Hakkokin Dan'uwa A Kan Dan'uwansa
Da farko muna iya cewa musulmi duka 'yan'uwan musulmi ne saboda haka hakkin da yake hawakan
dan'uwa yana hawa tsakaninsu amma dan'uwa na jini yana da kari kan dan'uwa na musulunci da kamar wajabcin sadar da zumuncinsa. Daga cikin hakkokin dan'uwa akan
dan'uwansa su ne: Yi masa nasiha da kare shi daga wahalhalun da zaka iya taimaka masa wajan maganinsu kamar taimakonsa wajan sana'a, da samun magani, da kudin makaranta, da biyan bukatunsa, da kokarin kawar masa da talauci, da taimakonsa a kan makiyinsa.
Malam Muzaffar a Littafinsayana
cewa: Daga cikin mafi girma da kyawun abin da Musulunci ya yi kira zuwa gareshi shi ne 'yan'uwantaka tsakanin musulmi a kan duk sassabawarsu da martabobinsu da mukamansu.Kamar yadda mafi munin abin da musulmi suka yi a yau da kuma kafin yau shi ne, sakacinsu wajan riko da wannan 'yan'uwantaka ta musulunci.
Domin mafi karancin koyarwar wannan 'yanuwatakarita
ce "Ya so wa dan'uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, kuma ya ki masa abin da yake ki wa kansa, kamar yadda zai zo a hadisin Imam Sadik (A.S).
Ka duba ka yi tunani a kan wannan dabi'a mai sauki a mahangar Ahlul Baiti (A.S), za ka samu cewa yana daga mafi wahalar abin da zaka iya samu wajan musulmi, da musulmi zasu yi wa kansu adalci su san addininsu sani na hakika, su yi riko da wannan dabi'a ta so wa dayansu dan'uwansa abin da yake so wa kansa, da ba a ga zalunci daga wani ba ko ketare iyaka, ko sata, ko karya, ko yi da wani, ko annamimanci, ko zargi da mummuna, ko suka da karya, ko wulakanci, ko girman kai.
Idan da musulmi sun tsaya sun fahimci mafi karancin ma'anar hakkin 'yan'uwantaka a tsakaninsu kuma suka yi aiki da ita, da zalunci da ketare iyaka sun kau daga bayan kasa, kuma da ka ga 'yan Adam sun zama 'yan'uwa suna masu haduwa da juna cikin farin ciki, kuma da mafi daukakar sa'adar zamantakewa ta cika garesu, kuma da mafarkin malaman falsafa na da na samar da mafificiyar hukuma ya tabbata, da sun kasance masu musayar soyayya a tsakaninsu, da ba su bukaci wasu hukumomi da kotuna ba, ko 'yan sanda, ko kurkuku, ko dokokin laifuffuka, da dokokin haddi da kisasi ba, kuma da ba su rusuna wa 'yan mulkin mallaka ba, kuma da dawagitai ba su bautar da su ba, kuma da kasa ta canja ta zama aljannar ni'ima kuma gidan sa'ada.
Bugu da karin cewa, da dokokin soyayya sun jagoranci rayuwar 'yan Adam kamar yadda Addini yake so na koyarwar 'yan'uwantaka, to da kalmar neman adalci ta bace daga harsunanmu da ma'anar cewa, ba za mu zamanto muna bukatar adalci da dokokinsa ba ballantana har mu bukaci amfani da kalmarsa, saboda dokokin soyayya sun isar mana wajen yada alheri, da aminci, da sa'ada, da murna, domin mutum ba zai bukaci amfani da adalci ko dokoki ba, sai idan ya rasa soyayya daga wanda ya wajaba ya yi masa adalci, amma a wajan wanda yake nuna masa kauna da soyayya, kamar da, da dan'uwa, sai dai ya kyautata musu ya hakura da dama daga abubuwan da yake so, duk wannan sakamakon so da kauna ne daga yardar zuciya, ba don adalci ko masalahar kansa ba.
Sirrin haka kuwa shi ne cewa mutum ba ya so saikansa
da kuma binda ya dace da kansa, kuma mustahili ne ya so wani abu ko wani mutum da yake wajen ransa, sai dai idan yana da alaka da shi, kuma ya shiga ransa. Kamar kuma yadda yake mustahili ne ya sadaukar da zabin kansa gareshi a cikin abin da yake so yake kuma kauna saboda wani mutum da ba ya sonsa, ba ya kuma kaunarsa, sai dai idan yana da wani imani mai karfi da ya fi karfin son ransa, kamar imani da kyawun adalci da kyautatawa, a yayin nan yana iya sadaukar da dayan abubuwan da yake so, ya yi fansa da shi saboda son wani.
Farkon madaukakan darajoji da suka wajaba musulmi ya siffantu da su, su ne; ya kasance yana jin hakkin 'yan'uwantaka ga sauran mutane, idan kuwa ya kasa wannan, to zai gaza aikata mafi yawa da haka saboda galabar son ransa, saboda haka yana wajaba a kansa ya cusa wa kansa akidar son adalci, da kyautata biyayya ga shiryarwar musulunci, idan kuwa ya gaza hakan to bai cancanci ya zama musulmi ba sai dai a suna, kuma ya fita daga soyayyar Allah (S.W.T), kuma Allah ba ya da wani buri a kansa kamar yadda zai zo a hadisi mai zuwa.
Saudayawa sha'awar mutum takan yi galaba akansa
, sai ya zamanto mafi wahalar abin da yake fama da shi, shi ne, ransa ta yarda da adalci, balle kuma ya samu imani cikakke da ya fi karfin sha'awarsa.
Saboda haka ne ma kiyaye hakkin 'yan'uwantaka yazama
daga mafi wahalar koyarwar addini idan babu imani na gaskiya game da 'yan'uwantaka. Don haka ne imam Abu Abdullah (A.S) ya ji tsoron yiwa
sahabinsa "Almu'ula Bn Khunais" bayanin tambayarsa game da hakkin 'yan'uwantaka sama da abin da ya kamata ya bayyana masa, domin tsoron kada ya koyi a bin da ba zai iya aiki da shi ba.
Sai Mu'ula yace[
52]: Menene hakkin musulmi a kan musulmi?
Sai Abu Abdullahi yace
: yana da hakkoki bakwai wajibai, babu wani hakki daga cikinsu sai ya wajaba a kansa, idan ya tozarta daya daga ciki to ya fita daga soyayyar Allah da biyayyarsa, kuma Allah ba shi da wani buri a gareshi.
Saina
ce masa: A sanya ni fansa gareka!Mecece?
Sai yace
: Ya Mu'ula ni ina mai tausasa wa gareka, ina tsoron ka tozarta ba zaka kiyaye ba, ko kuma ka sani ba za ka aikata ba.
Nace
: Babu karfi sai da Allah.
Yayinnan
sai Imam (A.S) ya ambaci hakkoki bakwai, bayan ya fada game da na farkonsu cewa: "Mafi saukin hakki daga cikinsu shi ne ka so wa dan'uwanka kamar yadda kake so wa kanka, ka kuma ki masa abin da kake ki wa kanka".
SubhanalLahi!Wannan shi ne hakki mai kankanta, to yaya wannan hakkin mafi kankanta yake a garemu yau mu musulmi?
Kaicon fuskokin da suke da'awar musulunci amma basa
aiki da mafi kankantar abin da ya wajaba na daga hakkokinsa. Abu mafi ban mamaki kuma shi ne, a dangata wannan rashin ci gaban da ya samu musulmi ga musulunci, alhalin laifi bana
kowa ba ne sai na wadanda suke kiran kansu musulmi amma ba sa yin aiki da mafi karancin abin da ya wajabta musu da su yi aiki da shi na koyarwar addininsu.
Domin tarihi kawai, kuma don mu san kawukanmu da takaitawarta zamu ambaci wadannan hakkoki bakwai wadanda Imam (A.S) ya bayyana su:
l- Ka sowa
dan'uwanka musulmi abin da kake so wa kanka, kuma ka ki masa abin da kake ki wa kanka.
2- Ka nisanci fushinsa, ka bi yardarsa, kuma ka bi umarninsa.
3- Ka taimake shi da kanka, da dukiyarka, da harshenka, da hannunka, da kafarka.
4- Ka zamanto idonsa, dan jagoransa, kuma madubinsa.
5- Kada ka koshi, shi kumayana
cikin yunwace, kada ka kashe kishirwarka shi kuma yana jin kishirwa, kada ka zama a suturce shi yana tsirara.
6- In kana da mai hidima shi kuma dan'uwanka ba shi da mai hidima, to wajibi ne ka tura mai hidimarka, sai ya wanke masa kaya, ya dafa masa abinci, ya gyara masa shimfida.
7- Ka kubutar da rantsuwarsa, ka amsa kiransa, ka gaishe damaras
lafiyarsa, kuma ka halarci jana'izarsa. Idan kuwa ka sanyana
da wata bukata sai ka yi gaggawar biya masa ita, kada ka bari har sai ya tambaye ka, sai dai ka gaggauta masa.
Sannan ya rufe maganarsa da cewa: "Idan ka aikata haka to ka hada soyayyarka da soyayyarsa, kuma soyayyarsa da soyayyarka".
Akwai hadisai da yawa da suka kunshi ma'anar da ta zo a wannan hadisi daga imamanmu (A.S), wasunsu daga littafin Wasa'il a babobi daban-daban.
Tayiwu wasu su yi tsammanin cewa abin nufi da 'yanuwantaka a hadisin Ahlul Baiti (A.S) ya kebanci tsakanin musulmi ne wadanda suke daga mabiyansu a kebance, amma komawa ga ruwayoyinsuyana
kawar da wannan zato, koda yake sun kasance ta wani bangare suna tsananta musantawa ga wanda ya sabawa tafarkinsu kuma ba ya riko da shiriyarsu. Ya wadatar ka karanta hadisin Mu'awiya Dan Wahab da yace[
53]:
Na cemasa[
54]: Yaya ya kamata gare mu mu yi tsakaninmu da mutanenmu, da kuma wadanda muke cudanya da su na daga mutane wadanda ba sa kan al'amarinmu".
Sai Yace
: "Ku duba Imamanku wadanda kuke koyi da su ku yi yadda suke yi, na rantse da Allah!su
suna gaishe da maras lafiyarsu, suna halartar jana'izarsu, suna ba da shaida garesu da kuma a kansu, kuma suna bayar da amana garesu".
Amma 'yan'uwantakar da Imamai suke son ta daga mabiyansu, tana saman wannan 'yan'uwantaka ta musulunci, Kuma ya isar ka karanta wannan muhawara tsakanin Abana Bn Taglib da Imam Sadik (A.S) daga hadisin[55] da Abana ya rawaito da kansa yana mai cewa: Na kasance ina dawafi tare da Abi Abdullah (A.S) sai wani mutumi daga cikin mutanenmu ya bujuro mini wanda ya riga ya tambaye ni in raka shi wata biyan bukatarsa, sai ya yi mini ishara, sai Abu Abdullahi (A.S) ya gan mu.
Sai yace
: Ya Abana kai wannan yake nema?
Nace
: Na'am.
Yace
: Shin yana kan abin da kake kai?
Nace
: Na'am.
Yace
: Maza ka tafi zuwa gare shi ka yanke dawafin.
Nace
: Koda ya kasance dawafin wajibi?
Yace
: Na'am.
Abana yace
: Sai na tafi, bayan nan -wani lokaci- sai na shiga wajansa (A.S) na tambaye shi game da hakkin mumini. Sai yace
: Bari kada ka kawo wannan! Ban gushe ba ina sake tambaya har sai da ya ce: Ya Abana ka raba masa rabin dukiyarka, sannan sai ya kalle ni ya ga abin da ya shige ni, sai ya ce: Ya Abana ashe ba ka san Allah ya riga ya ambaci masu fifita wasu a kan kansu ba?
Nace
: Haka ne!
Yace
: "Idan ka ba shi rabin dukiyarka ba ka fifita shi ba, kana fifita shi ne kawai idan ka ba shi daya rabin!
Nace[
56]: hakika a yanayinmu mai ban kunya bai dace ba mu kira kanmu muminai na hakika.Mu muna wani waje ne, koyarwar Imamanmu (A.S) tana wani wajen.
Kuma abin da ya Shigi zuciyar Abana zai Shigi zuciyar duk mai karanta wannan hadisin, saidai
ya juya fuskarsa kawai yana mai mantar da kansa shi kamar wani ake wa magana ba shi ba, kuma ba ya yi wa kansa hisabi irin na mutumin da yake abin tambaya.