Ta biyu:-
marahalar tabbatar da tabbatuwar hakan a aikace dangane da Imam Mahdi (a.s)
Kuma bincike a wannan marhalar zai kasance ta hanya biyu:
Ta hanyar akida. 2- Ta hanyar tarihi
Ta Daya:-
HANYAR AKIDA:
Tabbatar da ita zai yiwu da bayanai guda uku:
Hakika wannan kebantar na suna daga cikin abubuwa na ba kamawa wajen fahimtar Mahdi (a.s) a wajen Ahlulbait, domin tabbatar wannan fahimtar - kamar yadda ya gabata - lamari ne da yake dauke da tabbatacen dalili, yankanke, kuma hakan na bayyana bacin waninsa, kuma a dabi’ance wannan yana kai mu zuwa ga kudurcewa da fakuwar limami na goma sha biyu. Kuma muddin limamai goma sha biyu ne kadai, sannan ayyanannu ne a wajen Allah Madaukaki, haka kuma - ya tabbata cewa - ba gudummawar mtuane a cikin zabinsu, to ba wani abu a kanmu face kudurce ci gaban rayuwar limami na sha biyu da tabbatar rayuwarsa sa a kamar sauran ‘yan’adam da kuma cewa zai bayyana bayan haka a zagaye na karshe daga rayuwar mutane, sannan a dabi’ance baya yiwuwa ga mutumin da ake kaddara masa irin wannan hadafin, ake kuma kaddara masa wannan doguwar rayuwar, ya zamana ya yi ta a bayyane!, ba makawa sai dai ya yi ta a boye, yana mai buya da fakuwa daga idanuwa, sai dai idan da za a kaddara rasuwar Imam Mahdi a tsawon lokaci na dabi’a kamar sauran mutane, sannan kuma ya dawo duniya ya sake wata sabuwar rayuwa a lokacin da zai bayyana, illa iyaka kuma hakika kaddara faruwar hakan na lazimta yankewar hujja a wani lokaci mai rabewa daga mutuwarsa zuwa bayyanarsa. Kuma wannan ya sabawa Hadisin Saklaini wanda ya yi nuni bisa lazimtar littafi da (Itra) Ahlulbaiti (a.s), da rashin rabuwarsu a cikin wani zamani daga zamuna har tashin kiyama da gangarawarsu zuwa tafkin - kausara -, kamar yadda hakan yake wajabta yin kuduri da (raja’a) wato komen Imam Mahdi (a.s) zuwa rayuwa bayan mutuwarsa, alhali ba wanda ya fadi wannan daga cikin Musulmai.
Ruwayoyin da suka yi nuni bisa siffantuwar Imam Mahdi (a.s) da fakuwa, kuma hakika wasu daga cikin littattafan Sunan sun ambace su misalin: Yanabi’ul Mawadda da Fara’idus Simdain.
A cikin Yanabi’u daga littafin Fara’idus Sumdaini daga Bakir daga babansa daga kakansa daga Ali (AS) ya ce: Manzon Alalh (SAW) ya ce: “ Mahdi daga ‘ya’yana yake, da sannu zai faku daga idanun mutane, idan kuma ya bayyana da sannu zai ciki kasa da daidaito da adalci kamar yadda aka cika ta da danniya da zalunci”. [83]
Kuma a cikinsa dai daga Fara’id an karbo daga Sa’idu dan Jubair daga dan Abbas Allah ya yarda da su ya ce: Manzon Allah (SAWW) ya ce: “Lallai Aliyu shi ne wanda na yi wa wasiyya, kuma daga ‘ya’yansa akwai tsayayye abin saurane Mahdi zai cika kasa da daidaito da adalci kamar yadda aka cika ta da keta da zalunci, na rantse da wanda ya aiko ni da gaskiya ina mai bushara da gargadi lallai wadanda suka tabbata kan imani da imamancinsa a lokacin fakuwarsa su suka fi daukaka fiye da jar wuta”, ma’ana wuta mai ci ganga-ganga”. Sai Jabir dan Abdullahi ya tashi zuwa gare shi, sai ya ce: Ya Manzon Allah, tsayayye daga ‘ya’yanka zai buya? Ya ce: “Kwarai na rantse da Allah domin Allah ya tsamar da masu imani ya shafe kafirai”. Sannan ya ce: “Ya Jabir, lallai wannan wani lamari ne daga Allah kuma sirri ne daga Allah ahir ka yi kokwanto domin kokwanto a cikin almarin Allah mai girma da buwaya kafirci ne”.
Ya kuma zuwa a cikinsa a shafin da aka ambata daga Hasan dan Khalid ya ce: Aliyu dan Musa Rida ya ce: Hakika na hudu daga ‘ya’yana dan shugabar mata ne, da shi Allah zai tsarkake kasa daga dukkan keta da zalunci shi ne wanda mutane za su yi shakka a cikin haihuwarsa kuma shi ne ma’abocin fakuwa, to kuma idan ya bayyana kasa za ta haskaka da hasken Ubangijinta”. [84]
A cikinsa dai, daga Ahmad dan Ziyad daga Da’abil dan Aliyyu Bakhuza’e a cikin labarin zuwansa wajen Imam Ridha (a.s) da kuma kasidarsa da ya rera mai (kafiayr) ta, zuwa inda ya ce: “Imami a bayana (shi ne) da na Muhammad bayansa dansa Aliyyu bayan Aliyyu sai dansa Hassan bayan Hasan sai dansa Hujja tsayayye kuma shi ne abin sauraro a cikin fakuwarsa kuma abin yi wa bayayya a lokacin bayyanarsa, zai cika kasa da adalci bayan ta cika da zalunci, amma yaushe zai tsaya? Wannan labari ne na lokaci, hakika babana ya bani labari daga iyayensa daga Manzon Allah (SAWW) ya ce: “Misalinsa kamar misalin alkiyama ce ba za ta zo muku ba sai katsahan”. [85]
An samo daga cikinsa dai daga littafin Gayatul Maram daga Jabir dan Abdullahi ya daukaka shi: “Mahdi daga ‘ya’yana yake sunansa suna na alkunyarsa alkunyata, mafi kamar mutane da ni a halitta da dabi’a, fakuwa za ta kasance gare shi da dimuwar da al’umm za su bata a cikin ta yana gabatowa kamar tuararo mai haske zai cika kasa da adalci kamar yadda aka cikata da zalunci”.
A cikinsa, daga fara’idul simdaini a shafin da aka ambata a cikin fara’idul simdaini a cikin sahifar da aka mabata daga Bakir (a.s) daga iyayensa daga Ali (a.s) ya yi rafa’in hadisin cewa: “Mahadi (a.s) daga cikin ‘ya’yana yake fakuwa zata kasance a gare shi da dimuwar da al’ummu zasu bace a cikinta - har zuwa inda ya ce - kuma zai cika duniya da adalci kamar yadda ta cika da danniya da zalunci” [86]
A cikin sa daga manakib daga Abi Ja'afar Muhammad dan Bakir (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce farin ciki ya tabbaata ga wanda ya riski tsayeyyen alayen gida na kuma yana mai yin koyi da shi a lokacin fakuwarsa kafin tsayawarsa kuma yana yin biyayya ga waliyensa kuma yana kin makiyansa wadannan su ne abokai na ma’abota soyayya ta mafi karamcin al’umma ta ranar alkaiyama.
A cikinsa an karbo daga abi basir daga Sadik Ja'afar dan Muhammad daga iyayensa daga shugaban muminai ya ce Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Mahdi (a.s) daga cikin ‘ya’yana yake sunansa irin nawa alkunyarsa ma irin tawa kuma shi ne mafi kamanceceniyar mutane da ni a halitta da halayya zai faku kuma mutane zasu shiga rudani har sai mutane sun bata sun bar addininsu a wannan lokacin sai tauraro mai haske zai gabato ya cika duniya da adalci kamar yadda ta cika da zalunci da danniya”. A cikin littafin akwai irin wannan Hadisin, sai dai shi ya ce: “A sannan ne zai gabato kamar tauraro mai haske ya zo da ajiye-ajiyen Annabawa (AS)... ka karanta Hadisin. [87]
A cikinsa a shafi na 494 daga gare shi daga Jabir dan Yazid Baju’ufe ya ce: Na ji Jabir dan Abdullahil Ansari yana cewa: Manzon Allah ya ce da ni: “Ya Jabir lallai wasiyyaina kuma shugabannin Musulmi a bayana na farkonsu Aliyu ne sai Hassan, sai Husaini sai dansa Aliyu sannan Muhammad dan Ali wanda aka sani da Bakir da za ka riske shi kai Jabir, idan ka hadu da shi ka gaishe min da shi, sannan Ja’afar d an Muhammad sannan Musa dan Ja’afar sannan Aliyyu dan Musa sannan Muhammad dan Ali, sannan Aliyu dan Muhammad sannan Hasan dan Ali, sai tsayayye, sunansa sunana, alkunyarsa alkunyata dan Hasan dan Ali wanda Allah Madaukaki zai bude gabashi da yammacin kasa a hannunsa, shi ne wanda z ai buya ga barin masoyansa buyan da ba mai tabbata a kan fadi da imamancinsa sai wanda Allah ya cika zuciyarsa da imani”.
Idan Mahdi (a.s) bai kasance Imami ma’asumi ba, ya kasance gamagarin mutum daga gamagarin Musulmi, to zai zama ba wata alaka tsakaninsa da bayyanar Masihu (a.s) tare da shi, domin shi yana daga Ulul Azmi, balle ya karfafa Mahdi (a.s) ya kira Kiristoci zuwa ga yin imani ga Annabcin Annabi (s.a.w). To ba makawa Imam Mahdi ya zamo ma’asumi, tun da shi Imamanci ba abu ne da yake karbar da’awa ba, abu ne da yake bukatar ayyanawa daga sama da nassin Annabi da zai bayyanata, kuma wannan bai gudana ga wasun imamai sha biyu ba, hakika wafatin Imaman da suka gabata tare da bunne jukkunansu a sanannun gurare abu ne da ya tabata, kuma imami na sha biyu ya yi saura ba a san mutuwarsa ba har yanzu. To ke nan ba makawa da yin kuduri da ci gaban rayuwar wannan imamin daga haihuwarsa zuwa lokacin bayyanarsa a karshe zamani, domin ya cancanci karfafawar Annabi Isah gare shi.
Shari f i mai girma Sayyid sami Albada r i yana fada game da haka:
“Hakika bayyanar Isah za ta kasance tana da bukatuwa zuwa ga faffadar masaniya da ilimi da jagoranci karkashin Mahdi (a.s) bisa la’akari da cewa shi Annabi Isa (a.s) mai yin shaida ne gare shi kuma mai temakawa ne wajen isar da sakon da zai daga muryarsa da shi da littafinsa kuma mai yin biyayya ne a gare shi. Shi Mahdi (a.s) a bisa surantawar ‘yan Sunna ba shi da damar da zai iya mamaye Isa (a.s), (ma’ana ya zama a karkashinsa) kai ba ma shi da damar da zai iya mamaye wasu daga kungiyoyin Musulmi.
Su - suna ganin - sam ba shi da ikon mamaye Isah, domin shi Isa Annabi ne Ma’asumi abin karfafawa da Mu’ujizozi, misalinsa kuwa ba zai yiwa wani mutum ya doru a kansa ba alhali ba a karfafa shi da mu’ujizozi da isma da cikakken ilimi ba.
Ba zai kasance mai iko bisa doruwa akan
dukkan Musulmi ba ba tare da karfafawarw Ubangiji da mu’ujizozi da isma da kuma cikakken ilimi ba. [88]
Ta biyu: HANYA TA TARIHI:
Zai yiwu mu tabbatar da ita da bayanai guda uku:
Lallai tarihi - kamar yadda ya gabata - ya shaida da haihuwar Imam Mahdi (a.s) be kuma ba da shaida kan rasuwarsa ba, wanda hakan yana yin nuni bisa ci gaban rayuwarsa to tun da ba mu ganin Mahdi (a.s), kuma ba ma kebance wani mutum daga mutane da sunan cewar shi ne Mahdi (a.s) dan Imam Hasan Askari (a.s) ba, to ba makawa yana raye ba tare da bayyana ga mutane ba.
Hakika tarihi ya shaida da faruwar wasu abubuwa a fili wadanda suka maimaitu ga Imam Mahdi a zamanin fakuwarsa, har an wallafa littattafai a kan wannan kamar littafin (Tabsiratul Wali fi man ra’al Ka’imil Mahdi (a.s)) na sayyid Hashimil Bahrami, kuma Sheikh Abu Dalibil Jalili Attabrizi a cikin littafinsa [89]
ya ambaci mutum 266 a littafinsa daga wadanda suka ga Imam Mahdi (a.s) a karamar fakuwarsa tare da ambaton kissoshin mafi yawan su, kuma ya kebance fasali ga wadanda suka gan shi a babbar fakuwa, sannan ya ambaci littafi ishirin da wasu su suka rubuta, a cikinsu akwai kissoshi da labaran tarihi game da haka, to yanzu za mu ambaci wata kissa da Sayyid Sadruddin Assadar ya kawo ta a cikin littafinsa (Almahdi (a.s) ) ya ciro ta daga Shaikh Abdulwahhab as-Sha’arani a littafinsa (Dabakatul Urafa) fi Ahwalish Shekh Hasan Iraki: (game da wasu halaye na Sheikh Hasan Iraki):
Ya ce: “Na yi kaikawon zuwa wajensa tare shugabana Abil Abbas Alhuraisi, sai ya ce: Shin za ka yi min izini in ba ka labari na daga farko lamari na zuwa wannan lokacin tamkar kai abokina ne na yarinta? Sai na ce da shi: E, sai ya ce: Na kasance saurayi a Damashk, ina yin sana’a, mun kasance muna haduwa ranar Juma’a a wajen da ake wasa da wargi da shan giya, sai fadakarwa daga Allah ta zo min wata rana da cewar shin dan wannan aka halicce ni?! Sai na bar su a kan abin da suke na gudu daga gare su, sai suka biyo bayana ba su same ni ba, sai na shiga wani masallaci na Umawiyyawa, na samu wani mutum yana magana a kan kujera game da sha’anin Mahdi (a.s), sai na yi tsananin begen haduwa da shi, na zamo bana yin wata sujjada face sai na roki Allah madaukaki da ya hada ni da shi, to a wani dare bayan sallar Magariba ina yin sallar sunna, sai ga wani mutum ya zauna a bayana ya shafi kafadata, sannan ya ce da ni: Allah ya amsa addu’arka dana! Me ke damunka? ni ne Mahdi (a.s). Sai na ce: Za ka tafi tare da ni zuwa gida? Ya ce: Eh, sai ya tafi tare da ni kuma ya ce: Ka ware min kebantaccen wajen da zan zauna, sai na kebe masa wani waje sai ya zauna a waje na har yini bakwai da dararensu”. [90]
Kuma Sheikh Aliyyu dan Isah al’arbili ya fada a cikin Kashful Gumma: Hakika mtuane suna ciro kissoshi da labarai game da abubuwan keta al’adar suka faru a hannun Imam Mahdi (a.s), wadanda bayanin su na da tsayi, kuma zan ambaci kissoshi biyu daga wadannan abubuwan ban mamaki wadanda suka faru kurkusa a zamani na kuma wasu mutane suka ba ni labari daga cikin amintattun ‘yan’uwana.
KISSA TA FARKO: Ya kasance a wani gari mai suna Hilla tsakanin Furatu da Dijla akwai wani mutum sunansa Isma’il dan Hasan, ya ce: Ya ku ‘ya’uwana Isma’il ya fada mana cewa; wata rana ya fita daga gida yana fama da ciwo mai zubar rowan sirkami a cinyarsa ta hagu girman ciwon dake kafarsa ya kai [91]
gwargwadon jinkin hannun daya, sai likitoci suka kasa maganinsa, sai ya zo Bagadaza ya ga likitoci, sai suka ce: Ba maganin wannan ciwon, sai ya fuskanci Samurra ya ziyarci Imamai biyu Ali Alhadi da Hasan Askari, ya roki Allah Madaukaki da kaskan da kai, kuma ya nemi taimako daga Imam Mahdi, sannan ya koma Dijla, sai ya yi wanka ya sa tufafinsa, sai ya ga wasu mahaya su hudu suna hanyarsu ta fito ta kofar katangar birnin garin, dayan dattijo ne yana rike da mashi a hannunsa da wani saurayi sanye da wata riga mai kaloli, shi wannan mai mashin na dama da hanya, sai wasu samari biyu a hagun hanyar, wannan saurayin mai riga kuwa na tsakiyar hanya, sai mai rigar ya ce masa: Kai gobe za ka koma zuwa iyalanka, sai ya ce da shi: To, sai mai rigar ya ce; Matso kusa in ga ciwonka, sai ya matso kusa da shi, sai ya miko hannunsa ya matse masa ruwan ciwon da hannunsa har ya yi masa fami, sannan ya koma ya daidaita a kan sirdinsa, sai tsohon mai mashin nan ya ce: Ka rabauta kai Isma’il, wannan fa Imam (a.s) ne, sannan suka tafi sai ya tafi tare da su, sai Imam ya ce: Koma sai ya ce: Ba zan rabu da kai ba har abada, sai Imam (a.s) ya ce: Akwai maslaha a komawarka, sai ya ce: Ba zan rabu da kai ba har abada, sai dattijon ya ce: Kai Isma’il ba ka ji kunya ba! Imam (a.s) yana cewa da kai koma har sau biyu kana saba masa! Sai ya tsaya sai Imam ya dan yi ‘yan taku zuwa gare shi, sannan ya ce: Ya Isma’il idan ka isa Bagadaza ba makawa baban Ja’afar zai neme ka, yana nufin Khalifa Muntasir Billah, idan ka je wajensa ya baka wani abu kar ka karba, kuma ka ce da yaron mu Rida ya rubuta maka zuwa ga Aliyyu dan Awadha domin ni na yi masa wasiyya ya baka abin da kake so, sannan ya tafi tare da mutanensa, be gushe a tsaye yana kallonsu ba har suka faku, sannan ya zauna a dandariyar kasa zuwa wani dan lokaci yana cikin damuwa da bacin rai yana kuke saboda rabuwa da su, sannan ya zo Samurra sai mutane suka hadu a gefensa, suka ce: Mun ga fuskarka ta canja mai ya same ka? Sai ya ce: Shin kun san wadannan mahayan da suka fita daga gari suka wuce ta gefen ruwa? Suka ce: Ai wasu manyan mutane ne ma’abota tarin dabbobi, sai ya ce da su: A’a, Imam (a.s) ne da mutanensa, saurayin nan mai babbar riga shi ne Imam (a.s) ya shafe ni da yardajjen hannunsa mai albarka, sai suka ce: Nuna mana sai ya yaye cinyarsa ba su ga ko da alamar ciwon ba. Sai suka mutsuttsuka tufafinsa saboda shafa suka shigar da shi wata taska suka hana ganinsa don kar su taru a kansa, sannan mai sa ido (wakili) ta bangaren Halifa ya zo taskas ya tambaye shi game da wannan labarin da sunansa da nasabarsa da kasarsa da kuma fitowarsa daga Bagdaza a farkon wannan satin sannan ya tafi ya bar shi. Sai Isma’il ya kwana a taskas ya yi sallar Asubah ya fita tare da mtuane har ya nisanci Samurra sai mutanen suka yi bankwana suka dawo, ya zamo shi kadai har ya isa wani guri, sai ya ga wasu mutane sun taru a wata tsohuwar gada suna tambayar duk wanda ya zo wucewa kan sunansa da nasabarsa da kuma daga inda yake, yayin da suka hadu da shi sai suka gane shi da alamomin da aka ambata suka cukurkuda rigarsa suka dauketa dan neman albarka, to dama wakilin Halifan ya rubuta zuwa Bagdaza ya sanar da su halin da ake ciki. Sai wazirin ya nemi Sa’idu Rid h iyyuddin da ya sanar da shi gaskiyar labarin. Sai Radhiyyiddin ya fita - wanda dama ya kasance yana daga cikin abokan Isma’il kuma shi ya sauke shi a gidansa kafin fitar sa Samurra, lokacin da Ridhiyyiddin ya gan shi da jama’a tare da shi, sai suka sauka daga dabbobinsu ya nuna musu cinyarsa ba su ga komai ba, nan take Ridhiyiddin ya suma, sananan ya rike hannunsa ya shigar da shi wajen waziri yana kuka kuma yana cewa: Wannan dan’uwa na ne kuma mafi kusancin mutane zuwa zuciyata, waziri ya tambaye shi kissar sa, shi kuma ya hakaito ta gare shi, sai waziri ya kawo likitocin nan da suka ga cuwonsa (suka duba shi), ya tambaye su yaushe kuka gan shi suka ce tun kwana goma, sai waziri ya yaye cinyar Isma’il babu wata alama, suka ce: Wannan aikin Masihu ne, sai wazirin ya ce; Mu mun san wanda ya aikata sannan waziri ya kai shi wajen Halifa shi ma ya tambaye shi kissar sai ya hakaito masa abin da ya gudana sai ya ba shi dinare dubu, sai ya ce: Ba ni da damar karba ko da kwayar zarra daga cikinta. Sai Halifan ya ce: Wa kake jin tsoro? Sai ya ce: Wanda ya yi min wannan ya ce min: kar ka karbi komai daga baban Ja’afar. Sai Halifa ya yi kuka, sannan Ali dan Isa ya ce: Na kasance ina hakaito wanann kissar ga wasu mutane dake waje na, sai ya kasance a wajen akwai Shamsuddin dansa, ni kuma ban san shi ba, sai ya ce: Ni dansa ne na tsatsonsa, sai na ce: Shin ka ga cinyar babanka a lokacin da take da ciwo? Sai ya ce: Ni karamin yaro ne a lokacin da yake da ciwon cinya, sai dai na ji kissar a wajen babana da babata da makusanta na da makota kuma na ga cinyar bayan ta gyaru ba wata alama a jiki har ma gashi ya tsuro a gurin. Ya kuma cewa: Na tambayi Sayyid Safiyyiddin Muhammad dan Muhammad da Najmuddin Haidar dan Aisar, ya ba ni labari kan ingancin wannan kissar kuma su sun ga Isma’il a lokacin da yake da cutar da kuma sa’adda ta warke, kuma dansa ya hakaito min cewar babansa ya je Samurra bayan warakarsa sau arba’in don kwadayin lokacin da zai sake ganinsa ya zo masa.
KISSA TA BIYU:
Assayidul Baki dan Udwa Al’alawi Alhasani ya hakaito min cewa; babansu Udwahu bai yadda da samuwar Imam Muhammadul Mahdi ba,yana
cewa; Idan ya zo ya warkar da ni daga wannan rashin lafiyar na gaskata zancen su? Yana maimaita wannan zancen to a wani lokaci mun taru a lokacin isha na karshe, sai baban mu ya yi kururuwa sai muka zo masa cikin gaggawa sai ya ce: Ku riski Mahdi a yanzu ya fita daga wajena, sai muka fita ba mu ga kowa ba, sai muka dawo masa ya ce: Wani mutum ne ya shigo min ya ce: Ya Udwa sai na ce: Labbaika, ya ce: Ni ne Mahdi (a.s) na zo gare ka ne don in warkar da cutarka, sannan ya mika hannunsa mai albarka ya matsa saman cinyata ya tafi, sai ya fita sannan ya bace bat kai ka ce barewa, Aliyyu dan Isah ya ce: Na tambayi wani kan wannan kissar ba a wajen dansa ba, sai ya tabbatar min da ita. [92]
Daga nan ne wasu daga manyan masana na sunna Imani da rayuwarsa da wanzuwarsa har ma ya dauwama a zantuttukansa. Hakika Sayyid Sadruddin ya ambaci wasunsu, ya ce: Daga cikinsu akakwai Sheikh Muhyiddin ibnul Arabi a cikin Futuhat bisa riwayar sheikh Abdulwahhab Ash’arani a littafinsa Alyawakit wal Jawahir wanda ya watsu sosai ya ciro shi daga littafin (Is’afur Ragibin), ba kuma na zaton zai yadda a jingina masa zaton wasu mtuane ba tare da ya tababtar ba.
Daga cikinsu akwai shi Shehu Abdulwahhab Assha’arani a littafinsa (Alyawakit fil Jawahir) bisa abin da ke cikin Is’afur Ragibin a in da ya ce: Mahdi (a.s) da Imam Askari haihwuarsa ranar tsakiyar daga Sha’aban shekara ta 255 kuma yana nan a raye har sai ya hadu da Isa dan Maryam, haka Shehu Hasanun Iraki ya ba ni labari dangane da Imam Mahdi (a.s) yayin da ya hadu da shi kuma Sayyid Aliyyul Khauwas ya dace da shi bisa haka. [93]
Daga cikin su akwai Shehu Abdullahi Muhammad dan Yusuf dan Muhammadul Kanji a littafinsa (Albayan fi Akhbari Sahibiz Zaman) bisa abin da Is’afur Ragibin ya nakalto, ya ce: Daga dalilai a kan cewar Mahdi na raye wanzajje bayan gaibarsa har zuwa yanzu, da kuma cewar ba abin da zai hana wanzuwarsa; wanzuwar isa dan Maryam, da Khidr, da Ilyas daga waliyyan Allah Madaukaki, da kuma wanzuwawr Dujal mai ido daya da Iblis la’ananne daga makiyan Allah, wadannan wanzuwarsu ta tabbata a littafi da Sunnah. [94]
Daga cikinsu dai akwai: AL Shaikhul Ariful Fadilul Khojihu Muhammad Barisa a littafinsa (Faslul Khidab) bisa abin da ke cikin Yanabi’l Mawadda bayan ya ambaci haihuwar Mahdi da kuma cewar Allah Madaukaki ya ba shi hikma da rarrabe zance tun yana karami, kamar yadda ya yi baiwa ga Yahya da Isa ga wannan, ya ce: Kuma Allah Madaukaki ya tsawaita rayuwarsa kamar yadda ya tsawaira rayuwar Khidir (a.s). [95]
Daga cikinsu akwai Sheikh Sadruddin Alkaunawi a cikin sashen wasiyyoyinsa ga dalibansa yayin rasuwarsa bisa abin da ke cikin Yanabi’ul Mawadda, a inda ya ce: Hakika littattafan da ke wajena daga littafan dibbu da littafan masu hikima da na falsafa, to ku sayar da su ku yi sadaka da kudinsu ga mabukata, amma littafan tafsiri da hadisu da na sufanci to ku kula da su a dakin littattafai, ku karanta kalmar tauhidi (La’ilaha Illallahu) dubu saba’in a wannan daren ku isar da gaisuwa daga gare ni zuwa ga Mahdi (a.s) [96]
Na ce: Zai yiwu a ce wannan fadin na sa baya nuni bisa samuwar Mahdi da rayuwarsa domin ta yiwu ya fadi haka ne, da kaunar ya riski bayyanarsa, sai dai na farkon ya fi bayyana.
Daga cikin su akwai Sheikh Sa’aduddini Alhamwi bisa abin da ke cikin Yanabi’ul Mawadda, yana cirowa daga littafin Sheikh Aziz dan Muhammadun Nafsi, yayin zancen sa a cikin jeranta waliyyai: Hakika Allah Madaukaki ya zabi waliyyai sha biyu a cikin wnanan al’ummar daga Ahlulbaiti ya sanya su halifofin Annabinsa mai girma, har ya ce: Amma karshen waliyyan wanda shi ne karshen halifofin Annabi kuma majibincin lamari na ga sha biyu cikamakin waliyyan, shi ne Mahdi ma’abocin zamani. [97]
Daga cikinsu: Sheikh Shihabuddini Alhindi wanda aka sani da Sarkin Malamai a littafin (Hidayatus Su’ada ala ma fiddurarul Musawiyya) ya fada yayin ambatonsa ga Imamai sha biyu, shi ya faku yana da rayuwa mai tsayi kamar yadda yake ga wadannan muminan, Isa da Ilyas da Khidir da kuma wadannan kafiran Dujal da Samiri.
Daga cikinsu akwai ba daya daga masu falala da masana, domin abin nan da yake bayyana daga wakokinsu na Arabiyya da Farisanci wadanda aka ambata a Yanabi’ul Mawadda da waninsa daga sashen littafan manakib (darajoji), cewa suna ganin rayuwar imam Mahdi (a.s) abin sauraro kuma shi rayayyae ne ana azurta shi saboda siffata shi da ya yi da wulaya da imamanci da halifanci da wakilcin Annabi Muhammadu (s.a.w) kuma lalle shi ne wasidan kwararo baiwar Ubangiji”. [98]
c- A tabbatar da bayani na uku mun dogara da abin da sayyid shahid Muhammad Bakir ya rubuta a inda yake cewa: “hakika fakuwa gwaji ne da al’ummu suka rayu da ita da ta kai nisan kusan shekar saba’in wacce ita ce fatarar fakuwa ta farko, domin mu bayyana hakan, zamu yi shimfida don gabatar da fikira takaitacciya kan gajeriyar fakuwa”. [99]
hakika gajeriyar fakuwa ta kasance a matsayin mataki na farko a lokacin imamancin tsayayye abin sauraro amincin Allah Ta'ala ya tabbata a gare shi hakika an kaddarwa wannan imamamin tun lokacin da ya karbi imamanci al’umma da ya buya daga idanuwan mutane ya wanzu yana mai nesantar da sunansa daga abubuwan da suke faruwa, ko da kuwa ya kasance yana kusa da abubuwan da zuciyarsa da hankalinsa, hakika an lura cewa lalle wannan fakuwar idan ta faru katsaham zata haifar da bugawar kwakwalwa kan tsarin zamantakewar a’imma a cikin al’ummara musulmi, saboda wadannan tsare-tsaren da aka saba tafiya a kansu na saduwa da Imam a ko wane lokaci, da kuma yin alaka da shi da komawa zuwa gare shi don warware matsaloli mabanbanta, idan Imam ya faku daga shi‘arsa katsaham kuma suka yi tsammanin cewa shagabancinsa na ruhi da tunani ya yanke, wannan fakuwar [100]
zata sabbaba babban ba zato ba tsammani a inda ba ‘a tsammace shi ba kuma wannan zai iya tarwatsa samuwar shi’anci baki dayanta kuma ya daidaita haduwarsa, sai ya zama ba makawa da ayi wa wannan fakuwar shimfida, don wadanna mutanen su saba da ita a hankali, kuma yanayin ya samar da kansa a hankali a hankali kan tushensa, kuma wannan shinfidar ta kasance ita ce: yin gajeriyar fakuwa wacce Imam Mahdi (a.s) ya buya a cikinta daga idanun mutane, duk da cewa ya kasance a ko da yaushe yana da alaka da jiga-jigan mabiyansa da shi’arsa da wakilansa da na’ibai da amintattunsa, daga sahabbansa Wadanda suka a matsayin igiyar sadarwa tsakaninsa da mutane muminan da suka yi imani da tafarkin imamamnci [101]
Hakika tsanin da ke tsakanin mutane da imam a wannan lokacin ya kasance ta hanyar mutum hudu wadanda su wadannan wakilan sun hadu a kan tsoron Allah, kuma masu tsantseni ne kuma masu tsarki a lokacin rayuawrsu, ga su kamar haka:
Usman dan Sa’idul A mri.
Muhammad dan Usman dan Sa’idul A mri.
Baban Kasim Husaini dan Ruh.
Baban Hassan Aliyyu dan Muhammadus Samuri.
Hakika wadannan hudun [102]
sun gudanar da mafi muhimmancin wakilci bisa jerantuwar da aka ambata, duk sanda dayansu ya rasu sai dayan ya maye shi a bayansa da ayyunawar Imam Mahdi (a.s).
Me mayewar ya kasance yana haduwa da ‘yan Shi’a ya dauki tambayoyinsu zuwa Imam, ya bijiro da matsalolinsu gare shi ya karbo amsoshin tambayoyin da baki zuwa gare su wani lokacin kuma a rubuce [103]
mafi yawan lokaci, kuma jam’ar da suka rasa ganin imamainsu su na samun damar yin alhini da rarrasar kawukansu ta hanyar wadannan wasikokon da ganawa ba ta kai tsaye ba. kuma na lura cewa dukkan sa hannu da wasikun da suke zuwa daga Imam Mahdi (a.s) da rubutu iri daya ne da tsari daya [104] tsowon wakilcin wakilan nan guda hudu wanda ya kai kusan shekara saba’in, Samurri ya kasance wakili na karshe, ya kuma bayyana karewar lokacin karamar fakuwa wacce ta kebantu da ayyanannun wakilai, daga nan ne babbar fakuwa ta fara wacce ba a samu wasu ayyanannun mutane da za su zamo tsani tsakanin Imam da Shi’a ba, hakika ya bayyana karewar karamar fakuwa da babbar fakuwa tare da tabbatar da karamar fakuwar don burin riskar babbar da karewawr cikin karamar, domin ita - kamar yanda aka ambata a baya - ta kare ‘yan Shi’a ne ta hanyar bin matakai don gudun fadawa karo da jin rauni kewa saboda fakuwar Imam, ta samar da daidaita yanayin ‘yan Shi’a a kan tushen fakuwa, ta yi musu tanadi ta hanyar bin matakai don karbar tunanin wakilcin wasu daga Imam, da wannan ne wakilcin ya juya daga daidaikun kebantattun mutane [105] zuwa tsari na gama-gari. [106]
Shi ne tsarin Mujtahidi adili wanda ya sa n lamuran duniya da na addini, wanda ya dace da canjawar karamar fakuwa zuwa babbar fakuwa.
To yanzu zai yiwu ka auna wannan matakin bisa sakamakaon abin da ya gabata, don ka fahimci cewar Mahdi wata hakika ce da wata al’umma ta rayu da ita, kuma jakadu da na’ibai suka yi bayanin ta tsawon shekara saba’in ta hanyar cudanyarsu da sauran mutane, kuma ba wanda ya shinshini wata alama daga gare su a wannan lokacin mai tsayi cewar suna wasa da kalmomi ne kawai, ko ‘yan dabarbaru ne da nakalto wa mutane karya. Shin za ka iya surantawa - dan Allah - da cewar wata karya za ta iya rayuwar har shekara saba’in har mutum hudu majeranta su rike ta kuma dukkansu sun rayu a kanta, su tabbata a kan tushenta, suna cudanya da mtuane a matsayin abin da za su rayu da shi a kawukansu su rika ganinsa a idanuwansu, ba tare da wani abu ya shige su na kokwanto ba, har ma ya zamana akwai wata kebantacciyar alaka tsakanin wadannan mutum hudun ta yin imani da wannan kadiyyas da suke da’awar cewa suna tare da ita kuma suna rayuwa dai ta?!
Hakika tun da ana cewa; Igiyar karya gajeriya ce, kuma zance na gaskiya na tabbatar da cewa ba zai taba yiyuwa a aikace a lissafin na hankali karya ta rayu da irin wannan yanayin da kuma tsahon wannan lokacin, ba tare da wadannan alakokin ta hanyar karbar sako da bayarwa sannan ta samar da amincewa ga dukkan wadanda ke kewaye da ita.
Haka nan za mu ga cewar zahirin karamar fakuwa zai yiwu mu yi la’akari da ita a matsayinta na ilimi da aka sani kuma mai yiyuwa a aikice bisa gwaji don tabbatar da cewa aba ce mai afkuwa, don ganin an sallamawa Imami jagora (a.s) , ta hanyar haihuwarsa da rayuwarsa da fakuwarsa, [107]
da kuma gamammiyar sanarwa da shelar da ya yi game da babbar fakuwa wacce ya buya, ya tabbatar da ita ta fuskar rashin fitowa fili ya bayana kansa ga kowa[108] ”. [109]