Ziyarar Kabarin Manzo A Mahangar Kur’ani Da Sunna
A: A Mahangar Kur’ani Maigirma
Kur’ani mai girma yana bai wa al'ummar musulmi umarni da su je wajen manzo su nemi gafararsa sannan su nemi manzo (S.A.W) don ya nema musu gafarar Allah madaukaki: "Duk lokacin da suka zalunci kawunansu (suka yi zunubi) idan suka zo wajen manzo suka nemi gafara kuma Manzon ya nema musu gafara wajen Allah, lallai Allah mai rahama ne kuma mai karbar tuba. "[32]
A wani wurin ciki Kur’ani Allah madaukaki yana zargin munafukai da cewa duk lokacin da aka neme su da su je wajen ma'aiki don ya nema musu gafara sai su ki: "Idan aka ce musu ko zo manzo ya nema muku gafara, sai su juya fusakunsu (don nuna rashin amincewa) zaka ga suna kin maganarka suna masu nuna girman kai. "[33]
Shehin malamin nan kuma Ahlussunna, Takiyyuddin Subki, Ya yi imani da cewa: Msuslmi a wannan lokacin ma tare da amfani da wannan aya suna iya zuwa wajen manzo su nemi gafararsa kuma Allah ya gafarta musu. Ya kara da cewa duk da yake wannan aya ta shafi lokacin da manzo yake a raye ne, amma neman gafara ta hanyarsa bai kebanta da lokacin da yake a raye ba. Saboda wannan wani matsayi ne wanda aka bai wa manzo (S.A.W) don haka sakamakon rabuwarsa da duniya wannan matsayi ba zai kau ba.
Mai yiwuwa a ce: Wannan abin da ya zo a cikin wannan aya da muka ambata a sama, ya kunshi nuna matsayi da daukaka ta manzo ne kawai, amma aiwatar da wannan ya kebanci lokacin rayuwarsa ne kawai, amma ba lokacin da baya duniya ba, ta yadda alakarmu da shi ta yanke.
Amma wannan magana sam ba abin karba ba ce, domin kuwa dalilan da zamu ambata a nan gaba suna bayyana cewa rasuwar manzo sam ba ta da wani tasiri a kan wannan al'amari, don haka mutuwa da rayuwarsa babu wani bambanci duk daya ne:
1-Mutuwa ba tana nuna karshen dan Adam ba ne, mutuwa wata sabuwar kofa ce don shiga wata sabuwar rayuwa kuma duniyar da duk abin da yake a ckinta ya fi abin da yake a duniyar da ta gabata ga rayuwar dan Adam, saboda haka mutum rayayye ne a waccan duniya yana gani kuma yana ji. Musamman shahidai wadanda bayan sun dandana shahada zasu cigaba da karbar ci da sha daga Allah madaukaki, kuma suna cikin jin dadi na musamman ta hanyar ruhinsu. Saboda haka zamu yi bayani a kan wannan a nan gaba a cikin bahasin rayuwar barzahu.[34]
2-Ya zo da yawa a cikin ruwaya cewa: Salatin da musulmi suke yi wa manzo akwai mala'iku na musamman masu isar da wannan salati zuwa ga manzo (S.A.W) don haka duk inda mutum yake idan ya yi wa manzo salati zai isa zuwa ga manzon. Kamar yadda yake cewa: "Ku yi mani salati, salatin yana isa zuwa gare ni daga duk inda kuke".[35]
3-Musulmi a wajen tahiyar salla an umurce su da su yi wa manzo sallama, sannan su yi masa gaisuwa, "Assalamu alaika ayyuhan nabiyu warahamatullahi wa barakatuhu" Wannan gaisuwa ba wai kawai an umurci musulmi ba ne da su yi ta zuwa ga manzo amma shi ba ya jin abin da suke yi, Manzo yana raye kuma yana sauraren mu lokacin da muke yi masa salati.
Wadannan abubuwan da muka fada a sama suna nuna cewa Manzo yana raye a rayuwar barzahu, sannan yana da alaka da mu kuma yana jin abin da muke yi. Sannan yana jin rokonmu kuma yana biya mana bukatunmu a lokacin da ya dace. Saboda haka a nan ya kamata mu ce wadannan ayoyi da muka yi bayani a sama, Suna da ma'ana mai fadi, saboda haka yanzu ma suna kiranmu da ziyarar manzo a kabarinsa kuma mu nemi gafara kuma ya nema mana gafara ga Allah, sannan mu nemi bukatunmu daga gareshi. Saboda haka ya zo a cikin ziyarar manzo da ake karantawa a haraminsa cewa mai ziyara ya nemi gafarar Allah ta hanyar manzon tare da kula da ma'anar ayar da muka yi bayani a sama. Saboda haka ziyarar manzo ba wani abu ba ne sai kawai yin salati ga manzo da kuma neman bukatu da gafarar Allah ta hanyar mazon. Saboda haka wadannan ayoyi na sama suna iya zama sheda a kan inganci da mustahabbancin ziyarar manzo (S.A.W).
Wata sheda kuma a kan wannan batu shi ne, bayan rasuwar Manzo wani balarabe ya shigo Madina yana karanta wannan aya da muka ambata, sai ya ce: "Na zo wajenka ina mai neman gafara daga zunubaina kuma ina mai neman ceto gareka zuwa ga Ubangijina".[36]
Sannan muhimmin abu kamar yadda Subki yake cewa: Kiran al'ummar musulmi da su ziyarci manzo kuma su nemi gafara da bukatunsu daga gareshi wata alama ce ta karrama manzo da girmama shi. Kuma tabbas wannan girmamawa ba ta kebanci lokacin rayuwarsa ba, saboda girma da mukamin ruhinsa a wajen Allah wani abu ne wanda ba mai shakku a kansa kuma madawwami ne, saboda haka bai kebanta da wani zamani ba sabanin waninsa.
Saboda haka ne malaman Tafisri suka tafi a kan cewa, girmama manzo bai kebanci lokacin rayuwarsa ba, saboda haka dole ne a kiyaye shi har bayan rasuwarsa. Har ma ayar da ke umurta musulmi da su rika magana a hanakali a gaban manzo, tana nan a matsayinta, inda Allah yake cewa: "Ya ku wadanda kuka yi Imani kada ku daga muryarku saman muryar Annabi[37]".
Saboda haka bai kamata mutum ya rika magana da karfi a cikin haramin mazon mai tsaira ba. Sannan wannan aya an rubuta ta a kan kabarin manzo, wanda duk ya je wannan wuri ya gane wa idonsa hakan.
B: A Mahangar Sunna
Mun ga hukunci da matsayin Kur’ani a kan wannan al'amri, yanzu abin da ya rage shi ne ku ga kuma me Sunnar manzo ke cewa a kan hakan..
Ruwayoyi da dama sun zo akan wannan batu na ziyarar kabarin manzo, kuma malamai sun yi kokarin tattara su da kuma tabbatar da danganensu. Saboda haka a nan a matsayin misali zamu kawo wasu daga cikinsu kamar haka:
1-Takiyyuddin subki (ya yi wafati a shekara ta756h) a cikin littafinsa "Shifa'us sikam" ya ruwaito hadisi tare da sanadi ingantacce. [38]
2-Nuruddin Ali bn sahmudi (ya yi wafati 911H) ya ruwaito ruwaya 17 akan wannan batu, a cikin littafinsa na tarihin Madina sannan kuma ya inganta sanadinsa.[39]
3-Muhammad fukki daya daga cikin Malam Azahar tare da shafe sanadi ya ruwaito matanin ruwayoyi 22 a kan ziyarar manzo.[40]
4-Allama Amini tare da tare da bin diddigi wanda ya ci a yaba masa, ya tattara ruwayoyi da dama a kan ziyarar manzo (S.A.W) saboda haka a nan kawai zamu yi nuni da daya daga cikin ruwayoyi da ya samo daga littafi 41 da a ka ruwaito a kan hakan. Al-Gadir
Saboda haka kawo dukkan ruwayoyin da danganensu ba zai yiwu ba a nan, saboda haka kawai a nan zamu takaita ne da kawo wasu kawai daga cikinsu. Wadanda suke son karin bayani sai su koma zuwa littafin da aka ambata a sama.
Hadisi na farko: "Wanda duk ya ziyarci kabarina aljanna ta wajaba a gareshi"[41]. wannan hadisi Allama Amini ya ruwaito shi tare da sanadi daga littafi 41.
Hadisi na biyu: Dabarani a cikin mu'ujamul Kabir, Gazali a cikin ihya'u ulum daga Abdullahi bn umar, Manzo yana cewa: "Duk wanda yazo ziyara kuma saboda kawai ziyarata ya zo, to ya wajaba in cece shi a ranar kiyama. "
Hadisi na uku: Darul Kutni ya ruwaito daga Abdullahi bn umar cewa manzo (S.A.W) ya ce: Duk wanda ya ziyarce ni bayan wafatina a lokacin aikn hajji, to kamar ya ziyarce ni a lokacin da nake a raye. "
Hadisi na hudu: Darul kutni ya ruwaito daga bn Umar cewa manzo (S.A.W) ya ce: "Duk wanda ya ziyarci kabarina kamar ya ziyarce ni a lokacin da nake a raye. " A nan ya kamata mu yi nazarin matsayin ziyara a wajen Imaman Ahlul-bait (A.S)