wajen bayar da wajibinsa ba idan kuwa muka kyale su ba za su shiriya ta hanyar waninmuba[ 15]

Mazhabin Ahlulbaiti ya yi Allah wadai da malamai da mawaka da suka sayardakansu .An yi wannan sukan ne saboda kokarin farkarda zukatan wadancan malaman ko kuma zukatan mabiyansu. Imam yana fadawa Kumait, sha’irin Ahlulbaiti, da lafazin suka:- yabon Abdulmalik kayi?

Ya ce:- Ban ce da shi ‘ya shugaban shiriya’ ba, abin da na ce shi ne ‘ya zaki’ zaki kuma kare ne, ‘ya rana’ rana kuwa jamadatu ce, ‘ya kogi’ kogi kuwa mataccen abu ne, ‘ya maciji’ maciji kuwa kwaro ne mai wari, ‘ya tsauni’ tsauni kuwa kurman dutse ne. Sai Imam ya yi murmushi. Kumait sai ya rera wannan baitin gaban Imam:- Zuciyar da so ya tsare ya aure? Ban da yaranta tasa har da guri, Wannan mimiyar ta kafa mararraba tsakanin alkiblar Alawiyya da ta Umawiyya a daraja da kuma halaye ta hanyar dawwamammar zaiyanawa mai kyan gaske.

Wata rana Ikrima almajirin ibn Abbaswanda yake sananne ne, mai matsayin ilmi a cikin al’ummar wancan zamanin ya je yin mukabala da Imam sai haibarsa da natsuwarsa da ruhinsa da tunaninsa suka kama Ikrima. Abin da kadai ya iya fada shi ne:- “Ya dan Manzon Allah hakika na zauna gaban Ibn Abbas da waninsa sau da yawa amma irin abin da ya same ni yanzu bai taba samu na ba”. Sai Imam ya amsa masa da cewa:- “(Kai kana gaba ga gidaje wadanda Allah ya yi wa daukaka kuma ake ambaton sunansa a cikinsu)[16]

Ta wandansu fuskoki daban na ayyukan mazhabin Ahlulbaiti a wannan zangon kuwa, akwai jerin zalunci da fir’aunanci da kisa da azabtarwa da kora, da suka kewaye Ahlulbaitin Manzon Allah da mabiyansu ba don komai ba sai domin kokarin da suke yi na iza matacciyar zuciyar mutane da girgiza rayukansu wadanda suka yi sanyi da zaburar da kwantacciyar azamarsu da shiryar da su zuwa harakar juyi.

Alminhal bin Umar ya ruwaito cewa:- “Na kasance ina zaune tare da Muhammad bn Ali Albakir (a.s) sai wani mutum ya taho ya ce da shi: Yaya kuke? Sai ImamBakir( a.s) ya ce:- “Lokaci bai yi ba da za ku san yanda muke? Misalinmu a wannan al’umma tamkar Bani Isr’a’ila ne a da,ana yanka ‘ya‘ya maza ana barin (raya )mata. Ka saurara!Lallai wadannan suna yanka ‘ya‘yanmu maza suna barin ‘ya ‘yanmu mata. Larabawa sun yi da’awar fifiko bisa baibayi. Sai baibayin sukace : ‘Mene ne dalilin haka?’ Sai sukace : “Muhammadu balarare ne daga gare mu” Sai suka ce da su: “Kun yi gaskiya.”Kuraishawa kuwa suka yi da’awar cewa suna da wani fifiko bisa sauran larabawa. Sai sauran larabawa sukace “Mene ne dalili?” Sai suka amsa da cewa: ‘Muhammadu bakuraishe ne’. Sukace da su: ‘Kun yi gaskiya’. Idan mutanen nan sun yi gaskiya, to muna da fifiko bisa mutane domin mu zuriyar Muhammadu ne, mutanen gidansa kuma makusantansa masu kebanta da shi, waninmu ba ya tarayya da mu a wannan” Sai mutumin ya ce da Imam; “Wallahi ni ina son ku, ku Ahlulbait”. Sai yace da shi: “To ka dauki bala’i a matsayin riga, domin kuwa wallahi shi (bala’i) ya fi kusa da mu da kuma shi’armu bisa ga gudanar igiyar ruwa a cikin kwari. Da mu bala’i zai fara sanan ku”[ 17]

Da ganin alamar cewa mutumin ya girgiza saboda zaburarwar da ya ji sai Imam ya yi maza ya zana masa tafarkin kiran, ya fayyace.Shidai tafarki ne wanda aka shimfida shi da jini da kwalla, Imam kuwa shi ne madugun tafiyar, bala’i yana samunsa da farko kafin ya kai ga shia’rsa.

A tsakanin shi’arsa alakar Imamtana da wadansu sifofi kebantattu. Za ka gan shi cikin mabiyansa tamkar yanda kwakwalwa take a tsakanin gabban jikiyana ciyar da ruhinsu yana karfafa masu haraka da himma ba tare da yankewa ba. Akwai hujjoji a hannunmu wadanda suke bayyana wannan alaka mai bawa mabiya manufofi da karantarwa mabayyana da kuma tsara al’amuransu bisa tafarki hadadde, lasaftacce.

Misali; A farkon haduwar Jabir Alju’fi da ImamBakir( a.s) sai ya masa wasiyya da kada ya fada wa kowa cewa daga Kufa yake ya kuma yi fita irin ta mutanen Madina .Da wannan Imam yake koyar da darasin rike sirri ga wannan sabon dalibi wanda ya ga alamun iya rike sirri tattare da shi. Wannan dalibi mai cancanta sai yazama ma’abocin sirrin Imam. Tsakaninsa da hukuma kuwa lamarin ya kai ga abin da Nu’man bin Bashir yace :-

“Ina mai lizimtar Jabir bin Yazid Alju’fi yayin da muke Madina sai ya shiga wurin Abu’far (a.s) ya yi masa bankwana ya fitoyana farin ciki. (Mukakama hanya) har muka isa Al’ukairaja, daga kewayen Madina, a ranar Juma’a.Muka yi salla. Munkama tafiya kenan sai ga wani mutum dogo mai duhun fatar jiki da wasika a hannunsa. Sai Jabir ya karbe ta ya sunbace ta yasanya takan idanunsa. Sai ga shi arubuce( ( Daga Muhammad bin Ali ( Bakir) zuwa ga Jabir bin Yazid)), ga kuma danyen bakin yumbu a kanta. Sai yace da shi: ‘Yaushe rabonka da shugabana?’ Sai mutumin yace : ‘Dazun nan; sai ya ce: ‘kafin salla, ko bayan salla? Sai yace : ‘Bayan salla.’ Sai ya warware hatimin ya cigaba da karantawa, yana daure fuska har ya kai karshenta, sannan ya nade ta. Daga nan ban sake ganinsa yana dariya ko farin ciki ba har muka isa Kufa”.

Numan ya cigaba da cewa: “Mun isa kufa cikin dare, kashegari sai na tafi wajen Jabir Alju’fi saboda girmama shi, sai gashi ya fito bisa dokin kara yana rataye da wadansu kulle-kulle, tamkar yanda mahaukata ke yi, yana rerawa kamar haka: ‘Na san Mansur mutumin mutane; Mai umurni ba’a umurtansa’ da wasu baitoci irin wannan. Sai ya kalli fuskatana kalli tasa amma bai ce da ni komai ba, ni ma ban ce masa komai ba. Saina juya ina kuka saboda abin da na gani.Sai jama’a, babba da yaro, suka kewaye mu. Sai ya tafo har ya shigo dandali, yakama zagawa tare da yara mutane na cewa Jabir bin Yazid ya haukace. Wallahi bayan ‘yan kwanaki sai ga takardar Hisham Ibn Abdulmalik an aiko ta gareni kan batun shi. Tana cewa: ‘Ka binciki wani mutun mai suna Ja’bir Ibn YazidAlju’fi ?’sai mutane suka ce: ‘Allah ya kiyaye ka’.Da mutun ne mai ilmi da daraja da sanin hadisi, ya yi aikin haji sai ya haukace. Shi ne wancan a dandali bisa dokinkara yana wasa da yara. Sai na ce: “Godiya ta tabbatar ga Allah wanda ya hutar da ni kisansa’.[ 18]

Wannan misali nena alaka tsakanin Imam da mabiyansa na kusa. Yana bayyana tsananin tsarisa alaka kazalika yana nuna wani misali na matsayin hukuma kan mabiyan Imam. Wannan yana tabbatar mana cewa, masu iko ba cikin cikakkiyar gafala dangane da alakar Imam da mabiyansa na kusa suke ba, a’a, suna sa ido kan wadannan alakoki, suna kokarin gano su da kuma yin fito-na-fito da su.[19]

Sannu a hankali bangaren fito-na fito a rayuwar Imam Bakir (a.s) da ta shi’ayana tabbatar da wani fasali na rayuwar Ahlulbaiti (a.s).

Nassoshin tarihi da riwayoyin hadisi wadanda suke hannunmu basu faiyace samuwar wata matsananciyar harakar fama a siyasance wacce Imamyake aiwatarwa ba. Wannan rashin bayyanannar famayana da dalilai, kamar su wanzuwar wani yanayi na jabberanci da azabtarwa mai mamaye da rayuwar al’umma, abin da ya tisalta wa mabiyan Imam wadanda su kadai ne masu masaniya kan rayuwarsa ta fuskar siyasa da su yi riko da takkiya. Saidai martani matsananci wanda magabta (hukuma) suke mayarwa yana nuni da aikin jihadi mai zurfin tasiri da ake yi. Yayin da karfin mulki iri na Abdulmalik Ibn Marwan,wanda ake daukarsa a matsayin mafi karfin sarakunan Umayyawa, yayin da yake daukar mafi tsanani da tsaurin mataki kan Imam Bakir, ba wata tantama, wannan yana nuna cewa halifan yana jin tsoron hadarin da harakar da Imam da mabiyansa ke gudanarwa take tattare da shi ne. Da a ce Imam ya shagaltu ne da aiyukan ilmantarwa kadai ba tare da ya ba da himma kan gina tunani da tsare-tsare ba, to da sai mu ce ba maslaha ce ga masu mulki ba su matsawa Imam din lamba domin wannan mataki yana iya sa wa shi da mabiyansa su dauki matsayin fushi matsananci tamkar wanda mai tawayen nan ba’alawe Shahidin Fakh, watau Hussain bin Ali ya dauka.

A takaice, ana iya fahimtar matsanancin matsayin da hukuma ta dauka dangane da Imam Bakir (a.s) ta fuskar mayar da martanin da take yikan aiyukan Imam masu sabawa da ra’ayin masu iko.

Daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a karshen rayuwar Imam Bakir (a.s) akwai kiransa da aka yi zuwa hedkwatar halifancin Umayyawa watau Sham (Dimashka). Halifofin Umayyawa sun yi niyyar bincikar matsayin Imamkan hukuma. Wannan yasa suka yi umurni da kama shi da kuma kai shi Sham cikin cikakken tsaro. A wasu riwayoyi ance wannan umurni ya hada har da dansa matashi watau Ja’far Sadik.

An kawo Imam fadar halifa. Kafin haka Hisham ya yiwa jama’arsa shiftar yanda za su fuskanci Imam yayin da yake shiga. Abin da ya shirya shi ne, shi halifa zai fara bijiro da tuhumce-tuhumcekan Imam sannan jama’a su ci gaba.

Abubuwa biyu yake da niyyar cimmawa:na farko shi ne raunana azamar Imam da sanya masa rashin yarda da kai. Na biyu: Kokarin sukar Imam a cikin taron da ya hada jagaban jama’ar halifanci da kumana Imamanci a waje guda, sannan daga bisani a yada wannan cin zarfin ta hanyar kakakin fada kamar masu jawabi da masu wa’azin sarki da kuma ‘yan laken asiri, kuma da haka ne Hisham yake fatar samawa kansa nasara kan abokin hamayyarsa.

Da Imam ya shigo fadar halifa, sabanin yanda masu shigowa sukasaba da yin gaisuwa ga halifa da sunan shugaban muminai, sai ya fuskanci dukkan mahalarta yana mai nuni ga ilahirinsu, ya ce: assalamu alaikum. Sannan ba tare da jiran izininzama ba sai ya yi zamansa.

Wannan abin da Imam ya aikata ya cinna wutar hasada da kufe a zuciyar Hisham. Nan take sai ya fara jefa muggan maganganu yana cewa: ‘ Ya Muhammad Ibn Ali ba’a gushe ba wani daga cikinku yana rarraba kan musulmi, yana kiran mutane da su bi shi, yana kuma da’awar shi ne Imami (shugaba ) saboda wauta da karancin sani ………[20]Ya dai ci gaba da sukar sa.

Bayan Hisham yagama sai jama’a suka karba, suka ci gaba da maimata wadannan tuhumce-tuhumce da soke-soke. A tsawon wannan lokaci Imam uffan baice ba, yana sunkuye da kai cikin natsuwa, yana jiran damar ba da amsa. Yayin da mutanennan suka kare duk abin da ke gare su, wuri ya yi tsit, sai Imam ya mike ya fuskanci jama’a, ya yi yabo ga Ubangiji ya yi salati ga Manzonsa (s.a.w.a) kana ya yi jawabi.

Wannan jawabin ya kunshi kalmomi ne matakaita masu kwankwasa tare da bayyana rauni da kuma sakar akala tamkar kumakiwanda wadancan ‘yan amshin Shatan suka yi. Kazalika ya nuna matsayi da daukaka da Ahlulbaiti suke da shi, kamar yanda ma’aunan musulunci suka tabbatar, ya kuma wulakanta duk abin da halifa da jama’arsa suka mallakana kazamar dukiya da kuma iko. Ya ce:- ‘Ya ku mutane ina kuke tafe ne?Ina aka nufa da ku? Da mu Allah ya shiryina farkonku kuma da mu ne zai cikata (shiryar da) na karshenku. Idan abin gaggautawa na mulki naku ne to (ku sanicewa ) abin da aka jinkirtar na mulki namu ne sannan kuma babu wani mulki bayan namu saboda mu ne ma’abota kyankkyawan karshe. Allah mai girma da daukaka yana cewa: “Kuma kyakkyawan karshe ya tabbata ga masu takawa”[ 21].

Wadannan kalmomi matakaita wadanda suka kunshi wawaitarwa da kokowa da zalunci, da albishiri da bazarana, da tabbatarwa da kuma raddi duk a lokaci guda, ba shakka masu girgizawa ne tare da sa mai sauraro yin imani da cewa mai fadarsu shi ne ma’abocin hakki.Sakamakon haka, Hisham sai ya ga babu abin da zai yi face umarni da a jefa Imam kurkuku. Imam Bakir( a.s ) ya ci gaba da aikinsa na gyara hatta a cikin gidan kaso, al’amarin da ya yi tasiri matuka kan fursunoni. Da labari ya kai ga Hisham,sai ya ji tsoron cewa irin wannan farkawa za ta faru a hedkwatarsa wacce aka kiyaye daga tasirin Alawiyyawa. Sai ya yi umarni da fitar da wannan fursunan (Imam Bakir) tare da wadanda suka dauki ra’ayinsa da kuma aika su da daggawa zuwa Madinawanda shi ne mazaunninsa. Umarnin ya hada da cewa idan sunkama hanya kada kowa ya yi wata hulda da wannan ayari wanda halifa yake fushi da shi. Kada a ba su guzurin abinciko ruwan sha.

Bayan kwana uku ana tafiya ba kakkautawa abinci da ruwan da yake tare da su sai ya kare, a wani birni da ake kira Madin. Saboda umarnin Hisham, mutanen sun kulle kofifin birnin suka kuma ki sayarwa wadannan bayin Allah da komai. Yunwa da kishi suka yiwa mabiya Imam tsanani. Sai Imam ya haura kan wani tudu wanda daga bisan shi ana iya hangar cikin birnin ya daga murya da kyau ya ce:- “Ya ku mutan garin da mutanensa suka yi zalunci! Ni ne falalar Allah mai wanzuwa Allah yana cewa”:- Falalar Allah mai wanzuwa (bakiyyatullahi ) ita ce mafi alheri a gare ku idan kun kasance muminai, kuma ni ba mai tsaro ne a kanku ba”.

Mai riwaya ya ci gaba da cewa: Akwai wani tsoho tukuf a wannan birni, wanda ya ce da su: ‘Mutanena, wallahi wannan kira ne irin na Annabi Shu’aibu( a.s ). Na rantse da Allah idan ba ku fita kuka sayarwa wannan mutumin (abin da yake bukata) ba za’a kama ku daga birbishinku da kuma karkashinku. To lallai ku gaskata ni kuma ku bi maganta, dominni mai nasiha ne a gare ku’.

Mutanen garin sai suka amsa kiran dattijon nan, suka fita da gaggawa suka sayar wa Abu Ja’afar (Imam Bakir (a.s)) da sahabbansa da abin da suke bukata.[ 22]

Karshen wannan ruwayayana nuna mana irin dirar da halifan Abbasiyawa yake yi kan mutane da kuma jabberancinsa. Bayan mutanen birnin sun budewa Imam da sahabbansa kofofin gari sai aka rubuta dukkan abin da ya faru aka aikewa Hisham. Sai ya aiko da takarda zuwa hakimin Madin da umarnin cewa yakama wancan dattijon ya kashe. Allah ya ji kansa da rahama![ 23]

Tare da wannan hali, Imamyana nisantar duk wani matsanancin fito-na-fito da yin gaba da masu mulki. Ba ya daukar takobi ba ya kuma yardarwa masu garaje zare tokobi,yana dai shiryar da su ta hanyar hikima. Takobin harshe ma Imam ba ya zarewa idan ba aikinsana gyara da sauyi daga tushe ya bukaci hakan ba. Kuma bai yardarwa dan uwansa Zaid, wanda fushi da motsin rai ya kai masa iya wuya, yin tawaye ba. A ‘a, shidai aikinsa yana ba da karfi ne wajen shiryarwar da wayar da kai da tunani, hakan kuma gina tushen manufa (aidiyoloji) ne tare da kula da takiyya a siyasance.

Saidai wannan salon bai hana Imam ya bayyana wa mabiyansa “harakar imamanci” ba, kamar dai yanda muka yi nuni da shi, bai kuma hana shi karfafa musu babban burin shi’an nan na kafa sahihin tsarin siyasa mai bin tafakarkin Imam Ali (a.s) ba. Wani lokaci mayana tunzura zukatansu gwargwadon bukata saboda raya wannan burin.

Daya daga hanyoyin da Imam Bakir (a.s) yake kwadaitar da mabiyansaita ce ishara ga zamanin mai haske wanda zai zo nan gaba. Wannan kumayana nuna yanda Imam (a.s) ya kwatanta zangon da yake raye a harakar imamanci. Hakam ibn Uyainayana cewa: wata rana ina tare da Abu Ja’far (a.s) alhali gidan na cike makil da mutanen gidansa sai ga wani dattijo ya tafo yana tokarawa da mashinsa har ya tsaya bakin kofa ya ce:

Aminci da rahamar Allah da albarkarsa su tabbatar gare ka ya dan Manzon Allah (watau ya yi sallama). Sannan ya yi shiru. Sai Abu Ja’far ya amsa masa: Aminci ya tabbata gare ka da rahamar Allah da albarkarsa. Sai dattijo ya fuskanci mutanen gidan yace : assalam alaikum, sannan ya saurara har jama’a suka amsa sallama gaba dayansu. Sai ya fuskanci Imam yace : “Ya dan Manzon Allah ka kusantar da ni gareka, Allah Ya sanya ni fansarka. Wallahini ina kaunarku, ina kuma kaunar mai kaunarku. Kuma wallahi bana son ku tare da son mai son ku saboda kwadayin abin duniya. Kumani ina kin mai gaba da ku ina kubuta (bara’a) daga gare shi. Kuma wallahi bana kin shi ina kubuta daga gare shi domin wata kullalliya da ke tsakaninmu. Wallahini ina halatta abin da kuka halatta shi, ina haramta abin da kuka haramta shi ina sauraron umarninku. To shin kana mini tsammanin (alheri ) ,Allah ya sanya ni fansar ka? Sai Imam ya ce:“ Taho nan, taho nan” ya zaunar da shi gangarsa sannan yace:-

‘Dattijo! Lallai wani mutum ya zo wa babana Ali bin Hussain (a.s) ya tambaye shi tamkar abin da ka tambaye ni sai babana (a.s) ya ce da shi:- Idan ka mutu za ka zo ga Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali da Hassan da Hussain da Ali ibn Hussaini, kuma za’a sanyaya zuciyarka, za ka ga farin ciki, za’a tarbe ka da hutawa da kyakkyawan abinci tare da Masu daraja, Marubuta ( kiramun katibuna ). Idan kuma ka rayu za ka ga abin farun cikin da Allah zai sanya ka ciki za ka kasance tare da mu cikin kololuwar daukaka”.

Cikin gigicewa saboda girman wannan albishiri,dattijo sai ya ce:`Ta yaya,ya kai Abu ja’far?Sai Imam ya maimaita masa maganar da ya yi. Sai tsohon nan ya ce:Allahu akbar! Ya Abu Ja’far idan na mutu zan zo wa Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali da Hassan da Hussain da Ali ibn Hussaini, kuma zan ga abin farin ciki, a kuma sanyaya min zunciya, a tarbe ni da hutawa da kyakkyawan abinci tare da Masu daraja, Marubuta idan na cika? Idan kuma na rayu zan ga abin da zai faranta mini rai, kuma in zama tare da ku a kokoluwar daukaka?” Sai tsoho yakama kuka sai da ya kai kasa. Yayin da mutanen gidan Imam suka ga yanayin da dattijonnan ya shiga sai su ma suka kama kuka.Sai dattijo ya daga kai ya nemi Imam ya mika masa hannunsa. Sai ya sumbanci hannun ya sanya shikan idanu da kumatunsa sanan ya yi ban kwana ya fita. Imam yana kallonsa yana cewa:- Wanda ya so ganin wani mutum daga mutanen aljanna to ya dubi wannan (mutumin).[24]

Irin wannan fayyacewa tana karfafa ruhin buri a zukatan da suke rayuwa cikin yanayin zalunci da danniya, takan wanzar da tunkudawa zuwa ga manufar da ake bida wacce ita ce kafa adalin tsari na musulunci.

Shekara goma shatara na imamanci Imam Bakir (a.s) aka yi aiki na gudana bisa wannan mikakken layi mabayyani. Shekara goma shatara na koyarwa kan manufar gini da dabarun kare kai da tsare-tsare da kare haraka da takiyya da karfafa ruhin sa-rai da sauransu.

Shekara goma shatara ana gudanar da wannan tafiya mai tattare da kaya da munin hanya wanda yake bukatar kokari da ijtihadi mai yawa. Lokacin da wadannan shekaru suka kawo karshe, ranar rayuwarsa mai albarka ta zo faduwa, sai abokan gabansa suka yi ajiyar zuciya domin a zatonsu idan wannan jagora mai shiryarwa ya tafi za su huta da tushen farkarwa da izawawanda ya dade yana hana su hutu da barci.

Amma hakan bai yiwu ba domin Imam ya tabar da burinsu ya kumasa wannan dama ta kubuce musu saboda ya sanya wafatinsa ya zama tushen shiryarwa, musabbabin farkawa sannan kuma hanyar wayar da kai mai dorewa. Imam ya umarci dan saSadik( a.s) a karshen rayuwarsa, ya umarce shi da wani aiki wanda samfuri ne mai gwanin ban sha’awa daga samfur-samfur na takiyya da kuma salon kira wadanda Imam Bakir (a.s) ya yi amfani da su a zangon zamani wanda ya kebance shi A cikin ruwaya daga Abu Abdillah Sadik (a.s) ya ce: ‘Babana ya ce da ni: Ka ware abu kaza daga dukiyata saboda a mini zaman makoki na tsawon shekara goma a Mina a ranakun Minan”.[ 25] ..Ita wannanruwaya , wadanda suka yi bincike kan rayuwar Imam Bakir basu dube ta da kyau ba kuma sun gafala ga barin ma`anoni masu girma wadanda ta kunsa. Imam ya rasu ya bar dirhami dari takwas, yayi umarni da aware wani abu daga ciki a baiwa masu kukan mutuwarsa a Mina. Yin kukan rasuwar Imam a Mina ya kunshi ma`ana mai girma .Lallai shi aiki nena raya tushen nan da ya kasance a ko yaushe yana watsa hasken wayar da kai da farkarwa da kuma sanya ruhin kamuji da gwagwarmaya.

Zaben Mina kuwayana nufin wanzar da aikin a tsakiyar taron jama`a masu tahowa daga dukkanin sassan duniyar musulunci a dai dai lokaci guda daya tak da ake zaune wuri guda yayin aikin haji. Saboda dukkan ayyukan haji ana gabatar da su ne cikin halin motsawa ba tare da sararawa ba idan ba a Mina ba, inda ake kwana biyu ko uku, saboda haka alhazai suna samun isashshen lokaci domin sauraro da ganin kukan rasuwar Imam a wannan wuri zai kuma sa a yi tambaya kan ko wane ne wannan mamacin? Za’a kumasami jawabi wajen mutanen Madina wadanda suka yi zamani da shi. Za suce shi daya daga ‘ya’yan Manzon Allah ne, kuma shi ne malamin fukaha`u da masana hadisi. Za’a kuma tambayi dalilin da yasa ake makokinsa a wannan guri, shin mutuwarsa ta bambanta da ta saura ne? To wane ne ya kashe shiko ya sanya masa guba? Shin ya kasance wata barazana ga mulkin Umayyawa ne? Dadai sauran su.Gomonin tambayoyi aka yi ta jefowa yayin da ake kukan rasuwar Imam a wannan wuri, sannan masu tambaya suna samun amsa. Kuma labarin ya yi ta watsuwa cikin garuruwa, sako sako, bayan komawar alhazai kasashensu. Akwai kuma masu zuwa daga Kufa da Madina takanas saboda amsa wadannan tambayoyi da yada ruhin shi’a suna daukar damar taron musulmi, damar da ba’a samun tamkar ta a wancan lokacin.

Haka Imam ya rayu, haka kuma ya tsara al’amura domin abin da zai zo bayan wafatinsa. Tsira ta tabbata gare shi ranar da aka haife shi da ranar da ya yi jihadi da ranar da ya yi shahada a tafarkin Allah da kuma ranar da za’a tashe shi rayayye.

Imam Bakir (a.s) ya rasu yana da shekara hamsin da bakwai a duniya, a zamanin Hisham bin Abdulmalik, wanda yake daya ne daga sarakunan Banu Umayya wadanda suka fi iko. Duk da matsaloli da wahalhalun da suka addabi sarautar Banu Umayya a wancan zamanin wannan bai hana su aikata makida ga zuciyar shi’annan mai bugawa, watau Imam Bakir, ba. Hisham ya yi ishara ga barorinsa cewa su sanyawa Imam guba, da haka ne kuma ya cimma burinsa na hallaka mafi hadarin abokan gabansa.


3

4

5