• Farawa
  • Na Baya
  • 15 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 17063 / Gurzawa: 4339
Girma Girma Girma
Gudummawar Mace

Gudummawar Mace

Mawallafi:
Hausa

Dukkan hakkokina cibiyar Muassasar alhasanain (a.s) ne, kuma yada rubuce-rubucen tare da ambaton inda aka dauko su ba shi da matsala. Muassasar alhasanain (a.s)

Gudummawar Mace

Mawallafi: Mu'assasar Al-Balagh

GUDUMMUWAR MACE WAJAN GINA AL'UMMA

Wallafar: Mu'assasar Al-Balag

Fassarar: Yakubu Ningi

Gabatarwa

"Muminai maza da Muminai mata kuwa masoya juna ne; suna horo da aikata alheri suna kuma hani da mummunan aiki.." Surar Taubati, 9:71.

"Ya ku mutane, hakika Mu Muka halicce ku daga namiji da mace, muka kuma sanya ku al'ummu da kabilu (dabam-dabam) don ku san juna, hakika mafi girmanku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku tsoron Allah..."Surar Hujarati, 49:13.

Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai.Tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Muhammadu da tsarkaka daga lyalansa da zababbu daga Sahabbansa.

Zamantakewar dan Adam ba ta tabazama a wata rana cikin wadatuwa daga mace ba, alhali kuwa ita ke matsayin rabin samuwarsa ko ma fiye da haka. Dukwanda ya nutsa cikin zurfin tarihin dan Adam, zai ga cewa, hatta a lokutan da suka fi koyaushe ci baya, mace na da wata babbar gudummawa, duk kuwa da cewa wannan gudummawa ta faku daga gannai.

Idan har wayewar zamani ta fuskanci yin ta'akidi akan gudummawar mace (a rayuwa) da ta da yekuwar kiyaye hakkokinta, duk da cewa na bayyane ne kawai, to Musulunci tun farkon bayyanarsa, ya yi kira kan cewa mace ta taka rawarta a rayuwa, kuma ta dauki nauyin da ya hau kanta wajen ginin wayewar bil-Adama. Allah Madaukaki Ya ce

"Sai Ubangijinsu Ya amsa musu (cewa): `Hakika Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki ba daga cikinsu, namiji ne ko mace', sashinku daga sashi yake..." Surar AIi-Imrana, 3:165. Idan har mace a lokacin jahiliyya ta kasance wani kashi da aka yi watsi da shiwanda kuma ya fada karkashin tsiraici da kaskancin matsayi, to a cikin zamantakewar Musulunci ta dawo ta zama mutum wadda ke da abin koyi ga sauran muminai. Tarihin Musulunci ya shaida wasu lokuta masu muhimmancina wasu fitattun mata, kamar Uwar Muminai Khadija, da shugabar matan duniya Fadimatu (a.s.).

Wata kila karnonin karshe-karshen nan, saboda jahilcin da ya bayyana cikin wasu garuruwan Musulmi kamar sauran garuruwan duniya, sun shaida wani nau'i na kangiya ga mace daga irin tasirin ta na dabi'a, da hardiya ga tafiyarta na cika; abin da ke sanya tilascin yunkurar wa da tunatar da tunane-tunanen Musulunci da suka ta'allaka da ita, domin kuwa sanya mace a fagen da ya dace da ita cikin rayuwa, yana da babbar gudummawa cikin yunkurin al'umma da bunkasarta.

Babu shakka kan cewa wannan gudummawa ya saba da hakikanin yadda mace ke rayuwa a al'ummun da ke bin abin duniya na zahiri, wandanda suka janye wa mace karamarta da mutuncinta, suka so ta zama na'urar tallace-tallace a kafafan watsa labarai, kuma kayan wasa wadda masu kudi ke amfani da ita bisa son zuciyoyinsu; a karshe sai mace ta rasa matancinta, uwartakarta, daukakar tunaninta da taushin ranta, ba ta girbe komai daga hakan ma face ta'addanci, yin watsi da ita a gefe, yanke kauna, wahalhalu da shigar iyali cikin halin kaico da wastewa.

Binciken da ke hannunka, ya kai mai karatu, wata 'yar sassarface a kan gudummawar mace da ayyukanta cikin al'umma bisa tunanin Musulunci. Muna fatan zaisami lura da muhimmanci daga gare ka.

Dukka godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai .

Ma'anar Al'umma

AI'umma:na nufin tawagar nan ta mutane da ta hadu daga daidaiku, wadanda alakokina akida da amfanonin rayuwa iyakantattu suka hada su. Idan har wannan ne gamammiyar ma'anar al'umma, to al'ummar Musulmiita ce wannan al'umma wadda ake gina alakokin kuma ake tsara amfanoni a cikinta bisa asasin Musulunci. Za mu iya ta'arifin al'ummar Musulmi da cewa:

"Taron Jama'ar da a siyasance suke zaune a wani lungu na kasa, wadanda suka yi imani da Musulunci, kuma ake tsayar da alakokinsu da tsarin rayuwarsu a bisa asasin Musulunci".[ 1]

Don haka al'ummar Musulmi al'ummace ta akida, wadda ke da abubuwan da suka kebanta da ita da siffofinta da ke bambanta ta da wasunta na daga al'ummu.Ita al'umma ce da ta kebanta da tunane-tunanenta, halayenta, dokokinta, tsarin rayuwarta, dabi'unta da sannanta. Hakika AIkur'ani mai girma ya takaita wadannan siffofi da cewa "Rinin Allah, ba kuwa wanda ya fi Allah iya rini, kuma mu Shi muke bautawa". Surar Bakara, 2:138.

Mafarin AI'umma

Daga cikin al'amura na asasi da babu makawa a kan karanta su, binciken su da bin diddiginsu a ilmance, akwai mas'alar nan ta tashin al'umma da rayuwar zamantakewa, da sanin dalilai da musababbin shi (tashin); saboda abin da ke cikin na murdewa da haduwa da alakoki.

Don bayyana ra'ayin Musulunci game da tashin al'umma da haduwar rayuwar zamantakewa, bari mu karanta abin da ya zo daga ayoyin AIkur'ani wadanda ke magana game da sha'anin zamantakewa, kuma suke kira zuwa ga ginin al'ummar dan Adam, da rina rayuwar mutum ta hanyar hada gamammen zaman tare bisa asasai karfafa da akidu tabbatattu; ga wasu daga cikin ayoyin kamar haka

"Ya ku mutane, hakika Mu Muka halicce ku daga namiji da mace, muka kuma sanya ku al'ummu da kabilu (daban-daban) don ku san juna, hakika mafi girmanku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku tsoron Allah..." Surar Hujarati, 49:13. "Akwai daga ayoyinSaYa halittar muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku, lalle cikin wannan akwai ayoyi ga mutanen da ke tunani." Surar Rumu 33:21. "Shin su ne za su raba rahamar Ubangijinka? Mu ne muke raba musu arzikinsu a rayuwar duniya, kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hidima; rahamar Ubangijinka kuwa, ita ta fi abin da suke tarawa (na duniya)." Surar Zukhrufi, 43:32.

Darasi da bin diddigin wadannan ayoyi zai fitar mana da sabubba da dalilan tashin al'umma, wadannan sabubba kuwa su ne

1-Tubalin asalina ginin zamantakewa shi ne gamammun dokokin dabi'a na auratayya, wadanda suka hadu daga saduwar jima'i ga mace da namiji; ke nan su ne tubalin asasi na ginin rayayyen zamantakewa ta fuskoki biyu: Abin da zai auku a gaba da halayya.

Wannan alaka wadda ke nufin kariyar nau'i, kuma take tunkudawa zuwa jima'i don nufinjin dadi; ta dukkan bangarorinta biyu na halayya da `yan Adamtaka tana tsayawa ne a bisa asasin kauna, jin kai da samar da natsuwa.

Da wannan AIkur'ani ya dauki mace a matsayin tushen natsuwa ta hanyar tabbacin hankali da na zamantakewa ga namiji da rayuwar zamantakewa baki dayanta; wannan kuwa saboda kosar da rai daga son wani jinsi da jaraba ta jiki daga gare shi, suna haifar da kawar da damuwar rai da na zuciya, da cika irin faragar da rai din ke da shi, da sarrafa karfin bukatar jima'i da halayya don tabbatar da daidaici ga jinsosin biyu da ke tsaye a kan asasin cika ta hanyar gamammiyar dokar auratayya ta halitta.

Daganan nauyin da ya rataya a wuyan mace wajen gina rayuwar al'umma mikakkiya kuma mai lafiya ta jiki da zamantakewa ke iyakantuwa; saboda ita ce mabubbugar natsuwa, kauna, tausayi da jin kai cikin rayuwar zamantakewa.

2-Sanayya: Abuna biyu da ke sa mutum hada rayuwar zamantakewa, shi ne ka'idar nan ta sanayya tsakanin mutane, abin da ke tsaye a bisa asasin nan na jin son zaman tare wanda masana falsafa ke nunawa da cewa: 'Mutum mai zaman tare ne bisa dabi'a". Jarabce-jarabcena halayya da zamantakewa sun tabbatar da cewa mutum ba ya jin tabbas da kwanciyar hankali, kuma mutuntakarsa ba ta cika sai da zamantakewa da rayuwa tare da wasu.domin shi yana da matsananicyar bukata ta rai kuma mai Zurfi zuwa ga wasu, saboda haka ne ma Allah Ya fad'i cewa: ".-don ku san juna"; kalmar sanin juna na nuni ne ga boyayyen abin da ke tura mutum zuwa zamantakewa da hada al'ummar dan Adam.

3-Musayar amfanoni: Sababina uku daga sabubban gina al'umma shi ne musayar amfanoni na abin duniya dabam-dabarn. Hakika Allah Ya so daidaikun mutane susami cika da irin karfi da kwarewarsu ta tunani, jiki da hankali, kuma wannan cika na tabbata ne ta hanyar musayar amfanoni tsakanin daidaiku. Kowane mutum -shi kadai- yana da bukatu da wasu abubuwa da yake nema masu yawa, kuma ba ya iya samar wa kansa da su duka; don haka yana bukatar wasu, su ma suna da bukata da shi, wannan sabani cikin kwarewa wanda daga gare shi ne ake samun sabani cikin nau'o'in abubuwan da ake samarwa da hidimomin da mutum ke iya yi ga wasu, da musayar wadannan abubuwa da amfanoni da hidimomi don biyan bukatu, shi ne wanda AIkur'ani mai girma ya yi maganarsa da cewa

"..kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hidima..." Surar Zukhrufi, 43:32.

A bisa wannan asasi ne ayyukan zamantakewa ke faruwa, kuma (haka) ya fassara tubalin faruwar ayyuka a cikin al'umma don rayuwa tasami cika kamar yadda gabubban jiki ke cika wajen cika ayyukansu.

Hakanan AlKur'ani ke yi mana bayanin abubuwan da ke haifar da al'umma, mutuntaka da abin duniya. Kuma cikin dukkan wadannan tubaloli da asasai, gudummawar macena bayyana karara tun daga tushe, sawa'un ta bangaren abin duniya ne ko ta halayya ko aiki cikin rayuwar zamantakewa, ita babbar sashi ce ta al'umma. Hakika alkaluman mutanen duniya baki dayana nuna cewa adadin mata a duniyar dan Adam ya wuce adadin maza.

Ta wannan hange na cikan aiki da AIkur'ani ya bayyana a baya, za a iya ginin gudummawar mace kamar yadda ake ginin gudummawar namiji daidai-wa-daida cikin tsaikon manufofi da halayyar Musulunci, mace ba asasi ta biyu ba ce, ba kuma karin halitta ba ce, duk kuwa da cewa jarabce-jarabcen dan Adam sun tabbatar da cewa gudummawar namiji wajen gina ilimi da tattalin arziki ya fi gudummawar mace zurfi da yawa kuwa, amma nata gudummawar wajen hada shika-shikan ruhi don gina iyali ya fi gudummawar namiji girma nesa ba kusa ba kuwa.wannan shi ne abin da AIkur'ani ya nuna da cewarsa:­

"..Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don yasami natsuwa da ita". Surar A'arafi, 7:189. Kenan namiji shi ne yake natsuwa zuwa ga mata, ya sami tabbaci da rayuwa tare da ita, ita ce cibiyar haduwa kuma tsaikon aminci, kauna da soyayya. AIkur'ani na magana a kan 'natsuwa' a wurare da yawa, ta nan za mu iya fahimtar ma'ana irin wadda mace kan samar ga mijinta, za mu fahimce shi ta hanyar fadarSa Madaukaki

"Akwai daga ayoyinSa Ya halittar muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku.." Surar Rumu 33:21. Da fadarSa "..Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don yasami natsuwa da ita". Surar A'arafi, 7:189.

Za mu fahimci kimarkalmar `Natsuwa' a zaman tare ne yayin da muka san cewa AIKur'ani ya siffanta alaka tsakanin miji da mata da cewa alaka ce ta (Natsuwa, kauna da soyayya).Ke nan bari mu karanto kalmar `natsuwa' a wurare da dama cikin AIkur'ani, don mu san ma'anarta a zamantakewa da iyali. Allah Madaukaki ya fadicewa: ­"(Allah) Ya sanya muku dare a natse" wato mutane na nastuwa a cikin shi natsuwa na hutawa. Haka nan Allah Ya fadi cewa "Ka yi salla gare su lalle sallarka natsuwa ce garesu".wato suna natsuwa da addu'arka, kuma hankalinsu na kwanciya da ita. A wani wuri kuma Ya ce "Shi ne wanda ya saukar da natsuwa a zukatan Muminai"

Ya samar da tabbas da kwanciyar hankali.Malaman harshen larabci sun yi wadataccen sharhi a kan kalmar, tare da bayar da misalai, inda duk suka fassara `Natsuwa' da: Kwanciyar hankali, rashin jin kadaici da duk abin da ka sami tabbas tare da zama da shi kuma ka huta da rayuwa tare da shi.[ 2]

Da haka za mu iya fahimtar natsuwar da mace ke samarwa ga mijinta da iyalinta, wato shi ne: hutawa, aminci, dauke kadaici, tausayi, albarka da tabbaci, kamar yadda za mu iya fahimtar sirrin zabar wannan kalma mai ma'anoni da yawa, da AIKur'ani ya yi.

Hakika darussa na ilimi sun tabbatar da irin tasiri da yanayin rai da halin mutum ke da shi a kan daukacin harkokinshi cikin rayuwa; saboda a tabbace yake a ilmance cewa ayyukan zamantakewa, alhakin aiki da neman abin duniya, na daga noma, sana'a, hada-hadar siyasa, zamantakewa da hidima ga al'umma kamar ayyukan gudanarwa, aikin injinya, karantarwa, aikin likita, kasuwanci, fannoni da sauran irinsu wadanda kowane daya daga namiji da mace ke yi; duk suna da tasiri kai tsaye daga yanayinsu na halayya. Namijin da ke raye a tsakiyar matsalolin iyali da damuwar zuci da bacin rai, samun shi ga abin duniya kadan ne, hakanan nashadinshi wajen aiki da tunanin kirkiran wani abu cikin ayyukan shi su ma suna tasirantuwa, kuma matsalarsa na karuwa wajen alakarsa tare da abokan aikinsa da wadanda yake da alaka da su.

Da haka dabi'ar alakokin auratayya tsakanin namiji da mace ke taimakawa wajen kyautata matsayinnema da samun, ta hanyar bayyanar tasirinsu na rai da zuciya a kan iyawar mutum da harkokinsa na yau da kullum, da alakarsa da neman abinci da abokan aikinsa.

Ba ma kawai wannan ba, Uwa na taimakawa wajen bunkasa al'umma da gina ta a tunani, abin duniya, da dabi'u ta hanyar tarbiyyantarwa da fuskantar da su; domin yaron da ya tashi nesa daga kunci da damuwar rai da matsalolin iyali, zai tashi mai mikakkiyar mutuntaka, mai kyakkaywar alaka da mu'amala da wasu, haka mai bayar da gudummawa mai kyau ga al'umma. Sabanin yaron da ya tashi cikin yanayin iyali da ke cike da matsaloli da tashe-tashen hankula da mummunar mu'amala ga yaro, irin wannan zai tashi ne birkitaccen mutum, mai adawa cikin dabi'u da alakokinsa; don haka ne ma mafi yawan halayen laifuka da mujirimanci cikin al'ummu na samo asali ne daga mummunar tarbiyya.

Akwai kuma wani fage daga fagagen ginin al'umma da Uwa ke taka rawa a cikin shi kamar yadda uba ke takawa, wannan kuwa shi ne fagen tarbiyya mai kyau. Yaron da ke tashi a bisa son aiki da kiyaye lokaci, ake fuskantar da shi fuskantarwa ta karantarwa mikakkiya ta hanyar iyali, kuma yake cigaba da karatunshi, kuma yana gina iyawarsa na kirkire-kirkire, zai zama wani da ake amfana da shi ta hanyar abubuwan da yake samarwa na kwarewa da sannai na ilimi. Sabanin malalacin yaron da iyayenshi ba sa kwadayin fuskantar da shi ga aiki da samar da wani abu, domin shi zai zama na'ura ga wasu, kuma irin wadannan na haifar da ci baya mai yawa da ta6ar6arewar samar da abubuwa da daskarewar rayuwar zamantakewa, tattalin arziki da ilimi.

Haka fagagen gini ke kulluwa tsakanin tarbiyya, samarwa da bunkasar tattalin arziki, halayya da zaman lafiyar al'umma, kuma irin gudummawar mace wajen ginin zamantakewana bayyana a dukkan wadannan fagage.

Tubalin Ginin Al'umma

Alaka tsakanin daidaikun mutane a rayuwar zamantakewa kamar alakace tsakanin haruffan (wani) harshe, matukar wadannan haruffa ba su hadu ba kuma an tsara alakokin da ke tsakaninsu ba, gamammen ginin harshen ba zai samu ta yadda zai dauki tunanin mutum ya suranta jiyayyar rayuwar mutum gaba dayanta ba.

Haka ma daidaikun mutane, ba sa daukar siga ta mutuntaka da hada al'umma da ke da samuwarta da tushenta da ya bambanceta daga samuwa da tushen daidaiku sai sun shaje da wasu alakoki, sun tsaru da alakokin da ke tsara harkokinsu da halayensu, wadannan alakoki su muka sammata da Tubalan ginin al'umma, wadannan kuwa su ne:­

1-Akida: Alakar akida na daga mafi girman alakokin dan Adam wadanda ke hada daidaikun mutane ta mayar da su abu daya da ke hade kamar jiki daya; kamar yadda hadisin Annabi ya nuna haka da nassinshi "Za ka ga Muminai cikin tausayin junansu da kaunar junansu da jinkan junansu kamar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta koka, sai sauran sassan jiki ya dauki zazzabi da hana barci".[3]

Akida na da tasirorinta da abubuwan da take haifarwa na halayya da jiyayya a aikace cikin alakokin mutane baki dayansu, kuma tasirorinta na fadada daga gini zuwa kyautatuwa da kiyaye ginin zamantakewa; don haka za mu sami AIkur'ani mai girma yana bayyana wannan alaka da cewa

"Muminai maza da Muminai mata kuwa masoya juna ne; suna horo da aikata alheri suna kuma hani da mummunan alkl.." Surar Taubati, 9:71. Wannan aya mai albarka tana tabbatar da akidar kauna tsakanin maza da matan da suka yi imani da Allah Madaukaki da sakonSa, haka nan tana tabbatar da ka'idar tunani da halayya da suka fi kowace ka'idar ginin zamantakewa karfi. Macena shiga cikin wannan alaka a matsayin wani tubali na asasi, kamar yadda ya zo cikin nassin AIkur'ani, tana shiga cikin da'irar soyayya, kuma tana daukar alhakin gini, sauyi da kawo gyara ga zamantakewa kamar yadda namiji ke daukar na shi daidai wa daida; wannan na bayyana karara cikin nassin AIkur'ani da ambaton shi ya gabata a baya.

Da wannan mace ke samun wannan matsayina shakalin ginin zamantakewa, take kuma da nauyin da ya hau kanta ta hanyar alakar kauna ga daidaiku da al'umma da dukkan jinsosin biyu namiji da mace.

2-Dokoki da tsare-tsare: Ana ta'arifin doka da cewa ita ce: "Wasu gungun ka'idoji da aka tsara don halayyar daidaiku a cikin al'umma, wadanda kuma hukuma ke tilasta mutane a kan mutuntasu ko da kuwa ta hanyar yin amfani da Rarfi ne a lokacin da haka ya zama dole. "[4]

Don haka dokar zamantakewaita ce hanyar da ke tsara harkokin al'umma, take kuma hada daid'aikunta, kuma take fuskantar da su da sha'anoninsu, kamar yadda dokokin dabi'a (na halitta) ke tsara motsin rana da wata da sauran irinsu. In ba tare da doka ba ba, za a iyagina surar zamantakewa ko bunkasata ba.

Dokokin Musulunci kuwa, su ne dokokin da aka ciro daga AIKur'ani mai girma da Sunna mai tsarki don tsara al'ummar Musulmi daidai da tunani da manufofin Musulunci, don su suna magance matsaloli a kan asasin ilimi; don haka ne ma (dokokin) suka yi la'akari da dabi'ar rai da jiki ga kowane daya daga namiji da mace. Bayan an gina su a kan kai'doji na ilimi, ana kasa dokokin Musulunci zuwa kashi uku kamar haka

a-Dokoki da hukunce-hukunce da suka kebanci mace.b-Dokoki da hukunce-hukunce da suka kebanci namiji.c-Dokoki da hukunce-hukunce gamammu da ke hawa kan namiji da mace baki daya, wadannan su ke da fadi a fagagen dokoki da hukunce-hukuncen Musulunci. Wannan nau'ina tsari mai la'akari da jinsi, yana kallafa wa mace, kamar yadda yake kallafa wa namiji, wanda kowannensu ke motsawa a fagage biyu, na farko a fagen da ya ke6anta da jinsinsa kuma da yanayinsa na jiki; na biyu kuma ya hado dukkan al'umma da duk gininshi da haduwarsa.

3-AI'adun Musulunci: AI'ummar Musulmina da al'adunta wadanda ke matsayin wani tubali na asasi daga tubalan gininta wadanda suka kebanta da ita, wadanda kuma ya wajaba a kwadaitar a kansu a kuma tabbatar da su don kiyaye ka'idojinta.

4-Hidima da musayar amfanoni: Ta bayyana gare mu ta hanyar ayar nan mai girma: "..kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hidima..." Surar Zukhrufi, 43:32. Cewa bukatar zuwa ga wasu shi ne sababin asasina shigar mutum cikin taron mutane da hada ginin Zamantakewa; don su shiga aikin musayar amfanoni, kamar yadda rayayyun abubuwa da dabi'a ke musayar amfanoni tsakaninsu a fagensu na dabi'a da ya kebanta da su. Ta haka mutum zaisami biyan bukatarsa, kuma ya taimaka wajen cikar rayuwar dan Adam.

A sakamakon bunkasar bukatun mutum da al'umma, da sabanin daidaikun mutane daga maza da mata wajen kudura da iyawa ta hankali da jiki da rai; da karfin irada, sai kebance aikin kowa ya faru a cikin al'umma a hankali a hankali ta wata fuska, ta wata fuskar kuma tare da zabin mutum ga aikinsa na zamantakewa, wato nau'in aikin da zai yi cikin al'umma, kamar noma ko aikin likita ko kasuwanci ko karantarwa da wasun su, ko wani mai tsare-tsare daga gwamnatin Musulunci, ta fuska ta uku, wato wanda nauyin tsara al'umma da fuskantar da kudurarta ke wuyansa, don biyan bukatun daidaiku da magance matsalolin da ke samo asali daga bukatu daban-daban. Cikin abin da zai zo za mu yi nazari gudummawar mace a wadannan fagage, mu dan yi bayani akansu ko da kuwa a takaice ne.

Bambance-Bambancen Yanayin Halitta Da Ke Tsakanin Namiji Da Mace

Daya daga cikin mas'alolin ilimi da kowa ya mika wuya garesu a tsakanin masana halayyar dan Adam da likitanci, shi ne cewa kowane daya daga namiji da macena da yanayin halittarsa ta kebanta da shi, da cewa a dabi'ance dole a sakamakon haka ayyukan mace a cikin rayuwar zamantakewa ya saba da na namiji.don haka daidaitar rayuwar zamantakewa na bukatar kowane daya daga namiji da mace ya kiyaye bangare da yake ciki na jinsi, namiji ya kiyaye mazantarsa mace kuma ta kiyaye matancinta.

Hakika AIkur'ani mai girma ya yi bayanin bambanci halitta da ke tsakanin jinsosin nan biyu, abin da ya haifar da bambancin ayyuka, haka nan ya bayyana inda jinsosin biyu suka dace, Allah Madaukakin ya ce

"Kuma kar ku yi burin abin da Allah Ya fifita wasunku da shi a kan wasu. Mazana da sakamakon abin da suka aikata, haka ma mata suna da sakamakon abin da suka aikata.Kuma ku roki Allah daga falalarSa, hakika Allah Ya kasance Masani ne da dukkan komai". Surar Nisa'i, 4:32.

Haka nan hadisai sun yi ta'akidi a kan cewa mabayyanar kamala cikin mutuntakar kowane daya daga namiji da mace, suna da alaka da irin kebance-kebancen nau'i ga kowane daya daga cikinsu, da kiyayewarsa a kan su da daukakarsa da su, don haka hadisai suka hana kamantuwar mata da maza, kamar yadda suka hana maza ma hakan. Darussan halayyar dan Adam da gwaje-gwajen da aka gndanar

Haka nan ya zo cikin wani rahoto da jaridar Ittila'at ta kasar Iran ta kawo, a adadinta na 20,482, fitowarta ta 21 ga watan Maris na shekara ta 1995, daga wakilinta a Madrid ta kasar Spain, inda yake cewa "A shekara ta 1995 kashi 72 bisa dari na Rananan yara na raye ne a KarKashin ubanninsu, amma yanzu kimanin kashi 60 bisa dari daga cikinsu suna raye ne ba tare da ubanni ba. Yawan saki da fitinun uwaye sunsa maza sun gudu daga gidaje. Marubucinnan dan Kasar Amirka (David Blanc Horn), bayan ya bayyana wadancan alKaluman Kididdiga a cikin wani littafi na shi, ya kuma bayyana cewa: "Samun iyaye maza na gari na buKatar samun kyakkyawan misali na mata (wato yana bukatar samun mata na gari), wannan shi ne dalilin gudun iyaye maza daga gidajensu a Amirka.' Hakanan wakilin jaridar Faes ta Fcasar Spain, a wani rahoto na shi da ya bayar daga Amirka, ya bayyana cewa: Himmatuwa mai yawa da matan Rasar Amirka ya kare da cutar da ubanni da haramtawa `ya `ya inuwar ubanninsu".

A wani rahoto da jaridar Itiila'at, a adadinta na 20,407, fotowar ranar 31 ga watan Yulin shekara ta 1995 ta dauko daga ofishin kamfanin dillancin labaran Iran (IRAN) da ke London game da yanayin da kananan yara ke cikin a Biritaniya, am bayyana cewa "Majalisar Dinkin Duniya, a wani rahoto nata, ta yi kakkausar suka a kan yanayin da yara ke ciki a Biritaniya, da kuma dokoki da tsarin lura da yara a wannan kasa. Rahoton,wanda hukumar kiyaye hakkokin yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta shirya, ya nuna cewa dokokin da ake amfani da su a kan abin da ya shafi lafiya da ilimin kananan yara da shigar da su cikin al'umma a Biritaniya, ba a yi la'akari da cewa ya wajaba dokokin su lura da amfanonin yaran ba. Masana a hukumar kiyaye hakkokin yara ta Majalisar Dinkin Duniya na ganin cewa dokokin da suka kebanci kananan yara a Biritaniya sun fi mayar da hankali a kan yin ukuba da kulle yara da balagaggun matasan da suka karkace.

Daga cikin wuraren da ake suka a cikin wannan rahoto akwai karuwar yawan kananan yara da ke rayuwa cikin halin talauci a Biritaniya, da karuwar alkaluman rabuwar aure, da raguwar tallafin hukuma ga matalautan iyalai, da karuwar yawan yara da samari da ke sake suna kwana a tituna.

Hakanan masu rubuta rahoton sun bayyana damuwarsu da mummunar mu'amala da amfani da miyagun kwayoyi da fyade da ke fuskantar kananan yara.

Kamar yadda majiyoyin Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana, rahotannin majalisar game da yanayi kananan yara a kasashen Sweden, Norway da Denmerk sun yi soke-soke kamar irin na rahoton kasar Biritaniya".

Haka nan ya zo cikin jaridar Jumhuri Islami, a adadinta na 4,485 cewa "Ofishin kamfanin dillancin labaran Jumhuriyar Musulunci ta Iran a Born (ta fcasar Jamus) ya bayyana rahoton hukumar kidaya ta kasar Jamus (a shekara ta 1993) na cewa: adadin `ya `ya mata da ubanninsu ke tarbiyyantar da su su kadai yana ci gaba da karuwa a kowace shekara. Rahoton yakara da cewa: A halin yanzu akwai kimanin uwaye mata dubu 455 a jihohin Jamus ta gabas (wato kashi 12 bisa (Tari na jimillar uwaye mata da ke wadannan jihohi ke nan) da ke tarbiyyantar da ya yansu su kadai. A gefen wannan kuma, daga uwaye mata miliyan 7 da ke jihohin Jamus ta yamma, kimanin dubu 915 (wato kashi 12 bisa dari)na uwaye matan suna daukar dawainiyar tarbiyyar 'ya `yansu su kadai. Da wannan kenan zai zarna akwai kimanin uwaye mata miliyan daya da dubu 370 a tsakanin uwaye miliyan 9 da dubu 260 da ke tarbiyyar 'ya`yansu su kadai a tarayyar Jamus.

Kamar yadda wannan rahoto ya nuna, kashi 46 bisa dari na wadannan uwaye a gabashin Jamus, da kashi 30 bisa dari daga yammacinta duk ba su yi aure na shari'a ba; kashi 43 bisa dari na wadannan uwaye kuwa mazajensu sun sake su, kasancewar kuma rike 'ya’ya a hannun uwaye mata yake, ya zama musu dole su dauki dawainiyar tarbiyyarsu.

Haka nan a kasar Jamus akwai fiye da uwaye mata miliyan 9.26 da suka haifi 'yaya alhali shekarunsu na haihuwa bai kai 18 ba, kuma miliyan 5.4 daga cikinsu ko da yaushe ko rabin lokutansu suna ayyuka ne a wajen gida, banda kuma ayyukansu na gida da ayyukan tarbiyyar yara. Wani abu da ya kamata a bayyana a nan shi ne cewa yawan halin rabuwar aure a halin yanzu ya ninka yadda ya kasance a shekara ta 1968, wato ya karu daga dubu 65 da ya kasance a shekara ta 1968 zuwa dubu 135 a ‘yan shekarun nan, kuma a kowace shekara ana rijistar aurarraki dubu 390 a kasar Jamus, wadanda kashi 33 bisa dari daga cikinsu ke karewa da rabuwa, har ma wannan adadin a manyan garuruwa irin Hanburg ya kai kashi 50 bisa dari".

Har ila yau jaridar Ittila'at a adadinta na 20,503 ta dauko wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da kamfanin dillacin labaran Iran (IRAN) ya kawo kamar haka

"Taimakon kasar Amirka ga hukmar (UNICEF), bai kai na kasa daya daga cikin kasashe 20 masu arzikin masana'antu a duniya ba.Bankin kula da Kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ma ya tabbatar da haka, ya kuma kara da cewa: Duk da Amirka da ke bayar da taimakon dala biliyan 9.7, ita ke martaba ta biyu bayan Kasar Japan wajen taimakawa hukumar UNICEF, wannan adadin kudi kuwa ba komai ba ne face kashi .15 bisa dari din kudaden shiganta, alhali kuwa Rasar Holland da sauran kasashen yankin Sakandanebiya su ke marhala ta daya a wannan fagen; domin taimakonsu na kaiwa kahi 8 bisa dari na kudaden shigansu. Shugabannin hukumar UNICEF sun nuna damuwarsu akan raguwar taimakon da kasashe masu zarafi ke yi ga matalautan kasashe, har ma sun kara da cewa: 'Wannan abu na faruwa ne a daidai lokacin da rnuhimmancin taimakawa wajen kyautata lafiyar Kananan yara da kyautata yanayin ayyukan uwaye mata ke Karuwa a matalautan kasashe da tsananin gaske kuwa.' Kuma kamar yadda wannan rahoton ya nuna, a kowace shekara Kananan yara kimanin miliyan 13 a duniya ke mutuwa saboda cututtukan gudawa, bakon-dauro da sauransu.Haka nan kimanin Kananan yara miliyan 200 ke fama da rashin abinci mai gina jiki irin su vitamin A, abin da ke haifar musu da makanta!". Har ila yau ya zo cikin jaridar Ittila'at, a adadinta na 20,370, fitowar ranar 15 ga watan Disamban shekara ta 1994 cewa

"Kamfanin dillancin labaran Jumhuriyar Musulunci ta Iran (IRAN) daga Tehran ya bayarda labarin samuwar kananan yara kimaninrabin miliyan wadanda suka tarwatse a Amirka, a wasu lokuta ana aje su a wajen neman gina marayu, abin da al'ummar Amirka ke dauka a matsayin Kaskanci garesu. Wata marubuciya a jaridar Washintog Post mai suna Suzan Phildaz, ta rubuta cewa: 'Da yawa daga kananan yaran da ke da majibinta wadanda ke raye a karkashin iyalan da ke taimakonsu, suna fuskantar duka, wulakanci da mummunan mu'amala, kai!awasu lokuta ma ana kashe su.' Har ilayau Phildaz nacewa: 'Nau'in mu'amalar kowace al'umma tare da 'ya'yanta wata muhimmiyar alama ce da ke nuna hakikanin wannan al'umma.' Harila yau ta kara da cewa: Adadin kananan yara da ke watse sai kara yawa yake yi a Amirka kullum, har ta kai ga a wasu lokuta `yan sanda na gano jarirai a wuraren tara juji. A irin wannan hali taimakon uwaye matana kudade ba ya wadatarwa, maimakon haka, babu makawa a samar da wasu cibiyoyi don amsa manyan bukatun wadannan kananan yara."

Macea Inuwar Musulunci Ina Dalilin Sukar Matsayin Musulunci Game Da AI'amarin Mace?

Nazarin wannan al'amari (na hakkokin mace a Musulunci) na daga cikin manyan al'amurra na tunani da wayewa a wannan lokaci da muke ciki.Masu fada da Musulunci, `yan amshin Shatansu da wad'anda suka jahilci tunane-tunanen Musulunci, basu gushe ba suna ci gaba da kai hare-harensu na zalunci a kan tunane-tunane da shar'ance-shar'ancen Musulunci, suna masu ikirarin cewa anzalunci mace a Musulunci.

Ta hanyar nazari da bin diddigin asasan wannan yaki na tunani (game da hakkokin mace) tsakanin Musulunci da akidar abin duniya na zahiri da bai yi imani da addini ba, zai bayyana mana cewa tsaikon ka-ce-na-ce din duk ya kewayu ne a kan wani al'amari na asasi, shi ne tunanin rashin imani da addini da ke kira zuwa ga sakewa da kwance duk wani kaidi ga jima'i; wato wannan ra'ayi da a cikin shi mace ta zama wata na'urar jin dadi da biyan bukatun jaraba, wad'anda ke haifar da wargajewar iyali da al'umma da mace. Alhali kuwa Musuluncina kira zuwa ga karrama mace da dage wannan matsayi na wulakanci, da ba ta hakkoki da matsayin da suka ba ta daman yin kafada da kafada da namiji wajen gina rayuwa, da bayyana mutuntakarta a kan asasin 'yan Adamtaka madaukakiya, wadanda za mu yi bayaninsu a takaice a wannan babin.

Kafin mu fara magana akan wannan babi, ya kamata mu bayyana manyan sabubban wannan ka-ce-na-ce (na hakkokin mace), da dalilan sukan Musulunci na cewa ya tauye mata hakkokinsu.

Marubuta, manazarta, masu da'awa zuwa ga Musulunci, malamai da kungiyoyin kira da wayarwa ta Musulunci, masamman ma wadanda ke zaune a kasashen da ba na Musulmi ba, masamman a kasahen Turai da Amirka; dukkansu suna aiwatar da wajibin da ya hau kansu na bayanin wannan mas'ala mai muhimmanci ta hanyar bincike-bincike, nazarce-nazarce, da tarurrukan karawa juna ilimi a dukkan fagage, na siyasa, halayyar dan Adam, zamantakewa, iyali da zaman gari dabam-dabam.

Mafi girman dalilan da ke boye a karkashin wad'annan hare-hare da ake yi wa tunane-tunanen Musulunci a wannan fage, ana takaitasu cikin abubuwa masu zuwa

1-Ta'allaka wasu al'adu da suka ci baya da nazarin zamantakewa a Musulunci: Daga cikin al'amurra na asasi da ya wajaba a kan marubuta, wayayyun Musulmi da masu kira zuwa ga Musulunci su yi bayaninsu, akwai kuskuren da masu jayayya da Musulunci ko wadanda suka yaudaru da tunanin abin duniya na zahiri ko wadanda ma'anoni suka cakude musu kuma mummunar fahimta ta yi galaba suke yi, wannan kuwa shi ne cakudawa da rashin rarrabewa tsakanin abin da Musulunci ya ginu a kai na halaye da ka'idoji na Musulunci, da al'adun zamantakewa na ci baya da suka taso a wasu kasashen Musulmi da ba su waye ba. wadanda kuma suke sabawa ruhin Musulunci da ka'idojinshi da tsare-tsaren zamantakewa da alakokin jima'i da asasan alaka tsakanin namiji da mace; don haka sai suka shiga danganawa Musulunci -bisa jahilci ko da gangan- duk abin da suke shaidawa a kasashen Musulmi. A nan babu makawa mu yi ishara ga bambancin da ke tsakanin yadda al'ummar Musulmi take a halin yanzu da yadda ya kamata al'ummar Musulmi da ke tsaye a kan asasan Musulunci take, mun kuwa riga mun yi ta'arifin (bayanin ma'anar) al'ummar Musulunci.

Hakika wannan ci baya na zamantakewa da al'ummar Musulmi ke fama da shi, wani yanki ne na gamammen ci baya a fagagen ilimi, sannai, bunkasa, masana'antu, lafiya da saurarnsu.

Mummunan surar da wasu masu bincike game da zamantakewa ke cirowa daga yanayoyin zamantakewa dabam-dabam, kamar nazarin nan da aka gudanar a kan yanayin zamantakewar mace a kauyen Masar ko Iraki ko Maroko ko yankin saharar tsibirin larabawa da wasunsu; duk suna fitar da matsalolin mace ta hanyar hangen kauyanci da sahara wadanda suka ci baya kuma suke zaluntar mace.sa'an nan sai wadannan nazarce-nazarce suka shiga bayar da misali ga zamantakewar Musulunci da su.saboda mutanen wadannan wurare Musulmi ne. sun gafala da cewa wadannan tunane-tunane da ayyuka ba su da wata alaka da tunane-tunanen Musulunci da ayyukansa.kuma ba kawai suna karo da halayya da hukunce-hukuncen Musulunci ba ne. a'a har ma Musulunci ya kebe wani sashe daga tunane-tunanensa da dokokinsa da halayyarsa don yaki da su da sauya su.

2-Jahiltar Musulunci: Daga cikin matsalolin da ke tunane-tunanen Musulunci ke fuskanta a wannan lokaci da muke ciki, akwai jahiltar Musulunci da wasu ke yi, masamman ma a kasashen Turai, Amirka da sauran nahiyoyin da ba na Musulunci ba. Wadannanna jahiltar mafi karanci daga ka'idojin Musulunci.kai!suna ma yi mishi wata mummunar fahimta karkatacciya da ke siffanta Musulunci da siffofin: bata, ta'addanci, zubar da jini, ci baya da tsattsuran ra'ayi. Wadannan tunane-tunane na daga abubuwan da kungiyoyin Mustashrikai (masanan Turawa da su ke karantar halayyar kasashen Musulmi da addinin Musulunci don manufofi dabam-dabam),Sahyoniyawa( kungiyar Yahudawa masu tsaurin ra'ayi).da kungiyoyin Coci-Coci da mishan-mishan na Majami'an Kiristoci suka sana'anta.

Babuwata surar hakikanin Musulunci a kwakwalwar mutumin yamma, maimakon haka, duk abin da ke cikin kwakwalwarsa da fahimtarsa itace mummunan sura.kuma da mutumin yammaci ya san hakikanin Musulunci da ya yi maraba da shi.kuma da ya bude hankalinsa don yin muhawara ta ilimi.haka da ya karbe shi da `yanci da budaddiyar kwakwalwa.

A takaice za mu iya karanta wannan babbar matsala cikin jawabin da shugaban kasar Jamus Roman Hutsog ya yi a ranar 10/1/1995 a lokacin bikin girmama baturiyar nan masaniyar kasashe da al'adun Musulmi (Mustashrika) a kasar Jamus, Anamari Shamel, mai adalci cikin abubuwan da take rubutawa da fada, a lokacin bukin bata kyautar zaman lafiya da kungiyar marubutan kasar Jamus ta ba ta. Ya fadi abin da ya fada ne yana mai mayar da martani ga masu sukan kyautar zaman lafiya da aka baShame[ saboda kawai tana kariya ga tunane-tunanen Musulunci, kuma tana mu'amala da shi bisa gaskiya da adalci.tana kuma kira zuwa fahimtarsa da sauya mummunar surar da kafafan watsa labaran Turawa ke yi ga Musulunci da Musulmi; sai ya ce:­

"Akwai wani al'amari da ke bayyane karara cikin alaka da mu'amalarmu da Musulunci a wannan lokacin da muke ciki. Ba za mu yi karya ga ra'ayin da ya watsu a Jamus ba, idan mukace : abin da ke zuwa cikin tunanin mafi yawanmu a duk lokacin da aka ambaci Musulunci shi ne: `Dokokin uKuba na rashin tausayi' ko `rashin sassaucin addini' ko zaluntar mace ko tsaurin ra'ayi irin na adawa. sai dai wannan Kuntata yanayi ne da ya wajaba mu sauya shi; mu tuna da ambaliyar nan ta hasken Musulunci wadda tun kafin Karnoni shida ko bakwai ta kiyaye wa kasashen yammaci wani sashe babba na tsofaffin abubuwan tarihi, wadda kuma a wancan lokacin ta sami kanta a gaban wani irin nau'i na tunanin yammaci; babbu shakka (wannan ambaliya) ta ji cewa ashi (wannan nau'i na tunanin yammaci) mai tsaurin ra'ayi ne mara sassauci".

A yankin karshe na maganarsa, shugaban na Jamus ya yi bayanin dalilin adawa da Musulunci da cewa shi ne jahiltar da Turawa suka yi wa Musulunci, kan haka za mu same shi yana cewa

"Ashe ba ta yiyuwa dalilin rashin fahimtarmu ga Musulunci ya zamashi ne ginuwarsa akan asasai masu zurfi na al'umma mai riKo da addini alhali mu masu riko ne ta fuska mai girma da wani tafarki da bai yarda da addini ba?danhaka ya tabbata ya ya za mu yi mu'amala da wannan nazari mai matsala? Shin ya yi daidai mu siffanta Musulmi masu tsoron Allah da siffofin `masu tsattsauran ra'ayi, 'yan ta'adda' don kawai mu mun rasa ingantaccen riskar yadda izgili yake a zukatan mabiya wasu addinai, ko kuwa saboda mun zama ba za mu iya bayyana irin wannan ingantacciyar fahimta ba?".

Daga nan sai shugaban na Jamus ya bayyana cewa shi bai san Musulunci yadda ya kamata ba sai bayan da ya karanta littaffan wannan Mustashrika mai adalci (wato Shamel), sai ya ce "Tsinkayata ga irin wannan babban nau'i na fuskance-fuskance cikin tarihin Musulunci da hakikaninsa a halin yanzu bai fara ba sai ta hanyar littafan Anamari Shamel, akwai kyakkyawan zaton kuma cewa wasuna ma sun fuskanci irin wannan gwaji. Hakika muna bukatar musanya abin da ya kuke manana fahimtar sashinmu ga sashi... ".

Sannan sai shugaban na Jamus ya yi kira da a fahimci Musulunci don shata wani matsayi game da shi koma bayan matsayin da ya ginu a kan jahiltar sa, sai ya ce "Ina yin ikirari da cewa a gabanmu babu wani zabi face kara samun masaniya game da duniyar Musulmi matukar muna nufin yin aiki don kare hakkin dan Adam da Dimokuradiyya".

Sai kuma ya kara da cewa "Hakika babban dalilin son sanin Musulunci da fahimtar wadatacciyar wayewar nan ta shi ya samo asali ne daga kasancewarmu cikin wata wayewa da ba shi ba. Hakika kuwa uwargida Shamel ta fadaka da wannan bukata ta rai, ina fata kuma wannan ya zama shi ne yadda wasuna masu yawa ke ji.." . "Hakika Uwargida Anamari Shamel ta share mana fagen haduwa da Musulunci.. [11]

Hakika wannan rikici na bayar da kyautar zaman lafiya a kasar Jamus ga masaniyar kasashe da al'adun Musulmi (Shamel) a shekara ta 1995, da dacewan `yan siyasa da wayayyu daga ma'abuta tunani, shehunnan malamai, Turawa masana kasashen Musulmi da al’adun Musulunci, ma'abuta fanni da adabi a kasar Jamus, wadda ake dauka daga cikin manyan daulolin duniya a tarihin wannan zamani namu, da nasarar bangaren Shamel, wato masu kira zuwa a fahimci Musulunci a bisa hakikaninsa don shata matsaya, daga cikin wadanda ke sahun gaba na wadannan kuwa har da manazarta da 'yan siyasa, a cikin su har da shugaban kasar Jamus wanda muka karanta muhimman zantuttukansa; duk yana nuna mana wani abu ne mai girma daga abubuwan da ke wuyan Musulmi marubuci, manazarci kuma ma'abucin fanni da adabi.kamar yadda ya ke wuyan cibiyoyi da malaman addini.wannan kuwa shi ne nauyin yin bayanin Musulunci a bisa hakikaninsa mai haske.wanda yake tafiya tare da hankali da zuciya cikin sauki.tahanyar aiki da tafarkin nan na AIkur'ani wajen kira zuwa ga Allah Madaukaki:­

"Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangijinka da hikima da wa'azi mai kyau, kuma ka yi muhawara da su kan abin da yake shi ya fi kyau.." Surar Nahali, 16:125.

Wannan ka-ce-na-cena wayewa da ya faru a Jamus da yadda ya kare da nasarar masu kira zuwa ga fahimtar Musulunci, yana tabbatar mana da girman Musulunci, da shirin da d'an Adam ke da shi na fahimta da karbar Musulunci, duk kuwa yadda ya kai da isa. Wannan ka'ida da AIKur'ani ya tabbatar daita da fad'arsa:­

"Ku tafi zuwa ga Fir'auna don kuwa hakika ya yi tsaurin kai. Sannan kugaya masa magana mai taushi, ko watakila zai karbi gargadi ko kuma ya ji tsoron (azabar Allah)". Surar Daha, 20:43-44.

Daga nan za mu fahimci cewa Alkur'ani na horon masu kira zuwa ga Musulunci da su kare tunanin imani, kuma su yi magana ta Musulunci (hatta) ga wadanda suka fi kowa adawa da tsanantawa da kin imani, kuma kar su fada tarkon yanke kauna har su rufe kofar yin muhawara ta tunani.domin yanayi da halayen da ba a karbar zantukan Musulunci a cikinsu suna da sabani daga wata marhala zuwa wata, kuma daga wani yanayi na rai, zamantakewa, al'adu da tarihi zuwa wani; domin (da yawa daga) abin da aka ki karba a yau, ana karbarsa a gobe, kuma abin da aka ki yarda da shi ta wannan hanya, ana karbarsa ta wata hanyar.

3- Sha'awa da karkacewa ta jima'i: Watakila daga mafi bayyanar sabubban wad'annan da ke kira zuwa ga 'yancin mace ko sakewar jima'i akwai sababi na sha'awa da karkacewar jima'i. Hakika Alkur'ani mai girma ya yi magana game da wannan sababi, ya kuma bayyana had'arinsa da mummunar akibarsa. Allah yana cewa

"...Sai wasu suka maye gurbinsu a bayansu, wadanda suka watsar da Salla suka kuma bi sha'awace-sha'awace; to ba da dadewa ba za su gamu da gayyu (wani kwari nena azaba a jahannama)". Surar Maryam, 19:59.

Ya kuma ce "An kawata son sha'awace-sha'awace na mata da `ya'ya da dukiyoyi tsibi-tsibi na zinariya da azurfa ga mutane..." Surar Ali-Imrana, 3:14.

Ya kuma ce "..Wadanda kuwa suke bin sha'awace-sha'awace suna so ne su kauce mummunar kaucewa". Surar Nisa'i, 4:27.

A cikin wadannan ayoyi Alkur'ani na bayani ne game da hadarin sha'awace-sha'awace, da cewa suna samo asali ne daga jahilci da ya samo asali daga mummunan akida, da karkacewa daga madaidaiciyar hanya, wanda bayaninsu ya zo karara a wata ayar

"Wadanda suke kawo cikas a hanyar Allah, suna kuma son ta karkace alhali su masu kafircewa ne da ranar lahira". Surar Hudu, ll:l9 .

Abin da muka gabatarna alkaluman kididdiga suna magana a kan karkacewar jima'i saboda wasu dalilai na ayyuka da Alkur'ani ya yi bayaninsu ga mutane ya kuma tsawatar a kansu.

4-Mugun kullina gado da tsoron Musulunci: Daga cikin sabubban kai hari ga Musulunci da yi wa matsayinshi game da mace bakin fyanti, akwai mugun kullin da aka gada a kan Musulunci da yin aiki wajen munanta ka'idojinsa da daukakan halayensa tun daga bayyanar Manzon Allah (s.a.w.a.), wanda kuma ya ci gaba har zuwa yakokin gicciye. Duk wannan saboda tsoron Musulunci a matsayin shi na wani shiri na wayewa wanda ke rushe amfanoninsu da suka haddasa, kuma ba su gushe ba suna haddasawa a duniyar Musulunci, kuma yana gamawa da wuce-iyakarsu da mamayarsu ga duniya, masamman ma duniyar Musulmi; masamman bayan bayyanar wayewar Musulunci da bayyanar Musulunci a matsayin wani shiri da yunkure-yunkurenshi ke ginuwa, kuma wani rayayyen gwajin da ya aikatu ta hanyar tsayar da gwamnatin Musulunci a Iran.

Hakika kuwa manyan kasashen duniya sun watsa karti datsare-tsarensu, suka watsa'yan barandansu a ko'ina don yaki da wayewar musulunci, da sukar shirinshi da masu kira zuwa gare shi da wadanda ke dauke da tutarsa.