Hakkokin Mutane
Hakkin Mai 'Yantawa: "Amma hakkin mai 'yantaka mai ni'imata maka shi ne ka sani cewa shi ne ya ciyar da dukiyarsa kanka, ya fitar da kai daga kaskanci bauta da dimuwarsa zuwa ga izzar 'yanci da nutsuwarta, sai ya sake ka daga ribacewar mallaka, ya kwance ka daga kaidin bauta, ya fitar da kai daga gidan sarkar (bauta), ya mallaka maka kanka, ya ba ka damar bautar ubangijinka, kuma ka sani shi ne mafi cancantar mutane da kai a rayuwarka da mutuwarka, kuma taimakonsa wajibi ne a kanka da dukkan abin da yake bukata daga gareka, kuma babu karfi sai da da Allah".
Hakkin 'Yantacce: "Amma hakkin wanda aka 'yanta shi ne ka sani cewa wanda ka yi wa ni'ima, sai ka sani cewa Allah mai girma da daukaka ya sanya 'yancin da ka yi masa wata hanya ce zuwa gareshi, kuma tsari ce gareka daga wuta, kuma ladanka a duniya shi ne gadonsa idan ba shi da wasu dangi magada sakamakon abin da ka ciyar na dukiyarka (a kansa), kuma a lahira kana da aljanna".
Hakkin Mai Yin Alheri: "Amma hakkinwanda
ya yi maka alheri shi ne ka gode masa, ka kuma ambace shi da alheri, ka samar masa da maganar (mutane) ta alheri (a kansa), ka tsarkake yi masa addu'a a tsakaninka da Allah, mai girma da buwaya. Idan ka yi haka zaizama
ka gode masa a boye da a sarari, sannan idan ka samu dama wata rana kai ma ka rama masa (alherin da ya yi maka).
Hakkin Ladani: "Amma hakkim mai kiran sallah shi ne ka sani cewa shi mai tuna maka ubangijinka mai girma da daukaka ne, kuma mai kiran ka zuwa ga rabautarka, mai taimakonka kan sauke wajibin Allah da yake kanka, sai ka gode masa a kan haka irin godiyar da kake yi wa masu kyautatawa".
Hakkin Limami: "Amma hakkin limaminka a sallarka, shi ne ka sani cewa kai kana dora masa nauyin jakadancin tsakaninka da ubangijinka mai girma da buwaya ne, ya yi magana maimakonka kai ba ka yi magana mai makonsa ba, ya yi maka addu'a kai ba ka yi addu'a gareshi ba, kuma ya isar maka da tsoron tsayuwa gaban Allah mai girma da daukaka. Idan an samu wata tawaya tanakansa
ban da kai, idan an samu wata kamala to kai kana tarayya da shi, kuma ba shi da wani fifiko a kanka (cikin alherin da ake samu), sai ya kare maka kanka da kansa, sallarka da sallarsa, to sai ka gode masa a kan hakan".
Hakkin Abokin Zama: "Amma hakkin abokin zamanka sai ka tausasa masa dabi'arka, ka yi masa adalci a yin magana, kada ka tashi daga majalisinka sai da izininsa, amma wanda yake zama gunka shi yana da hakkin ya tashi daga gunka ba tare da izini ba, ka manta da munanansa, ka kiyaye alherinsa, kuma kada ka jiyar da shi komai sai alheri".
Hakkin Makoci: "Amma hakkin makocinka shi ne ka kiyaye shi idan ba ya nan, ka girmama shi idan yana nan, ka taimaka masa idan ana zaluntarsa, kada ka bibiyi sirrinsa, kuma idan ka san wani mummuna nasa sai ka boye masa shi (kada ka yada shi), idan ka san yana karbar nasiharksa sai ka yi masa ita tsakaninka da shi, kada ka rabu da shi gun tsanani, ka yafe masa kurakuransa, ka yafe masa laifinsa, ka zauna da shi zaman mutunci, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Aboki: "Amma hakkin aboki shi ne ka yi abota shi da fifita (shi) da yin adalci, ka girmama shi kamar yadda yake girmama ka, kada ka bar shi ya riga (ka) gaggawa zuwa ga wani alheri, idan kuwa ya riga (ka yin alheri) to sai ka saka masa, ka so shi kamar yadda yake son ka, ka kare shi daga abin da yake nufinsa na wani sabo, ka kasance rahama gareshi kada ka zama azaba a kansa, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Abokin Tarayya: "Amma hakkin abokin tarayya (wanda kuka hada hannun cinikayya) shi ne idan ba ya nan sai ka kare shi, idan yana nan sai ka kiyaye shi, kada ka yi wani hukunci sai da nasa hukuncin, kada ka yi aiki da ra'ayinka ba tare da tasa mahangar ba, ka kiyaye masa dukiyarsa, kada ka ha'ince shi cikin abin da yake babba ne ko karami na lamarinsa, ka sani hannun Allah yana tare da hannayen masu tarayyar (hada hannun jari) matukar ba su ha'inci juna ba, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Dukiya: "Amma hakkin dukiyarka shi ne kada ka dauke ta sai ta hanyar halal dinta, kada ka ciyar da ita sai ta inda ta dace, kuma kada ka zabi kanka da ita a kan wanda ba ya yabonka, to sai ka yi aiki da ita wurin biyayyar ubangijinka, kuma kada ka yi rowa da ita sai ka koma da hasara da nadama tare da jama'ar (tababbu), kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Mai bin Bashi: "Amma hakkin mai bin ka bashi da yake neman ka biya, to idan kana da yalwa sai ka ba shi, kuma idan ka kasancemaras
yalwa, to sai ka nemi yardar da shi da kyautata magana, ka mayar da shi daga kanka mayarwa mai taushi".
Hakkin Abokin Cudanya: "Amma hakkin Abokin cudanya shi ne kada ka yi masa 'yar rufe, kada ka yi maza zambo, kada ka yi masa yaudara, ka ji tsoron Allah madaukaki da girmama a kan lamarinsa".
Hakkin Mai Kara: "Amma hakkin abokin shari'a wanda ya yi da'awar wani abu a kanka, shi ne idan abin da yake da'awarsa a kanka gaskiya ne to sai ka yarda da shi yana kanka, kada ka zalunce shi, ka biya shi hakkinsa, idan kuwa abin da yake da'awarsa a kanka ya kasance karya ne, to sai ka tausasa masa, kada ka zo da wani abu kan lamarinsa sai tausasawa, kuma kada ka fusata ubangijinka game da lamarinsa, kuma babu karfi sai da Allah.
Hakkin Wanda ake Kara: "Amma hakkin abokin shari'a da ka kai shi kara, (ka sani) idan ka kasance mai gaskiya a kararka to sai ka kyautata maganarsa, kada ka yi musun nasa hakkin, idan kuwa ka kasance mai karya ne a kararka, to sai ka ji tsoron Allah mai girma da daukaka, ka tuba zuwa gareshi, ka janye wannan karar".
Hakkin Maineman
Shawara: "Amma hakkin mai neman shawara shi ne; idan ka san yana da wani ra'ayi (mai kyau ne) sai ka yi masa nuni da shi, amma idan ba ka sani ba, to sai ka shiryar da shi zuwa ga wanda ya sani".
Hakkin Maibayar
da Shawara: "Amma hakkin mai ba ka shawara shi ne kada ka tuhume shi idan ra'ayinsa cikin abin da bai yi muwafaka da kai ba na ra'ayinsa, idan kuwa ya yi muwafaka da kai to sai ka gode wa Allah mai girma da daukaka".
Hakkin Maineman
Nasiha: "Amma hakkim mai neman nasiha shi ne ka ba shi nasihar, kuma ya kasance kai abin da kake nufi shi ne tausayi gareshi da tausasa masa".
Hakkin Mai yin Nasiha: "Amma hakkin mai yin nasiha shi ne ka tausasa masa dabi'arka, ka saurara zuwa gareshi da jinka, to idan ya zo maka da dacewa sai ka gode wa Allah mai girma da daukaka, amma idan bai dace ba, sai ka mantar kada kuma ka tuhume shi, ka sani shi ya yi kuskure ne kawai kuma kada ka rike shi da wannan sai dai idan ya cancanci tuhumar ne, kowane hali dai to kada ka damu da lamarinsa, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Babba: "Amma hakkin babba shi ne ka girmama shi saboda shekarunsa, da daukaka shi saboda rigon da ya yi maka a musulunci kafin ka zo duniya, da barin jayayya da shi yayin husuma, kuma kada ka riga shi kan hanya, kada ka shiga gabansa, kada ka nuna jahilcinsa, idan kuwa ya yi maka wauta to sai ka jure ka daure, ka girmama shi saboda hakkin musulunci da alfarmarsa".
Hakkin Karami: "Amma hakkin karami shi ne ka tausaya masa cikin koyar da shi, da yin rangwame gareshi, da suturta masa, da tausasa masa, da taimaka masa".
Hakkin Mai Roko: "Amma hakkin mai roko shi ne ka ba shi daidai gwargwadon bukatarsa".
Hakkin Wanda ake Roka: "Amma hakkinwanda
ake roka shi ne idan ya bayar to sai ka karba daga gareshi da godiya da sanin kyautatawa, amma idan ya hana sai ka karbi uzurinsa".
Hakkin Mai Farantawa: "Amma hakkinwanda
ya faranta maka rai shi ne ka godewa Allah madaukaki sannan sai ka gode masa".
Hakkin Mai Batawa: "Amma hakkin mai munana maka shi ne ka yi masa afuwa, amma idan ka san yin afuwa zai cutar to sai ka nemi taimako (kansa). Allah madaukakiyana
cewa: "Kuma duk wanda ya nemi taimako bayan zaluntarsa, to wadannan babu wani laifi a kansau". (Shura: 40)".
Hakkin Al'umma: "Amma hakkin al'ummarka shi ne ka sanya aminci garesu, da tausaya musu, da tausasawa ga mai sabawarsu, da sabo da su, daneman
gyaransu, da godiya ga mai kyautatawarsu, da kame cutar da su, da so musu abin da kake so wa kansa, da ki musu abin da kake ki wa kanka.Tsofaffinsu su kasance tamkar baba ne gareka, samarinsu su kasance kamar 'yan'uwa ne gareka, gyatumominsu su kasance kamar uwa ce gareka, kanana su kasance tamkar 'ya'ya".
Hakkin 'Yan Amana: "Amma hakkin 'yan amana (wadanda ba musulmi ba da suke rayuwa tare da musulmi bisa yarjejeniyar rayuwa tare), shi ne ka karba daga garesu abin da Allah ya karba daga garesu (na
su yi nasu addinin da rayuwarsu), kada ka zalunce su matukar sun cika wa Allah alkawarinsa (ba su zalunce ka ba suna masu karya yarjejeniya".
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Saturday, June 04, 2011