Rudewar Makarantar Halifofi Kan Fassasrar Wannan Hadisin
Anan
tambayar ita ce: su waye halifofi?
Kafin mu zabawa wannan tambaya wata takamammiyar amsa, ya zama lalle mu kawa tsammace tsammacen da zasu iya hawa kan wannan hadisin, da kuma mecece ainihin manufar Manzon Allah (s.a.w) da shi, a nan muna da tsammani guda biyu kacal da ba su da na uku:
Ko dai manufar Manzo (s.a.w) ta kasance yin bayanin hakikanin yadda siyasar al’ummar musulmi zata kasance a bayansa a bisa yanayi bada labarin abin da za faru da yaye abin da zai gudana nan gaba, bisa asasin bada labarai masu yawa da suka zo daga gare shi a cikin shu’unai mabanbanta, sai abin da hadisin yake nufi ya zama bada labarin abin da zai faru da al’umma nan gaba kuma bari mu kira wannan da tsammanin da sunan “bayanin abin da zai faru nan gaba”
Ko kuma manufar wannan hadisi ta zama zartar da hukunci tare da nada imamai sha biyu a matsayin halifofi a bayansa sai ma’anar wannan zartarwar da nadawar su zama daga abin da shari’a ta yi umarni da shi, ba wai a bada labarin abin da zai faru a nan gaba ba ne, kuma bari mu kira wannan tsammanin da sunan “bayanin akida”.
A bisa madogarar bincike ta ilimi abin da ya hau kan mu shi ne mu kulli wadannan tsammanoni guda biyu mu zabi wanda shedodi da dalilai da hujjoji na hankali da na nakali ke tabbatarwa tsakanin wadannan fassarori biyu, sai dai da yake su makarantar halifofi tun a farko sun riga sun yi imanin da shar’ancin tsarin halifanci kuma sun ki yarda da ra’ayin ayyanawa (daga Allah), kuma sun riga sun kafa ilimin akida da na fikihun da suka gada kan wannan asasi, sai suka sami kansu a gaban tsammani guda daya kawai wanda babu maguda daga gare shi, wanda shi ne tsammani na farko, kuma sai ya zame musu tilas su yi ta’awilin dukkanin abin da ya ci karo da hakan sannan su riki tawilin na su komai muninsa da nisantar sa da kaidojin hankali da al’ada, la’akari da cewa lamari ne da ba shi da abin da za a musanya shi da shi.
Kamata ya yi a ce sun kalli hadisin kallo na ilimi ‘yantacce daga duk wani tunani da ya gabata, domin su da kansu su iya tabbatar da kuskuren wannan fassara da suka yi wa hadisin ta abin da zai zo nan gaba, idan har Annabi Muhammadu (s.a.w) ya kasance ya na kallon abin zai zo nan gaba ne to don me zai fayyace adadin halifofi goma sha biyu, tare da cewa lokacin zai ta tafiya ya ma wuce iya zamanin halifofin? Idan har manufar Manzon Allah (s.a.w) ta
kasace ingantaccen halifanci wanda ya yi daidai da ma’aunin shari’a to fa tabbas makarantar halifofi ba ta yarda ba kuma ba ta yi ittafaki ba kan wasun halifofi hudu, kuma wannan ne dalilin da ya sa ra’ayoyin su suka saba a wajen ayyana su wanene halifofi sha biyu.
A wajen Ibnu-Kasir su ne Halifofi hudu da Umar dan Abdul’azizi da wasu daga cikin banu abbas kuma yace
a zahiri Mahadi a cikinsu yake.
A wajen Alkali Badamashke (Al-damashki) kuma: Su ne Halifofi hudu da kuma Mu’awiya, Yazid dan Mu’awiya, da ‘ya’yansa su hudu (Walidu da Sulaiman da Yazidu da kuma Hisham) na kashe kuma shi ne Umar dan Abdul’aziz.
A wajen Waliyullahil Muhaddis kuma a ciki Kurratul ainaini - kamar yadda ya zo a cikin Aunil Abdi, su ne halifofi hudu da kuma mu’awuya da Abdulmalik dan Marwan DA ‘ya’yansu guda hudu, da Umar dan Abdul’azizi da Walidu dan Yazid dan Abdulmalik, sannan an nakalto cewa Malik dan Anas ya shigar da Abdullahi dan Zubairu a cikinsu, sai dai ya ki karbar magana Maliku yana mai kafa dalili da abin da ya rawaito daga Umar da Usman; daga Manzon Allah (s.a.w) cewa salluduwar Abdullahi dan Zubairu kan al’umma musiba ce daga cikin musibobin da zasu fada wa wannan al’ummar. Sannan ya yi raddi gawanda
ya shigar da Yazidu cikin su da cewa ya kasance mai mummunar rayuwa da halaye.
Inbu Kayyimul Jauziyya ya ce: “amma halifofi goma sha biyu (12) hakika wasu mutane sun ce daga cikinsu akwai abu Hashim da ibni Hibban da waninsa: hakika na karshensu shi ne Umar dan Abdul’azizi, hakika sun ambaci halifofi hudu sannan Mu’awuya sannan dansa Yazidu sannan Mu’awuya dan Yazidu sannan Marwanu dan Hakam sannan dansa Abdulmalik sannan Walidu dan Abdulmalik sannan Sulaiman dan Abdulmalik sannan Umar dan Abdul’aziz, kuma Mu’awuya ya rasu a farkon shekata ta dari bayan hujira kuma shi ne mafificin karnin da ya fi ko wane karni, kuma addini ya kasnace a wannan karnin ya kai kololuwa wajen daukaka sannan abin da ya faru ya faru”.
Kuma Nurbashti ya ce: hanyar da ta dace a bi kan wannan maganar da ma abin da ya biyo bayanta na daga abin da ke tattare da wannan ma’ana shi ne a dora maganar kan adalai daga cikinsu, domin hakika su ne suka cancanci wannan sunan kuma be zama lalle su kasance a jere ba, kuma ko da a kaddara cewa a jere suke (daya na bin daya). To hakika dai abin da ake nufi shi ne su zama wadanda suka cancanci wannan matsayi (sai jerantawar a nan ta zama) da ma’ana ta (majazi), wato (ana nufin wadanda suka cancanta a jere), maker yadda ya zo a cikin littafin mikat”
.
A wajen Makrizi kuma su ne: “halifofi guda hudu sannan Imam Hasan (a.s) sannan yace
da shi ne kwanakin halifofi shiryayyau suka cika, kuma be shigar da ko daya daga halifofin banu umayya ba, kuma ya bayyana a sarari cewa halifanci bayan Imam Hasan (a.s) ya zama mulkin zalunci ya ce: “ma’ana a cikin matsi da tsanani”. Kamar yanda be shigar dako
daya daga cikin banu Abbas ba yana mai cewa a lokacin halifancin su ne kan musulmai ya rabu kuma aka cire sunan larabawa daga diwani (gudanarwa) kuma aka shigar da turkawa cikin diwani.Sannan kabilar dailam ta karbi iko a hannunuta, sannan turkawa, suka kafa daula babba mai karfin gaske.
Sannan kasashen musulmai suka karkasu gida-gida, yazama
ko wane yanki na da sarkin da ke shugabantar mutanensa da tsanani yana mulkarsu da karfi”.
Haka zaka yi ta ganin cin karon makarantar halifofi a wajen tafsirin da suka yiwa wannan hadisin, da yadda suka rika fadawa ramin da zai yi wahala su fito daga cikinsa mutukardai
sun yi tsayin daka kan tafsirin su na abin da zai zo nan gaba.
Tabbar Suyudi ya fadi a cikin Hawi: “har yanzu ba a sami wasu halifofi sha biyu da al’umma suka hadu a kan su ba”.
Da ace tafsirin (hadisin mahdawiyya) bisa abin da zai zo nan gaba a kankansa ya inganta da baki dayan sahabbai sun yi imani da shi kafin wasunsu, kuma da alamomin hakan sun bayyana daga bakin halifofin su da kansu (ba a bakin wadanda suka zo banaynsa ba) kama da na farkon su ya ce ni ne na farkon halifofi sha biyu, kuma da na biyu ya ce, na uku ma ya ce, na hudu ma ya ce, har zuwa na goma sha biyu. Kuma da wannan da’awar tazama
abin alfahari kuma shedar da zata temaka wajen tabbatar da shar’ancin ko wanne daga cikinsu, a yayain da tarihi be rubuta wannan da’awar ga daya daga cikin sunayen da aka ambata a cikin jerin sarkar halifofi goma sha biyun da aka kaddara cewa su ne su ba.
Sannan tabbas hadisinyana
yin nuni kan cewa tsawon lokacin halifanci halifofi goma sha biyu ta game baki dayan tsahon tarin musulunci har ya zuwa karshensa (tashin duniya) lokacin da kasa zata kife da wannan da yake cikin ta a bayansu. Hakika malaman ahlussunna sun rawaito daga Annabi Muhammadu (s.a.w) yace
: “Wannan addinin ba zai gushe ba a tsaye har sai shugabanni goma sha biyu daga kuraishu sun shugabance shi idan suka yi wafati sai duniya da halaka tare da wanda ke cikinta”.
Alhali duniya ba ta halaka tare da na cikinta bayan mutuwar Umar dan Abdulazizi ba, ballantana ma yaduwar ililmin addini kamar fikihu da Hadisi da Tafsiri a karni na uku da na hudu ya kai tsororuwar sa ne a wajen fadada da gamawa wanda hakan ya kasance ne bayan mutuwar wadannan halifofi sha biyu na ahlussuna, tare da cewa (a lokacin) ya kamata kasa ta yamutse (ta kisfe) tare da wanda ke cikinta!.
Haka ma an rawaito daga jabiru dan samarata:” Wannan al’ummar ba za ta gushe ba al’amarin ta yana kan daidai tana mai cin galaba kan makiyanta ba har sai halifofi goma sha biyu daga cikin ta sun shude dukkaninsu daga kuraishu sannan sai rudani ya wakana” .
Idan har abin da ake nufi da rudani shi ne firgici da hargowa da rikita-rikita, to ya kamata ya zama wani abu makamancin irin haka be faru ba a baya har ya zuwa lokacin Umar dan Abdulazizi, sai dai tarihi be san wata fitina da firgici ya yawaita a cikinta ba kuma rudani ya tsananta lokacinta ba kuma cakuda gaskiya ta karya ta yawaita a cikinta, kamar fitinar Mu’awiya, da ya yi fito na fito da halifan musulmai ba, kuma wannan na nuna cewa abin da ake nufi da rudani - a nan- abu ne da ya fi hargowa da rikita-rikita da hatsaniya, wata kila abin da ake nufi shi ne barin duniya baki daya, kuma wannan abu ne da ba zai faru ba sai tashin kiyama ya kusa wacce bayyanar imam Mahadi (aj) za ta gabace ta, da kuma abin da zai faru bayan ciratuwarsa zuwa matsayi madaukaki (wato wafatinsa) na daga fare-fare.
Sannan menene ma’anar shigar da sarakuna cikin adadin halifofi, hakika ahlussuna sun rawaito, daga Sa’adu dan Abiwakas, daya adaga cikin wadanda aka yi musu bushara da aljanna kuma daya daga cikin mazajen shurar - su shida - da Umar ya zaba, Hakika wata rana ya shiga wajen mu’awuya alhali yana
daga cikin wadanda ba su yi masa muba’ya’a ba. Sai yace
: “amincin Allah Ta'ala ya tabbata a gare ka ya kai sarki, sai ya ce da shi ba ka da wata kalmar ba wannan ba? Ku muminai neni
kuma shugabanku ne. Sai ya ce e haka ne. Idan mun kasance mun sa ka shugaba!a
wani lafazin kuma cewa ya yi: “mu ne muminai kuma ba mu shagabantar da kai ba” hakika A’isha ma ta musa wa Mu’awuya da’awar da ya yi ta halifanci kamar yanda Ibni Abbas ma ya musa, haka ma Imam Hasan (a.s) kai hatta ma bayan an yi sulhu.
Kuma ya kasanceyana
daga cikin azzalumai bisa ittifaki saboda hadisin “ya Ammar da sannu azzalumar jama’a zata kashe ka”. Ban sani ba, azzalumin da ya zalunci halifan musulmi na shari’a, ta yaya zai zama halifan Manzon Allah (s.a.w) kan
muminai!!
Kuma meye ma’anar shigar da Yazidu fajiri,wanda
da fajircinsa da yadda ya rika keta alfarmar Allah Ta'ala suka bayyana a sarari - hakika da gaske wannan na daga cikin abin ban mamaki sosai! Domin ta yaya zai inganta ga musulmi ya sanyawanda
ya zubar da jinin ‘ya’yan gidan Manzon Allah (s.a.w), ya kuma sa rundunar sa ta yaki madaina mai haske suka kashe dubban gomomin mutane, har sai da ya zama ba wani mahalarcin badar da ya yi saura bayan yakin Hurra, (ya zama shi ma) - halifan Manzon Allah (s.a.w) ne! Tabbas haka yanayin yake dangane da sarakunan la’antacciyar bishiya bisa nassin Kur’ani mai girma, hakika Manzo (s.a.w) ya gansu a cikin barcinsa - kuma mafarkin Annabawa gaskiya ne kamar ketowar alfijir ya ke - suna wasa a kan mimbarinsa kamar yanda birai su ke tsalle-tsalle bisa ittifakin mafi yawan mafassaran daga ahlussuna, wannan kuma a yayani da suke fassara aya ta sittin daga surar isra’i, da abin da babu bukatar bibiyar kalmominsu.
Da wannan ne zamu ga sakamako guda uku kyawawa sun bayyana a sariri, wadanda su ne:-
Kuskuren tafsirin bada labarin abin da zai zonan
gaba kan hadisin imamai goma sha biyu.
Rawar da siyasa ta taka wajen mayar da makarantar halifofi zuwa wannan fafsiri.
Kadaituwar hakika ta shari’a bisa tafsiri na akida na shari’a wanda ke cewa wannan hadisin yana nuni ne kan nada imamai goma sha biyu ga musulmai, kuma shi ne tafsirin da aka kafa masa dalilai na hankali da na kur’ani da na hadisai masu yawan gaske wadanda zamu same su a yalwace a cikin kayan kolin imamiyya na da, da ma na yanzo a fagagen tafsiri da Hadisi da ilimin Kalam da na Tarihi.
Kuma da alamun cewa tarihi ya ki yarda face wanzar da imamai goma sha biyu daga ahlulbaiti (a.s) su kasance hakikani tilona
wannan hadisin da aka ambata, ba mai jayayya da su a kan haka hatta a matakin da’awa, na farkon su shugaban muminai Ali dan abi dalib (a.s) na karshensu kuma Mahadi dan Hasan Askari (a.s). a cikin wannan akwai hadisai madankaka da suke yin nuni a kan sa da ba a isa a iyakance yawansu ba, a nan ma zamu yi nuni zuwa daya daga cikin wanda Imamu Juwaini ba shafi’e ya fitar da shi a cikin Fara’dul simdaini, daga dan Abbas daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “ni ne shigaban annabawa kuma Ali dan Abi Dalib shugaban wasiyyai, kuma hakika wasiyyai na a baya na goma sha biyu ne na farkonsu Ali dan Abidalib na karshensu kuma Mahadi (a.s)” .
Daganan
ne wasu daga cikin mahakkikai suka tsammaci
cewa abin da litattafan hadisi suka fada na cewa Jabir dan Samarata lokacin da wani abu daga maganar Annabi Muhammadu (s.a.w) ya buya a gare shi sai babansa ya ba shi amsa da cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Dukkaninsu daga kuraishawa suke”. Ana tsammaci jawabin da baban ya yi, ya zama akwai canja magana a cikinsa, saboda marawaicin ya fadi dalilin da ya sa jawabin ya buya da fadin sa “sannan sai mutanen suka yi hayaniya suka yi magana”, “kuma mutane suka yi hayaniya” “sai ya fadi wata kalma da mutanen suka hana ni jin ta” “sai mutane suka yi iface-iface sai ban ji abin da ya ce ba” “sai mutane suka yi kabbara suka yi hayaniya” “sai mutanen suka rika tashi tsaye kuma suna zaunawa” dukkanin wadannan ta’awile-tawilen ba su dace da maganar da marawacin bai ji ba, domin sanya halifa a cikin kuraishawa al’amari ne da yake faranta musu ba kuma zai jawa cece ku ce ba, alahali abin da ya dace da wannan yanayin da mai ruwaya ya siffanta shi ne a ce imamanci ya kasance a cikin wasu jama’u na musamman ban da kuraishawa, kuma wannan ne abin da Kanduzi ya fada a cikin Yanabi’ul muwadda a inda ya ambaci cewa wannan maganar da Manzon Allah (s.a.w) ya fada ita ce: “Dukkanin su daga banu Hashim su ke”.
A yayani da ya bayyana a sarari cewa fassarar da aka yiwa hadisin imamai goma sha biyu a bisa bada labarin abin da zai zo nana gaba kuskure ce, ta bangare na farko, da kuma ingancin tafsirin wannan hadisi a bisa akida ta daya bangaren na biyu, da kuma tabbatuwar sunan Imam Mahdi (a.s) a cikin jerin sunayen Imaman Ahlulbaiti (a.s) da kasancewar sa shi ne Imami na sha biyu wanda Allah Ta'ala zai kawa gyara a duniya da shi bayan da ta cika da barna ta bangare na uku, ba wata dama ta yin shakku da ta saura a cikin tabbatar fahimtar nan ta akida kan lamarin mahdawiyyanci wanda makarantar Ahlulbaiti (a.s) ta dage kuma ta tsayu a kai.
Wannan damfararar alakar da ke tsakanin mas’alar Imamai sha biyu da kuma mahdawiyyanci zai iya kai ga ya fitar da tabbatunutu sakamako guda uku ga mahadawiyyanci kamar yanda muka gani a sarari a wannan binciken.
Hakika gazawar fassarar abin da zai zo a nan gaba kan imamacin immai goma sha biyu daga karshe hakan na nufin cewa fassara mahadawaiiyanci kan abin da zai zo nana gaba kuskure ne, ta yanda tabbas makarantar halifofi ta sanya fassara hadisin Imamai sha biyu a matsayin bada labare ne don ta zama ta riga ta gama tabbatar da ingancin abin da ya Faru a sakifa da kuma lamarin halifofi da cewa lamarin ya yi daidai a shari’a, kamar yanda ta ga cewa babau makawa sai ta karkatar da mas’alar mahdawiyyanci zuwa bangaren fassarar abin da zai zo nana gaba don ta gujewa tabbatar da imamancin Ahlulbaiti (a.s) da kuma rashin shar’ancin tsarin halifofi, kamar yanda tabbatar da ingancin tafsirin akida ga hadisin Imamai goma sha biyu shi ne daidai, daga karshe yana nufin tabbatar kasancewa fahimtar nan ta akida kan mas’alar mahdawiyyanci ita ce daidai.