Hada Salloli

Hada Salloli0%

Hada Salloli Mawallafi:
: Majma'u Ahlil-baiti
: Shekh Hafiz Muhammad Sa'id
Gungu: Ilimin Fikihu

  • Farawa
  • Na Baya
  • 14 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 11404 / Gurzawa: 4348
Girma Girma Girma
Hada Salloli

Hada Salloli

Mawallafi:
Hausa

Dukkan hakkokina cibiyar Muassasar alhasanain (a.s) ne, kuma yada rubuce-rubucen tare da ambaton inda aka dauko su ba shi da matsala. Muassasar alhasanain (a.s)

Hada Salloli

Mawallafi: Majma'u Ahlil-baiti

HADA SALLOLI BIYU

Wallafar: al'Majma’ul Alami Li Ahlil Bait

Fassarar: Hafiz Muhammad Sa’id

Da sunan Allah mai rahama maijin kai

Kura'ni Da Hadisi Suna Cewa: “Ka tsayar da salla ga karkatar rana zuwa ga duhun dare, da kuma karatun alfijir hakika karatun alfijir ya kasance abin halarta ne”.Surar Isra: 78

“Jibril (A.S) ya zo wajan Manzo Allah (S.A.W) sai ya sanar da shi lokacin salla, ya ce ka yi sallar asuba yayin da alfijir yaketo, ka yi sallar farko yayin da rana ta karkata, ka yi sallar la’asar bayanta, sallar magari idan kaskon ya buya, sallar issha idan shafaki ya buya, sai ya zo masa washegari, sai ya ce: Ka waye da safiya sai ya waye da ita, sannan sai ya jinkirta azahar yayin lokacin da ya sallaci la’asar a cikinsa, ya yi sallarla’asar bayanta, ya yi sallar magariba kafin faduwar shafaki, ya yi sallar issha yayin da sulusin dare ya tafi, sannan sai ya ce: tsakanin wadannan lokuta biyu lokaci ne”. Wasa’ilusshi’a: 3116, H 1- 4795

Gabatarwar Al'Majma’ul Alami

Lallaiyana daga cikin dabi’ar mutane su yi sabani a junansu, sai dai Allah yana son wannan sabanin ya takaita a cikin kewayen ingantaccen imani, saboda haka ne ba makawa ya zamanto akwai ma’auni tabbatacce da masu sabani zasu koma zuwa gare shi. Allah madaukakin sarki ya saukar da littafi da gaskiya domin ya yi hukunci tsakanin mutane da gaskiya cikin abin da suka saba acikinsa[ 1] .

Da babu wannan gaskiya guda daya, to da al’amarin rayuwa ba zai daidaitu ba, Wannan shi ne abin da Kur’ani yake tabbatar da shi kuma yake bisa ka’idar tauhidi, sannan sai daga baya aka samu karkata da sabani da camfe-camfe har mutane suka nisanta daga wannan asasi nisanta mai girma.

Ta haka ne ta bayyana cewa mutane ba su ne masu cancantar su yi hukunci da gaskiyako karya ba matukar sun kasance suna iya biye wa son rai da bata da zalunci.

Duk da littafin Allah ya sauka da shiriya ya kuma isa zuwa ga mutane…. tare da hakan son rai ya rinjayi mutanenan da can, kwadayi da tsoro da bata suka nisantar da mutane ga karbar hukuncin littafi da komawa zuwa ga gaskiya da yake dawo da su zuwa gareta.

Bata shi ne ya jagoranci mutane a tsawon zamani zuwa ga sabani da shisshigi da kin Allah, Jahilci ya zama wani sababin sabani da rarraba, sai dai shi jahili ya kamata ne ya tambayi malamai kamar yadda Allah ya fada: “Ku tambayi ma’abota sani idan ba ku saniba[ 2] ”.

Ta haka ne ketare iyakar jahili ya kasance zalunci da shisshigi ga wannan asaliwanda hankali yake amincewa da shi, kuma ma’abota hankula suke karkata zuwa gareshi, kuma lallai wannan shi ne mafi bayyanar ka’idoji da hanyoyi wadanda zasu toshe hanyar rarraba da sabani.

Musulunci shi ne addinin Allah dawwamamme da hakikarsa ta bayyana cikin nassin littafin Allah (S.W.T) da sunnar manzonsa (S.A.W) da ba ya magana da son rai sai da wahayi. Kuma Allah da manzonsa sun sani cewa al’ummarsa zata yi sabani bayansa kamar yadda ta yi sabani a lokacin rayuwarsa, don haka ne Kur’ani mai girma ya sanya wa al’umma makoma da zasu dogara da ita bayan wafatin manzo (S.A.W) tana tafiya tare da shi taku-taku tana kuma gabatar wa al’umma abin da suka takaita ga fahimtarsa da tafsirinsa, wannan kuwa su ne; Ahlul Baiti (A.S), sun tsarkaka ne daga dukkan dauda da kuma kazanta wadanda Kur’ani ya sauka ga kakansu Mustapha (S.A.W), suna karbarsa suna karanta shi suna hankaltarsa da kiyayewa, sai Allah ya ba su abin da bai ba waninsu ba... Kamar yadda manzo ya yi wasiyya da su a matsayin makoma ta gaba daya a hadisin sakalain mash’huri, sai suka kwadaitu wajan kare shari’ar musulunci da Kur’ani mai girma daga fahimta ta kuskure da tafsiri na barna, suka saba da bayanin ma’anarsa madaukakiya, sai suka zama makoma kuma madogara ga al’ummar musulmi, suna kore shubuha suna masu karbar tambayoyi da hakuri da juriya. Bayannan abin da suka bari mai yawa yana shaidawa da kyawon mu’amalarsu tare da masu tambayarsu da tattaunawa da su, kuma komawa garesu da zurfin amsawarsu yana nuni zuwa ga kasancewarsu makoma ta ilimi a wannan fage.

Hakika koyarwarsu ta kare abin da sukabari , kuma mabiyansu suka kwadaitu a kan kare shi daga tozarta, abin da yake nuni zuwa ga koyarwarsu da ta tattaro dukkan wasu rassa na ilimomin da suke kunshe cikin koyarwar addinin musulunci.

Kuma wannan makaranta ta iya tarbiyyatar da mutane da suke shirye domin kamfata daga wannan ilmi kuma ta fitar wa al’umma manyan malamai masu biyayya ga tafarkin Ahlul baiti (A.S), suna masu gamewa da sanin dukkan mas’alolin mazhabobi daban-daban, da kuma akidoji a cikin da’irar musulunci da wajanta, suna masu bayar da mafi kyawon amsa da bayanai a tsawonn zamanin da ya gabata.

Hakika majma Ahlul baiti (A.S) ya gaggauta yana mai farawa daga nauyin da yake kansa da ya dauka a kafadunsa domin kariya ga sakon musulunci wanda ma’abota mazhabobi da kuma masu akidu da suka saba wa musulunci suka damfaru da su, yana mai bin tafarkin Ahlul Baiti (A.S) da mabiyansu da suka kwadaitar da raddi kan kalu-balen wannan zamani da kuma kokarin dawwama a kan tafarkin gwagwarmaya daidai gwargwadon abin da kowane zamani yake bukata.

Ilimin da littattafan malamai masana ma’abota bin koyarwar Ahlul baiti (A.S) suka taskace shi a wannan al’amari ba shi da misali, domin shi madogara ce ta ilmi da yake karfafa da dogara da hankali da hujja, yake kuma nisantar son rai da zargi, yake kuma magana da malamai masu tunani daga ma’abota kwarewa, maganar da hankali yake yarda da ita kuma dabi’ar dan Adam kubutacciya take karbar ta.

Kokarin majma ya zo ne domin ganin an gabatar wa dalibai sabuwar marhalar wannan ilimi mai wadata a shafin tattaunawa da tambaya da kuma raddin shubuha da a kan tayar daga lokaci zuwa lokaci tsawon zamani, ko kuma ake kawo wa a yau musamman ma da taimakon wasu kungiyoyi masu kin musulunci da musulmi a cikin sarkar sama ta intanet da makamantansu, muna masu nisantar abin da yake maras kyau, muna masu kwadayin motsa tunanin masu hankali da masu neman gaskiya domin su bude idanunsu a kan gaskiyar da koyarwar da Ahlul baiti (A.S) suka gabatar wa duniya baki daya a zamanin da hankula suke cika, alakar mutane da tunani take samuwa cikin gaggawa.

Ba makawa mu yi nuni da cewa wannan tattararrun bahasosi an tanade su ne a lujna ta musamman da Hujjatul Islam Abul Fadal Islami yake shugabanta tare da wasu manya da suka hada da Sayyid Munzir Hakim, da Shaikh Abudlkarim Bahabahani, da Sayyid Abdurrahim Musawi, da Shaikh Abdul Amir Assuldani, da Shaikh Muhammadul Amini, da Shaikh Muhammad Hashimi Al’amili, da Sayyid Muhammad Rida aali Ayyub, da Shaikh Ali Baharami, da Husaini Salihi, da Aziz Al’ukabi.

Kuma muna mika godiya mai yawa ga dukkan wadanan da kuma ma’abota falala da bincike da suka hada da: Shaikh Yusuf Garawi, da Shaikh Ja’afarul Hadi, da Ustaz Sa’ib Abdulhamid, domin bibiyar da kowannensu ya yiwa wadannan bahasosi da kuma bayanansu masu kima.

Fatanmu shi ne yazama mun gabatar da abin da zamu iya na kokarin sauke nauyin da yake kanmu game da wannan sako mai girma na ubangijinmu da ya aiko manzonsa da shiriya da kuma addinin gaskiya domin ya daukaka shi a kan dukkan wani addini kuma Allah ya isa shaida.

Majma Ahlul baiti (A.S)

Birnin Kum

Gabatarwa

Mazhabobin musulunci gaba daya sun hadu a kan halarcin hada sallar azahar da la’asar a lokaci guda, da kuma tsakanin sallar magariba da issha a lokaci daya, amma an yi sabani a kan dalla-dallan wannan Magana ta fuskacin sharudda da dalilan da zasu sa haka, daga ciki akwai wanda ya tafi a kan cewa ya halarta a Arfa da Muzdalifa, daga ciki akwai wanda ya kara da lokacin safara, da dai sauransu.

Amma abin takaici shi ne sai ga wasu suna tuhumar makarantar Ahlul baiti (A.S) da cewa sunsaba wa shari’a, saboda kawai su sun yi hukunci da cewa hada salloli biyu ba uzuri ma ya halatta, alhalin dalilin shari’a a gun jama’a biyu (Sunna da Shi’a) suna karfafa halarcin kamar yadda zamu gani.

Don haka ne zamu yi bincike game da wannan mas’ala gun wadanda ba mabiya Ahlul baiti (A.S) ba, da kuma dalilan shari’a da suka dogara daita mu ga hakikanin asalinta daga asalin shari’a, sannan sai mu yi la’akari da matsayin Ahlul baiti (A.S) kan wannan mas’ala cikin wadannan bayanai masu zuwa:

Abu Na Farko :

Lokutan Salla Malaman musulmi sun yi bincike game da lokacin salla, sunsaba a kan cewa; shin wannan lokacin sharadin inganci ne ko kuma sharadin wajabci?

Mazhabar hanafiyya ta tafi akan cewa ba sharadi ba ce ta wajabci, ba kuma shardin inganci ba ce, domin suna cewa: Shigar lokaci sharadi ne na gabatar da salla, da ma’anar cewa; bai halatta ba a yi salla sai lokacin ta ya yi. Don haka ne muka samu sun hadu da wasu daga mazhabobi a kan cewa salla ba ta wajaba sai lokacinta ya yi, idan lokacin ta ya yi to a lokacin ne mai shari’a yake maganar yinta lokaci mai yalwa, da ma’anar idan ka yi ta a farkon lokaci ta yi, idan ba ka yi ba a farkonsa to ba ka yi sabo ba, idan ya riski salla dukkanta a lokaci to ya zo da ita kamar yadda mai shari’a ya nema daga gareshi kuma ya sauke nauyi, kamar yadda idan ya yi ta a farkon lokaci da tsakiyarsa, amma yin salla gaba dayanta bayan lokaci ya fita ta yi sai dai ya yi sabo da jinkirta ta ga barin lokacinta[3] .

Idan salla ba ta inganta sai bayan lokaci ya shiga sai muce idan sharadi ne ta aiwatar da salla, ko sharadi ne na inganci ko sharadi ne na wajabci, to wane lokuta ne aka shar’anta yin salloli biyar a cikinsu gun mazhabobi, yaya zamu san su?

Muna sanin lokutan salla da karkatar rana da kuma inuwa da take faruwa bayan karkatar rana, da wannan ne muke sanin lokacin azahar da shigar lokacin la’asar, sannan sai faduwar rana da shi ne muke sanin magariba, sannan sai boyuwar shafaki ja ko fari a kan wani ra’ayi, da wannan muke sanin shigar lokacin issha sannan sai farin da yake bayyana a sasanni da shi ne ake sanin lokacinassuba[ 4] .

Amma lokacin salloli biyar a mazhabar Ahlul baiti (A.S) to asalinsa yana daga abin da ya zo daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce; “Jibril ya zo wajan Manzo Allah (S.A.W) sai ya sanar da shi lokacin salla, ya ce ka yi sallar asuba yayin da alfijir yaketo, ka yi sallar farko yayin da rana ta karkata, ka yi sallar la’asar bayanta, sallar magari idan kaskon ya buya, sallar issha idan shafaki ya buya, sai ya zo masa washegari, sai ya ce: Ka waye da safiya sai ya waye da ita, sannan sai ya jinkirta azahar yayin lokacin da ya sallaci la’asar a cikinsa, ya yi sallar la’asar bayanta, ya yi sallar magariba kafin faduwar shafaki, ya yi sallar issha yayin da sulusin dare ya tafi, sannan sai ya ce: tsakanin wadannan lokuta biyu lokaci ne”[5] .

Da wannan ne lokutan salla biyar da aka wajabta ya zama guda uku, lokacin sallar azahar da la’asar da lokacin sallar magariba da issha da lokacin sallar asuba, ubangiji madaukaki yana fada: “Ka tsaida salla da karkatar rana zuwa duhun dare da kuma ketowar alfijin, hakika ketowar alfijir abin halarta ne[ 6] .

Faharur Razi yana cewa: Idan muka fassara duhu da farkon bayyanar duhun, wanann yana nufin farkon lokacin magariba, koda yaya ne, ayar tana maganar lokuta uku na salla ne: lokacin karkatar rana, da kuma lokacin magariba, da kuma lokacin alfijir, wanan kuma yana nufin karkatar rana ya zama lokacin azahar da la’asar sai ya zama lokaci ne na tarayya tsakanin azahar da la’asar, farkon magariba kuma lokaci na tarayya tsakanin azahar da la’asar, wannan kuma yana nuna halarcin jam’i tsakanin azahar da la’asar da kuma tsakanin magariba da issha kai tsaye, sai dai dalilai ya zo a kan cewa jam’i a lokacin zama ba uzuri bai halatta ba, sai ya zama ya halatta saboda uzuri na tafiya da ruwan sama da sauransu[7] .

Allama hilli yace : Azahar da la’sar kowanne yana da lokaci biyu; Lokacin da yakebanta da kuma lokacin da yake na tarayya, wanda yakebanta azahar daga karkatar rana zuwa daidai lokacin yin ta (gwargwadon yin raka’a hudu) la’asar kuma daidai gwargwadon yin ta a karshen lokaci, amma tsakanin nan duka lokaci ne da suka yi tarayya a ciki.

Magariba da issha su ma suna da lokuta biyu; Wanda yakebanta da magariba shi ne gwargwadon yin ta bayan faduwar rana, issha kuma daidai gwargwadon yin ta a rabin farko na tsakiyar dare, sauran lokacin da yake tsakanin haka ya na zama tarayya tsakaninsu, saboda haka babu wata ma’ana ga jam’i a gunmu (domin kowacce an yi ta ne a lokacinta), amma waninmu su sun kebe wa kowacce daga azahar da la’asar lokacinta, haka ma magariba da issha kowacce da lokacinta saboda haka su a gun su akwai ma’ana ga jam’i[8] .

Abu Na Biyu :

Hukuncin Hada Salla Biyu Da Dalilansa Gun Mazhabobi Idan mun san lokutan salloli biyar dalla-dalla, muka kuma san lokacin da yakebanta da kowacce da kuma lokacin da yake na tarayya, sai mu tambaya, menene hukuncin shari’a a hada salloli biyu; sallar azahar da la’asar da kuma sallar magariba da issha a lokaci daya?

Dukkan mazhabobi sun tafi akan halarcin hada azahar da la’asar a Arfa, da kuma Muzdalifa tsakanin magariba da issha.

Malikui da Shafi’i da Hanbali banda hanafiyya sun halarta hada salloli idan akwai uzurina ruwan sama, da tabo, da cuta, da tsoro, da sauran uzurori, amma sun saba a kan haka a hada salloli a lokacin tafiya kamar yadda ya zo a littattafansu.

Shafi’iyya sukace : Dalilan hada salla su ne tafiya, da cuta da ruwan sama da tabo tare da duhu a karshen wata, da a hajji da Arfa da Muzdalifa. Abin da ake nufi da safara ba bambanci ta kai kasruko ba ta kai ba, kuma an shardanta kada ya zama tafiyar haramun ce ko ta makaruhi, amma ya halatta ga mai tafiya ta halal ya hada tsakanin azahar da la’asar hadawa ta gabanin lokaci da sharadi biyu:

Na daya: Rana ta karkata yayin da yake sauka wajan yada zangonsa domin hutawa.

Na biyu: Ya yi niyyar tafiya kafin shigar lokacin sallar la’asar da kuma sake yada zango domin hutawa bayan faduwar rana, idan ya yi niyyar sauka kafin rana ta yi Ja, sai ya yi sallar azahar sannan sai ya tafi, ya kuma bar la’asar har sai ya sauka, domin shi zai sauka a lokacinta mukhtari, babu wani dalili da zai sa ya gabatar da ita…

Shafi’iyya sukace : Ya halatta a hada salloli biyu da aka ambata; gabatarwa ko jinkirtawa ga matafiyi da tafiyarsa ta kai kasaru da sharadin tafiya, ya kuma halatta ya hada su hadawa ta kafin lokaci saboda saukar ruwa, amma sun sanya wa hadawa ta kafin lokaci sharudda.

Hanbaliyya suka ce: Hadawa tsakanin azahar da la’asar da kuma magariba da issha hadawa ta gabata ko ta jinkirta ta halatta, amma bari shi ya fi, kuma ya halatta a hada tsakanin azahar da la’asar hadawa ta gabanin lokaci da kuma tsakanin magariba da issha ta bayan lokaci a Muzdalifa, an shardanta a wannan halaccin ya zama shi matafiyi ya halatta ya yi kasaru, ko ya kasance maras lafiya da zai wahala idan ya bar hadawa, ko kuma mace ce mai shayarwa ko haila, duk wadannan ya halatta su hada sallolin saboda tsoron wahala yayin kowace salla, haka nan mai istihala mai uzuri kamar mai yoyon fitsari, haka nan malamai na Hanbaliyya suka halatta hakan ga wanda ba ya iya samun ruwa ko taimama ga kowace salla, haka nan wanda ba zai iya sanin lokaci ba kamar makaho ko wanda yake rayuwa karkashin kasa, haka nan ya halatta ga wanda yake jin tsoro ga kansa ko dukiyarsa ko mutuncinsa, ko wanda yake jin tsoron kada cutuwa ta cim masa idan ya bar neman abin rayuwa, wannan kuma sauki ne ga ma’aikata wadanda barin aikinsu zai yi musu wahala.

Wannan al’amura duka sun halatta hada salla tsakanin azahar da la’asar ko magariba da issha da gabatarwa ko jinkirtawa, kuma an halatta jam’i tsakanin magariba da issha kadai saboda kankara da sanyi da tabo da iska mai tsanani da ruwan sama mai jikawa ga tufafi, kuma ya zama akwai wahala ga hakan, ba bambanci a nan tsakanin mai salla a gidansa ko masallaci ko kuma hanya mai rufi, abin da ya fi ya zaba wa kansa abin da ya fi sauki na hadawa ko gabatarwa ko jinkirtawa, idan al’amuran biyu saukinsu suka daidaita to abin da ya fi sai ya zabi hadawa ta jinkirtawa. Kuma an shardanta a duka nau’in jami’ ya kiyaye jerantawa tsakaninsallolin[ 9] .

Hanafiyya sukace : Bai halatta ba ya hada salloli sai a lokaci daya, ba a tafiya ba, ba a zaman gida ba, ta kowane hali, sai da wani uzuri:

Na farko: A jam’in gabatarwa:

1- Ya kasance a ranar Arfa.

2- Ya kasance mai harama da hajji.

3- Ya yi salla bayan limami.

4- Sallar azahar ta kasance ingantacciya, idan ta bace to dole ne a sake ta, anan kuma bai halatta ba ya hada ta tare da la’asar, sai dai ya yi sallar la’asar idan lokacinta ya shiga.

Na biyu: Ya halatta a yi jam’i a magariba da issha jam’in jinkirtawa da sharadi biyu:

Yazama a Muzdalifa.

Ya zama mai harama dahajji[ 10] .

Amma Ibn Taimiyya ya amsa yayin da aka tambaye shi game da wannan mas’ala sai ya ce: Ya halatta hada wa ga tabo mai tsanani da iska mai tsanani mai sanyi a dare mai duhu da makamantan wannan koda babu ruwan sama mai saukowa a mafi ingancin maganganun malamai, wanna shi ya fi su yi salla a gidajensu, domin barin hadawa a masallaci da yin salla a cikin gida bidi’a ce da ta sabawa Sunna, domin Sunna shi ne ya yi salla biyar a masallaci, sallar hadawa a masallaci shi ya fi salla a gidaje daidaiku da ittifakin malamai wadanda suke halatta hadawa kamar Maliku da Shafi’i da Ahmad”[11] .

A wanann fakara zamu kawo bincike game da ruwayoyin da littattafai sihah suka ruwaito wacce take karfafa halarcin hada salla babu wani dalili.

Abu Na Uku :

Ingantattun Littattafai Suna Karfafa Halarcin Hadawa Kai Tsaye 1- Daga Sa’id dan Jubair daga dan Abbas ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya yi sallar azahar da la’asar a hade, da magariba da issha a hade ba tare da wani tsoro ba ko tafiya[ 12] .

2- Daga Jabir dan Zaid daga Ibn Abbas ya ce: “Na yi salla (raka’a) takwas a hade tare da Manzo (S.A.W)[ 13] .

3- Daga Jabir dan Zaid daga Ibn Abbas: “Hakika Manzo (S.A.W) ya yi salla a Madina bakwai-bakwai, takwas-takwas azahar da la’asar da kuma magariba daissha[ 14] .

4- Daga Abdullahi dan Shakik, ya ce: Dan Abbas ya yi mana huduba wata rana bayan sallar la’asar har sai da rana ta fadi, taurari suka bayyana mutane suka rika cewa salla-salla, ya ce: Sai wani mutum daga Bani tamim ya zo masa bai gushe ba yana cewa salla-salla, sai Ibn Abbas ya ce da shi: Ni zaka sanar sunna, kaiconka? Sannan sai ya ce: Na ga Manzo (S.A.W) yana hadawa tsakanin azahar da la’asar da kuma magariba da issha, sai Abdullahi dan Shakik ya ce: Sai wani abu na kokwanto ya same ni, sai na zo wajan Abu huraira na tambaye shi, sai ya gaskata maganarsa[ 15] .

A wata ruwaya sai Ibn Abbas yace : “Kaiconka!mu zaka nuna wa salla? Mun kasance muna hada salla biyu ne a lokacin Manzo (S.A.W)[ 16] .

5- Daga Ibn Abbas: “Manzon Allah ya yi sallar azahar da la’asar a hade a Madina ba tare da tsoro bako tafiya”. A bu zubair yace : Sai na tambayi Sa’id me ya sa (Manzo) ya yi haka? Sai ya ce: Na tambayi Dan Abbas kamar yadda ka tambaye ni sai ya ce: Yana son kada al’ummarsa ta wahala ne[ 17] .

6- Daga Dan Abbas ya ce: “Manzo (S.A.W) ya hada sallar azahar da la’asar da kuma magariba da issah a Madina ba domin tsoro ko ruwan sama ba”[ 18]. A wani hadisin Abu Mu’awiya, ance da Dan Abbas: Me yake nufi da hakan? Sai ya ce: Yana nufin kada al’ummarsa ta wahala[ 19] .

7- Daga Ma’azu dan Jabal yace : “Manzo (S.A.W) ya hada sallar azahar da la’asar da kuma magariba da issha a yakin Tabuka, ya ce: Sai na ce: Me ya sa ya yi hakan? Sai ya ce: Yana nufin kada al’ummarsa ta wahala[ 20] .

Buhari a sahihinsa ya rawaito wasu ruwayoyi da suka yi nuni karara da halarcin hada salla ya kuma ambaci wannan a karkashin fasalin ‘Jinkirta azahar da la’asar’ a babin ‘lokutan salla’;

Daga Jabir dan Zaid daga Dan Abbas: “Annabi ya yi salla a Madina bakwai da kuma takwas, azahar da la’asar da kuma magariba da issha”. Sai Ayyuba ya ce: Tayiwu a dare mai ruwan sama ne sai ya ce: Ta yiwu[ 21] . Sharafuddin ya yi ta’aliki a game da karshen wannan magana da akakara wacce ba ta cikin ruwaya da cewa: Ba komai suke bi ba sai zato.

Daga Amru dan Dinar ya ce na ji Jabir dan Zaid daga Ibn Abbas yana cewa: “Manzo (S.A.W) ya yi salla raka’a bakwai a hade (magarib da issha) da kuma raka’a takwas (azahar da la’asar) ahade ” [22] .

A babin sallar issha yana cewa: Daga Ibn Umar da Abu Ayyuba da Dan Abbas: “Annabi (S.A.W) ya yi sallar magariba da issha a hade a lokacin dayarsu[ 23] .

Abin da dan mas’ud ya karbo yana karfafar wannan yayin da yake cewa; “Annabi ya hada sallar (a Madina) azahar da la’asar, da kuma magariba da issha, sai aka tambayi Manzo (S.A.W) me ya sa hakan, sai ya ce: Na yi ne domin kada al’ummata ta wahala[ 24] .

Al’amari Na Hudu :

Masu Sharhin Muslim Da Buhari [Suna Kawo Dalilin Halarcin Hada Salla A Zaman Gida Daga Wannan Ruwayoyi Da Cewa Domin Kada Al’umma Ta Wahala Ne]

Nawawi ya tattauna a sharhin Muslim game da tawilin wannan ruwayoyi da suka gabata bisa fassarar asasin mazhabobi, ga abin da yake cewa:

Malamai suna da tawili ga wannan hadisai bisa mazhabobinsu, daga cikinsu akwai wanda ya yi tawili bisa cewa an hada salla ne saboda ruwan sama, ya ce wannan ya shahara gun wasu jama’a dagamagabata[ 25] .

Yace wannan mai rauni ne kwarai da ruwayar Dan Abbas da take cewa: “Babu wani tsoro ko ruwan sama”. Daga cikinsu akwaiwanda ya yi tawili a kan cewa saboda ruwa ne sai ya yi sallar azahar, sannan sai hadari ya tafi sai ta bayyana lokacin la’asar ya yi sai ya yi ta. Wannan kuma batacce ne domin idan sun yi wannan tawili ga azahar da la’asar to me zasuce game da magariba da issha.

Yace : Daga cikinsu akwai wanda ya ce ya jinkirta ta farko ne zuwa karshen lokacinta sai ya yi ta, yayin da ya gama sai ya zama lokacin la’asar ya shiga sai ya yi ta sai ya zama ya yi wani hadi tsakaninsu hadi suri. Yace : Wannan ma mai rauni ne kwarai, domin ya saba wa zahirin hadisi sabawa mai tsanani.

Ya ce: Aikin Dan Abbas yayin huduba, sai mutane suka rika cewa salla-salla, da kuma rashin kulawa da su da dalilin da ya kafa da wannan hadisi domin nuna aikinsa daidai ne da jinkirtawar sallarsa zuwa lokacin issha, da kuma hadawa gaba daya a lokacin ta biyu, da kuma gasgatawar da Abu huraira ya yi masa da rashin musawarsa, bayani ne a fili da yake nuna raunin wadannantawilolin[ 26] .

Akwai raddin wannan tawiloli da Bn Abdulbar ya yi da kuma khadabi da wasunsu da cewa: Hadawa din rangwame ne ga al’umma, da ya kasance jam’i ne suri, da ya fi wahala da ka zo da ita a lokacinta {domin jam’in suri ya fi ma rarrabawar wahala}, domin kula da zuwan karshen lokacin (ta farko) da kula da farkon lokacin (ta gabanta) wani abu ne wanda masana da malamai ba zasu iya gane shi ba ballantana sauran mutane.

Suka ce: Hadawa ba komai take nuna wa ba sai rangwame, fadin Dan Abbas: Yana son kada ya wahalar da al’ummarsa, suka ce hadisan sun nuna gabatar da hadawar tare a lokaci guda ko a lokacin ta farko ko kuma a lokacin ta karshe, wannan kuma shi ne abin da ake fahimta daga ma’anar hadawa, wannan kuma shi ne mahallin da ake jayayyaakai[ 27] .

Nawawi ya ce: Daga ciki akwai wanda ya yi tawili a kan cewa saboda uzuri ne na rashin lafiya da makamantansu, kamar Ahmad dan Hanbal da Alkali Husain da Khidaibi da Mutawwali daRuyani[ 28] .

Wasu malamai sun yi raddin wannan tawili, yayin da suke cewa: Idan da ya zama saboda rashin lafiya da ba wanda zai yi salla tare da Manzo sai maras lafiya, wanda kuma a zahiri ya yi jam’i da sahabbansa, kuma wannan shi ne abin da Ibn Abbas ya fada asarari[ 29] .

Al’amari Na Biyar :

Abubuwan Da Suke Karfafar Hadawa Akwai dalilai da dama da sukekarfafa ra’ayin da yake halatta hada sallolin a zaman gida, daga cikinsu a kwai:

1- Ma’abota sahihan littattafan ban da buhari sun ware wani babi a littattafansu da sunan “Hada salloli biyu” sun kuma kawo ruwayoyi da suke nuna halarci da rangwamen haka, sai wannan ya zama dalili a kan hadawa a zaman gida da tafiya da uzuri ko ba uzuri[30] . Da ba haka ba ne da sun ware babi na musamman game da hada salloli a zaman gida da kuma babi na musamman game da hada salloli a lokacin tafiya, sai ya zama sun kawo ruwayoyi ne kai tsaye ba kebancewa. Kuma idan Buhari bai yi haka ba, abin da sauran suka yi ya wadatar kamar Muslim da Tirmizi da Nisa’i da Ahmad dan Hanbal da Masu sharhin Muslim da buhari, kuma buhari ya kawo wasu hadisai saidai karkashin wasu maudu’ai daban.

2- Fatawar malamai da rashin halarcin hadawa ba tare da wani kebewa ba, ta ginu ne akan wasu tawiloli da ba su da wani asasi daga wadannan ruwayoyi. (Sai don tawailina kashin kansu domin ya yi daidai da mazhabobinsu).

3- Shelantawa a fili da ma’abota sihah suka yi cewa Manzo ya yi haka ne domin kada wani daga al’ummarsa ya wahala, wannan yana nufin an shar’anta hadawa domin saukaka mata da rangwantawa babu wani kebancewa, da kuma rashin wahalar da kai saboda rarrabawa, sannan hadisan da suka yi magana game da hadawa alokacin safara ba sa takaita da lokacin safara domin su hadisai sakakku ne ba su da kebewa, kuma ba ma’ana batun tafiya ya shigo cikinsu ko rashin lafiya ko ruwan sama ko tabo ko tsoro, su wadannan ruwayoyi sun shafi kowane yanayi kuma suna aiwatuwa a kowane yanayi kuma a kowane lokaci[31] kamar yadda Karin bayani zai zo a bahasin al’amari na shida.

4- Malamai sun halatta hadawa a zaman gida.

Nawawi yana cewa: Wasu jama’a daga malamai sun halatta jam’i a zaman gida ga mai bukatar hakan idan bai dauke shi al’ada ba, wannan kuma shi ne maganar Ibn Sirin da Ash’habu daga sahabban Maliku, da kuma Hidabi daga Kifal da sahabban Shafi’i da kuma Abu Ishak Maruzi da kuma wasu malamai daga malaman hadisai kuma shi ne maganar Ibn Munzir.

Yace : Wannan kuma maganar Ibn Abbas: “Yana son kada al’ummarsa ta wahala” yana karfafarsa, domin bai sanya dalilinsa rashin lafiya ba ko wani abu da su masu tawili suke kawowa.

Wannan magana da yawa daga malamai sun ambace ta kamar Zurkani a sharhin Muwadda da Askalani da Kisdi da wasunsu na daga mutanen da suka yi taliki a kan hadisin Ibn Abbas game da hada salloli biyu[32] .

Al’amari Na Shida :

Sabawar Mash’huriyar Maganar Sauran Mazhabobi Ga Abin da Ya Zo KararaA Ingantattun Littattafai A wannan fakara zamu yi nuni zuwa ga ruwayoyi da suka zo a sihah, kuma suka yi bayanin mas’alar halarcin hadawa tsakanin salloli biyu koda babu wani uzuri, wanda wannan ya sabawa ra’ayi mash’huri na mazhabobin ahlussunna:

1- Sihah sun kawo cewa Manzon Allah (S.A.W) ya hada tsakanin salloli biyu a zaman gida ba tare da wani uzuri ba, kamar yadda Sahihulbuhari[ 33] ya kawo, da sahihul Muslim[34] da sunan Abu Dawud[35] da sunan Tirmizi[36] da sunan Nisa’i[37] da Muwadda Maliku[38] da sunan Darukudni[39] da Mu’ujamul kabir na Tabarani[40] da Kanzul Ummal[41] .

Kuma wannan ruwayoyi sun ambaci cewa manzon Allah (S.A.W) ya hada salloli biyu ba tare da wani uzuriba[ 42] .

Mun samu a ruwayar Dan Abbas a lokacin da yake nakalto mana duka nau’o’in biyu daga ruwayoyi wato hadawa ba tare da wani uzuri ba,wanda ya fahimci rashin wani sababi na daban daga aikin Annabi (S.A.W) kuma Abu huraira ya karfafi wannan aiki na Dan Abbas yayin da aka tambaye shi.

Sannan Dan Abbas ya yi kaico ga mutumin da ya yi masa musun jinkirta sallar magariba daga farkon lokacinta, da kuma hadawa tsakanin salloli biyu babu wani uzuri da fadinsa: Kaiconka!mu zaka gaya wa Sunna? Mun kasance muna hadawa a lokacin Manzo (S.A.W)[ 43] .

2- Sannan ruwayoyin sun yi nuni da hadawa sake-ba-kaidi, kamar fadinsa: “Manzo ya yi mana sallar azahar da la’asar, magariba da issha ba tare da wani tsoro ko safara ba[ 44] .

Kuma Manzo ya yi sallar azahar da la’asar a hade a Madina ba tare da tsoroko safara ba, Zubair ya ce: Sai na tambayi Sa’id saboda me? Sai ya ce na tambayi Dan Abbas kamar yadda ka tambaye ni sai ya ce: Yana gudun kada al’ummarsa tawahala[ 45] .

A yakin Tabuka ya yi jam’i tsakanin azahar da la’asar da kuma magariba da issha, saina ce: Me ya sa ya yi haka? Sai ya ce: “Yana gudun kada al’ummarsa ta wahala[ 46] . Kuma ya hada ba tare da ruwan samaba[ 47] , kuma ya hada sallar azahar da la’asar da magariba da issha ba tare da cewa akwai tsoro ko ruwan sama ba[48] , da hadisin na yi salla a bayan manzo (S.A.W) takwas gaba da ya da kuma bakwai gaba daya[49] , wadannan ruwayoyi dukkansu suna nuna rashin kebancewa da lokutan uzuri.

Na’am akwai ruwaya daya da Tirmizi ya rawaito da ta saraya ta fuskacin sanadi, daga Abu Salama Yahaya dan Khalaf Al’basari: Mu’utamar dan Sulaiman ya ba mu labari daga babansa daga Hanash, daga Ikrama, daga Dan Abbas, daga Annabi (S.A.W) yace : “Wanda ya hada salla biyu ba wani uzuri ya zo wa kofa daga kofofin zunubai”.

Abu Isa da Hanash suka ce: Wannan Abu Ali Arrahabiyyi shi ne Husaini dan Kais kuma shi rarrauna ne gun ma’abota hadisi, Ahmad da waninsa sun raunatashi[ 50] . Buhari yace : Hadisinsa duka karya ne kuma ba a rubuta hadisinsa. Akili ya ce: Wannan hadisi na wanda ya hada salla ba uzuri ya zo wa kofa daga kofofin bata ba a la’akari da shi, ba a san kowa ba sai shi, kuma ba shi da asali, domin ya inganta daga Dan Abbas cewa: Annabi (S.A.W) ya hada sallolin azahar dala’asar[ 51] , saboda haka wannan ruwaya ba ta da wani kebancewa.

3- Matsalar fatawar da wasu malaman mazhabobi suka bayar game da mas’alar hada salloli biyu, sai suka bayar da fatawa sabanin abin da ruwayoyi suka zo da shi, da wannan yana komawa zuwa ga fahimtar lokutan salla na shari’a na salla da kuma kasa su gida biyu tsakanin lokuta kebantattu da kuma na tarayya, don haka ya kamata ne a yi tambaya a ce: Shin ya halatta hada salloli a lokacin da yakebanta da daya?

Saboda haka ya kamata ne sabani a wannan mas’ala ya kau saboda sabawar maudu’i, domin a mazhabar Ahlul baiti (A.S) suna ganin lokaci yana tarayya ne tsakanin duka sallolin biyu, kebantarsa da daya yana zama ta fuskacin rigo ne, domin babu wani lokaci na musamman da yakebanta da daya, domin zai ishesu su duka, sai dai dole ne daya ta gabacidayar[ 52] .

Malaman mazhabobin musulunci sun hana hada salloli biyu a lokacin dayar saboda a wajansu kowace salla tana da lokacin da yakebanta da ita saboda haka maudu’in yasassaba[ 53] .

Ashe kenan a wannan mas’alar kowanne daga jama’ar biyu Sunna da Shi’a kowayana hukunci da abin da yake sabanin abin da daya yake nufi, sabanin yana yiwuwa ne idan maudu’in magana ya zama daya ba tare da ya saba ba.

Al’amari Na Bakwai :

Hukuncin Hada Salla A Mazhabar Ahlul Baiti (A.S) Mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) sun kafa dalili akan halarcin jam’i tsakanin salloli biyu da hadisai masu yawa, musamman da ya zama ita wannan mas’ala tana da alaka da lokutan salla ne, muna ganin ya zama dole mu yi bayaninsa kafin mu san hukuncin hada sallolin.

Ubangiji ya ce: “Hakika salla ta kasance wajibi abin sanya wa lokuta a kan muminai[ 54] .

Ubangiji ya ce: “Ka tsayar da salla ga karkatar rana zuwa ga duhun dare da kuma karatun alfijir hakika karatun alfijir ya kasance abin halarta ne[ 55] .

Masu tafsiri sun yi sabani game da kalmar duluk sai wasu mutane suka ce: Karkatar rana, wannan shi ne fadin Ibn Abbas, da dan Umar, da Jabir, da Abul’aliya, da Hasan da Sha’abi, da Ata’a, da Mujahid, da Katada.

Sallar da aka yi umarni da ita, ita ce azahar, kuma shi ne aka ruwaito daga Abu Ja’afar da Abu Abdullahi (A.S), da wannan sai ya zama ayar ta hade dukkan lokutan salla biyar, sai su yi salla da karkatar rana azahar da la’asar, sallar dare su ne magariba da issha, ketowar alfijir kuma sallar asuba, wannan su ne sallolibiyar[ 56] .

Tabrasi ya ce: Zai iya yiwuwa kafa dalili da wannan aya a kan hakan, a ce: Ubangiji madaukakin sarki ya sanya karkatar rana, wannan shi ne karkata zuwa ga dare lokacin salloli hudu, sai dai azahar da la’asar sun yi tarayya a lokacin karkatar rana zuwa faduwarta, magariba da issha kuma sun yi tarayya a lokacin faduwar rana zuwa duhun dare, sai asuba da ta kebanta da lokacin alfijir, a fadinsa da kuma ketowar alfijir, a wannan aya akwai bayanin wajabcin salloli biyar, da kuma bayanin lokuta. Kuma wannan yana karfafa abin da Ayashi ya ruwaito da sanadinsa daga Ubaid dan Zurara daga Abu Abdullahi (A.S) a wannan aya, ya ce: “Allah ya farlanta wasu salloli guda hudu da lokacinsu daga karkatar rana zuwa rabin dare, salla biyu daga ciki lokacinsu daga karkatar rana zuwa faduwarta, sai dai daya dole ta zama bayan daya, da kuma wasu salloli biyu farkon lokacinsu daga faduwar rana zuwa rabin dare, sai dai daya dole ta kasance kafindayar[ 57] .

Shaikh Tusi yana cewa: Idan rana ta karkata to lokacin azahar ya shiga kuma yana kebantar daidai gwargwadon a yi salla raka’a hudu, sannan bayan haka sauran lokaci na tarayya ne tsakaninta da la’asar, har sai inuwar komai ta zama kamar misalinsa, idan ya zama haka to lokacin azahar ya fita, lokacin la’asar ya rage, farkon lokacin la’asar idan ya zama daidai gwargwadon sallatar raka’a hudun azahar ne, karshensa daidai yadda inuwar komai zata ninka shi biyu, farkon lokacin magariba idan rana ta fadi, karshensa idan shafaki ya buya shi ne jan rana, farkon lokacin issha da zaran shafaki ja ya buya, daga mutanenmu akwai wanda ya ce: Idan rana ta fadi to lokacin salloli biyu ya shiga, kuma babu sabani tsakanin malamai a kan cewa farkon lokacin issha shi ne buyan shafaki[58] .

Yana mai fada a kan mas’alar hada salloli biyu: Yana halatta a hada sallar azahar da la’asar da magariba da issha a safara da zaman gida, da ruwan sama da ba ruwan sama, da kuma jam’i tsakninsu a farkon lokacin azahar idan ya yi jam’i tsakaninsu yahalatta[ 59] .

Daga ruwayoyi da suke nuna halarcin jam’i ba wani dalili zamu kawo wannan:

Daga Abdullahi dan Sinan daga Imam Sadik (A.S) ya ce: Manzo (S.A.W) ya hada sallar azahar da la’asar da kiran salla daya da ikama biyu, ya kuma hada magariba da issha da kiran salla daya da ikama biyu ba tare da wani daliliba[ 60] .

Daga Ishak dan Ammar daga Abu Abdullahi (A.S) yace : “Manzo (S.A.W) ya yi sallar azahar da la’asar a waje daya ba tare da wani sababi ba, sai Umar ya ce da shi: Shin wani abu ya faru ne game da salla? -Ya kasance mafi jur’ar mutanen a kansa- Sai (Manzo) ya ce: A’a, sai dai ni ina son in saukaka wa al’ummata ne[ 61] .

Daga Abdullahi dan Umar: “Annabi (S.A.W) ya yi salla a Madina yana mazauni ba matafiyi ba, yana mai hadawa gaba daya, yana mai cikawa gaba daya[ 62] .

Bayanin Abin Da Ya Gabata A Takaice

Ya bayyana a wannan mas’ala ta lokutan salla cewa, ta kasance wani abu ne da dukkan mazhabobi suka yi ittifaki a kai da dan sabani tsakaninsu.

Lokutan salloli biyar uku ne; Azahar da la’asar lokacinsu daya, sallar magariba da issha lokacinsu daya, amma sallar asuba tana da nata lokaci da yakebance ta, kuma kowanne daga salloli hudu akwai wani lokaci da yakebance shi kamar yadda muka yi bayani.

Hukuncin hada salloli a mahangar cewa lokacin daya ne, to a wajan dukkan mazhabobi ya halatta, amma an samu sabani ne yayin da wasu suka zo da kebancewar sai a tafiya, ko kuma a zama a Arfa, ko rashin lafiya, ko kasawa, ko tabo, ko ruwan sama.

Amma mabiya Ahlul Baiti (A.S) sun tafi a kan halarcin hadawa ba wani uzuri, ko uzurin tsoron wahala, bisa dogaro da hadisaisahihai[ 63] da suka zo daga Ahlul baiti (A.S). Kuma kwatankwacinsu sun zo daga ingantattun littattafai gunAhlussunna[ 64] , sai dai sun yi tawilinsu, sai tawilin ya zama hukunci ne da suka fitar ba abin da ruwaya ta zo da shi ba ne.

Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai.

____________________

[1] - Bakara: 213.

[2] - Anbiya: 7. Da Nahal: 43.

[3] - Alfikihu Ala Mazahibul Arba’aWa Mazhabu Ahlil Baiti (A.S) 1180.

[4] - Alfikihu Ala Mazahibul Arba’a: 1182.

[5] Wasa’ilusshi’a: 3116, H 1- 4795.

[6] - Alisra’i: 78.

[7] - Tafsirul Kabir: 2127.Tafsirin Ayar 78 Daga Surar Isra’i.

[8] - Tazkiratul Fukaha: 2365.

[9] - Alfikihu Ala Mazahibul Arba’a: 1487.

[10] - Alfikihu Ala Mazahibul Arba’a: 1487.

[11] - Alfatawa Na Ibn Taimiyya: 314.

[12] - Sahih Muslim: 2151.

[13] - Masnad Ahmad: 1221.H 1921.

[14] - Sahih Muslim: 2152.

[15] - Sahih Muslim: 2152.

[16] - Sahih Muslim: 2153.

[17] - Sahih Muslim: 2151.

[18] - Sahih Muslim: 2152.

[19] - Sahih Muslim: 2152.

[20] - Sahih Muslim: 2152.

[21] - Sahihul Buhari: 1137.

[22] - Sahihul Buhari: 1140.

[23] - Sahihul Buhari: 1141.

[24] - Mu’jamul Kabir Na Tabarani: 10218, H 10525.

[25] - Irshadus Sari: 2222.H 543.

[26] - Muslim Sharhin Nawawi 5217. 5218.

[27] - Irshadus Sari: 2222.H 543.

[28] - Muslim Sharhin Nawawi 5218.

[29] - Muwadda Malik Sharhin Zarkawi: 1263.

[30] - Layali Bishawar: Na Shirazi: 37.

[31] - Masa’ilun Fikihiyya Na Sharafuddin: 22.

[32] - Muslim Sharhin Nawawi 5218.

[33] - Sahihul Buhari: 1140.

[34] - Muslim Sharhin Nawawi 5215.

[35] - Sunan Abu Dawud: 26, H 214.

[36] - Sunan Tirmizi: 1355, B 24, H 187.

[37] - Sunan Nisa’i: 1491, H 1573.

[38]- Muwadda: 91, H 332.

[39] - Sunan Addarukudni: 1395, H 5.

[40] - Al’mu’ujamul Kabir Na Tabrani: 10218, H 10525.

[41] - Kanzul Ummal: 8246, H 22764.

[42] - Sunan Daru Kudni: 1389, H 1, 2, 3.

[43] - Muslim 2153.

[44] - Muslim Sharhin Nawawi 5215.

[45] - Muslim Sharhin Nawawi 5215.

[46] - Muslim Sharhin Nawawi 5215.

[47] - Sunan Abi Dawud: 26 H 1214.

[48] - Muwadda: 91, H 332.

[49] - Sunan Nisa’i: 1290.

[50] - Sunan Tirmizi: 1356, B 24, H 188.

[51] - Sunan Tirmizi: 1356, B 24, H 188.

[52] - Wasa’ilusshi’a: 3116, H 1- 4795. Da Khilaf Na Shaikh Tusi: 1257.

[53] - Alfikihu Ala Mazahibul Arba’a: Kitabus Sala, Mabahisul jam’i bainas salatain.

[54] - Nisa’i: 103.

[55] - Isra’i: 78.

[56] - Majma’al Bayan: 6282, Tafsirin Ayar 78 Daga Surar Isra’i.

[57] - Majma’al Bayan, Tafsiril Kur’ani Na Tabrasi: 6283, Tafsirin Aya Ta 78 Daga Surar Isra’i.

[58] - Alkhilaf Na Shaikh Tusi: 1257.

[59] - Almabsud: 1140.

[60] - Alwasa’il: 3160 K 32 B Jam’i Bainassalatain, H 1.

[61] - Alwasa’il: 3160, K 33, H 2.

[62] - Alwasa’il: 3162, K 33, H 8.

[63] - Alwasa’il: 3160, K Salat, B 33, H 1, 2.

[64] - Sahihul Buhari: 1140, Da Muslim Sharhin Nawawi: 5215, Da Abu Dawud: 262, Da Nisa’i 1491, Tirmizi: 1355, Da Muwadda: 91, Da Kanzul Ummal: 8246.