• Farawa
  • Na Baya
  • 11 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 2439 / Gurzawa: 2520
Girma Girma Girma
Canjin Ra'ayi

Canjin Ra'ayi

Mawallafi:
Hausa

BADA'U-CANJIN RA'AYI-

Wallafar: Al-Majma'ul alami Li Ahlil-bait

Fassarar: Hafiz Muhammad Sa’id

AL-BADA'U -SAMUN CANJIN RA'AYI-

Da Sunan Allah Ta'ala Mai Rahama Mai Jin Kai

Kura'ni Da Hadisi Suna Cewa:

“Allah yana shafe abin da yake so, kuma yana tabbatarwa, kuma a gunsa akwai Ummul Kitabi” Surar Ra’adi: 39

“Wanda ya raya cewa, Allah madaukakin sarki yana samun canaji a wani abu, da bai san shi ba jiya, to ka barranta da shi”

Biharul Anwar: 4111, H 30.

Gabatarwar Al-Majma'ul alami Li Ahlil-bait

Lallai yana daga cikin dabi’ar mutane su yi sabani a junansu, sai dai Allah yana son wannan sabanin ya takaita a cikin kewayen ingantaccen imani, saboda haka ne ba makawa ya zamanto akwai ma’auni tabbatacce da masu sabani zasu koma zuwa gare shi. Allah madaukakin sarki ya saukar da littafi da gaskiya domin ya yi hukunci tsakanin mutane da gaskiya cikin abin da suka saba a cikinsa[1] .

Da babu wannan gaskiya guda daya, to da al’amarin rayuwa ba zai daidaitu ba, Wannan shi ne abin da Kur’ani yake tabbatar da shi kuma yake bisa ka’idar tauhidi, sannan sai daga baya aka samu karkata da sabani da camfe-camfe har mutane suka nisanta daga wannan asasi nisanta mai girma.

Ta haka ne ta bayyana cewa mutane ba su ne masu cancantar su yi hukunci da gaskiya ko karya ba matukar sun kasance suna iya biye wa son rai da bata da zalunci.

Duk da littafin Allah ya sauka da shiriya ya kuma isa zuwa ga mutane…. tare da hakan son rai ya rinjayi mutane nan da can, kwadayi da tsoro da bata suka nisantar da mutane ga karbar hukuncin littafi da komawa zuwa ga gaskiya da yake dawo da su zuwa gareta.

Bata shi ne ya jagoranci mutane a tsawon zamani zuwa ga sabani da shisshigi da kin Allah, Jahilci ya zama wani sababin sabani da rarraba, sai dai shi jahili ya kamata ne ya tambayi malamai kamar yadda Allah ya fada: “Ku tambayi ma’abota sani idan ba ku sani ba[2] ”.

Ta haka ne ketare iyakar jahili ya kasance zalunci da shisshigi ga wannan asali wanda hankali yake amincewa da shi, kuma ma’abota hankula suke karkata zuwa gareshi, kuma lallai wannan shi ne mafi bayyanar ka’idoji da hanyoyi wadanda zasu toshe hanyar rarraba da sabani.

Musulunci shi ne addinin Allah dawwamamme da hakikarsa ta bayyana cikin nassin littafin Allah (S.W.T) da sunnar manzonsa (S.A.W) da ba ya magana da son rai sai da wahayi. Kuma Allah da manzonsa sun sani cewa al’ummarsa zata yi sabani bayansa kamar yadda ta yi sabani a lokacin rayuwarsa, don haka ne Kur’ani mai girma ya sanya wa al’umma makoma da zasu dogara da ita bayan wafatin manzo (S.A.W) tana tafiya tare da shi taku-taku tana kuma gabatar wa al’umma abin da suka takaita ga fahimtarsa da tafsirinsa, wannan kuwa su ne; Ahlul Baiti (A.S), sun tsarkaka ne daga dukkan dauda da kuma kazanta wadanda Kur’ani ya sauka ga kakansu Mustapha (S.A.W), suna karbarsa suna karanta shi suna hankaltarsa da kiyayewa, sai Allah ya ba su abin da bai ba waninsu ba... Kamar yadda manzo ya yi wasiyya da su a matsayin makoma ta gaba daya a hadisin sakalain mash’huri, sai suka kwadaitu wajan kare shari’ar musulunci da Kur’ani mai girma daga fahimta ta kuskure da tafsiri na barna, suka saba da bayanin ma’anarsa madaukakiya, sai suka zama makoma kuma madogara ga al’ummar musulmi, suna kore shubuha suna masu karbar tambayoyi da hakuri da juriya. Bayan nan abin da suka bari mai yawa yana shaidawa da kyawon mu’amalarsu tare da masu tambayarsu da tattaunawa da su, kuma komawa garesu da zurfin amsawarsu yana nuni zuwa ga kasancewarsu makoma ta ilimi a wannan fage.

Hakika koyarwarsu ta kare abin da suka bari, kuma mabiyansu suka kwadaitu a kan kare shi daga tozarta, abin da yake nuni zuwa ga koyarwarsu da ta tattaro dukkan wasu rassa na ilimomin da suke kunshe cikin koyarwar addinin musulunci.

Kuma wannan makaranta ta iya tarbiyyatar da mutane da suke shirye domin kamfata daga wannan ilmi kuma ta fitar wa al’umma manyan malamai masu biyayya ga tafarkin Ahlul baiti (A.S), suna masu gamewa da sanin dukkan mas’alolin mazhabobi daban-daban, da kuma akidoji a cikin da’irar musulunci da wajanta, suna masu bayar da mafi kyawon amsa da bayanai a tsawon zamanin da ya gabata.

Hakika majma Ahlul baiti (A.S) ya gaggauta yana mai farawa daga nauyin da yake kansa da ya dauka a kafadunsa domin kariya ga sakon musulunci wanda ma’abota mazhabobi da kuma masu akidu da suka saba wa musulunci suka damfaru da su, yana mai bin tafarkin Ahlul Baiti (A.S) da mabiyansu da suka kwadaitar da raddi kan kalu-balen wannan zamani da kuma kokarin dawwama a kan tafarkin gwagwarmaya daidai gwargwadon abin da kowane zamani yake bukata.

Ilimin da littattafan malamai masana ma’abota bin koyarwar Ahlul baiti (A.S) suka taskace shi a wannan al’amari ba shi da misali, domin shi madogara ce ta ilmi da yake karfafa da dogara da hankali da hujja, yake kuma nisantar son rai da zargi, yake kuma magana da malamai masu tunani daga ma’abota kwarewa, maganar da hankali yake yarda da ita kuma dabi’ar dan Adam kubutacciya take karbar ta.

Kokarin majma ya zo ne domin ganin an gabatar wa dalibai sabuwar marhalar wannan ilimi mai wadata a shafin tattaunawa da tambaya da kuma raddin shubuha da a kan tayar daga lokaci zuwa lokaci tsawon zamani, ko kuma ake kawo wa a yau musamman ma da taimakon wasu kungiyoyi masu kin musulunci da musulmi a cikin sarkar sama ta intanet da makamantansu, muna masu nisantar abin da yake maras kyau, muna masu kwadayin motsa tunanin masu hankali da masu neman gaskiya domin su bude idanunsu a kan gaskiyar da koyarwar da Ahlul baiti (A.S) suka gabatar wa duniya baki daya a zamanin da hankula suke cika, alakar mutane da tunani take samuwa cikin gaggawa.

Ba makawa mu yi nuni da cewa wannan tattararrun bahasosi an tanade su ne a lujna ta musamman da Hujjatul Islam Abul Fadal Islami yake shugabanta tare da wasu manya da suka hada da Sayyid Munzir Hakim, da Shaikh Abudlkarim Bahabahani, da Sayyid Abdurrahim Musawi, da Shaikh Abdul Amir Assuldani, da Shaikh Muhammadul Amini, da Shaikh Muhammad Hashimi Al’amili, da Sayyid Muhammad Rida aali Ayyub, da Shaikh Ali Baharami, da Husaini Salihi, da Aziz Al’ukabi.

Kuma muna mika godiya mai yawa ga dukkan wadanan da kuma ma’abota falala da bincike da suka hada da: Shaikh Yusuf Garawi, da Shaikh Ja’afarul Hadi, da Ustaz Sa’ib Abdulhamid, domin bibiyar da kowannensu ya yi wa wadannan bahasosi da kuma bayanansu masu kima.

Fatanmu shi ne ya zama mun gabatar da abin da zamu iya na kokarin sauke nauyin da yake kanmu game da wannan sako mai girma na ubangijinmu da ya aiko manzonsa da shiriya da kuma addinin gaskiya domin ya daukaka shi a kan dukkan wani addini kuma Allah ya isa shaida.

Al-Majma'ul alami Li Ahlil-bait

Birnin Kum – Iran.

Bada'u A Cikin Kur’ani Mai Girma

Ana la’akari da Bada’ a cikin al’amura na kalam na tauhidi da aka tayar da bahasi mai fadi a kansa tsakanin malaman Ilimin Sanin Allah. Wannan kuma ya faru saboda wasu abubuwa masu jan hankali da suke kan maganar Bada ne. Domin Bada a lugga yana nufin bayyana bayan boyuwa. yana kuma hadawa da tattaunawa ta al’ada, da kuma wajan musanya ra’ayoyi da tunani da hadafi da manufofi, misalin a kan ce: “Da ra’ayinsa kaza ne sannan sai ya samu canji a game da ra’ayin” Abu ne sananne cewa canjin ra’ayi da wannan ma’ana tana kunshe da ma’anar jahilci da ya rigaya, da kuma faruwar sabon ilmi kan al’amarin. kuma dukkansu koraru ne ga Allah madaukakin sarki domin ilmin Allah madaukakin sarki ainihin Allah ne, babu wani jahilci da ya rigaye shi.

Sai dai idan muka zurfafa tunani kan ma’anar Bada a ma’anarsa ta lugga to zamu same shi yana hauhawa daga abu biyu ne:

1-Jahilci da ya rigaya.

2-Canjin ra’ayi da manufa da hadafi sakamakon sabon ilimin da aka samu.

Sai mu tambaya wanne ne daga wadannan al’amura guda biyu yake kore Tauhidi? Na farko ko na biyu?

Kuma shin zai yiwu a raba tsakaninsu? Ta yadda za a samu wani canji a ra’ayi ba tare da ya kasance daga jahilci da ya rigaya ba ko kuma ilimi sabo da ya faru ba?

Amma tambayar farko: Zamu ga cewa a sarari yake cewa al’amari na farko yana kore tauhidi, kuma babu wani musulmi da ya karbi jingina wa Allah madaukakin sarki jahilici.

Amma abu na biyu: Idan canji ya zama yana lizimtar zati domin jahilci da ya gabata ne da kuma samuwar ilimi da ya zo. to a nan yana kore tauhidi, kamar yadda jahilci yake kore tauhidi haka ma canji yake kore shi. Amma idan canji ba ya samun zati yana faruwa daga wani abu daban to anan ba ya kore Tauhidi.

Wanna canjin na ra’ayi da yake lizimtar zati domin bayyanar ilimi da kuma bacewar jahilci, saboda haka ne kamar yadda ba zai yiwu a jingina jahilci ga Allah ba haka nan ba zai yiwu a jingina masa canji a ra’ayi ba (S.W.T) domin wannan yana nuna ilimi ne da aka samu, alhalin ilimin Allah ba wanda ake nema ba ne domin a samu. Shi iliminsa na zatinsa ne wanda yake shi mai tsayuwa ne da samuwar zatinsa.

Da wannan ne jawabin wadanna tambayoyi biyu ya bayyan a fili, kuma bari mu gani shin akwai aya a kur’ani da ta dangantawa Allah canji a wani al’amari, ko wani bangare?

Akwai wadanda sukan amsa cikin gaggawa game da wannan suna masu cewa alkur’ani mai girma ya kore duk wani canji ga Allah (S.W.T) suna masu dabbaka wannan aya: “Ba zaka taba samun juyi ba ga sunnar Allah”[3] . “Ba zaka taba samun canji ba ga sunnar Allah”[4] .

Sai dai wanan jawabi bai isa ba, domin kur’ani wani abu ne da ake fahimtarsa daga dukkan kur’ani, ba daga wani bangare ba kawai. Wannan kusan muna iya cewa yana zama rabin amsa ne, domin akwai wani bangare da yake jingina canji ga Allah da cewa: “Allah yana shafe abin da ya so yana kuma tabbatar da abin da ya so kuma a gunsa akwai Ummul kitab”[5] .

Da fadinsa madaukakin sarki: “Allah ba ya canja abin da ke ga mutane har sai sun canja abin da yake ga kawukansu”.

Aya ta farko tana nuna Allah yana shafe abin da ya so yana kuma tababtar da abin da ya so wanda wannan yake nuna canji da sakewa, amma aya ta biyu ta shelanta a fili cewa Allah ba ya canja halin mutane idan suka canja abin da yake ga kawukansu. Al’amarin tattalin arziki da siyasa na mutane yana nufin wani abu ne da Allah yake kaddara shi da zai iya karbar canji idan mutane suka canja rayuwarsu daga shirka zuwa ga imani, daga bata zuwa ga shiriya, to a nan akwai kaddarawa guda biyu; kaddarawa da ta zo daga halin mutane na biyayyarsu, da kuma kaddarawar Allah garesu a halin sabonsu, idan suka zabi biyayya sai a gudanar musu da na farko idan kuma suka zabi sabo sai a gudanar musu da al’amari na biyu, da kana ne abin da ya zo a ruwaya da yake nuna tasirin ayyuka wajan arzutawa da ajali da bala’o’i yake nuni.

Wannan kuma ba wanda ya saba daga muslumi game da hakan; sabani ya samu ne kan ma’anar “Bada” idan aka fassara shi ta yadda zai saba da ma’anar da ya saba da lugga da ya kore tauhidi, amma sabanin zai kau idan aka komawa ma’anar da ake nufi a isdilahi da ba ya lizimtar danganta jahilci ga Allah (S.W.T). Abin da ake nufi a koyarwar Ahlul baiti (A.S) shi ne “Allah yana kaddara wa bayi wani abu sannan sai ya canja sakamakon wani abu sabo da ya bayyana daga bawa sakamakon wani aiki daban da ya yi, tare da cewa Allah ya riga ya san duka al’amuran biyu zasu faru a dukkan halayen biyu”.

Da sun san wannan ma’ana da sun san cewa wannan wani abu ne da dukkan msulmi suka hadu akansa. Shi ya sa jayayya din kan lafazi ne kawai, kuma Allama Sayyid Abdulhusaini Sharafuddin ya yi gaskiya yayin da ya ce: “Jayayya tsakaninmu da Ahlussunna ta lafazi ce. Sannan sai ya ce: Idan waninmu ya dage a kan wanann jayayya ya ki yadda da ma’anar ‘Bada’ kamar yadda muka fada, to mu sai mu sauka a kan hukuncinsa sai ya canja lafazin da abin da ya so, ya kuma ji tsoron Allah a kan dau’uwansa mumini[6] .

Kafinsa akwai Shaihul Mufid a littafinsa yana cewa; “Amma amfani da kalmar Bada wannan ruwaya ce ta zo da ita wacce abu ne da yake tsakanin Allah da bayinsa, ba domin ruwaya ta zo da shi ba da take da inganci da bai halatta ba a yi amfani da shi ga Allah (S.W.T), kamar yadda da ba don ruwaya ta zo da cewa Allah yana fushi, yana yarda, yana so, yana jiji-da-kai, da bai halatta a gaya masa haka ba, sai dai yayin da ya zo a ruwaya sai ya zama yana da ma’anar da hankula suka tafi akai da ba sa kin ta, kuma tsakanina da sauran msulmi a wannan babi babu sabani, kawai sabanin da ake dashi a lafazi ne ba a wani abu ba, na kuma riga na yi bayanin dalili na a kan amfani da wannan lafazi. Wannan kuma shi ne mazhabar imamiyya gaba daya, kuma duk wanda ya saba wa wannan mazhaba yana sabani ne a lafazi ba a ma’ana ba[7] .

Kafinsa Imam Assadiq (A.S) ya fada a tafsirin ayar nan: “Allah yana shafe abin da ya so yana kuma tabbatar wa kuma a gunsa akwai Ummul kitab”. Ya ce; “Dukkan wani al’amari da Allah yake son shi to akwai shi a cikin iliminsa kafin samar da shi, ba wani abu da yake bayyana gareshi sai ya kasance da ma can yana da ilimi da shi, Allah ba ya canja wa sakamakon jahilici”[8] . A wani hadisin yana cewa: “Wanda ya raya cewa Allah madaukakin sarki yana samun canaji a wani abu, da bai san shi ba jiya, to ka barranta da shi”[9] . Sannan madogarar dalilin imamiyya a mas’alar Bada a bu uku ne:

1-Faidansa: “Allah yana shafe abin da da ya so ya kuma tabbatar da abin da ya so kuma a gunsa akwai Ummul kitab”[10] .

Da fadinsa: “Wanda yake sama da kasa yana tambayarsa, kowace rana yana cikin sha’ani ne”[11] .

2-Kamantuwar wanann mas’ala da mas’alar shafe hukunci a shari’a, Bada shafewa ne a samarwa, Naskh kuma shafewa ne a hukunci. Kamar yadda msulmi suka tabbatar da shafewa ga hukunci a shari’a kamar a mas’alar alkibla daga masallacin al’akasa zuwa ga masallacin ka’aba, kuma ba wanda ya saba a wannan na daga musulmi. Wannan kuma ba a gan shi a matsayin canji a ilimin Allah ba, bai kuma lizimtawa Allah jahilci ba da ya gabata, haka nan mas’alar Bada canji ne amma a samarwa ba tare da ya lizimta wa Allah jahilci da ya rigaya ba, ko sabawa ga iliminsa na tun fil azal, idan wani ya kawo matsala game da Bada, to sai ya kawo matsala game da shafewa, abin da duk muka fada game da shi a babin shafe hukunci haka ma yana iya zama dalili a babin Bada ba tare da wani bambanci ba ko kadan tsakanin al’amuran biyu. Suka a kan Bada yana zama maimaitawa ne ga sukan da yahudawa suka yi wa shafe hukunci a farkon shari’a yayin da suke ganin wanan bata ne da kuma rashin yiwuwar danganta shi ga Allah (S.W.T) kamar yadda ya zo na daga amsoshi da malaman msulmi suka ba su da kuma tabbatar musu da yiwuwar shafe shari’a ba tare da wanan ya lizimta samuwar tawaya ga zatin Allah madaukakin sarki ba, haka ma wannan yake yiwuwa ga Bada a babin halittawa da samarwa da kuma tafiyar da al’amuran bayi.

3-Tasirin ayyuka a game da makomar mutum; wanan kuma gaskiya ce tabbatacciya ta kur’ani, hada da cewa sunnar annabi mutawatira ta zo da karfafawa a kan hakan, da cewa ayyukan mutum na imani, da shirka, da biyayya, da sabo, da bin iyaye, da saba musu, da ciyar da talakawa, da kamewa ga barin hakan, da sadar da zumunci, da yankewa,… duk suna da tasiri wajan arziki da albarkar da kuma tsawon rayuwa da sa’ada. Wadannan al’amura suna daga abubuwan da kur’ani ya ambata saudayawa, kuma sunnar annabi ta karfafa su.

Fadinsa madaukaki “Allah ba ya canja abin da yake ga mutane har sai sun canja abin da yake garesu”. Wanda yake musun Bada musunsa zai kai shi zuwa ga musun wannan hakika bayyananniya ce koda kuwa yana imani da ita, ya sani cewa wannan abin da yake imani da shi, shi ne imamiyya take kira da Bada.

Maganar Malaman Imamiyya Game Da Bada

Wanann shi ne abin da malamai na imamiyya suka karfafa na da da na yanzu, Shaihul Mufid yana cewa: “Fadin imamiyya game da Bada an same shi ne daga ruwaya ba daga hankali ba… ba abin da ake nufi da shi sai bayyanar wani ra’ayi bayan waninsa da kuma bayyanar al’amari bayan ya buya, Ubangiji madaukakin sarki a dukkan ayyukansa bayyanannu ne a cikin halittarsa bayan ta kasance, kuma ayyukansa sanannu ne gunsa cikin abin da bai gushe ba”[12] .

Sheikh Tusi yana cewa: “Bada hakikarsa a luga shi ne bayyana saboda haka ne ake cewa katangun gari sun bayyana garemu kuma ra’ayin ya bayyana garemu… amma idan aka raba wannan lafazi zuwa ga Allah (S.W.T), to akwai abin da ya halatta a danganta shi gareshi da kuma abin da bai halatta ba; Amma abin da ya halatta Bada shi ne abin da yake halatta shafe hukuncin shari’a, a kan haka ne kuma ake fassara duk abin da ya zo na daga hadisan Bada wanda ya zo daga imamai (A.S) banda da ma’anar da ba ta halatta ba ga Allah madaukakin sarki na ma’anar samun ilimin da bai sani ba a da”[13] .

Sayyid Abdullahi Shubbair ya ce: “Bada tana da ma’anoni masu yawa wasu ana iya siffanta Allah da su wasu kuma ba ya yiwuwa a sifatan shi da su, kuma al’umma ta hadu a kan cewa; ma’anar samuwar ilimi bayan jahilci ba ya halatta ga Allah kuma wanda ya daganta wa imamiyya wannan to ya yi musu kagen karya kuma imamiyya sun barranta da shi”[14] .

Sayyid Abdulhusain Sharafuddin ya ce: “Abin da shi’a suke cewa shi ne Allah yana rage rashin lafiya ko ya dada shi, haka nan ma game da lafiya da cuta da dacewa da tabewa da bala’o’i da musibu da imani da kafirci da saurana abubuwa kamar yadda Allah (S.W.T) yake fada: “Yana shafe abin da ya so ya na kuma tabbatarwa kuma a gunsa akwai Ummul kitab”[15] .

Wannan shi ne abin da Umar dan Khaddabi ya tafi akansa da dan Mas’ud da Abi Wa’il da Katada kuma Jabir ya rawaito shi daga manzon Allah (S.A.W), haka nan da yawa daga magabata suna addu’a suna kaskan da kai ga Allah da ya sanya su cikin masu arzuta ba masu tabewa ba, kuma hadisai mutawatirai sun zo daga imamanmu (A.S) a cikin addu’i da aka ruwaito, kuma ya zo a cikin littattafan Sunan masu yawa cewa sadaka, da bin iyaye, da aikata kyakkyawa, suna mayar da tabewa ta koma arzuta kuma su dada tsawon rayuwar mutum, kuma ya inganta daga Dan Abbas ya ce: “Daukar mataki ba ya kawar da kaddara sai dai Allah yana shafe abin da ya so na kaddara da addu’a”. Wannan kuma shi ne Bada din da shi’a suka tafi akansa kuma sabaninmu da Ahlussunna a Bada a lafazi ne… abin da shi’a suka fada game da Bada da wannan ma’ana da muka ambata dukkan musulmi sun tafi akansa…”[16] .

Shaikh Aga Buzurg ya rubuta yana cewa: “Bada ma’anarsa a lugga shi ne; Bayyanar wani ra’ayi da babu shi a da da kuma canjin wani abu da aka sani bayan da ba a san shi ba. Wannan ita ce fahimtar dukkan mutane sai dai wannan mustahili ne ga Allah (S.W.T) saboda yana lizimtar bayyanar sani da wani abu da da dacan ba a san shi ba, ko kuma gajiya a kan aikata shi wanda Allah ya tsarakaka daga garesu… Bada da imamiyya suke kudurce shi; Shi ne wanda sauran musulmi suke imani da shi da yake sabanin abin da yahudawa suka tafi a kai na cewa; Allah ya riga ya gama komai kuma ba yadda za a yi wani abu ya canja gunsa “Hannun Allah abin yi wa kukumi ne”. Ko kuma idan ka bi maganganun yahudawa zaka ga cewa suna ganin Allah ya samar da dukkan halittu a tashi daya. Babu wani abu da za a samu gunsa sai ya kasance da ma can an same shi tun farko. Ko kuma masu ganin cewa Allah ya halicci mala’ika na farko da sauran rauhanai masu juya falaki kuma ya bar su su aiwatar da abin da su kan tafiyar da al’amuran bayi, shi kuma ya kau da hannunsa wajan tafiyarwa. To wadannan akidoji dole ne ga kowane musulmi ya kore su ya kuma kudurce cewa Allah madaukakin sarki: “Kowace rana shi yana cikin wani sha’ani...[17][18] .

Muhimmancin Bada Wajan Tarbiyyantarwa Da Ingantacciyar Akida

Ya bayyana kamar yadda ya rigaya cewa; Bada yana da ma’ana da take sananniya gun musulmi gaba daya kuma imamiyya ba su da wata ma’ana da ban da ta sabawa sauran musulmi, sai dai kawai ma’ana ta lugga da lafazi da aka fahimci kuskure ne dangantawa Allah jahilci kuma ya bayyana cewa bai halatta ba danganta wannan ma’ana ga Allah madaukakin sarki. Domin akidun musulmi ana auna su da ma’aunin asasinta na ilimi da kuma dalilanta na hankali ne wani lokacin kuma da sakamakon da take haifarwa, amma game da Bada akwai tambayoyi da zamu iya kawowa da kuma amsar su kamar haka:

*- Idan ya kasance Allah ya riga ya yi hukunci na farko kuma ya san ba shi ne zai yi tasiri ba zai kai ga wurgar da shi ne, to menene amfanin bayar da labarinsa? Menene kuma amfanin da za a samu daga Bada a wannan yanayin?

Amsa: imani da Bada yana da amfani ta bangare biyu masu muhimmanci, bangaren akida da kuma bangaren tarbiyya;

Fuska ta farko: Amma game da akida maganar da Allama majlisi ya kawo ta wadatar yayin da yake cewa: “Imamai (A.S) sun kai matuka wajan fadin Bada domin su yi raddi ga yahudawa da suke cewa Allah ya riga ya gama komai ya gama tsarinsa, da kuma wasu daga mu’utazilawa da suke cewa: Allah ya halitta halittu lokaci daya kamar yadda suke, wanda ya hada da ma’adinai, da shuke-shuke, da dabbobi, da mutane, kuma (suka ce) ba ya gabatar da halitta a kan duk wata halitta, domin gabatarwar tana kasancewa ne a yadda take bayyana ba a faruwarta ba da samar da ita. Wannan kuma sun same shi ne daga maganar malaman falsafa da masu imani da nazarin mala’iku da rauhanai masu juya falaki da su ne ke juya al’amuran bayi, suna ganin Allah ya riga ya bar tafiyar da al’amuran bayi, suna danganta komai zuwa garesu ba zuwa ga Allah ba”[19] .

Karfafawar imamai (A.S) a kan Bada ya zo ne domin raddin dukkan wata mahanga da wani ra’ayi da yake iyakance ikon Allah da kudurarsa, da kuma tabbatar da cewa wannan hakika ce tabbatacciya a siffofin Allah cewa yana halitta abin da ya so kamar yadda ya ga dama yana kuma tafiyar da al’amuransu kuma kaddarawarsa ba ta cire masa iko da nufi da zabi.

Kamar yadda Bada ya zo domin ya karfafi zabin mutum da nifinsa ta hanyar bayanin ikon Allah da yake cikin Lauhil mahafuz da ba ya karbar canji da kuma wani lauhin na shafewa da tabbatarwa wanda Allah ya halitta su tun farko cewa abin da aka zartar a cikinsa yana karbar ya canja shi daidai gwargwadon abin da mutum ya yi a wannan duniya na daga ayyuka.

Wato akidar Bada ta zo ne domin ta cika binciken nan na kaddarawar Allah da hukuncinsa saboda a kare wannan akida daga shige gona da iri domin kada a yi mata fahimta da ma’anar da zata cire wa Allah zabi da nufinsa. Saboda haka sai akidar Bada ta zo domin ta tabbatar da cewa kaddarawar Allah ba ta iya cire masa zabi kuma ba ta cire wa shi kansa mutum na sa zabin.

Fuska ta biyu: Ta fuskacin tarbiyya muna iya ganin akidar Bada ta yi tasiri wajan tarbiyyantar da rayuwar mutum. Allama majalisi ya bayyana dalilin da ya sa imamai suke karfafa Bada a cigaban maganarsa yana cewa: “Sai imamai suka kore wannan suka tabbatar da cewa Allah madaukakin sarki kullum yana cikin sha’ani ta hanyar rasarwa da fararwa, da kashewa da rayarwa, da makamantansu, domin kada bayi su bar addu’a da kaskantar da kai ga Allah da kuma rokonsa da binsa da kusanta zuwa gareshi da abin da zai zama maslahar duniya da lahira garesu, kuma domin su nemi yin sadaka ga talakawa da sadar da zumunci da bin iyaye da horo da kyakkyawan aiki da kuma kyautatawa ga abin da aka yi musu alkawarinsa na tsawon rayuwa da dadin arziki”.

Ta wata jihar akidar Bada tana daidai da al’amarin akidar tuba da kuma sharuddan karbarta gun Allah, kamar yadda tuba yake da mfani wajan gina mutane da kuma toshe musu kofar yanke kauna da bude kofar buri da kauna da samar da kumajin canji da kawo gyara haka nan Bada yake da wannan tasiri a rayuwar mutum. Kai Bada yana zama daya daga abubuwan da suke lizimtar tuba da sauran ayyuka, domin dole ne mai tuba ya yi imani da cewa alkalamin Allah bai bushe ba a Allon shafewa da tabbatarwa, Allah yana shafe abin da ya so ya tababatar da abin da ya so ya arzuta wanda ya so ya tabar da wanda ya so daidai yadda bawa ya lizimci kyawawan dabi’u da kyawawan ayyuka ko kuma abin da yake yi na munanan ayyuka. Saboda haka ikon Allah da nufinsa ba haka nan kawai yake ba babu hikima ba, kai da bawa ya tuba ya yi aiki na gari da wajibai ya kuma yi riko da kamewa sai a fitar da shi daga cikin tababbu a sanya shi cikin masu arzuta, haka nan ma akasin hakan.

A kan haka muna iya fahimtar zancen imamai (A.S) cewa: “Ba a bauta wa Allah da wani abu da ya kai (imani da) Bada ba”[20] .

A wata ruwayar “ Ba a taba girmama Allah da wani abu da ya kai (imani da) Bada ba”[21] .

Da kuma wata ruwaya; “Babu wani annabi da Allah ya aiko sai ya daukar masa alkawarin dabi’a uku; furuci da bautar Allah da kuma sance dukkan gumaka kuma da fadin Allah yana gabatar da abin da ya so ya jinkirta abin da ya so”[22] .

Tambayoyi Da Amsa Game Da Imani Da Bada

Akwai tambayoyi da aka yi game da Bada kamar haka;

1- Imani da Bada yana iya kai wa ga wasa ya zo daga Allah (S.W.T) domin tare da ya san cewa za a samu canji a lokacin bayar da labari, ya zama wasa kenan.

Amsa: Wasa yana kasancewa ne idan an kaddara ba wani manufa da amfani da bayar da labarin zai samar, wannan kuma ba zai yiwu a iya tabbatar da shi ba domin akwai yiwuwar samun amfani da manufa da amfanin yana komawa ga bawa ne.

2- Idan annabi ya bayar da labari da faruwar wani abu sannan sai aka sami Bada a labarin farko ba makawa ya zama ya dogara ne da wani abu wajan bayar da labarin farko, kuma yaya annabi ko imami zai yi game da bayar da amsa kan abin da ya fada a baya?.

Amsa: Bari mu bayar da misali; Da wani zai sha guba mai halakarwa da zata kai ga mutuwa tabbas kana iya bayar da labarin mutuwarsa bayan awowi kuma wannan labari gaskiya ne idan an yi la’akari da abin da ya kai ga mutuwar, da mutuwar ba ta faru ba to dole ya zama saboda faruwar wani abu da ya hana afkuwar hakan, kamar zuwan likita da zai yi masa magani da cikakkiyar kwarewa, wancan bayar da labarin ba karya ba ne kuma ba a ganinsa bayar da labari ba dalili, haka nan al’amarin wahayi da yake bayar da labarin abin da zai faru a nan gaba duk gaskiya ne idan an yi la’akari da sababi wanda yake da sharadin rashin faruwar abin da zai hana aukuwar hakan, saboba haka a nan babu wani abin ki da zai lizimci wannan magana sai dai rashin sanin annabi ko imami da faruwar abin da ya hana aukuwar hakan, muna iya cewa Allah yana iya ba wa annabi labari da faruwar abin amma ya ki ba shi labari da abin da zai hana afkuwarsa saboda wata maslaha da take ga bayi[23] .

3- Faruwar Bada yana iya kaiwa ga tuhumar annabi ko imami da karya?.

Amsa: Tuhumar annabi ko imami da karya zunubin yana kan wanda ya yi haka ne, domin tuhumar idan ta zo daga kafiri to wannan ba mamaki domin da ma ya ki duk imani da Allah da annabta da makoma, idan kuma ya zo daga mumini to imaninsa zai hana shi, idan kuwa bai hana shi ba to wannan mai raunin imani ne.

Muhimmi a nan shi ne Bada ba dalili ne na hankali ba da zai sa tuhuma da karya, da yawa ma Bada yana bayar da yakini ne kamar a kissar Annabi Ibrahim (A.S) da aka umarta ya yanka dansa, fansar dan da wani abu yana bayar da yakini ne na farko da yanka dansa Isma’il (A.S). Ba don labarin farko ya zama gaskiya ba da ba a umarce shi da yanka rago ba maimakon dansa, domin fansa a nan tana nufin canji (Bada).

Bayanin Abin Da Ya Gabata A Takaice

Bada da ma’anar samun canjin ra’ayi mustahili ne ga Allah madaukaki kuma imamiyya ba sa imani da shi, wanda ya yi imani da hakan a wajansu kafiri ne kuma dole a barranta daga gare shi[24] .

Na’am Bada wanda yake hankali ya yarda da shi kuma wajibi ne a yi imani da shi, shi ne wanda ayar kur’ani mai girma ta yi bayaninsa: “Allah yana shafe abin da ya so yana kuma tabbatar (da abin da ya so) kuma a gunsa akwai Ummul kitabi”. Wannan shafewa da tabbatarwa ga abin da Allah yake bayyanarwa a harshen annabinsa ko waliyyinsa a zahiri yana zama domin maslahar da take cikin bayyanarwar ne, sannan sai ya shafe shi, sai abin da ba shi ne ya bayyanar ba ya faru tare da cewa Allah ya san hakan tun farko.

Bada ya yi kama da shafe shari’ar da suka gabata da shari’ar annabinmu Muhammad (S.A.W), ko kuma shafe wasu hukuce-hukunce da shari’ar ta zo da su da wasu hukunce-hukunce da suke bi musu[25] .

Wanda bai yi imani da Bada da wannan ma’ana ba hakika ya kayyade kudurar Allah da nufinsa, kamar yadda kur’ani ya yi nuni da hakan domin raddi ga wasu akidojin yahudawa a fadinsa madaukakin sarki: “Yahudawa suka ce: Hannun Allah abin yi wa kukumi ne, an sanya hannuwansu a cikin kukumi”[26] ![27] ”.

Wannan akida ta yahudawa ta shiga cikin akidun wasu daga kungiyoyi da mazhabobin akidu na musulmi ban da mazhabar imamiyya.

Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai

Makomar Bincike

____________________

[1] - Bakara: 213.

[2] - Anbiya: 7. Da Nahal: 43.

[3] - Fadir: 43.

[4] - Ahzab: 62.

[5] - Ra’ad: 39.

[6] - Ajwibatu Masa’ili Jarillah: 79.

[7] - Awa’ilul Makalat: 92-93.

[8] - Biharul Anwar: 4121, H 63.

[9] - Biharul Anwar: 4111, H 30.

[10] - Ra’ad: 39.

[11] - Arrahaman: 29.

[12] - Tashihul I’itikadatil Imamiyya: 66.

[13] - Iddatul Usul: 229.

[14] - Masabihul Anwar: 133.

[15] - Arra’ad: 39.

[16] - Ajwibatu Musa Jarullah: 101-103.

[17] - Arrahman: 29.

[18] - Azzari’a: 351-53.

[19] - Biharul Anwar: 4129-130.

[20] - Usulul Kafi: 1146. Kitabut Tauhid, Babin Bada.

[21] - Usulul Kafi: 1146. Kitabut Tauhid, Babin Bada.

[22] - Usulul Kafi: 1147. Kitabut Tauhid, Babin Bada.

[23] - Dubba kissar Annabi Yunus (A.S) da mutanensa wanda ya bar gari yana mai yakini cewa sun halaka bisa sunnar Allah. Hafiz Muhammad.

[24] - Aka’idul Imamiyya: 45.

[25] - Aka’idul Imamiyya: 46.

[26] - Ma’ida: 64.

[27] - Ma’anar hannayen Allah abin yi wa kukumi ne: Baya iya canja wani abu da ya hukunta ba yadda zai yi, wannan kuma shi ne ainihin iyakance iko da kudura na Allah. Ba kamar yadda wasu suka dauka ma’anarta tana nufi rowa ba domin ba wanda ya fi imam Ali (A.S) da Ahlin gidansa sanin ma’anar kur’ani. Kalmar infaki a ayar ba ta zo ba ne a matsayin karina da take nuna ma’anar ciyarwa sai dai ita tana nufin ma’ana mai fadi ta ayyukansa da ba su da iyaka. Ayoyin da suke magana a kan maudu’in da suka biyo bayan ayar suna nuna haka a fili da cewa; da sun yi aiki na gari da Allah ya canja hukuncinsa akansu.

Hafiz Muhammad Sa’id.

Abin da littafin ya kunsa

Kura'ni Da Hadisi Suna Cewa:2

Gabatarwar Al-Majma'ul alami Li Ahlil-bait 3

Bada'u A Cikin Kur’ani Mai Girma 6

Maganar Malaman Imamiyya Game Da Bada 9

Muhimmancin Bada Wajan Tarbiyyantarwa Da Ingantacciyar Akida 11

Tambayoyi Da Amsa Game Da Imani Da Bada 13

Bayanin Abin Da Ya Gabata A Takaice 14

Makomar Bincike 16

Abin da littafin ya kunsa 17