Hakkokin Da Suke Tsakanin Mutane
Kowane mutumyana
da hakkoki masu yawa a kan dan'uwansa mutum musamman abokin zamantakewa na kasa ko gari, ko makaranta, da duk wani waje da alaka ta kan hada juna kamar wajan aiki. Babban ma'aunina
hakkin junanmu a kanmu shi ne wanda ya zo a cikin Hadisai na cewa: "Mu duba duk abin da muke so a yi mana sai mu yi wa mutane shi, mu kuma duba duk abin da muke ki a yi mana shi sai mu guji yi wa mutane shi"[29]. Misali kana kin a wulakanta ka, kuma kana son a girmamaka, to anan
sai ka ki wulakanta mutane kuma ka girmama su.
Wannan hadisi da za a yi aiki da shi, da Duniya gaba daya ta zauna cikin aminci, da ta juya ta zama kamar aljanna, da so ya game tsakanin mai kudi da talaka, da mai ilimi da maras ilimi, da miji da mata, da 'ya'ya da iyaye, da malami da dalibi, da mai mulki da wanda ake mulka, da dukkanin nau'i na mutane gaba daya.
Wannan hakkoki kuwa sun hada nisantar cutar da waninmu ta kowace hanya kamar dukako
da kuwa dalibinmu ne, amma a kasashenmu duka wani abu ne mai sauki. Kai a makarantun Furamare dana
Allo har yakan yi muni kwarai; mai dukan ba ya neman izinin Shugaban musulmi, ko uban da, sai a yi ta jibga ko mai kankantar abu.
Duka ba ya halatta koda kuwa uwa ce ga danta sai da izininuba[
30], ko dukan uba ga dansa ko wanda Shugaban musulmi ya ba wa izini. Shi ma uban a matsayin tarbiyyantarwa da yazama
sai ta hakan, kuma ba mai cutarwa ba. Ko kuma miji ga mace mainushuzi[
31], shi ma a mataki na uku na karshe[32] kuma ba mai cutarwa ba, sai kuma Shugaban musulmi ga mai laifi kamar a haddi ko ladabtarwa.
Daga cikin hakkin mutum a kan waninsa shi ne ya shiryar da shi abin da zai amfanar da shi, kamar hakkin mutane a kan likita na ya nuna musu hanyar tsafta da kare lafiya, da yadda zasu tsara abinci da abin sha mai sanya lafiya, da magunguna, musamman ta hanyar Gidan Radio da Talabijin; Da maras lafiya zai tafi wajan likita sai ya cutar da shi to dole ne ya biya shi diyya, amma idan da gangan ne sai a yi masa kisasi.
Kamar yadda yake wajibi ne a kan malami ya shiryar da al'umma kuma ya ilmantar da ita, mai kudi kuwa ya yi odar abin da yake tattalin rayuwa na al'umma kuma ya sanya farashi da talaka zai iya saya cikin sauki, haka ma injiniya ya kyautata mota ta yadda ba zata zama hadari ga mai hawanta ba, mai gini kuwa ya kyautata shi.
Hakanan
yana kan mai sayan kaya ya girmama mai sayarwa shi ma mai sayarwa ya mutunta mai saya, likita da marasa lafiya, mai kudi da talaka, malami da marasa sani, mai haya da dan haya, mai aiki da shugaba. Bai kamata ba shugaba a ma'aikata ya rika kallon masinja kallon wulakanci, hakki ne akansa
ya girmama masinja, ya tuna shi ma dan kasa ne kamarsa kuma ma'aikaci da bai fi shi da komai ba a wajan Allah sai dai idan ya fi shi takawa domin ita ce ma'aunin fifiko. Haka ma dan hayar mota kamar Taksi da Bos (hayis) kada yazama
idan ya ga fasinja yana ganin naira goma ne ko biyar ko ishirin, hakki ne a kansa ya ga mutum yake kallo kafin ya ga Naira ishirin, kuma ya yi mu'amala da shi ta mutunci da girmamawa tsakanin juna.
Haka nan alakar na kan mota da na kan jaki, da na jirgin sama da na kasa[33], duka daya ne a wajan Allah kuma ba mai fifiko sai da takawa, rashin kiyaye wannan da mantawa da Allah ya sanya rashin kiyaye hakkin juna.
Wani misali a kan haka shi ne; wata rana wani mai kudi shahararre ya taba kade wani almajiri da mota a kan titi, maimakon mutane su nemi ya bayar da kudin magani a kai almajirin kyamist tun da shi ba shi da mutuntaka domin ba ya ganin almajirin mutum ne kamarsa don ko taba shi bai yi ba, sai suka zo suna ba shi hakuri. Har da cewa: Ai da ma haka almajirai suke basa
jin magana. Haka mutakabbirin ya hau mota ya wuce! Shi kuwa bawan Allahyana
ta nishi har ya samu da kyar ya taka. Su kuwa mutanen ba mai ji a jikinsa cewa an jiwa
wani mutum daga cikin mutane masu hakki kamar kowa ciwo! Wallahi da dabba ce aka kade da sun fi ba ta muhimmanci!.
Daga cikin hakkin mutun a kan dan'uwansa mutum taya shi bakin ciki idan wani abu ya same shi musamman ma dan'uwa na jini ko na Addini da makwabci, kamar idan an yi masa mutuwa to ya kamata ne bisa koyarwa ta Manzo (S.A.W) a yi abinci kwana uku daga makwabta ana kai musu kamar yadda ya koya mana kyawawan dabi'u da fadinsa: "Ku yi wa iyalan Ja'afar abinci hakika wani al'amari da ya shagaltar da su ya same su"[34]. Amma abin sai yazama
bisa akasi, maimakon a kai gidan mutuwa, sai ya zama su ne kuma za a shagaltar da su da ciyar da masu taruwa.
Idan muka waiwayi alakar mai kudi da yaronsa al'amarin ya kai ga ana iya samunyaron
Alhaji da rashin lafiyarsa bai fi a kashe kudi kankani a kansa ba ya warke amma yana iya mutuwa alhali Alhajin da ya yi wa hidima a gida, da shago, da kanti, shekaru masu yawa yana gani sai dai ya mutu. Wani kumayana
aiki karkashin uban gidansa amma canja riga mai tsada yana iya tayar da mugunyar tsatsar nan ta hassada a zuciyar uban gidan, sai ya ce da shi: Ka tattara naka ka yi gaba kuma ka bar min shagona.
Akwai wata kabila da galibinsu ba ma musulmi ba ne amma har bikin yayeyaron
shagonsu suke da shi. Idan kuwa ka duba bangaren kere-kere to anan
sun yi nisa, sannan wasu abubuwan idan kana nemansu ranar lahadi to lallai ka wahala domin sun kulle shaguna. Don haka idan ana son mafita da cigaba
ya zama dole ne a siffantu da siffa ta gari a bar hassada da kyashi, a cire duk wata dauda daga zuciya. Idan wani ya cigaba
ta hanyarmu sai mu gode wa Allah, amma rashin kishin kai da son ci gaban juna, da rashin kyawawa dabi'un musulunci ya sanya ana danne hakkin juna, kuma mu sani cewa dukkan ayyukanmu suna da hisabi a Lahira.