Abu Na Biyu
:
Hukuncin Hada Salla Biyu Da Dalilansa Gun Mazhabobi Idan mun san lokutan salloli biyar dalla-dalla, muka kuma san lokacin da yakebanta da kowacce da kuma lokacin da yake na tarayya, sai mu tambaya, menene hukuncin shari’a a hada salloli biyu; sallar azahar da la’asar da kuma sallar magariba da issha a lokaci daya?
Dukkan mazhabobi sun tafi akan
halarcin hada azahar da la’asar a Arfa, da kuma Muzdalifa tsakanin magariba da issha.
Malikui da Shafi’i da Hanbali banda hanafiyya sun halarta hada salloli idan akwai uzurina
ruwan sama, da tabo, da cuta, da tsoro, da sauran uzurori, amma sun saba a kan haka a hada salloli a lokacin tafiya kamar yadda ya zo a littattafansu.
Shafi’iyya sukace
: Dalilan hada salla su ne tafiya, da cuta da ruwan sama da tabo tare da duhu a karshen wata, da a hajji da Arfa da Muzdalifa. Abin da ake nufi da safara ba bambanci ta kai kasruko
ba ta kai ba, kuma an shardanta kada ya zama tafiyar haramun ce ko ta makaruhi, amma ya halatta ga mai tafiya ta halal ya hada tsakanin azahar da la’asar hadawa ta gabanin lokaci da sharadi biyu:
Na daya: Rana ta karkata yayin da yake sauka wajan yada zangonsa domin hutawa.
Na biyu: Ya yi niyyar tafiya kafin shigar lokacin sallar la’asar da kuma sake yada zango domin hutawa bayan faduwar rana, idan ya yi niyyar sauka kafin rana ta yi Ja, sai ya yi sallar azahar sannan sai ya tafi, ya kuma bar la’asar har sai ya sauka, domin shi zai sauka a lokacinta mukhtari, babu wani dalili da zai sa ya gabatar da ita…
Shafi’iyya sukace
: Ya halatta a hada salloli biyu da aka ambata; gabatarwa ko jinkirtawa ga matafiyi da tafiyarsa ta kai kasaru da sharadin tafiya, ya kuma halatta ya hada su hadawa ta kafin lokaci saboda saukar ruwa, amma sun sanya wa hadawa ta kafin lokaci sharudda.
Hanbaliyya suka ce: Hadawa tsakanin azahar da la’asar da kuma magariba da issha hadawa ta gabata ko ta jinkirta ta halatta, amma bari shi ya fi, kuma ya halatta a hada tsakanin azahar da la’asar hadawa ta gabanin lokaci da kuma tsakanin magariba da issha ta bayan lokaci a Muzdalifa, an shardanta a wannan halaccin ya zama shi matafiyi ya halatta ya yi kasaru, ko ya kasance maras lafiya da zai wahala idan ya bar hadawa, ko kuma mace ce mai shayarwa ko haila, duk wadannan ya halatta su hada sallolin saboda tsoron wahala yayin kowace salla, haka nan mai istihala mai uzuri kamar mai yoyon fitsari, haka nan malamai na Hanbaliyya suka halatta hakan ga wanda ba ya iya samun ruwa ko taimama ga kowace salla, haka nan wanda ba zai iya sanin lokaci ba kamar makaho ko wanda yake rayuwa karkashin kasa, haka nan ya halatta ga wanda yake jin tsoro ga kansa ko dukiyarsa ko mutuncinsa, ko wanda yake jin tsoron kada cutuwa ta cim masa idan ya bar neman abin rayuwa, wannan kuma sauki ne ga ma’aikata wadanda barin aikinsu zai yi musu wahala.
Wannan al’amura duka sun halatta hada salla tsakanin azahar da la’asar ko magariba da issha da gabatarwa ko jinkirtawa, kuma an halatta jam’i tsakanin magariba da issha kadai saboda kankara da sanyi da tabo da iska mai tsanani da ruwan sama mai jikawa ga tufafi, kuma ya zama akwai wahala ga hakan, ba bambanci a nan tsakanin mai salla a gidansa ko masallaci ko kuma hanya mai rufi, abin da ya fi ya zaba wa kansa abin da ya fi sauki na hadawa ko gabatarwa ko jinkirtawa, idan al’amuran biyu saukinsu suka daidaita to abin da ya fi sai ya zabi hadawa ta jinkirtawa. Kuma an shardanta a duka nau’in jami’ ya kiyaye jerantawa tsakaninsallolin
.
Hanafiyya sukace
: Bai halatta ba ya hada salloli sai a lokaci daya, ba a tafiya ba, ba a zaman gida ba, ta kowane hali, sai da wani uzuri:
Na farko: A jam’in gabatarwa:
1- Ya kasance a ranar Arfa.
2- Ya kasance mai harama da hajji.
3- Ya yi salla bayan limami.
4- Sallar azahar ta kasance ingantacciya, idan ta bace to dole ne a sake ta, anan
kuma bai halatta ba ya hada ta tare da la’asar, sai dai ya yi sallar la’asar idan lokacinta ya shiga.
Na biyu: Ya halatta a yi jam’i a magariba da issha jam’in jinkirtawa da sharadi biyu:
Yazama
a Muzdalifa.
Ya zama mai harama dahajji
.
Amma Ibn Taimiyya ya amsa yayin da aka tambaye shi game da wannan mas’ala sai ya ce: Ya halatta hada wa ga tabo mai tsanani da iska mai tsanani mai sanyi a dare mai duhu da makamantan wannan koda babu ruwan sama mai saukowa a mafi ingancin maganganun malamai, wanna shi ya fi su yi salla a gidajensu, domin barin hadawa a masallaci da yin salla a cikin gida bidi’a ce da ta sabawa Sunna, domin Sunna shi ne ya yi salla biyar a masallaci, sallar hadawa a masallaci shi ya fi salla a gidaje daidaiku da ittifakin malamai wadanda suke halatta hadawa kamar Maliku da Shafi’i da Ahmad”
.
A wanann fakara zamu kawo bincike game da ruwayoyin da littattafai sihah suka ruwaito wacce take karfafa halarcin hada salla babu wani dalili.